Breaking News

ZAFIN KAI 50

 Arewabooks@Mamuhgee_*

50


Bude baki tayi nutsuwar muryanta a bayyane ta gaida dd babba cikin ladabi da sanyi.


Murmushi me sanyi dd babba ya sake cikin kulawa ya amsa tareda tambayarta Yaya school.


Sake Dan qasa tayi da kanta tana damqe hannuwanta dake Dan rawa cikin nutsuwa tace "lafiya kalau."


Dawood da kaman baya gurin dd babba ya kalla kafin ya Maida kallansa kan benazir din da ita Kuma batasan ma da waye a gurin ba ya Dan sauke numfashi Mai sanyi da kulawa sosai yace


"Benazir ga mijinki Nan a zaune ki gaidasa."


Faduwa Mai tsanani gabanta yayi kirjinta ya fara bugawa da qarfi ahankali ta Dan karkata gefensa batareda ta dago ba kanta a qasa ta Bude baki muryarta na Dan rawa sbd sanyi tace


"Ina wuni."


Shi Kansa DD din shiru yayi na seconds sbd kalman dd babba ta cewan ga mijinta a zaune yasa ya Tina da auren mata biyu ne a hannunsa wainda babu wadda yasan ta inda zai iya sakata a mizanin lissafin rayuwarsa harma da matsayi na matar da ake tinanin yayi rayuwar Jin dadi kwanciyar hankali da nutsuwa da ita.


Batareda ya juya ya kalleta ba ya amsa Kai tsaye tareda miqewa ya fice Yana Ciro wayarsa da kiran Lizz ya shigo.


Bayan fitarsa dd babba ajiyan zuciya ya sauke tareda numfashi kafin ya saki qayataccen murmushi mara sauti ahankali Yana jinjina Kai.


Benazir data kasa motsi ya kalla yace


"Jeki benazir ki saki jiki kiyi karatunki ki qarasa wannan session din a gwada sauya Miki gurin karatun "

Godiya ta sake masa cikin sanyi tareda masa fatan Qarin lafiya tai masa seda safe ta fice.


Ita kadai ta Isa sashensu Dan haka tana Isa babu kowa a palon tana dap da Isa dakinta taji kukan Amnah ta juyo Kai tsaye sbd mantawa a hannunwa Amnah din take tintini.


Juyowanta yayi daidai da shigowansa palon Shima Yana kokarin riqe Amnah din dakyau sbd kaman zata Fadi da motsin kukan datakeyi.


A kyakyawan farar fuskarsa idanuwanta suka sauka gabansa a yayi mummunan faduwan Daya saka hannuwanta rawa da fitan numfashi da sauri tayi saurin dauke idanuwanta zata shige daki taji muryarsa me nutsuwa da kamewa yace


"Karbeta."


Saida ta damqe hannuwanta ta tattara nutsuwanta guri Daya kafin ta iya dago qafafunta ahankali ta iso gabansa ta tsaya


Ya dago Amnah ya miqa mata tasaka hannuwanta dake Dan rawa ta karbeta tareda juyawa Kai tsaye tayi bedroom dinsu ta shige


Shi Daman tin kafin ta juya ya juya Yana cigaba da amsa cikin rashin daga hayaniya.


Bayan shigarta daki Hana kanta zama tayi bare dadewa acikin rawar hannuwanta da faduwan gaba ta hau kintsa Amnah hannuwanta na Dan rawa har lokacin.


Tana gama shirya Amnah itama tayi Shirin kwanciyar ta kwanta tareda rintse idanuwanta.



***Washe gari morning lectures take dashi Dan haka da wuri ta shirya tayi breakfast a dining tareda Umme da itace ta hada musu kaya a jaka yau ma Zeenah Kuma tana bacci suka fice yauma cikin wata tsadaddiyar Noriea Abaya ash da Rolling.


