Breaking News

Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 56-60

 




BOOK 2



                 56-60



Official


By

AsmaBaffa



SADAUKARWA GA

ZAINAB USMAN



*MISKI 3in1 Alfirdaus*🌹 Albishirinku💃   original miski daga *Egypt* miskin da koda yaushe Kuna yabawa dashi  yana dauke   1.*Musk oil* ana shafawa agaba bayan gama al'ada inda hali za'a iya ringa sawa Koda yaushe yana maganin infection yana gyara gaban mace sosai 🙈ko yaushe gurin yakasance cikin kamshi 😇bayaga haka sunnah ne amfani da miski

  2.*Musk cream* Ana shafawa ajiki gaba daya musamman wajan cinyoyi yana sa jikin mace koyaushe yakasance cikin kamshi kuma yana gyara fata, yasa tayi laushi 

 3.*Turaren tsarki* wannan turaren karshe ne 🔥 🔥 ba lallai se bayan gama period ba koda yaushe zaki iya rinka tsarki dashi yana gyara gurinnan🙈 sosai, kuma ana shafawa a hammata  yana kawar da  da wari karku bari abaku labari 🙍‍♀️👱‍♀️


Masu bukata ku ne wannan number

09065959708



Page naku ne


Jannat collection

Mhiz Auwal 

Faeezah

Jalloty

Zuwairayahaya8

Ameesha couture








         Hammad shine driver Ahsan,duk Wanda Yazo siyen Awara kyauta ake bashi ta dai dai kudinsa da zai siya,sai data kare tas ya bawa Cele botikanta ta karba tace na gode ta juya ta wuce gidan Kaka,tana tafiya tana irga kudinta tana Wakar larabawa ta Nancy ba uwar data iya kawai haukarta take fada , Ahsan yana binta da mota bata gane ba har gidan Kaka a kofar gida ta tsaya gidan dogon gida wajen Hawa goma sha nawa amma Cele haka ta dinga kwalawa kaka Kira,Kakaaaaaaaaaa kamar me Kiran Sallah,Kaka ne ya dawo daga masallaci da gudu tunda Cele ta ganshi da gudu tace to shegun Suna bayansa muke nan kullum a gudu sabo da kana kasar mutane itama kafin Kaka ya karaso tayi cikin gidan da gudu,Kaka ne ya shigo a hankali,tace Kaka sun tafi? Yace wa? Masu kame wanne kame Kuma  wasa jini fa nakeyi ni sabo da na Kara kwarewa a gudu,Cele tace wallahi kaban tsoro na zaci askarawa ne wannan gudu haka haba Kaka,Kaka yace yau naji yar jakar Uba Idan ban fara koyon tsere ba sai yaushe,kina ganin garin nan irinmu gaba daya mun zama Yan tsere ba yaro ba babba ni yanzu motsa jikina zan dinga yi kullum da safe,Cele tace Kaka,yace Naam tace Ahsan din yaki zuwa yaki dawowa bakin Dan Iska wlh Idan bai zo ba sai na masa rashin mutunci muna yin aikin hajji zamuyi tafiyar mu,ni yanzu Number din Umma ce bani da ita bani data kowa,Kaka yace Allah ya kawo shi yar nan Cele ko aure kike so ne yanzu? Cele tace ae yanzu hankalina yayi wajen aure Kaka,Nima inyi Auren nan na shiga gwagwarmayar rayuwa,in hau gadona ni kadai na kwanta,Kaka in dafa abinda nake so kana gidana dakinka daban duk zani muna tare ko? Kaka yace ke kadai ma zaki kwanta a gadon haka ake auren,dariya Cele ta saki tayi dage da kafafun ta tare da dafa kafadar Kaka kamar sa'anta tace na sani Kaka ai na sani wai irin yar kunyar nan.

  Allah ya kawo na gari tace Ameen.


   Cele da Kaka suka fito tace muje mu fara siyayyar tsaraba kafin muyi aikin hajji mu tafi Nigeria ko,Kaka ya bita hannunta rike cikin na kaka suna tafiya tace Kaka Allah kayi kumatu duk ramarka ji yanda ka Dan ciko,Kaka yace Madara wasa ce? Zaki da maiko ba wasa ba Yar nan baki ga nayi kiba ba,ke kuwa har yanzu kumburin nan bai barki ba Cele ko sai an Kara Miki jini ne? Cele tace Alla ya kiyaye inshallah zan murmure ai akwai abinci me kyau, Shagon da suka shiga suna siyayya Cele tana ta jidarwa Ummanta kaya da Yan uwanta sai gani suka yi masu kantin sun shigo sunce komai ya musu su zaba an biya kudin,Cele tace waye haka ne? Kaka yace oho ke bari na gwangwaje kaina nima cewar Kaka ya dinga jidar kaya Cele ma haka masu tsada tunda sunji ance komai su zaba an biya sai da suka gama sannan aka shirya musu a Leda suka tafi,Ahsan yana ta jin Dadi ya riga ya biya mu su,suna tafiya a hanya sunyi nisa wani balaraben ya tare su a hanya ya Mika musu kudi da dan yawa yace sadaka bayan Ahsan ne ya aiko shi ya kawo,Cele ta Kalli Kaka tace adduar mu fa ta karbu a dakin Allah,lokacin kudinmu Yazo cewar Kaka,yace muje mu sha abin nan me sanyi iskrim yake ko me,Cele tayi dariya tace Ice cream Kaka,yace kune Yara mu Kam bakin mu ya gaji da miyar kuka tun muna Yara,suna zuwa wajen Ice cream din sai da suka gama siya zasu biya kudi wani balaraben ya shigo yace ya biya musu su je,Cele daga ji an biya tace Kaka ai kadan muka siya mu Kara,yace mu Kara zasu biya Allah ne yake ciyar damu,suka Kara da yawa aka ce nan ma an biya,Cele tace anya kuwa babu aljani a harkar nan,Ahsan yana bayan su basu sani ba suna juyowa ya juya baya ya tafi,sun zaci kawai wani balaraben ne,amma Cele tace wlh kamar Ahsan wancan Dan banga fuskarsa bane,Kaka yace ke wannan da gani ko a kasar nan me kudi ne Kalli ma kalar jallabiyarsa Kalli takalminsa,Kai Kaka Ahsan dinma haka yake,Kaka ya sheke da dariya yace Cele kina takari Zaki samu kalar wancen ko ta baya ka kalle shi kasan ba karya, ke dai muje a bar zancen,Cele tace shike nan tunda baka yarda ba amma shi Allah ba abinda ya gagare shi zai iya hadani ma da sarkin garin nan.


