Breaking News

YAR ZAMAN WANKA Book 2 Complete

Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375  ko katin mtn  300 Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134 idan complete ne 500

 *

         KAR KI SAYI LITTAFINA DAN KI FITAR MIN, IDAN DAN KI FITAR ZAKI SIYA ADANA KUƊINKI HAJIYA BUƘATA

            1️⃣1️⃣

    Gabaɗaya matsin gadon da na bango ya sanya ya takura sosai, saboda  wajen ya masa kaɗan akwai ƙunci sosai hakan ya sanya yake nishi dakyar. Ihu da kururuwar da Inna ke yi wanda ya tashi Hassan da Husaini bayan tashin Sadiya da ta yi cewa take.

"Innalillahi yau na ga ta kaina tsofai-tsofai da ni a ce an kawo min farmaki, mutane basa tsoron Allah ko kaɗan yo ban da lalacewa ma ina mamora a jikina jiki duk yaba" Cewar Inna tana rusa kuka kamar wata ƙaramar yarinyar da aka yiwa dukan kawo wuƙa.

"Haba Inna wai dan Allah ya kike so mu yi da ranmu ne, ke abin magana baya yawa a wurinki yanzu tsakani da Allah cikin daren nan ki tashi kike rasga kuka kina wasu maganganu marar kan gado" Cewar Sadiya tana miƙa hannu ta ɗakko duka yaran daga gadonsu ta ɗora su a kan cinyarta.

"Lallai Sa'adiyya baki da imani, to wallahi ta Allah ba taki ba maimakon ki tambayeni dalili sai ki rufe ni da faɗa kamar dai ke ce uwata mai daddawa?"

"Tambayar me zan miki Inna bayan kin tasheni kin tashi yaran nan, gashi kina ta faman yi da bakin ki sai kin tashi mai gidan"

"Waye me gida? Na ce waye me gida?Me gida ko dai me gira, ai sai dai a kira mijinki me gira mutumin da ya kwanta yana sheƙa bacci kamar matacce har aka samu wani garsamemen ƙato ya tsallakeshi a falo ya shigo nan zai haikemin, ban da jaraba irin ta ƴaƴan zamani me za a ji a jikin tsohuwa"

"Wai Inna ni fa ban gane ina maganarki ta dosa ba?"

"Na faɗa miki wato sangamemen ƙato ne ya zo ya shiga cikin bargona, dan wulaƙanci ya ƙanƙameni, wata irin ƙanƙama da ya mini wallahi ke kya ce wutar lantarki ce ta kama jikin mutum, bai tsaya iya nan ba sai da ya min ta turawa" Ta faɗa tana sakin kukan takaicin abin da aka mata.

  Imran da ke tsakanin gado da bango ya sauke wata ajiyar zuciya jin Inna bata gane shi ba, ta ɗauka wani ne ya shigo gidan.

"Ya Allah ka ɗora mana abin da za mu iya, dama baka ɗorawa bayinka abin da ba za su iya ba, ni ma na fi kowa da na tsaya kike bani labarin da duka shiruftu ne kawai na tsufa" Sadiya ta faɗa tana kwantar da Husaini da ya sha nonon ya koma bacci.

"Uwaki Rakiya ce take shiruftun tsufa, na ce uwaki Rakindaɓo ita ce mai shiruftun tsufa, yo Allah na tuba har a nunawa na kwance farin wata, ras nake ina sane da komai ba wani tsufa "

"To Inna in ba tsufa ba menene kin ce wai an miki ta turawa dan Allah hankali zai ɗauki wannan wa ma zai gane meye kike nufi bayan ke kan ki baki san me kike nufi ba"

"Babu mai fahimta kam sai mahaukaci, tun da labarin ƙanzan kurege ne nake baki, wato ga mahaukaciya tana bada labarin da mahaukaci ne kaɗai zai gane"

"Allah baki haƙuri, ni dai ki faɗa min wallahi bacci ne a idona" Cewar Sadiya tana kwantar da Hassan da ta gama bashi nono. Wani numfashi Inna ta sauke ganin giftawar da Hassan Sadiya ta yi da shi zuwa gadonta sosai gabanta ya bada rass.

"Na faɗa miki garda'u ne ya shigo ya shiga bargona ya ƙanƙameni har da min ta turawa"

"Mafarki dai kike amma babu wani mai sunan wannan da ya shigo hasalima mu kaɗai ne"

"Bari dai na miki gwari-gwari tun da na ga ke kan kwakwa gareki to ƙwarto ne ya shigo, ya shiga cikin bargona, ya rungume ni har kiris ya min(kiss) wato ya haɗe bakinsa da bakina mai zunzurutun sauran gooron da na ci na kwanta"

  "Subhanallahi! Kwarto kuma Inna, haba Inna wai dan Allah meye damuwarki ne, har waye zai shigo gidan nan in har gaske kwartanci ya zo yana gani na ya j...

  Imran da ke matse gefen gado ji ya yi kamar ya fito ya rufe Sadiya da duka jin ta ce wai kwarto ya barta ya nemi Inna amma ba hali dan yanzu idan ya fito ya yau sai ta Allah.

"Rufe min baki dan Allah, ƙarya zan miki kenan?" Inna ta katse ta tana jan wani dogon tsaki haushi ya sa ta tashi ta sakko daga kan gadon ta nufi makunnar fitilar za ta kunna.

   Imran da ke ganin abin da Inna ke shirin yi ne ya shiga tashin hnkali dan ya san tana kunna fitilar asiri zai tonu, kuma ya san matsawar Inna ta ganshi kashinsa ya bushe. Aikuwa bata yu wata-wata ba ta kunna fitilar Imran saurin sadda kan sa ƙasa ya yi yana fatan kar Allah ya s Inna ta hangoshi. Inna tana kunna fitila idanunta suka sauka a kan Imran dake laɓe kansa sunkuye.

"La'ilaha illallahu muhammdur rasulullahi S.A.W " Cewar Inna cikin karaɗi tana tafa hannuwa. 

"Menene Inna" Cewar Sadiya tana kallon Inna.

"Sakko Halima maza-maza ga kwarton nan a ɗakin shege be dai bai samu damar guduwa  ba, taso Imirana ku taho da taɓarya da madokai yau sai  mun masa dukan kawo wuƙa, hatta mazaƙutarsa (al'aurarsa) Sai mun kwankwatseta mu ga gaba da abin da zai je kwartanci gidan matan mutane"

  Imran hawaye kawai yake zubarwa yau ina zai kai wannna abin kunya.

  Da sauri Sadiya ta diro daga gadon gabanta na dukan uku-uku wai kwarto.

"Subhanallahi! Kwarto kuma Inna, haba Inna wai dan Allah meye damuwarki ne, har waye zai shigo gidan nan in har gaske kwartanci ya zo yana gani na ya j...

  Imran da ke matse gefen gado ji ya yi kamar y fito ya rufe Sadiya da duka jin ta ce wai kwarto ya barta ya nemi Inna amma ba hali dan yanzu idan ya fito ya yau sai ta Allah.

"Rufe min baki dan Allah, ƙarya zan miki kenan?" Inna ta katse ta tana jan wani dogon tsaki haushi ya sa ta tashi ta sakko daga kan gadon ta nufi makunnar fitilar za ta kunna.

   Imran da ke ganin abin da Inna ke shirin yi ne ya shiga tashin hnkali dan ya san tana kunna fitilar asiri zai tonu, kuma ya san matsawar Inna ta ganshi kashinsa ya bushe. Aikuwa bata yu wata-wata ba ta kunna fitilar Imran saurin sadda kan sa ƙasa ya yi yana fatan kar Allah ya sa Inna ta hangoshi. Inna tana kunna fitila idanunta suka sauka a kan Imran dake laɓe kansa sunkuye.

"La'ilaha illallahu muhammadur rasulullahi S.A.W " Cewar Inna cikin karaɗi tana tafa hannuwa. 

"Menene Inna" Cewar Sadiya tana kallon Inna.

"Sakko Halima maza-maza ga kwarton nan a ɗakin shege be dai bai samu damar guduwa  ba, taso Imirana ku taho da taɓarya da madokai yau sai  masa dukan kawo wuƙa, hatta mazaƙutarsa (al'aurarsa) Sai mun kwankwatseta mu ga gaba da abin da zai nemi matan mutane"

  Imran hawaye kawai yake zubarwa yau ina zai kai wannna abin kunya.

  Da sauri Sadiya ta diro daga gadon gabanta na dukan uku-uku wai kwarto.

ne yau a gidanta a ɗakinta taɓɗi.

"Lallai yau idan Abban twins ya kama mutumin nan sai dai uwarsa ta haifi wani" Cewar Sadiya.

  Imran kuwa a ransa cewa yake

"Sadiya ni ne ma yau na san babu mai fahimtar da Inna cewa ba wajenta na zo ba ke ma da kike halalina tana sanya min ido a kn ki bare kuma ita ai cewa za ta yi dan kin haihu ne na je wurinta saboda jarabata" Ya faɗa a ransa yana zubar hawaye ga matsin da yake ciki na gadon ga kuma tashin hankali.

   Waige Inna ta fara aikuwa ya hango kwalbar humra ƙatuwa a kan madubi da sauri ta sungumota tana cewa.

"Yi maza Halima taso mijinki kar kwarton nan ya shammacemu ya tsere ni bari in fara da wannan bata yi wata-wata ba ta ɗaga kwalbar ta rotsa a kan Imran. Wani uban ƙara ya saki da ya sanya Sadiya da Inna gane shi.

   A zabure Imran da ke kwance falo a ya tashi zaune gabansa na faɗuwa hannu ya sanya ya dafe kansa da ya yi mafarkin an rotsa masa kwalba, jin babu danshin jini ya tabbatar da mafarki yake, sai huci yake yana sauke numfashi da sauri gabansa kwa bai bar faɗuwa ba ga wani gumi da ke sarto masa duk sanyin da ake amma shi gumi yake.

Kallon falon yake duk da ba haske amma yana so dai ya tabbatar duk abubuwam da suka faru a mafarki ne, ƙaran saukar munsharin Inna da yake jiyo wa daga cikin ɗaki shi ya sanya ya ƙara tabbatarwa mafarki yake, jaɓas ya koma ya kwanta yana sauke numfashi, tuno da yadda ya haɗa bakinsa da na Inna a mafarki hakan ya sa ya ji zuciyarsa na bala'in tashi har wani amai na neman taho masa hannu ya kai kam harshensa ya taɓa yana so ya ji goron nan na Inna a bakinsa amma jin babu komai bai sa ya daina jin tsantsani da  tashin zuciya ba da sauri ya tashi zaune ya miƙe ya kunna fitilar ya sheƙa waje da gudu jin aman na neman zubowa, amai yake kwarawa tun ƙarfinsa, ƙaran ƙolon amansa ne ya farkar da Inna daga baccin da take, tashi ta yi ta kunna fitilar ɗakin, kallon   Sadiya dake bacci cikin mamakin ganin fitilar falo  kunne ya sa ta nufi falon tana son tabbatar da Imran ne ke amai, ganin baya falon kuwa ta tabbatar shi ne san ta san sheɗanin aljanin nan da ta gani jiya zai iya yin komai, fitowarta tsakar gidan ya yi dai dai da wani irin murɗawa d cikinta ya yi, dama tun kan ta kwanta take jin cikinta na wani iri babu daɗi.

   Ganin Imran na sheƙa amai ta sanya takalminta ta nufi wurinsa tana cewa.

"Imirana lafiyarka kuwa kake ta sheƙa amai da talatainin daren nan ko laulayin ciki kake?"

 Jin muryar Inna ya sanya Imran jin wani tashin zuciyar hakan ya sanya ya cigaba da ƙwaƙulo wani aman"

   "Kai dai ka san jarabar da ka ci kake amai" Ta faɗa tana surar buta ta shige bayi ta ɗan kara ƙofar jin gudawa na neman zubo mata, ga tsoron aljanin jiya a ranta ga kuma gudawa da bata da haƙuri ko jinkirin fitowa.

Ƙaran yadda Inna ke sakin kashi ya sanya Imran jin gabaɗaya duniyar ta masa zafi, haka ya kunna famfo ya wanke fuskarsa da bakinsa ya kora aman ya kashe fanfon ya lallaɓo a hankali ya dawo ɗaki dan gabaɗaya ji ya yi ya galabaita da aman da ya yi, haka ya dawo falo ya kwanta, amma daga ya rufe idonsa bakinsa yake gani cike da goron bakin Inna haushi da takaici ya ishe sa. Bare da ya ki ta shige bayi ta daddage tana sakin gudawa ko ƙaƙƙautawa babu ƙaran kashin sai amsa kuwwa yake masa a kunnuwansa. Inna kuwa jin bata jin ƙaran aman Imran hakan ya bata tabbacin ya bar wurin, cikin sauri ta yi tsarki, ta ɗauki ruwa a cikin kwantainer da ake ajiyewa a bayi ta yi floshing ta fito tana jan ƙafa dakyar. Falo ta shigo ta zauna daɓas a kan kujera, Imran yana jin shigowarta, ya runtse idanunsa da ƙarfi dan ba ma ya son ganinta bare ya tuna mafarkinsa da ita.

"Imirana, Imirana, Imirana? Ta kira sunansa sau uku amma bai amsa ba kuma bai buɗe idon ba.

"Kai dai wannan yaro da mugun hali kake wallahi, kana ji ina kiranka amma ka ƙyale ni, dama maganin gudawa zan ce ka bani idan kuna da akwai a gidan" Banza ya mata.

  "To ta Allah ba taka wallahi Imirana, ace ina maka magana amma ka ƙyale ni dama kana sheƙa amai ma dana maka magana ka ƙyale ni ... Kafin Inna ta gama magana ta ƙara jin cikinta ya bada wani ƙululuuu da hanzari ta tashi ta fita ta sanya takalmi a baibai ƙafar dama a ta hagu ta hagu a ta dama ta nufi bayi duk da tana jin tsoron aljani amma kashin da ua matso ta ba zai ruƙu ba kuma dai ganin Imran idonsa biyu ya rage mata tsoron.

Sai da ta kwashe mintina sannan ta dawo tana zuwa za ta cire takalmi ta ga yadda ta sa a juye.

"Kai Allah raba bawa da wahala gauro a teburin mai shayi, ni Azumi matar Malam yau na ga takaina wallahi, tsabar ruɗewar da na ji cikina ya yi ashe takalmin ma baibai na sa"Ta faɗa tana zaunawa a kan kujerar falon.

   "Kai dai wannan yaro baka da imani kana ganin yadda nake sawu wani kan wani  zuwa bayi amma ba za ka iya ce min sannu Inna ba" Ta faɗa tana kallon Imran da ke zaune ya dafe kai. Kafin ya bata amsa ta ji cikin ya murɗa alamar gudawar ta taho aikuwa ta matse ƙafafuta ta zauna ta ce

"Kai ina dalili hallaw wani kashin ne ke shirin fitowa to babu inda zani kuma ciki ka gaji da ƙuginka ka barni, yo daga dawowata ace wani kashin ya taho bayan yanzu kafin in dawo sai da na tsaya na tsage shi tas, na tabbatar na gama babu wani saura" Ta faɗa tana ƙara matse ƙafafunta tare da zaunawa daram tana danna saitin mazaunanta a kujerar dan kashin ya koma sai wani gaba take tana baya kamar wacce take kan lilo wai duk dan kashin ya koma.

Amma da yake gudawa ne ko alamar komawa bai yi ba, haƙori ta sanya ta danne harshenta da ƙarfi sosai idanunta suka firfito , ai babu shiri Imran sai ganin Inna ya yi ta yi bakin ƙofa a sukwane, takalmin ma a hannu ta ɗauka dan kashin dab yake da zubowa.

  Imran dariya ya fara har da ƙyaƙatawa yadda ya ga Inna ta fita da gudu-gudu tamkar an biyo ta.

 "Wa ya faɗa miki barno gabas take, ai faɗa da mahaukaci ba daɗi, wallahi ba dai ni kika rufe a ɗaki da miciji ba na miki magiyar duniyar nan kika ƙi buɗewa har sai da na gama galabaita da shiga tashin hankali sannan kika buɗe ni kak rinƙa min dariyar na yi fitsari a zaune wai na rakuɓe a jikin bango kamar ƙadangare, son matata ta raina ni, ai dama na sha alwashin sai na rama dan bashi kika ci gashi nan yanzu kina karɓar sakamako" Imran ya faɗa yana dariya tare da tuna muguntar da ya yiwa Inna da dare wacce ta sanya ta gudawa.

Yadda Imran ya yi ya sanya Inna ta samu ruɗewar ciki. Kafin su kwanta da daddare bayan kowa ya watse lokacin da Imran ya dawo sai ya tarar da Inna zaune  a falo da kwanon furarsa a gabanta za ta sha, wani haushi da takaici ne ya sanya ya kasa cewa komai dama ga haushinta da ya wuni yana ji ta rufeshi da miciji a ɗaki yana ta tunanin hanyar da zai bi ya rama sai ji ya yi ta ce.

