Breaking News

Yar Aikin Karuwai Book 1 Page 71-75

    71-75





Official


By

AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA





*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_

 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


_nfection_

_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_


_Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._

*08089965176*

*07084653262*




Page naku ne 


Maman Hibbat

Ummu Zee

Murjamashi

Ummy

Maman Zahra

Maman Walida

Mom Khalisat

Ummee

Beauty Zahra

Aminaidriskafe

Ummu Afnan

Mufeedart

Jagabanyakubu

Samira Haru Batir

Manaajahooh



Gaisuwata ga

Maman Samha

         






        Direct gidanmu na nufa Ina zuwa dakin Sera na nufa sai gani na tayi na fado dakin Ina kuka,saman katifar mu na fada Ina cin uban kuka,Sera tace Wai lafiya nifa bana son irin wannan Iskancin,me aka Miki? hawayena na goge nace ki Kira wise da star munfi kusa na muku bayani,Wise ce ta shigo da sigari a hannunta tana Sha,Star kuwa codeine take kurba Kamar me Shan lemo ta zauna itama tace ke lafiya Miracle kike kuka haka,a nutse na basu labarin komai karshe nace ni bana so mijina ya sakeni shi yasa na gudo,Wise tace tab wannan bazai wuce aikin kishiya ba idan itace ma zata Yi bayani da kanta ta tabo bala'i ta jawa kanta,Star ta furta yanzu bai baki takarda ba baza ki zauna a nan ba duk tsiya aure Yana da daraja ga mu da muke kaunarki da gaskiya tashi mu tafi na kaiki gidan wata kawata ce, babbar mace ce Bata da aure mijinta ya mutu ya bar Mata dukiya na taba taimaka Mata lokacin da motarta ta samu matsala a daji Hanya zata je arewa shine dalilin haduwar mu tayi tayi na daina karuwanci na koma gidanta zata rike ni naki yarda muje can ki zauna ko Nawwar yazo mu Kuma zamu ce baki zo nan ba gudun Kar ma ya ganki ya sakeki,dariya Sera tayi tace wato Miracle kice gudun saki ne ya fito dake tun kafin ya dankara miki saki? Nace ae Suka kwashe da dariya,nace ba Maganar Wasa bace wannan tam Ina zumbura baki,Sera tace ga abinci nan yanzu na dafa sai ki ci ki tashi ku tafi, dama yunwa nake ji naci na koshi Muka fito ni,Sera,wise da Star muka tafi can wajen Matar me suna Hajiya Abida, Muna zuwa ta karbe mu da murna gida ne hadadde me kyau da motocinta biyu tana da Yara uku duk suna Arewa Bauchi a nan suke makaranta sabo da su samu tarbiyya ta addinin musulunci,gata da Yar aikinta mace daya,sai Namiji a bakin gate shi ke Mata wanki da guga da kula da gidan,gida ya Sha flowers da furniture masu kyau.

  

    Muna zuwa ta karrama mu sosai aka kawo Mana kayan motsa baki,sai da Muka danyi hira da ita sannan Star tace Hajiya Yar uwata na kawo miki ajiya tana da aure sai ta fadawa Hajiya abinda ya faru dani a gidan Nawwar,Hajiya Abida ta tausaya tace bazai wuce sharrin kishiya ba so take a koreta Kuma ta Allah ba tata ba,da sauri na furta Inshaallah Ina nan da mijina mutu ka raba,na kalli Hajiya nace Ina son mijina sosai da ban damu da auren ba amma zuwana Makkah Allah ya amsa Addua ta yanzu bana sha'awar bariki ko kadan mijina da aurena sune a gabana,tallan duwawu na gama Inshaallah,Hajiya Abida tayi dariya ita kunya ma muke bata sabo da magana direct muke fada ba wani sakayawa,a nan gidan su Star suka barni, Suka koma gida Suka tattara mutanen gidan Wanda ake mutunci su Yar Zabil duk dai wanda suka je bikina suka zauna  sama katuwar tabarma guda biyu da alawoyi da yawa a leda suna zaune sunfi mutum ashirin,Santana yace dan Allah wai Kun taramu kunce akwai magana Yar uwarmu Miracle tana da matsala a gidan miji,Madula tace to me za muyi Mata itace ta Kai kanta in Banda Addua me zamuyi Mata,Seraline tace yawwa duk da mun San mu masu laifine a wajen Allah amma Addua itace zamu hadu muyi shi yasa na tara mu,wata me suna Destiny tare da Peace Wanda su arna ne dama Suka ce muma zamu Yi Mata irin tamu oya a fara.


