Breaking News

ZAFIN KAI 14

 Mamuhgee 14_


Bayan Annen tagama cinye abincin ta kwantar da ita bayan ta sake gasa mata fuskarta da bakinta ta fito tafara duka ayyukan gidan.


Bangaren dabbobinsa ta nufa tahau sharewa ga yawa gurin ga qazantar kashinsu da suka tattaka da abincinsu ruwa duk sun zubar a gurin haka suke share gurin kullum so biyu a wuni shiyasa kusan duka bayansu basada qwari wahala ta cinyesu.


Sai bayan karfe goma ta gamo da bangaren dabbobin tadawo tahau gyaran gidan,

Daga dakin Ababan ta sharo da palonsa ta dawo na hande ta sharo ta sharo nasu ta share tsakar gidan ta tattara ta cika baron da suke cikawa da shara kullum akai babbar bola a zubar,ta ja baron taje bola ta zubar tadawo tayi diban ruwa a famfon dake bayan gidansu ta cika dukkanin drums na gidan kafin ta zauna tafara wanke wanke tana gamawa ta dora girkin rana bayanta na wani irin riqewa amma ba daman nunawa.


Wanka ta shiga sbd jin ana kiran sallah kenan karfe biyu takusa kenan.

Tana fitowa wanka sallah tafara yi kafin ta sauke girkin ta kwashe a kulan da ake kwashewa ta tsaya ta kalli uban wankin shago da aka kawo gashi tanason guduwa taje exams dinta ko yayane tinda kudin abin hawansu na hannunta Sumayyah Sulaiman ne zai kaita.


Anne data tashi tayi sallah ne taga Benazir din nata wankin kayan  zuciyarta ba dadi sai kawai ta qaraso ta amsa wankin tana nuna dauriya da cewan ta warke Benazir din taje makaranta.


Ta hakura da jarabawar ta yau dan haka tace Annen taje ta kwanta kawai amma Annen taqi ta takurata dole ta shirya ta fice da sauri zuwa makarantar.


Tana fita mashin ta hau cikin sauri suka ringa gudu ya ajeta ta ciro kudinsa hannunta na rawa ta miqa masa ta shige.


Koda ta isa hall din dazasuyi exam din har anfara badan Allah yariga ya qaddara sai tayi exam din ba da bazasu barta ta shiga ba dan kuwa daqyar aka bari ta shiga bayan anc cinye fiyeda rabin time din exams din amma dayake ta dage tayi karatunta tana shiga tafara rubatawa cikin saa.


Sumayyah batasan Benazir din ta shigo makarantar ba dan haka tana fitowa exam dinta karfe qarfe hudu sai kawai suka wuce gida da sulaiman.


Benazir hudu da rabi ta fara neman Sumayyah koina bata gantaba gashi kudin hannunta bazai kaita gidaba sbd cikin sauri ba canji ta barwa mai mashin daya kawota sadaka tinda tasan sunada me maidasu gida.


Duk inda take saka ran ganinta ta duba bata ganta ba dan haka taje ta duba inda Sulaiman ke jiransu taga bayanan ta tabbatarda sun wuce.


Numfashi ta sauke mai dumi jikinta na sanyi sbd tana hango nisan tafiyar da zatayi ra qafa kafin ta isa gida.


Fitowa tayi tafara tafiya da qafa kanta hanyarta bata iya tsayawa kallan mutane ko wasu guraren sbd kada ta qara batawa tafiyarta lokaci.


Tafiya takeyi ba tsayawa mai nisa ko rabi batayiba magriba tayi ta qarawa kanta sauri sbd Ababa idan ya rigata komawa gida Allah ne kawai zai fiddata.


Tafiya takeyi tana qara sauri hankalinta na qara tashi da duhun dare dakeyi.

Qafafunta wani zugin gajiya suka fara ga bayanta kaman zai rabu da siririn qugunta amma ba sanya qara sauri takeyi.


