Breaking News

ZAFIN KAI 28

 Arewabooks@Mamuhgee_*

28


Ganin security din na sake nufosa ya sanya Ababan zubewa ya zauna gefen Dd babba Yana sake Dan saita muryarsa cikin nuna nutsuwa da mutuntuwa ahankali Yace


"Ranka ya Dade gurinka nazo tin safe an hanani ganinka a waje na wuni tsaye har Rana ta fadi akaina,

Alhaji ka saurareni maganar danake tafe da ita Mai tsananin girma da mahimmanci Ce sbd maganar Rai da mutuwa akeyi data shafe ahalinka da nawa ahalin."


Kalmarsa ta qarshe Ce ta Saka Dd babba waiwayowa ta kallesa tinda ya fara magana bai juyoba,


"Maganar Rai da mutuwa tsakanin ahalinsa dana kaantes?


Daga Ina wannan din yake?

Lafiyayye ne ko kuwa?" Shine kallan da Dd yayi wa shugaban securities na gidan nasu kafin ya maida kallansa kan Ababa Dake a shirye qyam zantikansa a tsare tsaf cikin ransa da zai jero.


Ganin kallan da Dd ke masa yasa take yayi fuskar tausayi da bacin Rai tareda bayyanarda baqin cikin rayuwa na tareda shi kaman Wanda yayi rashin uwa da uba da kowa na duniya.


Cikin nutsuwa Securityn ya Dan matsosa Yace


"Bismillah malam ko¿Mu Dan je daga waje sai naji abinda ya kawo ka zaa duba matsalarka,muje Bismillah.


Girgiza kai Ababa yayi cikin sake bayyanarda Yana cikin balai da masifar rayuwa Ya sake Maida kallansa kan Dd babba dayake shafa adduarsa daya gama Yace


"Ranka ya Dade Dan Allah ka saurareni,

Kai kadai ya kamata yaji matsalar data kawo ni,

Ina cikin tashin hankali da masifar da bazan iya kallan jamaa ba,

Ni nawa mutuncin ya Riga ya fara rauni a idan duniya,

Banda zabi ne shiyasa nazo Dan kaima kasa muguwar tsautsayi ko kaddara zance data faru tsakanin 'dan gurinku da 'ya.....


Bai qarasaba Dd ya juyo ya zuba masa idanuwansa masu kwarjinin arziki da dattako sbd a duniya idan akwai abinda Dd babba ya tsana Ji shine hada Kalmar

"wani abu ya faru tsakani"


Ababa kuwa sake qasqantar dakai yayi idanuwansa na bayyanarda hawaye masu bayyanarda radadi da zafi tareda quncin rayuwar tsaka me wuyar dayake son nunawa Dd babba Yana ciki.


Shiru Dd babba yayi tsawon mintina Yana nazarin Ababa da kukan dayake Yi a matsayinsa na dattijo kafin ya dago kalli Securityn Dake tsaye a kansu cikin nutsuwa Yace

"Ba komai kaje kawai"


"Yes Sir" Yace tareda kallan Ababa ya juya ya bar gurin ya fice masallacin gabaki daya.


Saida securityn ya fice gabaki daya 

Dd babba ya Dan sake kallan Ababa Bai basa Daman magana ba sukai shiru sai da limamin masallacin ya gama nasa lazimin ya fice ganin alaman magana zasuyi Kila Mai mahimmanci musamman duk Wanda yasan Dd babba yasan baya wasa da tattali da Hana kowa yaji sirrin ahalinsa,

Bai yarda ko yayane wani yaji sirrin kaates ba sbd a yanda suka kafu Allah ya girkasu da sanin sirrinsu Kawai zaa iya ganin an rusa su,

A baya hakan yaso faruwa dasu Amma ya tsaya tsayin daka Allah ya taimakesa ya Hana matsalar rusa ahalin daya wahala yagina,

Ginin da har jikokin jikokinsa inshallah bazasu San meye talauci wahala da quncin Rashi na arziki ba saidai wata jarabawar ta rayuwa daga ubangiji.


Kalman Ababa ta cewa "wani qaddara ko tsautsayi tsakanin ahalinsa na kaantes da nasa" ya sakasa basa Daman sauraransa dan farajin koma menene idan ba mahaukaci bane lullube a cikin kaya Bai sani ba.