Sai yamma ko yau din ta dawo a gajiye sosai,

Sallah magrib tayi tayi wanka tea kawai Tasha ta kwanta bacci ya dauketa tabar Amnah a can gurinsu Umme 

sallar ishai ma sai cikin dare ta farka tayi taga Amnah kwance gefenta an Kwantar mata tasan Umme ce ko Zeenah suka kawo mata ita.



******Ahankali rayuwar makarantan da Amnah ta sabo da ita tin tana Jin stress da gajiyan Hakan harta Saba Bata Jin komai yanzu musamman Mai aikinta Nafisat na kokari sosai gurin kulawa da Amnah Bata wasa da lamarin Amnah ko kadan,. hakama drivernta Ahmed Yana mata biyayya kaman Bai girmeta nesa ba kusa ba Amma sbd a qarqashinta yake biyayyarsa tayi mata yawa take Gani.


Rayuwar gidan ta Saba a yanzu da ita kusan ta ko Ina,


Dd babba kauna me tsanani da kulawa yake nuna mata Wanda kusan kowa ya fara shedar da Hakan musamman da yanzu takai komai nata kaman ba lissafi ake Siya mata har Abinda Bata buqata sosai Dan haka itama a zuciyarta matsayin dd babba da Umme a ranta daban suke,

Tana Jin su kaman zata iya iya komai dominsu kaman yanda zata iya komai domin Annenta idan Bai Saba sharia da musulunci ba,


Wannan ya sakata Sake kokarin Sakin jikinta tana sabawa dasu sosai.



Har lokacin Bata sake haduwa da DD kaante ba sbd kusan duk lokutan Dayake zuwa gidan Bata Nan kokuma ta shige Dan haka Sam Basa haduwa hakama bisa ga umarnin dd babba babu Wanda yayi wa Dawood din maganar yanada mata a gidan kaman yanda Shima ya nuna ya manta kokuma Daman auren Dan karban Amnah ne yayisa.


Kullum sbd Amnah yake zuwa gidan ya dauketa sai idan zai tafi zai dawo da ita,.Hakan yasaka yanzu benazir barinta wasu lokutan idan zata tafi makaranta.



***Lokaci ya Dan ja ahakan har sukai exam suka sake samun hutu Kuma alhmdllh wannan Karan karatun me nutsuwa da kwanciyar hankali takeyi.


Ababa Bai taba kiranta ba sbd kudin da dd babba ke Basa Yana dakatar dashi daga Neman Benazir sbd ta samu nutsuwan karatunta ba tsoro ko firgicinsa,


Annenta kuwa a yanzu dd babba da Kansa yake saka Abbakar Yana kaiwa Ababa ziyara Akai Akai ana dubo lafiyarta tin komai sai ahankali ake tafiyar da rayuwar.


Ababa da ake Kaiwa ziyara Akai Akai ta sakon kudi Kuma baa tura masa ta bank a hannu ake Kai masa dole ya ringa inganta rayuwar Anne sbd duk Abbakar yazo ya ringa kame kamen kada ya Gane Annen na cikin tsananin ukuba da wahala ga ciwonta ya tashi babu Wanda ya sani

Dan haka dolensa ya ringa inganta Annen da abinci da kulawa sbd yawan zuwan da ake masa.


Koda dd babba ya tabbatarda sun samarwa Anne sauki ta Hakan sai ya bawa benazir tabbacin Annenta yanzu tana cikin Aminci inshallah Dan saita Kwantar da hankalinta tayi Abinda Annen kesan tayi.




******Benazir Ababa kaante take amfani dashi a yanzu da rayuwarta ta samu sauyi Kwata kwata,


Kamanninta sun sauya sosai sbd lafiyan jiki Dana fatan dayake bayyane a tattare da ita,

Ta ciko koina Amma har lokacin batai qiba ba,

Jikinta na cikakkiyar mace a yanzu bayyane yake sbd hutu Daya ratsata ba laifi kam sosai.


