Breaking News

ZAFIN KAI 95

 *_Arewabooks@Mamuhgee_*

95


ZINNIEE’s SECRET 

(One stop shop for a new sensation)


Kina Neman kamshi mai sanyaya zuciya❓

Shin kina Neman kamshi da dada❓

Ko kuwa kamshi mai ratsa zuciya kikeso❓ko Kayan gyaran jiki kike nema dry skin ne dake ko hard skin tabbas kinzo inda za’a share maki kukan ki 


Tabbas Zinniee’s secret ya gama da damuwarku Ina mata masu aji mace mai aji ai Sai da gyara .tabbas Zinniee’s secret sun gama da damuwarki Hajiya ta.


Zinniee’s secret sun tanadar muku Kaya kamar……

Room freshener 

Toilet spray 

Bed spray 

Dish wash

Mopping mist

Kai har ma da 

Feminine wash

Akwai 

Glowing soup dinmu mai kyau da inganci.

Glowing cream 

Face cream da kuma body scrub 


domin samun dadadan Kayan kamshi.da Kayan gyaran jiki maza garzayo Zinniee’s secret 

Zinniee’s secret DUNIYA ne !!


Zaku iya yi mata magana a wadannan kafafan sadarwar kamar su—IG-@Zinniee’s secret 

TIKTOK@ Zinniee’s secret 

Ko ku tuntube su a wannan number 08080840567  za kuma ku iya mata magana ta hanyar Watsapp da wannan number.

Zinniee’s secret suna nan a kano Hadeaja road Kano state.


Zinniee’s secret one stop shop for a new sensation.


Zinniee’s secret got u covered,a trial will convince you.


********

Bayan tafiyarsa acan gidan Bilal kuwa Bena sanyi jikinta yayi Amma Bata nuna ba sbd tasan saiyayi zazzabi sosai akan yajin tinda cikinsa baya Rena yaji koman qanqantarsa.


Cup din data Basa ice tea din dake ajiye kan dining ta dauka tareda Kaiwa bakinta ahankali tana qarasa shanyewa cikin nutsuwa da sanyin jiki.


Bilal ma kusan sharp sharp yayi Breakfast dinda kusan duka gidan Basuyiba sbd zuwansu D din.


Yana gamawa ya fita tareda sulaiman Dayazo daga nasa masaukin shima suka tafi yakaisa airport ya hau jirgin ticket Daya Siya masa na komawa.


Sumayyah ce ta jawo Anne suka fito itama taci abinci kafin Annen ta koma dakinta tayi wanka ta fito ta shirya cikin Riga da zani na lallausan atampa masu tsada da Bilal ya Siya kaman hauka kala kala aka Dinka matasu da mayafai da hijabs da takalma hardasu komai dai na amfaninta da zata buqata ansiya Wanda momyn Abdul ce da Sumayyah sukaje siyayyan duk da sumayyah Batada sakewa sosai a cikin mutane har lokacin Amma dai a yanzu Datake tareda dukkanin wainda zuciyarta ke tsananin so cikin kwanciyar hankali da samun nutsuwan rayuwa sai tana sakewa da walwalanta sosai musamman Bilal Da akowace daqiqa nuna mata yakeyi itace sarauniyar rayuwarsa,gidansa, dukiyarsa da zuciyarsa.


Ta Wani bangaren Kuma tinda ta dawo hayyacinta babu Wani Abu Daya shiga tsakaninsu sbd sabuwar kunyarsa ta tin asali Datake jinta aciki sosai,

Shi Kansa bayason takura mata sbd ganin se yanzu ne zasuyi rayuwar auren gaske kowannensu Yana cikin hayyaci cikakke da nutsuwarsa Kuma a yanzu ne asalin sonsa Dayake ranta tana cikakkiyar lafiyayyarta zai shigo cikin rayuwar aurensu.


Dan haka Shima Kansa a zaqe yake da son kasancewa da ita a muamalan aure tana cikin nutsuwa da hayyacin kanta.


