Breaking News

Yar Aikin Karuwai Book 1 Page 56-60

         56-60




Official


By

AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA



Page naku ne


Khadija Dandume

Mrs Mukhtar

Maman Afrah Ik

Fairdausi m Sani oum Meenal

Mrs Aminullah

A'eesha

Aisha S Maibankeey

Mom Islam

Khadeeja Sageer(Umee)



Gaisuwa gareki 

Aida Maman Tasnim






     Anga rida ridan yan Mata ai ni yarinya nake tashi cikinsu,damasu Dj dinmu Muka dira speakers manya manya sun Kai goma Sha biyu kida suke badawa kamar zasu fasa gari,Inna har Yan matan kauyen ta rabawa alawa, dama mu mun Saba ba abinda ya dame mu da Kauye katon dakin  da Inna ta gyara ta bamu Muka baje dayan dakin Kuma kayanmu Muka ajiye,sai da Muka tsara komai akan ba shaye shaye duk me Shan wani abu tayi hakuri zuwa kwana daya, Yan matan Kauye kasa zuwa cikinmu suka Yi dama Yara ne gidan Dagaci ne Kawai da Mairo ita Kuma Bata zo ba, komai mun siya na abinci, tun kafin muzo na turawa Bala kudin ya siyo ya Kai gidan Inna,Wani abin Kuma da abinmu Muka zo,amma Muna zuwa Inna da matar Jangudo an dafa Mana shinkafa da miyar,salat Kawai Muka yanka Muka ci Muka barta ga lemukan biki Muna ta sha,akwai abincin Kuma da Muka bayar a cikin birnin Kano za ayi Mana fried rice sai waina da miya,alala,da tuwon shinkafa miyar Agushi har na angwaye su fried rice ce da pepper  chicken sai waina da miya, har fura mun bada ayi ta Yan gayu munyi order duk kudin Nawwar ne Wanda ko waya bamu yi sai da dalili,Yara sun zo gidan Inna sun tsaya Mana a Kai suna kallo sabo da Muna zuwa duk kana nan Kaya Muka saka a jikinmu ko wacce sura a bankade wani yaro ne zai Kai 13yrs ya tsurawa Wise Ido sanye da half vest da dan guntun wando gashin nan yaji gyara gata itama fara Kuma ta Kara da Mai tayi Kal Kal,wise ta kalli yaron ta Mika Hannu wuf ta kamo shi tace Dan ubanka zo na baka nono ka sha,ihu ya saka zaiyi kuka yana wutsil wutsil tace ai sai ka Sha nono shegen yaro ka tsura min ido,zuwa nayi Ina dariya na kwace shi ya fice da gudu, Star tace gobe fa sai an kawo Mana motoci biyu sabo da zirga zirga,nace karku damu za a kawo ai na fadawa Ango yace Already an kawo motocin ma har Wanda zasu kwaso angwaye daga airport Kun San Yana da mutane a nan, Inna kuwa da makwafta suna ta Shirin abincin da zasu bawa Yan Kauye mutan kauyen, Bluetooth speaker muka kunna a gidan muna ta rawa,sai dare bayan munyi sallar Isha nace wai Mandula baza ta zo bane,kin manta a cikin Kano fa gidan kawarta ta zauna itace zata taho da abincin idan an hada,sai Kuma me Make up da zata taho da ita,nace ai sai ku fada min yanzu ita za a kaiwa mota? Sera tace ae mana nace ai to an huta ma mota daya tayi ko wacce zamuyi amfani da ita? Wise tace yeah ku tashi mu dan zaga garin Mana mu gani tunda gobe ba time,wasu Hijab Muka saka wasu abaya Muka fito kamar mutanen kirki dake da wutar nepa ko Ina haske ana ta hada hada a kauyen mun fito duk inda Muka yi sai kallo harrrrrr samari ana ta cacar baki,wani me tsaurin Ido Sani ya turo yaro wai Ya nuna Yar Zabil tazo,nace inji wa? yace Sani na gidan Sale me Alewa dariya nayi nace sisi baza ki samu ba ubansa ma Alawar Dinya Madi yake siyarwa,Yar Zabil tace kut ni a kauyen nan ai duk sai dai na aike su ta ja tsaki Kai muje,Sera tace Sani guy na taba tsinka Masa Mari tana Dariya.


