Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 8

 



Part 02 Page 8



gintse kiran hajiya qaraman tayi tana zake jan tsaki mai qarfi sosai,can gasan ranta tana in zafin tsawar da mansura tayi mata

"'Lallai duniya tayi lafiya" ta gayawa kanta da kanta,banda haka mansura ko kallon banza bata isa tayi mata ba bare tsawa har irin wannan. Qwafa taja tana dukan tafin hannunta da dayan hannun,ko a yanzun ta tabbatarwa kanta bashi mansurar taci,sai kuma ta biyashi da abu mafi zafi.


*_DR JARMA_*



Suna gama waya da fauziyya din ya ajiye wayar a gefansa yana binta da kallo,cikin shekarun nan yana samun kansa cikin nazarce nazarce,kamar ana yi masa bitar wasu kura kurai da ya tafka a shekarun raywarsa na baya. A yanzun bayajin zai sake tilastawa wani cikin 'yayansa yin wani abun daya zama ba bisa ra'ayi ko son zuciyarsu ba,hakan yasa duk yadda yaso ga kawo SÄAHAR cikin ahalinsa bai aikata hakan ba kai tsaye,saidai yayi wani abu da ya zama yayi pushing toufeeq din zuwa ga neman auren da kansa,ta yadda ko a gaba sunansa bazai fito cikin wanda yake ganin ya tilastashi ba,duk da yana jin alkhairai masu tarin yawa zasu fita daga gurinta tun saninta na farko da yayi a rayuwarsa kafin ma aje ga ganinta.


Wayar tasa ta sake qara a karo na biyu,ya waiwaya yana duban number da ake kiransa. Zumbur yayi yana sake zama sosai yana duban wayar,yakai hannunsa ya murza idanunsa cike da dumbin mamaki number wayar da ya mallaketa shekara guda kenan ya kuma gaza kiran mamallakiyar number, yau sai gashi number tana yawo saman screen dinsa a lokacin da bai taba zata ko kawowa ba. Haka kawai yaji ya gaza daga kiran,sai wani fat fat fat da girjinsa yakeyi,yau shi SHIFA ke kira? ,bayan tsahon was shekaru da suka shude da tarin galubale ZAQI DA MADACI?


Kamar wanda aka fuzga bayan tsinkewar kiran va sanya hannu hannun nasa yana rawa ya dauki wayar ta shiga bin kiran.


Shuru kaman ba za'a daga ba,yanata addu'a cikin ransa akan ta daga din,ya tabbatar bata da number dinsa ne kuma ko yanzu baya saka ran tayi saving kafin kiran nasa,yadda ta alqawarta masa a can bayan sai data tabbatar da halaccin haihuwarta,ta cika alqawarin,kamar yadda tace ta barshi har abada,amma akwai wata eana da zata waiwayi abinda ta haifa a cikinta. Ta barshi din,wanda kod wasa bata taba gwada nemansa ba,yaranta dai batayi fushi dasu ba ko ganqani,bata bari komai ya shafesu ba.


Tana dab da tsinkewa,kamar ba zaa daga ba sai kuma yaji an daga din,shuru ne ya biyo baya,abinda ya tilasta masa yin magana a wani yanayi dake nuni da kamar yana d'ari d'ari


"Assalamualaikum warahmatullah"


"Waalaikumus salam warahmatullah" ta maida masa amsa har sai da kowanne lungu na jikinsa ya amsa da muryarta,muryar da ya dauki shekaru masu tsaho ba tare da kunnuwansa sun jiye masa su ba,muryar da bazai taba mantawa da ita ba har abada


"Barka da wannan lokaci,na kira ke na shaida maka ni da ahalina zamu sauka a nigeria bikin d'ana kuma d'an uwa a garesu,zamu sauka cikin gidan d'ana in sha Allah,bawai ina gaya maka wannan labarin ba saboda neman izini 


kamar yadda ake bugata,na shaida maka

ne saboda kayi magana da 'yaruwarka,ka

gaya mata jiya ba yau bace,sannan muna

da buqatar zaman lafiya ayi biki lafiya

a gama lafiya kowanne bago ya koma

muhallinsa,gargadine wannan daga gareni,ina

fatan zaka isar mata" iva abinda ta fada kenan

ta yanke wayar.


