Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 38

 



Book 02 Page 38



Tunda ya shaida mata ta daina fita company ya

zamana kamar gaba ita ta kaita. Gaba daya tayi qaura

daga sashensa ta koma dakin fadeela ta tattara

hankalinta akan yarinyar, gefe guda kuma tana soma

musu shirin fita asibiti ita da fadeelan ba tare da kowa ya sani ba.


Cikin ilkinsa ya fara jin rashin dadin sassan gaba

daya,a hankali ya fara taba ruhi da zuciyarsa,tun yana

tunanin ba komai bane, sabo ne kawai da hausawa ke

fadin turken wawa ne, har ya karanci lamarin ya fara zarta haka. A hankali ya fara rasa baccinsa saidai ya yita juyi saman gadon yana tuna sweet moment din nan,wanda yabar masa wani irin tunani me yawan gaske da kuma dadi da sanyaya zukata.


*******Shi daya ne zaune a falonsu, sai tarin ayyukan da suka sanyashi a gaba,wanda gaba daya sam sam baya jin dadinsu,yana yinsu ne bisa tilas. Gefe daga kuma abinda ya faru dazun tsakaninsa da meenal ke dawo masa,yarinyar ta koma masa tamkar wata zautacciya,tun tana bashi dariya da mamaki abun har ya fara qureshi, bata kunyar fadi masa komai a gaban kowa, ko a dazu sai da yayi kamar zai mammareta ya samu ta fita a sashen. Ajiyar zuciya ya sauke yana ajjiye aikin da yakeyi din,jikin kujerar ya koma ya jingina yana dan lumshe idanunsa, babu laifin wadda yake gani sai nata, itakam wai kamar babu zuciya a qirjinta?, da gaske bata damu da al'amuransa ba,bata kishinsa haka yana nufin bata sonshi fa kenan. Ya baiwa kansa da kansa wannan amsar, abinda ya sanyashi sakin ajiyar zuciya me nauyin.


Fadeela ce tayi sallama ta shigo,ya daga kai yana duban yarinyar sai ya saki murmushi. Da gaske qiba takeyi abinta,abinda suka debe tsammani kwata kwata daga shi,sun dauka jikinta ne a haka.


Da sassarfa ta iso gareshi, ta fada saman cinyarsa tana kiran sunansa, hancinsa ya shaqi wani daddadan qamshi daga jikin yarinyar


"Ya akayi kika fito at this time haka? bakiga dare ya fara ba?" Juyi tayi a jikinsa


"Ko aunty N batasan na fito bafa?, hmmm cewa tayi itama dare yayi tunda munyi shirin zamu kwanta, kaj ma har turarenta ta shafa min" ido ya lumshe ya bude,yana jin dadin qamshin qwarai, zuciyarsa ta motsa shi qwarai,sai yaji bazai iya jurewa ba,don haka ya miqe yana cewa ina zuwa 


Dakinsa ya shiga ya dauki wayarsa ya saka slippers sannan ya kama hannun fadeela suka fito Sassansu suka nufa kai tsaye idanunsa suka sauka a sashen hajilya qarama,yau kwana biyu kenan baiji motsinta ba duka kwanakin ya gaza takawa sassanta ya gaidata kamar yadda ya saba, haka kawai yakejin kamar an cire hakan fit daga zuciyarsa, sake tunawa yayi da kiran da nadeeya tayi masa dazu tana shaida masa,taji hajiyan na magana cikin waya,gobe yinin bikin qawarta, kuma kamar a can zasu wuni. Kansa ya dauke daga gurin,cikin kamewar nan tasa yayi sallama cikin falonsu nadeeya


Tun bai gama yin sallamar ba ba kuma tare data daga kai ta dubeshi ba gabanta yayi wani irin faduwa, kafiya da taurin kanta ya sanya taqi daga kai ta Kalleshi,sai taci gaba da sabgarta. Idanunsa a kanta har ya qaraso falon. Nadeeya ce ta fara gaidashi, ya amsa yans miqa mata hannun fadeela tare da yi mata alamar su tashi a gun lokacin yana gaisawa da baba ramatu.


Sai a sanann ta dan daga kai ba tare data kalli sashen da yake ba tace


"'Barka da dare, ina yini?" Sai ta mige da nufin barin gurin


"Inda ban wuni ba zaki ganni?, dawo ki zauna" ya fada da husky voice dinsa. Haka kawai jikinta taji ya mace mata,sautin muryarsa ya nuna a dakensa yake, kamar sautin da ta sani lokacin yana MT JARMA dinsa na asali.


