Breaking News

TABARMAR KASHI Book 2 Page 61

 "HUGUMA*




• TABARMAR KASHI_*



Book 02 Page 61



Shuru ne ya ratsa dakin, nauyi kallon da yake mata ya yiwa idanu da gangar jikinta, saita zame idanunta zata sunkuyar da kanta qasa.


"Mom twins" ya furta a hankali yana jin farinciki yana ratsashi. Qaramin murmushi ta saki a kunyace tana maida kanta gefe,sai yasa hannu ya juyo fuskar tata


"Ki gayawa maji ba zaki ba.......am telling you akwai matsala, komai zai iya faruwa kika bita" fararen idanunta ta daga ta kalleshi tana dan bata fuska


"Maji din? i can't* sosal ya sake zubawa fuskarta ido,sai tadan ja da baya kadan tana sake dubansa


"What do you want from me?" Ta samu kanta da furtawa ta yadda labbanta kawar ya iya kalla ya fahimci me tace


"I want to wakeup to you every morning and fall asleep to you every night ban shirya bin tsarin maji ba,please help me, tell her zaki iya warkewa koda muna tare" ya qarashe maganar yana sake matso da fuskokinsu kusa dana juna,har tana iya jin fitar numfashinsa sosai.


Idanunta ta lumshe tana jan ajiyar zuciya


"Bazan iya gaya mata ba" ta fada a shagwabe, har sai da tsigar jikinsa ta zuba


"'Zan gaya mata ni, zance mata ni dake duka bama so"


I "No please"


"'Whay?" Ya tambayeta still idanunsa suna cikin nata suna wani irin narkewa da gaunarta


"Inajin kunya"


"Ni kuma bana ji" wani garamin kukan shagwaba da

batasan daga ina yazo ba ta shiga sauke masa, take ta soma kunnashi,jikinsa duka ya amsa. Hannu yasa ya jawota ta fada jikinsa, sautin qaramin shagwabben kukan nata yana sauka a wuyansa yana ratsa tattausan gashin fuskarsa yana taba kunnensa kadan kadan


"If you kiss my neck, am not responsible for what

happens next" yayi maganar kamar yana rada mata a kunne. Da sauri ta janye fuskarta daga gareshi, amma sai yayi caraf ya rigota yana ritsata da narkakken kallonsa


"| crave you emotionally and physically do you even

realize how amazing you are to me?" Kasa bashi amsa

tayi, saboda kalamansa suna mugun kashe mata jiki tare da dasa wata sassanyar soyayyarsa mai matugar garfi a jininta


"Am sorry" ya sake cewa,yadda yayi maganar ya sakata daga kai ta kalleshi


"Sorry for what?"


"For loving you too much" dukka hannayenta ta bude ta zagaye bayansa dasu,ta kuma kwantar da kanta a girjinta, sosai take iya jin bugun zuciyarsa cikin kunnuwanta,da muryarta mai laushi da wani irin nutsuwa tace mishi


"Kalamanka suna da zagi kamar zuma,All very sweet,i'll never get enough of you,i want to spend the rest of our lives together, baka qetare iyaka bai feel the same way and i can prove it to you in sha Allah" ta qarashe maganar tana cusa kanta a tsakiyar qirjinsa saboda nauvinsa da takeji.


Kamar me jin bacci haka ya dinga lumshe ido saboda zagin da kalamanta sukayi masa


"You're the only person who makes me smile constantly" ya furta yana qoqarin daga fuskar ta daga qirjinsa,a sannan yaji ba abinda yake buqata irin ya dandana lips din da suka furta masa wadan nan kalaman masu zaqi


"Your lips on mine tell me better than your words" ta fahimci kiss yana daya daga cikin weakness dinsa,kuma babu abinda zai hana maji tafiya da ita,don haka ta bashi cikakken hadin kai tare da maida masa martani me kyau.


Basusan me vake faruwa sai muryar maji da sukaji tana fadin


"Subhanallahi" shi ya fara zare fuskarsa daga tata tare da rigeta da kyau don kada ta firgita. Basuga maji din ba sai gofar data maida ta rufe da sauri tare suka dauke idonsu daga kan qofar suka mayar fuskokin juna. Tuni kunya ta lullube sãahar,ta kebe baki zata masa complain, ya dora yatsansa saman lips dinsa da sukayi jaa


"Shshshsh" vace da ita saita maida maganar da tayi niyyar yi din, abinda ya bashi daman gyara mata gashinta da ya hargitse. Yanayi yana kallon cute face dinta,ba magana a tsakaninsu sai bugun zukatansu kawai, kowa na tuna tarayyarsa tare da dan uwansa.