     Seraline tace ni shugaba da na tara wannan taro zan Fara,Salati goma ga annabi,Mandula tace ya ma akeyi ku dan tuna min,Allahuma salli ala muhammadun wasallim na Fadi dai dai ko? Yar Zabil tace to Allah ya amsa hakane tana wani fari da Ido tana karairaya,Santana yace karami ne a salatin akwai na Ibrahimiyya shine darrr amma wannan yafi sauki Suka karanta,Seraline ta sake cewa suratul bakara kafa uku uku,Allah ya daidaita Miracle da mijinta Nawwar su dawo su jone su manne Kamar da,Allah ka duba kawar mu Miracle Kar ka bari Aurenta ya mutu Allah karka bari Nawwar ya saketa,ko wace ta hada Mata wannan tuggu Allanmu kayi fata fata da koma waye kayi raga raga da ko waye,kasa gobara ta kone dakin ko waye,Idan Sabreen ce Allah kasa duwawunta yayi tsutsa,su Kuma sauran suna cewa Ameen Seraline ta furta fatiha ta shafa tace wata tayi Mana itama,kowa a ciki yayi Miki Miki suna kallon kallo duk sun manta ma adinnin nasu sai sunyi tunanin yanda ake yi.


    Wise ta daga hannu sama tace Suratul Tauba kafa daya,ba Wanda ya iya har ita me fadar,Suratul bakara ma ko aya daya ba wacce ta iya fada bare Tauba,ai Kuwa bata jira ba itama taci gaba ta daga Kai sama da hannaye tace Ya Allah mun San mu masu laifi ne kullum sai munyi maka laifi ita kanta Miracle babu irin laifin da bata maka ba ta bada gabanta da baya duk har center an daki harka da ita yanzu ta tuba tayi aure tana son mijinta tana son aurenta,Ya Allah Muma gamu dai Muna ta siyar da local government dinmu masu laifi ne mu ya Allah ta Kara kwalawa da karfi ya Allah duk Dan iskan cikinmu Wanda baya ji Allah kayi daga daga damu...kowa baki ya bude yana kallon Wise tana jawo musu masifa duk cikin addua,Santana yace ke rufani ki sayani ke Wise min Shiga Uku,wise da taci gaba tace tunda munki ji gamu ya Allah kayi maganinmu Allah karka kalli laifinmu ka yafewa miracle ka yafe Mana karka bari Nawwar ya sake ka barta da mijinta ya Allah karshe tace Fatiha Alhmdllh an karba Addua ta karbu,Star ce itama ta daga hannu sama ana cewa Ameen tace Ya Allah Suka hada baki tare da furta Ameen,ta sake Furta Allanmu Suka ce Ameen wannan haka yake Allah ga bayinka,Star tace Allah Nawwar,Nawwar,Nawwar mijin Miracle zai saketa ya Allah karka bashi dama,Ya Allah ka sa Masa tausayin miracle da kaunarta Allah karka bashi damar sakin Yar uwar mu,Miracle tana son bawanka Allah karka bari a saketa kasa ya nemi matarsa miracle ta koma gidanta Allah kasa tana komawa ya Mata ciki ta haifo Yan biyu,Ameen Suka hada baki.


    Madula ce ta karbe Adduar da furta istingifari kafa dari,kowa ya Fara Astagafurillah har kafa dari dari Suka Yi abinsu sannan bata rokawa Rabin komai ba ta shafa tace Ameen,Santana ya karbe Yana cewa Allah ka daga gidan Nawwar kayi sama da shi ka kife shi a kasa ka hada da Sabreen din a juya kanta kasa a cake ta karairaye Allah karka kashe ta a barta ko Ina a karairaye shike nan ya Allah Suka furta Ameen,Manduwa tace Allah kasa mota ta kade Sabreen tayi Mata markaden kayan Miya a kwalta,Yar Zabil ta saki wakar kasida ta yabon manzo suna amsawa tayi baiti Daya suka Shafa da Ameen..Daya bayan daya kowa da Kalar adduar sa,Peace christain itace ta karba ta Fara wakar church sannan tace Papa God tana wani fari tace Jesus abeg ka taimaki Miracle mijinta ya maidata gidanta,we are all sinners kullum sai munyi zunubi Papa God ka taimaki Yar uwar mu Suka hada baki da Ameen,Peace ma wakar church tayi ta yabi Jesus sosai sannan tace Ameen a haka sai da kowa yayi adduarsa ya Gama sannan Sera ta bude Alawa chocolate me shegen dadi Suka rabawa junansu ko wacce guda biyar biyar Suka bare suna ta sha Wai Sadaka ce maganin masifa ,Suna haka Saurayin Seraline ya buga Mata waya yace ya dawo gari daga Dubai tazo zata Taya shi kwana daga nan ta kwashi kayanta sai hotel dinsa,Suma sauran haka duk sunyi Shirin tafiya aikinsu kamar ba sune Suka Gama Addua yanzu ba.


