Breaking News

TABARMAR KASHI Book 2 Page 67

 "HUGUMA*



•_TABARMAR KASHI* 



Book 02 Page 67




• TURK'ASHI_*


Tarrrr baby fadeela da a lokacin da kwanan watan dake a rubuce b'aro b'aro ya nuna tana da shekaru uku ne a duniya ta bayyana,sanye da wata pink gown wadda tsahonta yake iya qaurinta, an raba dogon sassalkan gashinta gida biyu an matseshi da pink din bands gananu masu kyau‚ba takalmi gafarta sai pink sock's me ‘yar teddy qananu a samanta.


Tana tsave saman stair na can qarshe, bakin qofar da idan aka budeta zata sadaka da ainihin babban parlor zuwa bedroom din toufeeq. Bubbuga qofar takeyi a hankali tana faman kiran sunan ameesha 


"Mommy, Imommy yunwa nakeji, mummy kingi fitowa tun dazu,kizo ki bani abincin bacci zanyi mommy, mommy don Allah" daga yadda yarinyar ke magana tana goge hawayenta zai nuna maka ta jima tana bugun gofar, kuma tabbas har ta fara gajiya da bugawar. Zamewa tayi ta tsugunna bakin gofar dakin dai dai lokacin da video din ya dauko hoton hajiya qarama.


Cikin sand'a da alamu na rashin gaskiya ta zame takalman gafarta ta ajjiye gasan stairs din, ta fara takawa cikin sanda da takatsantsan, ta yadda ko cikakken motsinta baka isa kaji ba. Bata tsaya ba har ta cimma fadeela wadda ta bawa stairs din baya, babu kuma ta yadda za'a yi taga tahowar wani don kamar ma ta fara gyangadi a wajen.


Kamar qiftawar ido da budewarsa ta miga

hannunta ta finciko gashin kan fadeela ta wancakalar da ita , abinda yayi sanadiyyar wata muguwar gangarowa da yarinyar ta farayi ba matakala bayan matakala ba,'ah bibbiyu bibbiyu ta dinga tsallakewa jikinta da kanta yana buguwa ta kowanne sashe, kama daga tiles din dake shimfide a wajen zuwa garfen jikin stairs din


"Ab......mom....abbyyyy...." Sunan data furta kenan na qarshe ta qarsa gangarowa stair din garshe ji kake tassss! kanta ya bugu da marbles din.


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sãahar ta furta da garfin amo cikin gigicewa tana kama fadeela gami da kauda fuskarta daga gain jinin dake malala saman kanta. Tsam fadeelan ta riqeta da gaske,ga mamakin säahar kuka yarinyar ta saki


"Randa na fadin nan ko anty? tun daga ranar abby yace bani da lafiya,ashe fadowa nayi daga stairs" yarinyar dake lullube cikin jikin säahar ta fadi.


Tuni Dr jarma ya mige tsaye yanajin jikinsa kamar an kwara masa tafasashen ruwan zafi, maji kuwa tafukan hannayenta ta sanya ta lullube fuskarta tana kiran sunayen Allah duk nau'in wanda yazo bakinta cikin gigita da bada amannar tabbas fauziyya ba mutum bace.


Nadeeva gam ta rige maji tana wani irin kuka,tsoron haiiva garama yana mugun shigarta, tana jin kamar zata dauki wuga a yanzun nan ta sossoke cikin kowa a cikinsu.


"Bagar annamimiya ni zaki shiryawa wannan sharrin?.


"Shut up!, Ba sharri bane" toufeeq ya furta yana qogarin zaqulo nasa memory din ya jona musu da abinda suka gama gani yanzu. Doka wayar yayi da gasa saboda rawar da hannunsa yakeyi ya kuma samu ya cire memory din da gyar. Fusge wancan yayi ya watsar don ko ganin Ralarsa bayason yi ya saka na hannunsa.


A hankali video din ya fara da nuna blank kafin fitowarta daga bedroom dinta cikin tsakiyar daren tai zaman irga tablet din. Wani dadi ya ratsa hajiya qarama,qasan ranta ta cika da fatan ya kasance komai yayi formatting ne.


Tsulum kamar wadda aka jeho sai gata ta fito,wani annamimin gumi ya soma tsatstsafo mata ta kowacce kafa ta jikinta. Komai ya fara bayyana tiryan tiryan, tun daga nan har zuwa isarta dakin fadeela,musanyan magungunan da kalaman bakinta da sai da taji kamar ta hadiye kanta da kanta a lokacin


_bagar matsiyaciya,kin kusa fita daga rayuwata,kin kusa barin gidan nan, gidan nan gidan meenal ne, toufeeq da abinda ya mallaka dama wanda ubansa ya mallaka duka na meenal ne da abinda zata haifa_


*Qarya ta gare bori ya kar boka*


"Innalillahi wa inna laihi raji' un, allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahla,wa'anta taj' alal hazna iza shi'ita sahla" shine abinda Dr kawai yake fadi jikinsa na wani kakkarwa da mazari,ko ina na jikinsa yana rawa kai kace ciwon fargadiya yana shirin kamashi.


