Breaking News

Tabarmar Kashi book 2 page 58

 "HUGUMA*






•_TABARMAR KASHI

_*



Book 02 Page 58



Tun daga ranar bai sake bari ameesha taga

fadeela ba, kamar yadda ameeshan bata sake ganin

fuskarsa ba sai a hoto ko a media. Duk wanda zai tilasta masa yabar ta ta dinga ganin diyarta ya musu rantsuwar da suka tabbatar babu janyewa,duk da bai fito ya furta ainihin abinda ya rabasu ba,dr jarma kawai ya shaidawa saboda gudun kada yace ya maidata dakinta, ko ya bata diyarta,shi kurna ya gayawa hajiya qarama. Hajiya qaraman murmushi ta saki


"Ehe, ka gani ko? ni dama na jima ina ganinta tana

shigowa da maza gidan, to amma idan kayi magana

yanzu za'a ce ka takurawa surukarka shi yasa na

bari, amma kullum ina addu'ar Ubangi ya nuna maka".


"Ince ga yadda na rayu a wadan nan shekarun cikin ciwuka masu zafi guda biyu bata baki ne,ciwon fadeela da kuma mummunan ciwon da ameesha ta dasawa zuciyata,da gyar nima na qwaci kaina daga bugawar zuciya saboda mummunan hawan jini daya kamani wanda da gyar na qwaci kaina daga gareshi Allah ya kawomin waraka don ya dubi zuciyata akan ban zalunci kowa ba.tun daga sannan ta cire kowanne aminci a zuciyata daga kan diya mace, nayi mata uzuri duk da yadda bayyanar halinta na aureta mun zauna nayi haquri da ita mun rabu na tausaya mata na dawo da ita,na sanya qafa na ture duk wani aibunta saboda ganin kamar ta canza,ashe lumbu lumbu tayimin take cin dunduniyata,A DUNIYA AKWAI ABINDA YAFI CIN AMANAR WANDA KA AMINCEWA CIWO DA ZAFI!" ya furta wani irin dumi yana fita daga numfashinsa, alamu suna nuna cikin gololuwar bacin rai yake


"Babu" yaji sãahar ta fada cikin rawar muryar daya tabbatar kuka takeyi.


Hannunsa yakai ya shafi fuskarta,sai ya samu fuskartata jige sharkaf da hawaye,zuciyarsa ra motsa sosai. shi da itan dukkansu an bar musu wani tabo da har su mutu ba zasu daina tunashi ba,ba kuma lallai su fasa jin ciwo idan an taba musu gurin ba,sai ya zameta daga jikinsa cikin nutsuwa,ya sauka daga saman gadon ya kunna fitilar dakin, haske ya gauraye ko ina.


Stool ya jawo gaban gadon,ya zauna sosai yana kallonta da idanunsa da suka canza launi zuwa kalar ruwan goro kamar an disa jini a cikinsu.


"Tashi" ya furta a tausashe yana miga mata hannunsa. A hankali ta yaye duvet din sannan ta sanya tattausan hannunta saman nasa ya migar da ita ta zauna sosai,sai ya koma shima ya zauna sosai din, yayi folding hannayensa a qirjinsa yana dubanta kai tsaye


"Kiyi haquri, na karanta miki diary ba tare da izininki ba" kai ta daga ta kalleshi sai suka hada do,wasu sabbin hawaye suka zarto mata tana jin tausayinsa yana sauka a girjinta,wasu similarities dake cikin labaran su suna dawo mata


"Yayi fama da yawa,shi din bayan yaudara da cin amana harda nakasa ta barwa 'yar cikinta 'yar cikinsa?"


"I hope you forgiven" kai ta gyada masa a hankali.


"Thank you" ya furta yayi shuru na wasu 'yan daqiqu vanason hada abinda zaice da ita, saboda yanzun lokaci ne da zai nema dukkan wata yarda tata du gina kammalalliyar rayuwar da yake buri,iska ya furzar daga bakinsa,sannan ya sake mayar da dubansa a kanta


"Duk da Allah yana iya jarabtar bawansa ta duk sigar da

yaga dama, amma ina kyautata zaton an zaluncemu ne ni

dake, shi vasa Allah ya hada tarenmu da qaddararmu

waje daya,ya kuma hukunta ni dake mu zama miji da

mata me yiwuwa dama can cikin littafin gaddararmu dani dake din mili da matar ne amma may be idan tun a karon

farko ya gaddara mana zama miji da matar, akwai

possibility din ba zamu san darajar juna da kimar juna

ba, shi yasa ya fara jarabtarmu ta yadda idan zaman

namu yazo zamu riqe juna rigo dan gaske ba tare da

wasa ba" vakai garshen maganar yana sauke

numfashi, idonsa akan kyakkyawar fuskarta


"Hajiya qarama" ya furta sunan da shima ya sanyata

dagowa


"Sai yanzu na fahimci dalilinki nagin aminta da kowa ciki harda NI kina da experience ta wannan fannin wanda ni bani dashi ban taba experiencing haka a rayuwata ba.


