Breaking News

Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 31-35

 BOOK2


   


                 31-35



Official


By

AsmaBaffa



SADAUKARWA GA

ZAINAB USMAN



    MASU AUDIO WANNAN BOOK NA SIYAR DA SHI BAN YARDA A JUYA MIN LITTAFI AUDIO BA




Ina masu bukatar unique kitchen utensils . fabrics adult and children's wears  shoe's and bag's.

Da masu bukatar ahada musu lefe ko masu bukatar iya luggage's din kawai  duk inkazo

R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE.

Zaku samu duk abinda kuke bukata ko a awanne state kake zaa kawo


   Masu bukata ga number. 0703 455 9202


https://chat.whatsapp.com/LAizQA6PofSLoFhQ7XeaQx



PAGE NAKU NE 

Mum Basma

Hafsa Abdullahi

Faeeza

Sumayya Auwal sa'id

Ummu Lateefah

Maryam T Baliya

Murjamashi

Fatima Bintu

Mmn Mubeen

Khadijah/mashi

Aneesat

Mrs A

Hussaina S Alsn







   Ina kusa da Auta Nawwar ya dawo ya kori Auta sit din baya shi ya zauna a kusa dani,Auta yace ni na huta ma matar taka da duk yawu gareta,nace Auta Inshaallah sai ka auri mace tana samun ciki kullum yawu da amai suna hanya yace ba Amin ba.

   Muna sauka Auta dama ya Kira abokinsa Afif shi ya dakko mota Nawwar yace wlh bazan shiga tukun wannan yaron ba yaje yayi hatsari da mu,nace dan Allah kayi hakuri muje ba abinda zai faru Auta Kuwa har ya Shiga gaban mota ya kame,da kyar Nawwar ya yarda Muka shiga baya,Auta Wayar Omaira ya kira ta daga,yace ke gamu nan mun shigo gari Ina ne gidan naku Omaira ta musu kwatance,Umma da sauran Yan Uwa kaf an taru ana jira a gani wacece ake tunanin jaririyar da ta bata oho,Abba Yana zaune a kusa da Uwa Babarsa suna cewa wallahi baza su kawo tsintacciya a hada jininmu da ita ba ace wata Yar uwa ce bazai yuwu ba,Abba yace yanzu haka ma irin Kama ce da Allah yake halittar bayinsa da ita zamu gani ai,su Bilkisu da Umma duk suna Palo a zaune suna jira,Omaira kafin mu karaso ta fito kofar gidansu wani ginin bulon siminti tsoho tukuf da shi dama unguwar tasu gata ga irinta,Nawwar Yana ganin Omaira yace gaskiya jininku ce wannan ba sai an tambaya ba ma,Omaira ta rike kugu a kofar gida tana tsaye sanye cikin riga da wando ta dora hijab maroon ya wuce gwiwarta, suna parking Nawwar ya fito ta bishi da kallo tace tace amma daga madagaska kake ko bawan Allah,Nawwar Bai shirya dariya ba sai da yayi yace a'a daga Masadonia nake,Miracle ya zaga ya budewa kofa,Omaira tace hamshakiya mandiya kofar ma Sai an bude Mata,Kafar Miracle Omaira tabi da kallo Tasha takalmi me tsada da tsini ta fito sanye ciki wani danyen leshi me tsada Golden and White jaka da takalmi da mayafin Golden tayi kyau na mamaki sai kamshi suke na musamman,Auta ya fito tuni ya harde hannaye a kirji Yana jingine jikin mota anyi tsaiwar samari,Jakar Miracle Nawwar ya daukar mata Wai baza ma ta rike jaka ba,Omaira tace sannu Alhaji Bawa sunan wani wai Bawa to ai da Kai aka sawa sunan ma,Auta Murmushi yayi,Miracle tace ke dan Allah kin ishe mu ki Kai mu gida sai shegiyar magana.


    Omaira gaba tayi tace ku biyoni a bayana suna tafiya tana juyowa tana kallonsu tana sake juyowa ni Miracle na Mata ambola nace kanwar uwarki,Omaira ta juya tana dariya Suka shiga gidan ta kwala Sallama Salamu Alaykum Umma ga yarki marar mutunci ta zo,Nace Mijin uwarki ke Omaira kike ko wa nace Mijin uwarki,tace ai an saki Umma bata da miji Nace to tsohon mijin uwarki,Abba yana zaune ya saki baki yace Kai na yarda wannan 'yata ce babu tantama,Uwa Mahaifiyar Abba tace gayyar tsiya naji mace daga zuwa sai zagi kana zaune tana zaginka,yace ai bata San nine ubanta ba shi yasa duk yarana basa ci min mutunci suna daraja ni banda Cele kam Yar banza me Kai Kamar murhu,Kallon Abba nayi nace Sannunku ya amsa sama Sama,Uwa Kuwa ko kallona bata Yi ba Kawai Nawwar suke kallo suna washe Masa baki sunga me kudi,Uwa harda tashi ta jawo tabarma sabuwa ta shimfidawa Nawwar tana zauna,ta kalli Auta tace Dan Samari Zauna,Auta a ransa yace kin taimaki kanki da Kika ce samari baki ce yaro ba,Zama Suka Yi Abba Yana ta jera musu sannunku da zuwa sannunku,Uwa tana lale marhabin marhabin lale lale ta kwalawa Rahma Kira tace kawo musu ruwa mana,Ni Kuwa mamaki ya kamani ni sunki kulani Amma Nawwar da 

Auta shi Kamar sune Yan uwansu,Abba yace Allah ya muku Albarka babarku tayi farar haihuwa gaku maza Kuma gaku Kuna Kama da alama dai wa da kani ne,Auta yace ae nine kanin shi wannan yayana amma da kadan ya girmeni Wai Nawwar ne ya girme shi da kadan shi da matan ma su Sultana sun girme shi aure kawai za a musu sun girma,domin su sun shiga University tuni ma,Auta ya kalli Rahma a ransa yace wannan kwaila ce kirjinta ba komai sai tsayin kafa,Raheema ce ta fito itama ta gaida su Suka amsa Auta itam ya Kare Mata kallo sai kace munafuki a ransa yace wannan Daya tayi Mata kwari ta tsunbure baza ta girma da wuri ba kafin ta murmure za a dade itama dai kirjin ba komai kamar faifai ita kanta nonon take bukata a shayar da ita Ina zata Iya shayar da kamata Ina,Nawwar Yana kallon abinda Auta yake Yi na kallon matan hararar Auta yayi,da sauri  yayi kasa da Kai da sauri.


