Breaking News

ZAFIN KAI 63

 _Arewabooks@Mamuhgee_*

63


Tinda suka tafi Bena ta kashe wayarta Bata waya da kowa sbd tasan Amnah dole zata ce a kira mata daddynta haka Shima tasan zai iya Neman numbernta Dan kawai magana da yarsa Amma Kuma ita Bata bugatan komai ya sake hadata dashi a yanzu dayake shirin tarewa da matarsa.

Dd babba ma Daya fahimci Bata bugatan communicating da kowa dake Nigeria sai Bai takurata ba Shima sai dace ake samun tasa wayar Dan haka kusan can gida sai hidimar bikin ta rage armashi sbd rashin Jinsu a waya

Akai Akai ita Bena kwata kwata tinda ta tafi babu Wanda ta sameta bare ayi magana da

ita.

Daddyn Amnah din da Kansa ya karbi numbernta yayi kira yayi sakon 'yana bugatan magana da 'yarsa Amma duka shiru Dan haka

Shima gabaki Daya hankalinsa ya bar komai ya koma kan buqatan Jin 'yarsa. 


Shirin tafiya Australia ya fara dayaga duna kokarin share sati babu labari ba zancen komal.

Dad kaante ne da ummensa suka dakatar da tafiyarsa sbd bikinsa akeyi bazai yiyuba ya tsallake ya tafiyarsa.

Hakanan ya fasa tafiyan Ya zauna Amma ba

Dan ya fasa ba matigar suka wuce sati uku

Basu dawoba zaije yaga lafiyan yarsa ya dawo.

Bikin da Akai na kece Reni da sa'a tareda

Barnar dukiyar gaske kafin aka gyara part din

Bilal tareda Maida part din sabo fil komai aka sauya daidai Amarya yar gata masu arziki.

Tafiyar su Bena da sati biyu cif aka kammala bikin Amarya ta tare cikin kaantes a part din

Bilal da yanzu yake nata.


Batada was qawaye sbd mummynta itace qawarta Kuma abokiyan shawararta da duk

Wani Abinda zatai tare sukeyin abinsu,qawarta

Daya Kuma bama bahaushiya bace 'yar Wani minister abokin daddynta Dan haka daga ita sai Mummynta da qawarta Rumah suka kawota sai Ummen DD din da Zeenah dakuma mum Khadija,Siyam Bata jeba sbd tanayin

Bena sosai Dan bayan Zeenah Bena batada

Kawa kaman Siyam din,itama Zeenah taje ne sbd zamanta dole Amma duk da haka da Bena na Nan ko tana dole bazata je ba gaskia zata zauna da ita ta rage mata radadin zuciya Koda

Bata nunawa ita Bena din.

Bayan Kai Amarya aka watse mummynta kafin su wuce ta tsaya sukai magana tsakaninsu

Mai Dan tsayi kafin ta fito suka bar kaantes kowa ya watse aka bar Safnah din ita Daya lokacin DD Yana wancan gidan nasa Yana hutawarsa sbd bayason ajiye kowace mace a wancan gidan shiyasa yace a gyara mata ta zauna cikin kaantes.


Bai dawo kaantes ba sai after 11 ya shigo da motarsa da kaf kaantes babu irinta yayi parking ya fito sanye cikin guntayen kayansa

Daya Saba sakawa Kai tsaye ya wuce sashen

Bilal din Yana shiga a Palo ya taddata

Tana ganinsa ta miqe tsaye tana ajiye wayarta data amfani da ita ta kallesa tare da masa sannu da zuwa batareda damuwa da time din

Daya shigo dinba dama kayan jikinsa dake bayyanarda daga hutawa ya fito.

Amsa gaisuwanta yayi tareda yimata barka da zuwa kafin ya Dora da yimata Saida safe ya nufi hanyar dayasan Nan ne bedroom dinsa anan ya shige.

Bata ji komaiba Dan tasan waye Dawood din game da zafin Kai da ajinsa Dan haka ta sauke Dan garamin numfashi tareda daukan wayarta ta nufi bedroom dinta itama ta shige tana wurgi da wayar kan gado ta wurgar da mayafinta Shima tana sake qaramin tsoki tace "Yana nufin haka zan kwana bayan duk

Abinda mummy ta dirka min Nasha?

Mitss"

A tsakiyan dakin ta tube kayanta ta jefar ta wuce toilet ta wanke duk makeup na fuskarta tayo wanka tanata fama tsoki a hankali sbd

Sam batada hakuri.

