Breaking News

TAYI MIN KANKANTA 12

 




*12*




A harabar asibitin yayi parking,sannan ya fito ya taka zuwa office É—in aminin nasa.


Da sallamarsa ya shiga office É—in cike da fara'a ya taso suka rungume juna,suna É—an dukan juna a baya,sannan suka koma kan doguwar kujera suka zauna.


Muhammad ne ya fara magana cikin yanayin damuwa"Abokina ina cikin damuwa fa,?"


"wacce irin damuwace wannan,?"abokin nasa ya buƙata cike da kulawa.


"jibi daddy ze ɗauramin aure da wata ƴar ƙanwarsa,na rasa inda zan tsoma raina".


A razane ya miƙe tsaye yana ja da baya,take duk wani annurin fuskarsa ya kauce kamar wanda yacewa gobe ze mutu.


Cikin kakkausar murya yace"HAMMAD kana nufin alƙawarin auren ƴarfillo daka lalatawa rayuwa yatashi a banza kenan?"


Miƙewa muhamnad yayi ya ƙaraso kusa da abokin nasa ya dafa kafaɗarsa yace"JAMEEL kafi kowa sanin irin son da nakewa ƴarfillo,wallahi babu macen dana keso a zuciyata sama da ita,kullum jameel bana iya bacci sabida ita,wallahi akan ƴarfillo zan iya ɓata ran kowa,sede itama wannan dazan auran akwai abun tausayi game da itan,kwatankwacin kaddarar data faɗawa ƴarfillo itama hakanne,wallahi zan auri yarinyar ne,kodan jihadin da zanyi na auranta Allah ya kawomin ƴarfillo na cikin sauƙi,pls jameel in baka fahimceni ba bame fahimtata"muhammad yayi maganar kamar zeyi kuka.


Waigowa jameel yayi,ya dubi hammad yace "b haka bane hammad ay kai mijin mace huÉ—une,bana de so ne sanadin auran da zakayi ka mance da Æ´arfillo shine yasa"


"har abada bazan mance da ita ba jameel,kuma zanci gaba da nemanta har se inda ƙarfina ya ƙare"Muhammad yafaɗi cike da tabbatarwa.


Jameel kwantar masa da hankali yaci gaba dayi akan auransa da zahra,inda yace ya daure yayiwa daddy biyayya hakanne zesa in ya kawo Æ´arfillo ya amince ya aureta.


Sosai Muhammad ya gamsu da shawarar aminin nasa,duka yakaiwa jameel yace yana dariya"wato jameel,da ace yadda kanka ke kawo wuta haka zuciyar ka take da nigeria batayi asarar soja ba,amma wai daga harbi ɗaya a baya,sega resigning letter wallahi ka bada maza,ay gashi nan ka ƙare a kallewa mata al'aura,da wuri zaka makance"ya ƙarasa maganar yana dariya.


Duka jameel yakai masa yace"ay duk namijin da baya gudu baya tsawon rai,da asara gara gidadanci,taya na hango lahirar nasha da ƙyar zan bari a ƙarasa ni,kaima kaga zaka iya ne shiyasa baka fita ba"


"bazan taɓa barin aykin soja ba Jameel sede in ze shiga tsakanina da ƴarfillo to tabbas zan fita".


Haka de sukai tayiwa juna barkwanci,basu rabu ba se dare,agajiye muhamnad ya dawo gida,zuciyarshi fal farinciki kamar yaga Æ´arfillonsa.


To bari mu waiwaya baya😄


Kowa ta turo data se in ci gaba😎


No comments