Breaking News

Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 86-90

 


BOOK 2 



                86-90



Official

By

AsmaBaffa 



SADAUKARWA GA

ZAINAB USMAN



         

*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce  mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin  gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu  za ki yi godiya,  sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki.  Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka   kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in  abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin  Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga  cikin  abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯 

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa  guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari

DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

*08089965176*

*07084653262*



Page naku ne 

Ummu Shureim

Pretty

Nina

Oum Arifullah

Mmn Zee

Ummita









          Mairo suka furta gaba dayansu,Mairo ta tsaya tana kallon su daga baya durkusawa tayi ta zube gwiwoyinta a kasa tana hawaye sosai,tace Dan Allah Abba Gwaggo ku yafe min,Dagaci yace Mairo me yasa kika tafi kika bar gida tunda kaddara ta Riga ta afka mana Kuma ba kowa ya jawo ba face mu muka jawa kanmu domin duk mai aibata Dan wani burinsa yaga masifa ta fadawa wani musulmi to Kansa yake wa karshe Kansa zata fada,duk hakki ne ya ja mana hassada tayi mana yawa burinmu kar wani yaci gaba sai mu,mun zalunci Rabi tun tana karama har ta girma ba abinda bamu yi mata ba gashi duk tsiya Yanzu a karkashinta muke, Rabi ita ce cin mu itace Shan mu komai namu Rabi ce,shi yasa aka ce Idan ka haifi da baka San wa ka haifawa ba tabbas iyayen Rabi mu suka haifawa ita,Dagaci ya bawa Mairo labarin komai tun daga barinta gida,Itama Mairo ta basu labari tun daga barinta gida zuwa zaman saudiyyarta.


    Dagaci yace to mene amfanin wannan tafiyar taki to Allah ya taimakeki kinje kinyi aikin hajji kaddararki ce Allah yayi sai kinje yanzu gobe da Asuba zamu tafi wajen Rabi ta haihu,Mairo tace zanje Nima,Mikewa tayi ta rungume Gaji,Gaji tace ai kin bani haushi mene na barin gidan Wanda ya Miki cikin Yazo da Kansa ya bamu labarin komai Bai dade da zuwa ba muka ji labarin yayi aure dama zuwa yayi ya aureki Kuma aka ce kin gudu wlh baki gani ba ya dinga kuka yana bada hakuri ya tuba sosai me rufin asiri kin kudu kin wa kanki, iyayensa ma sunzo da shatara ta arziki,Mairo tace na yafe masa duniya da lahira Nima Allah ya yafe min bari na yaye Madina na Kai musu abar su,Gaji tace Idan yace zai aureki fa? Mairo tace har Abada ai bazan iya zama da shi ba Idan na tuna Raina zai ta baci,Mairo tayi murna jin Gaji zata yi aure,Dagaci ya Kalli Madina yace gata kuwa kyakyawa sai dai kaico ba Yar sunna bace Allah ya rabaki da gorin mutane, gwara a bawa ubanta can ya karata bari ta Kara wayo muje har gida a Kai musu abinda dansu ya shuka gashi ya nuna ya girbi abinsa.


    Auta part dinsu ya koma abinsa cike da murna ya dauki Salma ya  mata gashin da take ta fada masa,nan ma kuka ta sha shi,ya shirya abarsa cikin doguwar Riga yar kanti me siririn hannu yana gamawa ya faki idonta ya dumbulu na shanunta,Salma sai da ta zabura ta make shi suna dariya,Sannan ya wanke bedsheet din ya shanya yayi wanka abinsa tare da tsarkakewa ya fito ya tsaya a jikin mudubi yana kallon Kansa a mirror yace ya na ganni kamar mace me ciki irin wannan ja Dana Kara yau,Salma inda ya ajiyeta a bakin bed din tana nan a zaune kamar gunki bata cewa kala bata kukan Kuma,Auta ya furta yes Auta yau kayi rugurguza ba irin Yaya Nawwar ba sai da aka Nemo masa magani, sanyi ya gama da shi,amma yaron da ake rainawa ko babba bazai ja da shi ba,ya juyo ya Kalli Salma yace ko ya kika ce ya kika ji lafiyar tawa? Salma ta dauke Kai gefe can tare da hade rai,Auta kuwa kasa kasa yake magana Wanda shi yasan me yake cewa banda jin kunyar ya mace gaskiya ba raini.