Sumayyah a gidan tana isa ta tadda cewan Benazir din ta tafi makarantar itama 

Take hankalinta yayi mummunan tashi sbd sun dawo daban daban Allah yasa kada Hande ta fada kuma Allah yasa Benazir din ta riga Ababa dawowa.


Karban wankin da Anne bata gama bane har lokacin tayi amma hankalinta gabaki daya yana kan Benazir dake waje ga magrib tayi.

Addua takeyi tana qarawa akan Benazir da dawowarta.


Bata iso gida ba sai bayan sallar ishai qafafunta daqyar suke daukanta ga maqoshinta ya bushe qam sbd tsoron abinda zata tadda gidan da azababbiyar gajiya.


A tsakar gidan ta tadda kowa a tsaye ana jiranta 

Anne da sumayyah data gama shan dukan wahala kan Dawowa  bata jira Benazir din ba duk kamanninta sun sauya sbd marika suna rakube gefe tsaye kansu a qasa jikinsu na rawa da tsoron abinda zaiyiwa Benazir.


Hande ma na gefe zaune kan kujera tanata fada akan ita bataga amfanin karatun nan nasu ba sbd fandarewa zasuyi idan suna shiga mutane.


Ababan a tsaye yake yana Nazarin matakin da zai dauka,

Qarasowa Benazir tayi ta tsaya tsakar gidan jikinta da zuciyarta a mace sbd tasan Hukuncinsa akanta yau ba gudu ba ja da baya dan haka tsaya kanta a qasa batareda tace komaiba.


Shiru gurin yayi bayan fadan Hande babu abinda yake tashi tsawon mintina kafin ya dago ya kalleta da idanuwansa da sukai jajir da bacin rai da masifa 

Cikin muryar kai tsaye yace


"Daga ina kike?

Ina kika je?

Me kika tsaya yi kike dawowa gida yanzu?


Bata dago kanta gabaki daya ba ta bude baki jiki a mace cikin nutsuwa tace


"Kudin abin hawan ne bai isaba da muka dawo daban daban sbd Anne ba lafiya shine ta rigani dawowa nikuma na dawo da qafa"


Kallan Sumayyah yayi tasake yin qasa da kanta zuciyarta na karyewa sbd tasan dukan Benazir din zaayi itama.

Dawo da kallansa kan Benazir yayi yana maimaita kalman sun dawo daban daban din wato dan barnar kudin Abin hawa.


Hakuri Benazir ta bude baki ahankali zata basa ya saukar mata da wani lafiyayyan mari a fuska wanda yasa habo zuwar mata nan take amma takasa saka hannu ta tare jinin 

Ya sake sakar mata wani marin a dayan gefen take gudun jinin habon ya qara gudu kanta na qasa.


Qafa yasa zai harbeta Hande tace barta haka ai ko yanzu gashinan taga hukuncin hakan tinda ga jini nan nai mata gudu a hanci.


Bai saurari Handen ba sbd kafin dawowar tata jinin sa idan an auna yakai 200 da yan kai sbd tashin hanakali da masifar idan itama ba guduwar tayi ba dan wlh da saiya kusa kashe uwarta.

Dukanta ya ringa yi takai ta qafa zuciyarsa na tafasa da bacin rai da baqin cikin tareda zazzabin dolen data sanyasa.


Hande ce ta qwaceta tabasa hakuri ya fice daga gidan ita kuma Benazir din sumayyah tayi saurin qarasowa ta kamota jikinta tana fashewa da kukan tausayinta dan take taji ta dena jij nata zugi da radadin sbd ganin dukan Benazir dinta.


