Breaking News

Tabarmar Kashi book 2 page 60

 "HUGUMA*



_TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 60



"'Excuse me" Dr marhooma ta fada tana tashi hadi da fita daga office din. Da gyar ya zare idonsa daga kanta

kamar zata bace masa idan yabar kallonta ya fidda

wayarsa yana jin qirjinsa har yanzu cike da farinciki,ya

rasa dawa zai fara wanna maganar, idan ya kira sajjad

yasan tabbas! Tsiya zaita masa, infact ma zai addabeshi

ne ya buwayeshi, qila har sai dr yayi musu tsakani ma.

Maji dinsa ce ta fara fado masa a rai, fuskarsa na fidda

murmushi ya soma neman layinta yana qiyasta irin

farincikin da labari zai bawa zuciyarta.


Tun da safe yake aikin lallashinta har sukayi

breakfast sukayi shirin wucewa asibiti shi da ita,sai nan nan yakeyi da ita da al'amuranta yayin da ita kuma take basarwa a shekarun ita kadai tasan yadda ta rayu, cikin baqinciki da daci da qunar rai, inda Allah ya taqaita wahalarta ita din me yawan addu'a ce, bata wasa sam da addu' a,amma abune mai matugar ciwo ka bawa mutum rayuwarka ka zauna dashi fisabilillahi amma ya jefeka da miyagun kalmomi,yasa hannu ya tankwabe dukkan wata kyautatawa taka ya kuma yi maka kallon maciyin amana.


Ko yanzun data gama saka komai cikin handbag dinta caraf yayi ya kama hannun jakar ya riqe, ta waiwaya ta kalleshi ya marairaice mata gaba daya,sai taga ya koma mata mahmud dinta zam a zamanin quruciya da samartaka


"A saussautamin mana shifa ta,ko don idanun yaran nan‚banason su fahimci abinda yake faruwa"


"Sakarmin jakata,meye ya rage dama wanda basu san ka viwa uwarsu ba"


"Bakina bazai gaji da neman afuwa ba" ta fuskanci ba sakar mata jakar zaiyi ba,ita sai ta sakar masa tayo gaba ya biyota a baya. Dakin su nadeeya suka wuce don duba hajiya garama.


Nadeeya na fesa turarenta itama ta gama shirinta sukayi sallama suka shigo. Tana zaune saman gado, idanu da kuma fuskarta dukka sun wani qoje,dare daya Allah ya saukar mata da wani irin rudani da razani daya sake firgita nutsuwarta ya kuma hana jininta saukowa kamar yadda likitan yakeso.


Da sauri ta kauda kanta daga kallon maji, cikin ranta tana jin yadda ta muzanta, majin kuma na mata wani kwarjini da cika mata ido. Tayi kyau sosai cikin wata doguwar riga data dorawa madaidaicin hijabi, fuskarta da jikinta suna nuna nutsuwa kwanciyar hankali da kuma cikakkiyar kamalarta,abubuwan da ta tabbatar itadin ta rasa dukkansu.


Cikakkiyar sallama majin tayi wadda ta sanyawa hajiya garama faduwar gaba, bata ma iya amsawa ba sai nadeeya ce ta amsa, ranta na mata wani irin dadi. Ashe dama haka tarayyar iyaye biyu yake? a duk sanda taga maji da Dr a tare, sai taji kamar an sabunta mata duniyarta,ita ta yiwa majin da Dr gurin zama,sanann ta koma gefe tana hada tarkacenta cikin jaka.


Da dr suka fara gaisawa, gaba daya ta zama wani iri, ciwo kam ciwo yana mintsinin zuciyarta,iya kallon maji da Dr kawaj a mazaunin miji da mata a karo na biyu kadai ya usheta masifa da tashin hankali.


"Sannu da jiki" maji tace da ita a taqaice tana maida hankalykan wayarta da kira ya shigo. Qasa qasa hajiya garama din ta amsa, hankalinta nakan maji amma idanunta akan Dr suke da yake tambayarta tasha magani da abinci.