"Imirana har an dawo kai wai baka da aiki sai zaman gida kamar mace, baka je ɗan yawo ba cikin abokai ku ɗan zanta, kai kullum a gida, haba ina dalili kai ɗan zaman majalissar nan ma na maza baka yi, daga an yi sallar isha'i sai a ganka ka shigo gida zunƙwai-zunƙwai ka kama ƙofa ka garƙame, ina ga masu barka ma da suke zuwa da dare gidan suke samu a rufe" Ta faɗa tana tashi ta fita.

  Shi dai bai ce komai ba, kallonta kawai yake yana ji kamar ya rufeta da duka har sai ta daina motsi. Tana fita wata dabara ta faɗo masa da sauri ya buɗe hannun frige inda ake ajiye magunguna, ya ɗakko wani magani da aka rubuta masa kwanaki da ya kasa tsugunno (Ya kasa kashi) Shi ne likita ya rubuta masa da ya sha sai cikin ya saka ya samu ya yi kashin, murmushi kawai yake ganin ya samo hanyar da zai rama abin da Inna ta masa da sauri ya ɗauki maganin guda huɗu ya zuba mata a cikin furar ya gauraya ya mayar da maganin da sauri ya koma kan kujera ya zauna yana latsa waya kamar bai tashi daga wurin ba duk wannan abin da ake Sadiya tana bayi bata ma san Inna ta buɗe frige ta ɗauki furar Imran ba.

  Ana jimawa sai ga Inna ta dawo riƙe da kofi ta kalli Imran da ke danna waya ta taɓe baki ta zauna ta ƙara ruwa a furar t gauraya ta shiga shan abinta ba tare da ta san ami Imran ya zuba a ciki ba.  Sai da ta sha sama da luday bakwai ta ɗago kai ta kalli Imran da ke latsa waya bata san ba yana ganinta ta gefen ido ba yana dariyar ƙeta a ransa.

"Imirana dan Allah zan baka shawara amma kar fa aka ce santin fura ne ya sa na faɗa, ka daure ka gine wancan filin na tsakar gida kai ma ka yi turaka irin ta maza amma ina dalili kana ɗaki ɗaya da matarka kuma ko yanzu ka zauna ina shan fura kana zaune hakan bai kamata ba" Ta faɗa tana ƙara cika ludan ta sha.

  Wani kallo Imran ya jefa mata, ya cigaba da abin da yake.

"Ka huta tun da ba zaka gina ba, to wallahi idan Halima ta sake haihuwa na zo ZAMAN WANKA baka yi turakar ka ba kana shigowa gidan nan zan fara maka waƙa in ke cewa ɗan cikin mata baki ya koshiye ya ci tuwon mata gumba yake jira ɗan karannana wa zai baka" Ta faɗa tana rausaya kai kamar ƙadangaruwa.

   "Za ki san duk wannan abin idan cikin ki ya ruɗe kika ringa zuwa bayi " Ya faɗa a ransa. Tana cikin shan furar ne Sadiya ta fito daga bayin wata kunya ta rufeta ganin Inna na shan furar Imran amma haka ta dake ta ƙyaleta gudun magana dan ta san yanzu idan ta yi magana sai cibi ya zama ƙari. Da wannan cakwakiyar suka kwanta to shi ne Imran ya yi mafarkin ya shiga bargon Inna shi ne da ya tashi yake kwara amai ita kuma hakan ya yi daidai da lokacin da maganin da ta sha a cikin fura ya fara aiki shi ne ta fara gudawa.

   Yana dariya jin ƙaran tafiyarta ya yi shiru ya dake, haka ta shigo falon tana tafoya dakyar kamar ƙwai ya fashe mata a ciki.

  "Wash kai mai za a yi da cutar kashi, haba ka rinƙa tsugunno babu ƙaƙƙautawa" Ta faɗa tana durƙuwasa a tsakiyar falon dan ji ta yi ƙarfinta ya ƙare, durƙusawa ta yi irin durƙuson masu naƙuda gwiwoyinta a ƙasa ta shiga ƙwalawa Sadiya kira dan duk abin nan da ake Sadiya tana ta shigar bacci.

   Sadiya da ta fara jin kiran Inna sama-sama haka ta daure ta buɗe idonta ganin ƙwan ɗakin a kunne Inna bata kan gadon sai ta tashi zaune.

"Wayyo Sadiya ba kya zo ba in baki wasiyya dan ni na san lokaci ya yi, mu kuma haka Allah ya yi da cutar kashi za mu mutu, mu tashi a lahira muna ta tsula kashi, yo na ji an ce kowa da abin da ya mutu yana yi zai tashi a lahira yana yi, mu kuma haka za mu yi ta keta mutane a filin ƙiyama muna ɗoyi "Inna ta faɗa tana sakin kuka jin cikinta ya sake kiran ƙululuuu.  Haka Sadiya ta taso ta fito a ranta tana jin haushi wannan ZAMAN WANKA ko jaraba ace bala'in safe da ban na rana da ban da daren ma ba a barka ka huta ba.

Amma kuma ganin Inna a durƙushe cikin wani yanayi sai ta nufe ta da sauri.

"Inna lafiya dai?"

"Ke ma dai Sadiya da shegantaka kike wallahi, yo ke da kika ganni na yi durƙuson naƙuda ma har kya tambaya lafiya, rabona da in yi durƙuson naƙuda tun lokacin hainuwar ubanki, amma yau cutar kashi ta sanya na kasa zama da ɗuwaiwukana sai durƙuso" Ta faɗa tana dafe ƙasa da hannuwanta.

"Subhanallahi! Inna me kika ci haka ya ɓata miki ciki?"

"Haba Sa'adiyya har kya tambaya ma menene zai ɓata min ciki ni da bani da ɓataccen ciki gareni ba, ni ai cikina sunansa komai da ruwanka dan komai na bashi karɓa yake, amma yau dai kin ga an saɓa lamba dan kuwa kashi nake ratatata,  amma Imirana kin ganshi nan magana ma ta gagara"

 "Sannu Inna "Cewar Imran .

"Riƙe abinka in dai duniya ce yau naka gobe ma ɗan uwanka kaima wani abun zai sameka ai"

"Babu abin da zai same ni"

"Imirana... Ƙaran da cikin Inna ya sake saki ne ya hanata ƙarasa maganar tata, 

"Halima riƙeni kar in ɓata miki ɗaki dan ba zan iya tafiya ba ma, haka Sadiya ta kamata ta kaita bayin ta jirata da ta fito a ƙofar bayin ma ta watsar da takalman nata haka Sadiya ta kamata ta mayar da ita, frige ta buɗe ta ɗakko maganin gudawa ta bata cikin ikon Allah sai kashin ya tsaya haka suka koma suka kwanta baccin wahala ya ɗauke Inna. Kafin baccin ua ɗauketa take ta tunanin abin da ta ci ya ɓata mata ciki haka, a nan tunanin furar da ta sha ya faɗo mata nan kuwa ta tuna ta tafi ɗakko ruwa ta bar furar a wurin hakan ya sanya ta yi shakku a kan gudawar tata haka kawai ta ji bata yadda da Imran ba "Tabbas Imran ne ya min wannan abun" Ta faɗa lokacin da ta ke kwance kafin baccin ya ɗauketa,

"Wallahi Imirana sai na rama wannan abin da ka min dan wallahi sai ka san Azumi ka yiwa hakan...

      Duk wacce ta san san ta fitar min littafi ta siya ta mn mgn in bata kuɗinta,

  Masu son a tallata musu hajarsu

   mmn afrah      09030283375

[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: ```Wannan littafin kuɗi ne 300 

  Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375  idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

      DAN ALLAH KAR WACCE TA SAYI LITTAFINA DAN TA FITAR MINI,IDAN DAN KI FITAR ZA KI SIYA KI RIƘE KUƊINKI HAJIYA BANA BUƘATA.```

                 1️⃣2️⃣

           WASHE GARI

     Bayan Inna ta yi sallah ta fita duk da jikinta babu ƙwari, ta hura wuta ta ɗora ruwa, dan Sadiya cewa ta yi ta barta ta ɗora amma Inna ta ƙi dan a cewarta Sadiya ɗanyen jiki gareta na jego, shi kuma jikin jego bai son garaje haka dai ta rinƙa komawa tana iza wutar har ruwan ya tafasa. Bayan ta yiwa Sadiya wanka ta barta a bayin ta fito, haka ta haɗa ruwan wankan yaran amma da ta zo maimakon ta shiga can cikin bedroom sai ta ajiye a falo, haka ta kwaso komai da za ta buƙata ta dawo ta ajiye a falon. Husaini ta fara janyo gadonsa ta ajiye ta koma ta janyo na Hasan tana jan sunayen Allah a ranta. Imran da ke zaune yana kallonta ganin tana shirin tuɓe Husaini ya ce.

"Inna wai kina nufin a falo za ki wanki yaran nan? Bakya jin yadda ake sanyi ai cikin ɗakin ya fi ɗumi"

  Banza ta masa ta cigaba da cirewa Husaini famfas, sai da ta gama tana shirin tsundum yaron a ruwa Imran ya sake mata magana a karo na biyu.

"Haba Inna ai da tausayi fa ace kin wankesu a falo baki ji har iska shigowa take ba"

  Dakatawa Inna ta yi daga ƙoƙarin saka Husaini a ruwan ta kalli Imran a shelaƙe tana yatsina fuska ta ce.

"Wai ni kai ka ji na shiga harkar ka ne a yau? Ko baka san idan mutum ba ya ta taka ba ka rabu da shi ba" Ta faɗa tana harararsa dan tun da ta zargeshi da zuba mata abin da ya ɓata mata ciki sai take jin mugun haushinsa saboda irin yadda ta yi ta sawu bayi.

"Yau kuma Inna ke ce bakya son magana?"

"Kai ka kiyaye ni, na faɗa ba na son maganar, kuma da kake zancen wankan yara a falo to ina sane wai karuwa ta taka matar aure, a nan na yi niyyar zan musu wanka" Ta faɗa tana sanya Husaini a ruwan ta shiga yi masa wankan. Shi dai Imran bai sake magana ba ganin ta wani haƙiƙice tana magana. Sai da ta gamawa Husaini ta shirya shi tsaf ta kwantar da shi dan tun tana shafa masa mai bacci ya ɗauke shi.

   "Bismillahir rahmanir rahim, li'ila fi ƙuraishin, aniyar kowa ta bishi, iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in" Cewar Inna lokacin da ta miƙa hannu za ta ɗauki Hassan.

   "Ana tsoronka ɗan mayya, ya ce daga ni har uwata" Imran ya faɗi karin maganar yana kallon Inna.

"Tsoro wajibi ne ai,har gwara wata wainar da ta wake, wani da ya laɓe jikin bango dan tsoro har da sakin fitsarin wahala" Cewar Inna tana cirewa Hassan kaya amma kuma gabanta n dukan uku-uku. Jin maganar da Inna ta faɗa Imran ya ɓata rai dan sai ta tuno masa da jiyan a ransa ya ce

"Fitsari ai ba ni kaɗai ba ke da kika yi arba da aljani kike saki fitsari a tsaye tafiya ma gagararki ta yi sai da rarrafe kika shige ɗaki, har da kwanan ƙasan gado"  A fili kuma ya ce.

  "Ki yi ki wankeshi dai kafin ya sawaya, dan yana fara sawaya zan fice in garƙameki a falon irin na jiya"

  Muƙut Inna ta haɗiye wani yawu da bata san lokacin da ya taru a bakinta ba, jin abin da Imran ya ce na sawayar Hassan, kallon yaronkawai take tana ƙiyasta yadda za ta yi wurgi da shi idan ya zama miciji a hannunta.

"Dan Allah Imirana ka sassauta muryarka kar fa yaron nan ya ji ka tuna masa ya sawaya, ni fa dama saboda gudun sawayar tasa na ƙi zama a cikin ɗaki na fito falo dan idan na ga ya ɗakko sawaya in bar maka shi in gudu" Cewar Inna cikin sanyin murya.

   Dariya ya ƙyalƙyale da ita ya kalli Inna ya ce.

"Wai dama dibara ce kika yi Inna, taɓɗi lallai kuwa kin kama riɓaɓɓiyar igiya dan babu abin da zai hana ni gudu, miciji fa"

  Inna Kallon Hassan take da yake wani miƙa  hannunsa yana wani markwaɗewa ta ce.

"Haba Hasanunu daure-daure ka maida baiwarka ka ji ɗan albarka, idan na wanke ka, na gama shiryaka sannan uwaka Halima ta fito daga wanka sai ka sawaya in ma mesa za ka koma wato babban miciji sai ka koma, amma wallahi jiya ma ban ji daɗin karon ba tun da ka sawaya na rinƙa tsuma ga ubanka Imirana ya kulle ni a ɗakin ai ka sani dan kana ciki kaima har saman drower kaya na ɗane sai gani a ka ɗare-ɗare ba ka ganni ba lokacin ai mun haɗa ido da kai da ina saman ko?" Inna ta kai ƙarshen maganar tana rausaya kai kamar ƙadangaruwa, ta faɗa da alamar tambaya kamar dai yaron ya ma san me take cewa.

" To ka yi haƙuri ka ji, Inna Azumi ce matar Malam wallahi ZAMAN WANKA  na zo wa uwarku Halima ka ga ai baƙon ka annabinka, ni da za ka bi ta tawa ma da ka tsaya a mutum ɗinka har na gama ZAMAN WANKANA na tafi in yaso idan na bar muku gidanku idan ka sawaya ka koma miciji kar ka dawo mutum sai ka yi sati guda ko ma wata guda iyayenka su yi ta famar tsere da kwanan zaune dan nasan dai ba wanda zai haɗa ɗaki da miciji ya yarda ya runtsa dan tsoro ba zai barshi ya yi ko da gyangyaɗi ba bare a kai ga bacci"

"Haba Inna wannan wace irin kuɗuba ce kike yiwa yaron nan?"  Imran da bai san yadda aka yi ba ya miƙe tsaye sai ganinsa ya yi tsaye cankarkar a tsaye.

"Yo ba dole ba in masa kuɗuba ya bari sai na tafi saboda babu daɗi ni tsohuwa ina ganin tashin hankali muraran amma ku da yake da ƙwarinku kuma da sauranku, sannan ma ku kuka haifesa sai ku yi rayuwarku da shi a micijin"

"Dan Allah Inna ki bar wannan maganar ki wankeshi kawai"

"To" Ta ce rana tsunduma Hassan cikin ruwa tare da karanto fatiha da salatul fati"

  Ganin ta sanya Hassan ɗin a ruwa sai hankalin Imran ya ɗan kwanta ya koma mazauninsa ya zauna yana haɗiye wani yawu muƙut.

   Ta gama wanke wa Hassan kansa zuwa fuska ta ɗauraye tana cikin saɓa masa jikin, Imran sai kallonsu yake gabansa na faɗuwa dan shi ko kaɗan bai cire rai daga cewar Hassan ɗin ba zai koma miciji ba, ji yake kamar ya tashi ya fice amma kuma ba ya so Inna ta zargi wani abu haka dai ya daure ya zauna ba dan ya so ba.

A ɓangaren Inna ma haka abin yake wankan take masa amma kamar wanda ta riƙe wuta, tana wanke yaron ne dan dai ba yadda za ta yi, a haka ta juya bayan yaron inda yake fatar miciji ta shiga wankewa cikin tsoro dan gani take tamakar miciji take yiwa wanka, tana ta saƙawa a ranta cewar in ba lalura ba babu yadda za a yi ta haɗa hanya da yaron nan ba bare kuma har ta wankesa.  Juyo cikin yaron da Inna ta yi sai gani ta yi ya koma kamar fatar bayan, idanu ta zaro har tana ɗauke numfashinta dan ta lura Hassan ya fara sawaya. Dakatawa ta yi da wankan ta ajiye sosan.

  Imran da ya lura da yanayin Inna ya sauya amma dai bai san dalili ba dan bai ga abin da ta gani ba ya ce.

  "Inna cigaba da masa wankan mana na ga kin ajiye soson kuma baki ɗauraye masa jikin ba kin bar masa duk kumfa" Ya faɗa kamar wanda ke jira a ce masa kulle ya ce cass dan gabaɗaya a tsorace yake.

   Shiru dai Inna bata tanka masa ba, tana ganin ikon Allah kawai tana jin kamar ta saki kuka ta yi ta ƙugawa jama'a su kawo mata ɗauki in ba ƙaddara ba ace tana riƙe da miciji, halittar da cikin mintu kaɗan za ta sareka ta yi ajalinka lokaci guda.

   Gabaɗaya jikin  Hassan ɗin ya fara sawaya, Imran da ya lura da hakan ya ƙame a zaune tamkar soja, gabaɗaya ya tsorata da lamarin yaron dama da ace ba ɗansa bane babu dalilin da zai sa ko hanyar da yaron yake ya bi amma kuma addu'a ta rigayi fata yaron ya fito ta tsatsonsa ne dan haka yanzu babu yadda zai yi amma a ransa ya fara tunanin bin shawarar Inna ta kaiwa Hassan bakin ruwa dan gaskiya ba zai iya da wannan tashin hankalin ba, gashi mahaifiyarsa ta faɗa masa cewa Hassan mutum ne kawai baiwa ce da Allah ya masa.

  Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Inna da Imran kowa rai fal tsoro kamar farar kura, ganin jikin yaron ya rikiɗa ya zama miciji kansa ne kaɗai na mutum, hakan ya sa Inna sakin wani fitsari ganinta riƙe da miciji da kan mutum. Sakin uban jikin ta yi ta kama kan kaɗai ta riƙe sai uban jikin ya shige cikin ruwan.

"In..In..Innaaa riƙeshi da kyau kar ki je ki sake shi a ruwan nan ya shaƙi ruwan a hanci da bakinsa ya masa illa ko ma ya mutu" Cewar Imran yana wani zare ido kamar ya ce as ya zura da gudu.

   "Ni da zai mutu ma da kowa ya huta" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.

  "Haba Imirana ai na yi jarumta ma da na iya riƙe kan dan na tabbata da kai ne da tuni ka sakashi a ruwan in limewa ma zai yi a ruwan ya lume"

   Gabaɗaya kallon ikon Allah suke sai da Hassan ya koma miciji dukansa, har lokacin Inna tana riƙe da kan,hannunyenta riƙe da wuyan micijin, kallonta kawai Imran ke yi so yake ya tashi ya gudu ya barta amma ƙafafunsa sun ƙi bashi haɗin kai, dan duk jikinsa karkarwa yake dan ko jiya ya ga matuƙar ƙoƙarin Inna da ya rufe ta a ɗaki da micijin, dan da ta rufeshi ji ya yi kamar ya mutu saboda fargaba da tsanani tsoro, ga wani mugun tashin hankali da ya tsinci kansa a ciki yanzu kuma ga ta riƙe da kan miciji.Inna da ke ta hawaye tana jan majina a hanci ta ce.

"Wallahi da ace wannan ba ɗan Halima bane da tuni na daɗe da cikawa rigata iska, na haƙura da ZAMAN WANKAN a ce abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kamar cin tuwon kishiya, kullum jiya i yau, na rantse da Allah da tuni na koma inda na fito gwara gorin Tsalla ya kashe ni dan na san iyakaci ta ce koroni aka yi"

  Duk surutun nan da take Imran ba fahimta yake ba so kawai yake ya tsere.

  "Imirana, matso ka riƙeshi, sai ka zungureshi irin yadsa Halima ta masa jiya ya dawo mutum" Cewar Inna tana kallonsa.

"Am, uhm, wato Inna ki bari wato ainashin Sadiyar ta fito sai ta zungureshi ai kin san da yake a cikinta ya rayu shi yasa ita in ta taɓashi zai dawo"

"Zancen banza ma kenan, wato haka zan yi ta riƙe da wannan abu... Sai kuma ta yi shiru ta kasa ƙarasawa ganin micijin ya kafeta da ido. Imran ma ya ga hakan sai ya yi saurin aro jarumta ya miƙe tsaye dan kar fa micijin saran Inna zai yi ya san kwa tabbas idan ya gama da Inna kansa zai dawo shi kuma bai shirya mutuwa ba.  Inna ganin ya miƙe sai ta gama gane abin da yake shirin yi hakan ya sanya ta tuno da abin da ya mata jiya da dare da kuma alƙawarin cewa sai ta rama da ta yi, hakan ya sanya ta gama shirya abin da za ta masa, musamman da ta tuna cewa Hajiya Amina ta ce wani malami maƙocinta ya ce duk yadda yaron zai zama miciji babu abin da zai yiwa kowa ba zai yi sara ba, sai dai shi miciji ganinsa ma abin tsoro ne gashi da kwarjini musamman wannan Hassan ɗin da girma yake yi sosai idan ya sawaya.

Wata dariyar ƙeta ta yi a ranta, tunawa da irin muguntar za ta masa hakan ya sa ta saki kan micijin da ta riƙe da hannu biyu ta riƙe da hannu ɗaya ɗayan kuma ta miƙa ta damƙo harshen rigar Imran, idanu ya zaro ganin abin da Inna ta yi wani faɗuwa gabansa ya yi da mugun ƙarfi dan ya san matsawar suka haɗa hannu da Inna to tabbas ba za a kwashe da daɗi ba, dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka hannu ya sanya zai fincike rigar amma sai ya ji ya kasa domin Inna ta mata riƙon kazar kuku kamar ma ba tsohuwa bace ta riƙe sai ka ce wani ƙaƙƙarfan ƙaton ne ya riƙe masa.

"Ka zaci za ka iya ƙwacewa ko, to ko uwaka Amina na riƙe sai dai ta saduda saboda ƙarfina da naku ba ɗaya bane kuna nan binni kuna cin kayan daɗi wanda basa riƙe ciki ni kuwa ina can ƙauye ina cin tuwo da danbu wanda suke gina jiki" 

"Haba Inna bayi fa zan je in shiga ya kika riƙe ni"

"Tusugunno za ka yi ba fitsari ba, ban da rainin wayo ni zaka buɗewa ido to wallahi sai dai ka saki fitsarinka a tsaye kamar saniya, dan ba zan sake ka ba, ni ma nan jigilif nake da fitsarin kayana jargaf kamar na yi iyo a ruwan maliya"

   Imran ganin Inna na janyo shi ya sa ya kakkafe tana jansa yana togewa, haka ta janyoshi ta dawo dashi kusa da ita ta ce.

"Sa hannu ka taɓa yaron nan ya dawo mutum"

  Idanu ya zaro ya shiga girgiza kai yana roƙonta ta sake shi.

"Ka taɓa shi na ce, ya dawo mutum yo ban sa ma lalacewa ni da nake ɗorin ɗosano ma na taɓashi bare kai"

"Inna ki min rai dan Allah"

"Ranka yana hannun Allah"  Cewar Inna tana ƙara damƙe rigar Imran sai da ya gama tsurewa sosai ta ga idanunsa sun fito sai zare su yake kamar wanda ya yiwa sarki ƙarya, aikuwa ta sanya ƙafa ta danne harshen rigar Imran, ta sanya hannayenta biyu ta ɗago Hassan a siffar miciji ta ɗorawa Imran a kan cikinsa da yake data janyoshi kwantawa ya yi reran, haka ta .

ɗora masa micijin kan micijin a wajen sai tin haɓar Imran idanun Imran cikin na micijin.

Imran hatta numfashinsa kasa shaƙa ya yi duk tunaninsa ma yadda aka yi Inna ta shammacesa har ta masa riƙon da ya kasa ƙwacewa.

"Ka sanya hannu ka shafa kansa ya dawo mutum in wankesa kafin uwarsa ta fito"

   Ta faɗa tana kallon idanun Imran da ke kafe cikin na micijin dan ya kasa motsa ko da yatsansa ne bare ya iya ɗauke kansa.

"Imran a mace ko a raye? Kai kamar ba namiji ba"

"Wallahi ko maza maza ne ni dole in ɗauke wuta Inna wannan in ban mutu ba ma ai kwanana ne a gaba" Cewar Imran a zuciyarsa hawaye na bin fuskarsa.

Hannu Inna ta miƙa ta ɗan taɓa micijin aikuwa ya ɗan motsa ya kaɗa jela, Imran kuka yake kawai marar sauti.

"Ba ni ka sanyawa abu a fura ba na rinƙa sawu bayi kamar mahaukaciya sabon kamu, daga na dawo wani kashin ya dawo na koma bayin har sai da na dawo na kasa zama da ɗuwaiwukana, ƙarshe sai durƙuson haihuwa na yi, bayan rabona da in yi durƙuson haihuwa tun na naƙudar uban Sadiya amma sai gashi ka sanya tarihi ya maimaita kansa"

   Ganin dai ba ya motsi sai Inna ta sake zungurin micijin aikuwa micijin ya fasa kansa kamar zai sari Imran diff kake ji jikin Imran ya saki, ashe suma ya yi, hakan ya yi dai dai da shigowar Sadiya.

Wani salati Sadiya ta saki tana yin kan Imran da sauri, hannu ta sanya ta zunguri micijin aikuwa sai ya dawo mutum tare da sakin kuka ɗaukansa ta yi, ta ɗora a kafaɗa ta sanya hannu ta shiga jijjiga Imran amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.

"Inna garin ya haka ta faru" Sadiya ta faɗa tana sakin kuka cikin tashin hankali. Wata harara Inna ta jefa mata, ta kalleta ta ce to uwar ƴan son miji ba mutuwa ya yi ba suma ya yi, kuma ba komai ya sumar da shi ba illa soyayyar irin ta uba da ɗa "

Banza ta yiwa Inna ta ajiye Hassan a kan gadonsa da har lokacin bai yi shiru ba ta fita da sauri ta ɗakko ruwa a kofi tana zuwa ta sheƙawa Imran, amma shiru kake ji  wai malam ya ci shirwa, sai da ta ƙara masa ruwan sai ya sauke wata ajiyar zuciya ya buɗe idanun yana wani ƙiƙƙiftawa saboda bai gama dawo wa hayyacinsa ba, dariya Inna ta ƙyalƙyale da ita kallonta Sadiya ta yi cikin jin haushi ta ce

"Haba Inna ya haka mutum ya suma kuma kike dariya.

  Dariyar dai Inna ta cigaba da yi sai da ta yi ta ishe ta sannan ta ce.

" Barni in dara Sa'adiyya wai baki ga yadda idon Imirana ya yi ƙulu-ƙulu ba, kamar an sanya goruba a cikin kwanon sha, ji fa yadda yake kwance magashinyan ko zaune ya kasa tashi"

"Wai ma garin yaya haka ta faru Inna dan  Allah ki bar dariyar nan"

"Baki lura da kyau bane Halima kalli yadda na jiƙe da fitarin tsoro da wahala, to kalli wandom mijinki ma ya saki fitsarin shi ma, amma saboda ragwanta, Imirana har suma ya yi amma ni ina tsohuwa babu abin da na yi, wai fa ɗaukan Hassan ya yi ya ɗora a kafaɗa shi ne kawai Hassan ya koma miciji a kafaɗar tasa wannan ne dalilin da ya sa ya suma kin ga kwa dole na yi dariya ni da bakina Allah ba ya tsaga min ba a hana ni walawa sai ka ce wani kututturen icce"

  Cewar Inna dan bata so Sadiya ta fahimci abin da ke faruwa.

Wani takaici ne ya tokarewa Imran jin abin da Inna ta faɗa, hakan ya sanya ya fara yunkurin tashi zaune dan shi bai ma san ya yi fitsarin ba sai da ya ji ta faɗa.

  "Kama shi mana Halima, bari in taimaka miki, Imran yana ji yana gani aka kamashi da Inna aka zaunar da shi dan duk jikinsa babu ƙarfi tsoro da fargaba sun yiwa gaɓɓan jikinsa katutu hakan ya sanya gaɓɓan yin sanyi.

Inna sai jera masa sannu take saboda kawai neman magana shi kuma Imran yanzu kawai idanunsa a kan Hassan yake da ke kuka gabaɗaya ji ya yi ya tsorata da yaron, Sadiya ɗaukansa ta yi, ta bashinya sha sannan Inna ta ɗaukeshi ta masa wankansa tas aka yi sa'a bai sawaya ba.

    Haka dai aka gyara falon kowa ya gyara jikinsa kafin Ashrof ta zo ta gyagygyara  gidan duka, Imran kuwa ya ƙufuli Inna a ransa sosai.

      ```DA YAMMA```

   Ƴan barka na ta shigowa ƴan unguwa da kuma dangin Mama da kuma abokan arziƙi, Mama da Hajiya Amina tun da suka yi la'asar suka tafi gida, Imran kuma ya fita ba ya nan, Inna da ta fito za ta je kicin, Imran ta gani ya shigo daga waje waya a kunnansa yana magana bakin nan a washe kamar gonar auduga sai sakin fara'a yake. Kallonsa Inna ta yi, ta wuce abinta, lokacin da ta dawo sai ta same shi yana cewa Sadiya.

"Yanzun nan ya iyo min waya wallahi ya ce suna hanya za su zo shi da matarsa barka "

"Ikon Allah to yaushe suka zo garin" Cewar Sadiya tana washe baki ita ma.

"Kin san ai yanzu an maido da shi Kano da aiki yana barek ɗin cikin garin nan" Cewar Imran.

"Allah sarki ka ce yau muna da manyan baƙi gaskiya yaushe rabon su da Kanon ma baki ɗaya sun yi zaman su a lagos abin su"

"Wallahi kuwa"

"Bari na duba ko sun zo" Ya faɗa yana juyawa ya fice. Inna ce ta taɓe baki ta kalli Sadiya ta ce.

"Wai Halima in ce dai gwabna ne zai zo gidan nan?"

"Gwabna kuma Inna"

"Yo in ba gwabna ba waye zai zo da kuka ta rarraba haƙwara a tsakaninku sai dariya kuke na ɗauka ai sai gwabna zai zo dan zai raba kuɗi ma ai a yi dariya"

"Kai ke kuwa Inna to abokinsa ne da ya tafi aikin soja, a Lagos yake aiki shekara da shekaru ma yana can tun kan mu haɗu da Abban twins yake aikin soja"

"Soja??? Inna ta tambaya.

  Kafin Sadiya ta bata amsa sai jin sallama suka yi, cikin muryar da Hausa bata wadaceta ba an ce

"Assalamu alekum" Mata da mijin suka haɗa baki wurin faɗa.  Idanu Inna ta zaro ta kalli Sadiya da ta amsa sallamar ta ce

"Wai Sadiya inyamuraine amma dan daga ji babu hausa a harshensu" Ta faɗa cikin raɗa-raɗa. Kafin Sadiya ta ce wani abu sun shigo tare da Imran, miji ne da matarsa da tsohon ciki sai ƴarsa ƴar kimanin shekaru biyar. Wani ƙato ne baƙi kamar ya shafa shuni.

  "Tabɗi danƙari iko sai lillahi, mutum kamar buhun gero, tamkar dusa yake ci"......Cewar Inna da ta zabura ta tashi tsaye ganin girman mutumin.

           Masu son a tallata musu hajarsu 

09030283375

[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: ```Wannan littafin kuɗi ne 300 

  Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375  idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

      DAN ALLAH KAR WACCE TA SAYI LITTAFINA DAN TA FITAR MINI,IDAN DAN KI FITAR ZA KI SIYA KI RIƘE KUƊINKI BANA BUƘATA.```

            1️⃣3️⃣ ➡️1️⃣4️⃣

  Tsayawa baƙin suka yi cak jin furucin Inna Imran kuwa ji ya yi tamkar ƙasa ta tsage ya shige saboda tsabar kunyar da ya ji ta baibayeshi. Sadiya tamkar ta saki kuka dan takaici, ji ta yi dama ta ce Inna ta shige cikin ɗaki in baƙin sun tafi ta fito.  Dakyar Sadiya ta ƙwaƙulo dariyar yaƙe ta ce.

"Bismillah ku zauna mana, sannunku da zuwa" 

"Eh, eh, eh ku zazzauna mana" Cewar Imran shi ma cikin inda-inda.

  Zauna wa suka yi jikin matar sanyi ƙalaw sai wani haɗe rai take tana hararar Inna tamkar dai ita ta yiwa ba'ar.

"Ku da kuke  cewa su zauna daga matar har mijin babu na ɗauka, yanzu tsakani da Allah mutumin nan ya zauna a kujerarki Halima, sai dai a sayi sabuwa inda hali in kuma babu hali sai dai a jefar, dan babu kafintan da zai iya gyara kujerar nan, ko a duniya masu girman mutumin nan basu da yawa" Ta faɗa tana daga tsaye.

   Sadiya kuwa sai sigina take yiwa Inna da ido tana ta nuna mata ta yi shiru kar fa ta kunyata su.

"Ke ƙyaleni ni fa ƴar gaskiya ce wallahi, in zaka faɗi faɗi gaskiya komai taka ja maka ka biya, babu munafurci, yo ina zan yi munafurci Malam da yake faɗa mana cewa munafuki yana ƙasan kafuri a cikin wuta,  a ce kafuri wutarsa bata kai ta munafuki ba a zafi kin ga kuwa ai abin ba ƙarami bane, kuma wannan ƙifƙifta idon ma ki daina Sa'adiyya dan wallahi babu kyau, yafice da ƙyafuce, ke kuma da kike hararata wallahi ni ban san harara ba sai ido ya faɗi kuma me kike ci na baka na zuba indai ni ce ina dawo wa kan ki" Cewar Inna tana kallon baƙuwar.