Tsakaninta dasu Umme kauna da kulawa ce sosai shi kuwa dd babba baa ma fadan kaunarta Dayake a bayyane kusan bayan DD a cikin ransa yanzu ita din ce gata da Wani irin ilimi dayakesan ace 'yayan family dinsa suna dashi shiyasa yafi son Dawood tin asali sbd iliminsa da babu me shi ko a cikin iyayensa sai gashi matarsa ma ta kasance cikin masu irin baiwarsa.



Amnah da ayanzu tayi wayo tasan Daddynta kaman me sbd shine Wanda yafi Santa fiye da kowa a rayuwarsa yanzu.,


Duk Abinda takeyi idan taji muryansa  zata taka ahankali da tafiyarta da batai qwari ba taje gurinsa.


Duk Wani Abu na Amnah a yanzu shine ya siyesa,.komai nata daga fari sai black kaman yanda su kadai ne kalan Dayake sakawa hakama 'yarsa su kadai ne kusan kalan dayake Siya mata,Dayake fara ce tas kaman shine ya haifeta sai kalolin na mata kyau.


Duk wannan tsawon lokacin Basa haduwa,.daga shi har ita babu me buqatan ganin Dan uwansa Dan haka suke kaucewa haduwa da juna

Shi a nasa bangaren ma kaman har lokacin baiyi noticing nata ba.




Duk da tsawon lokacin da Basu taba haduwa suka tsaya gaban juna ha Abu dayan Daya hadasu shine kowannensu ya San qamshin Dan uwansa ko acikin qamshi nawa zasu shiga suna Gane na juna sbd Amnah.


Duk daukan dayakewa Amnah idan ta dawo hannunta qamshinsa a kame yake jikin Amnah da kayanta na turaren Caron poivre Mai Wani irin qamshi me sanyi da nutsuwa kuma duk qamshin Datake ji a mutane Bata taba Jin me irin qamshin wannan tiraren ba ko a familyn kaantes din kuwa Datake cude a cikinsu yanzu.


A nasa bangaren duk yanda baya bawa Abinda Bai shafesa mahimmanci ba Saida qamshinta dake jikin Amnah koyaushe samun shigewa Kansa Dan kuwa A jikin Amnah ne kawai yake samun wannan qamshin nata na aqua di parma da dd babba ne ya tsaya mata take amfanin da abubuwan da tsadansu bama gaskia bane a rayuwarta.


Wannan shine Wani communication da yake tsakaninsu kawai bayanshi babu Abinda yake hadasu da juna.


A bangaren Safnah kuwa tinda ta samu labarin yanada wata matar bayan ita ta daga hankalinta

Ita da mummynta suka dagawa hajiya da Daddynta harma da Umme hankalin akan Safnah ta fasa bataso Saidai ita a saketa kokuma a saki waccar dayar matar.


Umme da Alh basheer hankalinsu tashi yayi Amma suka ringa lallabata kada ma Dawood din yaji a take zai saketan ba Batawa Kai lokaci.


Da suka ga abin yaqi sauki sai dad dinta ya hanata dawowa yace tayi zamanta sai ansamu mafita.


Itama Umme amincewa tayi da Safnah din tayi zamanta tukuna su shawo kan Dawood din,

Ta Wani bangaren Kuma ita ummen tafison Safnah tayi zamanta acan kafin Dawood yafara noticing Benazir da ayanzu tafi Jin ta a zuciyarta matsayin matan Dawood akan Safnah duk da itama tana kaunar nata sosai.


Dd babba kuwa shiru yayi musu akan zancen safnah din da akace shakara Daya ya rage mata a karatu ta gama ta dawo ta tare Amma tsaban Rena hankalin mutane har shekaran ta wuce ba dawowan Safnah wadda itama ko sunan dawowanta Nigeria din bataso tafison DD din ya ringa zuwar mata can yafi mata.


Benazir ce matar Dawood a zuciyarsa Dan haka kaman yanda iyayen Safnah sukai biris da zancen dawowanta Shima yayi musu biris 

Abinda ya sani Dawood tinda ya auresu su Biyun to saiya zauna dasu.




