Breaking News

ZAFIN KAI 39

 39


Dd babba ne ya shigo dad kaante na bayansa suna kallan Ababan a tare sbd Jin Abinda ya fada zuciyoyinsu na karban sakon nasa da sanyi batareda sun ankare ba.


DD kuwa Dan rintse idanuwansa yayi Shima a hankali sakon na sanyaya zuciyarsa duka batareda sun saniba Dan kowa tashin hankali yasa sun manta da akwai jinin da Bilal ya bari duniya,


Sun cire Rai daga samun Abinda zai dawwamar musu da kaunarsa da soyayyar da suka kasa nuna masa sai gashi Allah ya dawo musu da jinin Bilal tsatsonsa.


Daga dd babba har dad kaante suna zaunawa kallan Ababa Dayake star kallansu Daya bayan Daya sukai 

Dd babba na sake sauke ajiyar zuciya a Karo na babu adadi sbd Bayajin Dadi sosai tin lokacinda rasuwar Bilal din ta riskesu babu me isashiyar lafiya a gidan.


Ahankali dd babba ya Bude baki yace


"Abinda aka samu din lafiya take itama?"


Gyada Kai Ababa yayi cikin zumudinsa Dayake boyewa Yace


"Lafiyarta kalau daga ita har uwar"


Umme ce ta Bude baki cikin hawaye masu sanyi ta zube gaban dd babba cikin bayyanarda quncin ranta da qanqantar da kai tace


"Babba Dan Allah a kawo min Babyn Bilal ni ta kowace hanyar aka sameta Ina sonta a hakan,

Ina buqatan ta a hakan,

Zan reneta a hakan,Dan Allah kabada Daman a kawo min ita sbd ita kadai ce jinin Bilal dazata maye mana gurbin Daya bar mana....kukane yaci karfin Mai qaramin sauti da cin zuciya.


Dad kaante ma kallan dd babba yayi cikin rashin qwarin gwiwa Dana jikinsa da ba lafiyar Shima yace


"Ta hanyar dawo da ita Nan zamu ingatanta rayuwarta yanda ya dace harma da Hana kowa sanin matsayin nata tinda da Yana Rayen a yanda kayi alqawari ranar sunanta ranar daurawa iyayenta aure."


Shiru dd babba yayi Yana sauraronsu Wanda ko Basu roqa din ba a yanzu da Bilal baya duniyar bazasu banzatar da jininsa Daya qwal Daya bari ba a duniyar sbd jininsu ce Kuma itace a yanzu zata maye gurbinsa a zuciyar mutane da yawa a familyn.


Ababa zufane ya fara tsatsafo masa cikin rigarsa Yana kallan bakin dd babba yaji Abinda zai fada akan roqon iyayen Bilal din.


DD ne ya katse musu zancen Kai tsaye a natse da cewa


"Akwai buqatan Wani tinani ne Daman akan dawowan babyn hannun mu?"

Muna buqatan sai muyi nazari ne akan Hakan?

Kai tsaye daga lokacinda ya fado duniya ita din ta zama kaantes,

Akwai dalilin barinta Wani gurin ne daga lokacin da ta amsa sunan?


Shiru iyayensa sukai sbd shi Daya ne Daman yake fadan maganarsa a tsaye gaban dd babba ba acikin raini ko rashin daa ba Amma shi Sam baya kwana kwanar magana ko inane kuwa yinta yakeyi Kai tsaye ta gaskia da gaskiarsa.


Ababa kuwa Jin ana nanata maganar karban baby dai,baby dai baby dai sai kawai ya Dan gyara Yana kallan DD Da kyakyawan fuskarsa yake a kame duk da idanuwansa sun Dan fada a kwana dayan.


Dd babba cikin sanyi ya Bude baki cikin Yana kallan Ababa yace


"Kaji dai ko malam Ababa?

A kawo mana yarinyar zamu karbeta tinda dai a yanzu mutuwa ta shiga tsakani Allah beyi zamu cimma manufar hada iyayenta aure ba.


Hummmmmnnn" Ababa ya sauke Wani boyayyan numfashi Yana Jin Kansa na daukan zafi Amma dai ya daure yana daidaita Kansa.


Dagowa yayi idanuwansa taf da hawayen da baisan lokacinda ya janyosu take ba.