   Ni Kuwa Ina Shiga Bilkisu Babba tace Masha Allah wannan twin din Cele ce gaskiya sun zuba min Ido suna kallon suturata da irin kyan da na tsula kudi basa buya idan akwai su,baki na zumburo nace sannunku,Suka amsa da yawwa,Umma na kalla cikin doguwar rigar atamfarta me kyau kamar Yar balarabiya,na durkusa a gabanta nace Ina kwana tana Murmushi ta amsa ta rike hannuna tace ga Yan uwanki ki gaida su, yayyenki ne na juya na gaishe su su Rahma Suka gaishe ni,Omaira ma ta gaishe ni,nace Ina wacce naga hotonta a kasko tana suya? dariya Suka Yi Suka ce Yar jarfa kenan Cele a kasko kenan sunanta Rufaida ana ce Mata Cele Amma fa Cele a kasko ita Yan biyunki ce tare aka haife ku itama ba anan gidan ta taso ba,nace mijina Yana tsakar gida,Aunty Bilki tace ai ya Zama dan gida ya shugo Kawai ayi labarin a gabansa,Nawwar na Kira nace ku shigo,Abba da Uwa Suka tabe baki yace maza da Shiga cikin Mata jeka kuje Kar ace Ina bakin ciki,Nawwar ya mike da Auta tuni kamshinsa ya cika ko Ina yayi sallama ya shigo palon Kato ne,Su Aunty ne Suka tashi suka bashi doguwar kujera shi da Auta Suka zauna.


    A kasa ya zube ya gaida Umma da su Aunty ma sauran ma suka gaida shi,bayan ya zauna aka kawo Mana ruwa da lemon da su Aunty Bilki Suka siyo Bilkisu ta fita ta shiga kitchen sune suka Yi girki aka kawo mana tuwon shinkafa danya miyar egusi sai meet pie me kyau, nace mun fa koshi,Aunty Bilkisu sai bala'i ai ba sai kin nuna mana mu talakawa bane dama ai mun San bamu Kai kici abincinmu ba kunfi karfinsa amma dai ke in baza kici ba ai su zasu ci,aikin banza duk Dan gidan nan inda yake sai ya nuna hali haba,Baki na bude nace ni daga nace na koshi sai ki kamani da fada haifata Kika yi,ciki ne dani ko baki gani ba abinci sai mai da yaji nake ci gashi Nan me cikin ki tambaye shi kiji,Nawwar yace kuyi hakuri bata cin abinci sai mai da yaji,Umma tace ko kunya babu Rabi kike ko,cikin shine abin kunya ni da ba shege nayi ba da ubansa kowa yasan dai me akeyi a samu ai aure nayi,Nawwar shi Kuma yace ae da auren mu Umma,su basu Saba Jin rashin kunya haka ba da tarbiyyarsu Kuma a Arewa suke da saukin fitsara sannan a gaban Mahaifiyarsu Suka taso,Bilkisu ta share zancen tace amma ai kwana zakuyi ko? Nace a'a Ina Zan iya kwana gashi nan ku tambaye shi idan zai yarda to bai Saba barina unguwar kwana ba na tafi na barshi da wa da dare fa a'a bazan kwana ba nikam, Umma tace ke a hannun wa Kika taso ne haka Rabi baki da kunya haka,Baki na turo nace ni nace ku jefar dani da Kun San da haka kuka jefar dani sai yanzu an ganni na girma na zama abar moriya za ace bani da kunya tuntuni ba sai a rikeni a bani kunyar ba,shi waccen mutumin me Jin haushina waye ne haka,Umma tace babanku ne mahaifi,nace Ni ku bani labari na sani nice yarku ko ba ni bace,Umma Ido ta tsura min ta fara bamu labarin asalinmu.


    Tace Mahaifinku dan Asalin Nasarawa Lafiya ne a wani kauyen Fulani rugar Jam,Mahaifinsu da Mahaifiyarsu  Abu wacce ake Kira da Uwa su Tara Suka Haifa bakwai Mata biyu maza yanda ita kanta Abu Uwa kenan dukkan Iyayenta Mata Suka Haifa mutum Daya ne Namiji a ciki su hudu Mata namijj daya Kuma duk suna nan da rai ita Uwa itace Babba a cikin Yan uwanta sai Sa'ade,Baballe da Binta Uwa Kuma data yi aure danta daya tal ta Haifa a Duniya Muazu shine Mahaifinku Abba kenan tun yana matashi mahaifinsa ya rasu Bayan sun dawo Kaduna da Zama sakamakon fada da ya barke tsakanin Fulani da manoma gaba Daya kusan Dangin Mahaifinku suna nan Kaduna Wanda basuyi aure ba ma duk a nan suka Yi aure,Uwa ta Sha wahala da Danta sabo da bata da miji sai Yan Uwa ne suke taimakonta lokacin ma a gidan haya take,sabo da danta ta kasa yin aure Wai Kar ta auri wani mijin ya tsanar Mata da tunda mazan yanzu ba kowa ke son yayan wani ba,tana sana'oi kala kala da haka ta dauki nauyin Danta har ya gama Secondary sannan aka turashi makarantar Allo can Kano har ya Zama katon Saurayi Yana Almajirci ya samu wata Hajiya ta dauke shi Yana Mata aiken gida a can har ya Isa aure a wancan Zamanin kenan.

