Breaking News

Tabarmar Kashi book 2 page 59

 "HUGUMA*




*_TABARMAR KASHI_*



Book 02 Page 59



*****Tunda gari ya waye ta fara maganar tafiyarsu

asibiti,yana cikin duvet yana wani almurin bacci da

sãahar din tasan na neman magana ne kawai, don sau

uku tana kamashi yana binta da kallo tana kai kawon

nata shirin tafiyar. Koda ta kammala gabansa ta

iso, idanunta a qasa a kuma shagwabe tana lanqwasa

yatsun hannunta


"Please na gama fa,kai nake jira" kallon qasan ido yakeyi mata zakayi zaton baccin yakeyi har yanzu, tayi masifar kyau,shigar da tayi ta karbeta,inda yana da hali wani abu shapeless zai samu ya lullubeta ta yadda babu me iya genta har balle yaga tudun qirjinta ko na mazaunanta


"A bani coffee to" ya fada muryarsa can gasa


"Okay" ta fadi da hanzari tana juyawa. Mini coffee maker ta kunna ta hada masa irin wanda yakeso har two cups, duk abinda takeyi din yana kallonta yana dariya qasan ransa, tare da tuno abinda ta jiyar dashi daren jiya wanda shi kam bai taba sanin akwai wannan abun ba.


Gabansa ta iso ta tsaya da mini tray tana cewa


"Ga coffee din" dan Jim yayi kamar bai jita ba,sai kuma ya miqe yana yaye duvet din,ya zauna sosai saman gadon ya miga mata hannu yana kallonta. Tray din duka ta miga masa, hannu yasa ya karba,da hanzari ya ajjiye shi saman bedside table dai dai sanda ta juya ya saka hannunsa ya kamota,fincikota yayi a tausashe sai gata gaba daya cikin jikinsa


"Me yasa baki da wayo kullum,ni da nace ki bani hot coffee saiki bani cold coffee?" Ya fada yana riqe da fuskarta yana kallon cikin idanunta. Zare masa manyan fararen idanunta tayi tana cewa


"Sai dava tafasa fa sosai,ka duba ka gani"


It was not hotter than you,and ba wani hot coffee da ya fiki,i like hot shower,a regular shower but with me in it"


"Don Allah,na yiwa fadeela alqawari zamu iso da wuri"

Tsayawa yayi da abinda yake shirin yi, yana dubanta da jirkitattun idanunsa


"'Me yasa zaki hukunci bayan kinsan idan baban fadeela yana guri rayuwarki da lokacinki duka nasa ne?" A yadda ta hangi fitina fal idanunsa tasan muddin bata lallabashi ba tsaf zai iya soke fitar ma


"Sorry i make a mistake but bazan sake ba" ta fada tana hada hannuwanta guri daya tana dan boye murmushin. fuskarta saboda yadda ta fahimci tayi masifar yi masa yankan hanzari. Kansa yadan juyar gefe guda


"Na fahimci idan akan fadeela ne zaki iya komai shine kikemin wannan 'var murvar don kawai a cuceni ko? yayi….. na yarda,but i need a kiss please"


"Tashin hankali" ta fadi qasa qasa,tasan kiss a gurinsa kamar wani mabudi ne na bude shi


"Eheen, baki shirya fita asibiti ba?" Ya tambayeta yana taba lips nashi da yatsansa. Yana gama fadi ta hade bakunansu ta fara masa yadda yakeso din, saidai daga garshe shi ya karba ragamar. Yadda ta zata din kuwa fara wuce gona da iri yayi, ta kama hannunsa ta riqe tsam don ba damar yin magana da baki, ya fahimci me takeson fada ya daga kansa yana dubanta


"Am sorry for being too forward but your lips make me wonder what the rest of you would taste like da safen nan". Bai bata dama ba ya warware shirinta tsaf yayi yadda yadda ransa yakeso . Bayan ya kammala ya sauka ya sauka ya barta yana mata dariyar cewar da takeyi


"Ka karya algawari " cikin kukan kissa da shagwaba


"Eh ai dama indai nine ta wannan fannin na dade da zama rules breaker, but duk da haka am sorry my

MOONBEAM" sai yayi kissing nata a tausashe ya wuce toilet.