*_PHYDOORS FOOD AND MORE_*💯🔥


*_Ina masoya Abincin gayu dana gargajiya da Sea foods? Ga ingantattu kuma tsaftattun kayan Phydoors Sea foods and more da muka tabbatar da dadi, kyau, inganci da tsaftarsu tareda saukinsu._*

*_Uwar gida, Amarya shin kun taba aikin Abinci da kayan Phydoors sea foods and more kuwa?_*

*_Idan baki taba ba ina shawartarki da gwadawa sbd a take zaki gano bambamci da kuma damar Girki masu dadi da ingancin da suka wuce ki._*


_*Phydoors sea foods and more Suna tare daku a koina sbd suna aika kakansu koina a duk Inda kikeso cikin tsari da packaging mai kyau da kulawa hakama ga sauki da Ragusa,Akace siyan na gari maida kudi gida.*_


*_Phydoors food and more is a food branded based in abuja and offered national wide delivery of her items, available food stuffs are stone free crayfish , egusi, palm oil, plantain powder in kg, prawns 🍤 , fried kpomo, some from as low as 2k._*

*_Contact her through this line 08062181151 or DM me let’s do paired order for minna and suleja. She’s based in abuja._*

_*Or visit her instagram handle*_ @ _Phydoors_Food_


Daki suka koma Kaman marayu suka zaune kowannensu jikinsa na radadi da zugi 

Benazir bata iya ko dago kai ta iya cewa kala ba sbd batasan me zata fada ba ko cewa.


Anne da kanta ta dafi ruwan zafi tazo ta zauna tana gasa musu fuskokinsu da jikinsu gabaki daya zuciyarta ba dadi,

Ta rasa tayaya zata iya ceto ko kubutar da 'yayanta ga wannan masifar sbd ita kanta ta kasa guduwa ko tserawa wannan rayuwar,idanma tinanin guduwa ko tserewa daga rayuwar gidan Ababan ya fado ranta wani masifaffen tsoro da ciwon hauka takejin kaman zai kamata shiyasa bata iya guduwa batasan cewan aikine yayi akantaba ya kafeta ko namanta zai ringa yankawa bazata iya guduwaba sai ranar dayace ta tafi da kansa.

A ranar ko abinci daqyar sukaci sukai salloli sika kwanta kowannensu zazzabi na rufesa mai qarfi.


Washe gari Benazir batada exam kuma Interval na kusan sati day take dashi dan haka Sumayyah ce kawai ta tafi itama sbd uban carry overs datake dasu ne hadi dana wannan samister din suka saka exams dinta yin yawa ba ranar da batayi.


Da zazzabi sosai a jikinta ta tafi makarantar jiki a mace  ga tsoro sbd bata taba fita ita daya ba bayan jiyan da yau din sun saba komai tare sukeyi da qanwar tata Benazir.

Koda ta isa a jujjuye tayi exam din farko ta fito tana fitowa ta yanke jiki ta fadi Allah yasa Ms Ayshah na kusa dan haka take aka dauketa ta kira sir Bilal 

ba bata lokaci yazo yakaita asibiti.


Acan ta wuni yau da babu Benazir daga ita sai shi shine yayi jinyar cikin kulawa sa ita sosai.


Sai yamma ta daga hankalinta kan komawa gida da kansa ya kaita bayan ta karbanwa su Benazir da Annenta maganin zazzabi acikin nata harma dana shafawa ciwo.


Data shigo gidan aiki sukeyi cikin matsanancin zazzabi dan haka tajasu daki suma suka sha aka shafa na shafawa Allah yasa sun gama aiki suna cin abinci take dukkaninsu bacci ya daukesu.


Washe gari ma koda ta isa maboyar dasuke hawa napep din sulaiman maimakon ra gansa Alh bilal din ta tadda da kansa dolenta tashiga basu wuce makaranta ba gurin likita suka fara zuwa ya dubata ya sake mata allurai sai daya sakata cin lafiyayyan breakfast da aka kawo ba bata lokaci daga Kaante Hotel and suites,

Taci abincin cikin kunya da takurawarsa kafin yabata magani tasha tukuna ya kaita makaranta ya wuce.