  Babu wanda ya yi magana, Imran kuwa yanzu lamarin tsohuwar nan ya fara bashi tsoro dan yana tsoron ya tanka ko ya mata wani abu ta masa ramuwar gayya ta fi ta gayya. Sojan kuwa kallon kan sa yake ta yi yana so ya tabbatar cewa wandonsa na sojoji ne a jikinsa ko kuwa dai tsohuwar bata lura da wandon ba ko dai ita bata cikin masu tsoron sojoji, dan tun da yake a duniya ba a taɓa ci masa fuska irin haka ba duk da tsohuwa ce yana ganin da girma amma ai ba hauka take ba daga shigowarsu za ta fara  musu wulaƙanci har da saurin miƙewa tsaye shi duk tunaninsa ma sara masa za ta yi ko kuma girmamawa ce ta sa ta yi hakan amma sai ya ga saɓanin hakan.

"Abdallah ina wuninku" Sadiya da take son datse maganar ta faɗa ƴar dariyar yake.

"Lefiya lo, Sediya, ya kake ya ya kuma babies?"  Shi ma sojan ya amsa cikin gurɓatacciyar hausar sa dan gabaɗaya zaman kudu ya daƙusar masa da hausar.

"Lefiya lo, to wallahi gwara ma ka ce lefe irin wanda ake yiwa amarya, yanzu fa aka kira ka da Abdallah haba ina dalili kana bahaushe ɗan bahaushe menene kuma lefiya, haka kawai kuna arar yaren inyamurai kuna ɓata mana yaren hausa" Cewar Inna tana komawa ta zauna. Babu wanda ya kulata amma Abdallah ji yake kamar ya shaƙe Inna dan da ace a hanya ne ta musu hakan sai ya mata hukunci. Ita matarsa ma ta kasa cewa komai wace irin tsohuwa ce wa wannan, ransu in ya yi dubu ya ɓaci da abin da Inna take, Imran kuwa kansa a sunkuye yake yana jin a ransa da a ce Inna daga ɓangarensa take a yau ɗin nan sai ta bar masa  gidansa dan ba zai iya da wannan abin kunyar ba. 

  Abdallah kuwa tun da Inna dama ta ce zai lotsa kujera da ya zauna ma sai bai saki jikinsa ba ɗan ɗosanawa kawai ya yi dan shi bai taɓa zaton har ƙibarsa ta kai ya yiwa kujera illa lokaci guda ba.

   Gaisawa dai suka shiga yi da tambayar bayan rabuwa, Abdallah yana jin daɗin ganin twins da ke kwance kan gadajensu sai addu'a yake a ransa Allah sa matarsa ta haifa masa dan tsohon ciki gare ta.

   "Zo yaki nan ƴar yarinya" Cewar Inna tana miƙawa yarinyar da suka zo da ita hannu, da yake yarinyar bata jin hausa dan iyayen basa mata sai bata fahimci me Innar ta ce ba ta dai ga tana miƙo mata hannu, matar Abdallahn ita ta sanya hannu ta dafe yarinyar dan bata so ta je wurin Inna aikuwa Inna ta kalleta ta taɓe baki tare da sakin dariya, sai da ta yi dariya sosai sannan ta ce.

"Wai bakya so ta zo wurina, haba ke kuwa baiwar Allah ki ji da halin da kike ciki mana yadda kike da tsohon cikin nan amma bakya gani ji kike ɗaya kike da kowa shi yasa kika ɗauki wani uban jambaki kika lafta a leɓe to wallahi baki ganki ba yadda kika san akuya ta ci dusa, haka ya miki danɓarɓar babu kyan gani, hodar ma ta miki busu-busu ita da ban fuskarki da ban"

  Ƙwallah ce kawai ta kawo a idon matar, dan tana ganin Inna ta gama da ita yadda ta tsaya ta ɓata lokaci a gaban mudubi tana kwalliya amma tsohuwar nan ta ce mata wai janbaki kamar akuya ta ci dusa, duk da dai tana jin ana cewa idan mace me ciki ta tsufa komai ma ta yi bata kyau saboda yadda wasu mata ciki ke maida su. Dama  dakyar ma ta samu kayan da suka shigeta duk wanda ya sanya rigar bata shiga zanen ma sai ta ga ya ƙi ɗauruwa. Mijin ne ya yi saurin kallonta yana mata alamar da ta yi haƙuri dan ba ya so su nunawa Imran sun ji haushin abin da aka musu saboda kar ya ji babu daɗi haka ta haƙura ta zauna amma ranta in ya yi dubu ya ɓaci.

"Yanzu dan Allah Halima kalli kan yarinyar can, sun jamɓara mata gashin doki a kanta kamar tsohuwar ƴar bori babu kyan gani wai su nan cinyewa ce ni wallahi ban ga ba abin so a gashin doki" Cewar Inna hankali kwance dan ita gani take dai dai take yi kuma gaskiya take faɗa.

Shiru dai ba wanda ya sake tankawa, sai ƙaran TV kawai kake ji da aka kamo tashar namun daji, matarce kallon ya ɗan ɗauke mata hankali, wani miciji da aka nuno ta gani ta ce  "Daddyn Amira ji wani misiji (mijici) ka san ina son misiji " Ta faɗa hankalinta a kan TV kalla kawai ya yi bai ce komai ba dan gabaɗaya ransa a dagule yake. 

   Imran ne ya ce "Sadiya miƙo musu yaran mana, tun a waya Abdallah yake cewa yana son twins" Cewar Imran yana sakin dariyar yaƙe wacce bata kai ciki ba.

     "Allah ya baku ƴan baiwa duka biyu mu ga ƙaryar inyamuranci" Cewar Inna tana hasaso yadda za su yi da zama da yara duka biyu masu baiwar sawaya zuwa micizai.

Tashi Sadiya ta yi ta ɗakko Husaini za ta baiwa mijin, ganin hakan Inna ta yi karaf ta ce

"Ki baiwa matar tasa mana shi sai a bashi Hassan ɗin kin ga sai su riƙe biyu a tare ko sa musu goshi" Cewar Inna tana ɗan washe baki dan ta hango diramar da za a yi saboda ganin Hassan yana miƙa ta san kwa daf yake da sawaya zuwa miciji, za ta ga ƙaryar soja. Sadiya da bata fahimci manufar Inna ba ta miƙawa matar Abdallah Husaini, ta dawo ta ɗauki Hassan da bata lura yana miƙa ba ta baiwa Abdallah shi. Sai yaba kyan yaran suke suna fatan su ma su haifi ƴan biyu.Ƴar tasu ce take ta dariya tana son a bata Hassan amma uban ya hanata yana mata magana Inna da ba sanin me suke cewa ta yi ba sai baki ta taɓe dan yarinyar bata jin hausa sai turanci.

"Za ka yi yaren nasara da kyau wallahi daga lokacin da ka ganka riƙe dumu-dumu da miciji.

"Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta yi dariya kawai tana ta kallonsu, ana jimawa sai kuwa Hasaan ya fara rikiɗa yana sawaya, babu wanda ya lura, sai da ya gama zama miciji sannan ne fa Abdallah ya zaro idanu ƴar tasa kuma sai ta matsa ta yi wurin inda Inna da Sadiya suke zaune, cikin jin tsoro, matar ma a sukwane ta tashi daga mazauninta tana zare ido ta yi wajen su Sadiya, Abdallah kuwa bakinsa ya kasa haɗa ko da kalma ɗaya ne sai zazzare ido yake ya kalli Hassan sai ya ɗago ya bi mutanen falon da kallo, jikinsa a take ya shiga mazari sai karkarwa yake . Imran kuwa tsaye ya miƙe yana so ya tallafawa baƙon nasa y karɓi Hassan ɗin dan ya ga alama ana jimawa Abdallah suman zaune zai yi saboda irin yadda fuskarsan ta bayyana tsoro muraran amma ya kasa ko da yunƙuri ne.

"Ashsha yau ake yinta wallahi a gidan nan, ga soja ga miciji ashe dai sojoji ma suna da tsoro" Inna ta faɗa tana dariya tana kallon Abdallah ba komai ke bata dariya ba irin yadda abokan biyu suke rarraba ido kamar mararsa gaskiya, shi kansa Imran kamar dai yau ya fara ganin Hassan ya zama miciji yadda yake ciccira ido kamar ka ce kulle ya ce cass dan dama a kusa da ƙofar fita daga falon yake a kan kujera amma ganin abin danke faruwa sai kawai ya miƙe tsaye. Sadiya kuwa gabaɗaya ma ta manta cewae ana taɓa Hassan ya dawo mutum gabaɗaya a ruɗe take irin yadda ta ga baƙin mata na yi kamar waɗanda aka sanya wa bakin bindiga a ƙoƙon kai.

Cikin jarumta da daddagewa Abdallah yake ƙoƙorin haɗa laɓɓan bakinsa domin ya karanto ko da addu'a ce amma tsabar tsoro da fargabar da yake ciki ya kasa ko da a magana ce, Kawai kallon ikon Allah yake wai shi ne ɗauke da ƙaton miciji haka miciji mai sanye da riga da wandon jarirai.Ganin  micijin ya kafeshi da ido yana dillo harshensa mai haɗe da dafin da ke cikin bakinsa wanda idan ya sari mutane dafin ke kashe su. Dakyar sai ya iya fara magana, ya fara jero national anthem (Taken Nigeri'a)  Wata dariya ce ta so ƙwacewa Imran ganin Abdallah ya daddage yana yiwa Nigeri'a kirari yana zayyano mata taken ta duk a tunaninsa addu'a yake karantowa. Inna kuwa sai dariya take abinta ta ce.

"Yau de maza sun faɗi yo soja kamar kai ga ƙiba tabarakallah kamar mai cin ƙatuwar tukunyar tuwo amma miciji ya razana ka"

dama ai karanbanin akuya yasa ta leƙa ɗakin kura, gaskiya Hassan kana birgeni yaro masomin babba ubanka ma baka bari ba da baiwarka, to yai kuma ga ubanka soja nan sai rattabo yaren nasara yake (Turanci) Har gwara ni ranar nan da na karanta alif an baki waw zal, a ce daga cikin baƙaƙen larabci suke amma shi ka ga" Ta faɗa tana dariyar. Abdallah kuwa sai gumi yake yana ta karanto taken Nigeri'a yake daga ya je ƙarshe sai ya dawo farko ya sake kamowa jikinsa sai maƙyarƙyata yake.

   Ganin abin da Inna ke yi Imran ya yi ta maza ya ƙarasa gaban Abdallah ya ce.

"Miƙo shi ka huta wannan gumi kamar ka yi tsere Abdallah" Ya faɗa yana tsaye a gaban Abdallah, shi ma Imran ya faɗa ne dan kar Abdallah ya ga bai kyauta masa ba amma har ga Allah ba zai iya ɗaukan miciji ba.

"Haba Imran ta yaya zan iya ɗaga shi ma baka ganin misiji ne (miciji) To wallahi ko kunama ba zan iya ɗagawa ba bare misiji dan Allah ka ɗauke kar in mutu saboda tsoro.

"Daddyn Amira ka bashi micijin mana ya za ka bar miciji a kan ka sai ya cutar da kai" Matarsa da ke rakuɓe jikin bango tun lokacin da ta ajiye wa Sadiya Husaini a kan cinyarta.

"Ƴar jakar uba kai, wa ya faɗa miki barno gabas take, to wallahi mu nan da kike gani abin kunya gaba muka bashi ba baya ba, ashe rainin wayo ne abin naki ɗazu kika ce misiji amma yanzu gashi nan kin ce miciji ashe da hausarku a bakinku kuke rainawa mutane hankali" Cewar Inna tana dariya.

    Babu wanda ya mata magana, Imran ne ya ce.

"Abdallah ya kake national anthem ne wai, duk zaman kudun ne ya sa ka manta da addu'a, Allah fa cewa ya yi Allahzina iza asabathum musibatun ƙalu innalillahi wa inna ialaihir raji'un, amma kuma kai sai kake karanta taken Nigeri'a ko Nigeri'ar ce za ta kawo maka ɗauki. 

" Abdallah dai bai ce komai ba dan ba ma ya fahimtar abin da Imran ke faɗa.

"Mummy let's go home, im afraid" Cewar Amira tana neman sakin kuka.

"Ke rufewa mutane baki kina ƴar hausawa kina magana da bakin nasara, uban leshi ma( let's)  Goron uban wa (go) "Cewar Inna tana zarewa yarinyar ido, da sauri ta matsa jikin Mummynta suka maƙure a jikin bangon tare suna rarraba ido.

   Miƙewa Inna ta yi cikin sanɗa, sai da ta je kusa da Imran da ya bata baya, ta shammacesa ta kama ƙasan rigarsa aikuwa yana ƙoƙarin fisge rigar amma sai da Inna ta dangwarashi ga Abdallah

. Aikuwa ya fara zazzare ido cikin tsoro ya kalli idon Inna da ta ɗaure fuska ya maida kallonsa kan Hassan sannan ya kalli Abdallah da zuwa lokacin bakinsa ne kawai ke motsi ba ma a jin abin da yake cewa.

"Yo kai Imirana haka ake, ai baƙonka annabinka, amma ka ƙyaleshi a cikin ɗimuwa, kuma da kake cewa ya kasa addu'a yana taken Nigeri'a har ƙwara wata wainar da ta wake kai fa sumewa ka yi da ka ga Hassan  a kan ka, kai da kake ubansa bare kuma shi da yake abokinka" 

 Imran ma dai ya kasa magana dan ganinsa dab da Hassan sai ya ji ya nemi nutsuwarsa ya rasa.

"Yiiii, wayyo, a kirawo tawagar sojoji su zo da bindigo su haɗo har da igwa (Motar harbi ta sojoji) Su kawo mini ɗauki" Abdallah yake sumbatu cikin tsoron yana sakin kuka.

"Wallahi babu mai harbe Hassan kawai ku yi addu'a ya dawo halittarsa ta mutane" Cewar Inna da ke tsaye a kan su Abdallah, cikinta har murɗewa yake kan dariya.

  Sadiya da tun da aka fara abin ta zabga uban tagumi hakan ya mantar da ita cewa tana taɓa Hassan ya dawo mutum, sai yanzu da Inna ta faɗa ta tuno da sauri ta tashi ta je wurin Abdallah ta taɓa Hassan aikuwa cikin sauri sai gashi ya dawo mutum tare da sakin kuka, ɗaukansa ta yi, Abdallaj da matarsa da Amira suka bi Sadiya da kallo cikin mamakin ganin tana taɓa yaron ya koma mutum.

Imran gefe ya rarrafa jikin ɗaya kujerar da matad Abdallah ta tashi ya je yana daga kan gwiwoyinsa ya kwantar da kansa a kan kujerar ya rufe idanunsa tare da sakin wata ajiyar zuciya.

Sadiya saka Hassan ta yi a nono, kafin su ankara matar Abdallah ta ja ƴarta sai ganinsu suka yi a bakin ƙofa. Shi ma Abdallah da jikinsa ya mutu murus tsabar kaɗuwar da ya yi, yunƙurin tashi ya yi, bayan wandonsa har da danshi-danshin lema wataƙila ya fara sakin fitsari ne tsabar tsoro.

"To fa yau ake yinta, lallai akwai maza, akwai mata maza, akwai muna maza kuma alamar ƙarfi dai tana ga mai ƙiba, yau dai mun tabbatar duk girman ɗan tsako ƙwai ya fishi, soja kake ko sojojo, wallahi yau dai sai matarka ta maka ruwan zafi za ka ji dama-dama saboda mutuwar da jikinka ya yi, in kunne ya ji jiki ya tsira" Cewar Inna tana kallon Abdallah da ya tashi dakyar ga nauyin jikinsa ga nauyin tsorata.

"Imran za mu wuce" Cewar Abdallah cikin sanyin murya, ya faɗa yana kallon Imra n da ya ɗora kansa a kan kujera yana sauke numfashi da ɗaɗɗaya idanunsa a rufe.

"Uhm, to,to, har za ku tafi?"

"Ya har za mu tafi baka gani abin da ya faru ne ko kai makaho ne" Abdallah ya faɗa yana ɓata rai, ga haushin Inna da yake mugun ji sai dai ya yi alƙawarin sai ya ɗau fansar wulaƙancin da ta masa yau. Haka ya juya yana shirin fita daga ɗakin Sadiya ta ce .

"To muna godiya ƙwarai, mumyn Amira ku gaida gida"

"Gida ya ji" Cewar Mummyn Amirar amma Abdallah da ido kawai ya bita bai ce komai ba. Imran ma miƙewa ya yi zai musu rakiya, yana kallon Inna da ta kafe su da ido shi da abokinsa tana sakin wani murmushin jin daɗi da alama wasan da ya gudana ya mata daɗi.

"To Sojojo ka gaida gida sai kuma ranar suna, kar kuma in kuma jin ko da wasa ka kira kanka Soja marmari daga nesa, in kunne ya ji jiki ya tsira, kai kuma Imirana ka dawo yanzu ka riƙe mata Hassan ta yi wankan yamma" Cewar Inna har lokacin bata tsagaita da dariya ba.

Fita suka yi suna tafiya kamar mararsa lafiya, dakyar Abdallah ya iya buɗe ƙofar motarsa ya shiga, matar ma da kanta ta buɗe suka shiga da ƴar saɓanin kullum da shi ke buɗe musu su shiga ya rufe. 

