Breaking News

ZAFIN KAI 45

 _Arewabooks@Mamuhgee_*

45


Benazir kasa ko motsawa tayi da maganganunsa hakama Anne data biyo bayansu ta tsaya daga wajen palon tanajin duka Abinda yake fadawa Benazir tayi qasa da kanta tanajin inama itama ta mutu ya rasa Abinda zai juya rayuwar Benazir a gidan aurenta ta samu tayi rayuwar kwanciyar hankali kaman kowa.


Wani Abu me nauyi ne ya tsaya kirjin Annen tana Jin jikinta na sake sanyi tinda masifar Bata qarewa benazir ba kenan,.Tayaya zata taimakawa 'yarta qwalli Daya data rage mata a duniya?

Tayaya zata Hana Ababa juya rayuwar Benazir a gidan aurenta.


Wani numfashi ta sauke ahankali hannuwanta na Dan rawa daga tinanikan da zuciyarta ke Bata.


Benazir kuwa numfashi itama ta saki boyayye Wanda yasakata qarasa sarewa daga duniyan gabaki Daya hakama tinaninta ya koma empty Bata ma iya Gane komai yanzu bayan maganar Ababa dake ta amsa sauti cikin kanta.


Kaman makauniya haka hande ta sake kamata ta tayar suka fito 

A lokacin ne suka tadda Anne a kofa wadda ta share hawayenta daga idanuwanta da babu sauran hawaye Kuma.


Ga mamakin hande Anne da kanta ta amsa Benazir ta nufi daki da ita ta shiryo benazir din da itama Bata iya komai sai yanda Akai da ita.


Duk yanda hannuwan Anne ke rawa sosai gurin shiryata Benazir na ji Amma Bata iya ko motsawa bare kallan Annen har suka gama ta itama ta sake shiryawa ta dauki Amnah da ta shirya itama ta dorawa benazir din a jiki ta rungumeta ahankali ta suka miqe Anne da riqe da hannun benazir din Daya suka fito.


Hande kallan mamaki takewa Anne data nuna qarfin hali da juriyar shiryo Benazir ta fito da ita da kanta.


Ababa baiyi Wani mamaki ba Dan yasan dole suyi Abinda yace din,


Baiyi mamaki ba sai lokacinda Anne da kanta ta Bude baki tace zata raka Benazir har gidan aurenta idan anbata dama.


Shiru Hande tayi tana kallan Annen Shima Ababan kallanta yayi Yana Maida kallansa gun hande yace


"Ciwonta Daman ya tashi ne shine baku fadamun ba?"


Lumshe idanuwa Benazir tayi batareda ta motsa ba 

Itama Anne Dan rufe idanuwan tayi ta Bude ahankali tareda girgiza Kai cikin sanyi tace


"Bai tashiba lafiyata kalau,kawai so nake na Rakata din sbd bansan yaushe zamu sake ganin juna ba."


Kallanta hande tayi zatayi magana cikin fada Ababa ya katseta da cewa barta ta tafi din tinda Daman ba kowa ne ze raka Benazir din ba ke kince bazaki ba gwara ita ta rakatan.


Da wannan hande tayita fadan waye ya taba ganin uwa ta Raka 'yarta gidan miji sai akan Annen wadda ita ta tabbatarda haukarta ce ta tashi shiyasa,Daman idan bakada hankali komaima zaka iya Yi.


Anne kuwa hannun Benazir kawai ta kama Bata dago Kai ga fadan hande ba suka fito.


A BMW 7-series aka Aiko Abbakar daukan benazir tareda mum Khadija wadda da kanta ta amso benazir Suka shigo mota harda Anne wadda dukkanin jikinta rawa yakeyi da Abinda yake zuciyarta datasan zai iya zama sanadin rayuwarta Amma tayi na'am da hakan Koda ta rasa ranta tasan ta taimaki 'yarta takuma tseratar da ita inshallah ta yanda ko bayan barinta duniyar Benazir zata rayu cikin aminci da kwanciyar hankali.


Har suka Isa babu me ko motsi bare magana a motar.


Tin a gate din farko jikin Anne ta tsananta rawa numfashinta na fita da sauri maqoshinta na bushewa tana Jin kanta na juyawa kaman ciwonta zai tashi Dan kusan duk ta fita Hakan takeji matiqar ba komawa gidan Ababa tayiba.


Daga benazir din har Anne babu Wanda hankalinsa da tinaninsa yake kan aljannar duniyar dasuka shigo sbd kusan babu Wanda yake hayyacinsa cikinsu.