Har ya fito tana kwance, ya zaci zai samu ta shiga daya daya toilet din dake parlor ta shirya, qarasowa yayi gabanta fuskarta na rufe cikin pillow


"Hello ko kina son gari ne?" Hararar wasa ta jefa masa

sannan ta sake qunshe kanta,can qasa tace


"Marata ce takemin ciwo*


"Ya salam* ya fada vana tayar da ita. Da gasken take don sosai ta rigeshi tana cije lips


"Let me help you kiyi wankan mu wuce asibitin sai kiga

likita ko?". Duk yadda taso dojewa bai fita ya barta ba,sai da tayi wankan ta fito ta shirya duka a gabansa,ga kunya ga ciwo,shi kuwa ya murje idanunsa,saima wani mayen kallo da yake bin ko ina na jikinta dashi har ta gama shiryawa


"Ko na sake warming maka coffee din,bakasha ba" kai

ya girgiza yana murmushi


"'Nooo,I got the better ai sukutun da guda daga wajenki”


kunyarsa ta sakata kau da kai, bayajin kunyat baro zance baro baro, sai sun fita kuma waje kaga ya kame kamar ba shine me b'arin zancan nan ba.


Sun samu an gama yiwa fadeela komai daya

Kamata, tasha magani an gyara mata jikinta,sai zaman jiransu. Sanda suka shigo kamar zata koma cikinsu,sosai farinciki ya cikata,ga abby dinta ga aunty N,duk inda ta waiwaya sune.


Basu wuce awa dava da isowa ba afifa da sajjad

suka iso. Sanda suka shigo sahar na saman gadon daga gefan fadeela tana bata fruit yayin da ogan yake zaune saman kujera a gaban gadon hannunsa goye a qirji ya tsaresu da kallo.


Migewa yayi ya bawa sajad hannu sukayi musabaha,afifa ta matsa kusa dasu bayan sun gaisa da toufeeq tana duba jikin fadeelan,shima sajjad din ya dubata,sai suka juya suka fice suna magana a tsakaninsu.


Ba jimawa suka dawo,a lokacin ta gama batan tana zaune daga gefanta tana tayata karanta wasu abubuwa da likitan dake kula da sashen magana na qwaqwalwa ya bata. A tausashe yake jifanta da wani irin kallo har ya qaraso daf dasu. Afifa ta kula,sai taja jikinta baya tana boye dariya qasan ranta.


"Moonbeam" ya furta gasa gasa yana dubanta. Kunya ta kamata jin ya maimaita sunan da ya sanya matan a gabansu afifa, ta daga idonta a hankali ta dubeshi, hakan yakeso sai ya marairaice mata


"Ki barwa su sajjad din ita kizo muje kiga likitan" kai ta jinjina, ta sakarwa fadeela dan qaramin littafin tana zamowa daga saman gadon. Kafin ta qaraso ya sanya hannu ya saita mata takalmanta, kunya da nauyinsu. sajjad ta sake kamata,ta zira takalman a nutse tana dawurwura na abinda zatace da afifa


"A dawo lafiya" kawai taji afifan tace sai bata ce komai ba tayi gaba kamar yadda toufeeq ya bugata.


"Dan tsaya" yace da ita bayan sun fito, ta tsaya cak ya qaraso kusa da ita, sai ya lalubi hannunta ya saka a nasa


"Yauwa to muna iya tafiya,naga alaman turawannan suma mayun mata ne" ya fadi yana wani tsare gida,abinda ya sanya qaramin murmushi ya kubce mata,sai taji dadi gasan ranta, karon farko kenan da taga haka daga wajen mijinta. Abinda adam bai taba damuwa yayi ba kenan, hasalima shi duk inda zasu shiga qoqari yakeyi aga kyanta,yana alfahari sosai da kyan da take dashi.


Ko cikin office din yana tsaye daga bayan kujerarta kamar wani bodyguard ita kuma tana a zaune.

Qwararriyar gynecologist ce da take a wani department daban a asibitin cikakkiyar musulma ce, abinda ya qara masa nutsuwa kenan,säahar tayi mata bayani dalla dalla da harshen turanci


"Ina zargin wani abu" likitar mai yawan fara'a da kirki ta fada bayan ta gama yi mata tambayoyi tare da duba report nata.


Scanning ta fara dayi mata cikin nutsuwa, kai kawai take gyadawa murmushi na fita a fuskarta,sai ta sanya hannu ta kirayi toufeeq tana tsaida na'urar kan wasu abubuwa guda biyu masu suffar wake ko gananun ayaba


"Kalli babies dinka" ta fada tana masa nuni da allon computer din da hannu. Ido sosai ya zubawa abun da take nuna masan,zuciyarsa na dan bugawa cikin wani irin zumudi da rikicewar tunani


"Ban fahimta ba likita" ya amsa mata shima, sai tayi murmushi tana sauke na'urar scanning din daga saman marar säahar


"Yanzu zanyi maka bayani,sauko madam" wannan karon kasa tsaiwa vayi va samu kujerar dake facing din säahar din ya zauna vana bawa likitan dukka attention dinsa


