Breaking News

Tabarmar Kashi book 2 page 56

 "HUGUMA*



•_TABARMAR KASHI_*



Book 02Page 56



Koda suka iso gidanma cikin motar yayi tafiyarsa ya barta bai kuma sake bi takan al 'amuranta ba,ya ajiyeta gefe saboda yadda tayi mugun bata masa rai saidai bai fasa sauke duk wani nauyi da haqgin ta ba, da kuma sauran bugatu da yasan mace me juna biyu zata iya buqata.


Fushi itama ta dauka sosai dashi, hukuncin data yanke na farko na qaurace masa a shimfida, abinda ta manta dama duka duka ina abun yake? sau nawa ta bayar da kai?.


Randa hakan ta fara faruwa migewa yayi ya zauna sosai ya kuma kunna fitilar dakin, idanunsa a kanta sanda take tattare kanta gefe guda cikin fushi 


"Me kike nufi?"


"Kai tsaye bazan iya bane, tunda nima ba wai ina samun abinda duk zuciya takeso daga gareka bane"


"Okay" kawai vace da ita. Tun daga ranar shima ya ajiyeta a side ya shiga sabgar gabansa. Tun tana daukar abun da saugi tana kumbure kumburenta har ta fahimci duk inda ta dosa shi ya wuce nan, tilas ta fara neman hanyoyin shiri. Shirin nasu babu jimawa sai kuma Allah ya saukar masa da wani ibtila'i a cikin kasuwancinsa. Asara ya dinga samu daya bayan daya,kafin kace meye wannan?, komai nasa ya tafi sai abinda ba'a rasa ba. To duk sanda vanayi irin wannan ya faru dole a samu sauyin rayuwa abubuwan da aka saba yi a baya dole a sassauta wasu ma sugi samuwa don dai a samu a tsira da abinda yayi saura,a kumayi qogari da tanadin mai da rayuwa kan bigirenta na asali.


Sam ameesha tace batasan zancan ba, kawai dai yayi niyyar wulaganta ta ne da tozartata, kamar yadda mata da yawa ba kasafai suke iya fuskantar irin wannan yanayi ba idan ubangiji ya jarabci mazaje da shigarsa ba (akwai mugayen mazaje asalan,wadanda ba'a san samunsu ba saidai rashinsu, mazajen da basusan su yalwatawa iyali ba,suna da arziqi amma matansu saidai suji labari ko su gani a iya jikinsu su kadai, irin wadan nan koda ibtila'i irin wannan ya fada musu,ba kasafai ake zargin mace da kau da kai da rashin nuna tausayi a kansu ba,muddin namiji tsayayye ne wanda yake hidimtawa iyali da wahalta musu kaman toufeeq a labarin nan, to butulci na garshe da zaki masa shine ki nuna baki damu da shigarsa matsala ba,sanann baki zama matar rufin asiri ba, Allah yasa mu dace)..


A wanann lokacin da yake fafutukar gain yayi maintaining rayuwarsa tare da goqarin cike gibi da guraben da da wanann babbar gaddarar ta fada masa,daga gefe kuma ameesha na zuba nata lalatar kala kala. Ko sau daya bai taba yunqurin kaita qara ba,saboda tausayin mahaifiyarta da ko yaushe adduarta Allah ya qaddara dogon zama a tsakaninsu, mutu ka raba.


Cikinta yana da wata hudu kacal ta matsanta masa sai ya saketa, tace sam ba zata iya zama dashi ba,ta gaji da zama cikin talauci bayan mahaifinsa shahararren mai kudi ne, muguntar kai ko kuma girman kaine yake damunsa?, Da bazai shiga dukiyar mahaifinsa ya amfana da ita ba?,itama ta samu damar cika duka burikanta da muradan rayuwarta?.


Maganganun data fada a lokacin masu tsauri ne sosai da suka sosa masa zuciya. Daga daren har wayewar garin bata barshi ya runtsa ba, haka ya dauki takarda ya rubuta mata saki guda daya. Har zai fita ya dawo ya yanka mata zazzafan warning


"Koda wasa wani abu ya samu cikina,na rantse da ubangijin sammai da qassai sai nayi miki daurin da koda dukka qasarnan gatanki ne basu isa su karbeki ba".


