Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 49

 


Book 02Page 49




Washegari har qarfe sha biyu na rana bai fito ba,yana kwance yana jinyar jiki da zuciyarsa gaba daya.

He's ready to meet them ko ina ma suka tafi ba tare daya gayawa maji ba,don bayason ta hanashi ko ta rogesa don yasan bazai iya ba,wannan ya sakashi ba shiri ya nemi Dr anwar,ya iskeshi cikin yanayin matsanancin zazzafan zazzabi,wanda dole ya sanya aka daura masa drip a parlor dinsa.


Ranar sukayi da Jacob zai dawo, amma baikai ga isowa ba, sannan Dr anwar yace lallai yaci wani abu,dole ta sanya ya turama nadeeya gajeran tex,sai gata ta iso parlor din a gigice


"Yaa moha,dama baka da lafiya?,jiya ba lafiya ka kwanta ba? me ya sameka?"


"Relax, relax" ya fada cikin coolness da jigatacciyar muryarsa da abubuwa da yawa suka tarar mata, idanunsa akan fuskar nadeeya wani irin tausayinsu yana ratsashi,waye yasan yawan adadin cutarwar da ta yi musu ne ma?. Ita dinma kallon toufeeq din takeyi,tana mamakin wanne irin ciwo ne haka farat daya da ya sanya fuskarsa ta faada?.


"Ki samo min tea da wani abu lite zanci kafin ruwan ya aare"


"Okay yaaya" ta fadi tana juyawa da hanzari ta fita a sashen,ya rakata da ido har ya gama fita sannan ya maida idanun nasa ya kulle.


Shawaginta na biyu kenan cikin gidan, saidai sam sam bataga wulgawarta ba,hakanan bataga motsin fadeela ba koda wasa,duk kuwa da cewa yau din weekend ne,baka rasa zirga zirgar yarinyar a farfajiyar gidan wunin ranar gaba daya,musamman idan basu fita ba, sannan shi kansa toufeeq an shaida mata yana cikin gidan,amma tun daga wayewar gari zuwa yanzun ace bai nemeta ba?,duk da ta dade da lura abubuwa nata canzawa, tun daga ranar da yarinyar ta amsa sunan matarsa kawo yau,to amma kuma lokaci ta bawa kowa,jira take ta gama yiwa kowa shirinsa na daban. 

Ko ubansa jarma da yayi tafiya ba tare da ya shaida mata inda yaje ba,da kuma adadin kwanakin da zaiyi kamar yadda ya saba shaida mata, tana sane da wannan, kuma ba zata taba bari hakan taci gaba da faruwa ba

Nadeeya na fitowa sukayi clashing da hajiya garama


"Ke,ke lafiya?" Hajiyan ta kira nadeeya da sauri,dan datakawa tayi


"Ba komai yaa toufeeq ne bashi da lafiya zan sama masa wani abu yaci kafin a gama qara masa ruwa" gaban hajiyan ya fadi, saboda a yanzun bata shirya wani abu ya samu toufeeq ba sam, shine hope dinta, shine kuma matakala sannan kuma tsananta na dukka plans dinta


"Me ya sameshi?" Ta tambayeta cikin damuwa, dan goge zufar goshinta tayi da tafin hannunta


"Ban sani ba mommy, kinsan sanin ainihin ciwon yaa moha ba abu bane me saugi tun asali"


"Na sani, jeki kawo masan" ta fadi tana wuce nadeeya zuwa sashen toufeeq din.


Sallamarta kadai yaji ya maida idanunsa ya rufe, ko da wasa baison gain fuskarta, domin har zuwa lokacin bai gama yanke matsaya akanta ba ganinta da idanunsa a wannan yanayin da yake ciki na iya tunzurashi, kuma. komal yana iva faruwa


"Muhammad" ta kirashi a hankali amma sai yayi banza da ita duk kuwa da hannuwansa suna motsawa kadan kadan. Sake kiran sunan nasa tayl a karo na biyu amma ya bawa banza ajiyarta,saukar muryarta cikin kunnensa dai dai yake da saukar tafasashen ruwan dalma.


"Ko ya samu bacci? na dawo anjima" ta fadi qasa qasa sai ta juva tana fita daga falon. Tun bata gama fita ba ya bude idanun nasa, yanajin kamar ya jawota yayi mata mugun dukan da sai ta gaya masa laifin da fadeela tayi mata a rayuwa,amma dole yayi aiki da hankalinsa a dukka hukuncin da zai yanke, saboda ya riga ya sani girman matsayinta wajen mahaifinsa, after all hausawa sukace idan baka iya kama barawo ba shi sai ya kamaka, saidai daga rana irin ta yau, koda fadeela tana gasar, to ba shakka ya haramta mata ganinta kwata kwata.