Mace ta biyu da tayimin cin amanar da har na koma ga

mahaliccina ba zan taba mantawa da ita ba" ya fadi

fuskarsa tana sake canza launi, alamun baqincikinsa ya sake ninkuwa fiye dana dazu


"Da idona,da kaina na kamata tana canzawa fadeela

magani,wanda daga qarshe bincike ya nuna magani ne

dake da illa ga lafiya da qwaqwalwa, nan asibitin na bayar aka gwadamin ingancinsa" ta girgiza saidai abun ba wani shahararren mamaki ya bata ba,ta riga ta gama duka wadan nan tunanin akan hajiya qaraman, ashe ta lissafa daidai, girgizarta daya yadda mutum mafi kusanci da kai zai ci amanarka har haka? inaga wani bare can wanda baku hada alagar komai dashi ba?.


""'dlan kin shirya cewa na sakeki bayan fadeela ta warke na roqeki kada ki furta min hakan, saboda wallahi wallahi ko sama da qasa zasu hade I can't divorce you" ya fada a raunane. Qasa tayi da idanunta tana jin nauyinsa kadan,kamar ya karanto abinda ta tsara a ranta kenan kafin isowarta qasar.


"'SAHR" ya kirayeta da suna da kuma lafazin dake ratsa kowacce jijiya ta jikinta. Fararen idanunta dake cike taf da hawaye ta daga ta kalli tsakiyar nasa idanun


"I Am done with people who suck on my life and energy and just leave me in the end like i was stupid to trust and give my all to them,SAHR...i just need one human to love me hard and never leave me alone....zaki iya yimin wannan alfarmar? coz naga abubuwa da yawa tattare dake da suke bani tabbacin na samo gold din da nake nema,you gave me a million reasons to love you,zaki yimin nima alfarma?" Ya fada yana riqe yatsun hannunta hopefully. Iconta ta lumshe kana ta budesu, shin idan tace bata sonsa ma a yanzu bata yiva kanta gundumemiyar garya ba? ya riga ya wuce da dukka tunaninta da muddin tace zata iya rayuwa babu shi tayi qarya matuga da gaske yayi mata wani irin ba zata ya qwace komai data mallaka,ya dandana mata meye ainihin so na gaske meye ainihin hidimar miji wa matarsa bawai hidimar mata ga mijinta ba,ya koya mata yadda zata so kuma a sota, bawai ya koya mata yadda zata soshi bane zallar bashi da intention na maida mata wannan zallar soyayyar kamar yadda adam yay ba


"Am ready to be your paradise" ta fadi da mafi dadin muryarta me taushi, sautin da ya ratsa masa kunne,ya kuma kashe kowanne fargaba bacin rai da damuwarsa dukka a lokaci guda,ya fidda wani kyakkyawan murmushi daga saman fuskarsa irin wanda bata taba gani ba


"Kice i love you Muhammad toufeeg, that's all I want to hear daga wannan dan mitsitsin bakin me tsiwa" ya furta yana kallon lips dinta da suka fara motsa shi yana masifar sonsu,suna daya daga cikin abubuwan dake motsashi a kanta,shi kadai yasan taushi da zaginsu.


Kunya ta kamata sai ta kisa fuskarta kan hannunsa dake rige da nata hannun


"Pleaaaaaaaassssseee.…say it mana" ya fadi mata a

mugun shagwabe har sai dataji kamar zata shide.


"Say it mana" ya sake fada har yana zamowa daga saman stool din, sai gashi durqushe saman gwiwoyinsa a gabanta


"Its what I want to hear SAHR karki haramta min,na rogeki ki fadi abinda kikeji a kaina tell me you love me.. only true love can heal all the wounds of the past" Kasa riqe kanta da zuciyarta tayi, idanunta a lumshe ta motsa bakinta


"You are the missing link of my heart, you are the best thing that ever happened to me I LOVE YOU AND I CAN'T LIVE WITHOUT YOU"


"Ya salam!, harda gari" Ya furta muryarsa na rawa,ya riqe hannunta da kyau yana dan jijigashi with so excitement


"Can you say that again?, I want to relieve the feeling" idanunta ta bude tarrr wanna karon ta zube masa,sai kuma ta janye su a nutse tana jin nauyinsa. Da sauri ya kamo fuskartata ya dawo da ita saitinsa


"Look at me once again with those bold beautiful eyes and say it please SAHR" juya qwayar idon tayi cikin nasa idon a rarrabe kamar me koyon magana ta sake maimaitawa din.


