Breaking News

ZAFIN KAI 74

 * Arewabooks@Mamuhgee_*

74


Kukan 'dan Umme ya fasa me qarfin gaske lokacinda ya samu Kansa a duniyan da baisan

Yaya take ba,

Pillon da kanta yake Kai ya saka hakoransa ya kanne Akai ya fizgesa tini pillon ya fashe lallausan gashin ciki Yana zubowa da tashi sama cikin Dan hasken da dakin yakeda shi.

Kukansa ya Hana nata fita sbd ita batada lafiya ko garfin da zata iya fidda nata kukan yayi sauti Dan haka dakin ya kauraye da kuka kawai Kuma ahakan Bai sauraraba tsawon lokaci kaman zai mutu yakejin Kansa sbd abubuwa da yawa.

A daidai lokacin da ya samu Kansa daga shi har ita lokaci Daya suka sume babu Wanda yasan halin da Dan uwansa yake ciki. *******Safnah a lokacin da ta fice daga gidan cikin dauriya ta ringa Jan motarta a hankali cikin highbridge sbd dokansu ne baa gudu da mota a cikin gurin hakama baa horn,duk

Abinda zaiyi qara ko Bada hayaniya baa yinsa a ciki har sai ka fice Dan haka zuciyarta kaman zatayi tsallake ta fito sbd sauri da takaici ta lallaba ta samu ta fito highbridge din tayi yar tafiya tayi nesa da gate din shiga gurin ta samu tabau Wani titin ta take motarta cikin tsananin gudu tana Jin zuciyarta na sake daukan rawa da azamar gaggawa.

Ko data Isa gida Momynta ta kasa hakuri har ta fito da mayafi a hannu da key din mota zata bita takai mata itama zuciyarta na tsalle cikin rashin hakurin jiya da gaggawa sbd matiqar

Basu Basa wannan yasha ba bayan biyan bugata drugs din ba sakinsa zasuyiba ana zuwa Asibiti zaa iya gano meyasa Wanda ba asibiti kawai ba gasarma gaba Daya kamasu zatayi idan aka kamsu da wainnan qwayoyin sun bawa Wani,waninma Dan gaban goshin familyn kaantes.


A harabar gidan suka hadu batama fito mota ba momy ta fasa shiga motarta ta nufota tana sauke ajiyan zuciya da washe baki tace

"Wai barkanmu da arziki,harna fito sbd na kasa nutsuwa da Abinda zai kawo matsala,

Karbi bama sai kin fito motar ba Maza koma kada ya shiga halinda zai kasa komai ma.

Itama Safnah ajiyan zuciya ta sauke ranta na sanyaya tas da farin ciki ta karba tareda kokarin juya kan motar tayi reverse tana cewa

"Momy da wuri Zaki kira Naseer ki San yanda zakiyi ki turasa can yaje asamu kaimu asibiti

Amma ki fara kirana sai kin tabbatarda na

Basa magananin hannuna."

Hankali kwance momy tace kije kawai da kaina zanzo kaiki Asibitin sbd tabbatarda babu Wani Abinda zaisa a Gane meyasha,

Kafin komai kina Isa ki tattara abincin Dayaci ki zubar karki bari a tadda abincin."

Gyada kai kawai Safnah tayi tana ficewa cikin sauri sbd a matse take Data koma din,bayan cikar burinta na zama matarsa cike take da zallan kwadayinsa da bugatarsa sod ta tabbatarda DD kaante Bai taba sanin ya ya mace take ba a bangaren kwanciya Dan haka duk macen datai sa'ar budesa a leda zata zama sanyin zuciyarsa

Duk seconds din dake tafiya a hanyarta ta komawa highbridge akan Idanuwanta suke tafiva Dan haka hankalinta Sam baya kan hanya Yana kan agogon motar tana Jin kaman kanta zai kama da wuta sbd azarbabi.

Bata ankara ba tayi cikin wata motar data saka right signal na sauka titi Wani mugun buguwa sukai wanda ya saka kanta buguwa da steering mota taji kaman kan ya fashe.

Mintina tayi a motar batareda ta iya daga kanta ba sbd tsananin azaban dayake mata har sai da me motar gabanta ya fito Yana Dan buga glass na motar ta Yana mata hannu ta sauke glass.

Sai alokacin ta Dan dawo daidai tana Dafe kanta ta sauke glass tana kallansa cikin kokarin sake dawowa daidai ta Bude baki tana Basa hakuri kawai sbd batason Abinda zai tsayar da ita ya Bata lokacinta na Isa highbridge.

Ganin halinda take ciki Kuma da ganinta mace ya sakasa Shima juyawa kawai ya kyaleta Yana tsoki ransa a bace.


