Breaking News

ZAFIN KAI 18

 _Arewabooks@Mamuhgee_*

18


Ranar da suka wayi gari da sassafe a dakin sumayyah ta ringa amai tana dafe kanta dake ciwo cikin galabaituwa sbd da zazzabi ta kwana kuma ta tashi dashi.


Tausayinta sukeji sosai sbd sanin malaria ce kuma basuda wani taimakon bata bayan Addua dasukeyi akan samuwar saukinta dan Ababa ko zata shide bazai iya siyo mata magani ba bare kaita asibiti sam babu wannan a tarihin gidanma kwata kwata,


Bilal ne baya wasa da ciwonsu kowane iri ne koman qanqantarsa gashi bayanan bai dawoba.


Bayan gama Aman na Sumayyah da Hande na jin yunqurinta na aman me qarfi amma tayi banza dasu sbd tinanin sun fiya raki,

Shiru Anne tayi tana kallanta da idanuwanta dasukai zuru zuru tana qure kallanta sosai akan Sumayayan wadda duk sun qarar da maganinsu dasuke boyewa akanta cikin kwanakin amma babu wani sauki gashi ciwon dai baa kwance rigis ba a laulaye take yinsa kaman wata me qaramin ciki.


Dummm kunnuwanta da kirjinta sukayi lokacinda takai qarshen wannan kalmar tata ta qarshe cikin ranta,

Wani busashen yawu mai kauri ta hadiye tana sake qure kallanta kan Sumayyar datayi fayau kaman mara jini tayi haske sosai.


Benazir ta kalla taga ita sam batai fayau din ba,

Dawo da kallanta kan sumayyar takuma yi ta sake kalla takuma kallan benazir data gama gyare gurin tana kallan yanda Annen ke kallonsu kaman me tantance kamanninsu.


Anne data kasa furta abinda shedan da zuciyarta suka dirsar mata rawa qafafunta da hannuwanta suka fara dauka tukuna bakinta dayake son budewa 

Daqyar ta fizgo kalmar


"Sumayyah! Yaushe rabanki da wanki?

Kinyi wannan watan kuwa??

Meyasa ciwonki yanayinsa daban wannan karan?


Benazir da bata fahimci maganar Annenba ci gaba tayi da kokarin saka kayan data nade cikin jakar buhun kayansu da ko zib babu,

Itama sumayyahn dake jin makoshinta a bushe ruwa masu dan sanyi takeson sha ba dama bata fahimci me Annen take nufi da wankin ba a hankali cikin rashin kuzari tace,


"Anne bayan kullum muna wanki kuma"


Nauyi jikin Annen yakuma dauka yawunta na dan sake kauri da wuyar hadiyewa tace,


"Al'adarki nake nufi Sumayyah,kinyi kuwa a wannan watan??


Dummmmm kunnuwan Benazir dana sumayyah sukai daukewar jin wucin gadi sbd tsananin bazata da girman zancen tareda rashin tabbacin inda ta dosa.


Idanuwa suka zubawa Annen duka kowannensu na hadiye wani yawu tsinkakke,

Benazir ta kalli kofar dakinsu tana tabbatarda hande bata tsakar gidan ta sake dawo da idanuwanta kan Anne da itama akansu take rarraba ido cikin faduwar gana da tsinkewa.


"Anne me kike fada haka ne?

Me wannan tambayar take nufi?

Daman budurwa tana fashin watan Al'adarta ne?


Sumayyah kuma miqewa tayi zaune daga kwancen datake tana kallan Anne da Benazir din itama zuciyarta na mummanan tsinkewa saidai dukansu daga ita har Benazir babu wanda ya kawo tinanin abinda Annen ke nufi har lokacin,

Sun firgita da tambayar ne sbd basusan me hakan ke nufi ba gashi tashin hankalin da basu taba ganinta acikinsa ya bayyana sosai akan fuskarta.


Anne bata da uwa, batada uba, batada dangi, ba amini ba makusanci,

Yayanta sune uwarta sune ubanta sune danginta sune Abokanta sune aminan shawararta suma kuma hakan ne a nasa bangaren itace uwa,uba,dangi,abokiya kuma aminiya babu wani boyo ko sirri tsakaninsu dan haka kai tsaye Annen ta kalli sumayyah kafin ta maida kallanta kan Benazir tace


"Ciwonta da yanayinta kaman name juna biyu shiyasa na tambaya,ni kaina tambayar zuwar mun tayi badan tinanina zai sauka akan hakan ba sbd rashin yiyuwar hakan.


Cikin slow Sbd tsananin firgita Benazir ta hana Annen qarasawa tana leqa kofa tace


"Anne wane irin tinani ne wannan shedan ya saka miki,

Tayaya zaki bari ma kiyi tinanin ciki a jikin daya daga cikinmu,

Ciki a gidan nan Ababa kona aure ne muka dawo masa dashi kinsan zai iya sittin Akanmu bare cikin da ba.....