     Salma tayi shuru da bakinta yace yau ba magana ne? Shiryawa yayi yace na wuce sai nayi Sallar Isha zan dawo,gabanta ya dawo ya durkusa tare da dora Kansa a cinyarta,baki ce a dawo lafiya ba,ni na aikeka cewar Salma ta furta da masifa,Allah ya huci zuciyarki My love farin cikina,ya mata kiss a kumatunta ya tashi ya fita,har ya fita ya dawo yace me kike son ci? Salma tace duk dai bana son cin komai ka siyo min tsire cikin nawa ma ba wani karba zaiyi ba amma ka hado da fruits Salat,da Yar yogurt,nasan ma kadan zan ci Amma dai ka karo da Chips tunda naga ba wani Abu me nauyi bane sai kazar nan da ka siyo min rannan to shike nan ka kawo na gwada ci,Auta yayi dariya a ransa,a fili yace ai nasan baki da ci bare yanzu da kike cuta,tace uhm ka hado da Ice cream, Auta Ido ya zaro yace to an gama.

   Salma tashi tayi ta gabatar da Sallar magriba ta koma ta kwanta ba bacci tayi ba.


    Auta kuwa ficewa yayi suka hadu da Nawwar a hanya Nawwar ya bishi da kallo yace Surukin Baso wannan farin cikin fa? Auta yace to kafi so nayi ta bakin ciki shike nan bazan yi farin ciki ba a gidan nan sai anji ba'asi,Nawwar yace tunda zaka kashe musu yarinya ai dole kace an sa ma Ido,Auta dariya yayi yace yanzu dai daya muke dakai abinda kake yi shi nake yi,Nawwar dariya yayi yace ai tunaninka yanzu Kai Daya muke? Auta yace Inshallahu kuwa,tsaki Nawwar ya ja ya wuce abinsa,Auta mota ya shiga tare da barin gidan

  Auta a titin ma yace yau tukin angwaye zanyi zaku ga gadara sai ya hau tsakiyar titi ya dinga tafiya kadan kadan me Keke ma wuce shi zaiyi,ya tare hanya shi bai tafi ba shi bai tsaya ba ana ta masa horn ko a jikinsa sai dai a kauce a wuce shi ga mutane da rashin hakuri wasu har da zagin Auta,har yaje ya gama abinda zaiyi yayi siyayya ya dawo ya kawowa Salma duk abinda tace a siyo mata,tana saman Sallaya sai da ta idar sannan ta cire Hijab din tana shagwaba tace a bani yunwa nake ji,Ya dakko plate ya zuba mata komai ya dauki tsire Salma tace da kazar zan fara,ya ballo kazar ya sa mata a baki ta yaga tace bana jin dandano sai dai na cusa ta haka,ta lumshe ido tana yatsina tace hakora na ciwo duk sun ji jiki su ma,Auta yana dariya ya dauka zai ci ta kwace tace baza ka ci min ba ai dai ka samu naka rabonka a jikina ka ko shi to ni kadai na isheka ko ban Kai ka koshi ba? Auta yace kin Isa ni na Isa nace kin Kai, sai dai ai Antena kika ciyar ke,Salma tace to baza ka ci ba ta kankane sai Abincinsa yaje ya ci ya kyalewa Salma nata taci ta rage ta Kai kitchen.