    Gidan Dagaci Muka shiga nace a nan na girma,Dagaci suna tsakar gida suna gulmata na kawo karuwai, sai gamu da yawan mu mun shigo dama tsokana nazo ba gaishe su nazo Yi ba,Dagaci Yana ganinmu ya mike da masifa ku fitar min a gida Kar ku lalata min tarbiyyar iyali ku tafi can gayyar tsiya,Star ce ta kalle shi da hularsa tasa Hannu tayi fatali da hular Dagaci tayi fatali da ita na sa kafa na take hular, tace Kai dalla rufe mana baki,nace tunda ka Mana you must collect nayiwa kirjin Dagaci kwass na rankwashi kirjinsa ,yace kuyi abinda zakuyi shegu tambadaddu sai nasa hukuma ta Kamaku ,Malika ta furta da kuwa ka taro bala'i wallahi da sai na sa an kwace sarautarka karka cika Mana baki muke da masu fada a kasar nan,nace ni da kaina sai nayi maganinsa mark my words,Mairo ce ta mike tace iyyeee anje birni anyi clean an tsinci turanci a kwalta to wallahi ke baki Isa ba ke din banza banzaye karuwai an zo ana mana burg....Mari taji tas tas tas har uku tuni Wise ta Gama da ita,hawaye ta saki da kuka, Star tace kina sake magana wallahi sai mun tara Miki gajiya baki san waye mu ba,ta nuna Dagaci tace Kai Kuma Muna nan zuwa kanka yanzu gidanka Muka zo amma nan gaba zaka ji mu karka manta bama gaggawar daukan fansa, Azzalumi an baka amanar marainiya kaci tunda kaci amanar Rabiah you must see shege, Gwaggo ce ta taso da bala'i Yar Zabil taci kwalarta ta hankadeta ta fada Kan Aunty Amarya tace yanzu biki Muka zo zamu dawo Kun tabo bala'i sai mun hanaka Shan ruwa a garin nan wlh wannan Dagacin sai an kwace zaka ga masifa,na kalli Gwaggo na furta idan Gaji ta dawo kuce ta shirya nace muje dan Allah dama kawoku nayi mu isar da sako,Wise ta dinga foli foli da tukane da kwanika a gidan da kafa,na nuna Dagaci nace dan gyatimarka akan na hanaka local government dina cikin dare kake zuwa gabanka a dage ya kalli samaniya kana rokata na baka hadin Kai shine kuka min sharri kuka bata min suna wallahi Allah sai ya bimin hakkina Kuma sai na ci takashin uwarku Dan me dirkawa uwarka ciki Ina bala'i harda hawaye naci gaba me chemist din da kuka sa ya rubuta Ina da ciki sai Kun karyata kanku na karasa Gaban Gwaggo da Amarya nace sai kun bada sheda a gaban kowa kafin ku bayar a lahira,Aunty Amarya na tugewa dankwali na wullar da shi nace ubanki ne yayi min cikin Yar gidan Ubale me tsire,ubanki Ubale shine ya min cikin? Aunty Amarya ta mike ita ga marar kunya nace wallahi kina magana sai nayi tsirara naci ubanki a nan sai na miki tsirara,komawa tayi baya tayi mukus,Gwaggo ta mike ta cakumoni nace ku barni da ita na dauki Gwaggo dama ba kiba nayi sama da ita na watsota waje Dagaci ya kasa motsi bai taba ganin jaraba irin wannan ba,Mero ta fito tana zagina Sera ta kamata ta dinga jibgarta Kamar ta samu jaka,Gwaggo ta mike ta rukuma kokawa dani ita ga Yar bala'i tana cewa Yar tsuntuwa Yar cikin Shege


   Dama munzo da Santana mutane da makwafta an cika ana kallo,Santana ya falfalo Yana ihu ya dora Hannu a ka Yana cewa na shiga Uku za a kashe Mana Yar uwa Yana gyara daurin zaninsa a saman Jallabiya ya kalli Su Wise yace kun tsaya za a kashe Mana Yar uwa ya dakko dutse wani Dan karami Yana yarfe Hannu Yana furta wash nauyi ya jefawa Gwaggo a hankali ya rike hannunsa da sauri Yana fari Yana karairaya ya furta na Shiga Uku zata min illa hannuna wooo, su Wise ne Suka hadarwa Gwaggo Muka lakada Mata duka,wasu Kuma Suka tafi wajen Aunty Amarya ta fada dakinta tana ihu Suka bita ciki Santana yace ko karkashin gado ta shiga ku kamota,Dagaci abin yafi karfinsa yasan shi kanshi Yana magana Karuwan zasu ci ubansa,Santana Yana ta ihu Yana Karuwai in action wlh an taro Barcelona da Madrid Dole a caskale wuuuuuu yau ana batakashi da kyar makwafta Suka kwaci Gwaggo Amma duk da haka zage zage take tana haki,Aunty Amarya suna fitowa ta sawa dakinta key,Dagaci Kansa buya yayi a dakinsa yaga shima zamu iya dukansa, mu kuwa ficewa Muka yi mun Gama kullawa dagaci yanzu kam,Dagaci yace ayi auren mu gani idan Zaki ji dadinsa gobe Kuma iya yina saina rusa auren nan kwafa ya ja ya tafi Yana lallashin matansa,Mero ta fara kuri tace ai sun tafi da su tsaya Mana su gani Ina ma Gaji tana nan yau da sai dai a mutu.