     Salma ganin Auta kullum yana motsa jiki Exercise itama sai ta sa hijab tazo tayi ta gudu a can karshen gidan inda Auta yake,Bai kulata bata kulashi kullum haka suke yi da sassafe.

   Bayan sati biyu yau Salma ta sha wanka cikin kana nan kaya ta tsula uban kyau,jean dogo sai Riga me kyau yau ba school, tana zaune ta harde kafa tana kallo, Mami ta fito tace kin fasa girkin ne? tace zanyi mana ai indai Ina gida ki Daina girki Mami zan dinga yi miki dan Allah,Mami tace to ba damuwa Salma,ta mike ta shiga kitchen ta shirya girki,zuwa yamma Wise ta shigo sai ga Auta ma anci gayu an dawo daga Office,Salma bata San Office yaje ba ta Kalli Auta kawai tace sarkin Mata Ina kaje mata Ina zaka mata,Auta ya Jita duk da a kasa kasa ta fada,yace na tabbatar Baso ba shi kadai yake Shaye Shaye ba harda ke ya hankadeta ta fadi a kasa , ya wuce bedroom,Salma ta fashe da kuka Dan ba karamin zafi taji ba, Wise tace Auta mene haka kuma ko juyowa baiyi ba,Wise ta daga Salma tace bakya jin magana Salma most you fight?,baki da gaskiya me kika fada masa naji kinyi magana kasa kasa,dama naji Rabi ta fada min abinda kike ma Auta bafa sa'anki bane sai kace ba wayayya ba,yaran yanzu ma da suka waye ai anci gaba,Salma tana goge hawaye tace Baso na ni ya maidani wajen baso na,Auta ne ya fito yace kutmar ......Baso....durun....Baso ya dinga durawa Baso ashar dake da Baso duk kunci kutmar .....Auta ya haukace wa Salma yace Ina daga Miki kafa bakya gani wai ni an fada Miki sonki nake yi ko dan baki San ta ya na kawo ki nan ba,wallahi baki Isa kin kasheni ba,kinyi kadan bakin cikinki ya kamani ke din banza village girl,Wise tace haba Auta mene ne haka,yace wannan da aurenta gwara yar Babydoll ta wasan Yara yafi min,ko naje na auri teddy wallahi da naga dama sai na fatattaka yarinyar a bed tana ganin sa'anta ne ni,Duk fadan da Auta yake a banza domin Salma ba jinsa take ba fitowa yayi ba Riga ta tsura masa Ido ta shagalta da kallon surarsa,Wise tace Kai Auta zan Kira Mami,Auta marin Salma yayi kadan yace daina kallona Mannerless,kumatunta ta dafe ba zafi ma ya mareta amma ta dinga kuka tace baza ka samu aikin gomnati ba a kasar nan, ko waya sai dai a siya maka Idan Ina nan duk inda kaje nema sai naje na hana,ke kike tunanin aikin gomnati nake nema Wanda ya dogara da gomnati shine a wahale,daga wajen aiki nake dan kiji na fada Miki mugun nufinki ya biki,Salma tana Shure Shure tace baza a biyaka ko sisi ba zaka gani aikin banza kake zuwa,Auta daki ya shige ya bar Salma tana kuka Wise tayi tayi akan tayi shuru taki,gajiya Wise tayi tace ke kan uwarki nace yar iskar yarinya wlh yanzu na tattakaki wa Zaki rainawa hankali Dan...Wise ta zundumo mata ashar, tace ke Yan iska ne mufa na can ciki Idan ban ci uwarki ba shegiya nake wlh sai na Miki dukan tsiya na rantse da Allah,Cinnaka ce ni ba ruwana dana gida bar ganin muna mutunci akan Auta wallahi duk sai na tattaro su Miracle mu yagalgalaki shashasha wacce bata San me take ba,yar kauye Kya zo nan ki mana hauka,Salma tayi mukus Wise tace wlh kina magana sai na kwada miki Mari duk nan da kike gani lafiya muka samu mun fiki hauka da kwaya,bariki Zaki nuna mana keee lallai tab,kyaleki yayi shi yasa kike iskanci,Wise ta fisge wayar Salma tace bari na Kira Bason a fada masa shi ya dauki mataki baza mu lamunci wannan ba,ke ko kunyar mahaifiyarsa bakya ji,Kara fa take Miki tunaninki bata jin haushi ne? Kin san yanda take son yayanta kuwa tana kula dasu mussamman Auta,to ba a nan gidan ba wannan iskancin tasss zamu sauke Miki shi,Duban duniya Wise ta rasa sunan Baso tace me kika sa masa? Salma jiki ya dauki rawa tace Dan Allah karki fada masa wallahi zuwa zaiyi ya dakeni,ohhh nan Kuma an kyaleki shine kike baje mana iskanci fada min sunan ko na karyaki,tace My love,Wise ta bude baki tace da auren naki,ai Baso yace zai sakeni na koma wajensa muyi aure,Wise takaicin Auta ya kamata tace Shima Auta ko shashasha me zaiyi da wacce ba shi take so ba,ai gwara na gayawa Auta kawai ya nemo wata ya Kara aure,Salma da sauri tace better wooo ahhh a fada masa, Wise Baso ta Kira bugu Daya ya daga ya fara auno zagi yace ba nace ki daina kirana ba wai da aurenki kike kirana,Wise tace matar Babansa ce,Yace ahhh chansa ma chansa chansa dai,to ya kike ya akayi ne ko baki gane bane,Wise tace dare dare Oga yace ah Wallahi Dare sai barawo, wannan ai tamu ce to Dare Allah wallahi ashe kin iya gaisuwar mu,Wise tace Sa'a dai wallahi,Baso yace Ina gaida ki,na karba master,tace dama Salma ce yace ae,tunda aka kawota kaga dai tafi wata guda to wallahi tunda tazo ta buwayi mijinta gaba daya ci masa mutunci takeyi ba abinda bata fada masa, Baso yace bani ita Dan burar....aka mikawa Salma waya,jiki na rawa ta karba tace hello sai da Baso ya mata ashar tafi goma,yace abinda nace kiyi kenan? zanzo garin gobe Dan uwarki,wayyo na shiga uku tace ta kashe wayar,tace Dan Allah Aunty kiyi hakuri ki bashi hakuri, Wlh na Daina, Wise tace kije ki bawa Mijinki hakuri na fada Miki karamar yar iska,tsabar taurin Kai Salma bata je ta bada hakurin ba haka Wise ta wuce,Mami tana jinsu taki fitowa tace gwara ma Bason yazo a huta ta hana min Auta sakat.