Yana gyara mata yafen mayafinta nadeeya ta tura gofar ta shigo,ya juya ya watsa mata wani kallo saita koma ta lafe tana cewa


"Maji ce ta aikoni,wai anty N ta fito"


"Bacemin daga gun" ya fada adan zafafe, sai ta juya ta fice tana gunshe dariya. Tunda taga maji ta fito tana

maimaita salati tasan tayi gamo ne.


Ba jimawa wayarsa tayi qara,daya duba yaga maji ce dole ya daga


"Okay to,in sha Allah" yace yana ajiye wayar,sai ya miqe yana zube hannayensa a aljihunsa yana dubanta,sai kuma ya miga mata hannun nasa, ba musu ta dora nata hannun saman nashi ya rige da kyau ya tasheta tsaye.


Duk inda suka gifta sai idanu yakai kansu tsakanin turawan dake kai kawo cikin asibitin, sai daya kaita gurin fadeela sukayi sallama sannan suka wuce gurin ajiyar motoci na asibitin inda taxi ke jiransu. Da kansa ya bude mata back seat kusa da maji,ya mayar ya rufe ya matsa baya yana folding hannunsa a qirji. Duk duniva banda maji ba wanda zai yadda yayi masa hakan,yana tsaye yana kallonsu har motar ta tashi suka fice a asibitin, ya bita da kallo yana jin kamar wani sashe na iikinsa ne aka tafi dashi


"Mr man" ya tsinci muryar sajjad daga bayansa, koda ya waiwayo sai ya dinke fuskarsa tsaf saboda yasan tabbas tsiya sajjad din zaiyi masa


"Muje ka rakani wani guri" yace da saijad din,sai yayi gaba yana biye dashi shima dai dariyar yake boyewa.

Kafin su isa already ma'aikatan hotel din sun gama shirya dakin. Sanda Dr jarma yaga maji na maida luggage dinta dakin sai ya kalleta


"Kada ki fara shifa indai baso kike muyi abun kunya a gaban surukarki ba" kallon shakulaton bangaro ta watsa masa


"Ai ba damuwa"


"Haka kika ce?" Ya tambayeta,sai bata amsa masa ba kawai tayi gaba abinta.


Tunda maji ta shigo dakin sam sãahar ta kasa sakewa,kunyar yadda ta gansu dazu ne keta dawainiya da ita.ko hada ido da ita ta kasa. Itama majin ta fahimci hakan ta kuma tabbatar idan tace tare zasu kwana zata kwana ne a takure,sai ta aika nadeeya toilet tace ta hada mata ruwan dumi ta shiga tayi wanka.


Shigar nadeeya toilet din sai ya zamana saura su bivu.a tausashe maii din ta kira sunanta.ta amsa ba tare data lya daga kanta ta dubeta ba


"Ki saki jikinki dani ba abun kunya kikayi ba,mijinki ne kuma lada zaki samu, saidai abu daya nakeso, ki kula da kyau saboda mu tsira da wadan nan bayin Allahn,nasan me yiwuwa ne moha bame haquri bane a take takensa dana gani, that's why na daukoki,kina cika kwanaki goman da likita ya fada zan maida masa ke, karki biye masa azo ayi aikin dana sani" kai ta gyada a mugun kunyace, dai dai sanda nadeeya din ta fito tace ta gama, ta miga mata babban towel ta zauna shirya musu abincin da aka kawo musu daga restaurant a hotel din.


Tare da maji din sukaci abincin dare,Dr mahmud na dakin hajiya garama yana fama da koke kokenta da a yau yakejin kamar yayi mata dukan tsiya,yana mamakin yadda ya dinga dauke wadan nan abubuwan nata tsahon shekarun, bai kuma taba ji ya gajiya ba sai yanzu?.


Maji tanata kaffa kaffa da sãahar din, sai data tabbatar taci abinci da kyau,ta kuma tambayeta bata bugatar komai sannan tayi musu sallama ta fito.


A qofar dakin sukayi kacibus da dr jarma,sukabi juna da kallo,sai ta kauda kanta tana mamaki, da gaske zaije ya taho da ita din kenan?, tana jin sanda ya saki ajiyar zuciya tare da wani qaramin murmushi ya juya ya rufa mata baya.