    

    Ni Kuwa Yar Asalin Taraba stare ce can Gembu kusa da Cameron Fulani ne usul ,iyayena ni kadai Suka Haifa tunda aka yayeni babana ya rasu sai Mamana Muna rayuwar mu nayi makaranta zuwa matakin secondary sai karatun Islamiyya Ina tallan fura da nono har kawar Mama tace tunda bamu da kudi Muna Shan wahalar Rayuwa me zai Hana a kaini gidan masu kudi wanke wanke da shara,Mama ta amince nima ita murna Zan zauna gidan masu kudi,Allah yayini da masifa kaf kauyenmu ba a taba ni a kwana lafiya bana yarda,aka samo min aikin wanke wanke da shara a Kano aka kaini gidan da Abbanku ke musu aike da wanki da guga,Hajiyar gidan da mijinta suna da mutunci matuka suna da dansu guda daya shine bashi da mutunci gashi suna ji da shi,lokacin ya so ya lalata min rayuwa Saura kadan ma yayi min fyade Allah ya kiyaye Abbanku ya kamashi ranar ya daku a wajen Muazu Almajirinsu duk da cewa kullum cikin fada muke da Abbanku Muna kishin juna shi Yana Dan aike ni Kuma nice me girki da gyaran gida.


   Dama gashi masifaffe nima masifaffiya har kokawa mukeyi dashi sabo da rayuwar yanzu da ta baya ba daya bace yanzu anfi lalacewa,Watarana idan Zan bashi abinci sai na zabo nama me tauri ko Kashi shi zan sa Masa yayi ta faman wahala da hakoransa ba zagin da baya min akan haka,idan Naga dama ma Sai naci Nawa na rage jagwalgwalona sai na dan gyara shi na Kai Masa a wulakance,Dariya Muka dinga Yi Ni da su Nawwar irin muguntar Umma data dinga hadawa Abba,taci gaba tace shima duk Sanda aka aikeni na fita to bazai bude min gate ba sai rana ta gasa ni na Sha wahalar gaske sannan zai bude min kofa Watarana ma Sai dai Hajiya taji ihu na tazo ta bude min,Watarana Ina wanki yazo ya kwaso min kayansa ya tsaya da bulala a kaina yace sai na wanke Masa shima ai ya girmeni,Ina wanki Yana tsula min bulala a gadon bayana ta Dole na wanke masa tunda shi Namiji ne ya fini karfi,Muna wannan zaman kullum fada tsakaninmu har na fada sonsa ban sani ba,shi kuwa dama bai damu dani ba duk masifa ta da rashin kunya na daina yi Masa ita sai dai kyautatawa tsakaninmu na Masa wanki abinci me Rai da lafiya,dake nice a kitchen din nama ma yafi me gidan ci da yawa duk shi nake kwashewa na bashi,ko Jollof nayi to Abbanku shi inda yafi Mai da dadi nan nake Fara kwashe masa,albashina ma idan na kaiwa Innata abinda ta dauka ta bani sai nazo na bawa Muazu kudin,ganin haka sai yace Yana so na sabo da yanda nake kyautata masa,Me gidan da nake yiwa aiki shine ya dauki nauyin bikinmu kaf danginsa da Uwa ma sai kaunata saukeyi sosai aka sa bikinmu da Muazu Wanda me gidan shine ya dauki nauyin komai,Kafin biki Kuma aka samu matsala dansa shine yayi yunkurin lalata min tarbiyyar sanadin dukan da Muazu ya Masa shine masu gidan Suka kore mu daga aiki gaba daya,Bikin ma yace ya fasa daukan nauyi,haka Dangin Abbanku da Nawa Suka dage aka samu aka yi Mana aure Muka zauna a gidan Haya Wanda mahaifiyarsa Uwa ta Kama Masa,bikina da shekara daya dai dai na haifo yata Bilkisu anan Kuwa kowa Yana so ana murna, ban Dade da haifar Bilkisu ba Mahaifiyata ta rasu itace kadai gatana Kuma ta Kare sai Yan Uwa haka a can Taraba, wata kazamar kwanika nayi kafin na Yaye Bilkisu sai na samu wani cikin a lokacin ma Uwa da Abba Basu damu ba sai da Suka ga na haifo yan biyu Nazifa da Nazira,daga nan suka fara guna guni Ina ta haifo musu mata tun Abba baya Jin zuga har ya Fara dauka yana yiwa yaran wulakanci,ana haka na samu ciki sai Suka Fara Allah dai yasa Namiji ne matan nan sun ishe mu,Uwa ba zagin da bata min ta Fara min habaici tace matan ma meye amfaninsu wasu ma Karshe su Zama Yan Iska, Ina girmamata sabo da uwar mijina ce Kamar uwata ce amma bata gani,tun Ina da ciki suke hada kai da Yan uwanta su fa wallahi yanzu baza su yarda a haifo musu Mata ba ehe,Ranar da na fara nakuda Ina Shan wahala Nakuda nake me tsawo Uwa tana kallona Ina wahala taki ko kulani,ciwo ya isheni na fito da rarrafe Ina hawaye nace dan Allah kisa a kaini asibiti,Uwa tace uban wa zaiyi asarar kudinsa ya kaiki asibiti ki haifo Masa mace babu me kaiki sai dai ki mutu,Kafafunta na rike Ina rokonta Ina kuka ta kwace kafafunta ta shige daki haka na koma dakina,Bilkisu lokacin suna Yara ba abinda zasu iya Yi min sai kuka suke na tura Bilkisu ta Kira min makwafciyar mu da muke mutunci wata dattijuwa itama bata nan ranar,Abbanku ne ya shige Uwa tace Wai matarka nakuda take wasu matan suna Kan Hanya,Fuska ya bata yace ai sai tayi ta haifar matan wlh ko ta Haifa bana so ni ba nawa bane ko barka Kar Wanda ya min ya juya ya fice, ana haka sai ga Dattijuwar Attine ta dawo daga unguwa Bilkisu taje ta kirata itace ta taimaka min har Allah yasa na haifo mace katuwa,tana yanke Mata cibi Uwa ta fado dakin lokacin wata Sabuwar nakudar ta taso min bana cikin hayyacina karfina ya kare ban San ma me nake Yi ba,Uwa ta kwace jaririyar ta zazzagi Attine ta fisge Yarinyar ta sakata cikin wani tsohon zani tace bama so wallahi Indai macece shike nan kullum mace mace Ina son jikokina maza a dinga haifo Mana mace sai kace gyada, Dana bazai kare a bauta ba ta fice da Yarinyar Attine tana rokonta tayi hakuri amma ko a jikinta mota ta Shige a yanda tace ita Kano taje ta jefar da yarinyar a wani kauye bata San ma kauyen ba,kafin ta dawo na haifo wata Yar tawa katuwa,bayan na dawo Hayyacina nace Attine yan biyu na Haifa Ina dayar? Attine tace Uwa ta kwace ta fice da ita, me yasa Kika bata Attine na fashe da kuka,kuka nake gashi bani da karfi a jikina da kyar Attine ta taimaka min nayi wanka da ruwan zafi aka gyara ko Ina Kal kal,Bilkisu na aika ta siyo min abinci naci Suma Suka ci,Attine ta wanke jaririya aka sa Mata sutura kuka nake an dauke min yata,Attine tana ta bani hakuri,Abba ya shigo yana zuwa ya shigo ya kafe Cele da Ido ya ja tsaki yace aikin banza aikin wofi,mene a mace in Banda ta dinga jawo maka magana gasu Nan Muna gani duk sun lalace sai fitsara,nace wasu ba amma ba nawa ba,yace nakin fin na wasu Suka yi wa yasan me nakin zasu Yi kika sani ma ko Yan bariki Kika haifa,Salati na saki nace wallahi ka cika jahili Kuma ka sani wannan Baki ka musu wallahi idan naji yarka ta Zama Yar bariki cewa zanyi Allah ya bada sa'a tunda tun a duniya ka musu baki,Tsaki ya ja yace to suyi mana dama tunda Kika haifi mace kin sani wata ma Sai tayi ciki a gabanki ya juya ya fice,nace ta Allah ba taka ba.