Girgiza kanta dake Dan juyawa tahau Yi tsawon mintina kafin ta dawo daidai Amma har lokacin kanta na Dan sarawa ta tada motar tabar gurin tana cigaba da tafiya sedai wannan

Karan bazata iya gudu ba idan har tanason kanta a Raye sbd kanta dake Yi Yana sarawa idan tace tayi gudu mummunan hadari ne zai iya faruwa da rayuwarta:

Lokaci mai Dan tsayi ya Jata kafin ta iso highbridge sbd Badan fitarta ba ta sani da yanzu komai yagama wakana tsakaninta dashi.

Tsoki tasake Dan ja lokacinda ta shigo highbridge din tanason tayi masifaffen gudu ta

Isa Amma ba Daman Hakan.

Ko data Iso tayi parking ta dauki maganin ta saka handbag dinta ta fito tareda rufe motar tayi ciki da sauri sai alokacin taji sanyi da farin cikinta ya dawo.


Password na kofan ta saka ta shiga ta mayarda kofan ta rufe tana dubawa palon baya Nan.

Hanyar zuwa bedroom dinsa ta kalla Amma

Bata nufa ba sai ta nufi dining da sauri tafara kokarin tattara abincin dining din tas ta kwashesu takai motarta ta zuba su baya jikinta na rawa ta sake tada motar kaman yar wahala da sauri ta sake fita daga highbridge din taje nesa da anguwan kadan ta zubar da komai a

Wani refuge ta dawo.

Securities din highbridge Suma ranar Saida sukai mamakin kaida kawon datakeyi a Dan haka Suka Yanke daga wannan fitan nata idan ta dawo ta sake fita bazata sake dawowa ba sbd in and out dinta na ranar ya cike kaidojin

Kai kawon baqinsu na wunin sbd tsaro.

Tana dawowa Sai data ganta a palonsa tsaye ta sauke ajiyan zuciya guda hudu a Jere kafin ta nufi bedroom dinsa ta Murda kofan tareda turawa Amma kofan Taki buduwa.

23 RA

Da sauri ta Kalli kofar sai alokacin taga itama

Saida password idan bana ciki bane zai Bude maka ka shigaba.

Wani azababben zufa taji yana kokarin karyo mata ta sake Murda kofan da qarfi tana turawa kaman wadda take Neman zaucewa.

Bubbuga kofan tahau Yi da Dan karfi har tana

Kiran sunansa tana cewa itace ta dawo ya

Bude mata kofan shikuma daga ciki daidai wannan lokacin ne bayaji baya Gani baya Gane komai bare Kuma Bena datake cikin karban azabar rayuwarta da Bata taba tsammani ba.

Dukan kofar takeyi nata magananin datasha

Yana taso mata gadan gadan itama shi take bugata kaman zatayi fitsari a wandonta tana ihun Kiran sunansa da karfi.


Watsi tayi da Jakarta da wayarta tana Bada himman buga kofa da turawa da garfi ko zata iya balla kofa.

Haukacewa take Neman Yi a palon ita Daya

Dan tini takejin ayau Yana Bude kofan wh Ko fyade ne saita masa.

Tana cikin masifaffen tashin hankalin kunnuwanta sukai mugun Jin data kasa fahimtar menene.

Dakatawa tayi hannuwanta da jikinta na mugun rawa sosai ta Dora kunnenta jikin kofar ahankali taii kaman ihunsa da kukansa takeji

Yana Kiran sunaye kala kala Wani mugun yanayl.

Yankewa gafafuwan sukai ta zube qasa

Amma Bata yarda ba da Abinda taji din ta sake kwantawa qasa ta Dora kunnanta iikin kofar Amma Bata Jin komai gwara ta saman Dan haka ta sake migewa jiki na tsananin fizga ta

Dora kunne.

Kuka ne yakeyi sosal,

Kuka ne bana ciwo ba bana azaba ba bana qunci ba,

To kukan me yake?

Sunan uban waye taji kaman Yana kira?

Wani mummunan busashen yawu ta hadiye dagyar ta makoshinta jiri da duhu suna Neman rufe idanuwanta.

Rawar da jikinta ya sake dauka wuta na cin jininta Yana tafasa ta rarrafa ta Nemo wayarta inda ta jefar ta Nemo numbern momy hannuwanta na kasa riqe wayar da kyau sbd rawar da suke daidai momy na daukan wayar itama wayan Bena data bari palon ta kawo haske alaman shigowan kira sai akan idon

Safnah taga sunan My Zee kaante baro baro jikin wayar da Annensu tana zaune batama

San anyi mata hotonba.

"Beeenaaaaa"...tafada sunan cikin kakkaryewan kalamai da mafi girman tashin hankalin rayuwarta.

Momy dataji yanda ta ambaci sunan Bena din take ta shiga rudani murya a rikice tace

"Wace Benar Kuma?

Meya kawo sunanta yanzu?