Jikinsa duka ya gama amsawa, sai ya mige cak vana garasawa saman gadon vana fadin


"How i wish i could listen to those words again and again,you deserved a kiss" bai sake bata second chance ba ya shiga aike mata da zazzafan sago,lips din nan dake tafiya dashi da kuma albarkatun jikinta bai daga musu gafa ko sau daya ba. A karon farko itama ta fara maida masa da martani, abinda ya taka muhimmiyar gudunmawa wajen haukatasu gaba daya shi da ita.


Sanda taji tana gogarin kaiwa wani waje saita riqd hannunsa numfashinta yana rarrabewa,da rinannun idanunsa ya kafeta shima nasa numfashin yana tsere da kyau


"You are halal for me jininki bai haramta min ke ba duk da ma dai fake jini ne,naga komai" ya fada yana matsar da hannunta gefe ya kuma ci gaba da abinda yakeyi,bakinta ya mutu murus ba abinda ya rage mata illa bada kai bori ya hau.



"_HAJIYA QARAMA_*


Wani mawuyacin dare ne a gareta wanda kaf tsahonsa bata samu bacci ba. Tana kallon nadeeya ta shirya ta kwanta abinta, tunda tayi mata sannu sau daya bata gara waiwayarta ba,duk da abun yadan bata mamaki saboda duk sanda take lalura tana tsaiwa a kanta fiye da abinda haseena zata yi mata, amma yau ta nuna halin ko in kula a kanta. Ba wannan bane damuwarta, damuwarta a yanzun shine kan yadda komai yake lalace mata, anya mutuwar bokanta bata da alaqa da lalacewar aikinta? tunda hatta da gawarta da akayi musu ayyukan tare a wancan lokacin,duk da ita tana zuwa sabunta aikin amma itama yanzun hakan ruwa yanata qarewa dan kada ne.


Qafe hudu da rabi na asuba sago ya shigo wayarta,a mugun razane ta mige hannunta na rawa wayar na neman faduwa a hannun nata, maimaita kiran


"Na shiga uku, innalillahi, na shiga uku" shine abinda ya tayar da nadeeya daga baccinta


"Me ya faru?" Ta tambaya a rude saboda ganin yanayin da hajiya qaraman ta shiga. Bata iya amsa mata ba sai hawaye data fara yi,abinda nadeeyan bata taba gani ba, don haka ta mige ta bude qofar ta tafi taso Abbanta.


Maji na zaune saman abun sallah har ya tashi ya bude mata gofar tayi masa bayani suka rankaya suka fice.


"Lafiyarki fauziyya?" Dr jarma ya tambayeta


"Yaava,plaza ta gaba daya wuta ta cinye ta" ta fada tana sakin kuka me ciwon zuciya. Guri ya samu ya zauna yana maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un shima. Dukka shagunanta ne a ciki da ta zuba kaya iri daban daban ake saida mata,wadanda ta bada haya basufi kaso daya cikin hudu ba.


Da ayar ya samu ya lallabata ta tsaida kukan


"'Kada ki damu, za'a san abinda za'a yi in sha Allah" wannan magana tasa ta dadada mata qwarai, tasan zata rage asara sosal daga wajensa,shi yasa ma bata gaya masa babu kaya masu yawa a dukka shagunan ba,don an kammala ciniki da lissafin shekara ta maqare duk wata dukiya tata a account, tana shirin zana tayi kasafi tayo order na dukka kayayyakin shagon nata a sake sabon zubi da lissafi sai kuma ga wannan tafiyar ta Germany ta taso mata.


Awa biyar tsakani, da safe likita yana dubata dr jarma na gefe suna magana da nadeeya kira ya shigo mata wayarta. Da daga wayar da fasa kukanta hadi da fusge hannunta duka cikin minti guda tana sake fasa kukan


"Daya plaza din tawa data ragemin yaaya wadda tafi kowacce girma,itama ta gone tun daga sama har casanta yaaya‚na shiga uku,wanne irin ibtila'i ne haka?"

Dr jarma yadan rufe idonsa kadan ya bude yana kiran sunan Allah, kansa yana sara masa da wani irin ciwo,gaba daya jiya bai samu isashen bacci ba wajen rarrashin maji data tubure masa kamar bata taba gainsa ba a rayuwa yanzun kuma ga matsalolin fauziyya daya na bin daya da wanne zaiji?

"Kiyi haquri ki kwantar da hankalinki,kinga yanzun nan likita ke maganar jininki bai sauka ba duk da magungunan da suka baki,zaki iya samun matsala kowacce lokaci muddin kikaci gaba da wanann abun"

"Ya kamata na koma gida yaaya na bincika meke faruwa, manyan plazas har biyu yau babu ko daya?"

"Karkiyi sabo fauziyya,Allah yana iya jarabtar bawa a duk lokacin da yaga dama bawai sai da dalili ba". Tsam nadeeya da haka kawai takejin takaicin yadda take sharban kuka kamar yarinya qarama ta miqe tana fita qasan ranta tana jan qaramin tsaki.



Zafafabiyar

No comments