      Cele tana masifa tace shike nan yanzu zanyi hatsari a Local government,anfi karfina lallashinta ya dinga yi bai mata dole ba,harda cewa ki tausaya min Babu wajen wacce zanje Idan ba ke kamar zai mata kuka,Cele tace ni baka tausaya min ba sai nice zan tausaya maka,yace ai gwara ke naki da sauki a kaina,ya dinga rokar Cele,Cele tace ya zanyi ka hana ka shiga uku a lahira, kadan zaka yi Idan ka wuce misali walla ...baki ya rufe mata da nasa yana kissing dinta wai kar ta rantse,tace ya haukace matar mahaukaci ta tabbata shike ,Ahsan yace kiyi kalaman jiya tace yo ai sai ana jin Dadi ake fada yanzu sai dai na wahala,ya damu shi ta dinga magana tace to ta fara yana kissing dinta a nutse ta furta Wicked ,ta lumshe ido lokacin da yake sarrafa boobs dinta yanda yaga dama tace Disaster, uhmm problem Ahsan yayi dariya ya fahimci tsab ba na dadi take fada ba,yaci gaba da sarrafa Cele tana cewa Trouble,yanda yake tsotse mata jiki dole sai da jikinta ya karbi sakon Ahsan,a nutse yake mata sucking Cele tace to na fara jin dadin,wai shi dole ne sai Anji dadinsa,yana nisa Cele har da kukan Dadi tace uhm uhm Cele karki kiji Dadi mana baki niyya ba, Ahsan kuwa sarrafata cikin salo da kwarewa har ya samu ya shige ta ya ci gaba da gwangwajewa, yau ma haka ya gwangwaje da Cele,kuma tayi dauriya bata yi kuka ba amma tafi jin zafin na yau ma akan na jiya sabo da bata warke ba ya sake, A ranar ta masa wayo tace Umma tace ka tafi Kaduna can zaka zaga dangi kaga kowa sai ka Kai lefe zanzo na sameka,Ahsan yace ba matsala mu tafi tare, tace ai ni jinyar Yar uwata nake Rabi ga Omaira tana nan ku tafi tare Idan ka gama komai ka dawo nan da kwana uku,Ahsan yace shi bai yarda ba indai hakane bazai je ba,Cele tace na shiga uku a can ma cewa zaiyi tare zamu kwana,Cele tace to ka bari sai zan tafi mu tafi gaba daya yace Yayi kyau,haka bayan sunyi wanka yace ta shirya su Dan fita su ga gari shiryawa tayi cikin wata fitted gown ta dora After dress marar kauri da kyar ya yarda ya hakura shi sai ta Saka nikaf, zata yi kwalliya ya hana za a kallar masa mata,powder kawai ya bari ta shafa da lipgloss,Shi kuwa jallabiya ce a jikinsa fara Kal cif cif shi,yayi kyau yana kamshi hannunta ya rike suka fito a kafa,a hanya hannunta ta zuro ta kasan hannunsa ta sarkafo damtsensa da hannunta daya suna tafiya suna hira sai da suka yi tafiya me uban nisa suka bace a hanya suka kasa komawa Hotel din,suka dinga dariya sai sunyi kamar sun gane sai su tsinci kansu a wata unguwar,Cele taxi ta tare musu ta fadi sunan hotel din sannan suka samu aka dawo da su.


     Washe gari shuru ba a ga Salma ba babu alamarta,Auta ne ya shigo part din Mami tace wai Salma kuwa kalau take? Auta yace Malaria ce ta mata karfi amma na kaita asibiti taji sauki ma,Dan iskanci har kuje asibiti baza ka sanar mana ba ai ko ya jiki ayi mata yace ta fa warke anjima kadan za ku ganta,tace to ba damuwa,Cele tazo gidan Ahsan ne ya kawota da driver dinsa ya sauketa kafin Yazo daukanta,tana shigowa suka gaisa da Mami,Mami taga Cele da fruits a ledoji ta ajiyewa Mami a gabanta tace gashi inji Ahsan,Mami tace angode, Cele tana tafiya Mami tace uban waye zai sake cin abin hannunki ba ni a ciki mijina ma bazai ci ba,ta Kai fridge ta ajiye ta fice ma Daga part gaba daya,Cele ba knocking ba komai ta banko kofar ta shigo ta samu muna kissing din juna da Nawwar,Kin fita tayi na mata Alama da hannu ta tafi tace wlh ba inda zanje ke kwananki takwas da haihuwa fa,Nawwar tuni ya janye jikinsa tun shigowar Cele,tace wallah Nawwar ta fara Sallah na rantse da Allah karya take maka a boye take yi, Nawwar murmushi yayi yace tuntuni nake zarginta,nace to ta fara Sallah,hararar Cele nayi,Nawwar ya mike ya fice,nace kinji Dadi to duk bakin cikinki sai nayi arba'in,dariya Cele tayi ta min gwalo tare da zama a saman bed din sai ga Star da Wise sun shugo,Star ta mikawa Cele hannu tace Yaya kike Amarya irin wannan kyau haka,Cele tace na gode Makarantar taku kuka je ne?