    Baso ranar motar dare ya bi,da sassafe ka rantse a garin ya kwana sai gashi,Auta yayi Shirin school itama ta fito Sumi Sumi sai ga Baso yayi Sallama Mami tana ji taki fitowa,Baso yana zuwa sallama yayi yace kuyi hakuri tana Ina,Salma ta saki ihu,Baso ya zaro belt din wandonsa ta koma bayan Auta Baso ya bita suka dinga zaga Auta, tana wayyo ka ceceni na shiga uku bazan Kara ba na tuba Dan Allah kayi hakuri ka yafe min iskanci nane ya jawo min,Auta kuwa Baso ya rikewa hannu yace kyaleta,Baso zai fisge yace Karka daketa,yace abinda nace tayi kenan,ke ni dake munyi Hannun riga,ba abinda na gaza yiwa yarinyar nan sabo da na fita hakkinta gata nan sabo da ita na hakura da sana'a muka siyar da gadon mu na siya mana Dan gida,Babu Wanda na bari yake zuwa zance wajenta sabo da kar ma a samu wani ya lalata ta,Ina so ta auri Miji na gari, ni ban cancanta na aureta ba,ban cancanta na aureta ba Ina ganin kamar na cuceta ne ma tunda ni nasan bana gari bane,shi yasa bana daga mata kafa Idan tace tana so na ni harga Allah a yar uwa na dauketa ba wacce zan aura ba sabo da ni ban cancanci Salma ba tana da hankali kawai tasa banzan tunani ne a ranta,Salma kiji da kyau ni bazan aureki ba ko kin kashe aurenki, bazan fada Miki ya mukayi da Auta ba amma Idan lokaci yayi zan fada miki,Idan Zaki zauna kibi Mijinki ki zauna ki yiwa kanki gata Allah yaga niyyata kuma ki sani nayi aure ma ni tuni sati biyu kenan amarcina nake ci,ya juya ya fice abinsa ko Sallama ba Wanda yayiwa.


     Salma a wajen ta sulale a kasa tayi zaman Yan bori tare da dafe Kai,Auta yace tashi mu tafi school,baza'a je ba wayyo Allah na shiga uku na lalace Baso...Baso...Basooooo.....Auta dariya ta kwace masa ya dinga sheka dariya,tace Mugu azzalumi bazan taba sonka ba duk Kaine ka jefa ni a wannan Halin,Wise ce ta shigo fuska a murtuke tace Zaki tashi ki tafi school din ko sai nayi fatali dake,tashi tayi tana kuka wayyo Baso tana Jan Jakarta a kasa kiiiii wayyo Baso...wayyo...wayyo zuciyata zata fashe,Auta yace yar banzar zuciyar da zata fashe ma kowa ya huta jarababbiya,bata kulashi ba a haka ta shiga mota tace motar ma baza a rufe ba ta barta a bude,Auta ya fito ya zaga ya rufe ya shiga yaja mota har sukaje tana kuka tace wallahi bazan ji me Malamin zai ce ba bazan ji ba.


    Ta fito tayi part dinsu idonta jajir ta zauna a class tayi zuru da Ido,Malami ne ya shigo Idan yayi magana aka amsa masa da yes sai aji Salma tace No Idan abin ace no sir ne sai tace yes wai ita bata ganewa bata ji ma,Malamin tambaya yayi a class aka daga hannu ciki harda Salma yana gama tambayar ta amsa tace is Baso,get out,ya koreta waje ta mike tace thank you very much sir ta fice,aka bita da kallo,har ta fice ta Bude kofa yace sorry sir I'm looking for Baso,are you mad who is Baso in this class akace babu,shi bai San ma suna bane,yace young lady what is Baso? Salma tace Baso Is Baso the most Handsome gentle man in the world,and also ...kafin ta karasa Malamin ya rufe kofarsa  ma, fita tayi ta tafi can kusa da bangaren su Auta ta samu waje ta zauna tayi tagumi,Auta yana zaune ta jikin window yana kallonta,abu kadan zai juyo ya kalleta,kallon wajen window din tayi karaf suka hada Ido a hankali ya Kalli inda lecturer yake,taci gaba da kallonsa ita,sake juyowa yayi yaga tana kallonsa da sauri ta dauke Kai,shi yaci gaba da kallonta ta juyo kafin ta Ganshi ya dauke Kansa,ta tsura masa Ido Shima kafin ya juyo ta dauke Kai.