    Sai cikin dare Uwa ta dawo Babu yarinya,a lokacin na fito nace sai ta fito min da yata,ta zazzageni ni kuwa naci kwalarta na hadata da bango na shaketa a bango Muna haka Abba ya shugo ya kwaci uwarsa ya kifa min mari,Allah yasa dai bai sakeni ba,washe gari Uwa taci gaba da kawowa yata hari zata sace ta,har aka rada suna ko hakika bata Bari an yankawa Cele ba tace ai baza ayi asarar kudi ba,Mijin Attine Malam Jibrin shine ya bada ragonsa da yake kiwatawa aka yankawa Cele,dama su basu taba haihuwa ba,su Yara man ko macen nema suke Allah bai basu ba amma ga wani an bashi baya so shi,Cele taci suna Rufaida sabo da rashin kauna sunan ma Sai dai suce na sa duk sunan da Naga dama su basu damu ba,Yan uwan Uwa ma haka suke zuwa su fada min Maganar da Suka ga dama ban Isa Kuma nayi magana ba,Muazu kuma ga son mace bai da hakurin Jima'i amma Kuma baya so ace Ina da ciki,Rufaida tana da Sati biyu na shiga wanka itace na wanka ma Sai dai na siya da kudina idan Ina so na gasa jikina shi dai bada kudinsa ba,sabulu na manta na dawo daki Kawai nayi arba da Sa'ade kanwar Uwa zata sace min Rufaida ta goyata,riketa nayi Muka dinga kokawa Allah yasa Ina da karfi na dinga jibgarta da kanta ta kwance min yata Saura kadan ta jefar da ita a kasa na kwace abata na ajiyeta a Kan gado na Kama Sa'ade sai da na kusa kasheta a dakina da duka motsi sai data kasa,a ranar Kuma Uwa tasa danta ya sakeni nace ba inda zani Zama daram,Rufaida na dauke gaba Daya naje har gidan Malam Jibrin nace na basu Rufaida halak malak su rike min ita,suka dinga murna har danginsu ba irin godiyar da basuyi min ba, shi Kuma Abba yasa jaraba baza a bayar Masa da ya ba a dawo Masa da abarsa Kuma Uwa ce ta zuga shi sabo da so suke su sace ta,Malam Jibrin ganin ma Haka sai ya siyar da gidansa ya siyi wani a wata unguwar dama sana'arsa siyar da kayan miya,bayan na Basu Cele sai da na dade sanadin sakin kafin Muazu ya dawo dani dakinsa sannan yazo kuma Yana min naci nayi hakuri a sasanta naki yarda sai da ya Sha wahala sannan sabo da yarana na hakura aka maida auren domin na rigada na saudakar da farin cikina ga yarana sabo da dama wasu matan yawanci yanzu zaman yayansu suke yi.