Zeenah ce da wasu baqin suka fito suka tarbi benazir Amnah na hannun Mum Khadija suka karbeta cikin farin ciki sukai ciki suna mantawa da Anne dake mota, benazir Kuma Daman babu Abinda take Ganewa sbd kanta ma Dayake Neman juyewa duk inda Akai da ita can take zuwa.


Anne data kasa fitowa hannuwanta da qafafunta na tsananta rawa Wani busashen yawu ta hadiye daqyar kafin ta Bude baki muryarta na rawa tana kallan Abbakar daya Bude mata motar Yana jiran fitowar ta tace


"Inason zanyi magana da dd babba Dan Allah ka mun iso"


Kallanta Abbakar ya juyo yayi cikin mamaki da tinanin lafiya Kuma bayan anyi musu Abinda suke so an auri 'yarsu.


Kaman zai Bata hakuri akan Hakan sai Kuma dai ya Ciro wayarsa ya kira wayar dd babban ya sanar masa Abinda yake faruwan.


Shi Kansa dd babba shiru yayi Yana nazari sbd baya buqatan ganin kowa yanzu Yana Dan fama da jikinsa da isashiyar lafiya na duk tashe tashen hankalin da akaita shiga a Dan lokacin dakuma auren da aka daura yau Dan haka yace baya buqatan ganin kowa.


Yanda jikin Anne ke rawa tana cikin matsanancin tsoro da ficewan hayyaci ya saka Abbakar cewa ta sanar dashi sakon zai isar mata.


Rawa jikinta ta tsananta ta kallesa tana tattara nutsuwarta ahankali tace zancen yanada mahimmanci sosai dd babban kawai zan iya fadawa gameda gaskiyar haihuwar Benazir ne.



Da sauri Abbakar ya dakatar da ita Yana juyawa koina sbd kada Wani ya jisu yace ta fito ta biyosa.


Kai tsaye palon dd babba ya nufa tana bayansa qafafunta na hadewa cikin tsananin tsoro da fargaba tareda zuciyarta dake hanata Amma bazata iya barin Benazir dinta ta gidan rayuwar aurenta cikin tsoron ranar bayyanar gaskia da Ababa ya ringa juyata kaman babyn roba ba duk da tasan hukuncin Hakan mutuwa ne gareta idan Ababa yaji.


Suna shiga palon Abbakar ya sakawa kofar key ya nuna mata guri ta zauna ya wuce ciki Dan sanar da dd babban.


Zaune take Amma duk sakan zuciyarta dap take da Faso kirjinta ta fado,

Hakama rawar da qafafunta da hannuwanta keyi qaruwa takeyi.


Fitowa dd babba yasakata sauke Kanta qasa Hana Dafe hannuwanta dake qara rawa sosai kirjinta na bugawa.


Zaunawa yayi ahankali cikin nutsuwa Ya dago ya kalleta yana ganin yanda jikinta ke kakkarwa gabaki Daya da alama tana cikin mawuyacin hali na shakkan Abinda zata fada Daya danganci gaskiyar haihuwar data fada.


Shi Kansa zuciyarsa Neman sauya masa tinani takeyi sbd son sanin wace gaskiyar ce take magana Akai.


Daga ita har shi kasa gaisawa sukai da juna ahankali ta Bude baki tafara da fadin Asalin maraicin data taso acikinsa zuciyarta na rawa hawayen Datake riqewa suna cika idanuwanta Amma radadinsu ya hanasu saukowa fuskarta.


Halinda dasuka taso ita da 'yayanta tafara jero masa muryanta na rawa Yana iya Jiyo quncinta da rashin madafarta a muryarta.


Yanda yayanta suka mutu Daya bayan Daya ta fada masa tareda saukowa qasa ta zube gabansa sai alokacin hawayenta masu tsananin zafi suka sauko ta fada masa gaskiyar haihuwar Amnah tareda fashewa da Wani irin Kuka tana rokonsa akan Benazir marainiyar da batada kowa saisu a yanzu ce.


Barazanar da Ababa zai ringa yiwa Benazir da ita ta sanar masa tareda sake fashewa da Wani irin Kuka mara sauti da radadin zuciyar Datake cikin qunci ta rokesa akan Amanar 'yarta benazir.


Tinda dd babba yayi gwagwarmayar rayuwa bai taba ji ko ganin Abinda ya tayar masa da hankali ba kaman abubuwan da yaji daga bakin mahaifiyar benazir ba,


Wace rayuwa take fada tayi itada yayanta kaman dabbobi,

Wane irin Uba ne mahaifi wannan Ababan?