     Auta yana aji ya Lula tunani har aka gama musu lecture Shima ya fito tana zaune taga sun fito yana tafiya yana kallonta ta dauke kanta karma su hada Ido,yana dauke Kai ta juyo taci gaba da kallonsa yana tafiya,wata macece glory tazo da gudu ta rungume Auta juyowa yayi yana balbale Glory da masifa yace Ina da mata na fada Miki ki faina min haka,zuwa tayi zata sake rungume shi ya zuba mata Mari ta dafe kumatu yaja tsaki ya juya yana masifa a ransa yace zata ja min wannan masifaffiyar yarinyar ta dameni ,Salma tana kallo baki ta turo gaba tace Ina za a hada wannan da Baso ai gwara Baso na mata ba wacce zata taba shi ta ja tsaki tace ballagajin Namiji me za ayi da irin wannan duk inda yake sai mata wlh bazai shafa min kanjamau ba,tashi tayi tana fushi ta fice daga Makarantar, Auta ya dakko motarsa ya biyota yana mata horn yace yar iska gardiyar banza sai wahalar dani take,aure Sam ba Dadi a ciki dama sai da Yaya Nawwar ya fada min ai gashi nan, da a baya Ina nasan wani tunani a rayuwa,na taba zaton akwai abinda zai iya hanani bacci a duniya,har na zauna Ina tunani sai wannan banzar, horn din duniya taki kulashi Idan ta koma Kuma ta fadawa Mami ayi masa fada.


   Fitowa yayi da niyyar mammaketa ya fito kenan wani me machine ya taho a dari ya takewa Auta kafa faduwa yayi ya rike kafar yana Kara da ihu,mutane suka taho Salma juyowa tayi ta Ganshi a kasa yana ihu ta Riga kowa tsallakowa tana cewa wayyo Sannu ta rike Auta tace kaga halinka ko sai fitina me ya kaika tsallakowa wlh baka jin magana yanzu gashi ka jawo an take ka,Auta yana murkususu yana rike da kafa cikin masifa yace ba ke kika jawo ba sai naci ubanki,Sorry ai ban San machine zai takaka ba ta furta, Yan school ne suka dauki Auta,Me machine yana ta bada hakuri Salma tace Kai Dalla yi mana shuru aikin banza sai ku dinga sharara uban gudu gidan wa zaka je haka ko sama zaka tashi ko matarka ce zata haihu ai sai haka ta ja tsaki ta shiga mota aka tafi da ita asibitin wani Dan ajinsu ne ya ja motar.


    Mami ta Kira ta fada musu kafin kace an cika Private hospital kamar wani Dan Gold,Mami ta tambaya me ya kaishi tsallaka titi,Salma tayi Miki Miki a hankali tace rigima fa irin tasa,fitinar tsiya baya ji,kowa dake wajen sai da Salma ta bashi dariya kamar itace Yayar Auta,Auta yace wlh itace gata nan ya kwashe zance ya fadawa Mami,Mami tace Wise Kira min Baso aka Kira Baso,Salma duk ta tsure,Mami da kanta ta fita sukayi magana da Baso yace ku sa masu gadi su huta ta dinga Bude gate tana rufewa sannan ta kula da Auta har ya warke abinci da komai nasa ita zata yi sannan ku kaita gadin gate,Mami ta dinga dariyar muguntar Baso,ta mikawa Salma waya yace kina ji na? Tace ae,yace gobe zanzo Zaki ci ubanki,Salma sai kuka Baso yace zaizo, a ranar aka yiwa Auta aiki wasu kasusuwansa na kafa sun goce kafar har ta kumbura sumtum.

   Washe gari da wuri sai ga Baso yayi kyan gani yanzu da gani ya samu canji,ya samu Salma tuni ta fara kuka tana bashi hakuri tace ko mene zanyi indai zaka hakura,Yace yanzu kullum da asuba gate Zaki tafi ki dinga tura kofa kina rufewa ga duk Wanda zai fita a gidan nan,Sannan abincin Auta duk kece Zaki yi,sannan ki kula da shi har ya warke,Salma tace haba Yaya Baso yace ke kinci....zanyi zanyi wlh, tsaki ya ja yace na sa a fada min Idan baki ba zan sani karki bari na bar abinda nake na dawo gidan nan sabo da ke wallahi baza kiji Dadi ba ya juya ya fice ko Sallama yayi tafiyarsa mota ya bi.

   

    Mami taji komai tana wajen,tace to gamu duk shedun Baso ne Idan kika ki yi zamu fada masa,Baffa ma da Papa da suka ji suka dinga dariya gaskiya Baso ya iya punishment ai gwara haka ko ta yi hankali,ba Wanda ya goyawa Salma baya Kuma kowa ya fita harkarta kamar yanda Baso yace musu, ba Wanda ke kulata a gidan yanzu.

   Washe gari aka sallami Auta an bashi sandunan karfen ya rike suka dawo gida gaba daya har Salma,tana fitowa Mami zata dauki jakar Auta,Baffa yace kyale Salma zata dauka,takaici ya kama Salma amma haka ta Bude mota ta dakko tana kunci,Baffa yace muje Honey Salma zata raka shi ciki ya janye Mami,Mami bata so a zakunci danta amma ta hakura suka tafi aka bar Salma da Auta,yatsa tasa ta taba shi wai muje  tana turo baki,yana tafiya da sanda tana binshi a baya a hankali har bedroom dinsa rike shi tayi ya zauna a gefen bed    ya kalleta yace abinci zanci na sha magani,me? ta tambaya, da fada yace abinci nace zanci na sha magani duk ba a dalilinki na shiga wannan Halin ba,ficewa tayi taje kitchen ta samu anyi girki ta zubo komai a tire ta shugo tare da ajiye masa a saman bed ta juya tayi ficewarta tana cika tana batsewa,Auta yayi murmushi kawai,yaci abincinsa ya sha magani ya kwanta,har ta zauna Wise ta shugo tace baki ji horn bane a gate kije ki budewa mutane gate,Salma ta tashi ta tafi tana hawaye ta hau tura gate tana fushi,Nawwar ne ya shigo ta rufe gate, duk babu masu gadi an basu hutu,Nawwar ya kalleta tace Ina kwana Yaya ya amsa da fara'a Shima yasan komai ya wuce ciki abinsa.

   Wani horn aka sake yi tazo ta bude tana faman yarfe hannu zafi wai hannunta Mami da Baffa ne zasu fita ta dauke Kai gefe daya,Baffa glass ya sauke ya mata horn taki juyowa yace hey gate woman juyowa tayi ta danyi murmushin gefen baki,suna fita ta tura gate ta rufe ta koma kujerar masu gadi tare da zama.