"To Abdallah nagode Allah bar zumunci, ranar friday ne sunan" Cewar Imran da ke riƙe da marfin ƙofar. Shiru Abdallah ya yi bai ce komai ba.

"Sojojo, Sojojo, kai Sojojo" Cewar Inna da ta fito daga cikin gidan riƙe da ledar viva.

"Imirana tsayar da su sun yi mantuwa" Cewar Inna tana ƙarasowa.

"Ga kayanku kun manta"

"Ki mayar na babies ne da muka kawo"

"To,to,to, Allah amfana madallah, Allah sa a daɗe ana yi sai kun zo suna" Ta faɗa tana juyawa ta koma cikin gida.

    Masu son a tallata musu hajarsu 09030283375

[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin kuɗi ne 300 

  Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375  idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

   A wurin Inna ta baro su ta dawo gida riƙe da ledar, tana shigowa ta ajiye ledar ta nufi kujerar da Abdallah ya zauna ta danna da hannunta, ta ƙara taɓa inda matarsa ma ta zauna ta taɓe baki ta ce.

"Halima kin ga abin da nake faɗa miki ko? Da kin ce mutanen nan su zauna a ƙasa dan wallahi baki ji yadda kujerar ta faɗa ba gabaɗaya ta lotse dan ji na yi har katako da ƙarfen ciki ina taɓowa musamman wacce Sojojo ya zauna, dai dai ma an yi ba bashi sun kawo kaya masu tsadar gaske" Ta faɗa tana taɓe baki ta zauna a ƙasa ta shiga fito da kayan jariran na cikin ledar kaya ne masu kyau da tsada har da turmin atamfa.

"Kai, kai, kai, taɓɗi ashe dai Sojojo an iya abin arziƙi, to Allah amfana" Har lokacin Sadiya bata ce mata komai ba dan ita yanzu abin Inna yana ɗaure mata kai sosai ta gaji ma da wannan ZAMAN WANKAN  gabaki ɗaya.

"Yo ko ki yi magana ko ki ƙyale, duk ɗaya dan kin ga wannan kayan da suka lodo miki  kamar bashi yake dan kin ga matarsa ma tsohon ciki gareta dole idan ta haihu ke ma ki ki mata" A dai dai nan Imran da ransa ke ɓace ya shigo da sallama ciki-ciki.Amsa masa Sadiya ta yi.

"Imirana ka ga abin arziƙin da Sojojo ya kawo maka, kaima dai Imirana wallahi da karambani kake, banda karambanin akuya mai sa ta leƙa ɗakin kura, ina kai ina wannan mutumin him guda dashi, yanzu a ce ka rasa aboki sai wannan rungujejen abu kamar himilin kaya ina abokin ka  Abida tun ranar da ya kawo mu shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, amma wannan Sojojon da kuka jeru sai na gan ka abu ɗul kamar ruwan aski.

  Banza ya mata ya shige bedroom dan daga Inna har Sadiyar ma haushinsu yake ji.

"Aniyarka ta bika Imirana in ƴaƴan naka kake yiwa baƙinciki dan an kawo musu kaya, wato so ka yi kuɗi ya bayar ka yi wuf da su ko?, gashi ma har yau babu sadakin gado babu dalilinsa, ka murtsuke ƴar mutane ka mata ciki ta haifa maka ƴaƴa har biyu amma har yau babu ragunan suna ga lokaci na ta tafiya, sai dai ka kawo wani ɗan nama a ƴar baƙar leda wai na me jego ne, yo wane irin me jego kawai a kawo tirkakkun raguna, ah to mun gaji da gafara sa bamu ga ƙaho ba, dan ba dani ba gaɗa a kabari in ji ƴan magana"

  Babu wanda ya ce komai shi ya shige ɗaki ya kwanta yana ta jiyo Inna yana kuma tunanin abin da zai mata.

"Oh ni Ashrofa sai ka ce an aiki bawa garinsu, daga cewa za ta je gidan su ƙawarta ta dawo amma har yanzu bata dawo ba"

"Me za ta miki to idan ta dawo ɗin?"

"Haba Halima har na rasa abin da za ta min yunwa nake ji"

"To ki zubo abincin mana"

"A'a ni ba shinkafa zan ci ba so nake ta dawo ta dafa mini indo momi (indomie) Taliyar yara akwai daɗi wallahi"

  Kallonta kawai Sadiya ta yi bata ce komai ba.

            ~DARE~

  Tun da ya kwanta yake juyi a katifar, ji yake kamar ya je ya iyo waje da Inna daga ɗakin nan ya kulle, dan gabaɗaya yau ba ya jin jikinsa dai dai. Zaune yake ya zabga uban tagumi mararsa sai murɗa masa take tana neman ɗauki, haka ya dafe marar yana yin salatin annabi S.A.W Ya daɗe a haka zuwa can ya tashi ya leƙa bedroom ɗin fitilar a kashe sai dai ɗakin ba duhu sosai da yake hasken farin wata ya ɗan shigo ta gefen labule. Ba ka jin komai sai ƙaran komai a ɗakin dan Inna ko munsharin ma bata yi, hakan ya sanya ya ɗan fara lalume har ya ƙarasa wajen gadon tsaye yake yana ta nazari so yake ya gano wacce ce Inna wacce ce Sadiya dan ya lura yanzu kowacce tana iya ɗaukan bargon kowacce ta rufa haka zalika suna iya canjin wurin kwanciya saɓanin da kowacce na kwanciya a gefen da take kwanciya.Kan gadon ya hau sai da ya zauna a tsakaninsu ɗare-ɗare so yake ya gane matarsa ya shiga bargonta ya kwanta a kusa da ita ko ya samarwa kansa nutsuwa, kunne ya kai ya kara a saitin bargunan dan ya tantance na Sadiya dan gabaɗaya kowacce ta rufa ne har kanta.

   Kunne ya miƙa jikin bargon Sadiya dan ya tantance ita ɗince a ciki ko kuma Inna ce a ciki. Garin kara kunne sai ya ɗan zame hannunsa ya buge na cikin bargon ashe dai Inna ce a ciki, wani uban juyi da ta yi da miƙa shi ya sanya Imran tsorata dan ya ɗauka zaune za ta tashi, idan kuwa ta gan shi a kan gadon a tsakiyarsu tabbas za a kwashi daru, da sauri ya yi wata shala sai gashi a gefen gadon wurin inda akwatuna suke, durƙusawa ya yi yana kiran sunayen Allah. Jin shiru babu motsinta sai ya ɗago kai a hankali ganin ta cigaba da barcinta sai ya lallaɓa ya fito daga ɗakin da rarrafe dan ba ya so ma ya tashi tsaye ta ji motsinsa a samu matsala.

Haka ya dawo falon wani haushi da takaici na damunsa, ga mararsa da har lokacin bata daina ciwo ba, fitilar falon ya kunna ya fita domin zuwa kicin.

"Kai da matarka halalinka amma kake raɓewa in za ka wajenta kamar wani kwarto" Cewar Imran a zuciyarsa, yana nufar kicin ya ɗakko jar kanwa ya jiƙa ya sha dan ya rage sha'awar da ke damunsa haka ya dawo ya kwanta yana jin ɓacin rai fal ransa, ya so ya shiryawa Inna wani abun cikin daren nan amma rashin nutsuwa da kuzari ba za su barshi ba haka ya haƙura ya kwanta yana cewa "In kere na yawo zabo na yawo wata rana za a haɗu.

     *WASHE GARI*

  Kamar kullum yau ma haka Inna ta haɗa ruwa sai dai cikin ikon Allah har ta wanki Hassan ta gama amma bai sawaya ba, haka ta shirya su tsaf.

         *DA YAMMA*

  Suna zaune a falo Ashrof, Sadiya da kuma Inna Imran ya fita ba ya nan, sallama ake yi a Ashrof ta amsa da ta leƙa sai ta ga Abid ne.

"Ya Abid ina wuni" Lafiya  ƙalaw Ashrof ya mama ina Hajiya Inna?"

"Mama tana gida Inna kuma tana ciki in nemanta kake"

"Kamar kuwa kin sani saboda ita na zo, ki ce tana nan ana shan ZAMAN WANKA"

"Eh" Cewar Ashrof tana ƴar dariya.

  Tare suka shigo Inna na ganin Abid ta fara murna tana cewa

"Lale da Abida sannu da zuwa"

  Shi ma dariyar ya yi ya zauna yana gaishe da Inna suka gaisa da Sadiyar.Ya tambayi kwanan yaran nan aka bashi amsa da lafiya ƙalaw.

"Wallahi abubuwa ne suka ɗan sha kaina ban samu na dawo ba, na ga yaran ba"

"To wane gani kuma kai da muka dawo da kai daga asibiti da su" Cewar Sadiya tana ɗan murmushi.

   "Haba Sadiya ke me yasa kike haka ne ni wai, ai in kin ji an ce za a ga mutum ba wai gani na ido ba ake nufi. Baki ga ƴan siyasa ba ko masu kuɗi idan ƴan maula suka je wurinsu sai su ce zan ganka zuwa gobe, to ai suna nufin za su sallami mutum da wani abun shi ne hausar" Cewar Inna tana kallon Sadiya, Sadiya kwa da Ashrof kunya ce ta rufe su ai hakan kamar roƙo ne. Wani yatsina fuska Sadiya ta yi take yiwa Inna kallon irin me yasa haka.

"Kai ka ji ni da mata, yo sai ka ce wani wanda na yi saɓo, kawai dan yarinta ta sa kun kasa gane inda maganar Abida ta dosa na warware muku zare da abawa  sai ki rinƙa zare min ido kamar dai ke ce uwata mai daddawa"

"Rabu da ita Inna ai gaskiya kika faɗa kuma ni ma dama irin ganin da na zo na musu kenan" Cewar Abid yana dariyar maganganun Inna sosai ya so ya dawo amm abubuwa suka masa yawa amma da tuni ya dawo ko dan ya ci dariya.Ya kuma ga irin zaman da ake tsakaninta da abokin nasa dan Imran ya ƙi bashi labarin komai kuma ya san tabbas akwai wata a ƙasa dan babu yadda za a yi a zauna lafiya tsakanin Imran da Inna.

"Ga wannan Inna naki ne wannan kuma na jarirai" Ya faɗa yana miƙa mata manyan ledoji guda biyu, ɗaya kayan jarirai ne da less mai shegen kyau na Sadiya, sai kuma ɗayar atamfa ce da goron cikin farar leda.

"Ayyiriri, taɓɗi yau ake yinta ai shi sa jiya nake tambayarka a wajen Imirana , nagode Allah saka da alkairi, ya buɗa maka, wallahi Abida ka fiye min Imirana sau dubu ka ga Imirana ko goron murtala (Ashirin) Bai taɓa siyo wa ya kawo min ba bare turmin zane" Cewar Inna tana sakin goɗa tana ɗaɗɗaga atamfar.

"La ba komai Inna in ba a kyautatawa tsofaffi ba wa za a yiwa"

"Kai dai da ka san hakan amma Imirana mai ya sani yaron nan banda ƙafafa da nuna shi mai gida ne"

"Imran ko Inna"

"Shi mana, bari ma na baka labarinsa, amma sai na fara baka daga farko ranar da na kwana ban yi bacci ba"

"Baki yi bacci ba fa Inna, garin yaya?"

"Wallahi fa Abida, haka kawai ban ji ba ban gani ba,ina ranar da ka kawo mu daga asibiti har nake baka labarin abokin Imirana wanda ke wasarere da jikinsa"

"Eh Inna na tuna"

"To wallahi a ranar nan ni na san irin kwanan da na yi a gidan nan" Ta faɗa tana share ƙwallah.

"Subhanallahi Inna ba dai a waje kika kwana ba da sanyin nan?"

"Haba Abida ana ga yaƙi kana ga ƙura yo ba gwara a saka ni a randa ba in kwana da irin kwanan da na yi ranar nan kai ni dai sai da na ji ina ma ban taho ZAMAN WANKAN nan ba, ni da na kwana a tsakanin katako sama katako ya tokare ƙasana katako "

"Katako kuma Inna"

"Yo a ƙarƙashin gado fa na kwana, bayan nna nawa da gado ya matse yadda ka san an yiwa mota lodin shanu haka na ji, wallahi ba dan na shafa man zafi ba da Allah kaɗai ya san me zai faru.

" Ta faɗa tana ɓantarar goron da fa ɗauka daga cikin wanda aka kawo mata ta ƙulle ledar.

"Garin yaya?"

  Shiru ta ɗan yi dan bata son faɗar gaskiyar dalilin da ya sa ta kwana a ƙasan gado dan har yau bata daina jin tsoron aljanin ba kuma har yau tana ganin kamar dai yana kallonta a gidan.

"Sanyin garin nan ya sa na kwana a ƙasan gado" Ta faɗa tana ƙara gutsurar goro fuskarta ɗauke da damuwa.

"Sanyi fa Inna, lallai sanyi bai kyauta ba" Ya faɗa yana dariya dan ya fuskanci bata faɗi gaskiyar abin da ya sa ta kwana a ƙasan gadon ba dan daga yadda ta faɗa ya san ta faɗa ne kawai, ga kuma 

yadda take bada labarin ma kaɗai abin dariya ne.

"Sanyi mana, ai ba fa shi ne abin da na fuskanta ba kaɗai, ka san Hassan ya zo da baiwa a jikinsa wato haka kawai sai yaro ya ringa saɓaɓa-saɓa ya bar ainihin halittarsa ya koma ta miciji"

"Miciji Inna" Ya faɗa da yana son tabbatarwa dan ya san dai Imran ya xe fatar bayan yaron ta miciji ce.

"Miciji mana, ai a washe gari da haihuwarsa ya koma miciji da kan mutum amma saboda rashin imani na Imirana haka ya garƙameni da micijin nan a ɗaki tun ina neman ɗauki har na gaji, ya sanya na rinƙa karanta alif an baki waw zal, kai daga ƙarshe dai sai ga Azumi a saman drower na hau can tsililiko ina reto"

  Dariya kawai yake, da jin labarin ya san dama tabbas a rina wai an saci zanin mahaukaciya dan ba za a ƙarƙe ƙalaw ba da Inna da Imran saboda basa jituwa.

.

"Lallai Inna kin yi ƙoƙari" Ya faɗa had lokacin ya kasa tsaida dariyarsa, Ashrof ma sai tayashi take duk da Sadiya ta bata labari amma sai ta ji kamar yanzu ne ake farkon jin labarin.

"Kai Abida baka cin ribar zance ne, ka tsaya ka ji yadda ta kaya mana tsakanin ni da Imirana ai bai fa ci bulus ba, mutuminka na sanya Sadiya ta ƙwala masa kira lokacin ya sha dariyarsa ya more, a raina na ce bakin dariya shi ne na kuka, ai yana shiga ɗakin na shammacesa a janyo Halima muka fito na bankeshi a ɗakin, kira yake Inna ki buɗe dan Allah, aikuwa na yi kunne uwar shegu na ce sai na rama sai da ya horu sosai a ɗakin na buɗe, ka san ya na ga Imirana" Ta faɗa tana dariya, su ma dariyar suke har Sadiya da ta kasa riƙe tata dariyar, hakan ya sanya Imran ya shigo yana ta sallama basu ji ba da yake bai wani ɓuga maganar ba dama jikinsa ya bashi ana cin namansa a gidan tun da ya ga motar Abid a waje ya san Inna tana nan tana bada labarinsa.

"Yana laɓe a jikin bango yadda ka san ƙadangare ya rakuɓe a waje ɗaya sai maƙyarƙyata yake kamar kazar da bazai ya kamata" Ai gabaɗaya suka ɗauki dariya har Inna a dai dai nan Imran ya shigo falon sai haɗe rai yake kamar zai kai musu duka.Ɗif suka daina dariyar sai Abid da ke ƙoƙarin danne dariyar taƙi tsayawa har ruwa idanunsa suka kawo saboda dariya sosai yake hango yadda abokin nasa ya yi, a rakuɓe a ɗakin ga kuma miciji a gefe, tsaf Inna ta iya bada labari yadda mai sauraro zai ji kamar a gabansa ake yi.

"Abokina ka dawo? Ka ganni kamar an jefoni daga sama ko ban maka waya ba" Cewar Abid yana goge ƙwallar idonsa da dariya ta sa ta taru. Wani mugun kallo Imran ya masa wanda ya sanya wata dariya ta ƙwacewa Abid aikuwa ya sakikayarsa dan ya kasa riƙeta.

"Ai abin akwai abin dariya Abida dan ma ba a gabanka aka yi ba" Inna ta faɗa tana dariyar dan ganin Imran ma sai ta sake ƙara ƙarfin dariyarta dan ta ƙular dashi tun da shi bai san abin arziƙi ba.

"Yo da kana siyo min ɗan goro da turmin zane, ai da na ɗan rangwanta maka ka san zuciya tana son a kyautata mata" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Kallai abin arziƙin da abokinka ya kawo min, wancan na gaban Asharofa kuma ya ƴaƴanka ne da matarka"

"Ta faɗa tana kallon Imran da ke ƙoƙarin ajiye ledojin da ya shigo da su.

