Breaking News

TABARMAR KASHI Book 2 Page 63

 "HUGUMA*



_TABARMAR KASHI*


Book 02 Page 63



"Me yasa Mohammed?" Ta jefa masa tambayar a mamakance tana karanto tsantsar duhun bacin ran dake qasan zuciyarsa, tana son karanto zuciyarsa kai tsaye, inn karatun da cikakkiyar uwar da tasan abinda takey, takewa yaron cikinta komai girmansa. Dauke dubansa yay ya maida gete ransa yana soyewa


"Zakiji maji a gaba, kiyimin afwa" shuru dukkansu sukayi shi da ita,jilkinta ya bata tabbas akwar wani gagarumin abu da ya faru,duk da ba'a shaidar dan yau amma ita din tayi amanna da Muhammad din d'ari bisa d'ari


"Shikenan,Allah ya rufa asiri" ta fada a sanyaye


"Ameen" ya amsa. Har ya miqe tace


"Ka dauki matarka ku wuce zan saki dakin dana Kama din tunda babu amfani, ruwanka ka taimaki likitocin Kan taimakon da sukayi muku don ku samu ganin diyoyinku, ruwanka kuma ka wargaza aikinsu" sai a sannan yaji kunya ta kamashi,yasa hannu ya shafi lallausar sumar kansa yana murmushi cike da jin kunya


"Allah ya saka da alkhairi ya qara girma". Kai kawai ta girgiza bayan wucewarsa, har ranta tana jin wani farinciki yana saukar mata,nutsuwa tana gauraye rayuwarta,ta tuna da darensu na jiya ita da Dr jarma din, komai nashi dare zuciyarta ya koma sabo. Yadda a ajiyan ya dinga bayyana mata bazai taba samun wata mace da zata maye masa gurbinta ba Itama tayr imanin hakanne a tata zuciyar, kawai tana ja masa aji ne saboda ya sake sanin muhimmancinta, tabbas, dan adam abun toro ne, kuma sharrinsa abun neman tsar ne.


_ya ubangiji dukkan wanda zai nufemu da sharri cutatarwa ko quntatawa ga rayuwa da farincikinmu,ya rabbus samawati ka shagaltar dashi da damuwoyinsa,kayi mana tsakani da shi tsayin nisan tazarar da bata da yaka don hasken fuskar annabi muhammad S A W.


*******

Qwarya qwaryar honeymoon suka gudanar a

Germany din tsakanin toufeeq da saahar. Wata irin narkakkiyar soyayya ce me matugar tsayawa a ral ke huda zuciyar kowannensu. Wani irin so me matuqar qarfi da tasirin karya kowanne qarfi kafiya zati da turjiya na zuciya. Karon farko saahar din ta koma masa tamkar wata raqumi da akala,gaba daya ya sauke mata tunaninta,ya goge haddar kanta tasss!!' ,ya tsiyayar mata da man kai babu wani abu da yayi saura cikin zuciya ruhi da gangar jilkinta sai MUHAMMAD TAUFEEQ din.


Gwarzon namijin da cikin lokaci qalilan ya tabbatar mata da karin maganar nan ta hausawa da suke cewa MAZA SUNA SUKA TARA Kuma KOMAI LALACEWAR AL' UMMA AKWAI NA GARI. Yayi nasarar cisge kowanne mummunan tunani a ranta damuwa da bad memories dake damunta,ya maye gurbinsu da wata zazzatar qauna soyayya da zallar kulawa. Irin nau'in kulawar da ta sanya ta dinga hango tsananin wauta da sokonci da take kallon abinda adam ke mata a baya da sunan KULAWA,sam sam babu hadi tsakaninta da wanna kulawar ta ainihi da toufeeq yake nuna mata. Sassanyar soyayya me tafiya da imanin diya mace, duk kuwa da cewa bashi da damar shiga gonarsa yayi ban ruwa,amma a hakan daga ita har shi cikin wani irin aminci suke.