    Star ta Kalli Cele tace Makarantar mu ta matan aure? ae ita nake nufi,Wise tace ai sai weekend muke zuwa a gidan Miracle ake mana yanzu mu kadai muke zuwa Babu ita tunda ta haihu,Cele ta furta tace da anan zamu zauna ai da na shiga amma nasan bazai yarda ba cewa zaiyi a Saudi zamu zauna sai dai muzo hutu,Idan kunzo hutun ai Zaki iya zuwa,baki da matsala mijina ne fa Malamin muka fara dariya,Star tace kar ma kice Zaki gaishe shi Shima mugun Dan hannu ne, ko mu ba gaisar shi muke ba munyi wutar gaske muce malam ya garin cewar Wise,Star tace ni kuwa watarana Idan bashi da lafiya Ina gaida shi nace ya jikin to Miji ya zama dole,Cele tace Makarantar kangararru ce kuce,Star tace na can ciki har ya gaji damu yace baza muyi hankali ba,Mayafin Cele ta cire ta ajiye gefe tace iyayen Haram Haram ba a nan da yanzu ya lullube ni sai kace wata Alawa.


     Na Kalli Cele nace Matar mahaukaci wannan walwalin amarci haka,dariya tayi ba Shiri tace to karya ne bai sake yi ba,nace wallahi karya kike ai kina shigowa naga tafiyar ta koma gidan jiya mu fa Cele sai dai mu Kalli mutum kawai amma indai Sabin shiga ne ana taba local government muke ganewa,Star tayi dariya tace Rabu da banza,Cele tana ta dariya tace wlh ni kunya ma kuke bani ku sai naga bakwa ji,Larabawan nan da naci suke,Wise tace har na nan ma haka da yawa suke ke ki kula da kanki,Salma ce ta tayi sallama ta shugo sanye da Katon Hijab har kasa


    Babu alamar an mata wani abu tazo ta zauna zata yi ihu tayi famu sai ta wayance ehooo jama'a kaga danmu ya Kara girma ta gangara gefensa ta kwanta so take ta huta amma Salma wai ta jawo shi gabanta tace Aunty Rabi kinga Nima da Nonon nawa da ruwa da na tayaki bashi,nace a gidan uban wa kika ga ana haka wallahi ko da wasa karki fara ko shayarwa kike an hana ba dalili ba komai Idan yaran suka taso suna son junansu fa kinga ai kin cuce su kin shayar da ko wanne so Tari wasu suna wannan shirmen bama a so a canjawa yaro nono Idan ba dole ba Wanda ya Saba sha shi ake bashi,Salma dariya tayi tace na sani ni fa wasa nake Miki yaushe zan bashi abin Autana ai ko rokata kika yi bazan bashi ba,Cele ce ta Kalli Salma tace Yar iskar yarinya sai balaga Auta shashasha ya kasa mata komai,Idan bashi da lafiya a bashi magani kullum bakinki zakwai,Salma dariya tayi tace rainona yake sai na Kara girma komai ya gama nuna yayi girma,Cele a ranta tace wannan karon Autan zan bawa ya sha,Zaki sani muryar Salma ta tsinta tace Aunty ya kwanan amarci ke kullum garau dake har yanzu bai ce komai bane,Cele ta bude baki tace wai ni sa'arki ce ne,Salma tace to ai gani nayi abinda kuke yi dai Nima Ina da me min maybe ma Idan muka tashi yin namu mufi naku Kokari,Cele tace karya kike Yar nan gyara zancenki wane mutum, ke kin Isa Auta ya ja da balarabe,Ke yanzu Idan Ahsan ne ya kamaki ai sai gawarki ki kiyayi kanki bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane ni kaina da ya nake kaiwa bare ke.