Cikin rashin kuzari Bena ta koma dakinta Kai tsaye itama toilet ta nufa ta zare kayan jikinta tayo wanka da ruwan zafi ta fito tayi komai ta shirya cikin Riga da skirt na atampa tayi sallah tana idarwa sai kawai ta Yanke shawarar kunna wayarta tinda Wanda aka sakata baro gida da nesanta kanta da kowa akansa yariga ya ganota ya sameta har inda Basu taba tsammanin zai samesun ba.


Faduwa gabanta ya Dan Yi sbd Jin damuwa da baqin cikin damuwar data saka kaantes musamman 'yarta Rabin ranta Amnah da dd babbanta Wanda tasan bayan D shine Wanda ya shiga mafi tashin hankali fiyeda kowa Amma tasan dd babbanta jarumin tsohon ne Hakan bazai sakasa fushi da ita ba.


Kunna wayar tayi Amma taqi tashi Dan haka ta miqe tsaye ahankali ta fito Palo Kai tsaye gurin TV data ga Bilal na saka charging ta nufa ta duba babu charger a gurin ta dawo ta nufi kitchen inda take Jiyo motsinsu sumayyah da momyn Abdul din tana Isa ta Kalli sumayyah dake wanke hannunta tagama blending kayan Miya da momyn Abdul ke koya mata aiki da kayan gidajen masu kudi da kalolin abincinsu sbd su wanda suka iya daban Wanda masu kudi irin su Bilal din da danginsa ke ci daban sbd su Sam basa Wani cin abinci da yaji su kuwa suna Dan ci.


Cikin nutsuwa da sanyi tace sumayyah ta aro mata charger din Yaya Bilal.


Goge hannu sumayyah tayi da towel tana fitowa daga kitchen din tana cewa Bena din su je.


A Palo Bena ta tsaya sumayyah ta nufi palonsa ta wuce bedroom dinsa Kai tsaye ta Ciro mata charger dinsa ta fito ta miqa mata tana tambayarta Kunna wayar zatayi tin yanzu??


Numfashi Bena ta sauke tareda kallan wayar tata dake hannunta cikin sanyi tace


"Eh,zan kunna idan banji Amnah yau ba bazan iya samun nutsuwan zuciyata ba,

Tana can cikin mummunan hali na rashina na sani tabbas,zan kirata na jita ko zan samu relief Nima."


Tana fadan Hakan ta wuce dakinta Dan saka cajin.


Sumayyah kuwa shiru tayi batareda ta dago ta Kalli Bena din ba Jin wadda ta ambata takuma tabbatarda waye Hakan,

Sanyi jikinta yayi tana rasa tinanin Yi akan Amnah wadda ta tabbatarda son da Bena takewa 'yar ko ita data haifeta iyakacinta kenan hakama ta tabbatarda so da kaunar da Amnah din kewa Bena maganar ma a kawo zancen ba itace ta haifeta ba duk be tasoba Dan haka wannan zancen na waye ya haifi Amnah tsakanin ita da Bena tanaga maganar Ababan dai dayace Bena ce uwar data haifeta har abada a Kansa zasu zauna Dan ita kam ta yafewa Bena ita Bata kaunar a tayar da zancen idan har Hakan ze yiyu.


Bena na shiga daki cajin wayarta ta saka tareda zaunawa gefen wayar tana Jin zuciyarta na Dan bugawa da sauri.


Zaman kusan awa Daya tayi wayar ta Dan Sam charging da yawa kafin ta zare ta miqe daga gurin ta koma kan kujera ta zauna tana kunna wayar.