"Zaman me kikeyi a nan?" Ya jefa mata tambayar kai tsaye yana soke hannuwansa cikin aljihun wandonsa, tambayar ta sanyata daga kai abisa dole ta dubeshi, sai taji bata da zarrar ci gaba da kallon nasa

"Kula da fadeela" ta bashi amsa tana kau da kai,don ta fuskanci izza ce sosai yau din akan fuskarsa. Kai ya girgiza, bayason yayi fushi wani me yawa yayi gogarin dai daita muryarsa


"Ki fidda komai naki kizo ki wuce part dinki,can din shine gidanki ba nan ba,karki bari na maimaita miki hakan,just five minutes na baki" daga haka ya wuce ciki. A daki ya samesu ita da nadeeya. Wani kallo ya jefawa nadeeya da ya sanyata shiga taitayinta


"Wato kece munafukar ko?" Ido ta fidda tana dubansa a dan tsorace


"Yaa me nayi?* Ta fada a karye


"Duk ranar da kuka qara bata guri ki tabbatar kashinkl ya bushe,don ba ku na aurowa ita ba" sosai maganar ta bawa nadeeya dariya, amma don dolenta ta cinye abarta, saboda ta san yin dariyar a gabansa ba qaramin match ta tarowa kanta ba. Sai ta karyar da kai


"Ayyah yaaya, kayi haquri nima nayi tunanin gaskiya

baik.


"Will you keep quiet maaa?" Ya furta a nutse


"Am sorry* ta furta itama tana kama bakinta.

Dan nazarin dakin yayi kadan,sanann ya K'arasa ya tsugunna a gaban fadeela


"Yau zaki kwana tare da anty nadeeya?, zan karbi aron nanny N dinki" murmushi fadeelar ta sake tana gyada kanta,sai ya shafa kanta 


"Good girl" waiwayawa yayi ga nadeeya ya sake wanu hade rai


"Ki kula da ita sosai, dole ki koyi abubuwan da take na bata kulawa, kar a bari ta fita, kada ta karbi komai daga hannun kowa,magungunan da antynta take bata su kadai zaki bata good night" ya fadi yana sake kissing goshin fadeela din sannan ya fita.


A falon ya sameta a tsaye, da alama fada baba ramatu keyi mata,amma fitowarsa ya sanyata yin shuru.


Gaba yayi abinsa,idanunta akan bayansa tayi qoqarin shanye abinda ya taso mata


"Fadeela fa?"


"Ba tare aka kawoku ba ko" ya bata amsa yana qarasa ficewa, cikin ransa yakejin dole ya zama jalirtacce, dole kuma ya karanta mata da gaske hi din mijinta ne, ita kuma itace matar,ya fahimci fada da baki bazaiyiwu ba, saidai taci gaba da karbar lectures din a karancenta.


A shirye yake ya gyara komai ya zama akan shiri, ta lasa masa wata zuma da tafi dukkan zumar duniya dadi zagi da Kuma gardi,baya tunanin jikinsa zai iya ci gaba da rayuwa hakanan ba tare da ta sake ci gaba da fitinarsa ba a rayuwa.


Zuciyarta kamar zata fashe sanda take isa sashen,har yanzu izzarsa da jin kansa yana nan,tsantsar rashin adalc da kuma yadda ya karya kowanne alqawari da yarjejeniyarsu. A falo ta sameshi, har cikin zuciyarsa da gangar jikinsa yaji giftawarta,amma bai ko dago kai ba, itakam ko sashen da yake bata kalla ba ta wuce kai tsaye zuwa dakinta.


Qamshinta ya gama rikitashi,yayi tsammanin zai iya ci gaba da aikinsa amma hakan sai ya gagara,ya zame takardar da yake dubawa daga idanunsa yana rufe idon,jikinsa da dukkan wata gaba ta jikin nasa suna amsawa


"Ya Allah" ya furta yana qanqame jikinsa, sai yasa hannuwansa ya tallafi fuskarsa yana sauraren bugun zuciyarsa da kuma fitar numfashinsa.

Ya kusa minti talatin a haka, daga qarshe ya tabbatar aikin bazai yiwu ba,sai ya tattara komai ya rufe, ya wuce dakinsa.