Duka hankula sai sukayo kansa,hankalin maji

'yayi mummunan tashi, ta dafashi da hanzari, toufeea ya garaso da gaggawa yana yunqurin zaunar da shi.


"Yaaya....don Allah yaaya!" Hajiya qarama dake gunjin kuka ta taso tana son isowa inda yake


"Kina garasowa nan zan manta dake wacace karki kuskura ki garaso nan, kiyi gaggawar fita a wajen nan,idan ba haka ba na sakar miki karnuka su yagalgalamin namanki da ranki!munafuka azzaluma annamimiya" Toufeeq din ya furta wasu hawaye masu tsananin zafi da radadi suna zartowa a idanunsa.

Idanuwan da sukayi wani mugun jaaa har baya iya ganin abinda ke gabansa sosai


"Yaaya..... toufeeq......


"Kibar gurin nan fauziyya,bana qaunar na sake ganin fuskarki har abada" Dr jarma da yake fusgar numfashinsa da qyar ya fada yana dafe qirjinsa,ji yake kamar zuciyarsa tana shirin bugawa.


Tunda uwarta ta haifeta bata taba ganin tashin hankali tozarta da abun kunya irin na yau ba,sanda take tafiya zuwa dakinta jiri ne yake angizata daga gaba zuwa baya. Meenal tana biye da ita itama cikin kukan,kukan nata da yake da nasaba da hango rasa toufeeq rashi na har abada. Yadda gaba daya parlor din ya rude ya birkice ya sanya dole maji ta gayyato juriya da dakiya irin ta uwa ta azawa zuciyarta da ruhinta, don dukkansu a yanzu suna bugatar wanda zai jagoranci tunaninsu ya kwantar musu da hankali


"Dauko mota Muhammad mu kaishi asibiti, nadeeya kira baaba rabi tazo takai sãahar daki ta huta, ki cire damuwa daga ranki, jarrabawa ce mun ganta kuma mun cinyeta a yanzun in sha Allah alhamdulillah, Allah dai yayi nufin sai mun gani ne kawai ki cire damuwa saboda abinda yake jikinki" dai dai toufeea ya dawo a gaggauce, ya kama Dr jarma wanda yaketa ambaton sunan Allah sanoda vadda numfashinsa da girjinsa suka rige va fita dashi zuwa harabar gidan. Sai da maji taga baaba ramatu ta kama hannun sãahar sun wuce daki da ita,tace fadeela ma ta zauna gudun shiga tunani sannan suka wuce asibitin.


Falon ya zamana babu kowa,hajiya qarama aneesa hajiya mansura da labiba sune suka rage.


Wata shu'umar dariya mansura ta saki, ta hada hannuwanta dukka biyun ta tafasu da kyau, tayi taku biyu ta tsaya gaban hajiya garama


"Tabbas abinda malam ya fada haka yake, faduwa guda biyun tawace da taki, nasara kuwa ta maji ce,a yau na tsinciki kaina banji takaici ko baqincikin yin nasarar wani ba..... Fauziyya kin dauka kai kadai ce kika iya shu'umanci? kin dauka ke daya aka yankewa tuggu cibiya a gabanki? kina tunanin zan zauna ne haka. sasakai kara zube ba tare da na tanadi mkaman gare dangi ba? bayan na san wacece ke?,ai duk makahon da kaii vace ayi wasan jifa to ya taka dutse ne.….na rasa mijina kin rasa dan uwanki!"


"Kin tafka babbar asara mansura butulu" dariva ta kece da ita


"Ashe? da kunya a idanunki har kina da bakin kiran wani butulu? ,kawai butulu sama dake? wadda taci amanar dan uwanta? taci amanar 'ya'yan dan uwanta? tunda kikaci amanar maji to tabbas ba wanda ba zaki iya butulcewa ba gwara ni.....kishiya ce kome nayi a kanta hada miji mukayi"


"Ke da gamawa da duniya lafiya har abada!" Hajiya garama ta furta a birkice tana jin kamar qwaqwalwarta zata hautsine


"Ke kuma idan aka leqa wuta ba'a ganki ba garwashin wuta ne ya rufeki fauziyya!"


"Dalla malamai ku gara gaba,yanzun ba wata sauran alaqa tsakaninmu daku" haseena da duka wadan nan maganganun basa gabanta ta fadi, don abu daya ke damunta a yanzu,ta yaya zata samu toufeeq?.