"An gode" Kawai ya ce tare da juyawa zai fita.

"Amma kuwa yau nan tabbatar ta mugun halin ka Imirana ace a kawo wannan uban kayan kuɗi amma ka yi godiya ƴar mitsitsiya, ina laifin ma ka ce an gode madalla Allah amfana Allah saka da alkairi ya bar zumunci, ka ƙara da cewa kai amma kayan sun yi kyau sosai har da Inna ma aka kawo wa to madalla, amma dan baƙinciki kake min kuma da baƙin halinka Imirana  shi ne ka ce an gode a takaice" Cewar Inna tana gatsinen gefen hanci.

"Haba Inna ai tsakaninmu ba godiya" Cewar Abid a fili yana ƙara maƙe dariyarsa. A zuciyarsa kuma ya ce na tabbata Imran ya ji Inna tana bada labari amma babu yadda zai yi da ita, kuma gashi magana take faɗa masa a kan ƙin doguwar godiya kuma ba yadda zai yi da ita lallai Inna ita ce maganin Imran.

"Ka ji ɗan arziƙi irin albarka, wallahi kana birgeni Abida...

"Idan ka gama neman maganar ka same ni a waje" Imran ya katsewa Inna maganarta yana  kallon Abid tare da ficewa cikin ɓacin rai.

"To ina fitowa " Cewar Abid yana bin bayan Imran da kallo dariya na cinsa.

"Kai rabu da shi yana ta ƙuncin rai ka yi zamanka a nan mu sha hira in maka abin ban faɗa maka ba"  Cewar Inna tana kallon Abid.

  "To  Inna"

"Ashrof miƙa masa yaran ya gan su" Sadiya ta faɗa cikin sanyin murya dan yadda ta ga Imran na harararta da ya shigo hakan ya sanya ta gane bata kyauta ba da aka zauna da ita ana bada labarinsa suna dariya.

  "Lah ta barsu ma tun da bacci suke kar a tashe su, ai ni nan tunda gidan zuwa na ne na gansu wata rana"

"Kana ji ko Abida jiya kurman abokin nan naka ya kawo  abokinsa Sojojo"

"Inna meye kuma Sojojo ko suna ne?"

"Ina kai ka, baka cin ribar zance"

"To ina jinki Inna"

"Nake faɗa maka Sojojo  ne dan bana kirashi Soja ba saboda ragwantarsa"

"Ragwanta kuma Inna"

"I mana" Inna ta faɗa tana kwashe duk yadda aka yi da Abdallah da ya zo barka da matarsa.

"Inna haka aka yi ashe haɗe su kika yi, kai abokina ba dama" Ya faɗa yana dariya

"Kai dai bari yo shi ma Imiranan ranar nan fa suma ya yi saboda Hassan ya sawaya ya zama miciji a jikinsa" Ta faɗa tana dariya. Haka suka sha ta dariyarsu har cikin Abid yana ƙullewa dan ya ma manta Imran na jiransa a waje. Sai can ua tuna ya musu sallama ya sanya hannu a aljihu ya ɗakko dubu ɗaya ya miƙawa Inna. Hannu ta sanya ta karɓa tana washe baki.

"Haba Abid ai da ka barshi hidimar ai ta yi yawa " Cewar Sadiya cikin jin nauyin Abid.

"Lah ba kamai ai...

"Rabu da ita kawai in banda baƙinciki meye wata dubu ɗaya dan ya bani kyauta zaki wani haƙiƙice kina cewa ya yi hidima ai dama kowa ya san ya yi hidima musamman da ya fi mijinki da bai san ya siye zuciyar mutane da kyauta ba sai baƙin hali da na zuciya fal ransa" Ta faɗa tana sanya dubun a cikin ƴar pos ɗinta.

  Dariya Abid ya yi jin abin da Inna ta ce haka kawai shi ds a ce za a barshi da Inna da ya huta d shiga damuwa ko ɓacin rai, saboda ita bakinta ba ya shiru kuma bata gajiya da abin dariya duk da ita tana yin komai dan raha ne.

"To Inna sai kwana biyu"

"Kwana biyu fa Abida sai ka ce an maka baki, yanzu sai ka iya kwana biyu baka zo mun gaisa ba, ai baka ji daɗin da na ji ba da ka bani bugun Abujar nan"

" To Inna idan na samu dama da lokaci zan ke leƙowa "

"To nagaode sosai" Ta faɗa lokacin da ta fito har ƙofar falon Abid ya sanya takalminsa ya fita.

"Oh ɗan nan da kirki yake Sa'adiyya ya fi min mijinki Imirana sau miliyan ma" Cewar Inna lokacin da ta zauna a kan kujera tana ƙara ganin atamfarta.

"Inna dan Allah kike iya bakin ki idan abokan Imran sun zo kin ga ko a fuska ya nuna ba ya so kina shiga shirginsu" Cewar Sadiya cikin lallaɓawa dan ta san Inna hukuma ce sai da lallashi.

"Ikon Allah, lallai Halima wuyanki ya fara isa yanka sauran kuma a gwada wuƙa a tabbatar, yanzu sabibi da Allah ni kike faɗawa wannan maganar to ni da banda ma gaisawa da muke a ɗan taɓa hira ina ni ina su, ni fa kawai dan na ɗaukesu ɗaya da ku ne tamakar jikokina in ba haka ba me ma zai haɗa ni da su, in kuma baƙincikin ɗan abin da zan ke samu kike yi to duk da babu wanda ya taɓa bani wani abin arziƙi in ba Abida ba"

"Abid Inna" Cewar Ashrof.

"Ke ki kiyaye ni, in ma  Abu zan kirashi ina ruwanki"

"Ki yi haƙuri Inna" Cewar Sadiya.

"Da haƙurin ta mutu sadakar nawa kika bani?"

"Allah baki haƙuri"

"Haƙuri kaya  ne naɗa gammo ki ɗauka"

Bayan fitar Abid Inna ta ce ta gaji da zaman cikin gidan fita za ta yi ta zagaya ƙafadunta dan ciwo suke mata, gidan Hajiya Amina za ta je.  Haka ta musu sallama ta fita ta sha wata atamfarta mae kyau, ta saka ɗan madinanta ta kama hanya ta fita, har Sadiya ta bata kuɗi ta hau ɗan sahu amma ta ƙi karɓa wai ita ta fi son tafiya a ƙasa saboda kalle -kalle.

  Hanyar gidan Hajiya Amina ta kama, har sai da ta je gidan bayan ta gama kalle -kalle da ratse -ratse. Haka ta je gidan Hajiya Amina suka gaisa ta ɗan jima sai kuma ta kamo hanya ta taho gida dan Hajiyar ma sai da ta yi ta yi da ita a kan ta zauna idan aka yi sallar magariba ta yi sallar sai ta tafi, amma Inna fafur taƙi zama dan ta fi so ta taho ido na ganin ido. Saboda ta fi so ta taho ido na ganin ido dan ta ga gari gari ma ya gan ta.

dan haka ta kamo hanyarta ta taho riƙe da ledar da Hajiya Amina ta zuba mata bakilawa. Tana tafe tana kalle-kallenta tana ƴar waƙarta a hankali, tana cewa.

"Carman dudu carman duduwa , carmagade, akwai wani baƙo a gidan mai gari, carmagade, ba duka ba ya lakuci, carmagade, in duka wa zai bashi ne, carmagade, aradu ta Allah ba zan bashi ba" Tana cikin yin waƙar ne ta hango wani ƙerarran gida mai shegen kyau tun daga nesa gidan ya birgeta. Dan dama ba ta hanyar ta bi ba a tafiya yanzu kuma sai ta canja hanya dan ta sake ganin wasu sabbbin abubuwa ba irin wanda ta gani a tafiya ba.

"Ikon Allah masu gidan nan kuwa sun san ana wahalar kuɗi kuwa a duniya, an ya kuww sun san sunan wani abu wai babu, ace wannan gida kamar ba a duniya ba" Ta faɗa tana tsaye tana ƙarewa gidan kallo.

  "Oh ni Azumi ina can a ƙauye ina fama da ɗaki ɗaya a gidan Malam kullum ana bala'i da Tasalla to ina kuma ga na ganni a gidan nan ina ga kuma sai an mana tsakani da Tasalla dan kar take faɗawa mutane ita kaɗai ce matar gidan" Ta faɗa tana ƙarasawa ƙofar tangamemen get ɗin da ke buɗe, sai da ta tabbatar babu kowa mai gadin ma ba ya nan...

    Masu son a tallata musu hajarsu MMN AFRAH 09030283375

             1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣

"Aikuwa dai sai na shashshafa gidan nan da hannu na, a saka a baka ai ya fi a rataya, ko da a ce baka da rabon zama a cikin waɗan nan gidajen a duniya to kafin mu je aljanna mu samu rabonmu gwara dai na taɓa in ji, ai da hanau gwara mannau" Cewar Inna tana dosar wajen, hannunta ta kai jikin ginin ta shafa shi da hannu biyu kamar wacca ta samu ka'aba har da jingina fuskarta a jiki ta goga fuskarma a jiki hagu da dama.

"Na taɓa ka da alkairi gidan ƴan gayu" Tana ƙara shafawa. Haka ta rinƙa bin wurin tana ganin ginin tana gyaɗa kai alamar mamaki.

"Oh ni ƴasu mutane masu kuɗin nan ko a ina suke samun kuɗaɗe haka su yi ta baje hajarsu a duniya son ransu, ko kuwa rijiyar haƙo kuɗin garesu irin wannan gida, to mu da bamu dashi haƙuri ya ganmu, dan ma dai da daɗi saboda Malam ya faɗa mana cewa ko a lahira sai talaka ya riga me dukiya shiga aljanna, yo kai da baka da kuɗi ina ka ga tarin tambayoyin da za ka amsa dangane da ina ka samo kuɗi kaza, ta wace hanya ka kashe su" Ta faɗa tana kama haɓa har lokacin kaɗa kai take kamar ƙadangaruwa. Leƙa cikin get ɗin ta ɗan yi daga inda take tsaye ta yi dogon wuya tana so ta ga ko za ta hango me gadi, amma babu abin da take hangowa sai tarin fulawoyi masu matsanancin kyau.

"Ni Azumi da a ce zan samu shiga cikin nan ɗin ma ba tare da na zauna na yi rayuwa a ciki ba, da wallahi tallahi iya hakan ma na godewa Allah kuma na ji daɗi, yo in ban shiga na gani ba na kashe ƙwarƙwatar ido na ba me aka yi da maza, kawai shiga zan yi komai ta fanjama fanjam" Ta ce tana takawa a hankali cikin sanɗa ta durfafi get ɗin, tana shiga sai ta ga ashe ma babu abin da ta gani a waje motoci ne gasu nan wasu a lulluɓe wasu a buɗe.

"Ikon Allah na kwance ya faɗi wato dai a duniya ma akwai aljannar duniya, lallai masu gidan nan kun huta amma duk da haka ba za mu shiga sahun ƴan Allah baku mu samu ba" Ta faɗa tana leƙa cikin wata mota tare da shafawa.

"Tabbas idan na koma garinmu duk mai son in bashi labarin gidan nan sai ya biya ko da kuwa Malam ne, Tasalla kwa ko a da kuɗinta bata da rabo dan ba zan bata labarin nan ba" Ta faɗa tana ɗaga kai sama tana ƙarewa benen kallo ga wasu hazbiya a saman suna ta waricinsu. Haka ta rinƙa kutsa kai cikin farfajiyar gidan tana ta kallo abinta.

"Ni ai yau ta waru wallahi yawon buɗar ido dai da wasu ke biyan kuɗi suna hawa jirgi su tafi ƙasashen waje, to ni ga nawa yawon buɗar idon a nan babu ko sisina bare taro, yo da na san akwai gidaje masu kyau kamar wannan a kusa da gidan Halima ai nan da gidan Halima babu nisa da nan zan ke tahowa in na gaji da zaman gidan, da dai in ke zama da wannan Imiranan me baƙar zuciyar tsiya ga mugunta ai gwara in zo nan in wanke dauɗar idona" Ta faɗa tana bin bayan gidan daga can ciki.

"Anya kuwa Azumi kya ke fitowa kina barin Imirana daga shi sai Halima a cikin gidan, bakya ganin wani abu zai faru" Wani ɓangare na zuciyarta  ya  tambayeta.

"Kuma fa da hakan ne wallahi, kar in je in fito yawon buɗar ido shi kuma ya je ya buɗe ƴar mutane a gida ya je ya rugurgujeta son ransa ya farke mata ɗinki a shiga uku" Ta faɗa a fili tana saurin juyowa dan ji ta yi ma kallon ya fita daga kan ta duk da akwai Ashrof a gidan kuma ƴan barka na zuwa amma sai take ganin Imran zai iya aikin Ashrof wani wuri dan ya cimma burinsa.

"Dole in yi maza ma in koma gidan dan yanzu komai ma zai iya faruwa amma in ina kusa dolensa ya ɗauki dangana ko ba ya so" Ta faɗa lokacin ta dawo hanyar fita, tana shirin ficewa ta hango wani wuri na shaƙatawa an jera faraen kujeru ga falawoyi kewaye da wurin.

sakin baki ta yi ya layar me tafiya tana dosar wurin a ranta tana cewa.

"Ai kuwa yau sai na ɗosana ɗuwaiwukana a kan kujerun nan" Haka ta ƙarasa wajen ta zauna a kan kujerar har da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jin una ma nan gidan Malam ne da kuwa kakarsu ta daɗe da yanke saƙa.

   Daga can wajen gidan wata mota ce ta faka a ɗan nesa da gidan, wasu maza matasa majiya ƙarfi suka fito su biyu, suka bar wanda ke tuƙawa a ciki.

"Kar fa ku yarda wani ya gan ku, ku bi a sannu, kun ga dai yanzu da sauran haske a gari magriba bata kai ga yi ba, dan dai ma unguwar masu hannu da shuni ce kowa yana cikin gidansa tun da shi me gidan ba ya ƙasar shi da matarsa, kuma Oga ya sanya an zo an ɗauke me gadin to ku tabbatar kun ɗakko tsohuwar nan kar ku bari a samu matsala, daga it sai ƴan aiki a cikin gidan, wallahi kar ku bari a samu matsala dan Oga ya ce ba ƙaramin kuɗi za a karɓa ba idan muka kawo masa tsohuwar nan domin Alhajin zai iya bayar da ko ma nawa ne idan ya ji an kama mahaifiyarsa dole ya bada kuɗin fansa idan ya ji za a aikata barzahu in bai bada kuɗi mai tsoka ba" Cewar wanda ke mazaunin direba cikin muryar dabanci

"An gama za mu yi duk yadda za mu yi mu kawo ta" Suka faɗa tare da juyawa suka nufi gidan, ta baya suka zagaya suka fara leƙen gidan daga wasu ƴan ƙofofi da aka yiwa gidan kwalliya da shi suna so su samo yadda za su shiga, duk da ba me gadi dan Ogansu ya sa an kama shi dan ma kar su zo ɗaukan tsohuwar su tafi ya kira me gidan ya faɗa masa, a kira ƴan sanda a sanar da su amma in suka ɗauketa kafin a gano hakan sun sanar masa sun kuma gargaɗeshi a kan kar ya sanarwa ƴan sandan. Hango Inna suka yi zaune kan kujera a wajen shaƙatawa ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

"Baaba ai ka ga tsohuwar ma a araha tana zaune ba sai mun sha wahala ba wajen shiga can cikin gidan"

"Wallahi kuwa ai kawai mu gewaya mu shiga gidan" Ɗaya ya faɗa, haka suka gewayo dan zuwa su shiga ta get ɗin gidan.

   Inna da ke zaune ta ɗakko alkakinta ta gutsura ta mayar a ranta ta ce.

"Kin ga Azumi tashi ki tafi, kar masu gidan su fito ki shiga uku dan ba makawa sai yadda hali ya yi" Ta faɗa tana tasowa dan ta tafi.

"Kai dakata mu laɓe gata nan ma za ta fito daga gidan, tsuntsu daga sama gashashshe" Cewar ɗaya yana janyo rigar ɗaya suka dawo suka laɓe.

Inna da ke tafiya hankali kwance tana ƴar waƙarta

"Duniya ba wurin zama ba, da ka cuta ƙwara a cuceka, yau taka gobe ta ɗan...

  Raf ɗin da aka yi da Inna da bata ma lura da samarin ba shi ya dakatar da ita daga ƴar waƙarta, bakinta suka danƙe da hannunsu suna waige-waige irin n marararsa gaskiya, cikin azama suka rinƙa ƙoƙarin kai Inna inda motarsu take, amma Inna sai turjewa take tana neman gagararsu. Idanun nan nata kwa ya fito ƙulu-ƙulu sai son tofa albarkacin bakinta take amma riƙon da bakinta ya sha ba na wasa bane.

"Kai Baaba wannan tsohuwa da shegen ƙarfi take, ka ga yadda take neman gagararmu" Cewar ɗayan yana huci kamar wanda yake kokawa da doki.