Ke sanar Dani meyake faruwa nei

Sakin wayar hannunta Safnah tayi tareda

Dora hannu Akai tanason fasa ihun dazai Tara mutane Amma Bata samu Damar Hakan ba ta

Yanke jiki ta Fadi gurin a sume.


lhun Kiran sunanta momy tafará Yi a waya tana tambayar lafiya Amma shiru ba magana ba motsi.

Rawa jikinta y dauka itama ta miqe tsaye tana sake Kiran sunan Safnah din Amma ba alamar akwai me Rai ma a kusa.

Wani zufan ne itama ya fara tsatsafo mata tana Neman tsinkewa sbd tagano dai yanzu kullum sabuwar masifa ce take bullo musu wata bayan wata

Kashe wayar tayi ta sake saka Kiran Safnah din tafara ringing harta katse baa dagaba,

Sake kira tayi har so biyu Amma baa daga ba tini tafara kaida kawo tana shiga fargaba da zafin zuciyar idan ba Wani abin ne yafaru ba,

Tsawon lokaci tanata sake Kiran Safnah baa dagawa gashi dare ya fara sosai Dan haka taji bazata iya Jira masifa ta sauko musu ba gwara taje ta dubo kada a Samu matsala.

Jallabiyar bacci ma ce a jikinta ta saka mayafi

Akai ta zari mukulli ta fito ta fada mota ta fice.

Cikin gudu sosai ta Isa highbridge da farko sbd lokacin snigarsu ya wuce dare yayi sosai kusan 1 na dare Dan haka Suka hanata shiga.

Cikin magiya ta nuna musu 'yarta matar D kaante tana ciki tanata Kiran wayarsu Basa dauka tana son duba ko lafiya.

Wayarsu securityn dake duty ya daga ya kira gidan DD kaante Wanda kowane gida Dayake ciki akwai numbern dasuke kiransu da ita landline,

Ringing wayar keyi sosai Amma babu Wanda ya dauka, Sake kira yayi har so hudu babu Wanda ya daga Dan haka ya karbi id card dinta ya duba tareda shigar da information dinta aka Bude mata gate din ta shige.

Tana Isa gidan tafara kokawan saka password kala kala Amma bata saniba.

Sharkaf take da zufa iya zufa cikin tashin hankali,.

Canke tafara na password din Amma duk baiyiba sai kawai ta hau tinanin ranar haihuwan Amnah kokuma ranar da Mahaifin

Amnah din ya rasu wato Bilal.

Tana fara saka na Amnah ya Bude a gigice ta fada tana legawa kada ta fada tarkon da batasan Yaya yake ha tinda batasan meya samu Safnah ba tajita shiru.

Cikin mummunan sa'arta da Safnah tafara cin karo a palon kwance ba Rai a tareda ita kaman ta mutu.

Ihu taso fasawa tayi saurin rufe bakinta ta zube gabanta tana jijigata da karfin gaske tana Kiran sunanta ahankali.

Ganin alaman da Rai jikinta yasakata nufar dining tana Neman hanyar kitchen a gigice ta samo ruwan sanyi a fridge ta zubawa Safnah wadda itama a gigice ta farka tana Neman rusa ihu momy tayi saurin rufe mata baki.

Kallan momyn takeyi jikinta na dawowa da rawa hankalinta na gushewa tace

"Momy Bena ce a cikin Daki da D,

Bena ce take kwance a kan gadon DD Yana mayar da ita mace,

Momy wIh bazan iya yarda ba kashesu zanyi duka kowa ya huta Momy bazan iya.....Bata qarasaba kanta ya sake juyewa ta Kuma sumewa tsabar masifa da balain Datake cikinsa.

Momy data shiga mummunan tashin hankali da tafasar zuciya itama batasan lokacinda ta fara ganin duhu duhu ba kanta na juyawa.

Me kenan ya faru?

Biyu babu zasuyi ko me?

Cabdijam,wIh bazai yiyuba idan har sun rasa

D to ko zaa mutu bazasu rasa bulama ba Dan haka bazata taba yarda asan asalin Safnah ba.

Kitchen ta nufa ta kunna oven batareda komai a cikinsa ba takai zafinsa qarshe ta fito ta dauki ruwa ta zubawa Safnah tana farfadowa ta figeta suka nufi hanyar fita tana cewa

"Maza muje wlh na banka musu wuta daga duniyar dasuka sai lahira"


Safnah da Bata hayyacinta tanajin Hakan ta

Kalli momy da sauri kafin tayi magana momy ta Nuna mata motarta tana cewa ki shiga kija motarki mu wuce gwara ko ya rasa tinda Mika rasa.

Wartsakewa Safnah tai da gyar take ganin gabanta suka ja motocinsu suka bar highbridge din.

Basuyi tafiya me nisaba Safnah ta kasa tuqi sbd yanayin Datake ciki zata iya samun hadari

Dan Bata ganin komai bayan duhu.

##MAMUH#

No comments