   Muka kwashe da shewa Cele ta tonawa kanta Asiri,Salma tace ai Allah nake ganin kamar Auta zai fishi kwazo kin san dake su Basu fiye karfi ba ni kuwa ba sanin abin nayi ba,Cele tace dake ance Miki abin a karfi yake,ai baiwa ce wannan sai Dan baiwa ke da kike da yaro,yarinya harka sai da balarabe  wani abin Idan aka Miki baki San sanda Zaki ji kin fara fiffike ba kin fara tashi sararin samaniya ba ,ke ki kiyaye kalar nawa ba a ja damu kwabarki ce zata yi ruwa,Salma tace ai duk abin Namiji sai dai bai samu zakwakura irin bu mu ai duk sanda muka yi ras zaku ganmu,ni kwance cikin makara kika ganni dan ubanki ko a asibiti kika ganni ranga ranga ana Kara min ruwa,Salma tace ashe kunyi ku? yaushe? Muka kwashe da dariya Cele da Salma,Salma tana ta rainawa Cele hankali,Cele zuciya ta kawo mata wuya Ina dariya Ina girgizata ina cewa take a chill pill please,Cele tace Salma kin jawa kanki sai an kaiki asibiti an Miki dinki,Salma tayi dariya tace Auta me tausayi ne da hakuri ta Ina zai min da zafi sai kace wasu Yan kauye,sanda ma zamuyi Sani zaku yi sai dai Muji naku mu ba me jin kanmu,haihuwa ma Idan muka zo Babu Kiran sunan Miji ba ihu da shake wasu.

  Nasan da ni take nace kanki ake ji Salma Allah ya bamu rai da lafiya zamu gani.


     Cele tace badan Auta ba Babu kyau kallon tsaraici wlh da sai nayiwa yarinyar Zigidir yau,Salma a ranta tace wai da asiri ya tonu wajen ba kanta,a fili tace uhm Cele tamu ke dai kice kina min bakin ciki kin ganni fes ke kuwa  waje ya ratattake,Cele Saman bed din ta haura nace karku kashe min yaro na,na janyo Dana Cele tace ta dauki Salma ta direta a kasa da karfi Salma ta dafe bango sai kuka wayyo na shiga uku ta fama min kafata,kuka sosai nace Cele mene haka Dan Allah tace Ina zargin yarinyar nan wlh ba wata virgin bace yanzu ni na San jiya sai ta Kai kanta tazo tana cika min baki,Cele tayi dariya tace karya take wlh ba kafarta ba can local government ne,Salma tace Allah kafata ce,Star tace rufe mana baki gulmammiya Auta yayi,Wise ta kyalkyale da dariya tace ai daga jin Zancen Salma na gane ta wlh sabo da ai tana iskancinta amma ba irin wannan ba baro baro ba, inyeee Yan Yara ashe an San harka na furta Ina dariya,Salma fuska ta rufe tace ni Kun sa ma naji kunya ya za ayi ace Ina karama yau ku ganni haka indai anyi,Cele tayi dariya tace lallai kina da ki fadi Salma,Ana yin Sallar Isha sai ga Auta ya shigo yace Autar Auta Salma ma wai naam Autana,yace taso mu tafi ki kyale tsofaffin nan,dariya mukayi Star tace Kai yaro yanzu fa ka fara,Auta yayi dariya yace soyayyar? muka tsaya muna mamakin muna mamakin munafuncin su Auta,Salma tace targadena ya dawo na kafa tana dingishi,Yace sai mun koma wajen me gyara kenan,tace ae yace to sorry ya dauketa cak ya juyo yace Cele zo ki Bude min kofa,ashar Cele ta dura musu,Wise tace ni Dana ne ta mike tare da bude masa ya fita, Mami suka wuce a Palo yace Sannu Mami Dan bude min kofar,Mami tace sai dai kuwa Idan baza ka fita wannan wanne irin iskanci ne a gabana Auta,Auta yace Lalura ce tasa Mami na fada Miki zazzabi take Malaria ta mata mugun kamu,yanzu ma Wise ce tace nazo jikinta yayi zafi,Salma ta fara rawar sanyin karya karkar a lullubeni da bargo Auta ya bude kofa ya fice da ita Suna fita suka dinga dariya kamar me tana dauke a hannunsa sabo da dariya kamar zai fadi da ita,Kicibus suka yi da Baffa da Papa sun shugo suna hira,kamar basu gani ba haka suka yi.