Cikin rawar muryar sautin kukan Dayake daurewa ya kallesu su dukan yace


"Wace jaririyar zaku karbe?

"Yar dake jikin uwarta zaa rabasu kwana daya da haihuwa?

Anyiwa "ya ta adalcin rabata da 'yarta  acikin wannan halin Datake ciki na rasa mijin aurenta?

Tayaya idan tayi aure Nan gaba zata kasa nunawa mijinta tana da wata 'yar a Nan?

Wannan zancen ai bazai binnu a Hakan ba,

Abar mana babyn Nima Ina kaunarta zan rungumi kaddara mu Reneta idan uwarta ta samu Muji zuwa gaba tayi aure taje da ita can sbd bazamu bar 'yar ta tashi babu Uba ba anan ne zaa San Yaya 'yar take Kuma waye ubanta Koda baya Raye,

Idan mutane suka shegantamun jika kokuma shi Wanda uwarta zata aura wataran ya sheganta mini ita nayi muku alqawarin bazan bari ba zan dauki mataki Kuma zan kula sosai da wannan babyn Amma kuyi hakuri bazan iya bari ku qwace mana ita ba a rabata da uwarta bayan wahala da gwagwarmayar da uwarta Tasha daga renon cikin zuwa haihuwarsa.


Yana gama fadan maganganunsa ya musu gaisuwar Bilal tareda sallama ya fuske ya juya Yana share hawayensa alaman iya gaskiarsa yake fada a matsayin Uba Kuma kaka.


A zuciyarsa kuwa qyam yake sbd yasan madokarsu Kuma itace ya doka Dan haka gida zai komawarsa Yana zaune zasu sake nemansa da yardar Allah.


Yana ficewa hawayen Umme suka qara gudu ta miqe tana ganin jiri tabar palon zuciyarta na nauyi.


Dad kaante ma kallan dd babba yayi jikinsa na mutuwa da zantikan Ababa Amma Kuma koma mene Suma suna buqatan 'yar ai a matsayinsu na kakanninta dasuka rasa mahaifinta.


Dd babba kuwa Jin Ababan kawai yayi Dan kuwa maganar komaima Bata tasoba yarinya bazata taba zama a wajen kaantes ba.


DD ma ficewa yayi daga palon sbd a nasa bangaren Shima yasan maganar barin jinin Bilal dinsa a Wani wajen ma har ana lissafin zuwanta agolanci tin yanzu ai baima San Hakan ba.


Babyn tagama dawowa hannunsa saidai uwar babyn ta hakura.


Ababa kuwa Yana fita Zeenah ta fice da driver suna fitowa ta karbi key tace ya jirata a hanya zataje ta dawo.


Bayan Ababa Zeenah tabi tiryan tiryan har gidansa.


Saida ta Dan jima a gurin cikin mota ta tabbatarda gidan ne kafin ta juya motarta tabar gurin.


Driver ta dawo ta dauka suka koma gida Kai tsaye gurin umme ta nufa daki ta sanar mata da ta gano gidan maman Babyn Bilal din.


*****Ababa na Isa gida shigewa yayi ya zauna palonsa ya rufe kofa ya fara warware tinani da abubuwan dake cikin qwaqwalwansa Dan ya huta shi Kansa sbd Kansa ya gama daukan zafi ya dauko maganar da baisan inda zata Kaisa ba tsakanin Ababa da Nobaba.


Amma dai koma yayane a mutu ko ayi Rai babu Wanda ya haifi wannan babyn idanba benazir ba ko duniya ma bazai yarda ta saniba bare kaantes.

Karatunta kuwa daga wannan lokacin babusa Dan kuwa haihuwa tahau kanta,


Su kuwa kaantes ba hawan jini suke fama dashi ba ko saukan jini ne bazai bayarda babyn ba matiqar bada uwar babyn zasu amsa ba.


Benazir da Anne a daki kuwa zaune suke shiru babu komai sai jaririyar dasuke lallabawa kaman Basa son ko motsata sbd so da kulawa.


A yanda rasuwar sumayyah tazo musu da har ita har babyn suka rasu da ba lallai su samu qarfin wannan tawakkalin ba Amma Suma kansu a yanzu sunsan Wani irin dangana ne da Basu taba tinanin zasu iya samu ba Allah ya Sako musu.