Baisan lya adadin sau nawa bakinsa ya furta godiya ga ubangiji ba,wato inda Ubangly bai cire ameesha daga rayuwarsa ba haka zai tabbata cikin quncin kurkuku da sunan AURE?,haka zai dawwama cikin mayaudariyar soyayyarta wadda bata da ma'ana ko gardi ko kadan?,cikin kwanakin KHADIJATU SAAHAR ta zame masa ALJANNARSA TA DUNIYA kamar yadda taci alwashi. Komai nata a nutse yake da want inn tsari me tsayawa a zuciyar namiji,tana da want irin Kula da takatsantsan a komai nata da sanya farincikinsa a gaban nata. Sun hadu sun kulle sun dinke sun zama cikakken abu guda.


_RAMIN KARYA kurarre ne_*



karfe uku na rana jirginsu ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na mallam aminu kano dake garin kano. Jirgin da yayo dakon iyalin DR MAHMUD JARMA da kuma surukansa. Toufeeq da sahar,dr din da kansa

• da sarautar mata maji, afifa da hayatee dinta sajjad, sal kuma sister nadeeya da shalelensu fadeela, daga gefe kuma hajya qarama ce dake ankare da takun kowa,cikin ranta da zuciyarta kuma tana jin duk wannan scenes din ya qare tun a Germany,dukkansu sun gama cin gaajiyar soyayyarsu, a yanzu lokaci ne da kowa zai girbe hukuncin data tanadar masa.


Duk da haka babu abinda ta tsana irin idanunta su sauka akan maji da Dr, ko kuma säahar da toufeeq,basu ba hatta nadeeya ta sakawa ranta wannan karon ba zata sassauta mata ba,ita kanta afifa saita fita daga da'irar danginsu tunda ta silar saahar ta shiga family din.


lauranin masoyan guda biyu,zaka rantse da Allah saboda hutunsu da jin dadinsu yasa aka shirya tafiya garmany, daga toufeeq din har saahar sunyi wani irin kyau sunyi fresh cikin sati biyun da suka qara akan kwanakin da suka shirya tahowar. Saahar ya hade mata da yanayin cikinta wanda ya samu cikakkiyar kulawa da tabbacin zamansa dai dai bisa mahaifarta, ya kuma sake zuba mata wani irin kyau kamar 'yar sarkin aljannu.


Toufeeq kuwa zai iya cewa kafff! Tsahon rayuwarsa bai taba samun nutsuwa makamancin wannan a rayuwarsa ba,nutsuwa ta ainihi tun daga gangar jiki zuwa ruhi.


Ko da soyayya bata burgeka kana kallonsu zasu baka sha'awa ta kowacce fuska,sai nan nan yakeyi da sahar din tamkar sarauniyar matan duniya, o yaya ta motsa sar ya tambayeta


"Me kikeso ne moonbeam?" A sannan dumin jikinsa kadai take bugata,amma tana jin kunya da nauyin nuna masa,ta tsinci kanta a wani yanay na tsananin son kasancewa dashi. Sanda ta fahimci hakan hankalinta ya tashi,ba da wanda zata iya maganar dashi sai bestie dinta.


Dariya afifa tayi sosai kamar zata kifa akan dan matashin cikinta,har sai da saahar da zuciyarta yanzu yanzu zakaga tazo kusa tace da ita


"'Ki yarfani yadda kikaso,dama aini na kawo kaina ko?"


Rigo hannunta afifa tayi tana qoqarin saita kanta


"Ki yafemin Bestie, Allah bazan ya riqe dariyata bane, nasan wannan yanayin zar yiwa moha dadi qwaral,ashe akwai wanann lokacin zaizo?"


"Ban sani ba,sakeni"


"Zauna kiji" ta fada tana daidaita dariyarta,sannan ta zauna tana fuskantar saahar din.