    Papa ya Kalli Baffa yace kaga kuwa me na gani? Baffa yace a satin nan ai zasu koma gidan su,Shima Nawwar yace Rabi tana cika 2days zasu koma gidansu nace a gaishe su, Papa ya manta shi rashin kunyar da yake tsulawa amma harda cewa yaran zamani basu da kunya.


    Auta bai dire Salma ba sai a saman bed ya kwantar da ita ya zauna a gefenta hannunssa Daya yana saman gashinta yana shafawa bayan ya cire mata hijab din daga ita sai bumshort da guntuwar riga me gajeren hannu purple,hannunsa dayan Kuma ya rike yatsunta yana murzawa a hankali yana wasa dasu,Ya kafeta da mayun idanunwansa itama haka basa ko kyaftawa,Lips dinta ta Dan turo kadan tare da dora yatsanta a saman lips dinta tana nuna masa wai ya mata kiss,Auta ya wani lashi labbansa jajaye cikin salo sannan a hankali ya fara kissing din Salma jin zai zurma ta ture shi tare da dukansa a damtsensa tace kadan fa nace tana Harararsa da wasa,sorry ya furta yana dariya.

   Hannunsa ya Dora a gefen fuskarta yana shafawa jikin hannunsa gaba daya ya kwantar da shi a saman Boobs dinta  yana fakewa da shafa fuska yana shafe kirji.


