Breaking News

ZAFIN KAI 13

 Mamuhgee 13_


Hakuri Sir bilal ya sake bawa Dad kaante tareda tabbatar masa da zasu dawo qarshen watan da yardar Allah harma da DD din idan Allah ya dorasa akanshi.


Cikin 'yar damuwa Dad kaante din yayi sallam da Bilal ya fito yana fidda wayarsa dan kiran Sulaiman da hankalinsa yake kansa.


Motarsa ya nufa batareda ya nufi babban part dinsa ba dayake gefen mansion din iyayensa ba duk acikin guri daya.

Yana shiga motar ya rufe ya saka kiran Sulaiman wanda shima yake zaune yana jiran kiran maigidan nasa dan sake kora masa bayani.


Kiran Sir bilal din na shigowa wayarsa ya dauka da sauri yana sake gaishesa kafin ya sake masa bayanin komai na abinda ya fahimta.


Shiru Sir bilal din yayi kafin ya kashe wayar yana tinanin menene zai saka sumayyah kuka da damuwa har a hanya?


Tada motarsa yayi yana kallon time sbd yanada meeting da baqin masu mahimmanci ga DD yana buqatan nutsuwa yayi magana dashi ta waya Dan haka ya daure ya wuce office idan Yaso washe gari da wuri zai sameta school yaganta. 


Washe gari Koda ya isa suna cikin exams dan haka ya zauna cikin motarsa yana jiranta.


Tsawon mintina talatin da shida yayi yana jira sai gata ta fito ta nufa inda suke zama yau din ma bata cikin kuzari sbd zuwa lokacin tagama saddaqar da masifar da zata shiga ta Ababa.


Kokarin zama takeyi qamshin tirarensa ya shiga hancinta ta dago da sauri tana ganinsa tayi saurin maida kanta qasa tareda zamewa ta durqusa ta gaidasa cikin tsananin girmamawa.


Yanayinta yake sake karanta yanason magana da ita amma sanin hankalinta bazai taba kwanciya ba sai yace ta biyosa kawai.


Kaman baiwarsa haka tabi bayansa kanta a qasa cikin nutsuwa.


Motarsa ya bude mata tashiga shima ya zagaya ya shiga tareda rufe motar yaja suka bar makarantar saida sukai tafiya mai dan nisa zuciyarta na bugawa 

Qafafunta tini suka fara rawa saidai bata iya magana ba.


Inda babu mutane sosai yayi parking ba tareda ya kashe motarba sbd Ac ya juyo ya kalleta cikin nutsuwa ya sauke numfashi mai dumi tareda ajiyar zuciya kai tsaye yace


"Meyasa kiketa kuka yau sulaiman yace akwai matsalan dayake damunki,

Ko zan iya sani idan ba damuwa.


Idanuwansa ya zuba mata yana jiran amsarta,


Shiru tayi bugun zuciyarta da rawar jikinta na bayyanuwa ga hannuwanta dake rawa.


Hannuwanta ya kalla yaga yanda suke rawa a hankali kafin ya maida idanuwansa kan fuskarta yana sake tabbatarda akwai matsalar dake damunta.


Maimaita tambayarsa yayi cikin kulawa nan ma kasa magana tayi ta girgiza masa kai kawai ahankali.


Ganin hakan yace


"Inaga zanje gidan da kaina naga Babanku sai naji ko wani ne a gidan ba lafiya"


Jin hakan yasa gabanta mummunan faduwa sbd duk yanda suka kai ga kamewa da kiyayewa tareda taka tsantsan koyaushe da zuwa gidansu yake musu barazana yana taimakonsu dan kuwa duk abubuwan dayake musu saiya basu tsoro ya firgitasu da cewan zashi gidansu gurin babansu suke yarda su karba taimkonsa.


Bude baki tayi cikin sanyin jiki da damuwa ta sanar dashi bata gane komai na karatun da sukeyi ne har jarabawar.


Shiru yayi yanason fahimtar zancen nata da kyau sbd jin zancen yayi kaman kai tsaye da yawa dan haka ya sake kallanta da kulawa yace

"Karantarwar ne malaman basu iya ba basayin yanda zaku gane kokuwa?


Shiru tayi sbd muzantar datayi saidai kuma daman su din ba masu wata darajar da zasuce basu saba da muzantar ba dan haka a sanyaye tace

"Aa nice bana ganewa,kaina baya gane komau" da wasu irin hawayen kunya da muzantar kai ta qarasa zancen.


Ya fahimci abinda take nufi dan haka jikinsa yayi sanyi da tausayinta dakuma nauyin zancen dan kuwa a familynsa marasa ilimi zaune a kansu basa karbuwa a Kaantes saukin abin suna dubawa hardana Addini ba iya bokon kawai suke so daga matayensu ba.


Ahankali ya sake kallanta yana sake jera mata tambayar yanayin yanda tayi last session dinta da yaya results din suke.