A gurguje nadeeya ta hada masa duk abinda zai bugata, tana fitowa falo zata wuce meenal ta shigo, ba wani sabo bane me yawa a tsakaninsu ba duk da cewa shekarunsu tazarar kadance ga kuma dangantakar dake tsakaninsu amma ko yaushe kamar bagin juna suke. Ita nadeeya mutum ce me faran faran da son jama'a ko kadan bata dauki duniyarta da fadi ba bata kuma dauki kanta ta aje can da nisa ba yayin da meenal take akasin haka tana da matugar fadin rai da jin kanta cewa ita din wata ce ta daban, gwanar girman kai da fadin rai, kamar zata wuce sai kuma tace


"Sister nadeeya baqo mukayi ne?" Sai da tayi gaba sannan ta amsa mata


"Yaa toufeeq zan kaiwa, bayajin dadi ne" ajiye komai tayi ta biyo bayanta da sauri, kwanaki kusan bakwai kenan tanason ganinsa amma kuma tana hagura saboda zazzafan warning din da ya aje mata kan shiga sashensa haka siddan ba tare da dalili me qarfi ba,a yau din kuwa ta samu dalili me qarfin.


Idanunsa da har yau basu gama dawowa dai dai ba va zubawa meenal,wani kwarjini nasa tare da zazzafan gaunarsa na sake hudata


"'Tsaya a nan" ya fada cikin tsawa, maganar tasa data sanyata jan burki ta tsaya din tana dubansa gabanta yana faduwa


"Daga yau sai yau, daga kuma rana irin ta yau, koda wasa, koda ganganci idan na sake gain gafarki a sassan nan sai na ballaki balluwar da bazaki moru ba kin gama tashi a aiki kenan har abada, bacemin a gun idiot!" Ga fada da tsawa me garfi wadda hatta nadeeya sai da hantar cikinta ya kada. Har takai qofa ta jiyo muryarsa yana cewa



"Ki hada dukka kayanki ki koma bangaren babarki, daga yau kar na sake ganinki a wannan sashen" kamar zata kifa haka ya garasa ficewa tana sakin kuka me sauti, bata ko damu da ma'aikatan gidan dake binta da kallo ba,har ta isa sashen hajiya qaraman ta sameta a parlor ta fadi a jikinta.


A rude ta dagota tana tambayarta


"Ke lafiya? me ya sameki haka?" Cikin sheshsheqar kuka ta gaya mata


"Banason qarya da sakarci, yanzun nan na shiga dubashi na sameshi yana bacci,sannan bugu da gari ma babu ta yadda za'a yi toufeeq ya gaya miki haka" masifa da fada sosai ta rufe hajiya garama dashi


"Haka kike gani ko? zan miki qarya ne?, komai nace yayi sai kinyi shakka, bayan a gaban idanunki yakeyin wasu abubuwan?, ina dukka tutiyarki da alfaharinki? ina abubuwan da kike alfahari da su? duk ni a wajena a banza suke tunda toufeeq kawai kin kasa mallakamin shi to wallahi wallahi nan da watanni biyu masu zuwa indai baki mallakamin muradin zuciya ta, kema ba zakiga abinda ranki yakeso ba" tsananin bacin rai ya sanya hajiya garama ware hannunta ta mari haseena, karo na farko da hakan ta faru tsayin rayuwarta


"Baki da hankali ni kike gayawa haka?" Dafe da kuncinta take duban hajiyan


"Ni kika mara momy?" Yadda tayi tambayar a tsaye tamkar hajiyarce diya ta mari mahaifiyarta haseena. kallon da take binta da shi ya sanyaya jikinta,sai a sannan ta tuna, mahaifinta sai da yayi mata bayani kafin va barta ta taho


"Ba'a bata mata rai,saboda tana da wani hali me kama da cutar tsananin fushi" da sauri ta kamo hannunta ta rige tana fadin


"Kiyi haquri, nayi miki alqawarin mallakar toufeeq a wata guda kacal, qasa da abinda kika buqata"


"Ashe zan take faranti kenan kowa ya rasa" muryar hajiya Muneera ta baqunci kunnensu, abinda ya sanya suka maida hankalinsu bakin qofa. Kaifin idanunsu bai hanata ci gaba da qarasowa falon ba, itama su take kalla


"Ashe da gaske ke din 'yar kunama ce fauziyya?,ni zaki yaudara kiyi wasa da tunani na? ki lasawa diyata zuma a baki yanzun kuma ki maye mata gurbinta da madaci?, tunda haka abun ya zama nafsi nafsi, kowa divan cikinsa ya sani to ki kwana da sanin muddin labiba bata samu toufeea ba haseena ma ta rasashi har abada" tana sauke furucin haseena na sauke mata lafiyayyen mari a fuska. Tsananin mamakin dava zarta zafin marin da shi hajiya Muneera ke kallon haseena baki bude


"Shashasha. ke har kin isa ki hanani samun muradin raina? ba mutum ba, ko mutuwa banajin tayi wannan isar"


"Kinyimin dai dai,ai da kin barta ma baki maretan ba" sai hajiya qarama ta matso gaban hajiya Muneera din tana mata wani kallo


"Bazance karki taka faranti ba,ki taka,amma ki takashi kina da sanin cewa idan zai bare zai bare ne harda aurenki da YAYA NA, zakiga mummunan sakamakon da baki taba tunanin aukuwarsa ba,karki manta inada qarfin sawa a auro a kuma saki a duk sanda naso hakan" Sai a sannan ta sauke hannuwanta daga kuncinta inda haseena ta mareta