     Cele kuwa Ahsan ne Yazo daukanta ta mike tace to mu Kuma haka Allah yayi damu zamu tafi turaka,Nace wlh badan Omaira ba to ba uwar da kike tsinana min an wani bar min ke kullum Miji sai sanda yaga dama zai kawo ki,dariya nktayi domin tuni su Star su sun tafi sai Omaira dake zaune tana ta faman chat,yanzu bata zama cikin mutane kullum tana dakinta tana faman chating ko waye oho,Cele tace ke Omaira wai da uban wa kike waya kamar bakya gidan nan,dariya tayi tace ke dai bari wani masoyi nayi tun bana sonsa har sonsa nake kadan yanzu,Cele ta zaro Ido tace Allah yasa ki gama bata lokacinki ki hadu da gurgu ko wani me mummunar kamar wannan ai ganganci ne,Cele tsabar mugunta sai ta fisge wayar tace na kwace ta baza ki kawo mana Dan online gida ba Yan Iskan Yara fitsararru Kar muje ya lalataki a waya ya fara cewa ki tura masa tsaraicinki yanzu mutane sun lalace haka wasu ke yi,Omaira ce zata yi kuka tace gaskiya ki bani waya ta,Cele ta murtuke fuska tace zoki kwata Idan ke kina jin karfinki ya Kai,Omaira ta kalleni tace Aunty ki mata magana ta bani wayata,nace ke Cele wai mene haka ki bata wayarta mana,Cele ta kalleni tace Allah Mrs Nawwar to zo ki kwatar mata,Ina shafa turare a jikina na Saka kayan bacci,nace wai tunaninki kinfi kowa karfi ne,naje zan fisgi wayar,Cele ta dauke Hannun tana dariya tace Rabin kauye ki kiyayi Cele kinga ke me jego ce,ganin Cele Ahsan ya mata illa ba uwar da zata iya,riketa nayi ta zura wayar a bra dinta,lallai sai na karba muka fara kokawa Cele tayi tayi ta dagani ta kasa tace shegiya Ashe dai kina da karfi,ni kuwa na dake duk na gajiyar da kaina kokawa da Cele ni na Isa ma na gwada dagata yanda najita a dire ta kama kasa,tace Dan dai kokawar bata fada muke ba Rabi wallahi da tuni na zubar dake a sume gwara ki kama kanki,Haushi naji na fara kokawar da gaske na hankada Cele ta bugu da bango tace Kai Kai kika buga min Kai amma na kyaleki ai me jego ce amma nasan karya kike ki kwaci wayar nan,da masifa na cakumi kirjin Cele,Nawwar ne ya shugo yace Kai mene haka da girmanku sai kace Yara,fisgo ni yayi na koma nace ni zata rainawa hankali kafin a haifeta aka haifeni ta maidani sa'arta,Cele tace au Rabi wai da gaske kike fadan? kwalarta na ci nace bata wayarta,Cele hannuna ta kama ta rike ta karfi ta cire ta Dan Murda kadan na saki ihu uuhhhh zata karyani,Sakina tayi Ina juyowa na daga hannu zan mareta Nawwar ya rike Hannun,Kamar zan tashi Aljanu haka na fara dube a dakin ko zanga abin kwalawa Cele,Cele ita kallona take yi tace Rabi haka kike da zuciya dama tab? to gaskiya zan fada Miki Avoid me Rabi duk ranar da kika kaini bango sai nayi raga raga dake,naga Alama har yanzu baki San wace Cele ba ban taba fada a gabanki ba,Rabi zata yi magana Nawwar ya mata tsawa tayi shuru,tace kinga banbancina dake kina jin magana ni kuwa bana ji,ke baki ji kunya ba Rabi gidanki fa nazo,ki kiyaye fada da Cele ba dadi ba a cin riba ki tambayi Omaira kiji,Rabi zama nayi zuciyata tayi sanyi nace ba Kya jin magana kin fiye jan fada ki bata wayarta shine Zaki fada min magana ke girmanku ne wannan ki dinga cin zalinta,Omaira ta Bude baki zata yi magana Cele ta nunata da yatsa da masifa zan Miki Kwari zan Miki Kwari ki kiyayeni Yan biyu ce ni ya zu na Miki Kwari Yar iska Yar gidan Abba Wanda baya son Yaya mata,Dariya ta bamu har Nawwar ta zaro wayar tace ungo gashi nan,har tabarrakin Ahsan ta kwaso munafuka ta sha min dadin jikina ta kawowa Omaira naushi ta janye hannunta,kallona tayi tace ke kuwa Rabi kika sake sai na tsumburar dake kin dinga kankancewa kenan ai tunda na fiki karfi to nasan Kwarin Yan biyu ma na fiki iya shi,Wlh kinci darajar danki ke mejego ce duk naji kema da karfinki hmmm ta juya tace na tafi sai gobe,nace Indai baki zo da wuri ba kawai ki koma gida bana son zaman kullum sai kinga dame kike zuwa,tace uwarki Rabin kauye da karfi,Omaira tace wai wai wallahi kin ciri tuta lallai Cele tana sonki Aunty Rabi tab ai da wani ne sai a shekara fadan nan bai mutu ba wallahi Kuma sai tayiwa mutum duka ai bala'in Cele har mamaki yake bani,Nawwar yace dama gida indai suka hada masifaffu to sai an dinga chasuwa wasu ko sha'ani suke yi to basa gamawa lafiya ku dinga hakuri,Omaira tace duk gidanmu masifaffu ne wlh inda kasan gado kowa haka amma Kuma kafin muyi fada a junanmu ana dadewa in Banda Cele da take ketawa kowa,watarana kamar bata da Kai,nace ke zanci ubanki Celen kike cewa bata da Kai,tashi ki tafi ko na Miki Kwarin Nima,Nawwar yace yanzu fa kuka gama fada duk Kun dawo kan yarinya ba inda zata je muna hirar mu,Ya hanata tafiya suka dinga labari da Nawwar, tana bashi labarin Samarinta data damfara kudi,Nawwar yace dole Baso yace kinfi karfinsa,Waye Baso? Yayan Salma,tace oh Wanda Yazo ranar suna mutumin nan Dan duniya ne daga na kalle shi ya daga min gira harda min fito,muka sheke da dariya,Omaira tace wallahi Nima na rama na masa fito na daga masa gira,Nawwar yace shi yasa yace kinfi karfinsa ashe da dalili,nace ai kuwa suna yanayi da Salma ta dai fishi haske ne ,Nawwar yace ai akwai hankali Baso ga tausayi,ga iya kula da mutane,Omaira tace ai Allah? na ganshi kamar masifaffe a haka,Nawwar yace ai sanyin Hali ne da shi ya dinga gayawa Omaira karya dan ta so Baso,yace ai yatsa aka sa masa a baki bazai ciza ba,Dariya nake kawai a Raina ni dai Ina jinsu,Yace ga taimakon bayin Allah da talakawa,kinga gidan da ya gina ai Omar akwai zuciya,Ni nayi Miki sha'awarsa ma Omaira da Zaki aure shi da kinyi dace,  dama ya fada mana yana ganinki yaji ki har cikin ransa,Omaira tace Allah sarki ai kuwa ya hadu wlh,Nawwar har da bata labarin mahaukacin da Baso ya kula da shi har warkewarsa,Omaira tace to wannan Idan ka aure shi wani naka ma sai ya huta,Muka hada Ido da Nawwar,yace Idan Zaki iya dan saurarsa muce ba matsala ya fara zuwa zance,Omaira tace Kai Yaya Nawwar kawai Kuma sai ace ni nake sonsa,Nawwar yace ai baki gane ba,baza ma muce kin san zancen ba kawai zamu yake shi Yazo ne,Omaira tace to Idan mun daidaita shike nan,Yace yawwa Omar da Omaira ya kika ji tayi dariya tace har na fara missing din Umma zan tafi na barta,Muka yi dariya tace sai da safe bacci zanyi,nace sai a Kori na chating tace ga dahir was zai tsaya a kila wa kala ta fita.