Batada zabi bayan fada masa gaskiar bataci komaiba a bayan duka wannan semister din ma courses din datake carry over dinsu yafi wainda zatayi a semister din yawa.


Wayarsa ya dauka ya saka kiran wata number ta wata lecturer mace wanda tana dauka kai tsaye ta hau gaishesa.


Cikin mutuntawa ya amsa yana tambayarta aiki da dama da student ta amsa da duk lafiya kalau,

Cikin natsatsen turancinsa daya kama bakinsa kusanma fiyeda hausarsa sbd zamansu a qasashen turawa fiyeda nan din idan ba yanzu daya dawoba sbd su biyu ne 'yaya maza a familyn kuma idan ba shi din ba DD bazai taba dawowa dan karban ragamar kula da huldodin kaantes ba.


Bayani sosai yayi mata akan zata samar masa da wadda zata ringa yiwa Sumayyah karatu yanda zata gane.


Kai tsaye ta amsa masa da an gama insha Allah ita da kanta ma zata ringa dan budewa sumayyah din karatun da engausa sbd a yanda ta fahimta may be harda turancin yasa bata gane karatun dan haka zata ringa gwada yi mata bayanin karatun da mafi hausa kafin idan tagane sai akoma na turancin.


Godiya yayiwa Ms Ayshan ya kashe wayarsa bayan ta basa time din dazai ringa kai mata sumayyah din gidanta.


Sumayyah data dan fahimci wasu abubuwan dayake tattaunawa da Matar shiru kawai tayi sbd iya saninta hakan bamai taba yiyuwa bane zuwanta wani gurin ita daya,

Me zata cewa Ababa,Anne da Benazir idan suka ji?


Bayani yakeson yi mata amma yana iya ganin tashin hankalinta afili akan zancen dan haka sai kawai ya dora hannuwansa akan steering motar yaja suka fara tafiya yana mata bayanin cewan zai sake magana da Ms ayshan ta ringa yi mata karatun a makaranta kawai ba sai gidanta ba.


Da haka ya maidata school ya tafi cikin sauri sbd yayi lattin meeting dinsa,


Ita kuma tana komawa wata exam din tashiga tana cikine Ms aysha din tazo nemanta dan haka tana fitowa kai tsaye office dinta ta nufa.


Da farko qare mata kallo Ms aysha tayi tana mamakin meya hada Sir bilal da sumayyah din amma kuma data qure mata kallan sai taga kyakkyawa ce hutu da gyara ne kawai bata samuba,to kuma koma menene ba ruwanta abinda yake gabansu zasuyi.


Gurin zama ta nunawa Sumayyah din tana mata tambayoyi daya bayan daya.


A tsarge sumayyah din take amsawa har Ms ayshan ta ringa dan janta da fira sbd ta saki jikinta ganin duk a kame take da rashin sakewa.


Ms Aysha wayayyar babbar mace ce kuma mai saukin kai da fahimtar komai cikin sauri,

Kai tsaye ta fahimci so da kaunar sumayyah mai tsanani a tareda Sir bilal gashi sumayyah din kuma kaman bagidajiya ce.


A ranar dai basuyi komaiba fira kawai Ms ayshan tayita janta dashi sbd tafison tafara sakewa da ita ta yanda zata fahimci matsalar karatun sumayyah din da kyau.




*_PHYDOORS FOOD AND MORE_*💯🔥


*_Ina masoya Abincin gayu dana gargajiya da Sea foods? Ga ingantattu kuma tsaftattun kayan Phydoors Sea foods and more da muka tabbatar da dadi, kyau, inganci da tsaftarsu tareda saukinsu._*

*_Uwar gida, Amarya shin kun taba aikin Abinci da kayan Phydoors sea foods and more kuwa?_*

*_Idan baki taba ba ina shawartarki da gwadawa sbd a take zaki gano bambamci da kuma damar Girki masu dadi da ingancin da suka wuce ki._*


_*Phydoors sea foods and more Suna tare daku a koina sbd suna aika kakansu koina a duk Inda kikeso cikin tsari da packaging mai kyau da kulawa hakama ga sauki da Ragusa,Akace siyan na gari maida kudi gida.*_


*_Phydoors food and more is a food branded based in abuja and offered national wide delivery of her items, available food stuffs are stone free crayfish , egusi, palm oil, plantain powder in kg, prawns 🍤 , fried kpomo, some from as low as 2k._*

*_Contact her through this line 08062181151 or DM me let’s do paired order for minna and suleja. She’s based in abuja._*

_*Or visit her instagram handle*_ @ _Phydoors_Food_



***********

A hanyarsu ta komawa gida Sumayyah ta fadawa Benazir komai tana tambayarta ya zatayi.

Numfashi Benazir din ta sauke sbd ita kanta yanzu karatunta ya cake wahalarsa take sha sbd yanda kusan semister din taqare mata gurin attending lectures din sumayyah da kula da sumayyahn gashi daman yau gabaki daya da tinanin yanda zata taimkawa 'yar uwar tata ta wuni har acikin exams dinta tinanin takeyi shiyasa yauma duka jarabawan datayi sai duai itama.