    Nawwar bai San na bar gidan bama,Bai neme ni ba gudun Kar ya yanke hukunci cikin fushi,kwana daya Shuru bai ga ko gilmawata Sabreen ma tayi mamaki bata ganni ba tace ko ya sakeni ne sai da ta duba ko Ina na gidan bana nan wani farin ciki ya kamata burinta ya cika tunda bata ganni ba tasan ma ya sakeni,Nan take ta Kira Jamcy tana bata labari tace ke aiki ya Kare ma mu kwanta mu huta ya saki shegiya,Jamcy a ranta tace Saura ke dan ubanki duk ku fita ku bani waje a gidan sannan na samu damar shigowa gidan.

    Wasa Wasa har kwana uku Nawwar bai ji ko motsi na ba,kasa daurewa yayi ya nufi dakina ya duba wayam,ko Ina sai da ya duba babu ni, wajen masu gadi yazo ya tambaya Suka ce oga ai tayi kwana uku da Muka ganta da akwati tana kuka ta bar gidan nan,hankalinsa tashi yayi yace to ni me nace Mata nayi magana ne da zata bar gida ya ja tsaki yace idan ta gaji ta dawo ya koma ciki amma me tunaninta sai ya hanashi sakat in banda Rabia babu abinda yake tunawa yace idan ta koma gidan jiya fa tsaki ya ja tare da furta to ni mene abin damuwa da ita tunda nasan ba sonta nake ba,ni kuwa har na Saba da Hajiya Abida Muna zaman mu girki ma tare da ni da Yar aiki muke yi na bata labarin ni Yar tsuntuwa ce taji tausayina, kullum Nawwar Yana raina in Banda tunaninsa bani da aikin yi,Ina tuna rayuwar mu tare da duk wani moment da muka Yi spending tare,yanda yake nuna min kulawa,yau ma bayan na gama komai dama wayata na kasheta gaba daya tunda na bar gidansa ban sake kunnawa ba,a saman bed dina nake kwance Ina tunaninsa ban San Sanda na Fara hawaye ba,a haka Hajiya Abida ta sameni,ta zauna ta taba kafata dan ban San ta shigo ba,a firgice na motsa na ganta,hawayena na goge a hankali,tace Rabiah yaushe Zaki daina kuka hakuri shi zakiyi Inshaallah zai neme ki,murmushin yake nayi har hakorin makana na Gold ya bayyana a hankali nace kina gani kwana na Uku su Sera sunce bai je Nema na ba Kinga Kawai ya kyaleni nayi rayuwata ya manta dani,Yana da Mata ba abinda ya dame shi dani, dama ba so na yake ba nice nake sonsa na rushe da kuka sosai,Hajiya Abida babu irin lallashin da bata min ba amma naki Shuru sai kyaleni tayi ta tafi.


      Nawwar kwanansa bakwai bacci sai barawo ya kwashe shi ala dole,a daddafe ya kwashe sati sati duk ya rame sabo da tunanina, Kuma ko Mami bata sani ba a wajen su Iyamami taji ya saki amarya su ma Sabreen ce ta basu labari sai Murna suke suna jifan Mami da babake maganganu har ta gaji yau Nawwar yazo da Yamma ta kalleshi Yana cin abinci tace Nawwar lafiya kuwa? Me Kika gani Mami? hmm tace a baya naga tunda kake tare da Rabiah baka cin abincina amma yanzu kullum anan kake cin abinci safe rana da dare,sannan baka da nutsuwa duk ka rame na rasa gane Kan abin sannan naji wajen su Iyamami suna min dariya Wai ka saki Rabia ta kawo kwarto gida,murmushin yake yayi yace ba haka bane Mami Kawai dan fada Muka Yi bata Jin maganata shine fa na Mata fada sai tayi yaji ta tafi ni Kuma banje na dawo da ita ba,Mami tace Kana da hankali Kuwa Nawwar ya zaka bar matarka ta tafi Kuma baka je ba,kuma kasan bata da kowa sai Yan duniya bariki dai zata koma tunda can ne gidan nasu,ashe karya kakeyi ba taimakon nata zaka Yi ba,Mami ita fa tayi tafiyarta,Nawwar baka da hankali gashi nan ka damu kana son Yarinyar nan kaki ganewa ne Kawai,Allah ya kiyaye ya furta, ni bana sonta Kuma bazan so ta ba ni na gaji ma bazan iya taimakon ba na fasa Kawai a bar zancen,Murmushi Mami tayi tace wai me tayi maka ne? yace ba sai kinji ba,tace to ai duk so ne gashi nan baka so aji laifinta Kar wani yayi tunanin wani abu a kanta anyway yanda ka gani koma mene Watarana zaka fada min ni dai na baka shawara ba dai dai bane baka saki matarka ba ka barta ta koma bariki ba Allah zai tambayeka.