A jikin benazir babyn take kowane lokaci sbd ita yanzu so na tamkar itace ta tsuguna ta Haifa babyn takeji Wanda Daman ko sumayyah na Nan tasan zata mata wannan son,yanzu Abinda yasa yafi qarfi da tsanani sbd batada uwa batada Uba sai su kokuma tace sai ita tinda Anne Allah ne kawai yasan yaushe da yaushe ne take daidai bare ta nuna mata soyayyar kaka.


Saidai Abinda Bata saniba ba kaman yanda take Jin yar cikin tsakiyan ranta kaman sumayyah ce a hannunta haka Anne ke Jin 'yar itama cikin ranta kaman sumayyahnta ce ta dawo musu a matsayin jaririya Dan haka kallan 'yar kawai idan tayi sai taji zuciyarta na Neman narkewa ta fashe da kuka shiyasa take Dan dakatar da kanta tana barwa benazir sbd itace uwarta a yanzu da babu sumayyah Dan tanada tabbacin akanta benazir babu sadaukarwar da bazata iyaba a ciki gidan tinda Suma dasuke manyan tana musu tin baya.



Sai yamma Ababa ya fito bayan ya cire kayan dayaje dasu kaantes ya Sako wainda yafi sabawa da sakawa na yadika marasa nauyi su kuwa idan zasu uwar shadda yakesha harda babban Riga sbd nuna mutincin Kansa.


A tsakar gidan ya janyo kujerarsa ta roba ya zauna gefen hande da itama zamanta kenan tsakar gidan kan tabarma ta fito Tasha iska sbd Kuma ta kasa ta tsare Basa buqatan bako kowane iri ne Dan kadama a ankare da halinda suke ciki na haihuwar banza a gidan.


Ita yanzu fatanta tinda sumayyah ta rasu tabarwa su benazir 'yar so take Ababa ya samowa benazir koma waye ya daura mata aure dashi benazir ta tafi da 'yar can su qarata gidan auren a huta kada yarinya ta girma jamaa su rasa inda aka samota idan Kuma auren bazai yiyuba to gwara tin wuri ace Anne ta haihu ta yanda ko yar ta girma babu Wanda zai San shegu suka fara haihuwa a gidan Suma Dan daga wuyan dasukewa mutane ya fadi.


Shi dai Ababa duk tinanin hande nata ne kawai nasa tinanin da burin daban Kuma nasan shine magana tinda shine me Yanke yanda yakeso ayi.


Abinci yayi Kiran Anne ta fito ta kawo masa sbd Bai samu Daman cin abincin Rana ba Yana ciki Saida yagama lissafe.


Ajiye masa abincin tayi zata bar gurin ya Kalli kofar dakinsu yace 


"Uwar me benazir takeyi a ciki da 'yar Amanata duk sai zafi da sauro ya cinyeta daki kaman dakin boka tsabar duhu da kaya."


Ahankali Anne ta Dan kallesa kafin ta Bude baki tace


"Idan anfito da ita waje akwai sanyi zai iya kamata"


Ajiye abincin Daya dauka zai fara ci yayi ya Kalli hande data matse fuska yace


"Wai hakane hande?"


A siqe handen tace


"Eh Amma Kuma ai da uwar datayi naqudar 'yar ce zaa ce kada ta fito dakin sanyi zai iya shigarta......


Katseta Ababa yayi Yana dire abincin hannunsa da qarfi yace


"To waye ne yace uwar datai naqudarta ta haifeta Bata gidan.?


Da sauri dukkaninsu suka miqe suna waiwaye hande cikin fargaba da tsoro Anne kuwa cikin mamaki da firgicin itama 

Hakama benazir take ta fito dakin rungume da babyn Yana raba idon son ganin sumayyah da Ababa ke maganar.


Kallan benazir data fito yayi yana sake fuska sbd lissafinsa da gabaki Daya yanzune zai hau daidai idan komai ya tabbata yace


"Kunga uwarta Nan wadda tayi cikin tayi naqudar Kuma ta haihu"


Page 40 👇👇👇👇👇

#MAMUH#

#BENA

#DD KAANTE

#KAANTES

#AMNAH KAANTE

#SAFNAH

#LOVE/ROMANCE

No comments