Bayan ficewan malam liman Dd babba ya Dan sake kallan Ababa daya share hawayensa hannuwansa na rawar tashin hankalin dayake tattare dashi da damuwa ya sunkuyar da Kai cikin rawan murya wani kukan na son sake zuwar masa Yace


"Ranka ya Dade 'dan gurinku Alh Bilal kaante Yana soyayya da 'yata bansaniba sai cikin qaddara kwatsam muka tsinta a jikinta,

Ranka ya Dade ku taimakeni kumin Rai wlh mutuwa zanyi idan ta haife wannan cikin a gida,

Bazata taba samun mijin aurena rayuwarta ta lalace,ta gurbace,ta nakasa,ta.....Jin shiru ba motsin Dd babba ba maganarsa ya Saka Ababan dagowa Ya kallesa kafin yaci gaba da bayaninsa.


Kallansa Dd babba keyi cikin wani irin yanayi na mamaki da Hana zancen kaiwa zuciyarsa bare shiga cikinta,

Yama rasa yanda zai juya zancen bare ya karba cikin Kansa Dan haka ya Dan sauke numfashi a hankali Yana Dan gyara zamansa sai alokacin ya Bude Baki cikin nutsuwa yace


"Meye sunanka?

Daga Ina kake?

Kasan Bilal kaante din Da kake magana akansa?

Ka taba ganinsa a zahiri?

Maana ka taba ganinsa tare da 'yar taka?


Wani zufa ne ya yankowa Ababa Amma Kuma a yanda ya zo ba gudu ba ja da baya wlh sai ankarba cikin yarsa ko kowa yasan Dan kaantes yawa yarsa fyade.

Dan haka sake tattaro nutsuwa yayi cikin daidaita murya Yace


"Sunana Ababa Sulaiman,

Daga kauyen bairi iyayena suke ni anan na tashi anan nake zaune da iyali na,

Alhaji Bilal din Kuma ban taba ganinsa ba a zahiri,

Amma ita ta san shi farin sani,

Ni dai rokona A yimun adalci ya duba lamarin sbd nine a cikin cutatarwa da qunci da bacin Rai,

'yata na asibiti yanzu haka Rai hannun Allah..



Shiru Dd babba ya sake Yi sbd zancan yafara basa mamaki da shakku Kuma,

Meye hakan yake nufi?

Ciki Bilal yaiwa wata ko me?

Sam ba halinsa bane,

Baya kula mata ma bare nemansu da fasiqanci,

Tayaya Rana tsaka haka kawai kaman almara kokuma aikin rashin hankali azo masa da zancen bama yanzu ne ake zarginsa da laifin kebewa da macen ba aa cikin ma gabaki daya aka zo da zancen har ansamu,


Wani nannauyan numfashi ya sauke zuwa lokacin zuciyarsa tafara sauyawa duk da haka dai zancen sam Bai shigesa ba bare karbuwa 

Yafara saka Ababan a jerin batan hanya yayi kokuma ansamu kuskuren gurin zuwa sbd sunan Kila yazo daya da wani Bilal din ba nasu ba.


Amma baya garage Sam a rayuwarsa Dan haka komai nasa yake yinsa a tsari da lissafi Shima kaman Ababa saidai nasa lissafin daya baya wasa dashi shine akan suna da mutuncin ahalinsa, sbd yayansa uku duk Maza Babu qaramin mutum a cikinsu,har senator akwai aciki hakama jikansa daya Minister ne tayaya zai bari mutuncinsu da sunansu ya tabu daga shi har 'yayansa qasa zasuyi Harma da sauran jikokinsa Dake dake cikin lokacin nasu sunan da mutuncin tinda sun zama Manyan mutane suma Dan haka lissafi indai akan ahalinsa ne baya batan lissafi ko garaje.



Kallan Ababa yasake ya sake sauke numfashi Mai dumi kafin Yace


"Ba damuwa naji zancenka,

Zaa warware Maka kuskuren fahimtar da aka samu akan lamarin duka,

Bilal kaante dakake Ji daban Wanda yanzu kake magana akansa daban,

Allah ya tsare gaba ya kare Yakuma shirya mana yayanmu duka,

Wannan sabanin fahimta ne kayi.


Da sauri Ababa ya Bude Baki zaiyi magana Dd babban ya dakatar dashi sbd shi ko sunan zancan baisan ana dangantawa da Bilal din dan ma dah da DD aka danganta zancen bazai iya danne bacin ransa ba ko Hana fushinsa bayyana akan wannan mutumin.


Miqewa yai tsaye a hankali cikin nutsuwa Yace Ababan ya biyosa

Suka fice masallacin zuwa cikin gidan Kaantes din.


Abinda yasa zai tafi da Ababan dan warware masa fahimtarsa da tinaninsa akan ya cire zancen sunan kaante ne kwata kwata acikin zancen basuda alaqa ko daya da maganar.