     Shuru yayi ma Mami Yana cin abinci Yana tsaki har ya gama ya tashi ya fice ya bar gidan,layinmu na bariki ya nufa Yana zuwa ya samu Sera a waje,taje Suka gaisa tace Ina kawata? Kansa ya daure yace wacce kawar taki bayan satinta guda da yin yaji Kuma nasan nan zata zo,Sera tace bata zo ba gaskiya to Ina Kuwa Rabia zata tafi bata sanar min ba,Nawwar ya zaro Ido yace Wai da gaske kike ba nan tazo ba idan Wasa kike ma kin San dai bana Wasa dake, Sera tace tab ai kuwa ita tasan inda ta tafi bata nan gidan wlh,Nawwar yaga fa da gaske ne hankalinsa ya tashi matuka,yace kira Inna kiji ko can ta tafi,Inna aka kira tace bata je ba ko kauyen ma ba Wanda yaga Rabi a can,Nawwar ya rasa inda zai saka Kansa gashi an wuce sati Ina zai neme ta,haka ya koma gida jiki a sabule,Sabreen tana Shan kallonsa sai Dadi take ji burinta ya cika ga mijinta baya cikin farin ciki, Addua da sallar dare ya Fara ba ji ba gani,har aka sake kwashe sati shi kadai ya fara hawaye shi matarsa yake so,a Daren ya tafi wajen Mami sai ganinshi tayi duk ya fada Yana zuwa har da kwalla Ya shiga bawa Mami labarin komai da ya faru tsakaninsu karshe yace Ina ji a jikina akwai wani Abu a kasa gaskiya Rabia baza tayi haka ba shi yasa ban dauki mataki ba ita Kuma Kawai sai tayi tafiyarta ya karasa da marairaicewa yanzu Mami ya zanyi wallahi karya nakeyi Ina sonta ban taba son wata ba Kamar ta kawai na kasa yarda da ita ne ganin a inda na dakko ta farko,Mami dariya tayi sosai tace tun ba ayi nisa ba ka fadi gaskiya,Nawwar yace Mami kina dariya Allah ni Ina sonta bazan iya rayuwa ba sai da ita,Mami ta zuba Masa Ido tare da furta Nawwar In love Rabia ta ciri tuta,yanzu mafita daya kaje ka lallaba kawayenta zai wahala Basu san inda take ba,Mami kije wajensu zasu fi Jin maganarki please,ka bani number Sera din Kawai yace bani da ita,tace to bari na shirya muje da Kai yaji wani sanyi a ransa.


       Ni Kuwa zuwansa na farko Sera ta Kirani a Wayar Hajiya Abida ta fada min na dinga murna Ina murna farin ciki nake ji marar misaltuwa amma Jin Shuru bai koma ba naji na koma gidan jiya,Bayan Mami ta shirya har layin Suka je yaci sa'a ya hadu da Star, Bayan sun gaisa ta gaida Mami wacce ta fito ta jingina a jikin motar tana kallon barikin da yanayin mutanen Dake wajen,tace lallai wannan bariki ce ta kirki,Star ai Sera ta samu tace dan Allah kizo mijin Miracle sun zo da Maminsa,wlh tausayinsa nake ji naga Kamar shima ya rame irin Miracle mu hadasu Kawai ko dan halin da Miracle ke ciki,Seraline Fitowa tayi Suka zo wajen Mami bayan sun gaisa Mami tace dan Allah Saratu idan Kun San inda Rabia take ku fada mana kunga harka ce ta aure ba abin Wasa bane please,Star ce tace mun sani amma mufa gaskiya baza a dinga dukar Mana Yar uwa ba,miji ya dinga dukanta yana Mata wulakanci sabo da bata da gata ya sameta a bariki a bagas shike nan da me zata ji da kishiya ko da su Dagaci ko kuwa da halin Dangin miji zata ji ga kuma uwa uba miji haka Kawai wlh baza mu yarda ba idan ba a sonta a kyaleta mu Muna son a barmu, Nawwar ya harari Sera sai da tayi dariya ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa Kika ce baki sani ba,Sera tace tuba nake amma Kar a sake taba mana Yar uwa Suka shiga bayan mota har gidan Hajiya Abida mace me Kamala da mutunci,yayi farin ciki ganin ba a bariki ta zauna ba yaji wani Karin kaunarta a ransa,Suna shiga Haj Abida ta fito Suka gaisa shima Yana palon,tace shine mijin Rabia akace ae,tace Kai mashaallah tayi dace bari na kirawota tana dakinta,tana Shiga ta samu Ina bacci,Fitowa tayi tace ai bacci takeyi,Nawwar yace bari na ganta ya mike tare da shiga dakin Kawai kayana ya harhada a kwati ya fito da su ya saka a mota ya dawo har inda nake kwance ya daukeni Kamar jaririya ya kaini gaban mota ya ajiyeni,Sera tace su a nan zasu yini gidan Hajiya Abida,Mami tace wato mace tafi uwa ni sai dai na zauna a gidan baya tana dariya ta shiga ta zauna Ina ta baccina sanye nake cikin doguwar Riga marar nauyi ta yadi me santsi kaina da hula a Kai me kyau,Mami ya sauke a bakin gate tare da cewa thanks sai nazo,ciki ta shiga tana Masa tsiya,Yana Hawa titi Kamar Zan farka Kuma ban farka ba sabo da na tara bacci Kuma ni Ina da nauyin bacci sosai, a hankali yake tafiya gudun Kar na tashi