Tana fitowa wanka kayan bacci kawai ta saka ta fito dauka dakin ta nufi bedroom dinsa ga mamakinta dakin baya budewa sai an Bude maka daga ciki idan daga waje ne sai da password.

Wani qaramin tsokin ta Kuma ja mara sauti tareda Dan knocking kofar

A daidai wannan lokacin shikuma yana toilet

Yana wanka cikin ruwan dumi a natse Dan haka har tayita knocking ta gaji ta koma dakinta Baijiba.


Yana fitowa yayi Shirin baccinsa bayan yagama shafa tirarika da body oil kadan ya kwanta tareda lumshe idanuwansa da gabaki.

Daya babu Abinda suke bugata da son Gani kaman 'yarsa.

Washe gari daga gurinsu Umme aka kawo breakfast daga shi har ita babu Wanda ya tashi daga bacci sai 10,

Shine ya fara shiryawa ya fito cikin Giorgio

Armani classy suits navy blue da Alexander

McQueen shoes take gamshinsa ya cike palon da inda ya fito,

Bai tsaya breakfast ba ya fice sbd yau meeting dinsa nada mahimmanci sosai a office.

Bayan fitarta sai daga baya itama ta fito sanye da kayan baccin brush kawai tayi ta fito ta zauna kan dining zata fara cin Abinda Mai aikin da aka bar mata daga cikin masu aikin

Umme ta shigo a natse kanta a qasa ta gaida

Safnah din.

Bata amsaba ta fara cin abinci ahankali tana latsa wayarta Dan Kiran mummynta tace

"'Ina dayan matan D take zaune??"

Dan shiru Salma tayi kafin ahankali tace

"Tinda aka Akai auren a bangaren Umme take zaune da Amnah"

Shiru Safnah tayi sai a lokacin take tinawa da matar tasa nada shegiyar 'ya wadda aka samu

ba aure.


"Tafi naji" tafada tana cigaba da cin abincin a hankali.

Aiki Salma ta wuce zata fara duk da babu inda

yakeda alaman buqatan Wani gyara koina fes

Amma dole hakanan ta hau goge kaya tana

Shirin shara da mopping before wadata koina

da qamshi.

Ita kuwa Safnah tana gamawa wanka taje tayi

ta shirya ta nufi gurinsu Umme tayi zamanta

acan Dan maitan son ganin wadda take amsa

sunan kishiyarts a baki kawai.

*****Bena sosai ta danne ta Hana duk Wani

azaban da zuciyarta take ciki ta sake suka

ringa samun hutu da nishadi tareda kulawa

da dd babba sosai Dan kusan itace ke Basa

maganinsa da lokaci yayi maganinsa da lokaci yayi

Hakama shi Kansa dd babban duk Kiran da

DD ke masa Sam yaqi nuna masa suna gida

Daya ma da Bena Dan haka Bai taba kwatanta cewan a Basa 'yarsa ba bare Bena.

Amnah kullum sai tayi rigiman son magana da daddynta shi ya saka Bena dagewa ta danne

Abinda yake cin ranta ta saki jiki tana bawa

'yarta nishadi suna Jin Dadin qasar yanda ya kamata.

Ta bangare Daya Kuma aikinta na office Bai dakata ba tana exchanging emails sosai da

Fahad gameda ayyukan office Dan haka take sake samun kwanciyar hankali da nutsuwa.

Bata saka ranar dawowa a kusa ba San Dan karatun Amnah da hutun ta yake kokarin qarewa Dan haka sbd Amnah kawai zata koma idan lokaci yayi.


****Acan Nigeria kuwa Safnah kullum a bangarensu Umme take wuni duk da ta samu sanin Bena Bata qasar da 'yarta,

DD kuwa kusan kullum baida time na zama gida Yana dawowa yaci abinci ya shige shikenan babu Wani Abu na kusanci da juna koma fira haka ta kauna da kulawa data taba shiga tsakaninsu kullum baya Wani zama sbd ko baya office yafi zama gidansa dake highbridge, yafi samun nutsuwa da kwanciyar hankali acan

Ya kasa sabawa da zama kullum kullum da mutum a guri Daya shiyasa duk inda yake tin asali baya zama cikin familynsa yafison yaje inda zai zauna shi Daya yayi rayuwan dayakeso gashi matiqan Yana cikin gidansa ba maabocin saka kaya masu nauyi ko tsayi bane

Dan Hakan yake zaban zama gidansa shi Daya yayi rayuwansa ba takura ba damuwa.