  Key Nawwar ya Saka a kofar sai da gabana ya fadi nace ya ka sa key yace sarkin tsoro ni ba abinda zan Miki bacci zanyi a nan zan kwana ya cire kayansa ya shiga toilet wanka yana ce min kawo min abinci,naje kitchen na zubo masa.


  Ganin dare baiyi ba Nawwar ya Kira Baso da Kansa ya tsara Baso yace ga wata dai dai kai kazo,Baso yayi dariya sosai yace to ni wai dole ne sai Kun min matar ko na ganta ai sai mun daidaita,Nawwar yace ai shi yasa muke so kazo ka gani ko zaka dace wlh tayi,Baso yace full option ce kace? Nawwar yace sai Wanda ya gani maza suna ta zuwa sun mata caaaa,Baso yace ka gane ko ka Dan min keeping dinta aside ko ya kace? Nawwar yana dariya a ransa yace ai Karka damu ka samu kazo kawai,yace weekend zan shigo ba yaawa ni ma na matsu na fara koton nan,tattabaru ma kana gani kullum a koto suke sai ni gandandan Dani Ina zaune Babu yar wata ta yin ae yane ai kaga ba magana Oga,Nawwar yace ya dai   kamaceka,yace chansa Oga sai nazo ba yaawa.

    Ni dai Ina jinshi Ina ta dariya nace tab Omaira ta shiga uku Chansa kadai ta isheta,Nawwar yace ai zata iya dashi dai dai take da shi naga bata jin magana itama,Dariya nayi ya dauke Jariri ya kwantar dashi a gadonsa dake gefe yace Yau babanka ne zaiji dumin Matarsa,Nima a bani  nonon da ake ta talla da shi kowa ya gani,dariya nayi ya maidani jikinsa,ya min rada na fara dariya zan gudu ya makalkaleni yace bafa wani abu zanyi babba ba,kawai ki sa na samu Salama, nace to Ina murmushi,yace sai kyau kike kina bulbul ni an barni a watse.









Kuyi hakuri bacci nayi na manta Allah🤣🤣🤣🤣




AsmaBaffa

[8/30, 10:20 PM] AsmaBaffa: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼

                MATAFIYA


BOOK 2





























No comments