     A hankali na bude idona bacci bai sakeni ba gefena na kalla na hango Nawwar Kamar a mafarki na zaci mafarki nakeyi idona na murza sosai naga dai ba bacci nake Yi ba a hankali na furta Ina yini,Tsaki ya ja ya kalleni Kawai tare da maida Kansa ga tukinsa,nace baka sakeni ba dama? Kafadarsa na dafa nace Wai Kaine Nawwar ba mafarki nake Yi ba? Shuru bai kulani ba,na sake cewa Wai kaina so nane da yawa haka baka Fushi da ni,Nawwar ne kuwa? Fuskarsa na leka tare da furta Nawwaru...Muka dinga Addua a kanka rabona da nayi Addua tun a Makkah sai da na bar gidanka,su Seraline Suka dinga taruwa irin yanda ake adduar rokon ruwa suna ta Mana Addua zo kaga yanda fuskar mu ke kyallin musulunci sabo da tsabar Addua wani haske goshin mu yayi na musulunci su Seraline Suka Yi wani hasken musulunci adduar da Suka min kaiiiiii gaskiya munyi addini Addua Kamar ba gobe kalli yanda nayi wata Kamala sai fa da na Zama wata Yar kwarya kwaryar waliyya gaskiya na Sha Addua ji nake wani fresh sabo da tsoron Allah


   Dariya yayi a ransa Wai a haka shine abin proud adduar tasu ta Dan lokaci a fili ya furta karki dameni ni,nace a hankali yanda bazai ji ba na furta almasifatu kanwar azaba,Ashe yaji ya tambaya me Kika ce? Cewa nayi ka jawo na rame kalleni rama har nono sun dawo wasu gasu nan Allah ya taimakeka baka tabawa da kaga ta kanka ji zaka Yi Kamar ka tsinko dan lemon zaki karami,dariya ta Kama Nawwar ya kasa dannewa sai da ya murmusa,nace tsaya a siyi pad matar taka an jima kadan Zan Fara yoyo na kusa,slow yayi yace ta Kare ne duk yawan wacce na siya Miki? nace ai kyauta na yiwa su Sera Kawai ka siya min wata sannan accnt dina ba kudi ka tura min sannan dinkuna na an dinka ban karbo ba,yasan halinmu da kashewa Kai kudi Kawai parking yayi a wani Shopping mall,nace ka taho da ice cream,kamar bai ji ba sai gashi ya siyo min har ice cream din, ya kawo min,tun a motar na Fara Shan abina,Muna tafiya Wai a Dole haushina yake ji,dariya ya bani nace dinkunan kala uku ne Dan fake fake ne 20k,yace sai kace ke aka zana a jikin kayan,dariya nayi nace ka dinga kyautatawa iyalinka Allah zai Kara buda maka duk nasan komai kanayi karka ji komai kayi komai ba komai duniya ce dole mu baza mu bita a Sannu ba da gudu zamu bi a barmu, nace Addua ta karbu, kunnawa min kida yanzu na warwasa,hmm yace Kawai Yana kallon na kunna kidana. 


      Sabreen tana Palo ita daya gidan duk dirty kaca kaca amma ko a jikinta sai sallamata taji mun shigo tare da Nawwar, Nace  Honey Kauye tayi na gode da barina da kayi naje unguwar nan kaga ko ba komai na gaisa da iyayena da Suka rikeni,naji dadin tafiyar nan kaga ai nayi zumunci,Sabreen a ranta tace wato dama ba sakinta yayi ba unguwa taje Kauye ashe Kuwa akwai bala'i wlh Zan iya kisan kai bari nayi sabon shiri,kwafa ta ja Ina kallonta bata ko kalle mu ba sai da kyar ta kalli Nawwar ta dauke kanta,ice cream Dina naci gaba da tsotsa na Mika Mata roba daya tare da furta uwar gidana ga roba daya nasa hannuna a saman kanta nace wannan gashin ai sai a zaci dambu ne mu rufa Masa wawa,kutmar....keda ice cream din ta kutuntuma min ashariya ko a jikina,shi kuwa tuni ya wuce samansa nima bangarena na wuce.


