Breaking News

ZAFIN KAI 58

 *_Arewabooks@Mamuhgee_*


58



Saukan hannunta kan towel dinsa ya sakashi dube idanuwansa dasukai nauyi ahankali yayi mata Wani irin Kallon kasala da Yana sake saka Kansa wuyanta ahankali fatar fuskansa na gogan fatan wuyanta zuwa kirjinta tana sake qanqamesa daga qugu.


Qamshinta Dayake shaqa ya saka idanuwansa qara nauyi Yana son janye kirjinta daga nasa dake Neman kashesa da zafin jiki Amma ya kasa motsawa sbd idan ya motsa a lakacin shi Kansa yasan towel din nasa zai iya kuncewa.


Yanda fuskansa ke gogan wuyanta ya saka jikinta mutuwa tayi shiru tsigan jikinta na tashi itama qamshinsa gabaki Daya na Jo Malone body wash dinsa ya cika mata iskar Datake shaqa a tsakiyansa gashi duk numfashinta Daya saiya daga kirjinta ya sake gogan nasa dakyau


Jin Yana Neman rasa Kansa gabaki Daya ya sakashi qarasa zagayota da hannuwansa ya manneta sosai da kirjinsa ta Yana rintse Ido ta yanda bazata ringa numfashi tana gogansa ba zafin jikinsa na tsanantuwa.


Tafin hannunta Daya ta dago ta Dora tsakiyan bayansa zata Zame dayan hannun na qugunsa Dafe da towel din datake tsananin tsoron ya Fadi.


Saukan tafin hannunta bayansa da babu kaya ajiki ya sanyashi qara cusa Kai cikin wuyanta ya sake Bude baki da muryan data sata qanqamesa da duka hannuwanta biyu cikin kunnenta yace


"Don't do that again"


Batasan lokacinda ta lumshe idanuwanta ta ba tana langabar da kanta gefe sbd dayan gefen Dayake shinshina wuyanta zuwa kirjinta idanuwansa a rufe.


Yanda yake shinshinata Yana hada fatarsa da tata yasa dukkaninsu mantawa da su waye su din dakuma inda suke tsaye suna aikin.


Rigarta data yaye hannunsa ya sauka kan cikinta ta ja numfashinta Daya so barinta da qarfi tareda Bude idanuwanta ahankali daidai Shima ya Bude nasa idanuwan suka Kalli juna tayi qasa da nata idanuwan tana shikuma ahankali ya sake Kai bakinsa kunnenta cikin sauti mara fita sosai yace


"Wannan ruwan ya huce Ina buqatan Wanda yafi zama colder"


Yana fadan Hakan ya zare hannunsa daga fatar cikinta ahankali tana rintse idanuwanta sbd yanda yake dauke hannun.


Juyawa tayi da sauri kaman zata Fadi tabar gurin tana Isa kitchen hannuwanta na Dan rawa ta dauko ruwan sanyin sosai ko nata Bata tsaya dauka ba ta fito baya palon Dan haka dakinsa ta Isa Kai tsaye tayi knocking ta shiga baya dakin Yana toilet ta ajiye ruwan da sauri ta fito ta koma dakinsu ta fada toilet itama.


Fuskarta dake Dan tsatsafo gumi ta wanke tana sauke numfashi ahankali ahankali har ta samu ta Dan dawo daidai ta fito jiki ba qwari tahau gadon ta kwanta ruwan ma Bata daukoba hakanan taji ta Dena Jin kishirwan Dan bazata iya sake fita ba.


Ta Dan jima kafin bacci ya dauketa Bata farka ba sai Asuba.


Tare sukai sallah da Zeenah suna gamawa Zeenah ta koma ta kwanta ita Kuma akwai aikin kamfanin kaantes da zatai Wanda Fahad ya tura mata Dan haka shi ta fito Palo ta zauna tahau Yi cikin pink kaya masu Dan kauri sbd sanyi da safa a qafanta.


Har kusan 7 na safe tana Aikin tana Kiran Fahad din a Wani abin.


8:30 Zeenah ta tashi ta fito ganin Bena na aikin ya sakata Yi musu breakfast da kanta gasashen chocolate and coconut bread da fries tayi musu se hot milk tea.


Shima yau yanada meeting na qarshe da zaiyi Dan haka 9 ya fito sanye cikin native wear yau dinma na blue cashmere da wula kaman Wanda yau ne daurin aurensa da matar Dayake so Dan Kansa da raayinsa bana wainda yake aure na umarni da cika burin iyayeba.


Waya takeyi da Fahad Koda ya fito shigar jikinta ta kayan loro Piana ya kalla kaman Amnah Takoma ga tea da Zeenah da miqo mata da chocolate coconut bread takeci ahankali tana cigaba da amsa wayar idanuwanta na kan laptop dake kan qafafunta.


Qamshin Caron poivre Daya fara gauraya palon a hankali ya sakata kasa dagowa tana hadiye tea din bakinta a hankali sbd Jin idanuwansa sun sauka akanta.


Zeenah ce ta washe baki cikin kulawa tayi masa Good morning ya Tako ahankali Yana amsawa.


Bena na ganin ya tinkaro tayi saurin ajiye cup din hannunta ahankali tareda Dan dagowa tana kasa kallansa tace "good morning" ahankali itama.


Yana isowa Bai amsaba cup din data ajiye na tea dinta ya dauka ahankali yakai bakinsa yasha kadan ya sake Sha har so uku kafin ya ajiye ya amsa gaisuwan Shima ahankali ya juya ya fice Zeenah data kasa gasgata Abinda yayi din ta miqe ta biyo bayansa suka fice tare suna magana.