Kasa qarasawa tayi tana girgiza kai sbd bazata iya qarasa fadan zancen bama a bakinta tsoro takeji dan kuwa iya maganar kawai gabaki daya jikinsu wata irin tsima yakeyi zuciyoyinsu na bugawa musamman Sumayyah datayi shiru sbd tama fita hayyacinta take sbd tinanin mai tattareda tsananin firgici da tsoro.


Anne kasa shiru tayi sbd takasa yakice tinani da tsoron cikin ranta ta kalli sumayyah zatayi magana Benazir ta katseta cikin roko da magiya tace


"Anne dan Allah kada tsautsayi yasa Hande taji zancen nan kinji"?


Sumayyah suka jiyo sika kalla tare Anne tace"


Bazakiyi magana ba to ke sumayyah?


Ido Benazir ta qura mata tana jiran amsar da zata bawa Annen sbd abar zancen ita zancen kawai gigita qwaqwalwarta yakeyi bare,


Kasa magana Sumayyah tayi saida Benazir takuma maimaita maganar Annen kafin ta dawo hayyacinta kai kawai ta daga musu zuciyarta na yamutsa da tashin hankali mafi muni.


Tana fadar haka Benazir ta roko Anne aka bar maganar sbd bama mai dadin fada bace.


Anne hankalinta bai kwantaba amma dai itama tunda tasan babu tsautsayi da qaddarar da zata saka 'yayan nata abu irin hakan sbd sunsan a yaya suke rayuwar gashi sumayyahn tace tayi aladar dan haka ta cire tinanin komai cikin ranta amma badan zuciyarta ta rabu da tsoro da fargaba ba.


Washe gari suna fita cikin Saa Bilal ne yazo daukansu ya dawo kenan dan haka ta ringa jera ajiyar zuciya daban daban har suka isa saidai bata iya masa wani zancen ba tinda ita kanta tasan bazai yiyu ace tana dauke da abinda Annen ta fada ba dan haka sai kawai sukai iya maganar da zasuyi ya tafi bayan yasa taci abinci sosai sbd ganinta dayayi duk ta rame tayi fayau kaman ya saceta yaje yayi jinyarta cikin kyakyawan guri mai nutsuwa da kwanciyar hankali tareda kulawa.


Har suka tashi sama sama take dan haka ta riga Benazir komawa gida tana isa gidan dole ta kamawa Anne aiki saidai ko rabi batayiba ta yanke jiki ta fadi Allah yasa Yauma hande bata gidan dan haka Anne cikin firgici ta zuba mata ruwa ta farfado sukai daki ta kwanta.


Koda Benazir ta dawo jikin nata yayi dan tsanani saidai tana bacci dan haka batayi dogon motsiba dan kar ta tadata ta fita suka cigaba da qarasa sauran aikin.


******Bayan kwana biyu sunata jinyarta a boye ba tare da sanin Hande ko Ababa ba,

Tana cikin rashin kuzari ko kadan ga yawan Amai yanzu datakeyi babu wata wata Anne cikin tashin hankali da baa saka masa rana ba tace wlh ciki ne a jikin Sumayyahn.


Benazir kusan sumewa tayi da zancen ita sumayyar kuwa daman bata hayyacinta,


A zaune suka kwana dare cikin matsanancin tashin hankali da fargaba da jiran tabbatarwa,

Daqyar sukaga gari ya waye cikin rashin sanya yau suka tattara sumayyar ta dan samu qwari suka fice makaranta sbd a can zasu samu tabbacin Zargin Annen.

Kaman yanda Benazir ke addua Alh bilal dinne da kansa yazo daukansu ganin halinda Sumayyah take suka wuce kai tsaye asibiti sina zuwa aka kwantar da ita.


Tashin farko likita ta iso musu da sakon ciki ne a jikin Sumayyah na sati hudu.


Wuta ce ta dauke masa Benazir kuwa duhu idanuwanta sikai lokaci daya kuma qafafunta na kasa daukanta ta zube qasa tana kokarin samun ganinta ya dawo.

Follow me on Arewabooks @Mamuhgee dan samun pages dasuka fi yawa.

#MAMUH#

#DD KAANTE #BENAZIR ABABA#LITTLE BENA#HOTHOT#LOVE#ROMANCE#ZAFIN KAI#BILLONAIRESromance#sumayyah Ababa.


ZAFAFA BIYAR🔥


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR 'KASHI

Safiyya Huguma


-FURAR DANKO

Billyn Abdul


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at

09033181070

09032345899


Zafafa🫶🔥🔥


ZAFIN KAI


No comments