       Ina hutawa Fitowa nayi na zage na Fara gyara gidan,Da dakinsa na Fara lokacin hankalinsa ya kwanta Yana zaune gefen bed dinsa Yana latsa system dinsa na wanke toilet kal kal na fito nasa Hannu tare da dauke system din daga gefen bed din na matsar da ita gefe sannan nazo na riko hannayensa biyu nace Yi hakuri ka tashi,mikewa yayi Yana Jin sanyi a ransa,bed din nake gyarawa Yana Kare min kallo kamar zai cinyeni sabo da sanye nake da guntun wando da kyar ya rufe min duwawu da rigata t-shirt peach wandon Maroon,Shi kuwa sanye yake cikin dogon wando da riga iri daya farare tas rigar me dogon Hannu harda hularta yayi kyau sai kamshi yake,Yana kallona Yana ganin girmana sabo da Ina da tsayi da Yar kibata normal komai yaji,sai da na gama da gadon nasa sannan nace zauna tare da rungume shi na zaunar dashi a haka na dawo Masa da system dinsa inda take sannan na share nayi mopping ko Ina ya dauki kamshi sannan na fito ko Ina sai da na gyara banda bangaren Sabreen,kitchen na Shiga na fara girkina gida ya dauki kamshi,Nawwar ya dade rabon da yaji kamshin nan sai ya dawo Palo ko Ina Yana shining ya zauna a nutse,su Sultana ne Suka shigo da sallamar su,na fito Muka gaisa na zauna Muna surutu Nawwar yace yunwa nake ji fa,tashi nayi na koma dakina na dauro zanin Atamfa akan dan gutun wandona,hakan ya Masa Dadi yace a ransa lallai kin Fara hankali.


     Waina da miyar da na Fara Yi na zubo musu da kemo da ruwa sannan na kawo musu chin chin,kitchen naje Ina aikina har na gama suna hira abinsu sai da na gama na zubo Masa nasa wainar inda yake na kawo gabansa a manyan flasks na koma kitchen Ina cewa da Kannensa kuci fa kun San dai nan ba bakon gida bane,idan bata Isa ba sai na Kara musu dan Allah kar ku ji kunya,Su Sultana sai Murna sukeyi sun samu aunty me kirki,sai da na kawo Masa komai gabansa sannan na zauna,sai da suka ci Suka koshi nace Mami tana son Masa?Suka ce ae nace to na zuba muku sai ku Kai Mata,shi kanshi yaci wainar nan sosai fiye da zato na,da zasu tafi haka na cika musu flask sannan miyar daban suka tafi da ita,suna tafiya na cire zanin na fito kusan tumbur dani, kallona Nawwar yayi kawai Ina mamaki a raina wai ya akayi bana birge shi ne,Sam baya sha'awata,cinyoyina na tale yanda Muka saba zaman mu na Yan kwalta,Muka sake hada Ido ya maida Kansa ga tv,gabansa na dawo na tsaya tare da furta ban gane ba fa,yace what? Nace Kai billahillazi sai kayi sha'awata na gaji koma yane Kawai kayi sha'awata yawwa ehe Indai ana so a zauna lafiya Kawai ayi sha'awata haka Kawai sai gana min azaba akeyi,Dariya na bashi ya dinga Kuwa kyalkyalawa Kamar ba Nawwar ba,tsayawa nayi Ina kallonsa,sai da ya gama yace dama wai dan ni kike yi? baki na turo nace ban sani ba,Hannu ya miko min na kalli hannunsa na Mika masa nawa hannun nayi a hankali ya jawoni na zauna a hannun kujerarsa ya Kare min kallo ya sake tuntsirewa da dariya,Fuska na kwabe cike da shagwaba na mike a fusace Zan bar wajen ya sake riko hannuna naji wani yarrrrr a jikina, jikinsa ya jawo ni na fado saman cinyarsa bayana yake karewa kallo ko Ina fari luwai luwai,a saman dokin wuyana ya dora bakinsa a hankali cikin wata irin murya me rikita mata ya furta me kike so? nace ba komai Kawai,oya Ina jinki me ya faru naga gardi rungume da matata? Sannan Wanda ya Kira fa Yana Miki ya gajiya? Nan take idona ya ciko da hawaye na zame a hankali na koma kasa na zauna sosai sannan na dago idona Ina hawaye,yace ba kuka nace ki min ba,nace idan na rantse zaka yarda? Kasan bana karya wallahi duk abinda nasan nayi shi Zan fada maka,ban San komai ba akan Wanda ya kirani a waya Kai sheda ne da ace Ina da maza masu kirana da ka sani amma Inshaallah very soon zaka fahimta,sannan Wanda yazo gidan kawai ganinsa nayi a Palo ya fado Ina kokarin guduwa ya damko ni Kawai na barwa Allah duk Wanda ya min haka Inshaallah asirinsa sai ya tonu,Kawai kasan mu a baya an San mu a duniyanci ko yaushe a zargi muke shi yasa da anga irin wannan za a yarda kasan a inda ka dakko ni Kuma na yarda na zauna da kai Kuma bana boye maka komai tsakani da Allah nake zaune da Kai,mu yanzu ba Wanda bazai Mana sharri ba sai ka Kai zuciyarka nesa fa sannan akwai abinda nake kokari ka samu shine shedata lokacin zaka yarda dani .