"Bavan kuma va bare da aure na alagarki da yayanki shine abu na garshe da zai garasa zirarewa daga farantin,wannan marin da 'yarki tayimin ki rubuta ki ajiye,sai ya zame muku nadama da ba zaku iya kauce mata ba, fauziyya kada ki manta,ni dake kar tasan kar ne‚wanda ya fasa a tsakanina dake baya ya raina Allah"


"Da kyau!" Hajiya garama ta fada sai haiiya mansuran ta tsugunna ta dauki jakarta data fadi a gurin,ta kuma juya tana fita daga sashen cikin matsanancin baqinciki vau ace yarinya kamar haseena da aka haifa a gabanta?,yarinyar da ko autarta ya girmeta ita zata daga hannu ta sauke a fuskarta?.


Gaba daya hankalinsa bai kwanta ba har sai daya tabbatar ya sanya a nema masa visan Germany. Duka duka so yayi ace ya samu cikin sati guda kacal,amma aka shaida masa bazaiyiwu ba,short stay ma zata iya daukan sati biyu kafin ta samu


"It's too long ya rabbi* ya furta qasa qasa yana karanta bayaman da aka turo masan. Hakanan don babu yadda zaiyi yayi accepting a hakan ya sanyama ranshi salama da dangana, amma ji yakeyi ranar kamar ba zata zo ba, kamar ba zasu hadu ba.


A ranar bayan Dr anwar ya cire masa garin ruwan yayi booking na daki a bristol palace, suit din da ya saba kamawa ya kama na tsahon sati biyun, sabodia baya jin zai iya ci gaba da zama gida daya tare da hajiya garaman. Ya riga ya saita camera din da wayarsa, koda yana can zai iya ganin dukkan abinda yaso. Nadeeya batasan abinda yake faruwa ba kawai taji toufeeg din yace ta shirya kayanta kaman na 2weeks zasu bar gidan su sha iska, hakanan ya tura baba ramatu gurin abokiyar zaman mahaiffyar sajjad, gidan ya rage daga hajiya garama sai masu aiki.



*******Cikin nasara fadeela ta kammala kwanakin da suka diba mata kafin aikin, duka gwaje gwaje sun kammala,hakama shirin aikin nata,aka sanya mata rana da kuma lokaci.


Zuwan ba zata sajjad da afifa sukayi mata ana ya gobe za'a yi aikin,batasan cewa tana da rauni ba sai da taga bestie dinta,ashe dai tana bugatar wani a kusa,ta rige hannun afifa da kvau hawave nason sauko mata


"C'mon bestie meye haka? u are strong woman,kinyi abinda ba kowa ne zai iya ba, kici gaba da addu'a,it will be successful surgery in sha Allah".


A ranar babu wani wadataccen bacci da tayi,kamar ko yaushe ta kwana tana sallah tare da addu'a me tarin yawa.



***K'arfe takwas na safe afifa ta shigo musu da lafiyayyen breakfast da sajjad yayi musu order. A tsaye gaban madubi ta samu säahar cikin black laffaya me adon silver a jiki. Agogon hannunta silver color take daurawa, komai nata cikin sanyi take yinsa,saidai tayi wani irin mugun sassanyan kyau,kayan sun haskata sosai tare da gara mata wani irin kwarjini, Wayarta ta jawo ta sake duba sagon toufeeq na daren jiya,wasu irin sagonni yake aike mata masu taushi da narkar da zuciya cikin kwanakin saboda koda ya kirata bata dagawa,haka kawai takeii a ranta kamar tayi masa wani babban laifi da bazai gogu ba,ta dinga jin kamar ta shaida masa abinda sukeyi a Germany. Idanun afifa a kanta har ta garaso, dai dai sanda fa ajjiye wayar ta maida dubanta kan afifa


"Afifa, am afraid" a nutse ta tako ta dafa kafadarta tana murmushi


"Karki saare bestie,khairan in sha Allah" sai ta miqa hannu ta dauko cup na tea data hada mata da plate dindake dauke da tarkacen chips dasu ketchup


"Kici wani abu kafin mu fita" kai ta girgiza


"'Bazan iya ba bestie, tunda nazo garin nan sau daya

nake iya cin abinci" ido ta fiddo


"Saboda me?" Kafada ta dage


"Ban sani ba afifa, kawai inajin cushewar ciki ne,sannannayi loosing apatite gaba dayaa, bakina bashi da taste"


"Kuma a hakan sai a duka yawon shaqatawa

kikazo fatarki tayi wani mugun fresh da haske kamar

wadda ke wanka da madara" wani marayan murmushi tasaki tana kaiwa afifan duka


"Ke har yanzu baki girma ba wai?,ga baby kina shirin ajemana,mutumin da bai iya cin abinci yaushe zai samu irinwannan nutsuwar da kike fada?"


"Eh kika sani ko babies din namu tare sukeson isowa" afifa ta fada tana murmushin tsokana. Dan tsuke fuska tayi tana harararta



Zafafa biyar

??????????????

??????????????

[05/10, 11:55 am] Mimah Yusuf: "HUGUMA*

No comments