Sai da suka dan taba hira da nadeeya kan yadda fadeela ke sake warwarewa da farincikin da yarinyar ke nunawa duk sanda aka gaya mata ta daina irin faduwar nan da takeyi


"Kinsan daxun me tace?" Kai säahar ta girgiza tana murmushi


"Bansan waye nafiso tsakanin anty N da abby dina ba" murmushi ya kubcewa säahar, Allah ne kadai yasan me ya ajjiye tsakaninta da fadeela tun bata wani santa ba amma Allah ya jarabceta da tausayin yarinyar, kafin daga bisani a hankali ya koma gauna, gauna tamkar ta d'a da uwa


Sai sha daya saura na dare sannan suka kwanta

kowa saman gadonshi. Dakin ya dauki shuru,sai dim light da nadeeya ta sanya musu,a hankali sai kwanyarta ta tafi tunani, ta maida idanunta ta lumshe. Ba abinda ke mata kai kawo sai fuskar toufeeq a mabanbantan gurare, tun daga farkon haduwarsu har zuwa yau cikin Saarland university hospital.


Doguwar ajiyar zuciya ta saki, tana gyara

kwanciyarta da taji sam batayi mata dadi ba,saidai duk da gyara kwanciyar da tayi hakan bai sanya taji dadin makwancin nata ba


"'Wai kewarsa nake?" Ta tambayi kanta cike da dimbin mamaki


"'Yes you missed him" wani sashe na zuciyarta ya bata amsa. Idonta ta sake lumshewa tana hasaso taushi dumi da kuma sassanyan qamshin dake fita ko yaushe a jikinsa


"Da gaske ni munafukar kaina da kaina ce" ta fadawa kanta da kanta qaramin murmushi yana subuce mata

Ashe duk yadda taje avoiding nasa a baya duk sanda yayi nufin rungume ta,ashe da gaske da yace tana pretending pretending din takeyi


"Ya Allah" ta fada gasan ranta tana runtse idonta. Sansa ta bude idanun nata ta danna wayarta don duba lokaci.


Har sha biyu saura na dare, ta sake maida idonta ta kulle ranta yana jagulewa gaba daya,wani matsanancin kewarsa tana ratsata har zuciyarta na quntata sosai. A karo na biyu ta sake bude idanunta, hakan yayi dai dai da hasken da wayarta tayi,ta miga hannu ta jawo wayar tana dubawa.


Sunan nan nasa ne da nadeeya tayi mata saving a wayarta ya bayyana. Tayi dan Jim,sai kuma taji ta cika da zumudin ganin abinda sagon ya qunsa,ta bude a nutse ta duba


_how are you?_ yace a taqaice, ta sauka qasa a hankali ta maida masa amsa a taqaice itama,ranta yana mata babu dadi, saboda ta saka ran jin kalamansa masu dadi da sukafi haka dadi a zuciyarta,saita tarar da gajeran

sago


_am fine_ ta amsa tana maida idanunta ta lumshe, qasa da second biyar taji alamun shigowar wani sagon


_are you sure?_ tabe baki tayi kaman zata saki kuka,saita maida masa still a taqaice


_"yeah i said am fine"_. Wannan karon ko idanun bai bari ta rufe ba ya maido mata amsa


_tell me the truth_


"Haka kawai zuciyarta tayi rauni, idanunta suka cika sosai da qwalla, kewarsa takeji ba dan kadan ba,a gaggauce ta maida masa itama


_i miss you okay?‚i miss you so much, and it's killing me_


Qaramin murmushi ya saki vana sauke gafafunsa dake saman qaramin glass table din dake gabansa,tsam ya miqe tsaye yana zura wayarsa cikin aljihun ya wuce can cikin daki ya jawo luggage dinsa ya soma cire wasu kayan yana fidda na jikinsa.


Minti daya biyu uku har minti goma tana jiran taj§ amsa daga gareshi amma shuru kakeji,ta rufe idanunta ta kuma bude har batasan iya adadi ba, qwallar da take


•I rigewa sai gata tana saukowa,me yasa ta zura jiki haka ta fallasa masa sirrin zuciyarta?. Sanda ya cika mintuna talatin sai ta gaza daurewa,ta sake daukan wayar ta rubuta wani sagon a tagaice


_hey,why are you not replying?_ tana turawa ta saki ajiyar zuciya tana dora wayar saitin fuskarta. Minti daya tak wayar ta qara haske

_am sorry. Am here front of your room, come outside and see me_ miqewa tayi ta zauna ba tare data zata ba tana raba ido, saita maida idanunta bakin qofar tana tantama. Taba qofar kadan taji anyi, mamaki sosai ya cikata,ta zamo a hankali daga saman gadon ta zura slippers ta nufi qofar dakin,ta murza key din ta cireshi daga jikin qofar, kafin ta bude har ya murda handle din qofar ya turota,sai taja da baya tana dubansa ta hasken waje daya ratso dakin mamaki yana kasheta.



Zafafa biyar

No comments