   Kitchen ta Koma tana girkin Auta tana zuwa bakin gate ko za a shigo sai faman zirga zirga take daga part din Mami zuwa Gate,tana sani ta zazzagawa Auta yaji da yawa a cikin abincin har ta gama ta hada komai a tire ta dauka ta nufi dakinsa yana kwance yana bacci tace Malam tashi ka jefa ni a masifa kazo kana wani bacci,Ido ya bude a hankali ya kalleta kawai ya ja tsaki yayi murmushi,ya kalleta again yace zan tashi zaune ya Miko mata hannu tazo ba musu ta taimaka ya tashi zaune tana fushi, yace kafar tana kaikayi a min massage kadan,kamar ta daki Auta zama tayi a gefen bed din,ya dora kafarsa a saman cinyarta,ta kalle shi da sauri ta turo baki ta kama kafar Auta me kyau ta fara masa Massage a hankali har da lumshe Idonsa, tana Dan yi yace ya Isa haka na gode,mikewa tayi yace a wanke min kaya ayi min guga sannan azo a taje min gashi,ni na Saka tara gashin wai ta juya ta koma kitchen ta ebo abincin itama ta tafi baki gate da shi tana ci a can tana turawa masu shige da fice gate,Sabreen ce tazo zata fita da motarta ta sauke glass tace me gadi a bude gate fast please sauri nake,Salma ta mike tana doka kafafu ta tura gate,Sabreen ta fice ta Maida ta rufe ta koma taci gaba da cin abincinta,tana gama ci ta koma ciki ta gyarawa Auta dakinsa ya shiga wanka lokacin,Fitowa yayi daure da towel rike da sandunansa yana dogarawa da kyar,ta wuce toilet din ta wanke Kal ta fito fuuu,ta dauki Cumb tace zauna Malam,Auta yace bai bushe ba, ya Mika mata karamin towel yace ki tsane min na gaji,tana hararsa ta karba ta dora a gashinsa tana tsane masa gashin har ta gama ranta a bace,ta dakko handrier ta fara busar masa da gashi har ya bushe ta dakko man gashinsa ta shafa masa kamar ta dake shi haka take ji, ta fara taje masa gashi yace da zafi fa irin wannan cisga haka,ya saki Kara tsayawa tayi tana kallonsa cikin kunci sannan taci gaba da tajewa a hankali ta gama tsaf ta dakko man lebensa na maza ta shafa masa tace oya yi haka ta hade lips dinta,Auta yayi yanda tace,ta gasa masa harara tace fitinanne ta doke shi kadan a gadon baya wani tasss tace ladan aikina.


    Wanka tayi a gurguje ta shirya cikin Atamfa Riga da skert maroon ta koma jikin gate da botikan wanki da kayan Auta ance Kuma baza ta wanke a washing machine ba tana zaune tana cin uban wanki kayan da yawa dan ma ba dirty,Mami da Baffa ne suka dawo ta mike ta Bude musu gate ta koma taci gaba da wankinta,Mami tace Allah yayiwa Baso Albarka ya kawo mana maganinta yar banza irinsu sai da wahala suke ganewa.

     Tana ta wanki ta daga 

 boxers din Auta tana bata rai tace bari Muji ta shinshina ta sake cewa bari Muji saitin wajen Abar inda take zama ta shinshina tace Allah ya taimakeka suna kamshi,da gani wannan tasa karama ce ko ta Baso baza ta Kai ba,yo sau nawa Ina ganin ta Baso a wando katuwa tafi karfina ma ta Baso,gashinta ta Sosa tayi dariya tace Allah ya shirya ni la'ilahaillallahu ai na Kalli ta Baso a wando na more bai sani ba.

    Kafin ta gama Mami ta fito ta fito tace gobe da sassafe ake bawa flowers ruwa da garden ki tabbatar kinyi,Salma kamar zata yi kuka haka tace to.

   Tana gama wanki ta shanya ta koma bedroom din Auta tace na gama maka Malam? yace yes you can go yana kunshe dariyarsa, tace yanzu da yajin nan ka cinye abincin nan? Yace ae mana au yayi yaji dama? Ido ta zaro tace tab wani takaici ya kamata shi bai ma San da yaji ba,Auta kuwa da kyar ya iya ci Kuma yana sani ya nuna mata ba yaji sabo da yasan dan ta bata masa rai tayi to ya nuna Sam baiji yajin bama. daure fuska tayi ta fice.

   Tana gama aikin nata tayi Shirin bacci ta fada saman bed sai bacci a gajiye.


