Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 6

 


Book 02 Page 06




Wani irin zuzzurfan nazari ta shiga yi,tanason ta yiwa kalaman nasa duba na fahimta,ta kuma nazarci ma'anarsu da kyau.

"Indai hasashenta yayi dai dai,indai ma'anar fassarar tana nufin abinda ta tsinkaya ne.....zai aureta ta kula da fadeela,ita kuma tayi rayuwarta tamkar macen da bata da miji,babu doka,babu oda,babu auratayya,babu sawa babu hanawa...a idanun duniya sunanta matarsa,amma a tsakanin su din bagin juna ne,kowa zaiyi harkar gabansa" wannan hasashe kadai ya haifar da kyakkyawan murmushi saman fuskarta


"Yes... yes" ta fada gasa gasa tana sakin murmushi


"Ta samu cikakkiyar mafaka,ta kuma samu dama irin wadda zata bata damar yin rayuwarta lya adadin tsahon shekarun da takeso ba tare da takurawa ko sanya idanun kowa ba". Sosai taji al'amarin ya kwanta mata,wanann din wata idea ce me kyau. A daren ta fara laluba card din da ya bata cikin jaka,sai ta tuna ta yasar dashi a falon batama fito dashi ba. Ji tayi a daren kamar ta fita ta dauko card din,amma dole ta haqura zuwa safiya.


Haka kawai kuma wani sashe na zuciyarta ke umartarta tayi addu'a. Bata wofantar da wannan shawarar ba,sai ta mige ta daura alwala, don dama ita din gwanace ta wannan fannin,dai daikun darare ne suke wuceta,farinciki ko baqincikinta tana juyeshi ne saman abun sallah, wanda hakan yake qara mata nutsuwa tare da hasken rayuwa,matsalolinta masu yawa kuma warwara take zuwa musu a qanqanin lokaci.


Raka'a shida tayi,tana gamawa taji wata nutsuwa na shiga ruhinta,kamar iskar dadin na dada sanyi da dadi,tana yiwa annabi salati idanunta suna lumshewa,a haka har wani daddadan bacci data jima batayi irinsa ba ya sureta.


Washegari bata tashi da wuri ba,saboda bacci tayi sosai,bayan ta farka tayi brush tare da alwala,ta dawo cikin dakin nata ta sakawa wayarta charge,ta kunnata ta zauna daga gefan gado,ta buda inbox ta turawa afifa sagon da tasan dole ne ta dawo gida koda bata nemeta ba,duk da jiya da magriba ta tafi zooroad


"Bestie aure zanyi"_ abinda ta tura mata kenan ta sauka tabar wayar a charge ta fito falo.


Masu aiki keta hidimar kimtsa gidan,da )alama aikinsu na safe yazo qarshe saina rana dana dare. Cikin sakewa suka gaisa kamar yadda suka saba,baaba rabi ta gaya mata maama tace a shaida mata idan ta farka,ta tafi gidan uncle ismail,yau din za'a kawo lefen zeenat qarfe uku na yamma,idan ta gama komai ta sameta a can saisu dawo tare. Tana amsa mata tana ficewa,tanaso ta samu card din kafin masu gyaran gurin su hada dashi su share.


Sai data danyi dube dube sannan ta ganshi,ta tsugunna ta dauka tana kallon rubutun dake a jiki. Rubutu ne dake cike da tsari da kuma ban sha'awa,full name dinsa email and phone duka a jiki. Dan tabe baki tayi,tana tuna irin izzarsa da jin kansa,wai yama akayi yasan wasu abubuwa haka a kanta?,ya akayi yasan ita din bazawara ce?,ya kuma akayi yasan gudun auren kowanne namiji takeyi?. lya hasashenta bata iya ganewa ba 


"Oho masa,shi ya sani" ta fada a fili tana komawa cikin gidan,ta shiga dakinta ta yiwa card din waje,sannan ta shiga hidimar gabanta.



********Sanye yake da long sleeve kaftan thobe button down, wadda daga qasa gefe da gefe yake a tsage,fara ce qal kamar yadda mafi yawa zabinsa kenan a kaya,hannun rigar ya tattareshi zuwa gwiwar hannunsa,yana riqe da mug na coffee kamar kullum yana kurba,idanunsa akan fuskar fadeela daketa faman gogarin zana wani dan tsuntsu.


Idan kace hankalinsa baya gurin bakayi kuskure ba,miskilar fuskar nan na hade kamar yadda take a koda yaushe,saidai sassanyan kyan nan da cikakken gashin girarsa zuwa jajayen lips dinsa zuwa kwantaccen gashin dake habarsa zuwa kuncinsa suna sake bayyanar da cikar kyawunsa tare da gara masa kwarjini.


Shan coffee din kawai yakeyi bawai don yana masa dadi sosai ba,tun wancan ranar da ya dandana wannan coffee din da kuma shayin gaba daya,dadinsa ya dauke dandanon dadin kowanne irin coffee,hatta nasa kuwa da ya tabbatar ya qware sosai gurin iya hadashi.