Safnah hakurinta Yana qarewa gameda zaman

Datakeyi da mutumin da takejin zuciyarta idan

Bata samesa ba komai zai iya faruwa, Zafi da bagin ciki sosai takeyi da irin zaman dasukeyi

Babu ranar da Bata Kai kanta dakinsa Amma

Bai taba barinta ko shigaba Bare ta samu

Daman Jan raayinsa ya kwana da ita Dan a yanzu tafi buqatan suyi kwanciyar aure akan komai sbd vanda yake fitowa daga shi sai dogayen wandina ba Riga kokuma guntayen wandina ba Riga jikinsa ya sakata qara mutuwa akansa sbd ita ko a turawanta datai ravuwa cikinsu DD kaante daban yake,

Komai nasa me aji da Jan hankali ne tareda daukan Ido.

Ahaka suka shafe sati biyar babu Wani gaba bare baya Dan haka itama ta rage zama gida kusan kullum saita fita sunfita da Mummynta sbd lamarin ya fara qundurarsu gashi hakanan

Safnah takejin Bata gaunar matarsa ta dawo

Bata gama samun Kansa ko hankalinsa akanta ba Dan haka daga ita har mummynta hankalinsu ya tashi suka kasa zama suka kasa tsayi. ******Watansu Bena 2 cif suka fara Shirin dawowa lokacin suna barin Australia Umrah suka wuce suka qara sati biyu kafin suka diro

Nigeria,

Jirginsu da Asuba ya sauka Dan haka Fahad ne ma yaje da Kansa da lafiyayyan motarsa ya daukosu,

Kallo Daya yayiwa Bena ya dauke idanuwansa

Yana kore shedan daga zuciyarsa sbd yanda kyanta ya daki kirjinsa,

Tafiyan wata biyu kokuma yace uku Amma komai nata ya qaru,

Kyau, lafiyan fata,hutu,nutsuwa,aji da burgewa duk komai ta garo hakama harda cikowa tayi kaman wadda babu Abinda taje tayo sai hutawa. Dd babba ma ya gara samun qarfi da lafiya sosai harma da kwanciyar hankali sbd kulawa da Bena ke Basa da yanda ya bar gida da hayaniyarsu yaje ya huta Abinsa.

Abbakar kuwa gibarsa yayo abarsa lafiya kalau ta hutu da cima me kyau duk da Baya Wani son abincinsu acan Amma cinsa yakeyi ya koshi Abinsa ya huta ya fita yawon Shan iska yaci Dadi San ransa

Amnah ma sosai tayi jikinta da haske data garo Daman ita ba skin din mamanta ta daukoba na baban Dan haka take fara tas kaman DD.

Koda suka shigo kaantes an shiga sallan

Asuba Dan haka babu Wanda yasan ma sun iso, sai a lokacin ta Ciro wayarta jaka ta kunna ta kira Nafisat, Nafisat ce ta kwasar musu kayansu zuwa ciki shikuma dd babba Abbakar ne ya shiga nasa kayan bangarensa kafin suka wuce masallaci sallah sbd alokacin ne aka tayar.

Suna shiga Kai tsaye bedroom din Zeenan suka shige Nafisat Kuma cikin duhun Asuban ta hau gyara dakin Bena din.

Sun shiga Zeenah Bata ma tashi sallan Asuba ba motsinsu da shigowansu dakin ya tayar da ita ta tashi zaune ahankali ta miga hannu tana kunna wutan dakin taga Bena tsaye tana ajiye handbag nata Amnah kuwa gadon ta fada sbd bacci ne sosai a idonta.

Da sauri Zeenah ta sauko gadon bacci na

Sakin idanuwanta gabaki Daya ta nufo Bena suka rungume juna tana cewa "Oh ya Allah finally Bena kin dawo."

Murmushi Bena ta sake ahankali tareda rungumeta itama tana cewa

"Kin dauka bazan dawo bane?"

Mintsininta Zeenah tayi tana janyewa daga jikinta tace

"Kinsa me kikai kuwa?

Meyasa Zaki Kashe waya ki Hana kowa Jinki for more than 2months,

Kin kusa sakawa kowa heart attack da rashin

Jinku.

Wani murmushin me sauti ta Kuma sakewa tana cewa 


"Ba gashi na dawo ba"

1

Kayanta tahau cirewa ta fada toilet tayo alwala batai wanka ba ta fito ta saka Riga da wandon bacci tayi sallah ta fada gadon Zeenah din ta shige bargo take baccin dake cinta da gajiya ya dauketa.

##MAMUH#

#DBENA

#TOO HOT

#MARRIAGE

#ROMANCE

#SAFNAH

No comments