Al'amarin ba qaramin farantawa haiiya garama yayi ba


"Ai duk mutumin daka ganshi a waje nan ne yafi dacewa da shi shi yasa Allah ya barshi a nan, ai duk inda talaka yake matsiyaci ne(ita ta manta tushenta),ni dama tunda naga idonta Muhammad nasan ba son Allah da ma'aiki takeyi maka ba,dukiyarka take so". 


Baice mata komai ba,saboda shi kadai yasan yanayin da yake ciki. Yayi tsammanin so guda daya ne tak!, ya dauka so na gaskiya shine so,wanda babu wani abu da yake iya canzashi, bai taba dauka akwai randa ameesha zata iya neman saki daga hannunsa ba saboda kawai raguwar abun duniya daga hannunsa, bayan bai gaza mata ta fannin ci sha suttura ko lafiyarta ba har a lokacin kuma. Duniya ta yiwa

•/ hajiya garama dadi, dama wani mugun tsana ta yiwa ameeshan,ko kusa ko alama bata gaunarta,don ko sau daya babu jituwa a tsakaninsu.


Sosai hankalin mamarta ya tashi, tayi kuka tayi fadan amma ameesha tayi kunnen uwae shegu,a sannan tayi wani irin kyau ta sake zama mace me aji ta kuma sake sanin cewa ita din matar manya ce duk ta silar auren toufeeq,ta samu sutturu masu aji, ta kuma sake smaun wayewar da take hangen doguwar shimfidaddiyar rayuwa data dara ta gidan toufeeq.yanzu abu daya ne zai zame mata cikas cikin da take dauke dashi,a galla akwai wasu watanni masu yawa a gabanta kafin ta haife ta kuma yaye,ita a yanzun koda haihuwarsa ta samu tayi, komai da zai biyo baya me sauqi ne.

Warning din da toufeeg ya karta mata shine abu guda daya da zai hanata juye cikin. Ta sani su din ba qananun mutane bane don dai kawai toufeeq din yana daukan kansa ba'a kowa ba, danginta kuma basa da garfin karawa dashi,so haquri ya zame mata dole kenan.


A zahiri tana son toufeeg sosai amma rayuwar data tsarawa kanta ta fuskanci ta sha banban datasa rayuwar da ya tsara,dole to ta ajiye nasa tsarin don cikar nata tsari da burin.


Allah me musanyawa bawan da ya dogara dashi daga mummuna zuwa abu mafi kyau cikin rayuwarsa.

Wata guda kacal da rabuwarsa da ameesha wani Erin

1 gofofin alkhairi suka dinga bude masa ta kowacce fuska.wasu alkhairan shi kansa bai taba tsammanin samunsu ba a irin wannan lokacin. Lokaci qalilan ya maida ninkin abinda ya rasa harda ma ninkin abinda ya rasa din a baya.


Cikin wata hudu kacal duk wanda ya kalleshi yasan ya samu sauyi na rayuwa fiye da rayuwarsa ta baya,ya warware sosai yaci gaba da harkokinsa,sabbin hanyoyin neman kudi suka bude masa fiye da zato.


Har a lokacin yana lissafe da watannin cikinsa dake jikin ameesha,kowanne wata yana aika mata da komai da yasan zata bugata, dai dai da ruwan sha na roba haka yake ajiye mata, komai na watanni biyu yake ajewa ninkin abinda zata bugata kenan, hakan baya hanashi sake aika mata da wani bayan kowanne wata.

Mamanta naso gwarai ta ganshi amma bata samu wannan damar ba, saboda bata da wayar hannu,sannan kuma shi kansa toufeeq din bai sake taka gidan ba tun daga ranar, amma kuma hakan bai hanashi yiwa mama din aike ba kamar yadda yakeyi mata a baya.


Tafiyar da yayi china wadda dawowarsa yayi dai dai da shigar cikin ameesha watan haihuwa, ya iso da siyayyar kayan baby me azabar yawa, har hajiya garama ta kasa jurewa


"Kai kam kamar wanda za'a haifawa taron arfa?, yariyar da basusan mutunci da darajarka ba toufeeq kae yiwa* wadan nan hidindimun?, kamar wanda ya rasa mafadi?"