     Sai da Muka gama yawonmu sannan Muka koma gida 11pm Muka kwanta bacci, a ranar Mairo ta Kira Gaji ta fada Mata abinda muka Yi musu,ita ga yar masifa tace gobe da wuri zanzo zasu ga inda ake masifa. washe gari tea Muka Sha harda harda kwai aka soya Mana duk kudi Muka bada aka siya, su Inna sun gama tuwon daurin aure da akeyi a kauyen tuwon danyar shinkafa miyar taushe duk an kwashe a Leda an adana a manyan cooler, 11:30am ne daurin auren,sabo da haka 11am angwaye Suka zo,duk munyi wanka ko wacce ta saka sabon kayan data dinka na kece raini Malika ta iya make up itace ke musu tana musu dauri,ni kuwa Amarya tsadajjen leshi na saka white and golden takalmina golden da jakata da mayafina,wata gown aka dinka min fitted amma a tsakiya an yanke rabi anbi wajen da adon abu,ta gaba sai kace riga da skert ne amma ta baya kuma fitted gown ce nayi mugun kyau, dake mulmul nake dai dai dani ga mazaunai manya sai na fito wata Queen,Mandula ce tayi parking da mota a gaban angwaye dake sanye cikin manyan shaddoji abokan ango da Yan uwan Baffa na can maiduguri da shi Kansa Baffan suna cikin hadaddiyar mota Baffa Kamar ya fasa ihu Yana ta kunci dansa zai auri bare marar asali Kuma ga Kauye ma abin ta ko Ina ba kyau, Nawwar da rukunin abokansa sun Kai su ashirin da wani abu harda Auta Nawaf kanin Nawwar, ango ya sha wata farar shadda da babbar riga ta zamani ya coka Yar hula kalar takalminsa farare komai fari,motar ma da aka dakko shi daga airport Fara,irin kyan da ya zuba ba a cewa komai kowa shi yake kallo a wajen,Ni Kam me Make up tana ta tsarani tsaf,Mandula ce ta murzo motar da Nawwar yasa aka Kai Mata a cikin birnin Kano taci wankanta itama cikin wani danyen material peach ta Sha make up light,takalminta me tsini ta fito gasu dama da kibarsu ba rammiya sakamakon supplement na yanzu da Mata ke dannawa cikinsu,Fitowa tayi tare da bude bayan motar komai an shirya shi na musamman take away dinmu ma da aka zuba abincin na daban ne,har lemuka duk an zuba a jakar take away din,su Sera ne Suka fito Suka tayata shigar da kayan ciki,ta Kira Khaleel ya bude bayan motarsa ta zuba musu nasu abincin na angwaye,aka bude mota Daya cikin na Iyayen Ango aka basu nasu da yawa, Suma aka ware nasu aka saka musu a mota sai da Mandula ta sallami kowa Saura na Yan daurin aure mutan kauye za a karasa basu,sun ware nasu Dana bakin su,tana gamawa ta kulle motar ta tako zata wuce Nawwar tace ango tana Murmushi yace sannunki kirjin biki,Auta ne yazo da sauri yace Ina Amaryar Yaya,Nawwar yace ga kawarta nan bita ta kaika wajenta,Mandula ta rike hannun Auta,tace ya sunanka yace shi Auta Kawai ake fada masa tace to,ya zama dan saurayi suka shiga gidan da shi, Kawai yaga Yan Mata iya Yan manta ya rasa wace Amaryar ma, an Gama kwalliya dauri ake min Yana ganina yace wannan ce ma amaryar naga tafi kowa,gabana ya tsaya Ina ganinsa na gane kanin ango ne domin sunyi kama,yace Amarya nace Auta ne naji ai Mami tana zancen Autanta yace ai duk tafi so na,nayi dariya yace yunwa nake ji Aunty,nace a bashi abinci ya zabi waina da miya yaci yasha lemo da ruwa yaci ya koshi yace anjima zanci fried rice nace to Allah ya kaimu,masallaci ana shirye shiryen daurin aure Dagaci yazo aka nuna Masa uban Ango da Ango Kansa


    Bakin ciki ya kusa kashe shi yace da gaske masu kudi ne ai larabawa ne cab ai sai yaje wajen Baffa ya Mika Masa hannu Suka gaisa yace bawan Allah mutum me Kamala irinka ka yarda danka ya auri Yar tsuntuwa tsintarta fa akayi,Baffa a ransa yace wallahi nima dole ce ta sa,amma a fili sai yace ae ai mun sani ita Yar tsuntuwa ba mutum bace? Iyaye ne suka haife ta sabo da Haka yaro Yana so Allah ya nufa wa ya Isa ya ja da ikon Allah,jikin Dagaci yayi sanyi matuka yace Babu riba Kawai na koma wajen malamina yafi min a daura kawai sabo da bacin rai zamewa yayi bazai ji an daura a gabansa ba ya koma gida,Liman sai Neman Dagaci yake a matsayinsa na Babba a gari Kuma Wanda ya rike yarinya amma an neme shi an rasa ashe dan kar ma aje nemansa gona ya tafi ya samu bishiya yayi shimfida ya kwanta Yana bacci abinsa.


    Mutanen garin sunyi Kara sun cika kamar kasa cikar da ba'a taba Yi ba a garin a daurin auren wata sai akan Yar tsuntuwa kaf garin nafi kowa tara dan Adam,wasu ma kallo ya kawo su,dubban jama'a ne Suka sheda daurin Auren Rabiah ta daina amfani da sunan Dagaci a matsayin Uba tuni ta koma Rabiah Muhammad Nawwar tunda bata da kowa a duniya ta zabi Muhammad Nawwar,Jin sunan da Liman ya kira ya sa Nawwar Jin dadi harda sunansa a sunanta Rabiah Muhammad Nawwar,shi Kuma Nawwar Ibrahim, Baffa shine waliyyin Amarya,Nawwar ya karbi Aurensa yanda yace babu Kara,ga masu uban Dj sun shirya tsaf,Sadakina dubu dari biyu,Jangudo da yaransa su Suka dinga raba goro a wajen da alawa sannan suka fitar musu da abinci tuwon da su Inna sukayi,Fitowa mukayi gaba daya kallo ya dawo kanmu,Nawwar ya tsaya a gabana nace to an daura? ya furta uhm,Nan aka Fara zuba ruwan pics ta ko Ina wayoyi ne ke tashi,ana haka me Dj suka saki ganga kida Kamar zai fasa kunnen mutane, Wise ce ta fara bude rawa a gaban dattijai Yan daurin aure Basu watse ba ta fara takawa kowa ita yake kallo,Abokan ango an baza Ido ana kallo wani Sabeer a cikinsu yace wannan tsagera ce ta kirki,Murmushi muka Yi mun San bai ga komai ba,Kafin mu rufe baki Malika taje tana mata liki farrrrrrrr da Yan dari dari tana gamawa tabi sahu tana cashewa,dariya ta Kama angwaye dan Kuwa Malika gwana ce a rawa yanda ta duka ta tana wargaza mazaunai tab,Wasu su Sera Suma suka shige suna zuba liki suna rawa,Angwaye ai sai Suka gyara tsaiwa Suka ce sun fasa tafiya yanzu Suka fito da take away dinsu,fararen kujerun da Muka aro haya aka jera musu da yawa Suka zauna a gaba sauran Yan kallo Mata da maza suna baya mu Kuwa iya kawaye Muna ciki,Mc yace Amarya kadai ake son gani a fili ai Nawwar yasan ya Zama dole nayi rawar nan ya sani ma shi yasa Bai ce ma komai ba.