A nutse ya ajiye mug din,bakinsa na dan fidda tururin ragowar zazzafan coffee din, idanunsa a kafe waje daya. Babu abinda yake masa kai kawo tare da ciwo a rai irin yadda ya zubda dukka makamansa ha gasqantar da kansa ya nema wata diya mace ta aureshi,abinda ya yiwa kansa alqawarin har yabar duniya bazai sake maimaitawa ba,sai gashi dare daya....tazo ta ruguza duk wani abu da ya sanyawa kansa doka da iyakoki a kai. Iska me zafi ya furzar yana dogara gwiwayoyin hannunsa akan qarfen balcony din hadi da fidda zazzafar iska a bakinsa. Ba komai ke sake rura wuta ke zafi a zuciyarsa ba,sai yadda ta tankwabar da tayin da yayi mata. Tana tunanin yana neman wani abu ne daga gareta? ‚bayajin banda fadeela akwai wani abu da zai sanya ya sake kallonta.


Abu daya ya sani,koda bata aminta ba,zaiyi dukkan abinda zaiyi,koda tsiya sai ya dawo da zamanta gidan taci gaba da kula da fadeelan


Karar shigowar saqo a wayarsa ya dauki hankalinsa,wayace da dukka kira ko sagon da zai shigo ya cikinta to me muhimmanci ne a gareshi,wanan yasa ya miqe tsaye ya sanya hannu a aljihun kaftan thobe din nasa,ya zaro wayar yana dubawa.


Sake dafe hannunsa yayi sosai

saman qarfen,tuntuni ya sanya jibril ya nemo masa number dinta,ya kuma yi masa saving nata. Haka kawai yaji yana buqatar zama,ya miqa hannu ya jawo wata kujera guda daya me azabar laushi ya zauna,ya lanqwashe gafafunsa a cikinta sannan ya fara karanta saqon


_I agreed,i will marry you,but under some conditions,idan ka shirya zaka cikasu..

..fine,am ready nima"_ dan garamin tsaki yaja,me ya kaishi irin wannan abunne wai


"Farinciki da lafiyar fadeela kake nema" zuciyarsa ta bashi amsa,sai ya girgiza kar yana gasgata hakan. Baiyi jinkiri ba ya fara tafa mata amsa


_i get the point, duk wasu conditions naki ki rubuta su kawai ki ajjiye basai naji ba,coz i know bani da case dasu,you are going to be my wife for the sake of fadeela,you can do whatever you want"_. Ta kusa a qalla minti guda tana duba amsar tasa,sai kuma ta saki murmushi,saboda abinda takeson ji kenan,zata zama free,zata samu 'yanci. Sauka tayi tana shirin ajiiye wayar wani sagon ya sake shigowa


_"Are you ready for the marriage nan da next week?"_tabe baki tayi,yama raina mata hankali, don ta amince kuma sai yayi mata zancan next week?, kwanaki hudu kacal fa gaba


"Nooo" kawai ta tura masa tana jan tsaki


"Alright,sati biyu kacal na qara,so let's start plan it,ki sanarwa da Dr zan turo magabatana nan da 3days"_. Juya wayar kawai ta dinga yi a hannunta,anya batayi kuskure ba?,anya zai iya cika alqawarinsa?,a yadda maza suke a yanzun?,ba alqawari babu amana. Kai ta girgiza


"Batajin komai zai faru,saboda kowa a cikinsu maradinsa yake karewa yakeson cikawa, kamar contract ne yanzun a tsakaninsu. Da zarar fadeela ta warke zata nemi saki daga hannunsa,shikenan contract ya qare,shi da ita kuma kowa zuwa lokacin ya cimma muradinsa.


Har washegari zuwa wata washegarin ta rasa wa zata tunkara tsakanin Dr girema da kuma maama dinta,ga afifa still bata nan,dole daga garshe gudun kada abban nata yayi bagin da baisan da zuwansu ba,ta dauki waya ta kira afifa tace ta dawo please. Tunda taji hakan tasan akwai wani Issue daya taso masa may be ta gaza warwareshi,don haka tabar komai tazo ta isketa,lokacin zataci abincin rana ne da yammaci,ta garso musu sukaci a tare: Sai da suka kammala,ta gyara gurin sannan ta dawo ta zauna tana fuskantar afifan


"'Bestie na fidda miiin aure" dan dubanta kadan tayi sannan tace


"An fidda miki dai,ko ba mahmud ba?,dama ai saura 3days deadline din da abba ya deba mana ya qare"


"Ba mahmud bane,wanann zabina ne,MT

JARMA" ta fada kanta tsaye tana duban reaction na afifa. Ta fusgi hankalin nata kuwa,don tsaiwa tayi da komai tana kallonta,kalmar na girgiza afifa,hadi da shiga kowanne lungu da saqo na jikinta. Girarta ta dage mata dukka biyun


"'Yes,kina mamaki ne?,nima mamaki naso baki dama kamar yadda kikayimin akan SAJJAD"


