Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 40

 


Book 02 Page 40



"Na shirya tafiya da fadeela don yi mata aiki ta rabu da lalurar da take fama da ita a sirrance ba tare da ko mahaifinta va sani ba bare mutanen da muke rayuwa

tare dasu ba"


"Allahu akhbar " maji ta maimaita har sau uku

"Kamar tare dake muke wanann tunanin? wannan shine abinda na shirya aiwatarwa na farko bayan na dawo Nigeria,na baki goyon baya alf bil alf(dari bisa dari)"


"Amma maji, banason kowa ya sani saboda ina tsoron kada a sanya abun yaqi yiwuwa" kamilin murmushi maji ta saki


"Fauziyya hajiya qarama,ko ba ita kike tsoron kada ta sanya moha ya hana ba?,ina da labarin yadda tayi ruwa tayi tsaki ta hana duk wata maganar da za'a tayar akan a yiwa fadeela aiki,na bar zancen ne akan cewa ni daya zan iya aiwatar da aikin, koda ita din bataso,saboda nasan duk inda takai ga girman kaidinta,bata isa ta sanya moha ya hanani ba.….....har yanzu bakisan me fauziyya ta yiwa rayuwata ba,zauna da kyau diyata yau na gaya miki labarin da masu shekaru irin naki dake rayuwa tare dani basu sani ba" a sanyaye sãahar ta gyara zamanta saman gadon sosai, tun kafin taji komai daga bakin maji jikinta ya sanyaya,ba abinda take haskowa sai fuskar hajiya qarama a sannan.



* TUNA BAYA 1988 *


Mummunar faduwa gabanta yayi,wani irin hargitsatsen kallo daya watsa mata shi ya sanyata cikin rudani, batasan me tayi masa banda kulle qofa da tafiya da key din,kallon daya watsa mata yafi qarfin wannan laifin, kallo ne na zallar qasqanci da kuma tsana,tasan dai ranar yau lafiya galau suka rabu,ya fita cike da murna zai karbo upper dinsa aiki ya samu,suna ta murna dukkansu tare da saka ran fita daga tsanani zuwa sauqi, sai dukka gwiwarta tayi sanyi da irin nau'in kallon da yake jefa mata.


Kafin ta qaraso ainihin tsakar gidan sai wulgawar fauziyya ta gani, wadda kanta ke daure da bandeji da yayi tsatstsafar jini gaba daya daga samansa,ta nufeshi a gigice ta cukuikuyeshi tana neman mafaka a bayansa,bakinta na wani irin rawa na zallar toro da firgici take cewa


"Na shiga uku akh, gata nan ta dawo,don Allah ka boyeni,kada ka bari ta qaraso,wallahi zata qarasa illatani kamar yadda taci alwashi" tayi maganar tana wani irin haki da tawar jiki, kamar wadda tayi gudun kwana da wuni.


Baki kawai ta saki galala tana kallon fauziyya,qwaqwalwarta gaba daya ta rikice,me take nufi ne? saita maida dubanta ga bandejin kanta tana mamakin me ya sameta daga fitarta


"Bata isa tayi miki komai ba,a yau qarshen al 'amarinta yazo, muguntarta a kanki kuma ta qare!" Muryarsa mai zurfi dake fita da amon fushi ta fusgi hankalinta, saita maida dubanta kansu gaba daya, kwanyarta na sake rikicewa da salon maganganunsu da ba ganewa takeyi ba.


Ci gaba tayi da kallonsa, saidai ya zaro biron dake.

gaban aljihunsa ya kuma dauko takarda a daya aljihun nasa,ya bude kan biron cikin fusata. Cikin mamaki me yawa taga fauziyya ta kama biron ta riqe gam


"Me zakayi yaaya, ka rufamin asiri don Allah, kada kace zaka saketa saboda ni" ta fada hawaye na wanke mata fuska. "Ki saki fauziyya,duk mutumin da bayason jininka kaima baya qaunarka,ban ga amfanin zama da ita ba, baya ga tarin dimbin gori da maganganun data fada a kanmu" kuka sosai fauziyya keyi,ta kuma riqe abun rubutun taqi sakar masa tana bashi haquri, abinda yayi masifar daure tunanin SHIFA, me yasa fauziyyan dake burin afkuwar haka ita ke bada haqurin kada a saketa?.


"Kinci darajarta,ki dubi abun kunya wanda kike quntatawa shine yayi silar kubutar dake daga afkuwar wani mummunan abu a kanki" mamaki ya sake kasheta,kanta ya daure tamau, tama kasa cewa komai baki sake take kallonsa har ya miqe ya nufi hanyar soron gidan,har yanzu zallar bacin ran dake saman fuskarsa bata gushe ba. Har yakai bakin qofar sai kuma ya dawo,ya tsaya gaban fauziyya dake zube tana kuka


"Tashi ki wuce ciki". Bai barta ba har sai daya rakata cikin dakinta,ya dan jima ma a ciki kafin ya fito,zuwa sannan shifa ta ja jikinta da qyar ta wuce zuwa nata dakin clkin mawuyacin hali,tare da hasashen me yake ta faruwa da ita ne a rayuwarta haka? tun ranar da fauziyya ta sanya qafarta a gidan da nufin zama dasu,na wata shidda kawai ta samu kwanciyar hanakali bayan zuwan nata,daga bayan wannan watanni shidan bata sake samun sauqi ko salama ba. 