To amma jin hakan yasata shiga nazari sbd Ms Aysha babbar mace ce da kusan makarantar kowa ya santa dan tanada kulawa da mutunta kanta dan haka idan har zata taimakawa Sumayyah karatun kuma acikin makaranta ha wani gurin daban ba to kaman duka an taimakesu ne sbd itama sanin sumayyah nada inda ake koyar da ita karatunta to itama zata samu nutsuwar yin nata karatun kada ayi haihuwar guzuma a tsakaninsu kowa da F.


Hankali kwance suka dawo gida saidai koda suka dawo Annensu ta kona kayan guga kaman yanda sumayyah tayi kwanaki,

Bai daketa ba ita amma wani mahaukacin marin daya taba lafiyar kunnenta daya ya shimfida mata a fuska take kunnanta daya ya dauke sauti batajin komai har dashi har sika dawo.


Fuskarta dukkansu suka kalla lokacinda suka shigo tana zaune tsakar gidan tana tuqa tuwon yamma datayi a tsakar gida kan gawayi.


Gefen fuskarta a kumbure yake shatin hannuwansa duka biyar sun fito baro baro akan fuskar,

Bakinta daga gefe ya kumbura shima yayi tsayi kaman anja ledar ruwa.


Karyewa zuciyoyinsu sukai da ganinta a hakan amma ba daman nunawa idan ba daki suka shigaba gashi hande na zaune tsakar gidan tana shan redionta hankali kwance.


Daki suka wuce bayan sun gaida Handen ta amsa 

Suna shiga suka tube abincin da sukazo dashi yau din jin sikai duk ya fice musu aka sbd ganin halinda Annensu take ciki.


Ajiye jakunkunansu dasuka gama yagewa da warwarewa tin na shekarar farkon da aka siya musu kuma ma na gwanjo ne.


Fitowa sikayi Benazir ta amshi aikin abincin kai tsaye taci gaba duk da ga magrib ana kokarin kira,

Sumayyah kuwa tarin wanke wanken dayake jibge ta debo ruwa a drum ta zauna tafara gashi tsaban tsaftar Ababa baa wanke kayan cin abincinsa so daya sai anyi so biyu a dauraye kusan so uku sbd duk randa yaji qamshin omon wanke wanken a cup idan zaisha ruwa kokuma a plate idan zaici abinci to wanda yayi wanke wanken saiya gagara shan ruwa a ranar sbd mari ko harbi da qafa.


Anne kuwa tsintsiya ta dauka ta hau shara sbd ayyukan daman koda suka dawo duk sun hade mata gashi tin karin safe sai abincin da Ababa din ya rage da rana Yabata yunwa ke cin hanjinta amma sam bata nunawa 'yayanta ne kawai suke mata kallo daya su gane halinda take ciki.


Sai bayan magriba suka kammala ayyukan sikai alwala suka shige ciki bayan anbasu kasonsu na abinci a roba daya suda Annensu daman haka aka saba tin lokacin sunada yawansu bare yanzu da iya su uku ne kawai.


Sallah sukayi suna idarwa Benazir ta fito ta dora ruwan zafi a kofin silver sukai zafi sosai ta dawo daki dasu ta dauki dankwalinta wankakke ta ringa taba ruwan zafin dashi tana matsewa tana dan gasawa Annen fuskarta da bakinta harma da idonta daya dayayi kwanciyar jini aciki.


Bayan tagama mata Annen taji dan saukin radadin da gurin ke mata suka fidda abincinsu sukaci suka koshi sauran Apple Biyu da wani tsadaddan cookies Benazir tayi masa wani irin boyo a cikin kayansu sbd Annensu taci ta safe dan yau sunga alamar ta jigata da yunwa sosai da alama andena bata abincin rana itama sbd suma baa basu yanzu idan suka karya suka fice sai sun dawo da yamma abasu na dare.


Da zazzabi mai qarfi Annensu ta kwana ko tashi zaune bata iya yi sosai,

Kallanta Benazir tayi taji bazata iya barinta ahakan ba kuma aikine zatayi bayan tafiyarsu har saita kusa sumewa kilan,

Dan haka taqi tafiya ranar makaranta sbd exam daya ce da ita kuma sai 2 na rana dan haka bayan fitar Ababa sumayyah ce kawai ta tafi ita ta zauna tabawa Annen apple da cookies din taci daqyar tareda ruwan lipton din da aka basu matsayin karin safiyar.

#MAMUH#

#DD KAANTE

#BILLONAIRESROMANCE

#CONTRACT#LOVE#MARRIAGE#ZURICH


ZAFAFA BIYAR🔥


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR 'KASHI

Safiyya Huguma


-FURAR DANKO

Billyn Abdul


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at

1487616276

Access Bank 

Bilkisa Ibrahim


Send your Shedan biya Anan👇

09032345899


MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇

09033181070


Zafafa🫶🔥🔥

No comments