    Bayan an maida aure sai da nayi shekara hudu sannan na samu ciki,Su Uwa Takaici ya ishe su suka ce sun San ma macece,haka na haifo macen Kuwa taci Suna Omaira,bayan shekaru uku na sake Haifo Yan biyu Kuma Rahama da Raheema Wanda dukkansu babu Wanda aka yankawa ragon suna.

   Cele Kuwa tunda ta shiga gidan Malam Jibrin suke gatata sai abinda take so ta taso cikin gata da Jin Dadi sabo da Attine ce take da zafin Nema komai ita kewa Cele,in banda Jan magana da masifa ba abinda Cele ta iya,sai da ta Isa Shiga makaranta Suka sata a primary tana karatunta tana gama primary Allah yayiwa Attine rasuwa tayi mutuwar farar daya,sabo da na basu Cele halak malak sai nace Kaka yasan yanda zaiyi da yarsa ya riketa Amana tasa ce,yayi murna Kuwa dalilin Cele ya sake auren wata bazawara ita kuma sai tazo tana gallazawa Cele azaba iri iri a wannan dalilin ya saketa ya sake auren wata itama dai ba irin wahalar da Cele bata Sha a hannunta ba dan ma Cele jajirtacciya ce,Watarana su Bilkisu idan zasu je su shigar Mata hanasu nakeyi nace ba ruwansu na rigada na bayar da ita,sabo da Haka ake son kyautar yaro idan ka bada to ka bada shi tsakani da Allah ba ruwanka da shishigi wajen marikinsa,sabo da yanzu abinda wasu keyi sai su baka dansu amma Kuma a sa ma Ido ana bin diddigi Yaya kake rike shi,duk abinda kake Masa ba'a gani sai ace kana zaluntarsa ba dama ka Masa fada idan yayi laifi uwarsa ko danginsa na uwa da uba duk sa Ido suna Munafunce munafunce amma idan danka ne ko kashe shi zaka yi babu me magana Dan riko Kuwa shi Kansa kana Masa amma baya gani tunaninsa Kawai zaluntarsa akeyi aike ko aiki baza ka sa yaro ba sai ace ka takura masa,ko uwar yaron suyi ta munafunci suna zuga yaron sai kaga yaro ya Raina marikansa Yana musu wulakanci iri iri.


    Nidai nasan dukkan Yan uwan Cele suna makaranta amma Kaka Malam Jibrin bashi da kudi da kyar ma suke ci su Sha Watarana ma Ina aika musu da abinci dama Attine ce me Neman kudin shi nasa sana'ar bata kirki bace Kuma ya tsufa,baya so a takurawa Cele shi yasa ma ya saki matar tasa bai Kuma kara aure ba daga shi sai Cele har ta Zama budurwa,batayi secondary ba ni Kuma banyi shishigi ba nayi Kara Kar Kaka yace na nuna ya gaza, duk yarana babu me zafin Nema irin Cele babu kuma me jaraba da masifarta,tun tana karama take Sana'a iri iri Kaka Yana bata jari har ta Fara kosan siyarwa safe da yamma,da rana Kuma tayi fanke da miya,dama Kuma tun tana Karama tasan mune iyayenta tasan Yan uwanta ba a boye mata ba labarin komai ta sani,ganin Yan uwanta suna zuwa makaranta sai tazo duk da Abba baya kulata Kamar ba shi ya haife ta ba haka Uwa ma,haka Cele take zuwa tace dan Allah a sata a makarantar boko amma sai dai ma ya daddaketa ya koreta Yana zaginta,Uwa ma haka tun tana hakuri har ta daina kyale su,in tazo gaishe ni ma Sai ya koreta yace ke tafi gidanku Yana kyararta,Uwa ma Haka take hantararta,inyi ta kuka ita kuwa Cele Allah ya bata jarumta bata damuwa,Watarana tazo gaisheni da yamma ta iske Abba a waje ya tareta yace ke gidan ubanwa Zaki shiga tace gidan Ubana,yace to baza ki shiga ba tace sai na shiga ko Kai baka Isa ba,baki ya rike yace ni din ? tace Kai waye ai ba ubana bane kai Allah ya kiyaye ace Kaine ka haifeni,yace to uwarki cikin Shege tayi ta sameki,tace ae ai gwara Yar shege ta tafi zata shiga gidan ya rukota Cele tace ita kuma sai ta shiga ya Kama yarsa da kokawa Suka dinga kokawa da Cele Kamar sa'arsa sai da ta shiga gidan Uwa ta samu a Hanya ta dauketa ta kaita cikin toilet ta jefata a ciki ta fito abinta.


    A haka Cele ta Raina su kullum tazo fadansu baya karewa ita Kuma baza ta kyale su ba data sake girma ma idan tazo duk inda taga Uwa to idan Uwa bata gudu ba sai ta dauketa tayi waje da ita ta ajiyeta a wajen ta kulle kofar gidan sai Sanda ta Gama abinda takeyi zata fita sannan Uwa ta shigo,wanka Cele  bata Isa tayi a gidan ba sai sun ci Mata mutunci shi yasa itama bata daga musu kafa gashi bata taso tare da su ba Babu wannan shakuwar kuma ma su ba Wanda suka kyale a yaran sabo da Mata ne su, Ni Kuma tunda Suka girma sune farin cikina su suke min komai haka Cele Yar Albarka Sana'ar nan tata kusan kullum sai ta kawo min kudin kashewa,sabulun wanka sabulun wanki omo duk suna tafe zata kawo,Yan uwanta ma Slifas ma tana siya musu har Uniform ta Sha dinka musu na school da kudin sana'arta ta min dinki bazai irgu ba,da tazo taga ba abinci a gidan zata Aiko min da su taliya Yar macaroni ko ba yawa Yar shinkafa kwano daya biyu haka,har su Bilkisu kafin su gama secondary sai data biya musu Rabin kudin waec da kudin da take sawa a asusu sauran Kuma na cika tunda Ina sana'ar Alala da kunu nima.