Kafin su shiga exam Ms aysha ta dan qara mata bayanin handout din course dazasuyi exam dinsa.

Bayan sun fito saida yayi magana da ita da wayar Ms aysha ya bata qwarin gwiwa da kalamai masu sanyi nutsuwa kafin tashiga wata jarabawar sai gashi kalamansa da dokinsa yasa ta dan tabuka abin arziki sai abin ya mata dadi.


Tana gamawa Ms aysha tasata jiransa sbd yace a tsayar masa da ita din.

Shine yazo ya dauketa bayan yaxo masu da abincin da aka saba kawo musu kullum daga Kaante H&S yau harda magani aka siya musu na zazzabi da qananun ciwuka haka.


Kafin sukai gidan dayake iya su biyu ne sosai yanzu yake bayyanar mata da soyayyarsa da kulawa sosai wanda yasata itama jin wani iri a duk lokacinda suke iya su biyun.


A gida kwana biyu da ake kawo musu magani sosai suke samun sauki dan Anne tini ta warware Benazir ce kawai takejin jiki a lokacin sbd ta daku sosai a ranar kuma ga azabar tafiyar qafan datayo sun kamata sosai shiyasa nata jikin sai ahankali.


Acikin kwana biyu da babu Benazir Sumayyah tafara samun shaquwa da sakewa da bilal da ms aysha dan kuwa sosai suke nuna mata wata irin kulawa da kauna,

Ms Aysha qawar Bilal ce sosai tin primary sukai karatu tare dashi da ita da DD wanda ba wata tazara ce tsakaninsa da qanin nasa ba dan haka sukai karatu tare saidai DD tinda suka gama junior class a secondary yabar qasar Dd babba yakaisa Zurich gashican ya zama dan zurich su kuwa har secondary da jamia suna tare kafin yabar qasar daga baya yakoma spain gabaki daya qarin karatu amma basu yanke muaamala ba sbd kusan baida Abokin dayasan sun shaqu dashi kaman Ms ayshan,

Mijinta ma sosai yake mutunci dashi kuma yana respecting alaqarsu sbd sun dade da komawa tamkar 'yan uwa,

Bata taba haihuwa ba duk tsawon shekarunta da aure saidai bata cire rai ba tinda da sauran lokacinta yanzu ne aurenta yake cike 19 years dayi.


Sosai Ms aysha take jan sumayyah a jikinta da kulawa da kauna mai tsafta sbd ganin dagaske Bilal yake sonta  so mai tsanani saidai haryanzu halinsa na gudun zuciya da tsoron batawa iyayensa rai yananan shiyasa yakasa bayyanarda soyayyarsa da alaqarsa da sumayyahn a fili dakuma qarin itama bayason sakata da matsala gidansu dik da haryanzu baisan taqamaimai rayuwar rashin yanci da azabar dasuke yiba a gidansu ya dauka dai normal tsoro ne na mahaifinsu sukeyi sbd yanada zafi da fada sosai.

#MAMUH#



_Mamuhgee 15_

Akace Salati baya hana daukan rai hakama qaddara yashi ce ko an daunqulata bata dunquluwa,zuciyar Sumayyah batai shawara da ita ba acikin qanqanin lokaci ta saka bilal cikin kanta.


Har Benazir ta samu sauki kuma interval nata ya qare ta dawo suka ci gaba da exams bata fahimci 'yar kusanci da shaquwan da Sumayyah ta samu da Ms aysha da Sir bilal ba sbd hankalinta gabaki daya akan jarabawarta ya koma sbd babu tsayawa yanzu saita gama duka exams din.


Sumayyah kuwa itama ba dan laifi Ms aysha na iya kokarinta akanta ga bilal yanzu da duk ranarda baizo ya ganta ba a wayar Ms aysha yake magana da ita.


Tin tana jin nauyin ms ayshan sosai harta dan sake da ita sbd a rayuwarsu basu taba samun kulawa,kauna ko tattali da sakewa daga wani ba wannan ne karan farko datake samun hakan daga Bilal da ms ayshan.