Duk wani farinciki nata ta warwareshi tasss ba tare da tasan meye dalilin da yasa taketa aikata hakan ba. A iya saninta,mahaifiyarsu mahmud macace mai kirkin gaske da kowa ke yabonta bayan rasuwarta, zamanta da fauziyya na watanni shidan nan,zama ne na kyautata mata da kula da ita,saboda

tana mata kallon mahmud, mahmud kuwa ba zata manta da soyayyarsa a gareta ba, duk da cewa ba kowa cikin danginta ke son aurensu da shi ba, kasancewarsa shi din dan Nigeria ne, ita kuma 'yar Algeria ce, duk da shi dimma

fari ne tas kalar yarensu da idan ba fada kayi ba za'a

dauka Algerian ne shi dinma, kasancewar ya fita daga

tsatson SHUWA-ARAB wanda asalinsu dama larabawan ne.


Wani irin zama tayi cikin dakin cikin qunci da

kukan zuci,da Muhammad da nadeeya kowa kuka

yake, amma kusan hanakalinta yayi nisa a tunani,taji

alamun kuke sukeyi,amma saboda tsanar tunani da

damuwa bata farga da kukan da sukeyi ba,har sai da

taga fadowar fauziyya dakin kamar wadda aka jeho.

Kafin tayi kowanne irin tunani ta dauke nadeeya dake

tsaye daga bayanta tana kiran sunanta ta hau jijjigata.

Sallamar mahmud da shigowarsa cikin dakin shi ya ankarar da maji dalilin wannan shigowar ta fauziyya ta ba zata,iya saninta ko daya bata iya tayata wahalar yaran,zafi ko sanyi koda azumi akeyi ita zata yi korai dinta fauziyyan na daga kwance, saidai ta fito ta debi abincinta ta koma daki, idan ta gama sabgoginta kuma ta wanke jikinta tayi ficewarta unguwa,ba zata dawo ba sal ta daidaicin lokacin dawowar dan uwanta.

Hannu yasa ya karbi nadeeyan, fauziyyan da ta sake tara wani qwallan ta dubi yaran


"Ku tayani bawa maji dinku haquri, kada tayi fushi da ni,ni din marainiya ce,bani da kowa sai yayana sai ita da nake saka ran ta zamemin makwafin uwa" ta qarasa fada tana share qwallar munafurci. Gaba daya jinin jikin maji so yayi ya tsaya da harbawa,tabi fauziyya dake ci gaba da sharar qwalla da kallo


"Ni kadai na isa na tsaya miki, jeki abinki" mahmud ya fada yana miqa mata leda daya da ya shigo da ita ta takeaway. Har qasa ta durqusa ta saka hannu biyu ta karba tayi masa godiya tana fita.


Wani kallo ya juyo ya watsawa maji, ba komai idanunsa face zallar bacin rai da har yanzu bai gushe ba "Yau na gani da ido na,ansha gayamin yadda yake wulaqantar da yaran nan,hatta a wajen aiki ba wata

Kulawar kirki suke samu ba,saboda baqin hali tun daga waje nake jiyo kukansu amma kin gaza rarrashinsu,to daga rana irin ta yau na soke batun aikinki, ki zauna a gida ki kulamin da yarana da 'yar uwata" yayi maganar yana kamo toufeeq,ya zaunar dashi gefansa nadeeya na saman cinyarsa,ya bude musu daya takeaway din ya fara

basu.


Har yanzu jin komai take kamar a mafarki,sai a lokacin ta samu qwarin gwiwar waiwayawa gareshi


"Allah S W T cewa yayi,yaku wadanda kukayi imani,idan fasiqi yazo muku da labari kuyi bincike a kansa kada ku afkawa wasu mutane cikin rashin sani da jahilci saiku wayi gari kuna masu nadama akan abinda kuka aikata.