   Ko ni Cele ban Isa da ita ba Matukar akan su Abba ne,Uwa dai itace ta sa Muazu ya sake sakina,Yana sakina Cele ta shigar da Kara Kotu akan Uwa tace sai na bar gidan,Muka je kotu aka zube zance Alkali yayi Nasiha ya jawowa Uwa da danta Aya da hadisi ya fada musu Allah sannan yazo ya musu fata fata yace ba inda zanje,Cele tace to azo a nunawa uwar mu wajen zamanta,Alkali yazo da shedu ya ware min dakina biyu da Palo da bedroom Dole Su Uwa badan sun so ba nake zaune a gidan,Cele ita ko da yan uwanta basa Zama lafiya Sabo da idan tayiwa Abba rashin kunya Su kan Mata fada sai ta hada dasu karshe ma ta tsani kowa tace duk bamu da hankali bamu san me muke ba bamu San yancin mu ba,ta daina zuwa gaishe ni amma duk da Haka tana aiko min kudin da sauran abubuwa,aka zo bikin Bilkisu Cele kayan kitchen da yawa ita tayi su ashe tunda aka sa bikin take tari ta sake dagewa da Sana'a badan cele ba da munji kunya a bikin Bilkisu Kuma ko bikin bata zo ba ,Bilkisu ta auri mijinta Yaseeer,har gida naje wajenta taki kulani sai da Kaka ya sa baki sannan ta kulani,Dariya Muka Yi har su Nawwar, Bayan shekara itama Nazifa da Nazira Suka samu Miji amma duk har na Bilkisu basu da karfi talakawa ne,Nazifa mijinta Usman,Nazira kuma Ishaq, suma dai sai rufin asirin Allah amma suna zaune lafiya.

   Cele da tace zata tafi Saudiyya Neman kudi babu yanda banyi da ita ba tace sai taje ai da bama sonta bayar da ita muka Yi kyauta sabo da ba a kaunarta sabo da Haka ita ta gaji da takaici tafiyarsu zasuyi ita da Kaka,Shima Kaka biye mata yake idan tana neman kudi to girki ma shi yake musu ta hanashi Neman kudi tace ita zata dinga yi shi Kawai ya dinga girki Kaka ya Zama shine macen ita Cele itace Namijin,amma ke Rabi Uwa itace ta jefar da ke koma Ina ta kaiki ta fimu sani.

   Nawwar ne yace a kirata,Omaira ta fita ta Kira Uwa da Abba suna tattabe baki Suka shugo, badan Nawwar ba ma baza su shugo ba,waje aka basu Suka zauna Nawwar yace Uwa dan Allah Sanda Kika dauke Yar uwar Cele Rufaida Ina Kika kaita,Uwa tace na manta memory na kwakwalwata ya goge lokacin bana iya tunawa kasan tsufa,Ni miracle Nace karki Raina mana hankali ki fada mana bamu da lokacin saurarar zancenki,Abba ya min tsawa yace ki kula ba a taba min Uwa,Uwa ta fashe da kuka tace kowa sai ya zageni tana matse hawaye,Miracle tace wannan kukan fa sai kace kinyi Zina ance za a jefe ki kinga wallahi Wallahi tun wuri ki Fadi gaskiya kafin na ebo Miki gayya guda su tara Miki gajiya ni kadai ma na isheki kafin nazo Miki da gayyata wallahi ba abin kunya bane in Miki zigidir, Uwa tace ni din? Ke dinfa kin San gwagwarmaryar dana Yi Kuwa,to bazan fada ba ki sa kaina gabas ki yanka ni dan ubanki,badai ubana ba,sai dai Nawa? Naki cewar Rabi,Uwa ta fashe da kuka,nace tabara idan ban ruguje Miki Baki ba shegiya nake kaji mata,Abba yaga Nawwar me kudi yayi mukus,Nawwar ne yayi magana yace Kinga dan Allah ki fada mana wannan kiyayayar ta Isa haka,shegu kudi me kudi ya sa baki Uwa tace dan Ina ganin mutuncinka ne Kawai a can kauyen Ungoggo naje na ajiyeta a jikin wani masallaci na dawo gida ta fadi sunan garin su Dagaci.


     Na kalleta nace Amma ban taba ganin marar Imani irinki ba Kuma wallahi sai Allah ya saka mana,ko a gidanku ana iya kera ko hanci ne bare mutum sabo da Kawai Allah yayo mu Mata,ke mecece ai sai ki canja kanki ki koma namiji,ki kerawa kanki Antenar maza kawai ki saka ki koma namiji,ke me yasa kika zo a mace? Da nasan haka kuke da wallahi da zuga guda zanzo muku su tara Miki gajiya,Ni dama ban sanku ba ke da Wanda Zan wuce a kwararo duk daya bare na daga Miki kafa,Ina ma na sanku da wuri Kuna yiwa Umma haka sai na kawo wani ya dirka Miki ciki,Uwa ta bude baki tace ku kashe ni ku huta,Nace Inshaallah bakin cikinmu sai ya kashe ki azzaluma,Kai Abba baka Yi dacen uwa ba wallahi bata kaunarka sam tunda bata son jininka,Jahila ce Kawai kaima ka biye mata,mu da Allah ya Mana baiwa masu tausayi  da Jin kai,ka raine mu ka bamu tarbiyya karshe mu Zama sanadin shigarka Aljana duk abinda Allah ya lissafa akan niimar mace baka ji Ina almajirantar taka take ko ba karatun kayi bane aikin gadi kayi a gidan Hajiya,dama wasu almajiran kaga sun Dade shekara da shekaru ko izu biyar Basu haddace ba sai yawon bara da iya shege kala kala,ni na taba Jin ma irinku sai kace Wanda aka haifo ku ana dura ashar babu Bismillah,Uwa na nuna da hannu nace duk yanda akayi lokacin da za samu cikinki Oven din da za a shiga shedan ne ya Fara shiga sannan baban Suka dinga gwamutse da Shedan Yana Jin dadi shedan ma na ji ta ta Zaki Yi Imani.