Koda suka gama exams suka fara zaman hutu daga bilal din har sumayyah jin sukeyi ba dadi musamman shi din.


Benazir Tinanin result da yanda wahalarsu ta qaru ba sauki yasata gaba,

Abincin dasuka saba dashi kuma na Kaantes H&S yanzu dasuke hutu ba daman cinsa sai suka taru sukai wata irin rama sbd yunwa kaman wainda ake dibansu ana girkin gidan dasu.

Yar lafiyar dasuka samu ta jiki sbd cimar dasike ci mai kyau da lfiya tini ta gagaresu sbd yanzu aiki ne kan aiki da yunwa kan yumwa duk sun sake ficewa hayyacinsu gasu yau lafiya gobe babu sbd marika da harbin qafa,Annensu kuwa tini Ababa ya haukatar da dodan kunnuwanta da marika dan haka yanzu kusan idan kana nesa da ita bata jinka sosai idan ba murya zaka dago ba.


Cikin ha ula'i da ukuba sikai hutun sika gama aka koma karatu,

Ranar dasuka koma mashin sika hau kaman yanda suke hawa a baya,

Sunje makaranta sun duba time table nasu kaman mayu suna cikin wainda basu qara ko kwana dayaba,


A gantale suka wuni makarantar sika dawo Ms aysha ma bata shigo ba ranar dan haka Sumayya jiki a sanyeye ta dawo gida.


Sallah sukai suka fito qarasa aikin da Anne bata gama ba suka shige bayan sinci Shinkafar da aka basu.


Washe gari suna fitowa suka ga sulaiman yana jiransu inda suka saba ba bata lokaci suka shige a yanzu dasuka fara ita boye abu kudinsu na makaranta sun dena bayarwa dika rabi suke boyewa suna sadakar rabin shiyasa harsun fara tara 'yan kudaden da ko basu fada ba na guduwa da Annensu ne insha Allah.


Suna isa makaranta Sumayyah na kama hanyarta Ms aysha ta aiko kiranta dan haka itama cikin jin sanyi a ranta ta nufa office dinta.


Cikin kulawa da farin cikim ganinta sosai ms aysha ta tarbeta tareda cewa ta zauna 

Nan ta fara tambayarta ya hutu da sauran abubuwan.


Bata wani jimaba ta tafi lectures saidai baa kira  Sir bilal ba yau din sukai magana.


Tana barin office din ms aysha ta kira Bilal ta sanar dashi irin ramar da Sumayyah din tayi sosai a dan lokacin hutun.


Suna fitowa da yamma maimakon sulaiman Bilal ne yazo daukansu cikin daya daga cikim motocinsa masu shigen daukan ido da hankaliz


Kaman marasa gaskia suka gaidasa ya amsa cikeda kulawa idanuwansa na kan sumayyah data kasa dagowa ta kallesa sbd kunya da farin cikin ganinsa.

Shiga motar sukayi suka bar makarantar tin kan wani ya gansu duka kama hanyar gida.


A motar Benazir kawai ya danyi magana da ita sumayyah kuwa da idamuwansa yake maganarsa da ita

Ita kuma bata iyaba bata ganewa duk sai neman rikicewa takeyi.


Suna isa a tare suka fice motar suka kama hanyar gida batareda Benazir ta taba tinani ko fahimtar wani abu na faruwa da Sir bilal ba da Yar uwarta.


Ayau abincinsu na musamman ne sbd da kansa ya karbo musu dan haka sina sallar magrib suka zauna sukaci suka koshi take Anne tafara amai sbd wunin ranar so daya taci abinci.


A boye tagama aman suka kwashe suka wanke sbd kada aga aman asan sunci wani abin bayan tuwon da akai gidan.