Murmushi afifa ta saki tana kauda kanta

gefe


"Sajjad banda kina cikin rudani hankalinki ba'a kammale yake guri daya ba,ya kamata ki fahimta wani abu da kanki.....na miki murna da kika samu zabinki,amma bestie,kome zakiyi ki yishi ba'a bisa kowacce manufa,kin sani.....na sani..... dole na garyaraki zuciyata taqi aminta da cewa MT JARMA shine zabinki, kusan kowa yasan dabin dake tsakaninku,yaushe soyayya ta shiga har kuka fahimci juna?" Sam sãahar batason afifa tace zata hanata aiwatar da qudurinta,a yadda ta tsani maza da abinda ya dnagancesu wannan ne kawai option din da ya rage mata,kuma dama a gareta guda daya da zata rayu cikin salama ba tare da wata alaqa tsakaninta da su ba


"Allah ya sanya alkhairi,kuma ina addu ar

Allah ya maida qogo masaki" bata fahimci maganarta ta qarshe ma,saita watsar,tunda dai bestie din nata bata kawo wani tarnaqi na fine,shikenan.


Afifa ce tayi mata rakiya gidan yaa

muhyiddeen,ta bawa anty farheen sago ta gayawa yaa muhyi din,shi kuma ya isarwa da abba batun. Sakato anty farheen din tayi cike da zallar mamaki tana kallon säahar din


"Yaushe reshe ya juye da mujiya kuma ummin abba?" Dan garamin murmushi ta saki tana kauda kai


"Tsarin Allah,haka qaddararsa take" jinjina kai kawaii anty farheen tayi,don ita kanta bata gama gamsuwa ba. A yadda tasan sãahar sarai da kafiya,bata da sassauci akan abinda takeso da kuma wanda takeqi uwa uba kuma gefe guda ga al'amarin daya sauya zuciyarta zuwa giyayya da gaba daga dukkan jinsin maza.


Sanda sãahar din ta shiga sallah lokacin afifa dake fashin sallah suka tattauna da anty farheen


"'Nafi zaton dukkansu akan wata manufa suka gina auren nan,amma dai koma menene,mu zamu bada gudunmawa waien tabbatuwar komai yakuma dore har abada,so zamu soma shirye shirye,kada ki nuna mata kin fahimci komai" kai afifa ta gyada.


To wannan magana da sukayi da

Anty farheen sai afifa ta saki jikinta,tun a washegari ita da anty farheen suka soma tsara abubuwa da gabatar da shirye shirye. Ta fannin säahar kuwa jin kanta tayi sakayau,ta tsinci kanta cikin wata iriyar walwala mara misali,hankalinta taji yayi mugun kwantawa,tana ji a ranta yanzu bata da sauran matsala a rayuwa. Saidai harkokin gabanta kawai takeyi,duk wani shiri da su anty farheen sukeyi tana gefe ta zuba musu idanu,gani takeyi bata lokacinsu da kuma kudadensu sukeyi,wani abun saidai ta kalla ta tabe baki,amma batace komai ba saboda abune da take ganin tsakaninta ne kawai da toufeeq din,babu wanda ta shaidawa manufar aurensu.


Kwanakin ukun da ya diba matan

baqi na musamman cikin girma daga gidan

Dr mahmud JARMA suka sauka a gidan Dr girema da kudin auren yaransu guda biyu.

Muhammad toufeeq ya bayar da zunzurutun kudin auren Khadija Muhammad girema har naira million daya,yayin da sajjad da ya tsunduma cikin soyayyar afifa tun ganinsa da ita na farko ya bada dubu dari biyar. Sajjad yaso qwarai a qara kudaden sufi haka,amma dr jarma yace sam,hakanma yaso yayi yawa,albarka yake nema musu. Magabatansu sun roqi sati uku kacal,dr girema da gannensa da suka karbi kudin tare basu ja ba,ganin yadda Dr jarma da kansa yaketa roqon ayi masa alfarmar hakan.


Da daren ranar dukka su biyun suna dakinsu,afifa waya take amsawa tsakaninta da anty farheen,duka maganarsu akan yadda shirye shirye zasu guda na ne,sayayyar kayan dakinsu zuwa gyaran jikinsu. Cikin satin takeso yaa muhyi ya samar musu da visa su ukun,china turkey ko Dubai,duk wadda tafi sauri da sauqi,su dora kayan ta sama yadda zayazo da wuri


"Amma ta sama anty akwai kudi fa"


"Karki damu,biyan buqata akeso,indai china ne ma babu matsala,akwai lucky cargo da kayan zasu iso cikin kwanaki galilan har nan kano(me bugatar hulda da amintaccen kamfanin saboda kawo kaya daga china zuwa Nigeria dukka states,sai ya tuntubeni ta wannan number don na hadashi da kamfanin kai tsaye 08187255862)". Sati guda takeso suyi a can,satin da suka dawo kuma sai a fara gyaran jiki da sauran hidimomin da suka shafi amare.


[14/09, 7:42 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*



* TABARMAR KASHI_*

No comments