    Har na gama bashi cikakkiyar amsa Yana kallona yace na gamsu da ke,nace na gode da fahimta da wani ne da tuni ya dade da sakina,me zance da Kai sai godiya,Ni Kuwa me zance da kai ai a duniya bani da kamarka Kuma na gode Allah ya saka a Aljanna firdausi,Ameen ya furta Yana Jin sanyi da wata nutsuwa a ransa,ya akayi kika daina min kiss? nace Naga Kamar baka so,ki daina daka tani ni kunya ce dani ba iya komai nayi ba yayi min wayo ban gane ba,dariya nayi na koma saman cinyarsa na zauna nace ka daina Jin kunyata nifa ba kunya ce dani ba zan iya tubewa a gabanka,yace Allah? nace ae to mu a fada Mana fitsara shi yasa nake so kaji dadi kaki Kai Kuma,Ni mene ma zaka ji kunyata ni ba malama ba bare ace Ina kwarjini,yace to ku ai Kun waye da irin wannan harka ni ai sai dai ki koya min,duk ban gane wayo bane,nace Kai da kake da mata bata baka ne? Yace to ita kunya ni kunya bama iyawa sosai, dariya nayi tare da furta ba wani ka iya kowa fa a fagen nan dan iskane Allah nayi kasa da muryata cikin rada na furta harda ubana tunda yayiwa uwata cikina,baki ya rufe da hannu yace Kika zagi Daddy,nace waye Daddy din ni bani da kowa gashi nan ana cewa Yar shege ce ni,mikewa nayi nace good night na wuce part dina,wanka nayi tare da tsaftace lungu da sakona yanda na Saba sannan na fito nan haka bayan nayi shirin bacci cikin wata guntuwar rigata pink,Ina Shirin kwanciya naji wayata tayi kara na duba Nawwar ne,Ina dagawa yace zo ki kawo min green tea, Fitowa nayi naje na hada Masa na nufi dakinsa Sabreen an Sha kwaya ana ta uban bacci.


      Shiga nayi daga shi sai boxers jikinsa ne me kyau ya dauki hankali na ina satar kallonsa na ajiye masa Zan juya yace Kun rainani a gidan nan ko wacce ranar girkinta sai tayi tafiyarta part din ta to daga yau nan kwana,Dadi naji amma na danne,kallona yake yi na zauna a gefe nima Ina kallonsa,muryarsa na tsinta yace kina son hakkinki ne a baki? Kai na girgiza alamar a'a,yayi mamaki yanda da nake roko amma yanzu nace a'a, Ido ya tsura min yace da gaske? nace da gaske na furta babu alamar wasa,to ni idan Ina so fa? dariya ya bani na danne sannan nace ni bana so yanzu,Zan iya tayaka kwana kamar da yanda baka taba ni,Amma yanzu ni harkar ciye ciyen nan ba so nake ba,ba kalau kike ba to infection ya kamaki,dariya na dinga yi nace akan me Infection zai kamani a toilet dinku ta gidan yawa da kike zuwa kina shiga ya Miki illa baki sani,3days Indai Kika ci gaba a haka asibiti zan kaiki dole kina da infection matar da kullum kike roko sai an lalata ki,pillow na dauka tare da rufe fuskata,baki ya bude yace ahhhhh gaskiya ba kalau ba ruqiyya kike bukata yau kece da kunya? harda rufe Fuska? Saman gadon na kwanta tare da kife kaina a Kan katifar Ina dariya kasa kasa yace Wai da gaske kike kunyata kike ji yau? mikewa nayi zaune duk na rasa inda Zan saka kaina wata kunyarsa nake ji,kaina na dauke na kalli gefe Ina murmushi na zaro harshe kadan duk cikin kunya,dariya yayi tare da furta ikon Allah Miracle guda yau da kunya addua tayi Allah ya amsa,dama kiss dinki da Kika Saba danne Ni ki min da shi Kika min yafi kunyar nan taki ni ban Saba gani ba,Jin yace Kiss na tashi na fece da gudu na bar dakin,ya tsaya baki bude yace kalau take Kuwa.