  Umma ce taga kayan Abinci ana ta sauke mata mota guda wai inji Miracle,murna ta ishi Umma, Omaira tazo tace na Umma ne ita kadai Wanda basa son mata ai Bai kamata suci kayan mata ba ta sa aka shigewa da Umma kayan Abinci kaf dakinta,sai sutura gasu nan iri iri wai Umma ta Dinka suma su Omaira da nasu,ga kudin cefane.sai murna suke har su Bilkisu wahala ta Kare,Abba da Uwa sai zare Ido suke sun rasa inda zasu sa kansu, Washe gari Nawwar ya turo abokinsa Khaleel ya dauki Umma zuwa cikin wani katafaren gida na gaske yayi kyau matuka a unguwa me kyau Umma taga komai an zuba furniture da komai na more rayuwa tace gidan waye wannan kuma? Khaleel yace naki ne inji Nawwar ki dawo ciki ki zauna takardun gidan ya Mika mata,Umma harda kukan farin ciki da ta tuna irin wahalar data sha a rayuwa da haihuwa a gidan Abban su Omaira,Khaleel yace ai ba kuka zakiyi ba Umma sanda kuka ga dama ku tare,Umma tace wa? Dannan ai nazo kenan tace na dai yi waya yaran su kwaso kaya suzo nikam ban komawa cikin ukuba,Khaleel yayi dariya yace to Umma fito ki ga motarki, ta fito suka zaga ta baya taga mota lafiyayya ta kirki me kyau arsh,ta shafa motar tace Allah yayi masa Albarka tana goge hawayen murna tace mutumin kirki Zaki dauka driver ya dinga tuka ki,Umma zakwkura ce tace na koya dai ai Koya zanyi Dan nan da lafiyata da komai,yace me aikin gida fa? Tace sai na aurar da su Omaira kaf sai a daukar min me aiki,yace to shike nan yana gamawa ya tafi,Umma kin komawa tayi shuru Uwa suka ga bata dawo ba ga Yara su Bilkisu sun dakko kurkura suna ta kwashe kayan sawa Dana abinci sauran tarkacen kayan dakin Umma kuwa Omaira ta fito tasa kafa tayi ball da tukunyarsu ta girki ta daki wani bahon wankan su tace Dan ubanku ku lalace tace Uwa ga kwance ne Kya dinga yiwa danki girki tunda bakwa son mata mu Allah ya mana tashi,Ku tashi ku tafi gidan uban wa ai nan ne gidan ubanku dole ku zauna ita uwarku duk inda zata taje to taje cewar Abba yana bakin ciki yaji Umma ta samu gida hadadden ga Alheri daban daban,Omaira taje gaban Uwa ta buga skert dinta da hannaye biyu tace a kada Miki buje a haka Zaki kare ta juya tayi fatali da wani tire dinsu ta bar gidan,Abba yana kallo wato shi baza su iya masa rashin mutunci ba sai uwarsa, Su Rahma suka tafi su tuni sunbi motar kaya,Omaira kuwa ba rawar da bata yi ba a gaban su Abba harda galala da kafafu ta fice,sai kallon gidansu suke suna Murna,Aunty Rabi taci sunanta Miracle wallahi cewar Omaira, su Bilkisu a sabon gida suka yini suna ta kallon motar Umma.


    Mairo zuwa yanzu a Hannun Mahmud ta jigata duk kuwa da abinci ta rame tayi duhu Dan man da take shafawa baya bari taje ko kofar gida ya kare tayi uwar Rama,yarinyarta kuwa tayi bulbul da ita,kullum Mairo a kuka take gashi ba dare ba rana sex yake da ita yana jin dadinsa kamar me,Mairo Addua ta koma Allah ya kubutar da ita ta huta,yau yana dawowa ko hutawa baiyi ba ya fara tube kayansa,Mairo hawaye ya zubo mata ko a jikinsa ya fara shafata Babu nutsuwa gagagaga ya shigeta,Mairo azaba tasa ta jawo kwalabarta data fasa ta boye a kasan gado tace sa masa a wuya tace sake ni Dan babarka suka fara kokawa zai kwace kwalabar Mairo ta Yanke shi da ita a Kansa,balarabe yaga jini ya saki Kara,Mairo ta fara Aljanun karya kamar gaske ta hau Aljanu ta barbaza gashinta tana ihu da hauka tana fari da Ido tana kafkafkaf kamar me fyarfyadiya tana gurnani,tsorata Mahmud yayi gashi da tsoron mutuwa Nan take ya saki Mairo duk da haka Sai da ta kafta masa yanka a hannu da kwalaba ya rike hannunsa yana Kara, ta dauki yarta ta fice da gudu Allah yasa yana sauri zaiyi sex bai ko rufe kofar ba,Mairo ta fito tana falfala gudu kamar za a kamata tana gudu tana kwarara ihu a gari ko wanne takari yaga Mairo sai ya kwashe da gudu Shima ya Kara gaba,tana gudu Cele tana siyayya taga mutane radada ga Mairo tana ihu fasa siyayyar tayi ta fito ta kwashe da gudu,Kaka Allah sarki ya dawo daga masallaci da sallayarsa yaga takari yuuuu suna uban gudu Shima yabi sahu sai ga Kaka cankal cankal da kafafu sirara, Yazo ya wuce su Cele,Cele ta tsaya cak tace Yasin bani da amfani tunda kaka ya fini gudu,Kaka kamar guguwa haka, taci gaba da gudu har cikin gida tace wlh sai mun bar garin nan wannan masifa da me tayi kama kullum mutum a gudu,Mairo kuwa sai da ta zo gaban askarawa ta zube a kasa tace da larabci Dan Allah ku kamani ku kaini Nigeria,dariya suka hau yi mata suka ce yau ba ranar kame bace ba a Basu umarni ba,tace Dan Allah ku taimaka wani ya boyeni ana baku damar kame ku fito Dani,suka ki yarda sai gidan Sadiya ta tafi tace wlh ko a kafa sai na tafi Nigeria,da kyar Sadiya ta lallaba ta tace ta bari tukun ayi aikin hajji sai ta tafi Mairo duk ta zauce, a zabure take ta cakumi Sadiya tace Allah ya Isa ke da uwarki tsinannu Kun jefa ni a masifa,kin san haka larabawan suke kika zugani nayi aure,Sadiya tace ahayye muka dai taimake ki,ke da kika gudu kika bar Iyayenki marar tarbiyya kinzo da cikin shege an taimakeki kina mana iskancin banza, Kuma larabawan an fada Miki kowa haka yake da sex da yawa ko a bakar fata ana samun irinsu Wanda basa gajiya sai kiga laifina wallahi sai na koreki Nima nan aure nayi gidan mijina ne kafin ya sakeni Ina caskar kudi zan Kara gaba,Mairo tace Allah ya hadaki da irin Mahmud suka yi kaca kaca daga baya suka shirya dai.


   Gwaggo ta warke fes sai dai yanzu tana dingisawa baza ta taba komawa dai dai ba,Dagaci an murmure Rabi tana masa aike akai Akai gashi yana ta kasuwarsa yanzu Jira suke ta haihu suje kafin bikin Gaji,Gaji ta samu Miji a cikin Kano yana da mata da yaransa uku lecturer dinsu ne a da,bikinta saura wata uku kafin lokacin suna sa rai Rabi ta haihu suna ta Shiri, yaran Dagaci mazan suna ta karatunsa suma,Gwaggo kuwa an nutsu lokaci kadan sai ta sa an Kira mata Rabi a waya sunyi hira tace Idan ta haihu zasu je. 