Murmushi ya subuce mata ganin toufeeq ne

yake Kira

"Assalamualaikum, Muhammad" maji ta fada tana murmushi. Kiran sunan kawai ya sanya hajiya qarama faduwar gaba,ya kuma gara sanyata maida hankalinta kan maji cike da mamakin toufeeq ne yake kira? ita ta mance ma lokaci na garshe rabon da yayi kiranta

"Lafiya alhamdulillah....too.... Ma sha Allah,ma sha

Allah,gamu nan a hanya muma zamu iso" saita katse wavar bakinta na furta

"Alhamdulillah zahiran wa bad'inan" Sai ta sauke wayar daga kunnenta tana murmushi sannan kuma ta mige

"Zan jiraka cikin taxi, marasa lafiyan sun garu" daga kai

Dr jarma yayi ya kalleta

"Waye kuma ba lafiya?" Murmushi ta kuma saki

"Surukarka zasu yiwa daurin mahaifa, Allah dai yayi cikin me zama ne, ba duka bane suka fita" muraran farincikin

Dr iarma ya kasa boyuwa


"'Ma sha Allah,nima yanzu zan fito" yace da mail


"'Allah ya kiyaye gaba fauziyya" maji ta fada tana ficewa abinta. Tsabar bagincikin da yake sussukar zuciyarta kasa cewa komai tavi. Ga mamakinta shima dr jarma din migewa yayi


"Zamuje wuce asibitin, daga nan akwai inda nakeso muje ni da maji din, inaga nadeeya ke ki zauna da ita kada a barta ita kadai,idan akwai wani damuwa saiki kirani" dr jarma ya fada.


"Don Allah abba zan biku, zaman hotel babu dadi wallahi" nadeeya ta fadi kamar zata saki kuka

"Jeki nima bana bugatar zaman naki" hajiya garama ta fada a qufule zuciyarta kamar zata fado gasa, cikin kwana biyu kacal ta fahimci yarinyar gaba daya ta canza itama, kamar bata Santa ba,duk wata damuwa da kulawa da take bata koda tana zazzabine yanzu babu shi


"'Ni nace ki zauna nadeeya,ya za'a bar mara lafiya shi kadal?"


"Taje yaya, kaima ka tafi bare ita" ta fadi tana jin kamar zata saki kuka


Tuni nadeeya tayi gaba abinta, don bata tsaya bama bare ta gane yadda suka qare da abban nata. Kasa zama guri daya hajiya qarama tayi, takai ta kawo ita kadai yau itace a wulaqance haka?,cikin dakin hotel bayan tana fama da ciwo? yau itace ba wanda yake daukan maganarta da muhimmanci bare ace za'a yi amfani da ita? anya batayi sake ba? zaman me ma takeyi ne wai a Germany? bayan matsaloli na shirin rufto mata su murqushe dukkanin nasararta?.


Ba'a jima ba suka gama mata daurin mahaifar aka dawo da ita daki, saidai sun roqi alfarma an dawo da ita department din su fadeela kusa da dakin fadeelan saboda abubuwa sufi yi musu sauqi. Yana riqe da hannunta tsam kamar za'a qwace masa ita,maji da Dr suka turo gofar suka shigo dakin.


Qoqarin yunqurawa takeyi ta tashi maji tace


"Yi kwanciyar ki d'iyata" ta iso bakin gadon. Sai a sannan toufeeq ya zame hannun nasa daga nata,ya matsa baya yana yiwa Dr jarma barka da isowa, qasan ranshi yana mamakin yadda suketa zirga zirga shi da maji din, gefe guda kuma ko yaushe ya gansu tare sai yaji zuciyarsa ta zurafafa da addu'ar dawowarsu da dinkewarsu a mazaunin ma' aurata kamar kowanne iyaye.


A kunvace ta gaida maji, majin ta hamsa

mata, sannan gasa qasa take mata tambayoyin da suka gara saka säahar cikin jin nauyinta. Duban toufeeq maji tayi


"Yaushe zasu sallameta?"


"Zuwa anjima suka ce,zatayi bed rest ne kawai koda a gida ne"


"Yavi kyau, zan wuce da ita gurina" maji ta fada tana ciro wayarta don ta sanya a sake samar musu wani

dakin wannan din kamar wata dama ce a wajenta da

wajen sãahar dinma gaba daya,zata sake waana Dr

jarma da kyau,itama kuma sãahar din zata samu

cikakken hutu,zasu kuma sake fahimtar juna tsakaninsu ta sake samun damar da zata shirya kyakkyawar alaqa tsakaninta da toufeeq din.


Tunda yaji maji ta fadi haka ya kasa sukuni,yayita

goqarin kallon qwayar idanun säahar din don yayi mata alama amma bata ko kalleshi ba. Cikin jikinta tasan za'a rina hakan indai toufeeq dinne da yake jin kansa kamar tuzurun da yayi aure kwanan nan, to amma ita kanta tana da bugatar hutun ko don su tsira da abinda take dauke dashi din karo na uku a rayuwarta shi kuma karo na biyu.