"Alamu sun nuna babies uku ne a mahaifarta,guda daya ne ye fita, yanzun haka akwai sauran guda biyu" daga shi har säahar din ji sukayi kamar jinin jikinsu ya daskare,ji yayi kaman kunnuwansa basu ji masa dai dai ba


"Karkiyimin irin wannan wasan likita, saboda bazan iya jurewa ba kic wasa ne daga baya" ya fada yana jin duniyarsa na kewayawa dash cikin wani madaukakin farinciki


"Ba wasa bane sir,shi yasa na kiraka na nuna maka su" kasa jurewa yayi saboda farincikin da yayi masa yawa,sai yaji kamar zuciyarsa ba zata iya dauka ba,don haka ya zamo saman gwiwoyinsa ya kamo hannun sãahar ya rige da kyau yana dorashi saman qirjinsa, idanunsa a lumshe yana ambatar sunayen Allah. Itama kasa rige kanta tayiyadda hannunta yakejin tsananin bugun zuciyarsa sai taji kamar a tafin hannunta zuciyar tasa take


"Wannan babban sakamakon ba zata da ubangiji yayi mana,duk da mudin ba wasu bayi bane masu tsananin biyayya ba a gareshi, bansan meye zanyi da zai sake sanyawa ubangijr ya sake yarda dani ya kuma aminta

dani ba ina da bugatar irin wannan falalar daga ubangiji

na a duk kowacce shekara idan zai bani, Alhamdulillahil

lazi lam yattakiz walada walam yakun lahu sharikun fil

mulki walam yakun lahu waliyyum minazzulli wa kabbirhu

takhbira" ya fada vana kifa hannun nasa a tafin

hannunta idanunsa na ciccikowa da gwallar da bayaso ta

zubo din,wannan hawayen yafison ya zubdasu a gaban

ubangijinsa don nuna tsantsar godiya a gareshi.

Sai da dr marhooma tayi gyaran murya sannan

ya tuna tana a wajen,don yayi nisa wajen lallashin säahar

da nata idanun suka kasa rige nasu ruwan hawayen


"Akwai bayanin da ya dace nayi muku" ta fadi tana gyara zamanta


"Amma likita,dama mata irina suna iya samun cikij 'yan

uku?" Tambayar da säahar taketa juyawa a ranta kenan ta kuma kasa rigeta. Murmushi dr marhooma tayi


"Kyautar Allah ce yana iya baiwa duk wanda

yaso,musamman idan a danginki akwai history na haifan

twins ko triple din, sannan yawanci matan da suka doshi

shekara talatin ko suka gota sunfi yiwuwar samun haife

haifen 'yan biyu ko uku ko hudu ma,duk da masu qasa

da hakan ma suna samu musamman wadanda ya zama musu kamar gado, lokacin da mace te saki qwai wato ovulation idan aka dace da gwan namiji ya hadu da nata @wan, maimakon ta gyangyashe qwai guda daya sai ta gyangyashe biyu uku ko hudu ko sama da haka,wani kuma yana rabuwa ne yayin gangarawa cikin ainihin qwaryar mahaifa sai a samu irin hakan, hikimar Allah ce duka yanayin yadda yaso a sanda yaso" dukkansu sun gamsu tsoron tare da tabbatar da afkuwar ikonsa suka shigesu, yayi ajiyarsa a muhalli daya,ya kuma fidda wanda bashi da rabon taka duniya,ya tsare sauran wadanda yaso suci gaba da wanzuwa


"Kamar yadda wancan likitan ya fada muku, tabbas mahaifarta tana da rauni, saboda haka zamuyi mata daurin mahaifa, sannan zamu bata bead rest wanda shi ko a gida zata iya yin abinta, saidai tana bugatar yallabai adan daga mata qafa don Allah daga yawan bugatu" ta gada tana sauke dubanta akan TOUFEEQ.

Murmushi kawai ya saki yana debe dubansa ya maida kan sahar, suka hada idanu sai ya kashe mata ido daya, yayi qasa sosai da muryarsa cikin harshen hausa yadda dr marhooma ba zataji ba yace


"Raguwa ce ke wallah, dama neman mafaka kike,to ai dai ba'a hanani shan dumin babies dina ba ko?" Ido ta lumshe tana sakar masa murmushi, sai yaja ajiyar zuciya 


"Wannan lumshe idon kawai na tsokanan magana ne saboda kinga bazan iya fanshewa ba?" Siriryar dariya ce ta kubce mata,sai tasa hannu kawai ta rufe bakinta tana kwantar da kanta gefe guda.



Zafafabiyar

No comments