  Rabi ta basu kabarin anga iyayenta ta fada musu komai tace zasu zo tare da su har gida,Dagaci sai yadawa yake a gari Rabi anga iyayenta,ance wacce Rabin? Rabi 'yata dana rike yar tsuntuwa iyayenta sun bayyana Alhmdllh zasu zo ma.

  Seraline kuwa ta dauke uwarta Inna ta Maida ta gidanta bangarenta daban sabo da ita kadai ta rage mata, Inna ana can itama.


     Gidan su Cele wasu dakunan da suke Empty sai gani tayi an kawo Yan daudu su wajen takwas gasu da Jallabiya ta maza, can babu zani  baza a barsu a garin ba sai dai sunyi bleaching kwalliya suke irin ta mata duk gasu nan a Makkah Yan daudu shekara da shekaru sai su tafi can da sunan neman kudi suna daudu a can suna luwadi sun cika gari suna ta batawa mutane suna,wasu ma sunfi shekara ashirin a can.

  Cele tace ya zama dole na bar gidan nan wallahi wannan zama a wannan gidan bala'in zunubi sai ya shafeka,wannan wacce masifa ce haka,dole a raina mu wlh dole a daina ganin Takari da mutunci,wasu ne suke bata wasu akewa takari kudin goro amma akwai na gari, Driver ne yayi Sallama da Cele ta fito ta ganshi da kantamemiyar mota ya juyata yanda baza ta Kalli gaban glass ba,Ahsan yana ciki yana kallonta,suka gaisa tace Kaine ka siyo min botikin Awara? Sannan kana ta min Aiken kudi? Hammad yayi murmushi yace ae nine,a gaskiya na ganki Ina sonki,Cele ta kalle shi tsaf tace kayi hakuri ni zuciyata ta Saba da ganin me haske balarabe nake so ga Wanda yake jajir kullum idona Idan Ina kallonsa zasu Kara haske,Hammad yayi murmushi yace kiyi hakuri ki bani dama,Cele tace bafa zan soka ba ni Karka takura min wani nake so ni,Hammad yace larabawan nan basu da kirki,Cele tace Allah ya kona me karya Karka harzuka ni,ko Ina akwai na gari akwai na banza,Wanda nake so na gari ne,Hammad yace kiyi hakuri naga har kin harzuka,please Idan ba damuwa zan canja miki gidan zama,Cele ta kalle shi tace bada ni ba ka hada Kai da wasu larabawan a siyar dani yanda suka yiwa kaka,Yace haba dai Ina muamula da larabawa amma na kirki tace Kai ka kiyayeni munga Abila habee ma karewar tuggu,mu fa a tafin hannu mu kuke muna da tarihin garin nan abinda suka aikatawa masu Imani nasan akwai burbushin su Abu jahal har yanzu ba ruwana a Africa ma akwai nasu,ka kyaleni na bar garin nan lafiya ana aikin hajji zan tafi Idan na sauke farali,driver Hammad yace ni dai Ina rokonki Idan kina so ma zan hadaki da Yan sanda su ai baza su cuceki ba,Cele tace amma ba mutun daya ba a taho da bataliya guda ayi min kwambo da su sannan na je,yace to na gode ya juya ya mata Sallama,Cele tace jibe shi wani guntu da shi Dan banza suffa kamar gajeren wandon Kaka ta juya ciki,yana komawa mota ya fadawa Ahsan yanda sukayi yayi dariya yace ai Yan Makkah suna Shan gori a wajen baki sabo da Annabin Rahma yayi Hijira sun Kori Dan uwansu.


    Washe gari motocin Yan Sanda sun Kai hudu ga mota Ahsan ya bada suka zo kofar gidan su Cele ba Ahsan a wannan karon,Yan gidan suna ta murna anzo kama Cele wai ta tsokani wani balaraben za ayi maganinta,sai suka ga ta hado kayanta ta fito tsakar gida tace na gaji da kwasar zunubi kullum Ina gidan fasikai,Boobs dinta tallafe tace abuna ya huta da kawo hari yanzu zai Kara bulbul,shegu inshallah sai an kamaku Daya bayan daya sai kunyi bursuna a kasar nan,suna jinta tana masifa tace Allah yasa na hadu da wata a hanya ta min magana ko ta nuna ta sannu wallahi sai na mata daga daga,in ance a fita filin badar Kun kasa sai madugo matsiyatan banza baza Kuga Annabi ba ta fice ta barsu,tana fita suka ce Alhmdllh haba jaraba ta tafi yau zamu huta.

   Kaka aka biya ya fito da kayansa Shima zai shiga gefen Cele yayi Bismillah yace Ubangiji ka rabu da sharrin Yan uwan kafiran zamanin baya ya shiga mota suka tafi,Cele tace kaka muyi alkunutu tun a mota suka fara karanta alkunut ita da kaka har aka kaisu dai wani gida a unguwar takari ne amma gidane dogo a hawa na biyu Cele take ita da Kaka,gidane hadadde na glass da Glass gidan glass takari suke Kiran gidan,2bedroom and Palo sai kitchen kowanne daki da toilet komai sabo ne a ciki me kyau Palo yasha kujeru da center carpet,Hammad yace Alhmdllh kuyi zamanku a nan Kuma ku daina wata sana'a zan dauki nauyinku,Cele tace Masha Allah,Allah yasa na soka a haka,nidai ba ruwana Idan ban so ka ba Karka kace na yaudareka ko na cuceka naci kudinka,bani na Saka ba ato,Kaka yace kwarai kuwa,Hammad yace sabo da Allah nayi suka masa godiya.