Suna ficewa Bena ta dago ahankali ta zubawa cup din idanuwanta tanajin jikinta na mutuwa takai hannu ahankali ta dauki cup din itama takai bakinta taci gaba da Shan tea din zuciyarta na sanyi.


Koda Zeenah ta dawo Bena har lokacin Bata gama Shan tea din ba sbd gabaki Daya kuzarinta takejin kaman ta rasa.


Zeenah na zuwa taso maganar Abinda DD din yayi Amma Bena ta fuske tana basarwa.


Qarasa aikinta tayi guraren 11 tukuna ta miqe Takoma daki tayi wanka ta kwanta bacci sbd tana buqatansa Kona mintina arbain ne.


Sai Data tashi bacci tayi girkin Rana Takoma tayi sallah tukuna tayi wanka ta fita itama.


Dukkaninsu su ukun kusan lokaci Daya suka dawo Zeenah ce tafara dawowa kafin shi tukuna ita daga baya.


Kowannensu wanka yayi yayi sallar laasar suka fito dining gabaki dayansu suka ci abinci babu Wanda ya iya kallan Wani tsakanin shi da ita har aka gama kowa ya tashi.


Bayan magrib shi da Zeenah suka fita Basu dawo gidan ba sai after 12 lokacin tayi bacci Dan haka Saida safe na tasan time dasuka dawo.


Dayake ya gama Abinda ya kawosa sai ya fara Shirin kowama A Daren ranar da zai tafi ya bawa Zeenah card dinsa Daya suka fita shopping sukaiwa kudi wulaqanci haka yasa akaiwa Amnah siyayyan abubuwan da ma wasu tanadasu sunfi nawa duk baa fara amfani dasu ban.


Bayan sun dawo sunyi wanka sun huta sunci abinci suna gamawa Amnah ta kira daddynta tace sai taga mummynta sunata Kiran wayarta Bata dauka dayake tabar wayar daki.


Dan dagowa yayi da idanuwansa yayiwa Bena dake Jin Abinda Amnah ke fada Kallo Daya itama shi ta saci Kallo daidai time din.


Idanuwansa rudata sukeyi Dan haka ta janye kallanta tareda qarasa shanye ruwan dake glass cup din hannunta ta jiye.


Kallan Daya sake mata ya sata tasowa suka dawo Palo suna zaunawa kan kujera Daya tana kokarin Hana bugawan kirjinta fita sbd Amnah dake kallansu hakama Zeenah.


Qaqalo murmushi tayi cikin kulawa sosai da kauna tace


"Baby me kike Jira bakiyi bacci ba haryanzu? Akwai school gobe fa"


Dariya Amnah tayi tana cewa


"Bazan iya bacci da wuri ba yau sbd murna my daddy is coming back tomorrow, right daddy?


Wani qayataccen murmushin da Bena Bata taba ganinsa yayi ba ya sake a natse 


Saura kiris ta kasa dauke kallanta daga Kansa ta samu ta dauke idanuwanta ta maidawa kan Amnah.


Cikin nutsuwa da kulawa hankali kwance yace


"Gobe Inshallah Daddynki ne zai dauko angel dinsa from school."


Tsalle tafara tana murna da cewa


"Daddy na matsu gobe yayi,


Mommy please ki dawo tareda Daddy I miss you both inason na zauna tareda mommy na da Daddy na kaman sauran yara kaman,


Kaji daddy? Please bring mommy with you.


Ahankali ya juyo ya Kalli Bena wadda ta kasa cewa komai.


Kallan Dayake mata ya sakata yar rudewa tana Hana kanta bayyanarda rudewan ta Dan basar ta hanyar kallan Amnah din tace


"Baby ni zan dawo daga baya ba na fada Miki nakusa dawowa ba?"


Bata fuska Amnah tayi tareda marairaicewa tana kallansu su duka biyun idanuwanta na cikowa da hawaye tace


"Ba ance matan daddy na ta dawo yau Nigeria ba naji Umme na waya tana fada nidai Daddy mommy na ce kawai zata dawo gida"


Tsit sukai dukkaninsu harda Zeenah data zauna lokacin 


Benazir kuwa hannuwanta ne suka Dan dauki rawa tayi saurin boyewa ahankali kada ya Gani zuciyarta na harbawa da qarfi.


Shi kuwa Bena din ya Dan kalla kafin ya Maida kallansa kan Amnah yace


"Ok Angel je ki kwanta da wuri sbd gobe ki samu karfin yiwa Daddy oyoyo,ok?"


Gyada Kai tayi ahankali tareda kallan Bena tace "goodnight mommy"


Ahankali Bena ta furta "goodnight baby.....Bata qarasa kira ya shigo wayarsa dauke da sunan SBB baro baro ajiki.


Miqewa Bena tayi ahankali tareda barin gurin ta koma dining Dan tattarawa taga Zeenah tini ta gyara komai Dan haka Kai tsaye bedroom dinsu ta wuce batareda ta juyo ba bayan tanajin idanuwansa akanta.


Bai dauki wayar ba tana katsewa Kiran ummensa na shigowa a natse ya dauka cikin nutsuwa yace


"Hello Umme barka da dare"


"Barka" ta amsa tareda cewa


"Safnah ta sauka a Lagos yau itama gobe zata qarasa porthacort inaga yakamata ka wuce can daga Nan sbd daddynta ya kira su dd babba maganar saka ranar biki da tarewanta.


Kashe wayarsa yayi bayan yacewa ummen to kawai sbd baisan me zai fada ba akan aurenda har aransa ya manta dashi.


Barin palon yayi Zeenah ma miqewa tayi ta nufi bedroom dinsu tana shiga Kiran Safnah na shigowa wayarta sbd DD Bai dauki nata ba Kuma ance suna tare.


#MAMUH#


#DBENA


#ZAFIN KAI


#ABABA


#KAANTES


No comments