  Sun kusan zuwa inda motar take ai Inna da ta ga sun doshi mota sai hankalinta ya tashi dan duk tunaninta ƴan yankan kai ne za su tafi da ita su yanke kan nata.

"Wayyo Allah na, wayyo Malam wayyo Tasalla ku kawo min ɗauki gani a hannun ƴan yankan kai, Malam da Tasalla duk da na san kun min nisa amma dole in kira sunanku dan na san idan na kira Sunan Imirana sai dai su gundule min har ƙafafu dan wallahi baƙin halinsa ba zai sa ya taimaka min b mutumin da ya tsane ni, bari in ƙwaci kaina dan ba zan yarda a cire min kai ba in mutu in barwa Tasalla Malam ta zauna ita ɗaya" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ja wani uban birki, aikuwa aka shiga turumurtu ita da su, har sai da na cikin motar ya ga Inna na neman ta gagaresu ya taso cikin hanzari rai a ɓace yana zuwa cikin ɓacin rai ya ce.

"Wai dalla malamai meye hakan sai kun sa asirinmu ya tonu yanzu ban da abin kunya har wannan tsohuwar ce kuka kasa kawo ta mota tana ta mayar da ku baya " Ya faɗa yana hucin ɓacin rai a zuciye ya kama Inna wai shi nan mai ƙarfi aikuwa ta daddage ta cije a wuri ɗaya ta ƙi gaba ta ƙi baya ganin wankin hula na son kai su dare su uku amma sun kasa jan tsohuwa sai laya ya ce su mata cali-cali aikuwa cikin lokaci guda mutum biyu suka kamo ƙafar Inna sai gata an mata cali-cali biyu riƙe da ƙafar ɗayan kuma da saman kan har lokacin hannunsa a riƙe da bakin Inna, a haka suka saka ta a motar biyun suka saka ta a tsakiya, ɗayan ya shiga ya ja motar da uban gudu a sukwane suka bar layin. Tuƙi yake amma Inna sai uban bige -bige take a bayan motar ta hana samarin nan biyu sakat duk ta tara musu gajiya kamar wanda suka yi dambe. Sai da suka daddafeta da iya ƙarfinsu sai haki suke sannan ne suka ɗan samu salama amma kuma sun ƙulle mata idanu, da wani ƙyalle bakin kuma ɗayan ya rufe mata da hannunsa.

Hanyar bayan gari suka nufa duk ta tara musu gajiya, ba dan uban kuɗaɗe da Ogansu ya ce za a samu idan sun kamo tsuhuwar nan da na jaki za su lakaɗa mata su jefar da ita.

Tafiya suke amma Inna hankalinta a matuƙar yashe yake dan tana gani lokacin barinta duniya ya yi domin kuwa ta haɗu da waɗanda za su fille mata kai.

"Allah na tuba, ka yafe mini kura kuraina, ka sa ni a aljanna, ka haɗa fuskokinmu a gidan aljanna da malam, amma banda Tasalla ita ma a kaita aljannarta da ban amma ba wacce za mu zauna da ni da Malam ba " Cewar Inna a zuciyarta hawaye zubo mata gashi babu damar ƙugawa dan an yiwa bakinta rub.

  A haka dai ta shiga shirya abin da za ta musu duk da tana ganin mawuyaci ne ta kuɓuta amma za ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin ta musu wani abin ko da zai ita kasancewa bata rama ba. Dama dai ta san zai yi wahala a ce ka rama abin da wanda ke shirin rabaka da duniya zai maka. Ganin ta tuno abin da za ta musu sai ta fara tunanin aiwatarwa. Hannun damarta da ke gefen wanda ke damarta, kuma a wajen cinyarsa hannun nata yake duk da ya riƙe ra amma kuma wajen kafaɗarta ne ya kama ya maƙalƙale, dan haka tsintsiyar hannunta ba a riƙe take ba, dibara ta yi ta miƙa hannun wajen inda al'aurarsa take.

"Yau zan yiwa mazaƙutarka (Al'aura) Damƙar da tun da ka zo duniya ba a mata ba, kai ko wanda ya maka shayi lokacin kana yaro ai ba damƙarta ya yi amma yau za ka gwammace kiɗa da karatu" Cewar Inna tana lallaɓawa da hannun har sai da ta ji ta je saitin inda za ta samu abin da take so, amma ba wai tana ɗora hannun a wurin bane, tunda hannun baya kai ga ɗorawa a wurin ba dan haka babu wanda ma ya san ƴar tsohuwa akwai abin da ta shirya, kawai tun da sun ga sun samu lagonta na maƙureta a tsakaninsu sai basu kawo komai ba.

   Laɓɓanta na baki ta shiga buɗawa a hankali yadda wanda ya riƙe bakin ba zai ankara ba dan ganin da suka yi ta saki jiki ta daina haure -haure da ƙoƙarin ƙwatar kanta sai ya sassauta riƙon bakin dama dan kar ta yi ihu ta tona musu asiri ya rufe bakin bare kuma yanzu da suka bar cikin gari suka doshi jeji inda ko ta yi ihun babu mai ji bare a ceceta ko a kawo mata ɗauki, sai da ta gama aunasu su duka biyun ta daddage ƙarfinta na bara ta damƙe gaban ɗayan(Mafitsararsa) Ɗayan kuma ta gantsara masa cizo, a tare suka saki wani uban ƙara mai firgitarwa, wanda hakan ya sanya direban ya taka wani uban birki dan ganin me ke faruwa suka saki ihu mai ƙarfi haka a tare bayan sun san suna cikin yanayin da suke buƙatar sirri duk da a jeji suke amma ya dace su kiyaye abin da zai zama tonuwar asirinsu, yana jan birkin ya waiwayo, har lokacin Inna tana riƙe da mazaƙutar ɗayan ɗayan kuma tafin hannunsa yana tsakanin haƙoranta ta musu mugun damƙa. Kowanne sai jijjiga yake kakar ya hau doki yana sukuwa saboda tsabar azaba dan wanda Inna ta damƙi mafitsararsa har balls ɗin ta haɗe ta damƙe. Ihu suke da iya ƙarfinsu suna neman ɗauki, gashi kuma saboda tsabar azaba sun kasa tunanin ɗaukan mataki ko yunƙurin ƙwatar kansu, dan burinsu kawai ta sakr su. Direban kashe motar ya yi ya juyo yana ɗura musu zagi, ashar yake surfa musu saboda bai san me ke faruwa ba, kuma bai lura ba dan wanda ya riƙewa Inna baki har lokacin hannun na a yadsa yake kamar ya riƙe mata bakin, direban kuma bai san an samu juyin mulki ba yanzu Inna ce riƙe da hannun me riƙon bakin a gefe ɗaya kuma ta damƙe mazaƙuta abinta.

Wata tafkekiyar dorina ya ɗakko ya buɗe motar yana riƙe da dorinar dan ya sha alwashin sai su duka jikinsu ya faɗa musu dan babu dalilin da zai sa su nemi jiƙa musu aiki, gabaɗaya sun jigata dan dama mafitsara makasar mutum ce haƙori ma dafi ne da shi, kuma shi wanda ta cija ɗin shi ma daga baua ta haɗa da mafitsararsa abu biyu ya haɗe masa goma da ashirin, a haka ya buɗe ƙofar cikin zafin nama, ya fito ai yana shirin  buɗe ƙofar bayan Inna ta yi sauri ta bi ta tsakanin kujerun gaba ta koma gaban motar da yake gilas ɗin motar baƙi ne wuluk na ciki ba ya ganin na waje haka na waje ba ya ganin na ciki, tana komawa mazaunin direba sai gata fito ta ƙofar da direban ya bari a buɗe, duk abin da take bai lura ba. Su kuma wanda ta jigata masu, mafitsara da hannun ɗayan jin ta sake su sai suka yi laɓar a kujera kamar wasu mararsa lafiya dan gabaɗaya sun jigata basu da ƙarfi ko kaɗan, sun leƙo barzahu sun dawo. Inna na fitowa hakan ya yi dai dai da duɗewar da direban ya yiwa ƙofar bayan ƙwaƙwakwarsa na ƙoƙarin tambayarsa me ke faruwa sai idanunsa suka nuna masa tsohuwar ma bata cikin motar, gabaɗaya kwanyarsa ta tsaya da tunanin kar dai aljana ce suka ɗakko ta ɓace bai san ba Inna tana bayansa ɗan sunkuyawar da ya yi zai leƙa cikin motar hakan ya baiwa Inna damar damƙar tasa mazaƙutar, dan ta tsakanin ƙafafunsa daga bayan ta miƙa hannu ta kamo, dan da balls ɗin ma ta fara cin karo kafin hannun nata ya kai ga uwar garken, haka ta riƙe gam ya rinƙa zabga uban ihu da kururuwa.

  Kina sha'aninki Inna

🤣🤣👋🤣🤣

    A yi hƙr yau kaɗan aka samu jiki da jini🤩🙏

    MMN Afrah 09030283375

Wannan littafin kuɗi ne 300 

  Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375  idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

  *Idan dan ki fitar min littafi za ki siya ki riƙe kuɗinki Hajiya ba na buƙata* 

             1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣

  Sai da Inna ta tabbatar ya damƙu, sannan ta sake shi, dafe jikin motar ya yi yana sauke numfashi, kallon kallo aka shiga yi shi da sauran yaran nasa, amma babu wanda ya ce wani abu. Inna ce ta warce dorinar hannunsa ta ce.

"Faɗa da aljani ba daɗi wa ya faɗa muku barno gabas take, ni dama duk ina jiyo abin da kuke faɗa tun daga inda nake, hakan ya sa na sawaya daga halittar asalin aljana na koma halittar mutum, kawai fitowa na yi a wurin da kuka ganni a zaune amma ba ni bace wacce kuke nema" Cewar Inna afili cikin wayincewa dan ɗazu da suka taho a mota bayan an ɗaure mata ido ta ji suna zancen mahaifiyar me gidan ce ita, hakan ya sanya ta gane sawun ɓarawo ta taka, a  zuciyarta kuma cewa take.

"Wallahi ba zan bari ba ku min lahani dan idan kuka san ni bil adama ce yaudararku na yi to na san na lahira ma sai ya fini jin daɗi, in ya yi aiki me kyau amma idan na nuna muku aljana ce ni tun da na ji mahaifiyar me gidan kuke son ɗakko wa kuka ɗakkoni a shegen son ganin gida me kyau irin nawa, da  ban yi dibarar cin kwalar mazaƙutarku ba da wallahi na san sai yadda hali ya yi"

  Ai fa gaba ɗayansu da suka fuskanci aljana suka ɗakko jin furucin Inna sai suka shiga kallon kallo kowa jikinsa na karkarwa. Ganin sun yi dim basu ce komai ba sai Inna ta ɗauka mgnart bata samu shiga bane, cikinta har ya fara kiran ciroma, tana hango yadda za su mata ɗaurin goro a dajin Allahn nan inda babu wani wanda zai taimaketa cikin azama ta yi wuf ta ce.

"Me kan agwagwa ku jirani ina nan zuwa, wani abu ne ya shiga tsakanina da bil adama amma ku je birnin sin ɗin ni kwa same ni a bangon duniya" Ta faɗa tana ɗaga murya ta canja muryarta ta zama kamar ta wani gardin da aka shaƙeshi, ita ala dole magana take da aljannu.

  Ganin yadda take magana sai suka ƙara tsorata, cikin bada umarni ta ɗaga dorinar nan ta ce

"Duk ku fito daga cikin motar idan ba ku yi saurin fitowa ba sai dai ku ga na maida samanta ya zama a ƙasa ƙasan kuma ya zama a sama" Da sauri suka fara fito su duka a layi kamar masu neman taimako, sai da suka fito su duka suna karkarwa Inna ta dubi ɗaya wanda ya ƙulle mata ido ya danne mata baki ganin ya yi wujiga wujiga kamar an tsamoshi a ruwa  ta ce.

"Tabɗi wai kai nan wuya ce ta sa ka yi tsuru -tsuru ya wannan? Dole mana ka jigata ka ji damƙa kamar a sanyawa akuya dabaibayi, tare da  datsa maka haƙori masu tsini dole ka ji jiki ai daga jin cizon ma ya wuce na bil adama ko ba haka ba?" Ta faɗa tana kallonsa kai ya shiga gyaɗawa kamar ƙadangare, ya ce

"Hakane iya aljana" Ya faɗa a fili a zuciyarsa kuma ya ce.

"Wallahi ji nake kamar hannun ba a jikina yake ba"

wannan haƙorin naki me tsini kamar mashi, ai daga ji ma ba na bil adama bane, sai dai naku aljannun"

"Ku zo nan kowa ya yi kamun kunne yau kowa sai ya faɗawa aya zaƙinta, yo ina dalili za ku mini cali-cali kamar wata gawa, haka kawai da raina ban mutu ba ku min kama -kama, ina ji ina gani, ai na muku ma da sauƙi"

  Haka ta sanya su suka kama kunne tsoro kuma kamar farar kura kowa ji yake kamar ya tashi ya zura da gudu saboda tsananin tsoron ganin gashi ga aljana.

  Haka Inna ta sanya su a gaba ga magriba ta kawo kai amma duk wanda ya yi wani motsi sai ta ɗaga dorinar ta zabga masa sai dai ka ji sun saki kuka kamar ɓeran daji. Babban nasu ne wanda shi ne direban da ya yi motsi sai Inna ta daddage ƙarfinta ta zabga masa dorinar har sai da ya durƙushe sannan cikin sauri ya tashi ya kama kunnensa.

"Kai dalla ka yiwa mutane shiru ragon banza da wofi, yo Allah na tuba da ƙarfinmu na aljannu na dage na dake ka ai da sai dai gyatumarka ta haifi wani, Allah na tuba jika dai jibgege amma mazaƙutar yara gareka abu kamar lagwanin fitila, in banda ma larura me zai sa ni taɓa jikinku ai ba zan iya ba ma, Allah tsari gatari da saran shuka".

A can wajen Ogansu kuwa sai jiran zuwansu yake amma shiru kake ji maye ya ci shirwa, yana shirin kiransu a waya sai wayar me gadin nan da aka ɗakko daga gidan da za sato tsohuwar nan, ta yi ƙara Ogan nasu ne ya ɗaga kiran dan dama a hannunsa wayar take, ganin an sa Hajiyar Alhaji, sai ya ɗaga aikuwa ya ji muryar tsohuwa tana cewa.

"Wai me gadi ina ka shiga ka barwa mutane get a buɗe" Cikin mamaki Ogan nasu ya cire wayar daga kunne ya kashe ta, jin maganar matar da ya sanya a kamo mamaki ma ya hanashi magana a take ya ɗaga waya ya kira wayar direban su Baaba aikuwa wayar ta shiga ringing Inna ta ɗakkota a mota ta kawo wa direban ta miƙa masa, yana ganin sunan Oga ya ɗaga da sauri Ogan ne ya fada magana

"Kuna Ina ne?" Ogan ya faɗa cikin ɓacin rai dan yana ganin sun raina masa hankali sun ce sun kamo tsohuwar a gidan amma gata tana waya.

"Oga gamu a nan dokar daji za mu ƙaraso kuma Allah bai yi...

"Dallah rufe min baki, ashe ku duka, dukan iska ne, kai banda sha ka tafi ne me yasa baku ɗakko matar nan ba ka ce kun je gidan kun ɗakko ta?"  Oga ya katse masa magana tare da bashi labarin wayar da suka yi da matar a wayar me gadi.

  Wannan maganar da Oga ya faɗa musu a waya da yake handafree aka kunna kowa yana ji, a take suka fara maƙyarƙyata dan hakan ya tabbatar musu cewa Inna aljana ce.

Jikinsu ɓari ya shiga yi suna ta kuka tare da baiwa Inna haƙuri.

"Oga ba yin kanmu bane wallahi ashe angamo muka yi muka ɗakko aljana ka ganmu sai wahala take bamu kamar an aikota ga ƙarfin bala'i kamar raƙumi, ban da ma da kwananmu a gaba ai da sai dai wasu ba mu ba" Cewar direban a zuciyarsa a fili kuma ya ce.

"Oga iya ce muka ɗakko kuma za mu maidata gidan"

Mahaukata kawai" Ya faɗa yana jan tsaki tare da kashe waya,dan shi bai san cewa aljana suka ɗakko ba. Sai da Inna ta basu wahala sosai dan har goyo -goyo ta sanya suka rinƙa yiwa junansu.

"Da kun san ni bil adama ce na san yau kuma kashina ya bushe yo in kun min da arziƙi ku min rigijib (duka) Ku barni in ƙarasa mutuwa da kaina amma na san dai ba za ku barni  a yadda na muku wasa da hankalin nan" Cewar Inna a zuciyarta.

Sai da ta gama zane su tsaf sannan ta ce

"To yanzu inaso ku maidani inda kuka ɗakkoni dan yanzu idan na ce zan ɓace guguwa ce za ta taso kuma wataƙila ta kwashe har ku a nemeku a rasa"

"Dan Allah kar ki ɓace ki taimaka mana "  Suka haɗa baki wajen faɗa.