    Umma ce ta bige min baki tace Kinga bamu labarin naki bana son fitsara,Zama nayi na dinga Basu labarina kaf komai da komai ban boye musu komai ba,Umma tace wannan barikin da Kika je bakin babanku ne gashi nan bazan ce komai ba wlh shi yace Yan bariki na Haifa a haihuwarki da Cele,ya kalli Cele tana jaririya yace sai tayi cikin Shege a gabana Kuma Allah ya taimakeni yaga zuciyata da zuciyarku Babu Wanda ya lalace Cele tafi kowa taka tsantsan da kame kanta nasan duk inda taje ba abinda zai same ta akwai kamewa.


    Uwa da Abba ne Suka tashi suna bata rai suna tsaki Suka fice suna cewa ayi mu gani ko a jikinsu Babu alamun nadama,Kallon Umma nayi da Yan Uwana nace ya Naga bakuyi min kuka bane Kun gama Jin labarina a banza ai ya kamata kuzo ku rungumeni kowa ta fashe da kuka Yan Uwa sun hadu Yar uwarku ta dawo amma kunyi kiyau miyau har Umma ma Ni baza ayi kukan ganina ba,Dariya sukayi Suka ce tab ai mu a jajirce muke ba komai ke bamu kuka ba,Kawai Dan mun ganki sai mu Fara kuka sabo da me,Nawwar ya kalli Auta shi tuwonsa yake ci ma Yana Shan lemo ba abinda ya dame shi,yace Kai sai ci ka iya ana ta labari kana nan,yace to labarin dogo yunwa nake ji,Aunty Bilki tace a'a kyale shi, Auta yace Yaya ka bar Aunty tayi ko kwana biyar ne,Nawwar yace to in tana so ta zauna,nace dama ka gaji dani daga tambaya sai kace to ai shike nan wlh zaka ga tsiya,Auta yayi dariya yace to ke ba a iya miki shike nan ki taho mu tafi tunda bakya son Umman taki, Nawwar yace zamu Zo dasu Mami sai mu koma tare ai,Auta yace Zan zauna Nima,Nawwar yace a Ina zaka kwana to yace a dakin su Omaira su bani gadon su koma kasa su sai su kwanta ni ba ruwana da mace yaro ne ni haka kuka ce,Omaira tace Allah ya kiyaye,Auta yace haba kawata harda ke,tace sai dai a kaika shagon Sagiru gashi nan makwafcinmu,yace ae a kaini Zan zauna akwai toilet hadaddiya bana son kazanta ni a unguwa sabo da toilet ba ko Ina nake kwana ba,Raheemah tace gidan su Sagiru me kyau ne ko Ina tiles dakinsa ma me kyau da toilet dinsa,ai kune kuka ce shago sai kuce dakin Sagiru,Rahma tace kuma Yana da tsafta Kamar mace,Auta yace ku fadawa Sagiru abokinsa ya zo, dariya Suka kwashe da ita,Nawwar yace Wai a Nan zaka kwana karya kake yanda Muka zo Haka zamu koma idan zamu Zo da su Mami ka dawo,Umma tace ka kyale shi Mana tunda Yana so,Nawwar yasan Auta Yan matan da ya gani ne ya makale sai ya zauna shima ba yanda ya iya da shi haka Suka Kira Afif zai maida Nawwar Airport, Nawwar ya bawa Umma dubu dari,dubu dari ya bawa su Bilkisu yace su raba ba yawa kafin nan gaba suna ta godiya,a gabansu na rike Masa hannu Muka fito tsakar gida zai bawa Uwa nace wlh kana bata munyi fada kasan da ya kamata Zan sa ka bata da ita da Abba ko kwabo sai uwata ta jika tukun muje na tura shi ta baya nace muje muje,dariya yayi yace Umma fa tana kallonki zasu ce bamu da kunya,nace muje ni dai,Uwa taga samu taga Rashi a gabanta na Hana a bata ko sisi wani Takaici ya sake kamata,Muka fito yace Abba fa nace Ina bazai ci kudina ba ai cewa Suka Yi basa son Mata,shiga mota please na bude Masa gaban mota ya shiga yace sai munyi waya,nace Bye yace I will miss you,me too My love su Bikisu suna Masa Allah kiyaye Auta yazo yace Yaya banzo da kudi ba ka bani kudi,yace bazan bayar ba,Yaya nifa na gano maka Dangin matarka shine kake min Haka,Zan maka transfer yace ni cash zaka bani, yace Auta baka ji wlh ya zaro kudi ya bashi yace Yaya Dubu ashirin kacal da me zanyi chilling a garin nan Ina fa da abokai,Nawwar yace muje Afif,Suka tafi aka bar Auta a wajen ya Kira Baffa ya tura Masa kudi ta account Kuma ya tura Masa,yasan Mami baza ta bashi ba ma.