      Duk fili suka bani na shiga aka canja min kida tun Ina Yi kadan kida Yana ratsani na karbi speaker nace Ango ka yafe min Zan tsokani shari'a da Speaker a hannu nake rawar Ina Jin kunya Wai a haka amma yanda nake Cashewa,Auta kanin Nawwar ya shigo Yana min liki hannayensa na rike da hannayena biyu Muna facing juna a haka muna rawa kasa ai Kuwa kawaye Suka rufe ni da ruwan Naira Dj yana caskar kudi,suna fita Angwaye Suka shigo Kai an zubar da Naira Kan uba,gajiya nayi na fita sabo da make up dina,Nawwar ko daya bai ma tashi ba tukun yace zaiyi nasa, Kawayene Suka shiga su Uku Malika da Wise tare da Manduwa yau ana Shan kallo Yan kauyen sai ihu suke ana kallon iya shege karara a haka ma munyi da sauki,suna fita aka Kira Ango da Amarya Muka mike muka shiga sabo da iyayin Nawwar Wai a filin rawar za a sa Masa kujera kamar wani sarki ya zauna a tsakiyar wajen Yana Shan ruwan roba,ni kuwa rawata na dinga yin cin koshi ka rantse ba Amaryar bace,mikewa yayi ya dinga zuba min ruwan Yan dubu dubu, ana ta dauka a wayayi,Sera ce tazo ta min rada kuyi kiss zamu dauka a waya nace bazai yarda ba,sai kace ba mace ba ai karuwancin Zaki tuna,dariya nayi Ina dan takawa yana min liki,na dora hannuna daya a kafadarsa na maida dayan ma a kafadar na dora yace ta ya Zan Miki likin Wai bakya Jin kunyar mutane ne fa abokaina zasu ce baki da tarbiyya nace sai yanzu suka sani kiss zamuyi dauka za ayi zai zame nace Allah kana guduwa sai na kunyataka a wajen nan ka sanni, ai Kai kace kaji ka gani ka aureni, mu bama Jin magana ka bani hadin kai,yace to kiyi sauri na gaji,Yatsa na dagawa su saira su dauka haushina yaji Yana ta fada bai Dace ba wannan a musulunci Wanda yanzu ya Zama ruwan dare mutane da yaran masu kudi gani suke birgewa ce wayewa ce,a hankali nace kaine fa zaka min Ido ya zaro tare da furta na shiga Uku nidai,please  karka kunyata ni Zan kunyataka wallahi, Ido ya rufe aka canja slow music a hankali na dora bakina a saman nasa ya min kiss a nutse ana dauka na rungume shi sai aka dauki tafi da ihu yeeeeeeee Yan kauyen Suka Fara cewa yeee ya tsotsi bakinta alquran,billahillazi bakinta ya lasa kunga sun rungume da gani sun Saba tun a waje,Yan matan kauyen shewa Suka dauka yau Muna ganin bariki yehoho ahayye chasss...,Khaleel bai taba zaton abokinsa ya fetse haka ba sai yau dariya ya dinga yi, sai da Muka gama likawa juna kudi Yana min Ina Masa sannan Muka fita,Khaleel yace Lover boy,Nawwar ya hade rai tare da Zama,abokai su abin ya birge su sosai dama duk gasu Yan gayu yaran masu kudi,Wise bata gajiya sake shiga tayi tana yiwa kanta da kanta liki tana cashewa,Autan su Nawwar yaga duwawuka sai tsalle suke yace wow ya radawa Nawwar irin wannan Zan Aura nima Yaya idan na girma da wuri za a min aure,Nawwar yayi dariya a ransa a fili yace sai kaci ubanka wlh ni ban San ma ya akayi ka biyo mu ba,Mami ce tace nazo yaci gaba da cewa Auren Kauye za a min da wuri ni wallahi ba sai na girma ba,na daina kula Yan class dinmu wajen Aunty Rabiah zanzo ta hadani da kawarta,Nawwar yace sai na zaneka bari mu koma gida tunda baka kunya,Shuru yayi bai sai sake magana amma ya zurawa Mata ido.


    A wajen muma muke cin take away dinmu har Yan Kauye Suma sun samu da yawa sun samu, tare zamu tarkata da angwaye mu koma can Anambra, duk munfi yin rawar wakokin Yan kudu su Muka iya Kamar kannen Naira merly, 2pm aka tafi Sallah wanka Muka sake tare da canja Kaya wannan karon ba make up Kawai dauri mukayi kowa tayi wacce zata iya, muka fito na sha shadda dark purple nayi kyau, su Kuma ankon Atamfa Suka saka me kyau sunyi kyau daga nan aka dora da kida da rawa tare da sabon liki, babu Wanda zai so ya bar wajen nan,sai lokacin muka raba waina da miya aka sake ci da ruwa da lemo, bamu Ankara ba har 5:30pm sai Inna ce tazo tace Yan Kai Amarya sun shirya,sannan Muka tashi daga kida,masu kida Suka hada kayansu da motarsu suka tafi abinsu suna murna sun Sha kudi.

