Breaking News

TAYI MIN KANKANTA 37

 



*yanzu nima inaso anunamin kwatankwacin soyayyar asayi SHIMFIƊAR AURENA 500 kacal muci gaba da son juna😄*



*37*




"ke har yanzu baki girma da haye min cinya bane?"mummy ta faÉ—i tana shafa kan zahra.


Dariya tayi sannan ta ƙara gyara kwanciyar tata,tace cikin shagwaɓa"kai mummy,nawa nike gaba ɗaya na,naga har yaya ma hawa yake wani lokacin"


"ay duk kun dena hawamin,ku kawomin jikokina su hau"mummy ta faÉ—i cikin nishaÉ—i.


Shuru zahra tayi,batace komai ba se murmushi.dan batun ya bata kunya.


Suna nan zaune a falon daddy ya shigo falon se ƙamshin turare yake irin nasu na manya,yana ganin zahra yace cikim fara'a "yau ,zahran tawace agidan nan ah lalle mina da babbar baƙuwa"


Zahra wacce tun shigowarshi data shaƙi ƙamshin turarenshi zuciyarta ta fara tashi daurewa kawai takeyi,


Guri daddy ya samu ya zauna,sakkowa zahra tayi domin gaisheshi,amma ina aman daya yunƙuro mata be bata damar yin hakan ba.


Tuni ta gama ɓata gurin da aman,hankalin mummy da daddy ne yayi mugun tashi,mummy riƙe take da ita,daddy na jero mata tambaya"zahra me ya sameki dama baki da lafiya ne?"zahra ba baka se ido,ga wani sabon yunƙurin aman tanayi,


Kamata mummy tayi ta kaita ɗakinta,kai tsaye ruwan wanka ta haɗa mata,ta rakata har toilet ɗin ta rufo mata ƙofar.


Masu ayki mummy tasa suka gyara gurin,daddy kuma É—akinshi ya wuce yayo wanka,yasako jallabiya sannan yadawo É—akin mummyn.


Ay yana shigowa zahra taji ƙamshin turaren da gudu ta kuma komawa banɗakin,ta fara kyalaya amai,bin ta mummy tayi da sauri,ta riƙeta har ta gama,ta wanke mata baki da fuska,sannan ta kamota da nufin su fito.


Cogewa tayi a toilet ɗin ta marairaice fuska tace "mummy ki barni anan turaren daddy ne bana son ƙamshin shi,shine yake sani aman nan"


Wani farinciki ne ya ziyarci zuciyar mummy wanda rabonta da jinshi tun lokacin data samu cikin surayya,wanda har a fuskarta seda ya bayyana.


Sakinta tayi ta fito bakinta a washe,daddy dake zaune zaman jiran fitowarsu kallon rashin fahimta yake mata, yace"hajiya ina É—iyar tawa kika barota kikazo nan kina min dariya?"daddy yayi tambayar cikin É—aurin kai.

Dariya mummy tayi sannan tace"Alhaji to ay kai jikan naka kaine baya yi dakai,dan turarenka ne ke sawa yake wahalar maka da Æ´ar taka"


Janyota yayi jikinshi,yana murmushi yace cike da faraa"kina nufin zahra ta cikine da ita?"gyaÉ—a mishi kai tayi tana dariya.



Rungume mummy yayi cike da faraa,yana sumbatarta a goshi yace"tukuicin wannan albishir hajiya,zan sauya miki mota"


Sosai mummy ke godiya,daga haka sakin ta yayi yabar É—akin,fanka mummy ta kunna,ta buÉ—e windows,turaren yagama fita,sannan ta kashe fankar ta kullo windunan,ta koma toilet É—in ta kamota suka fito,ta kwantar da ita akan gado.


Abinci mummy tasa aka kawo mata taci,tasha ruwa,sannan mummy ta É—ibi jininta sannan ta bata Æ´at kwalba tayi fitsari aciki .

É—akin data ware a mazaunin asibitin tafi da gidanka ta nufa,taje ta gwada komai dan ta tabbatar da hasashenta,ayko sakamako na fitowa cikinne.


Sosai mummy ke godiya ga Allah daya ara mata tsawon rai na ganin wannan lokaci.


Hammad ko nacan cikin abokai anata chapter,jikinshi ne yaji be masa daɗi kewar matarshi duk ta dameshi,hakanne yasa yayi musu sallama gefin magriba,ya tuƙo motarshi zuwa gidan iyayen nasa.



Muje zuwa


No comments