Hoton Annenta ne ya bayyana kan screen din wayar Wanda tayi mata batamasan tai mata shi ba sbd Bata hayyacinta a lokacin, 

Wani nannauyan numfashi me dumi ta sauke ahankali tareda saka password din wayar ta Bude tana kokarin saka numbern Amnah Kiran Amnah din Yana shigowa cikin mamaki ta Kalli wayar taga tabbas Amnah ce me Kiran wasu hawaye ne suka ciko mata Ido sbd ganin 'yarta na can na kiranta duk bayan lokaci Dan kawai ta samu sa'ar samun mummy dinta kaman yanda ta sameta yanxu.


Daga can bangaren kuwa Amnah data saka Kiran Badan ta sakaran yau ma zata sameta tana Jin wayar ta shiga ta tashi daga jikin Zeenah dake kwanta da ita a jikinta tana Aiki a laptop.,


Wani ihun murna ta saki jikinta na rawa sbd ta kasa yarda da Mummyn wayarta ta shiga.


Bena da nata jikin ke rawa itama dauka tayi ahankali tareda ambatar sunan Amnah cikin tsananin kewa da sonta me tsananin gaske.


Amnah Kuka ta fashe dashi me qarfi taba Kiran sunan Mummyn tata.


Zeenah data kasa yarda da gasken Amnah takeyi tanajin ta fashe da kuka tayi gefe da Abinda takeyi tana Hana ashi zaune da sauri ta amsa wayar hannun Amnah tana dubawa taga kira ne da gaske kuwa.


Cikin rawar murya itama ta ambaci sunan Bena din cikin mamaki me yawan gaske.


Bena na Jin Zeenah jikinta ya sake sanyi ta amsa tana rasa abin fada itama sbd hawayen dake sake cika idanuwanta.


Hannuwan Zeenah har rawa sukeyi ta kashe wayar da sauri ta saka videocall sbd sugani idan Bena din ne da gaske kada a yaudaresu.


Bena na ganin an kashe tasan video call zasu mata Dan haka ta kunna Data dinta ko kama Hawa daidai bataiba kiransu ya shigo.


Tana dauka ta bayyana kan screen dinsu take Zeenah itama ta zunduma ihun murna tana Kiran sunan Bena din cikin tsananin farin ciki da murna harma da hawaye duk a lokaci Daya.


Amnah kuwa Kuka takeyi sosai tana kallan fuskan mahaifiyarta datai kewa kaman zata mutu.


Ita kanta Bena farin ciki da sanyin zuciyar ganinsu takeyi Dan haka ta sake sosai tana share hawayenta dasuka gangaro tana kallan Amnah tace


"My baby kiyi hakuri kinji,

Mummy tayi lefi ki yafewa mummy Amma bazan sake ba my love,

Nayi kewankiu..  hawaye ne suka sake gangaro mata ta share tana kallan Amnah da itama ita take kallo babu Abinda takeso bayan ta jita jikin mahaifiyarta ta rungumeta.


Zeenah janyo Amnah tayi jikinta tana shafata tana kallan Bena da duk tayi Wani fayau kaman wadda tayi rashin lafiya a hankali cikin nutsuwa da sanyi Zeenah ta tambayeta tana Ina?

Meyasa ta tafi?

Meya faru?

Tasan Abinda ya faru anan kuwa?

Tasan halinda DD yake ciki na rashinta kuwa?


Shiru Bena tayi tana kasa cewa komai sbd batasan ta inda zata fara ba Dan haka tace tayi hakuri zata sanar da ita komai bayan sun hadu zancen bazeyi ta waya ba.


Kasa shiru Zeenah tayi tafara zayyana mata mummunan halin da D ya shiga sbd rashinta,irin ciwo daya kwanta duk sbd rashin sanin inda take.


Ita kanta Bena tayi ciwo da quncin me tsananin gaske sbd rashinsa din Amma bazata iya fada ba sedai wainda suke tareda ita sune suka fahimci Hakan.


Amnah ce tafara fadawa Bena yanda tayi kewanta da rigimar a yau takeson ta dawo kokuma ta fada inda take a kaita gurinta ita yau takeson ganin mummy dinta.