  A gurguje nayi wanka sabo da zafi na canja cikin Net less fari yasha hadadden dinki na Sha takalmi da jaka fari aka min dauri na yafa mayafi me kyau fari da adon silver,turaruka na shafa Wanda kayana komai an tattara su tuni sunyi gaba  Angwayen da Suka Fara tafiya su aka bawa Suka tafi da komai dama kayan lefe ne, Wanda na cire Kuma Sera ta ninke ta tattara komai a jakata da na zubo kayan sawa na biki suna wajenta tsinke namu bamu bari ba, Jangudo ne yace tunda Kai Amaryar ba addini bane iya kawayen ma sun Isa ga angwaye ai sun Isa Kai Amaryar


    Ba sai an sake wahalar da Ango ba Watarana idan ta haihu sai aje Mata,Inna tace hakan ma shawara ce shike nan aka fasa a Raina nace da ace Ina da iyaye Dole sai an rakani dakin miji amma ya zanyi haka Allah ya tsara min wannan yasa zuciyata ta karye na fashe da kuka,duk sun zaci kukan Kai Amarya nakeyi Suka dinga dariya Yar bariki da kuka za a kaita dakin miji  suna ta tsokanata, Nawwar ganin Ina kuka dariya ta Kama shi yace Amma Yarinyar nan ba karamar Yar rainin hankali bace lallai Ina ganin Yar duniya,ki gama  tikar rawa gata dama zaman kanta takeyi ta Gama sanin da Namiji me yayi Saura.


   Muna jikin Motar da Ango yake tsaye mu da kawayena kaf Inna tana cewa Allah ya tsare kinji Allah ya kade fitina,a zauna lafiya kinji dai nasiha ta to Allah ya bada sa'a ya bada zuria dayyiba na manta ma kuka nakeyi nace Ameen Ameen Allah ya bani me hankali,Inna sai da tayi dariya da su Star ana ta dariya har angwaye, Inna tace aure sai hakuri kiyi hakuri da mijinki komai yace to banda musu da gardama da taurin Kai,ba a jayayya da miji,Miji yafi Gaban Wasa,Nawwar Yana gefe yace dama ta rainani Kuwa Inna,Inna tace wallahi idan kina so ki gama da duniya lafiya kibi Allah kibi mijinki yanzu ba da bane baki da kamarsa,yanzu mulkinki ya Kare shi zai haye karaga shi zai Fara nasa mulkin sai yanda yayi dake,Nawwar yace ai tuni ma na fara Inna,Inna tace lokacinka ne banga laifinka ba dan nan kayi abinka,Amma mace dai ki sani Rabi bata da wani yanci Matukar a gidan miji take,ta kalli Nawwar tace wallahi kai Kuma idan ka zalunci marainiya ubanka zaka ci a wajen Allah yo Allah ba ruwansa,ka kula da ita ka Zama gatanta ka Zama mijin marainiya,kaga Allah Kai ya damkawa amanarta Amana fa aka baka banda banbanci tsakanin matanka ka kamanta adalci, Kar kaji Daya tafi daya iya kwanciyar aure ka wulakanta daya,su Star suka kaure da shewa, Nawwar ya kalli Inna da sauri,Inna tace ae zaka zuba min Ido ku maza imaninku a nan yake da kunji ba bayani to mutunci ya Kare abinda kuka iya kenan soyayyarku kwanciya da mace ba uwar da kuka iya a nan kuka iya soyayya musamman hausawa sai a lokacin za a fara Ina sonki bani da kamarki,kece gwanata,jarumata,dausayin raina, kece tekun zuciyata,ya turmin dakan dake lugude a zuciyata  Nawwar ya sheke da dariyar da bai shirya ba,kowa dake wajen motar dariya yake su Seraline harda ihu,Inna tace yo ai mun sani muma zamaninmu munyi soyayyar nan tsiyar maza wacce ce bamu gani ba,sai kana haihuwa shike nan an juya ma baya sabuwa ake nema Allah yasa kai a kudu kake Allah yasa dai ka koyi halin arziki,dariya na dinga Yi a boye cikin mayafi,Nawwar ma Dariya ta kume shi Khaleel dake Gaban mota da Driver sai dariya suke Kamar ba gobe,Nawwar yace mun gode Inna za a kiyaye,Inna ta furta ato kun girma dai idan Kun gyara ruwanku idan baku gyara ba ruwanku Inna tana gida tana baccinta.


    Zamu Shiga mota tace ban Gama ba ke Rabi na sanki da zafi yanzu ba a wa miji Fushi,ba Kuma a juyawa miji baya ke gaki Allah ya albarkace ki da Ido kamar Madara ki dinga sanyaya Masa zuciya da kallo,ke bakisan da kallo ma idan mace ta Isa sai tayi juya Miji ba,Nawwar Yana ta dariya yace banda ni Inna,Inna tace wane mutum karya kake yaro baka hadu da tsohon Hannu bane mu irinmu muka sa Namiji a gaba ai ya shiga Uku,Muka sake kwashewa da dariya kaji tsohuwa wa zai kalleta ma harda yabon kai, Rabi nace Na'am tace kuka bazai fishshe ki ba sai kin tashi sosai gidan kishiya zaki, ba a kishin fada,duka ko zagi gasa ake a wajen me gida,idan ta bashi Onga Kinga kayan Miya ne dai ko to karki sake kuyi abu iri daya a'a ke karki bashi Onga ki bashi Madara,Idan ta bashi Milo ke ki bashi farfesu,haka akeyin tsere  Nawwar kunya ta kamasu Ni Kuwa ko a jikina nace to Inna tace yawwa dare nayi kuje sai munyi waya,muka shiga mota kowa ya shiga Driver yaja mota dariya Kawai muke Yi Kamar me,Allah sarki Inna na bata Atamfa da leshi da sabulai cikin kayan lefena,sannan na bata kudi su Wise ma sun bata kudi akwai dadin Zama.