Securities na ganin Ababa bayan Dd babba suka Dan taso Dan dakatar dashi Amma Dd ya dakatar dasu Yace su barsa kawai zai gansa ne.


Ciki suka shige Kai tsaye 

Gate din na farko yasa hankalin Ababan tashi suna shiga gate na biyu asalin Inda harabar gidan take makekiya komai a tsare da kyau da aji kaman ya baro qasarsa yaji,


Motocin dasuka kunce masa lissafi yake kalla idanuwansa kaman zasu fado qasa,


Take lissafinsa gabaki daya kwata kwata ya kunce wlh bazai yarda ba cikin nan ya zube,

Idanma ya zube bazai yarda ba sai anbiyasa diyyar keta haddin yarsa da dirka mata cikin farko ba aure.


Wata firgita ya sake Yi lokacinda suka Isa office din Dd babban Dake cikin gidan Dake gefe daya daga bangarensa dayake farko farko.


Sanyin Ac daya tarbesa yasaka shi Saka lissafin Ac take a budget dinsa na gaba cikin abinda zaa kasafto masa.


Italian office set din dasuka qayatar da palon yake kalla Yana sake kokarin yaqi da Hana zallan zalamansa fita ya danne Kansa da nutsuwa da kame Kai.


Gurin zama Dd babba ya nuna masa daya daga cikin kujerun alfarmar Dake jere.


Zama yai Yana sake Satan kallan wata drawer dafi komai tsayi da wani glass a office din zuciyarsa na kissima masa Kila uwayen daloli ne a ciki.


Numfashi Dd babba yasake sakewa a karo ba adadi tin farkon Jin zancen dake tafe da Ababan kafin ya miqa hannu kan wayarsa Daya bari kan stool na set din kujerun dakin dazai fita sallah take ya nemo numbern Bilal ya Saka kiransa.


Yana dauka Kai tsaye Yace ya samesa Daman yasan da dawowansa Bai nemesa bane Dan ya bari ya huta kafin su zauna maganar aikin dayayo acan tsawon watannin biyu.


Jin Bilal aka Kira yasa Ababa Jin fargabarsa ta fada Dan kuwa gwara ayita ta qare din

Dan tin farko da yasan ya dawo ai shi zai fara tinkara kafin su qaraso gurin Dd din.


Shiru sukai Babu mai magana kowannensu yayi Nisa a nasa tinanin da shakkar yanda zata kasance.


Shidai Dd babba fatansa daya kawai duk tsanani kada ma ya kasance Bilal yasan wanna mutumin bare 'yarsan dayake magana Akai,

Zaifi farin cikin ace anzo masa da labarin sunyi asarar miliyoyin kudi masu yawan gaske akan wannan labarin ya sake kasancewa a zuriarsa,


Ya karbi jikan farko ta wannan hanyar bazai yarda ya rungumi tattaba kunnen farko ba ta wanna qaddarar sbd wani tabo da ciwo ne Mai qarfin gaske da haryanzu yake dandana ciwonsa duk da qaddarar ta banbanta da wannan.


Ya kasa karba Bilal zuciya Dari bisa Dari sbd baida shedan auren da 'dansa ya daura boye da mahaifiyarsu Bilal din farko har aka samu cikin,


Madaurin auren ya mutu masu shedan auren sun mutu tayaya zai yarda da auren nasu?


Ya kwato mutunci da sunansa daqyar yayiwa zancen lullubi da wata irin dukiya Mai yawan gaske da har kullum yake shakkar fitarsa sbd baisan ta wace fuska mutane zasu karbi matsayin Bilal din ba jikansa na farko,A matsayin Dan gaban fatiha ko a matsayin Dan Sunna.


Wannan dalilin nasa yasa har ko yaushe DD ne asalin Wanda zuciyarsa ta karba ta riqe bari bisa Dari fiyeda duka sauran jikokinsa sbd Saida ya sake daura auren Fatima da dayyab din tukuna hankalinsa ya karbi auren nasu kafin haihuwa DD da sauran kanwarsu.


Ta Ina yanzu zai fara da wannan Shima idan ya tabbata cikin ne daga ahalinsu wannan mutumin yake magana.

#MAMUH#

For more pages Kuyi joining VIP or Arewabooks


#DD KAANTE

#BENA ABABA

#CRAZY

#LOVE/MARRIAGE/ROMANCE

#SUMAYYAH ABABA

#BILAL KAANTE

#ZAFIN KAI

#MAMUHGEE

No comments