Da omo mai qamshi sika wanke koina dan haka dakin bayan qamshin omo babu abinday yakeyi baka cewa anyi amai.


Suna gamawa sallar ishai sukai kawai suka fito suka danyi wankin shago da baida yawa yau koda 9 tayi sun gama sun shige sun kwanta.


Washe gari ma Bilal ne yazo daukansu hakama a dawowa.


Saida suka share kusan sati da komawa Bilal ne yake kaisu da daukosu har saida tsarguwa da tsoron Benazir ya bayyana a fili tukuna Sumayyah ta rokesa ya dena zuwa din sulaiman yaci gaba da daukansu.


Koda result dinsu ya fiffito Benazir ta fadi Course daya Sumayyah kuwa a duka uku kawai taci suma da pass,


Dukan dasuka sha kuwa saida Sumayyah ta kwanta jinya sosai wadda ta qara mata shakuwa da kusanci da Bilal da ms Aysha dasuka fahimci babansu ne keda wani irin zafin dayake dukansu.


Kulawa da tattali sosai sumayyah ke samu daga ms aysha da bilal harma da benazir ana tattalinta saidai nata bai kai wanda sumayyahn take samu ba.


*******lokaci ya dan ja semister tayi nisa zuwa lokacin tafaru ta qare soyayya mai qarfin gaske ce a zuciyoyin Bilal da sumayyah wanda suke yinta boye batareda sanin kowaba sai ms aysha da benazir wadda ba qaramin shock ta shiga ba da Sumayyah din ta sanar mata amma kuma kirki da tsananin mutinci da girman kaunar da Sir Bilal ke musu yasata jin hope a ranta na akwai yiyuwar Allah ya kubutar dasu ta hanyar Bilal din kila.

Kuma ganin yanzu sumayyahn na gane karatu ba laifi yasata sake jin girman Sir bilal din da ms aysha cikin ranta,.


Tafiya tayi tafiya Ita kanta Benazir Ms aysha ta shaqu da ita sbd wani irin tsananin tausayinsu datake ji yasa mata kaunarsu sosai musamman Benazir wadda zuciyarta ke danqare da damuwa da quncin rayuwa fiyeda sumayyah sbd sumayyah yanzu Bilal shine sanyin dayake narkar da nauyi da quncin zuciyarta.


Sunyi hutun qarshen session din results dinsu yayi kyau Benazir bata fadi ko daya ba sumayyah ma kusan taci sosai dan iya biyu kawai ta fadi duka da sauran daqyar aka wucesu.


Zuwa lokacin boyayyar soyayyarta da Bilal tayi wani irin nisa da qarfi ta yanda aurenta yakeson yi matiqa saidai babban tashin hankalin daya fara tinkarosu shine mahaifinsa kai tsaye baiyi naam da maganar ba batareda yaji sauran bayanin ba yace sun riga sunyi magana da senate president 'yarsa zai aura.


Sumayyah ma a nata bangaren yanatason yazo yayi magana da Ababa amma tsoro ya hanata barinsa sbd abinda bai saniba duk ranar da ababa yasan sun taba kallan wani namiji ba bare soyayya wlh zai iya konata bare yayi alqawarin fasa idanuwansu idan hakan ta faru.


Ta bangare daya kuma cimar dasuke ci mai kyau da lafiya tasa fatar jikinsu da jikin nasu sauyawa sosai tayi fresh da kyau alaman ana cin cima mai rai da lafiya.

Komai yana son siya musu sbd yanason ya sauya rayuwarsu zuwa rayuwar da basu taba tinanin zasu kai ba,

Yanason barar musu da dukiyar da basu taba tinanin akwai ba,

Yanason inganta rayuwarsu ingatawar da wasu yayan masu arzikin basu samu ba sbd Nasu arziki da dukiyar da Allah yabasu kaates tanada yawan da bazasu iya fadar adadinta ba.