   Washe Gari Ahsan shopping yayi na suturu masu tsada da kyau harda agogo Rolex ya bawa Hammad yace gashi ka kaiwa Cele a matsayin Kaine,Hammad ya tafi gidan su Cele suna ta kallonn film da Kaka,Kaka ga lemo a gabansa yana korawa yace Ina goge duniya Alqur'an bana son barin garin nan,kinji Ko ciwon Kai banyi ba har yanzu,Cele tace to komai me kyau ake ci ba cuta,Kaka yace da a Nigeria ne da yanzu na shanye paracetamol yafi carton guda,maganin ma baya aiki duk kamfanunuwan mu sun gurbata maganin basa aiki Idan cuta ta kamaka ayi ta gabza maka kwaya da Allurai basa aiki,komai namu Babu me kyau,asibiti ma abinda aka ga dama akeyi,sai ayi ta shirme ga inda ya dace a gyara baza ayi ba Kai muna Shan wahala a Nigeria kawai rayuwa muke,muma da halinmu muyi ta sabon Allah ana jika kasa da jinin bayin Allah Wanda jinin mutum Daya mumuni ya Isa ya haifar da masifa a kasa yau mutane million nawa aka kashe,a kama wasu a gana musu azaba,a kama wasu masu aure mata a auri matan wasu aure kan aure su haihu da wasu,cin Amana,yaron me gida ya kashe me gidansa,a danne hakkin marayu,zinace zinace,luwadi ga lasbiyalizim wai yan Lesbian inji Kaka alkalai zalunci kowa zalunci,masu siyar da kayan masarufi zalunci awo ma baza a baka dai dai ba,Yan kasuwa su boye kaya su tashi abinsu kullum sai an Kara kudin kaya,daga an fitar da doka kafin ta fara aiki mutanen kasar sun karawa kayan Abinci tsada, awannan zunubin da zalunci Ina zamu kaishi,Cele tace kyale su Kaka Allah zaiyi hukunci ga shugabanni sabo da suna da ikon su sa baki a gyara baza su ce komai ba su suna da kudinsu ba abinda ya dame su komai tsadar Abu zasu iya siya ba ruwansu,mutane Yan kadan sun jefa milliyoyin mutane a mafisa.

   Hammad ne ya shigo yayi knocking Cele ta Bude masa ta gaida shi ya amsa yace gashi ya Mika mata,tace Kuma ma dai? gaskiya kana kashe mana kudi mun gode fatan dai nan gaba Idan banji sonka ba baza aji haushina ba? yace ba damuwa tace to na gode Allah ya Kara maka so na ya links shi sai dari indai hakane ni kuwa na sha kyauta,dariya Hammad yayi yace kefa baza kice Allah ya sa Miki so na ba,tace wayyo bana mararin samunka yayi dariya ya juya yace na tafi tunda babu Kara abin,tace yo ai gaskiya na fada.


   Salma tana ta aikinta kullum bata hutawa,Mami ce ta shigo kitchen ta iske ta tana girki tace sannu Mami,Mami tace yawwa kawai ta shareta,kamar tayi kuka tunda Auta ya fara ciwo basa zuwa school dukkansu,jinyar Auta take fama.

  Washe gari da sassafe ta tashi ta tafi barruwan flowers tana sanye da Doguwar Riga yar fitted me siririn hannu dark blue me layin layin fari tana aikinta Auta yana zaune a garden din yana latsa waya yana kallonta tana rike tiyo tana fesawa flowers ruwa tana bi layi layi ta bata rai kamar zata yi kuka,ta Kalli Auta ya dago ya kalleta ta dauke kanta yaci gaba da kallonta ta sake kallonsa ta gasa masa harara,tana gamawa ta wuce gate ta budewa Baffa zai fita ta yafa Dan karamin mayafinta,tana rufewa na shugo da motata ta Bude min gate ta kalleni na kalleta nace Masha Allah gaskiya Allah yayi halitta itama,Ina fitowa ta karaso da gudu tace Aunty Ina kwana,nace lafiya Alhmdllh nayi wucewata,Salma ta tsaya tace kowa ya tsaneni ta fashe da kuka ta koma kujerar me gadi ta zauna,dakin Auta ta shiga yace ki kaini Palo,ta rikeshi tana dafa bayansa yana dogarawa da sandunansa suka fito Palo,ta karbi sandunan ta jingine gefe,Mami tana kallo tace Auta bai karya ba,Salma ta fada kitchen da gudu ta fara girki,tana jin Karar mota ta fito da gudu ta fice ta bude gate aka fita ta rufe ta dawo kitchen da gudu ta iske Auta yana kwance a cinyar Mami sai shagwaba yake,Ina wajen Wise sai daga baya na shigo bangaren Mami na samu Salma ta fito daga kitchen da tire ta jerawa Auta komai a dining tazo tace ka taso,Mami tace jeka ka karya, tace ke a baki Zaki bashi sometimes baya ci da Kansa,Salma kamar ta fashe tace to ta koma dining tayi serving nasa ta hada masa tea tace Bude bakin ko Shima sai an bude maka? yace ae,Hannu tasa a kumatun Auta ta matse masa baki ya saki Kara tace to ka bude ance,ya Bude kadan tana bashi a baki,yana ci yace nifa Idan Ina cin abinci ana shafa min gashi fa inji Auta,Salma tace nidai mutuwa zanyi kowa ya huta kawai ta saci kallon Mami taga tana kallonsa hannunta ta sa a cikin gashinsa tace ko kunyar Iyaye Babu a gabansu za ayi wannan aikin ni wlh Ina da kunya ba a nan na taso ba, Auta yace ko a Kira Baso ne? tayi shuru taci gaba da bashi a baki tana shafa masa gashi,Mami ce tace dani Rabi Idan cikin ya cika watan haihuwa ki dawo nan sabo da gudun matsala,nace ae haka yace me gidan can Shima nan zamu dawo,Mami tayi murmushi tace so kike ta rainaki ko kina tsokanarta kema.

    

   Auta yana koshi yace na koshi a goge min bakina,Salma tasa tissue ta goge masa,yace zan kwanta a kaini kan gadona,harara ta watsa masa tace tashi ta rike shi har da yin tangal tangal zai fadi, tayi sauri ta ruko kafadunsa tare da Mika masa sandunansa suka tafi.




Masu Audio kar a juya littafi Babu izinina na siyar da shi,






Masu sharhi Ina godiya aci gaba Dan Allah




No comments