     Sauran duk sun rigamu zuwa airport muna zuwa dama jirgi na kasa Muka shiga da kayan mu Nan ma an Mana pics duk an watsa a media,har Muka sauka lafiya na Kira Inna nace mun sauka ta Mana fatan Alheri na rufa mayafina a Kai Amarya sosai,Mami da kawayenta su Uku da Maman Khaleel da Sufia a Airport suka tarbemu cikin shigar su ta Alfarma, sauran abokan Ango da Ango bayan an sake pics suka tafi kowa sai Khaleel da Nawwar Suka shiga mota driver ya ja su zuwa gidan Khaleel can suka Yi wanka a part dinsa Suka canja Kaya sannan suka Yi Sallar magriba da Isha suka zauna suna kallon pics suna Hira da labarin irin dadin da bikin yayi.


    Mu kuwa Mami tana gefe na a mota da sauran kawayena a wasu morocin Muka nufi gidan Sabreen,Mami a mota tana ta min Nasiha sosai akan zaman aure karshe tace dan Allah ki kiyaye ki farantawa Nawwar shima ya samu farin cikin da duk wani da Namiji ke samu karki biyewa rudun duniya da kawaye ki kula da aurenki ba abin Wasa bane shine darajar duk wata mace, rayuwar waje da Kika Yi wannan ya wuce da ba yanzu bane a manta da waccen rayuwar a Kama wannan kinji Rabiah dan Allah kiyi hakuri da halin kowa ku zauna lafiya,Kar naji ba daidai ba,nace Inshaallah,Mami tace ke ba yarinya bace Rabia kin San komai a kiyaye,Nawwar ya nuna Miki gatan da ba kowane zai iya ba,nace na sani Mami karki damu Inshaallah tace yawwa Yar Albarka Allah ya muku Albarka a haka Muka karasa gidan an canja tsarinsa gaba daya komai anyi sabo abin ya bada citta, Sabreen ta tashi a bacci tayi wanka ta fito Palo tana kallon furniture din da aka canja komai na gidan an canja an gyara ko Ina Yana kamshi mamaki ya kamata tace nasan dai anyiwa gidan nan gyara to waye yayi shara da mopping ko Ina na kamshi,wayarta ta tuna da ta kashe yau kwana kusan biyu bata tuna kowa lokacin ta sha kwaya da yawa,wayarta ta kunna ta kunna Data ta shiga WhatsApp Kawai taga wasu duk sun cire status din wasu sun saka bikin sabo da an kashe kudi musamman Dinner din,taga pics farrrr jamcy ta turo da videos ta bude nan ma Nawwar ta gani da Rabiah da kawayenta kamar ango da amarya,Pics din maza ta gani a masallaci alamar wajen daurin aure,sai ga pics din Amarya da ango a wajen daurin aure ga kawaye sai rawar Dj,tana bude wani taga Nawwar yayiwa Rabi Kiss a filin rawa suna ruwan kudi an ci uwar Naira,ihu ta saki tare da mikewa tsaye Zumbur tace na shiga Uku na,guda taji a gidan motoci suna ta shigowa,da gudu ta fada dakinta ta cire atamfar da ta saka ta canja Riga da wando tace yau za a kwashi bala'i kafin na sanar da Baffa da Iyamami,dama ba samu damar daukan Baffa a pics ba shi Yana daura aure ya fice ya bar kauyen daga nan ma kasar ya bari ya wuce US Dan karma a dame shi,yace wa Iyamami da Yan Uwa da matansa ya tafi Us su basu San ma daga wajen daurin aure ya wuce ba yayi haka ne Dan ace ai baya gari ma aka daura.


     Sabreen wuka ta dakko a kitchen ta rike tana huci Yan kawo Amarya Suka shigo Mami ce a gaba sai kawayenta da Kuma su Sera,ai Sabreen tana ganin gayyar su Sera sunfi ashirin suna guda suna cewa wata tara a zubo Mana twins,Wise tana shewa tace a bawa ango local government sosai,yau Ango zaiji banbanci ya samu GRA masu kirji fanko a ja baya,Allah ya taimaki ango an kawo masa me kirji a cike,Mami kunya ta kamasu gashi sunki yin Shuru sai fitsara suke suna cewa ayi magana mu naushi bakin mutum, da sauri Sabreen ta wayance wukar data dakko ta ajiye a Center table tace daga kitchen na fito Ina girki ashe kune ta juya salin alin ta maida wukar inda ta dakko,sai ta zagaye ta bayan kitchen ta fice waje tare da tare taxi ta fada motar ta bar gidan a million, tana fita a gidan ta fashe da kuka sai gidansu tana yiwa me taxi bala'i yayi sauri.


    Mami tace Sabreen fito Ina da magana da ku,Shuru shuru,Sera tace ta gudu fa ta bar gidan Naga fitarta,Mami tace Allah ya kyauta to,Sama aka haura da ni cikin hadadden dakina nima,sabo da a saman ma part uku ne,part din Nawwar,Nawa sai na Sabreen,kowa sai kallon gida yake ana yabawa,dukkan kayan lefena da tarkacen kayana har na gidan Karuwai da kayan gyaran jikina duk an kawo suna part dina su Misha su Muka bari tunda baza suje kauyen ba su suka shirya min komai na part dina har kayan Suka goge Suka gyara gidan ko Ina Kal Kal dama dakin ogan yasa key,Basu shiga part din Sabreen ba,sun Sha mamaki irin yanda suke karaf karaf a gidan amma bata tashi a bacci ba,ko Ina kamshi yake na musamman sunyi aiki babba na gyara gidan.