"'Me kike ci na baka na zuba meenal ya'aqoub aji?, awanni kadanne kuma suka rage muku a gidan nan yadda kuma ban samu toufeeq ba kema ke dashi saidai a hoto" labiba ta fadi tana jin sassaucin tashin hankalin data shiga a dazun, saboda tayi imanin ita da meenal dukkansu sun rasashi kenan.


"Zo mu tafi mommy bakin alqalaminsu suma ya riga ya bushe musu" labiba ta fadi tana damgar hannun hajiya mansura suna ficewa daga falon. Dukkansu ita da labiban zucivar kowannensu cike take da tashin hankali, komai sunayi ne kawai saboda idanun haseena da hajiya garama,amma sunyi amanna watan fara sanin wahala a rayuwarsu ta kama.


Kuka meenal takeyi sosai tana biye da hajiya garam cikin fushi da fusata da kuma tashin hankali, bata damu ko kadan da zubar hawayen idanun hajiya qarama din ba 


"'Ni duka bance kije ki aikata wannan abun ba,kinyi ne kawai saboda son ranki da biyan buqatarki,ni ba damuwa ta bane koma meye zai faru, kawai ni ki cikamin algawarin da kika daukarmin,ni toufeeq nakeso,na riga na tsarawa kaina da shi zanyi rayuwa" kalaman 'yar tata yayi mata tsauri da yawa, tana juyowa ta kwashe haseena din da mari


"Ban taba sanin baki da imani ba sai yanzu, kome da ake tuhumata akai fiye da rabi na aikata shine saboda jin dadin rayuwarki da kuma inganta rayuwar taki amma baki ganib..." Kafin ta rufe bakinta siraran yatsun haseena masu azabar zafi sun samu lafiyayyen muhalli akan fuskar hajiya garaman. Wani mugun shock ne ya shigeta har fitsari yana ballewa a wandonta,da gyar ta tattaro yawun bakinta ta hada kalaman


"Ni kika mara haseena ni uwarki da na dauki cikinki wata tara na haifeki?"


"To sai meye? don kece kika haifeni ai ba kece kika halicceni ba,ga mari ga tsinka jaka? ga duka ga rashin biyan bugata?, to tunda ke sauna ce kin kasa aiwatar da komai ni zan samawa kaina farincikin da kika gaza bani din" saita kewayeta kamar zafa bangaji kafadarta ta wuce dakinta da gudu gudu.


Sulalewa tayi ta zauna saman kujerar da tafi kusa da ita tana dafe da dukkam kuncinta guda biyu tana jinta kamar ba cikin duniya take ba. Tunda take a rayuwarta duk tashen gin jin maganarta taurin kai da* shaharar da tayi wajen iya garya da shirya makirci ko yayanta bata taba mari ba bare akai ga mahaifiya, sai gashi yau itace yarinyar data haifa,ta gwadawa gata fiye da kowa cikin duniya,taketa fadi tashin tara mata dukiyar da ko bayan ranta ba zata wulaganta ba,take ta yunqurin samar mata nagartaccen miji, yau itace ya shimfidawa fuskarta mari?.


Qarar jan luggage dinta ya sanya hajiya qarama din daga kai. Ta shirya abinta kamar yadda tazo cikin gananun kaya. Da sauri ta janye qafafunta wanda banda hakan tsaf zata murjesu tabi ta kansu ta miqe tana kiran sunanta


"Haseena baki da hankali ne? ina zaki haseena? wa kika sani?" Ta fada tana tarar gabanta cikin jin tsoron kada halayyarta ta tsananin fushi ta sanyata ta aikata abinda ba dai dai ba


"Dalla matsa ki bani guri,ni yanzu baki da amfani a gurina, toufeeq shine rayuwata, kuma na rasashi, tunda kuma na rasa shi a shirye nake na rasa komai nawa" ta fada tana jifanta da wani wulaqantaccen kallo sannan ta gogi kafadarta tana wucewa.


Tayi taga taga kamar zata fadi ta samu ta tsaya

kan gafarta, ta bude baki zata sake gwada yunqurin

tsaidata din sai sautin data sanyawa dukkan alert

massages na bankunanta ya fara tashi a jejjere. Da sauri ta miga hannu saman dan table din data ajjiye wayar dazu kafin ta fita tana dubawa, mamaki yana cikata na shigowar massages din a jejjere babu qaqqautawa.


"Na shiga uku......na lalace….meye haka?......kai jama'a

wayyo Allah na ku kawomin agaji….Zasu yasheni.......zasu talautani…..wayyo Allah wai ba kowa

ne a gidan" ta fada cikin budaddiyar murya tana kwasar hanya da mugun gudu tana fita daga sashenta.



Zafafabiyar

No comments