"Ina da sharaɗi"

"Muna jinki"

"Daga yau babu ku ba garkuwa da mutane ko da kuwa sauro ne "

"Ai wallahi mun tuba mu da muka yi garkuwa da  aljana ai ba ma ƙara ba"

"Ba aljana ba ce Inna Azumi ce matar Malam, kishiyar Tasalla ni ma da za mu ga aljanar yanzu da sai dai a shiga ceton  rai dan ƙafa mai na ci ban baki ba za a yi"  Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Ku shiga mota mu tafi, ɗaya ya shiga gaba ni da ɗaya mu shiga  baya ɗaya kuma ya tuƙa" Ta faɗa tana saurin shiga motar ta zauna dan tunowa ta yi da aljanin da ta gani a bayi , hakan ya sanya ta ji wani mugun tsoro dan bata manta karonsu ba. Haka suka shiga suna zazzare ido saboda tsoro Inna kuwa da ta shiga baya ta zauna a setin kujerar direban ta ɗaga ƙafafunta ta ɗora a kan wuyan direba, a haka yake tuƙin rai duk  ba daɗi wuyansa ɗauke da ƙafar aljana.

Haka ake tuƙin sun yi dif kamar ruwa ya ci su suna shigowa cikin gari ana fara kiran sallar magriba, dan haka wani wurin mai saida kayan marmari Inna ta nuna musu.

"Maza ku tsaya ku cikawa sarkin aljannu leda da kayan marmari san wannan ledar da kuma sa ta faɗi lokacin da kuka kinkimeni kamar kun samu tukunya alkakinsa ne da bakilawa, to yanzu ku ramawa kura aniyarta in ba haka ba kuna komawa gidajenku za ku ga an mayar da ku dajin da muka baro yanzu, in sau dubu za ku komo nan sai an maida ku"

"Za mu siya ma" Suka faɗa suna ɗakko kuɗi kowa ya bayar aka cikawa Inna ledar viva da kayan marmari masu yawan gaske, dan cewa ma ta yi gorubar bature ta fi yawa (Apple)  Haka aka ɗakko kayan  nan aka sanya a mota, har  ƙofar gidan da suka ɗauki Inna suka dosa za su  kaita amma sai ta ce, dama ai ita aljana ce kuma ba a nan take ba, nan ta ce bangon duniya za ta je amma sai sun kaita kan bola ta nan za ta bi ta tafi, haka ta rinƙa nuna masa hanya, a haka dai suka kama hanyar gidan Sadiya sun kusa ƙarasawa sai ta ce su ajiyera a wajen wata bola saboda a nan za ta bi ta koma hanyar aljannunsu, ita kuma ta yi haka ne dan kar a a je wucewa ta ƙofar gidan Sadiya Imran ya ya ganta a motar ya  tona mata asiri dan kaɗan da aikinsa.

A dai dai bolar suka tsaya, wanda ke zaune a mai zaman banza ya fito da sauri ya buɗewa Inna ƙofa ta fito aka miƙo mata ledarta shaƙe da kayan marmari.

"Gashi iya" Ya faɗa yana durƙusa gwiwoyinsa a ƙasa.

"Ku ajiye a nan sarkin aljannu zai sa dogaransa aljannu su zo su ɗauka" Cewar Inna a fili a zuciyarta kuwa cewa ta yi.

"Yo Ina dalili zan hau bola da abun da zan ci"

  Ajiyewar ya yi, gabaɗaya suna jin tsoro Inna kuwa dosar bolar ta yi tana addu'a a zuciyarta dan kar ta je ta yi gamo da magribar nan. Suna ƙoƙarin jan motar suka ga Inna ta fara wata girgiza da sauri ya ja motar suka bar layin a sukwane.

Sai da suka yi tafiya me nisa suka tsaya kowa ya kama gabansa dan sun ce sun bar garkuwa da mutane daga yau, sbd angamo da aljanar da suka yi yau, shi ma Ogan bayanin da suka masa a waya bayan barinsu wajen Inna  ya sanya an maida me gadin kuma sun fasa ɗakko tsohuwar da suka yi niyya dan suna ganin kamar idan za su ɗakko ta aljana za ta iya rikiɗa su ɗauki aljanar a maimakon matar dan haka shi ma barin garkuwa da mutanen ya yi ya koma ya kama sana'a.

Inna kuwa tana ganin gilmawar motarsu ta gefen ido, sai ta ɗan dakata, sai da ta tabbatar sun tafi sanna ta baro kan bolar da sauri ta suri ledar kayan marmarinta, tana ta waiwaye tana cewa

"Ja'irai ƴan iskan ƙarya yo me na manta gashi na samu kayan marmarina ko banza ai na ƙwaci kaina, da yanzu ina can wataƙila ma wani daga cikinsu ya far mini tsakar dare tsofai-tsofai da ni, ya je ma ya goga mini cuta mai karya garkuwar jiki" Ta faɗa tana shigewa gidan Sadiya, sai da ta sanya ƙafarta a cikin gidan tsoron aljanin gidan da ya tsorata ta rannan ya faɗo mata, tana fatan kar dai yana jin yadda ta yaudari samarin nan,  ya zo da dare ya tambayeta dalili.

"Assalamu alaikum, gafaranku dai masu gida" Cewar Inna lokacin da ta shigo gidan amma gidan shiru kamar ma babu kowa.

"Ikon Allah kun ji ina Halimar take ta barni ina ta faman rafka sallama" Ta faɗa tana shigowa tsakiyar falon amma babu kowa sai su Hassan da ke kwance kan gadajensu suna bacci.

"To ko dai bayi ta shiga, kenan Asharofa har ta tafi gida, to ai shikenan" Ta faɗa har lokacin ledar kayan marmarinta na riƙe a hannunta.

  Imran da tun sallamar Inna ta farko ya jiyo ta amma Sadiya bata ji muryar Inna ba, hakan ya sanya ya riƙe hannun Sadiya da ke shirin fita ya hanata ta fita kuma ya yi hakan ne saboda ya yiwa Inna abin da za ta kunyata. Sadiya kuma da yake ta ga yana ta ƙuncin rai sai ta kasa tafiya ta dakata, tsaye suke a tsakiyar bedroom ɗin, ya riƙe hannunta babu wani abu da ya ce kuma bai mata komai ba duk da tana ɗan tsoron yanayin nasa dan ta san shi bai iya riƙe kansa ita kuma jego take babu damar yin hakan.

"Sa'adiyya ba dai baccin magriba kike yi ba" Cewar Inna tana dosowa bedroom ɗin da ƙarfin gwiwarta, Imran da ya ji takun tahowarta ɗakin ya yi saurin janyo Sadiya jikinsa ya rungumeta, hakan ya yi dai dai da bankaɗa labulen da Inna ta yi.

Ledar kayan marmarin ta saki ta faɗi ƙasa, ta fara rafka salati, tana tafa hannuwa kamar wanda ta ga mazinata turmi da taɓarya. Sadiya da ta ji maganar Inna ta shiga ƙoƙarin raba jikinta da na Imran, aikuwa Imran ya riƙe ta ƙam ya ƙi sakinta dan yanzu yake so ya ga yadda tsohuwar nan mai tsuru-tsurutun tsiya za ta yi, dan shegen shishshiginta da zalama ne ya sanya ta zo masa wani ZAMAN WANKA dole ya nuna mata bashi da kunya ko ta tattara komatsanta ta bar masa gida ta haƙura da ZAMAN WANKAN.

"Imirana, kai Imirana, wai Imirana ba magana nake maka ba"  Cewar Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.

"Wannan an yi taƙadarin yaro wataƙila ma ba ya cikin hayyacinsa, sai na yi da gaske zai ƙyale ƴar mutane yo ban da jaraba ma yarinya tana jego amma ba zai ƙyaleta ba"

  Sadiya duk kunya ta kama ta sai kiciniyar ƙwace kanta take, amma Imran ya ƙi bata haɗin kai nema ma yake ya haɗe bakinsu amma sai kauda kai take"

"Na shigesu ni Azumi me idanuna ke gani, Imirana riƙe da Sa'adiyya ko shamaki babu a tsakaninsu, yanzu ba za ka saka ta ba Imirana ko dan kunya ta ma ai ka saketa, amma ka runƙunƙume yarinyar da jego take ɗanye sharaf, ai abin da kunya yin tsirara a gaban uban miji" Inna ta faɗa kamar ta saki ihu dan jin nauyin yadda ta gan su, gashi kunya duk ta kamata amma tsegumi da kuma son ganin ƙwaƙwaf dan kar a yi katoɓara ya hanata tafiya daga ɗakin.

Imran kuwa jin yadda Inna duk ta rikice sai ya sanya hannunsa ɗaya ya riƙe ƙugunta ɗayan kuma ya kai wajen ƙirjinta a ransa yana cewa 

"Ai tun da gane -gane gareki wallahi sai kin ga abin da ya fi ƙarfin ganinki, wa ya ce miki ana shiga tsakanin ma'aurata?" Ya faɗa a ransa.

" Na shigesu ni ɗiyar me daddawa jiƙar me barkono yau ina ganin abu , yo Imirana banda fallasa auren bashi ya za a yi ka rungumi me jego,  tabbas shi yasa ba a baiwa kura ajiyar nama nima da gangan ne na fita na barku a gidan in ban da tsautsayi zagin mahaifi ai dama ba a bar mutum kamar Imirana ba da mace a cikin gida, yo me nema a duhu ne ya samu a sarari" Ta faɗa tana ɗan tako ƙafarta ta matso cikin ɗakin, dan so take ta san yadda za ta yi ta ƙwaci Sadiya kar a yi abin kunya.

Har lokacin nan da Inna ke ta karaɗi Imran ko niyyar sakin Sadiya be yi ba so yake ya ga iya gudun ruwan Inna za ta fice ta basu wuri ko kuma za ta cigaba da tsayuwa kamar an dasa ta har sai ta ga abin da zai turewa buzu naɗi.

"Yau na tabbatar da waye kai Imirana, dan tabbas gani ya kori ji, ni kaɗai na san abin da ya faru da ni a fitar nan tawa daga gidan nan, kuma ni na san abin da hannu na ya damƙa (Al'aura) ya Allah kai ka san karatun kurma Allah ka tsare min idanuna da gani na daga abin da zai ɗaga min hankali, yo banda ƙaddara ma ni da ba na ƙaunar ganin mazaƙuta in ba ta Malam ba, me ya kaini na taɓa mazaƙutar maza har uku da hannuna, ji nake kamar na sa wuƙa na gundule hannun nan nawa da ya taɓa al'aurar da ba halalinsa ba" Cewar Inna tana sakin kuka, dan gabaɗaya sai ta ji birnin ta fita a ranta yau ta haɗu da maza da abin da ta musu kaɗai ne ya ƙwace ta gashi kuma yanzu ta dawo gida ta tarar da wata katoɓarar.

Imran kuwa furucin Inna ya sanya dariya ta kusa ƙwace masa, amma haka ya daure ya cigaba da ƙoƙarin kai hannunsa wajen ƙirjin Sadiya ita kuma tana ƙoƙarin bige hannunsa.

"Amma wannan yaro an yi me wankekken ido, bayan ƙwaƙumarta da ka yi babu shamaki tsakaninku, hallaw na shanunta kake so ka damƙo, to wallahi dai ka bi duniya a sannu a gaban idona baka jin kunya kake waɗan nan abubuwa kamar wanda uwarsa ta ce jeka ka ganiz shi yasa ashe ko zamana baka ƙauna a gidan na kafi so a barka ka ci karenka ba babbaka, ai dama idan ka ji makaho yana cewa a yi wasan jifa to tabbas ya taka dutse"

   Imran juya Sadiya ya yi yake neman kwantar da ita a kan gado.

"Halima wai duk a gaban idona fa ake sarrafa ki kamar wata injin kaɗin taliya, amma kin kasa kataɓus ki ƙwaci kan ki so kike sai sheɗan ya masa linzami ya haike miki da ɗanyen jegon, wallahi ki kiyayi biyewa ɗa namiji Sa'adiyya ina rabaki da kiwon kyalle kina kyalle ta haihu, , ni nan yanzu na ƙwaci kaina daga hannun maza ƙartai uku, bayan haka harda yaudarar kayan marmari amma ke a hannun namiji ɗaya kin kaya ƙwato kan ki kin barsa sai waricinsa yake a kan ki, sai ka ce wata matar shige, ai matar shige bata daraja amma ke kuwa da ba matar shige ba kya biye masa"

  Ganin Imran ya kwantar da Sadiya a kan gado Inna ta saki ihu me haɗe da kuka.

"Dan Allah Imirana na roƙeka dan darajar iyayenka ka rabu da yarinyar nan, kar amana ta ci ni, duk wacce taje ZAMAN WANKA tamkar an damƙa mata amanar me jego ne a hannunta, so kake ka je ka sa ƴar mutane ta yi ciki da goyo, ka farke mata ɗinki a shiga uku, bayan ɗinki bakwai Amina uwarka ta faɗa min an mata a mafitar ɗa (HQ) Sai ka ce wata ƙwarya amma kake neman maida hannun agogo baya, dama duk abin da aka yi da jaki sai ya ci kara, kuma ai dama abin kirki bai gaji kare ba, in ya yi ma dukansa ake"

"I luv u baby) Cewar Imran cikin wata murya da ya yi da gangan.

"Ƙarya yake miki wallahi yaudara ce kawai irin ta maza, duk da ban san fassarar abin da ya faɗa ba, amma na san magana ce me daɗi dan na ga a kan gado ya yi maganar kin san kuwa maza kalamansu basa tashi sai suna neman biyan buƙata to a nan za ki ji kalaman soyayya har da na siyarwa"

"Ina sonki masoyiya" Cewar Imran shi ma yana ƙoƙarin hayewa gadon, sai da ya hau gadon ya kife a kan Sadiya ɗare-ɗare, kicinyar tashi Sadiya ta shiga yi amma ya hanata.

"Lahaula wala ƙuwata illah billahi aliyal azim, Imirana kan ruwan cikinta za ta hau a gabana" Inna ta faɗa tana sauri ta yi taku ɗaya biyu sai gata a gaban gadon a sukwane, aikuwa ta shiga kiran Imran da ƙarfi tana cewa.

"Imirana kai, kai Imirana tasata (Ɗaga ta) tasa ƴar mutane, wallahi ban bari ka yi wannan aikin da na sani, azo ayi abun kan ji alawo, sai daga baya ake wallahi tallahi" Ta faɗa tana jan rigarsa, amma Imran ko gizau be yi ba, cikin sauri ta juya ta bar ɗakin har tana haɗawa da gudu -gudu ta yi tsakar gida gabaɗaya a gigice take.

  Imran kuwa ya ɗauka kunya ce ta sanya Inna ficewa daga ɗakin dan haka sai ya fara ƙoƙarin tashi, ai sai ya fara jiyo ƙaran gudun Inna kidif-kidif kamar an biyo ta, da sauri ya koma yadda yake ya yiwa Sadiya rumfa.

"Bari dai na yi maganinka na yi maganin sheɗan ɗin da ya rufe maka ido kake neman aikata aikin da na sani" Cewar Inna da ta dawo ɗauke da taɓaryar da ta ɗakko a kicin, ɗaya hannun kuma muciya, Sadiya da yake ita ce a kwance Imran kuma ya baiwa Inna baya bai ga abin da ta ɗakko ba, sai Sadiya ta ce cikin ƙaraji.

"Abban twins tashi taɓarya"  Ta faɗa tana turashi da ƙarfi da hannunta dan ta san kaɗan daga aikin Imna ta ɗaga taɓarya da muciyar nan sa rafkawa Imran dan tsaf za ta sauke masa su a gadon baya ta je ta lahantashi a shiga uku a zo ana a'i ina indo.  Imran turawar da Sadiya ta masa sai gashi a gafe rigingine a kan gadon, hango Inna ɗauke da madokai ta iyu kukan kura za ta hau kansu ya sanya ya yi wata adungure ya dira daga gadon sai gashi ba shiri tsaye a kan ƙafafunsa. Sadiya kuma da sauri ta tashi zaune ta miƙe tsaye dan dama ita dan ya mata nauyin kuka ne kuma ya hana ta ƙwatar kan ta amma dama da ba za ta yarda ta yi wannan abin kunyar ba a gaban Inna ta barwa kanta abin gori da abin faɗa marar iyaka a wajen Inna Azumi.  

  Ita ma Sadiya dirowa ta yi daga kan gadon ganin duk da Imran ya ɗaga ta amma Inna kamar bata fasa abin da ta yi niyyar yi ba, ganin da gaske tana shirin farmusu da taɓarya da muciyar ya sanya Imran yin wani uban tsalle ya bi ta bayan Inna ya fita daga ɗakin a sukwane, Sadiya ma da gudunta na bara ta fice suka bar Inna a ɗakin tana sababi tare da rufa musu baya cikin gudu -gudu sauri -sauri.

No comments