     A gefen bed dina na zauna komai nawa na dakin milk and brown ne,Ina zaune mayafi a kaina,sauran Suka ce to Amarya sai munzo nan da sati asha amarci lafiya,na dinga musu godiya Suka tafi,su Mami ma da Sufia tafiya sukayi ya rage daga ni sai Sera,Star da Wise,na cire mayafin Muna ta hirar bikin Muna kallon pics,nace in ya bari na siyi waya Zan tura please ,Sera tace wallahi Indai sun tabaki ki Kira mu,nace ya zama dole,ki kula sosai Kinga ta Fara daukan wuka Kar ta shammaceki cewar Wise Nace Allah dai ya tsare, Sallah nayi abina, Suka Shiga kitchen Suka Sha Madara da lemuka Suka dawo Muna zaune har 10pm sannan Suka min Sallama zasu tafi nace zanyi kuka karku tafi,Muka kwashe da dariya har ni, nace sai na biku ni Muna ta dariya,nace wayyo first night ya zanyi tsoro nake ji,Muka fito tare Muna ta dariya sai ga Sabreen ta dawo a compound ta ganmu har Amarya tace Yan bariki tayi ciki da gudu,shareta Muka yi Amarya ce da rakiya har waje kofar gida,Nawwar ne ya karaso da motarsa da mamaki glass ya sauke ya musu godiya sosai yace a fadawa sauran Yana godiya Suka ce zasu ji Suka Shige Napep din da Suka Kira sai gidan bariki, kirji na dafe nace Allah sarki Kwalta,Stree ohh duniya Ashawo work me Dadi da yanci ai Zan dawo ne soon ana sakina Zan dawo Yan Uwa Ina nan zuwa ba da dadewa ba nace bye bye Street Ina daga hannu,Nawwar Yana kallona Yana ji tunda a saitina yake glass dinsa a sauke yake,Kai ya girgiza yace in kin gama sai ki koma ko,ciki na shiga na koma dakina da sauri na rigashi shiga na zauna saman bed na jawo mayafina na rufe kaina zuwa fuskata na nutsu,ya shigo lokacin tsaki ya ja ya ajiye min ledata cike da nama da abin dadi,Daya ledar hannunsa dakin Sabreen ya nufa.


     Ya isketa ta dora Kai a jikin mudubi tana rusa uban kuka,shi dariya ma ta bashi yaushe ta Fara kishinsa,Kafadarta ya dafa tare da furta Babyna lafiya bai taba kiranta da Baby ba sai yau,mikewa tayi tsaye Zumbur tare  da daga masa Hannu tace dakata Malam me zaka ce dani zakayi aure ka fada min baza ka fada min ba sabo da cin amanarka sabo da zaka auri Karuwarka ai ka Dade kana cin Amanata tun kafin ayi aure ka Gama da ita dole ka boye min Kuma kaje gobe Iyamami tana nemanka,Murmushi yayi yace karki sake Kiran matata da karuwa ya Zama last idan ba haka ba Zaki ga abinda Zan Miki Kuma Iyamami ta Isa dani ne bazan je ba ki fada Mata kice nace baza a zo ba duk abinda zakiyi kiyi, aure kuma na kara ke kin Isa wace ke da sai na fada Miki tunda bacci Kika zaba kije ya isheki yaja tsaki tare da jefar mata ledar namanta ya fice abinsa.


    Part dinsa ya shiga ya kalli ko Ina kaca kaca duk dirty babu me gyara Masa shi kyankyaminsa ma yaji a haka yayi wanka ya fito ya shirya cikin kayan baccinsa ya kwanta sai bacci,ni kuwa ganin yaki shigowa na bude naci abinda zan iya na ajiye sauran nayi wanka da brush nayi Shirin bacci cikin gown Yar guntuwa ko cinya bata rufe ba peach nayi adduoi sannan na kwanta baccin gajiya ko farkawa banyi ba sai asuba,na tashi Ina saman Sallaya ya dawo daga masallaci ya bude kofata a hankali tare da lekowa ya ganni saman Sallaya juyawa yayi ya wuce abinsa ban ma San ya leko ba,part din Sabreen yaje ya duba tana ta bacci tashin duniya yayi taki tashi hakura yayi ya koma dakinsa ya koma baccinsa.


     8am na tashi na gyara ba garena Kal Kal Yana kamshi,fitowa nayi na gyara ko Ina har Palo dama ba dirty sabo da jiya an gyara,masu kula da compound sunyi nasu,part dinsa na shiga Yana bacci, toilet na fara wankewa sosai sai da ta dawo tana shining ko Ina,sannan na kunna turaren wutan na turiri Wanda ba hayaki yake ba da ruwa ake hadawa a kunna sai turiri Kawai, na fito a toilet na hau gyara Palon tunda na dawo palon ya farka a bacci amma bai nuna min ya tashi ba,gadon nasa na turawa na tura Yana Kai na kaishi gefe sai da na gyara side din sannan na dawo da shi inda yake dake ko waye akai kana danna Abu a jiki zai matsa da kansa,sai da nagama gyarawa shima dakin na hada turaren na turiri,na fesa room freshner me kamshin turaren wuta na, nazo na tattara kayansa kaf na koma toilet na zuba su a washing machine na wanke su tas naje na shanya a waje ta wajen garden,na dawo na iske ya shige toilet nace hmm ya tashi,haka na gyara bed din na canja bedsheet din sabo me kyau wancan na kwashe na kaiwa yaron gidan nace ya wanke a injin wanki idan sun bushe ya hada da kayan Nawwar dake shanye ya goge yace an gama.