Sosai qirjinsa yayi masa nauyi,ya fara jan

numfashi tare da fesar dashi


"Shifa,har yanzu tana nan da halinta bata

canza ba,babu daukan raini ko qasqanci,babu

gudu babu ja da baya akan gaskiyarta,sai

yaushe abubuwa zasu canza tsakaninta da

FAUZIYYA?" wannan din dukka halave da

dabi'arta ne. Bata yarda ta sakarwa abokin

adawa wasa ba,muddin ita ke da gaskiya sai

taga abinda zai turewa buzu nadi. Bai wani

damu da maganganunta ba,abinda yake kai

kawo tsakanin ruhinsa da zuciyarsa ya shafe

wannan. Gaba daya jikinsa ya saki,ya rasa

shifa shekaru masu yawa,kuma har yanzu

qaryarsa ta sha qarya yace ya samu koda rabi rabin madadinta ne. Shin meye abinda yasa ya kasa haquri da ita a wancan karon ne?.

FAUZIYYA sunan da yazo kansa, zalunci suka aikatawa shifa da gudunmawarsa kenan?, tambayar da tasa kansa sarawa har sai da yasa hannu ya riqe goshinsa da kyau. Dai dai lokacin da hajiya mansura ta shigo falon afujajan,zuciyarta cike da tsoro da fargabar abinda fauziyya zata iya aikatawa,gwara tun yanzu tasan wanne tudu ta dafa.


Guri ya samu ta zauna ba tare da tayi aakari da sauyawarsa ba


"Yanzu fisabilillahi Dr labiba tana da uba kamarka amma har ta rasa toufeeq? yaron da take mutuwar so?" Idanunsa ya aza a kanta,ransa ya darsu da mamakin me yasa kowa sai toufeeq?, cikin daurewa da son sake kashe wannan wutar yace


"Bance ya auri kowacce ba kamar yadda ban hanashi auren kowa ba,kawai abinda na sani shidin mijin mace hudu ne,kuma kowacce mace yakeso an bashi damar aurenta" shuru tayi ta rasa abun fadi,ranta na sake zafafa da abinda hajiya qarama tayi mata


"Haka ne,amma gaskiya ka jawa qanwarka kunne,na fara gajiya da gadararta da rashin ganin girmana,waishin ni ba matar yayanta bace? matsayin yaya kuma uwa nake dashi a wajenta fa" ji yayi kamar tana son hautsina masa kai,sai kawai ya miqe yana cewa


"Kunfi kusa" ransa a mugun quntace, da alama sam bata lura da yanayinsa ba,sai ya tuna wan! lokaci can baya,ko tuntube yayi muddin yaji zafi sai shifa ta gane,ya tuna wani lokaci acan baya sanda zuciyarsa ta afu ga rabuwa da ita.

Kamar haka yana zaune saita iskoshi,tayita tambayarsa abinda yake damunsa,a tsawace yace mata


"Kinga dalla malama kada ki dameni" bata yi zuciya ba,hakanan bata qosa ba ta juya zuwa daki ta dauko masa magani,ta fuskanci akwai ciwon kai saboda yadda yake riqe da kansa,fauziyya dake zaune a gefe tana masa sannu a jere babu gaqgautawa,ta biya kitchen ta debo ruwa ta dawo ta zauna gabansa,fauziyya na daga gefe tana balla mata harara,amma ko sau daya bata bi ta kanta ba,ta balle maganin ta miqa masa hade da ruwan


"Ka sha zaka samu relief, zuwa anjima idan bai sauka ba,akwai ragowar canji cikin salary dina dana yiwa yaro siyayya saika karba kaie asibiti"


"Yaaya,kada ka karba,wallahi ban yarda da maganin nan ba,don dazu wata qawarta tazo kuma na ganta da qulle quile a leda,suna ganina suka boye" ta juya da mamaki tana kallon fauziyya,daidai lokacin shi kuma yasa hannu ya tankwabe ruwan da maganin data siya da kudinta. Kallo daya tayi masa ta miqe tana zazzage rigarta data jiqe,ta waiwaya ta kalli fauziyya


"Shima wannan ya shiga sahun abinda nake neman haqqi a kansa a gurin Allah" daga haka ta taka ta bar musu gurin.