Rigimarta ce ta ankarar da Umme dake Palo halinda ake ciki itama ganin Bena din yayi mummunan daga hankalinta ta ringa fadan ta fada musu inda take tana murnan DD damuwarsa ta qare inshallah tinda ansamu Bena din a waya.


Hakuri Bena ta Basu da Basu tabbacin tana lafiya Kuma zata dawo Amma Bata fada musu inda take ba sbd Bilal da batasan Tayaya zata fada musu yana Raye ba Kuma tana ganin ba itace ya kamata ta sanar kusu din ba.


Suna gama wayar numfashi da ajiyar zuciya ta sake tareda Kiran wayar dd Kai tsaye tana Jin kewansa na kashe jikinta Shima.


Abbakar ne yaga Kiran nata ya duba dakyau ya tabbatarda Bena kaante ce Dan haka ya Kalli dd babba dake zaune Yana kallan labari sama sama Shima dd babban ganin kallan da Abbakar ke masa ya sakashi kallan wayar Yana tambayar waye me Kiran.


Babu Bata lokaci ya sanar masa Bena kaante ce.


Juyowa dd babba yayi tareda kallan wayar saga sunanta ita dince take Wani sanyi da numfashi me sanyi suka saukar masa ya karbi wyaar tareda dagawa Yana fatan yaji alkhairin ita dince.


Tana Jin muryansa ta kasa riqe kukanta data kasa fasawa kowa shi sai shi,

Kukane mara sauti sosai Dayake fitowa daga qasan zuciyarta na komai da komai ma.


Shiru yayi Yana sauraren kukan nata tsawon mintina kafin ya saauke ajiyan zuciya tareda Bude baki ahankali cikin nutsuwa da manyanci yace


"Ya Isa haka kukan,ya Isa,komai yazo karshe da yardar Allah."


Numfashi taja ahankali tareda share hawayenta da tissue tana dakatar da kukanta.


Cikin kulawa yace


"Kina lafiya dai ko?


Murya a dashe ta amsa da cewan lafiyanta kalau.


"Kina Ina??


"Abuja" ta amsa cikin sanyi tana sake share fuskarta.


Numfashi ya sake saukewa kafin yaci gaba da cewa


"Meyasa biki Neman kin fadamun ba a lokacinda suka koreki??


Ajiyan zuciya ta sake ahankali kafin ta fara masa bayanin komai again tin daga lokacinda ya Gane Safnah da Abinda ya biyo baya duk a ranar Kuma Suma ranar ne suka bar qasar.


Kasa sanar masa tayi da waye ya daukesu sbd batasan Tayaya zata fara isar masa da zancenba Dan haka gwara dai yaji daga D ko Bilal din sbd batasan tsarinsu da suka yankeba.


Cikin nutsuwa da fahimta da kulawa sukai magana sosai da dd babban kafin yace ta shirya itada Annen ze Aiko kokuma yazo da Kansa ya dauketa tareda godia ga Wanda ya taimakesun.


Shima yanda D ya rikice musu akanta ya fada mata Yana mata tsokanar kaka da jika da bayayi da Sauran jikokin nasa ta kasa magana tayi shiru cikeda kunya da farin cikin Daya mamaye zuciyarta akan Yanda take ji koyaushe gameda D din.


Koda sukai sallama da Zeenah ta sake waya anan suka jima suna magana Wanda yawanci duka zancen Zeenah ce takeyinsa.


Amnah aka Bata suka sake magana kafin tayi sallama dasu ta kira Dad kaante Shima suka gaisa Yanata murna ko gama magana yanda ya kamata Basuyiba ya kashe ya ringa Kiran D ya masa albashir Amma baya samunsa.

Naseer ya kira Shima tasa Bata shiga sbd dukkaninsu sun kashe wayoyinsu hutawa sukeyi sosai kansu ya sake yanda ya kamata.

##MAMUH#

#DBENA

#LOVE

#ROMANCE

#ZAFIN KAI

#KAANTES

#ABABAS


No comments