    Ciki Muka koma da Auta nace Kai da kake da abokai ma Kar dai su dauke Mana Kai,yace ai Ni yanazi nan nazo ba wajensu ba zadai su zo muje yawo ya kalli Raheemah yace kece kadai karama a gidan Nan ba tsayi ba kiba sai kace kece Cele da baki Sha nono na sati biyu bama ga Cele a hoto ma katuwa ita da Bata Sha nono bama ke kin Sha na shekara biyu amma sai kace me cutar yunwa gaskiya kiyi tsayi da Yar kiba haba,Raheema tayi dariya tace Rahma ce ta min kwari ance itace ta kwace girman,yace to ke Rahma ki dawo Mata da nata ku raba biyu,Umma tayi dariya tace Kuma ita aka fara haifa,Na jawo tuwon gaban Auta nace ku bani Mai da yaji,Umma tace ki bari a Miki wani abin mana Raheemah dafa mata wani abin,Nace ayi min danwake,Umma tace to ai Kuwa Babu kayan yi zo ki karbi kudi ki siyo nace a'a akwai kudi na zuge jaka aka bawa Omaira ta taje ta siyo,Muna ta hira Ina Basu labarin kawayena su Star da gidan su Nawwar a hankali Ina ta karasa musu labarina,sai magriba Muka Yi Sallah Auta tuni ya fice yawo da abokai sun dauke shi a mota.


    Sai Bayan Sallar Isha masu auren Suka tafi gidajensu sabo da Bilkisu yaranta biyu duka maza,Nazifa mace,Nazira ma namiji,Sai wurin 9pm Muna hira Auta ya shigo yayi sallama nace Auta Dadi aka siyo min naga leda,yace Yaya ne yace fa a siyo Miki kaya baki zo da Kaya ba ya Mika min naga dogayen riguna guda Uku masu kyau nace dama gobe nake cewa Zan siyo ko kala biyu ne kayan Omaira sun min kadan na Umma sun min yawa,dama Zanin Umma na daura da t-shirt,nace shi ya fada ma size din? Yace ae ya Mika min Daya ledar ta take away na kaji da Yogourt da lemo yace na Umma ne na siya mata ba naki bane karki Fara murna,Umma tace an gode dan Albarka,Omaira ce ta raka Auta gidan su Sagiru dama sun gayawa Sagiru,Suna Hanya Auta Yana bayanta Yana Kare Mata kallo.


     Cele Fitowa tayi ta a fusace tana hawaye cike da bacin rai ta nuna Maheerah da Yatsa tace Ittaqillah dan kutmar....ta tafi Kamar walkiya Maheerah ta zaci wajenta ta nufo tace bari na Fara cin uban Uwarki me warin tafarnuwwa tukun tayi wani mugun tafiya da Babar Maheera Kamar guguwa ta hada kanta da bango,ji kake kummm ta shaketa ta dinga jijigata ta jefar da ita a kasa,Maheera zata gudu tayi kanta Ahsan ya riko Cele ta juyo ta Kai Masa duka ya saketa ba shiri ta damko Maheerah ta gwarata da bango nan take ta Fadi ta sume sabo da kanta ya bugu Kuma cele bata hakura ba ta haye ruwan cikin ta tana dukanta baban Maheerah yazo zai masge Cele Ahsan ya rike hannunsa da sauri cikin larabci yace karka sake ka taba ta dashen ciki tayi mata ba izininta kuma budurwa ce bata San Namiji ba Kuma kudin Dana bata ko kwandala bata bata ba ai zalunci ne wannan, Baban Maheerah ya fisge hannunsa yace sai me akan anyi Mata dashen ciki wasu ma suke zuwa suna karuwanci su haihu bare dashen ciki,ita wacece bakar fata da ita bayi,Cele tashi tayi daga Kan Maheerah ta shatulo kafafun Baban Maheerah dake banbamin masifa ya Fadi kasa tim yaji targade a kafarsa, Ahsan ne ya rike ta ganin duk ta haukace tana ta kuka tana kwacewa tana fisgewa taga Babar Maheerah ta tashi Zata sake masgeta ya riketa sosai Yana lallashinta ya rungumeta sosai a jikinsa yana lallashinta,Kansa ya Dora a dokin wuyanta yana lallashinta Yana Bata hakuri,Babar Maheerah ruwa ta samo ta kwarawa yarta ta farfado Suka tashi jiki ba kwari da kyar Baban Maheera ya iya tashi Suka mike a gigice Suka bar gidan gaba daya.

 

   Ahsan sai da ya lallashi Cele ta dan daina kukan sannan ya shirya ya rubuta takardar saki ya tafi gidan su Maheerah zai Kai misu,Yana tafiya kuma Cele ta tattara nata ya nata kaf ta Masa rubutu da hausa normal ta ajiye a kujera, ta shiga dakinsa ta Bude inda yake ajiye kudade ta iba zasu Kai dubu dari uku a nan Nigeria tayi tafiyarta ta bar gidan,tana Fitowa Mota ta shiga taxi tace a kaita garin Makkah tasan acan Inshaallah zata hadu da hausawa Kuma  Nigeria zata dawo baza ta zauna a Saudiya ba ta Gama Zama a Saudiya har abada, so take tana zuwa ta samu me wuce Mata gaba ta dawo Nigeria ko taga Kaka ko Bata ganshi.


    Mairo Kuwa watan yarta biyar a duniya baza ma ta bari ta yaye ba akace ga wani balarabe amadina yake zaune bakar fata yake Neman Dan yemen ne zai biya kudi harda sarkar Gold,nan take tace ta yarda Indai zai aureta da yarta,shi dama Local government Kawai yake nema yace ba matsala ya biya kudi aka daura auren Mairo da Mahmud tsohon mijin Mami data Aura ta gudu shi Mairo take rawar kafa zata aura ance me kudi ne zata samu arziki,aka daura aure yau ango yazo ya dauki Amaryarsa da Kansa Yana zumudi ya samu sabo jini.



Ina godiya MRS CHIEF

No comments