Hankalinsa mummunan tashin dayayi yasaka nasa hannuwan rawa Shima ga Wani sabon tinanin tashin hankalin Daya shigesa akan maganar rasuwar sumayyah da Bilal dasuke dauka shi kadai ya rasu gashi yanzu da ana sanar dashi tareda sumayyah ya gudu,

To Yaya Akai gawa Daya aka Gani a motar,

Meyasa tinda Bilal ya rasu Basu taba ganin drivernsa ba Wanda kusan kullum Yana tareda Bilal din.


Me Hakan ke nufi?

Qaddara ce wanna ko Amanar Benazir ne da Allah yakeson damqa masa a hannuwansa sbd tinda ya karbo aurenta yakejin kaman shine gatanta Dana 'yarta.


Abbakar da Shima duk jarimtarsa Saida ya kasa motsawa daga inda kowannensu yake sbd sarawa Ababa takoina daga kafircinsa gashi a dare Daya Anne ta wargaza masa game dinsa ta shekaru.


Numfashin Dd babba sama sama yake Neman Yi 

Da gudu Abbakar ya dauko magani jiki na rawa ya Basa tareda ruwa Yana Dan masa firgita duk da akwai sanyin AC Daya cike palon.


Ajiyar zuciya da numfashi Mara karfi yayita saukewa tsawon lokaci Yana kokarin samun relief na attack dayake kokarin sake samu.


Tsawon mintina kafin ya iya dagowa da idanuwansa dasukai jajir ya Kalli Anne da Abbakar a hankali yace


"Wannan maganar zata tsaya a Nan tsakaninmu kada Wanda ya San gaskiyar ba Benazir ce mahaifiyar babyn Bilal ba sbd zata rasa kaunar data fara samu daga family,

Ni kadai ne nasani Kuma ni kadai zan sani har sai lokacin da nagama bincike akan gaskiyar rasuwar Bilal da sumayyah.....


Kallansa ya Maida akan Anne da ko numfashi Bata iyawa daidai sbd kukan datayi na tsawon shekarun Datake ajiye da maganar rayuwar dasukai da yayanta batada Wanda zata fadawa 

Yau ta fada taji Wani nauyi ya ragu a zuciyarta tana fadan Hakan yazama silar samun yancin benazir dinta da 'yarta a cikin Kaantes.


Cikin dauriya da Bata Wani irin radadin da dd babba keji a zuciyarsa game da dukkanin zancen ya sake kallan Anne yace


"Nayi Miki Alqawarin zama gatan benazir Koda auren jikana ko Bada aurensa ba sbd gaskiyar ki da maraicinku gabaki Daya,

Ababa ya rasa benazir har abada bazai sake samun damarta ba matiqar Ina Raye,

Benazir ta Riga ta zama kaantes daga lokacinda na amsa aurenta wa jikana Dan haka kije adduar samun zaman lafiya da mijinta kawai Zaki mata Amma wahalarta ta qare inshallah.


Wasu hawayen da Anne Bata taba yiba masu sanyi ne suka gangaro mata ta kasa magana sai sunkuyar da kanta datayi qasa tana tana tare hawayenta da tafukan hannuwanta zuciyarta na samun sukunin da ko mutuwa tayi yanzu batada damuwa.


Kirjin dd babba dake nauyi da zafi ne yasaka Abbakar Yi Kansa Yana kokarin kamasa

Dd babban ya dakatar dashi Yana cewa


"Ka maidata gida batareda kowa yasan na ganta ba."


Da sauri Abbakar din ya Kalli Anne yace su je.


Hawayen godia kawai Anne ta sakarwa dd babba batareda ta iya magana ba har suka fice.


Bata shiga cikin gidan ba Abbakar ya juya da ita zuwa gida a mota tana hawayen bankwana da Bena dinta da batasan ranar da zasu sake haduwa ba.


Kaman yanda dd babba yace kada kowa yasan sunyi magana dakuma alqawarinsa dayayi mata akan Bena yasa Koda ta dawo zuciyarta na da qwari da sukuni Kai tsaye daki ta shigewarta tana Hana kanta hawayen rashin Bena Amma takasa riqe kanta da fasa kukan yau ta wayi gari yanda tazo ita Daya gidan babu 'yayanta ko Daya a tareda ita.



Abbakar kuwa Yana komawa hankali tashe yadawo gurin dd babba da jikinsa ya rikice gabaki Daya cikin qanqanin lokaci ya sanar dasu dad kaante aka kira likita 

Shima Dawood dake gidansa anyi sa'a ya kunna wayarsa lokacin aka sanar dashi dd babban ba lafiya sosai dole ya fito da Kansa ya dauko key din mota ya tuqo da kayan jikinsa na gajeran Nike three quarter da sleeveless hoodie shirt ya nufo kaantes din.

##MAMUH#

#LOVE

#HOTHOT

#DBENA

#BABY MAMAH

#MARRIAGE

#SAFNAH

No comments