******Benazir na gama final exams dinta taje ta dubo Annenta wadda a yanzu tana zuwa dubota Akai Akai Kuma ba laifi Annen na cikin Aminci sbd kudin da dd babba ke bawa Ababa yaha hanasa Kiran Benazir akan saita gama karatu.


Hutun sati uku tayi sukai tafiya ita da Umme da Zeenah zuwa India dad kaante yaga likita harma da Ummen daga can suka wuce Costa Rica.


Watansu biyu suka dawo Benazir Bata rufa watanni biyar ba dd babba ya turata Cairo Wani business course na shekara Daya da wata biyar Kuma ita kadai ta tafi ba da Amnah ba dan haka take cikin kewan 'yarta sosai.



******Dd babba da Kansa yaje bikin kammala business course dinta har Cairo tareda Umme hakama Zeenah data gama nata karatun a Zurich gurin DD Daya jima da komawa Shima tare suka dawo Nigeria

Motocin dasuka je daukosu suna harda Abbakar Wanda yayi farin cikin dawowarta sosai sbd kaunar Dayake mata Shima kaman shine ya haifeta.


Amnah na ganin mummynta tazo da gudu cikin farin ciki ta maqale ta tana  cewa


"Mummy" cikin muryanta na Yara.


Rungumeta benazir tayi tana sake kyakyawan murmushin Daya qayatar da kyakyawan fuskarta ahankali cikin tsananin kaunarta tace


"Oh my, I missd my baby so much"


Dariya Amnan tayi tana sake maqale mummyn tata tana cewa


"Where's my daddy?"


Murmushi Benazir ta sake tana shafa fuskarta tace


"Baki ga Aunt Zeenah ba tana kallanki tayi missing naki sosai itama."


Gurin Zeenah din tayi da gudu ta fada jikinta tana mata oyoyo itama.


Umme dake dariyarsu tini tayi hanyar bedroom dinta a Dan gajiye tana cewa


"Daddynta kawai take tambaya yarinyar Nan"


Dakunansu da aka gama gyarawa suna sanyin qamshin suka nufa kowa yayi nasa 

Amnah na biye da Mummynta cikin tsananin farin cikin ganinta.


Ta sauya skin products nata zuwa Aesop Dan haka su ta fitar cikin kayanta ta Jere toilet kafin ta tube tayo wanka ta fito daure da blue towel   Brown skin dinta na daukan idon sheqin hutu da lafiya.


Mai Tai shafa sama sama ta fesa spray na turarenta ta saka pyjamas farare tayi sallan magrib da Akai a daki tasaka Nafisat ta kawo mata abinci taba fito ba tanayin ishai ta kwanta bacci.



Washe gari dukkaninsu kowa a daki yayi breakfast suna gamawa ita Kuma ta fita taje gurin dd babba daga can da kanta taja mota zuwa gidansu.


Ba laifi Bata samu Annenta cikin wahala ba Dan haka ta samu nutsuwa a can suka wuni ita da Amnah sai yamma suka dawo.


Tana parking suka fito kafin ta rufe motar Amnah ta saki hannunta da gudu ta nufi bayanta tana Kiran


"Daddy"


Ya Riga ya kawo bayan kaman yanda Shima ya Riga iso hanyar Dan haka tana juyowa akan fuskarsa idanuwanta suka sauka ta dauke Ido ahankali sbd kullum fatarsa qara daukan Ido takeyi.


Juyawa tayi zata bar gurin sbd Amnah tace


"Mummy ga daddynah ya dawo"


Cak ta tsaya tareda damqe handbag din dake hannunta ta juyo ahankali cikin nutsuwa da muryarta me taushi tace


"Sannu da dawowa."


Bai taba dagowa ya kalleta ba sai ranar sbd ranar ne yafara Jin qamshin aqua di parma a daga jikin nata direct ba daga jikin Amnah ba.


Kallan da yayi mata ya sakata Dan daga qafa zata bar gurin Amnah ta sake kiranta tana cewa tadawo kar tabarsu itada Daddynta a baya.

#MAMUH

No comments