     Kitchen na shiga bayan na Gama duk wani gyarana ko Ina sai kamshi, na gaji Kawai tea na dafa na soya dankalin turawa da kwai na kawo dining na shirya komai,na leka Zan kirashi na same shi Yana shafa lotion a bakin kofar nace na gama breakfast na koma dakina wanka nayi na shirya cikin atamfata super me tsada Riga da skert nayi kyau sosai Kamar zanje biki.


   Fitowa nayi na iske sai lokacin ma ya fito ya zauna a dining,Ina karasowa  na Masa gaisuwar Yan Jagaliya nace yane ya akayi ne? Kallona Kawai yayi na furta ina kwana ka tashi lafiya,ya amsa min da lafiya,sanye yake cikin kana nan Kaya wasu grey Riga da wando marasa nauyi,tea din na hada Masa na zuba Masa komai sannan na tura Masa gabansa,na hada nawa Ina Sha

    Yana mamakina duk surutu na yau banyi magana ba bance komai ba,ya bude baki zaiyi magana wayata ta dauki ruri,Murmushi nayi na daga tare da cewa Seraline,tace Amarya ya aka kwana nace lafiya lau ku fa tace lafiya sumul,ya gajiyarku?sai godiya ya amarcin fa an Sha kauna buri ya cika ko ta furta murmush na saki   hade da dariya nace ae Kinga dake virgin ce da yanzu sai mun Zo gashi wannan dariyar baki Isa kinyi shi ba nace to ya za ayi,Ina ogan naku,Ogana dai ko, dariya Sera tayi tare da furta to ki gaida shi nace zai ji,Yana  zaune yana Shan tea nace Seraline tace a gaisheka Ina amsawa yace,ya na ganki yau haka haka? Mika nayi da hamma nace gajiya ce kawai,rawar da kuka Yi ma ta Isa ta sa muku ciwon jiki,nace mun Sha aiki fa mijin Sabreen,Murmushi yayi yace mijin Sabreen ko ,nace ae ai nata ne ni da nazo temporary,hakane ya furta,nace na bar Mata kwanana gaba daya har na bar gidan nan na bar mata, jiya na kwana daya Ina ta irgawa kwanakin barina gidan nan kaga dai jiya aka daura kwana daya kenan, yace ke kin Isa kice Wai kin bawa wata kwananki ni fa Kinga ba abinda zanyi dake Hajiya,nace ai na sani nima ba so nake kayi wani abu dani ba yawwa ehe,Sabreen ce ta fito ta Sha wanka cikin kana nan Kaya tayi kyau tana zuwa sabon salo kujera ta ja ta zauna itama tare da furta Ina kwana Sweetheart, shi Kansa mamaki yayi bata taba gaisar da shi ba,sabo da Kar ya disgata yace lfy,ta ja cup ta hada tea dankalin gabana tasa Hannu ta janye da kwai sabo da tsokana,ban kulata ba na daure na share, Tsaki ta ja Wanda ya jawo Nawwar ya kalleta ya kamata tana kallona tana hararata, tace Yar tsuntuwa ma an iya girki ko a barikin Kika koya? Ko da yake ance karuwai sun iya girki fa,gashi kinci Sa'a kin auri daduronki,Nawwar ya Mata wata uwar tsawa, Murmushi nayi nace kyaleta ai gaskiya ta fada,Yar tsuntuwa ce Karuwa a da amma yanzu Kuma matar Nawwar dadiro na, na auri mijinki yanda ya narka kudi ya aure ni ke ba haka aka Yi ba,kyauta aka bashi ke lika masa akayi baya so aka Masa auren zumunci,kasa rike shi Kika Yi ya fita daukan karuwa Kuma ya sameni ya makale min da Kansa ya gani yace yaji a haka Yana so na sabo da idan bani to rayuwarsa tana cikin garari,ke ai kishin banza kike tunda baki San ma mene aure ba, da wata ce ke jiya a gidan nan baza ta iya bacci ba yanda muke zunduma ihun dadi daren amarci na tabbata da bakiyi bacci ba jiya to yau gidanku zaki tafi amma kina ta shaye shaye taya zaki sani Yar kwaya,Yar giya Yar Coccaine irinki dama wanne zaman aure zaki iya ai sai bacci...ya Isa haka bana son shirme Nawwar ya fada cikin fushi,na daki table da hanuna nace badai haka take so ayi ba to mu zuba mu indai fada ne harda na siyarwa dan kutmar...Dan me......shut up ya rike Hannu yace muje bana son rashin hankali,Yana Jana Ina tirjewa Ina wutsil wutsil Ina furta Dan babanki Yusuf da Uwarki Zuwaira munafuka Wanda basu iya tarbiya ba sai naci....Jana yayi muka haura sama da ya gaji ma Ina faman tirjewa sai ya daukeni cak,Sabreen ta saki kuka tana furta yanzu ta zageni haka a banza uwata fa Zuwaira tace yanzu Ina magana ta nada min uban duk ko ta gayyato karuwai suyi min jina jina to zata ci ubanta wlh nasan yanda zanyi tunda a fili tafi karfina.



   


*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_

 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


_nfection_

_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_


_Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._

*08089965176*

*07084653262*




No comments