Tunaninsa ya yanke sanda ya isa bedroom dinsa,sai ya zauna yana sake dafe kansa da kyau gami da kiran sunan Allah


"'La haula wala quwwata illa billah"


********Tuni sãahar taci gaba da harkokin gabanta,don bata dauki auren a bakin komai ba,bata kuma daukeshi wani abu me muhimmanci ba,sam kai ba zakace itama daya daga cikin amare bace. Komai afifa ta zabar musu sai tace da ita


"Yayi?"


"Yayi" kawai take cewa,wani lokacin ma kO daga kai ta kalli abun bata tsaiwa yi take amsa mata da yayin,saboda a nata ganin dukka wadan nan abubuwan bata lokaci ne kawai,meye na dukka wadan nan abubuwan akan auren da bashi da maraba da auren haya?


Yadda suketa shirye shirye gadan gadan shine ya fara dawo da ita cikin hayyacinta,ya kuma ja hankalinta,tun tana daukan abun da wasa har ta fuskanci da gaske fa ake. Kamar zaa aurar da wata shahararriyar budurwa?, hidimar da sam a aurenta na farko ma baa yita ba,sai gashi yanzun shi wannan auren yanata samun tagomashi. Abun ya fara taba ranta,har taji bata qaunar ma ayi mata zancan auren,saboda ita gaba daya a yadda ta dauki abun,zai kawo sadaki ne akwai a daura auren,ta tattara dan abinda take da ra'ayin dauka ta wuce gidan ta tare a dakin fadeela suci gaba da rayuwarsu kamar baya. Saidai abun yazo da akasin tunaninta,siyayya taga anata yi babu kama hannun yaro.


********Misalin qarfe hudu na yammacin ranarta qule a dakin tayi zamanta tana chart,tun bayan isowar charifa qanwar mahaifiyarta daga nijer gaba daya ta sake quntata a gidan,kullum akwai tsirfar da inna charifa zata tsiro da ita wai da sunan gyaran jiki,abun har ya fara cikata,yau dai tayi mata tawaye tace babu me bata mata jiki da wasu kwabe kwabe. Baki inna charifa ta sake tana kallon säahar din,ba wani shekaru ta bata masu yawa ba,duka duka bazai wuce shekara bivar ko shida ba


"Wai nikam wannan auren na soyayya ne kuwa? ina cewa afifa ita ke tayani ma hada kayan,kafin na gama kintsawa ita ta shirya"


"ita tanaso inna charifa kiyi mata,ni ki barni hakanan,ban buqatar komai"ta fada tana murie dilka din data fara murza mata a hannu,sannan ta fice a dakin.


Ko yanzun da take zaune a dakin sai takejin zuciyarta na mata wani quna,wannan abun da aketayi ita bashi takeso ba,bashi da faida ma sam a gurinta, tamkar ana shelantawa duniya ne,abinda ita a ganinta bai zama dole ba.


Turo gofar dakin akayi,kuma koda bata daga kanta ba tasan afifa ce,saboda wani irin gamshi da inna charifa ke jigasu dashi ita da afifan. Duk da taqi bataso, taqi kuma bada hadin kai,amma tana gaunar qamshin sosai,yana mata dadi qwarai. Saman kanta afifan ta tsaya itama tana basarwa


"Ummu chamsiyya tace na gaya miki,ki hada kayanki yau,gobe za'a fita dasu tare da kayan kafi gaba daya" a wani matuqar qufule ta daga kai daga wayar da take dannawa ta kalleta


"Ya isheki haka afifa,ke idan kina rawar kanki a kan saiiad ki daina sakowa da säahar,kaya na a nan za'a barmin su,ba inda zani dasu"


"Hehehe… ...ke kikace kinaso,da bakice kinaso ba da ba'a baki shi ba" afifa ta fadi harda tafa hannaye. Al'amarin daya sake qular da sãahar kenan,sai ga idanu da muryarta dukka sun dauki rawa,afifan sam bata kulata,duk wasu tambotsai da takeyi bata taba biye mata,saidai ma ta manna mata hauka kamar yadda tayi mata a yanzu. Bata da zabi illa ta barwa hawayen damar zuba,zuwa yanzu ji takeyi kamar tace ta fasa auren,to amma tasan qaryarta tasha qarya,babu me kallonta ma bare ya saurareta,kuma ma idan tace ta fasa....wani dole za'a sanyata aura,wanda zata zauna garqashinsa ta zama cikakkiyar mata a gareshi,gara wannan,da an gama wadan nan filile fililen dole kowa ya sama mata lafiya, uwa uba ma kuma bawai binta gidan za'a yi ba bare aga yaya zatay zaman auren.