A bangaren Ababa rayuwarsu bata taba canjawa ba da matsayinsu na kamar dabbobi gidan,

Dukansu da azabar da ake basu tana nan babu abinda ya sauya saima qaruwa sbd kullum karatunsu sake cin kudinsa yakeyi dan haka azabarsa akansu take qaruwa ga shagonsa na wanki ya sake bude wani sbd sosai kasuwancin wankin ke tafiya dan haka ya sake bude wani shagon kuma duk sune masu wanki da gugar kawai dai iyakaci yaran shagon su saka a leda ayi packaging kaman na kamfani a bawa me kaya idan yazo karba kuma yawanci manyan mutane sosai yanzu suke kawo wanki shagon dan haka manyan motoci matsu tsada ake aiko masu karban kayan wanki shima kansa Ababa tini ya tanadi mashin suka fara delivery din kayan da kansu idan an wanke.


Ms Aysha itace take taimaka musu sosai yanzu kusan itama a boye dan haka soyayyar Bilal da sumayyah taketa qara nisa da qarfi.


Sumayyah sun gama nasu karatun gyara ne kawai takeyi yanzu sabanin Benazir da yanzu karatunta yake qara nauyi sbd tana 300lvl gashi Accountancy take karanta.

Sosai hankalin Benazir ya duqufa kan karatunta sbd ganin sumayyah na gane kartu sosai dan haka ta dena damuwa da karatin sumayyahn ta kama nata.


Yanayin yanda karatin nasu ya hargitse yasa dole badan Ababa yaso ba a ringa raba musu kudin abin hawa sbd tsananta tsaronsa akansu duk wanda ya gama baya jiran daya ya dawo gida.


Nasir Ahmed wani dan kyakkyawan saurayi dayake final year dinsa a Accounting kuma kuma kusan shine guru din course mates dinsa tin Benazir na first year dinta Allah ya saka masa kaunarta amma bai taba tinkararta ba sbd yanda take kame kanta.


Ya dade yana bibiyarta amma ba fuska sai gashi Allah ya hadasu sanadiyar wani course da itace tafi kowa cinsa shine lecturer din ya hadata da Nasir yana qara mata haske akan course din sbd yanada matiqar wuyar gaske shiyasa malamin ya jinjina mata data cinye tana mace.


Karatu shine ya kawo mutunci da yar shaquwa a tsakaninsu amma sam babu sakewa sbd yanda take tsorace sosai da Muamalar tasu,


Shi kansa daya fahimci tsoro fa fargabar ganinsu da akeyi tare sai ya ringa sirrintawa yana samunta gurin zamansu da sumayyah inda ba mutane acan suke karatun.


Son Benazir yake sosai da gaske dan haka yake tsananin mutunta ta kuma ita kanta tana mutuntasa a zuciyarta saidai duk yanda zuciyarta taso saka mata wani abin daya zarce hakan saita hana kanta sbd idan suka bari wani abin ya shiga tsakaninsu to tabbas ita a bangarenta tasan suicide mission ne dan kuwa shi kansa Nasir din tasan saiya shiga tashin hankalin abinda zai biyo bayansa idan ubanta ya sani dan haka take dan baya baya da duk wani tinanin daban amma kuma zuciyarta ta basa matsayi mai mahimmanci amma bai zurfafa ba.

#MAMUH#

#BILLONAIREsROMANCE

#DD KAANTE

#BENAZIR ABABA

#CONTRACT

#insideLife#marriage#love#hotlove#Lover#Zafin kai#zafafa biyar#paidnovel#Mamuhgee#morepages@Arewabooks#


For more pages kuje arewabooks ko vip


ZAFAFA BIYAR🔥


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR 'KASHI

Safiyya Huguma


-FURAR DANKO

Billyn Abdul


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at

1487616276

Access Bank 

Bilkisa Ibrahim


Send your Shedan biya Anan👇

09032345899


MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇

09033181070


Zafafa🫶🔥🔥


ZAFIN KAI

No comments