Dan qaramin murmushi kawai ya saki,a sannan kome hajiya qaraman ta fadi baya bata ransa ko yaga cewa hakan ba dai dai bane, saidai idan abinda tace din yaji baiyi masa ba ko bai gamsu ba ya canza da abinda zuciyarsa ta kwanta da shi


"Mahaifiyar ta nagartacciyar macace,wadda nake da imanin da halinta tayo tare zamu tsufa ni da ita din, saidai mutuwa ta raba, haihuwa kuma ta fari ce hajiya, ko china din gaba daya ake da bugatar na siya masa indai arzigina ya kai zan siya din"


"To mara kunya,tashi ka bani waje" ta waske da fadin hakan ta bishi da kallo sanda yake barin wajen ranta a mugun quntace.


Lokacin da siyayyar kayan fitar suna nata da kayan baby ta iski ameesha ta gama saddaqarwa toufeeq din ya fara komawa CLASSY TOUFEEQ JARMA din da takeson gani, ta kasa zaune ta kasa tsaye a ranar sai data samu dukkan information da take nema akan TOUFEEQ din


"Turgashi, seema kina gain ban tafka wauta ba muddin na yarda na haihu a gida?bayan har yanzu da sonsa nake kwana da sonshi nake tashi?" Tace da gawarta da sukeJ zaune cikin dakinta dake eikin gidansu,wanda ta qawata fiye da kowanne guri na gidan. Tayi furucin ne a sanda take tsaye saman kan qawar tata da tirtsetsen cikinta da take lissafe da randa zata saukeshi ta huta



"Ba garamar wauta ba,wannan arzigin dake yafi dacewa,ke yafi cancantar ki cishi"


"Yanzu meye mafita?, ta yaya zan jawo hanakalinsa?"


"Ke kike da hanya kuwa" seema ta fada tana mata nuni da cikinta. Murmushi ta saki tana shafa cikin nata hadi da gyada kai,sai ta koma ta zauna ta jawo wayarta ta fara kiran number wayar toufeeq din.


Har ta garashi ringing dinta ta katse bai daga ba,a qalla ta kirashi ya kusa sau goma amma abiyi picking ba,wannan ya soma daga mata hankali,seema tace


"Yasan ke kike kiransa karanto min numbers din na kira miki shi a wayata ko za'a dace ya daga"


Harara ta watsawa seemar tana jin kamar ta mareta,ita zata bawa kura ajiyar nama?.


"An gaya miki yana daga baqin numbers ne? ai saidai ki dige kina kiransa amma bazai dauka ba,bari ki gani" ameesha ta fada tana gyara zama tare da tura masa gajeran text.


Ba dadewa saiga kiransa, murmushi ameesha tayi

ta migawa seema wayar


"Ki daga kice masa yazo yanzun kamar labour nakeyi yazo mu wuce asibiti" lokacin yana tare da wasu baqi,jin zancan yasa ya barsu ya tsallako ya taho.

Yayi mamaki da ya ganta tana fitowa lafiya sumul, Ransa kuma va baci da jin abinda vasa ta kirashi da wannan sigar data daga hankalinsa. Har ta gama bayaninta da koke koke baice mata ta tafas ba,sai data gama sannan ya juya ya bude motarsa zai shige kafin ya waiwayo


"Karki sake maimaita yimin irin wannan shashancin, don ni din ba mara aikin yi bane ba zaman banza nake ba da zaman jiran kiran wayarki" sai ya tashi motarsa yabar gurin.


Hankalinta yayi gololuwar tashi qwarai, saboda yadda take ganin so kulawa da qauna daga idanun

TOUFEEO din bata taba tsammanin zai juyawa buqatarta baya ba,musamman da ya zamanto a yanzun tana dauke da abu mafi soyuwa a wajensa a jikinta ba. A ranar da gyar ta iya bacci.


Kwana biyu kacal da faruwar hakan Allah ya yiwa mahaifiyarta rasuwa,wanda shine ya zama silar sassautowar zuciyarsa,ya kuma sauka daga dokin nagin da ya hau,ranar sadakar bakwai ya dauketa ya maidata gidansa da kansa. Ashe wasa farin girki!!



Zafafabiyar

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

No comments