     Ya zaci kunyar ta wasa ce,sai da ya fito breakfast dake yau bazai fita ba,sai yaga har na gaishe shi bana kallonsa Kuma gaisuwar ba irin wacce mafi akasari nake Masa ba to yane? ya akayi? Ya garin ne? Ina serving nasa ban kula shi ba Kuma ban kalle shi ba ,dariya ta kamashi Kamar wata sabuwa haka na koma masa, yace to za kawo English teacher din? nace Inshaallah,Baki ya saki yace wai kece da Inshaallah har kin San Allah yanzu? na sake cewa Alhmdllh ba laifi,tagumi ya zuba Yana kallo na,yace ko dama Ustaziya ce ne ta lalace,dariya nayi bai gama Shan mamaki ba sai da yaga na canja channel na kamo sunna tv, dama karatun Qur'ani inayi idan na ga dama sabo da yanda na Saba tun Ina kauye,Sabreen ce ta fito taga mun Gama break Muna kallon wa'azi dariya ta tuntsire da shi tace ba wani alaye da zaki mana Kai Allah ya tsinewa karuwa kaji,karuwa ta Kai duk inda ta Kai a duniyanci wato sabo da an kamaki da kwarto shine Zaki canja salo,kallonta nayi nace Subhannallahi wannan kazafi ne Allah ya hana, kiyi harkarki nayi tawa idan ba haka ba Zan ladabtar dake da ayoyin Allah,Nawwar dariya ta kamashi ya Saba shi ashariya da zagin fitsara iri iri a gidansa, Sabreen ma dariyar ce ta kamata ta wuce dining,Nawwar na kalla nace ka kaini gidanmu,me zaki yi Kuma da'awa zanje,Sabreen ta kwashe da dariya sai ga su Sera su wurin bakwai sun shigo,tashi nayi Muka Yi ihun mu da Muka saba tare da rungume juna,Nawwar ne yace sannunku da zuwa shi Kam suna birge shi da kaunar junansu da hadin kai,Zama sukayi Suka gaisa nace me zaku ci,Suka ce sai da rana yanzu sun koshi,Kallo na sukayi Wise tace Miracle ya hasken musulunci? Nace Alhmdllh ai na baku labari tun a waya sai naji Kawai tuba da nadama tazo min lokaci daya Kamar ana ruwan sama haka nake ji addini na zubo min da tsoron Allah kafin safiya na cika makil da tsoron Allah,Tagumi Suka zuba Suka kafe ni da Ido,nace Ina fada muku Kamar a mafarki na tashi naji tuba da tsoron Allah sun fado min Kamar yanda naji farar daya karuwanci nake so, Seraline tace no wonder gashi nan goshinki sai shekin addini yake,nace ah ai walwali nake yi,Yaranki sun samu uwa ta gari nace wallahi ku tayani murna Ina haihuwa yarana zasu Sha tarbiyya tun Ina da ciki yaron zai iya Karatun fatiha dariya mukayi gaba daya,na nuna Nawwar nace idan muna saduwar sunna ma idan ya gasu cikin Oven Babu kiri'ar da baya ja,


     Star tana dariya tace au memory din nasa ashe yanzu ba waka bace karatune a ciki? nace ae Mana,Nawwar Jin fitsarar tamu ta daban ya mike tsaye Star  tace mu Kuwa Muna nan sai siyar da takashi mukeyi,nayi dariya nace Allah ya shiryeku kawayena Zan ta muku addua,yawwa ki Mana Addua mu yanzu mun manta rabanmu da karanta ko Bismillah, Nawwar yaji tausayinsu Mandula tace Ina so na shiryu wlh Amma bazan iya ba karuwanci ya shiga jini na sosai bana so ma na daina dan a Ina Zan iya Shan sigari? Kun San bana free da hayaki duk yanda akayi Bob marly ya biyo ta tsatson mu shi yasa na gado shi,dariya Muka Yi nace wlh kuwa baki Isa ba gidan aurena ne nan ba bariki ba sai dai ki fita daga gidan ki Sha abarki,tace an gama ta mike ta fice daga gidan gaba daya a can Kan layi ta dinga bulbula hayaki,Baki da wani aiki mu tayaki? Nawwar a ransa yace Allah sarki ji kauna dan Allah kamar yan uwa,cikina Sera ta shafa tace Wai har yanzu baza muyi Yara bane kinki samun ciki haba Miracle ni wlh kin bani haushi ko bakya zagewa ne a daki harka,ki dage rana daya zaki samu,nace ke muke jira kizo ki koya Mana yanda akeyi dan uwarki kaji min yarinya,haka muke ta hira har Nawwar yayi bako Khaleel ne yazo gidan Suka ma can bangaren baki,Sabreen kuwa tana part dinta tana Jin haushi Nawwar Yana barina ina abinda Naga dama Kuma tana ganin wani kallo da yake min kullum kamar zai cinye ni.


     Washe gari Jamcy ce tazo ta bawa Sabreen wani magani tace guba ce ke tunda ita take yin abincinta ki sa Mata a abinci taci dan ubanta ba a lokacin zata mutu ba bare a gane a hankali zata fara aiki a jikinta tana lalata Mata kayan ciki a hankali har ta Fara cuta slowly sai mutuwa Kinga babu me ganewa,tafawa sukayi Sabreen tace an gama Indai ba mutuwa Yarinyar tayi ba to bazan ji dadi ba.





Masu Neman Jin wasu Audio na novels Dina kuje YouTube channel na S ZARIA TV



MASU SHARHI INA GODIYA MUSAMMAN YAN GROUP DIN YAR AIKIN KARUWAI.




No comments