Wanka yayi,ya shirya cikin wasu silk pyjama masu sulbi na kamfanin The Natalya masu asalin tsada da kyau, komai nasa designer yake amfani dashi,wannan ya sanya ya sake zama na musamman, kuma duk inda ya ratsa yake zama na daban cikin mutane, Comb ya saka yana gyara sumarsa me santsi da ban sha'awa, ya saka hair mist na sumar da Beard mist dukka ya shafesu.


Qamshin ya hade gaba daya daga sassanyan turaren jikinsa suka bada wani qamshi a musamman.

Ya kammala ya dauki qaramin towel ya goge hannuwansa,sannan ya fara kiran number wani company wanda suke akin sanya CCTV camera. A taqaice sukayi magana dasu, ya kuma zabi kalar wadda yakeso a sanyasa masa tare da da adadi. Har ya fadi adadin sun gama wayar yayi sake kira,yana buqatar qarin wata guda biyun,yadan saki murmushi wanna karon da ya tuna a inda za'a sanya masan. Sago ya tura musu sannan ya kashe wayar,ya hadata da key din dakinsa ya bude qofar ya fito.


Kayan jikinta kawai ta sauya bayan shigarta dakin,tanata kumbure kumbure da ququninta; tsakiyar hakan taji wayar afifa. Sai data fara dauke wayar daga kunnenta sabida ihun dariyar afifa data sajjad


"Am sorry hayatee, Allah besty kawai na kira, daga ita zan kashe wayar...ton thanks zataji" sai kuma tayi sallama


"Ku fita a idona ke da saljad Allah fa" sahar din ta fada tana bata fuska. Dariya afifa ta saki


"Sorry my bestie, kinsan eikin lokacinsa ne yanzun, shi kuma baya gaunar yaga attention dina akan kowa a irin wannan lokacin sai shi, bestie anya akwai abinda yakai aure dadi?, komai na cikinsa me dadi ne wallahi, please ki saki rai da zuciyarki ki tarairayi mijinki ki kula dashi ku more rayuwarku nan da lokaci kadan zaku manta da komai ke da shi he is nice man, kuma idanunsa kadai kika

Kalla wallahi kinsan za'a sha soyayya me zafi daga hannunsa, hayatee yana gaya min,idan yanason mace bai iya qaramar soyayya ba, kulawarsa da dukkan lokacinsa nata ne ragama yake migawa,shi yasa da aka cutar da shi abun yayi mugun tabashi"


"Bestieeee.....,meye dalilin da yasa kika kirani? don ki bani wannan labarin?" Kai fa girgiza tana qaramar dariya


"A'ah your visa is ready, hakanan ticket asibiti da hotel din da zaku sauka, duka hayatee ya kammala,na kasa boye masa besty amma, kiyi haquri saboda tsaro, amma yayimin alqawarin ba wanda zaya gayawa, shima ya jima yana kwatanta shammatar toufeeq,amma shi bashi da qwarin gwiwar da ke kike da ita,zamu biyo bayanki after kun isa, an kuma tabbatar da abinda za'a yi matan" ido ta lumshe tana sake jin qaunar afifa, ta tashi bata da yar uwa mace amma afifa ta maye mata wannan gurbin, ita kanta batasan girman matsayin da afifa ke dashi a gurinta ba,duk wani yanayi na rayuwa da ta zata tsinci kanta a ciki,afifa she's standing by her side a koda yaushe.


"Bansa ta yaya zan gode miki ba, saidal nace Allah ya barki da hayatee dinki"


"Ya salam,kin gamamin addu'a,rayuwa da mutumin kirki ai ba abinda ya fita dadi" ta fada cikin shauqi, har abun ya sanya säahar murmushi me sauti


"Dole naci gaba da yimiki uzuri, kin gama dulmiya*


"Wallahi kuma bana tunanin zan fito, jininsu toufeeq suna da iya rige zuciyar mace da sassanyar soyayya, hakanan suna da tsayawa a rai,ke kanki yanzun idan na rantse kin fara sonshi bazanyi kaffara ba,bazan taba yarda yadda ya shayar dake madararsa ba sannan kice bai dasa kowanne irin feeling a ranki ba..." Tana kaiwa qarshen maganar ya tura qofar ya shigo, abinda ya sanya sahar katse wayar ba tare data y sallama da afifa ba, idanunta a kansa

[29/09, 11:47 am] +234 703 451 7171: *HUGUMA*


No comments