Ranar wuni tayi a daki,don inna

charifa tayi rantsuwa indai ta ganta a waje ba abinda zai hanata danneta ta shafeta da kayan gyaran,tasan tsaf zata aikata,don ita din cikakkiyar buzuwa ce wadda ke tafe da tsananta da qiba,tasan kuwa muddin ta tausheta a kalankasin jikin nan nata ko motsi cikakke ba zata iya ba bare ta qwaci kanta.

Koda inna charifa bata fadi haka ba dama yau din bata da niyyar motsawa ko ina,hatta da wayarta a silent ta barta,tana daga kwance saman gadon da yake tana fashin sallah,duk wani motsi da kai kawo dake faruwa daga falonsu zuwa farfajiyar gidan tana jinta. Gidan kwanakin nan da bikin ya matso ya fara rayuwa da shige da ficen jama'a.


Taji shigowar anty farheen ma amma sai ta qudundune a duvet,don ita kanta anty farheen din nemanta take yau kusan sati amma taqi zuwa,tasan muddin taje fiye da rabin zancanta na auren ne,auren da daga ita har wanda zai biya sadakin nata basu saka a ka ba,amma su anty farheen din duk sunbi sun addabi kansu,wai lallai sai sun gyarata,bayan abubuwan data dinga yi mata sati dayan da sukayi a Dubai, wanda sai da tayi da na sanin binta ma saboda dirke dirke da abubuwan data bata ta tilastata amfani dasu. Acewarta irin gyaran da za'a yiwa afifa ita ba irinsa za'a yi mata ba,amma dai tanason tsakanin afifa da ita a kasa banbancewa acan cikin turaka.

Randa ta fadi wannan maganar yini sãahar din tayi batayi magana da kowa ba,idan ta tuno maganar sai taji kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu. Wai da waye zata hada gado ma?,da toufeeq?,wannan mutumin da ko sunansa bata qaunar ji? tanata qoqarin danne action dinta akan auren don kada duniya ta fahimci AUREN MANUFA ne,to amma yadda suke nan nan da bikin idan ba'a yi wasa ba zata kai inda zata gaza ci gaba da boyewar.


Sake turo gofar dakin akayi,aka dan tsaya kadan a kanta na was mintuna kafin daga bisani ta magantu


"Maji nata kiranki amma tace no answer"


"Maji”?Ta maimaita sunan cikin ranta,a guri daya tasan me wannan sunan,kakar fadeela,ta kuma san afifa bawai sanin maji din tayi ba.


Mamakinta ya gaza bayyanuwa,ta yaye duvet din tana kallon afifa daie tsaye tanata gyalli hadi da baza qamshi


"Wacce maji din?"


"Uwar mijinki" ta fada gatsal kai tsaye. Duk duniya afifa ce kadai zata yi mata haka ta ayaleta,sai taja siririn tsaki ta ja duvet din da nufin komawa ciki, dai dai lokacin kira ha shigo wayar afifa dake hannunta

"'Yauwa gashi ta sake kira" afifan ta fada tana matso da wayar kusa da sãahar din.


Koda ta tsani toufeeq tana qaunar fadeela,hakanan tanason maji tana kuma qaunar nadeeya. Mutanene masu wani irin karamci tare da maida dan kowa nasu,suna da wani irin saugin kai tamkar ba daga jininsu toufeeq ya fito ba,ba maji ba,duk wata dake da shekaru irin nata ma ba zata iya wofantar da ita ba,do ta samu cikakkiyar tarbiyyar wannan daga gida,tilas ta miqe ta zauna sosai,ta miga hannu tana amsar wayar tare da jefawa afifa harara sannan ta daga kiran tana

karawa a kunnenta,dai dai sanda afifa ta watsa

hannunta alamun ko a jikinta ta fita tabar mata dakin.

[15/09, 5:29 pm] Laila Abdulqadir: *HUGUMA*


No comments