"Akwai yanayi irin wanann dake iya samun mace me ciki dama, saboda qaruwar hormones dake jikinta, amma karki damu,tunda kwanakin da zaki wake ki koma mu'amalarku yayi,ba wani matsala, kibar toufeed yaci karensa kawai babu babbaka,nayi imanin zai sake haukace miki ne kawai, saboda a yanzun jikinki na sakin sinadaran da suke sake maida mace cikakkiya qwarai,kada ki damu,zan fahimtar da hayatee,ya daukawa yaa toufeeq hutu a kowanne branches na Kamfaninsa dake kowacce qasa har sal ya gama biyan bashin dake kansa" dariya wannan karon bestie din nata ta bata, sal kawai ta dungure mata kai,amma qasan ranta kunyar aritan takeji,itama ta fahimci haka sai tace


"No boundaries between us bestie, komal nawa ya shafeki, kamar yadda komai naki ya shafeni".


"Tunanin me kikeyi moonbeam?" Ya tambayeta yana dan Jan hancinta,kanta yana kwance akafadarsa


"'Ba komai" muryarsa ya sassauta yana yin qasa da muryarsa


"Na gane komai fa, kuma zan biya duka basussuka,ina

• tsoron qetare ryaka ne maji tace nayi wani abu da ba dai dai ba ta daukemin Kai,shi yasa nayi kawaici na qara wadan nan kwanakin akai, amma definitely am craving for you" sunne fuskarta kawai tayi ta rasa amsar bashi.


Madubi hajya mansura ta dauka tana sake kallon fuskarta da kyau, kamar yadda labiba ta kasa zaune ta Kasa tsaye,duk bayan mintuna saita duba make-up din Tuskarta. Dukkaninsu ita da mahaitiyar tata sun shirya tarbar uba da dansa, bayan cikakken shiri da kuma tabbacin da suka samu daga bakin sabon boka na musamman da mansura ta canza saboda gain bayan hajiya qarama. A yau din kacokam ta sauka gidan toufeeq don tarbar mijinta, labiba kuma ta tarbi touteeq ta Kuma ci gaba da zama a gidan tana farautar zuciyarsa kamar yadda tayi imanin hajya qaraman na cusa haseena cikin lamuransa ta qarfi da yaji don samun shiga a wajensa. Taci alwashin wannan Karon babu gudu babu ja da baya, kanta tsaye zatayi fito na fito da hajiya qaraman,ta kuma gama shirya duk wata hujja akan hajiya garaman koda zata nemi kawo mata wargi ko ta Kawowa shirinta tarnaqi. Manya manyan hujjoji ne da ake tanada saboda rana irin wanann,manyan hujjojin da kake ajjiyewa saboda tarwatsa maqiyi kuma abokin adawa a duk sanda yakejin zai tsallake lyaka da kuma gonarka.


Karo na uku hajiya mansura ta sake leqawa da

Kanta farfajiyar gidan ta window din sashen Dr jarma wanda bazai iya tuna yaushe rabonsa da shi ba. Da kanta ta sanya akayi masa gyara na musamman saboda zamanta a nan dinne kadai zai iya bata damar aiwatar da burinsu hankali kwance.


Duk da ta fara qaguwa da jiran isowarsu amma zuciyarta fes take saboda albishir din data samu daga mutumin da take Kira da malam.


"Akwai nasara a goben guda d'aya,akwai faduwa da asara guda biyu" bayanan da yayi mata kenan, bayan ya sake bata tabbacin hajya qarama na daya daga cikin faduwa da asara guda daya cikin biyun da ya lissata


"Nike da nasara!, tabbas nike da nasara!!" Abinda ta maimaitawa kanta kenan,saboda tako ina idan ta juya tunanita nasarar take hangowa kanta,cikakken shirt ta yiwa kanta da take da yaqinin babu faduwar!!, nasarar dal!...


-tofa jama'a, maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta,maga wake da nasarar,wake da asarar da kuma faduwa_


Zafafabiyar

No comments