Wannan kenan kayi tunani akai,sannan meye hadin matsalar nan da maganar fitata aiki mahmud?" A harzuqe yake kallonta


"Waye jahilin kenan? ‚ni ko 'yaruwata?,ki gayamin?. Ta tabbata kin rainanin d gaske, rainin da ake cewa kinyimin ban sake tabbatarwa ba sai a yanzun,illar mace ta dinga taimaka kenan,koda bakai ka buqata ba wataran sai irin wannan ta gifta a tsakaninku,Allah yasa ba ahaka kika aureni ba da na shiga uku wallahi wallahi, aiki kin daina yinsa,sannan duk wani abu da kikasan kin tallafamin da shi ki zauna ki rubuta daga yau zuwa gobe,tsinke kada ki dagamin qafa,zan maida miki abinki" qas tayi da kanta,hawayen da tun dazu basu zuba ba yanzu suke zuba,maganar da ya gaya mata yanzu tafi zancan barinta aiki ciwo,duk wani fadi tashin rufa musu asiri da takeyi bayan karayar arziqinsa,dai dai da rana daya bata taba jin ta qosa ko ya dameta ba, amma yau da wadan nan kalaman zai saka mata?,komai da tayi musu tayi masa ne saboda tana ganin ya cancanci fiye da haka,namiji ne shi me bala'in kulawa da gida da matarsa,sanda yake dashi babu abinda baiyi mata ba,a lokacin duniya tana kwance, fauziyya bata shigo rayuwarsu ba,sai lokacin ta tuna da kalaman haiia mahaifiyarsu,a duk sanda sukaje borno ba zata dawo ba ba tare da hajjan tayi gorafin fauziyya ba


"Fauziyya, fauziyya,Allah ya shiryamin dai kawai" ba yawan zama take dasu ba,shi yasa a lokacin ba zatace

• ga wani hali nata ba,hakanan ba zatace ga abinda ta taba yi mata maras dadi ba,ashe ita din kara da kiyashi ce daukan mara sani.


Ranar har ta kwanta bata sanyawa cikinta komai ba sai bacin rai da taketa kurba da dogon tunanin ta inda zata kamo bakin zaren. Bayan sallar isha'i tana jinsa shida yara a dakin fauziyyan sunata hirarsu abinsu,kamar ma bata a cikin gidan. Sanda yaran sukayi bacci ya kawo mata su ya shimfide mata su ya juya abinsa ya fice. Kasa haquri tayi,bayan awa daya ta shirya ta miqe ta bishi dakinsa. Tunda ya amsa sallamarta bai sake daga kai ya dubeta ba,gabansa ta tsugunna cikin sanyi da mutuwar jiki


"Ya kamata mu warware sabanin da yake tsakaninmu ta hanyar tattaunawa,bai kamata mu fara yin abinda bamu saba dashi ba" har ta gama maganarta baice ci kanki ba,hasalima shirin bacci ya tashi ya fara yi daya kammala ya haye gadonsa ya kwanta yana fadin


"Idan kin gama ki rufemin qofata" yaja bargo ya lullube har saman kansa. A ranar shifa tayi kuka tayi kuka har taji babu dadi, meye da meye wai fauziyya ta gaya masa haka me zafi? wannan iri fushin koda mahaifiyarsa ta tsinewa albarka ai iyaka kenan.


Washegari saboda bata samu bacci da wuri ba ta makara bata tashi da wuri ba,tana tsaka da baccinta ta dinga jiyo qamshi cikin hancinta,sai ta farka tana salati ganin ta makara,ta shiga toilet tayi brush ta fito tana qoqarin kama ayyukanta na gida,don ko ciwo takeyi babu mataimaki,haka zata rarrafa tayi ayyukan nata, Muhammad na taimaka mata da dauko wannan ajjiye,duk da shekarunsa ba wani kaiwa sukayi ba.


Mamaki ne ya kusa kasheta,don fauziyya ta gyare gidan fes an kintsashi,hatta da yaran tayi musu wanka,hakanan ta kammala breakfast tana ta shiryawa a cooler da take zubawa mahmud abinci, yara nata tsalle hannunsu daya chips daya soyayyan qwai,shi kansa qwai din da chips din batasan ina aka samoshi ba,saboda tasan duk kayan abincin data siya musu wancan watan sun qare. Jiki a sanyaye ta qarasa shiga kitchen din,suka hada ido da fauziyyan tana rufe cooler din,sai ta sakar mata murmushi


"Barka da tashi matar yaaya,nasan tun jiya akwai tambayoyi fal kanki ko?,to yanzun kina da minti talatin zuwa arba'in da zakiyi kowacce tambaya taki zan baki amsarta,saboda yaayan ya fita yomin cefane, zan iya saurarenki kafin ya dawo" kaman majin zata ce wani abun sai ta dauke kanta daga dubanta, dariya ta saki tana cewa


"Bari to na taimakeki na rage miki wasu amsoshin tambayoyin…..nasan kin shiga kogin tunanin meye dalili na na hana yaaya ya sakeki ko? ‚nayi hakanne saboda banason tafiyarki yanzu,nafison saikin gasu yadda ya kamata, idanunki kuma sun gane miki girman matsayina a wajensa da kuma qarfin izzata,ta yadda zaki rayu kina bada labari a duk inda kika zauna"

[02/10, 2:56 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*


No comments