Har akayi la'asar bai samu wanna damar ba, duka ya shiga damuwa walwalarsa ta ragu,sajjad na ankare dashi,yaji komai daga bakin afifa,ba abinda ya rage masa illa dariyar da yaketa boyewa,har suka idar da sallah,ya gama azkar dinsa, haqurinsa ha gaza,ya cire wayarsa ya tura mata gajeran tex


"please ki gayawa maji fa, bazan iya ba,Allah bazan jure ba"


Wayar na hannun afifa,sun gama waya kenan da maama data duba jikin fadeela da na sãahar din gaba daya, Murmushi afifa ta saki tana miga mata wayar. Sai data kalli fuskar afifa din sannan ta karba wayar ta karanta saqon,tana kaiwa qarshe ta daga kanta ta kalli afifan suka hada ido, saita watsa mata harara, dariya ce sosai ta qwacewa afifa


"Meye zaki nade tabarmar kunya da hauka a kaina? munafukai,kun gama gulmar baku son juna Allah ya toni asirinku shine zaku wani dinga dojewa,ni kinga tafiyata gwara naje naji dumin hayatee daga nan na duba fadeela ko ta tashi" ta fadi tana rolling mayafinta doguwar rigarta a kanta.


Fitar afifa ya maida dakin shuru, maji ta shiga wajen fadeela,Dr ya fita tun dazun, nadeeya kuma na saman abun sallah tana sallah. Gyara zaman wayar tayi a hannunta tana tunanin amsar da zata bashi, ita kanta tasan akwai rikici, har ta shiga gurin tura saqo aka tura gofar dakin aka shigo.


Muhammad toufeeq ne, hannunsa daya cikin aljihun wandon lallausan yadinsa, idanunsa carrr a kanta,yayi wani sanyi da laushi da yasa zuciyar saahar cika da mamaki,kawai don maji tace zata wuce da ita shi ya hautsina shi haka? wanne irin so ne haka?.


A nutse ya iso gaban gadon, kai tsaye ya yiwa kansa guri a gefan gadon shima kusa da ita, kafadunsu har suna gogar juna. Da sauri ta dubeshi tana masa nuni da nadeeya dake zaman tahiya zata sallame, sai ya daga mata gira murya can gasa


"And so what?" Ya fadi gaba gadi abinsa, hannunta ya lalubo ya rige cikin nasa


"Maji so take kawai ta horani yadda take hora Abba, dazu sailad vake gavamin va maida aurensu.lalurar fadeela yasa bamu sani ba" wani lafiyayyen murmushi dake qarawa fuskarta kyau ne ya kubce mata,bayan samun nasara a alkin fadeela wanzuwar cikin jikinta wannan shine labari na uku da yayi masifar sanya farinciki a zuciyarta. Kaman zaice wani abu sai ya waiwaya sashen da nadeeya ke zaune


"Tashi ki bawa mutane guri munafuka" ya fadi vana dan fidda fararen idanunsa waje. Batasan ya akayi ya fahimci ta sallame sallarta ba, sosai taso jin gulma shi yasa tayi kaman zaman tahiya takeyi, tanason taga wanna salon boyayyar soyayyar tanason taga salon soyayyar yayanta Classy anty N da muskilin yayanta yaa moha, ta tabbatar wanna kalar soyayyar zata kasance ta musamman,sai gashi ya baro jirginta. Hakanan ta miqe tana ninke abun sallar tana satar kallonsu har ta fita a dakin.


Dariya ce sosai ta kama nadeeyan,afifa dake fitowa daga dakin fadeela sukayi kacibus


"Lafiya sister nadeeya?"


"Anty afifa,wadancan mutanen,wai dama suna so suke kaiwa kasuwa?" Baki afifa ta tabe tana dariya


"Ko ba bestie ba, gulmammu, kowa ciwon dake ransa kadai ya sanyashi jin babu wani da zai sake burgeshi, basusan ita zuciya ba'a ci mata alwashi ba"


"Zo kiga don Allah" nadeeya ta fada tana yafito afifa.

Hannuwanta afifa ya daga tana dariya


"Wallahi bazan iya leqensu ba karna ganowa kaina abinda yafi qarfina" dariya suka sanya su duka suka wuce dakin fadeela tunda zaman dakin säahar din yafi garfinsu.



Zafafabiyar

No comments