Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 30



Book 02 Page 30




Sau biyu tana dora hannunta akan handle din tana janyewa. Tana tunanin yadda zata shiga dakinsa yau a karon farko, tana kuma tunani da tsoron kada ya fasarata.


To amma kuma zuwan ya zame mata tamkar wajibi,don kowa a gidan da zai buqaci jin yanayin lafiyarsa ita zai fara tuntunba daga bakinta kuma za'a so aji komai. Uwa uba fadeela, data tashi ta tabbata abby din zata nema.


Kuma ko babu komai rama alkhairi sai dan halak, shine mutum na farko daya fara kulawa da kuma lura da sauyawarta lokacin da ciwon kanta ya motsa.

Sama sama ta soma jin kamar muryar meenal daga falonsu,wanda daga shi sai hallway din da kuma bedrooms dinsu. Bata sake tunani na biyu ba ta murda gofar kawai ta shige. Dai dai lokacin da yake kwance cikin duvet, bai jima da komawa ya kwanta ba,saboda a jiyan bai samu wani cikakken bacci ba,gaba daya idanunsa ne suka soye yanata hada lissafin da bai samu nutsuwa a kansa ba sai da zuciyarsa ga bashi gamsuwa da rinjaye akan bangare guda. Koda ya samu baccin sai tashi farkawa ba sai qarfe shida na safe, alfijir ya fara ketowa sosai. A razane ya sauko, hanzarin da ya sanya kanshi sarawa ya rige kan yana takawa a hankali ya wuce toilet. Alwala ya daura ya zauna yayi sallarsa,ya duba first aid kit ya balli maganin ciwon kai yasha. Yana gama lazumin ya lallaba ya koma gadon yana sake qudunduna a duvet din. Idanunsa ya lumshe a hankali,yanayin da vake tsintar kansa kowacce asuba ya fara sauka ga jikinsa, abinda bai taba tunani ba saboda ganin yadda ya kwana yana fama da tunani bacin rai da kuma ciwon kai.


Matse jikinsa yayi guri daya vana lumshe idanunsa,abun mamaki sai ga hotonta kar cikin duhun idanunsa sanye da farar gown dinta me qaramin hannutsigar jikinsa ta zuba lokacin da ya tuna yadda jikinta ya gogi nasa,sai ya runtse idonsa da kyau ya juya yayi rub da ciki yana gangame pillow da hannunsa tare da ambatar sunan Allah a sarari.


Duk yadda yayi zaton na wasu mintuna ne zuwa awa komai zaiyi narke masa amma abun ya wuce tunaninsa,maganin ciwon kan da yasha sai yakeiin kamar maganin wani garin garfi ya sha bana ciwon kai. Sake tura kansa yayi cikin duvet din yana kiran sunan Allah gasa qasa,jikinsa yayi dumi sosai ,sai hucin numfashinsa da ya cika duvet din wanda ke gauraye da sassanyan night scent dinsa,da ya rufe idanunsa ita yake gani cikin mabanbantan yanayin da yake ganinta, idan kuma ya bude idon nanma ba sauqi, abun kamar wani tsafi ko sihiri.


Kamar cikin mafarki yaji tattausar muryarta tana yin sallama cikin dakin. Tsai da numfashinsa yayi na wucin gadi yana cike da mamaki da kuma tantama, idanunsa a rufe ruf ba tare daya motsa ba, kunnuwansa suna jiyo takunta cikin lallausan carfet din dake dakin duk da takun nata baya bada sauti.

Koda bata zurafafa kalle kalle a bedroom din baiya iska da gamshin da yake fiddawa kadai ya isa gaya mata na musamamn ne fiye da kowanne daki dake gidan.


Wasu irin furniture na alfarma masu tafiya da hankali, luxury curtains da suka mamave dakin suka sanvashi ya sake zama wani luf luf da babu lallai ka iva tantance dare ne ko kuwa rana?. Akwai wadatar hasken fitilu a dakin har kusan color biyu,farin qwai da kuma light blue sai suka hadu suka bada wata kwantacciyar kala me kvau a kowanne sashe na dakin,frames manya manya dake dauke da ayoyin tsari ne a kowacce kusurwa ta dakin. A kallon da tayi masa sai jikinta ya bata bacci vakeyi,abinda zataso tayi shine komawa,to amma zuwa lokacin ta jiyo muryar haseena daga bakin gofar dakin, zuwa lokacin ma har ta fara knocking.


Yau daya tak taji wani abu ya taba zuciyarta,wanda bata dorashi a mizanib komai ba sai na haushin rashin hankali da rashin kamun kan meenal din


"'Yau zataga qarshen fitsar" ta gayawa kanta d kanta,don haka sai t wuce bakin gadon kai tsaye ta zauna kusa dashi. A yadda ta zauna kawai sai da tsigar jikinsa ta zuba,ya runtse idonsa ta cikin duvet din yana sauke numfashi a hankali.


Zubawa lallausan creamy white duvet din idanu tayi tana sauraren knocking din da meenl ke ci gaba da


"Koda yayyanka uwa daya uba daya, bai cancanci kazo dakinsu a irin wannan lokacin ba,ko ita da ta taso a mazaunin auta yar lelen yayyenta,har suka gama rayuwarsu cikin gudan ko da safe maama bata bari taje a wannan lokacin. A nutse ta daga kanta jin ta fara murda gofar, tana nufin shigowa zatayi kenan? ta rantse yau saita nuna mata iyakarta, don haka ba tare da tunanin komai ba ta dage duvet din ta tura kanta gaba daya har zuwa rabin bayanta a ciki, abinda ya bawa numfashinsu d qamshin su damar gauraya guri day kuma lokaci daya,kowa ya zuqi hucin numfashin dan uwansa har cikin huhunsa.


Idanunsa ya lumshe yana jin yadda numfashinta ke sauke yana garawa duvet din dumi, ko sau daya bai motsa ba,har zuwa sanda aka tura qofar aka budeta.


Mugun bugawa zuciyarta tayi, saboda ganin qafafun mutum biyu cikin duvet daya, take zuciyarta ta ayyana nata ga abinda sukeyi


"Na shiga uku!" Ta fada da garfi tana sakin qofar, ta kuma juya da hanzari ta fice.


Qaramin tsaki säahar ta saki bayan ta tabbatar da ficewarta,sannan ta yungura zata miqe tana qogarin yaye duvet din. Hannunsa ya sanya ya zagaye wuyanta da kyau,a hankali yana warware idanunsa ya saukesu fes cikin nata


"Ina zaki?" Ya furta a hankali cikin salon rada da wani irin taushi yana kallon zara zara din gashin idonta dana girarta,wani abu yana tsarga masa saboda ya samu kusanci da ita fiye da yadda ya taba samu tsahon sanin da yayi mata a rayuwarsa,ainihin kamanninta hadi da cute face dinta yau ta zama kusa da shi sosai fiye da ko yaushe jarababben qamshin nan nata gaba daya ya cika duvet din. Tsigar jikinta ce ta tashi saboda iskar daya baza mata saman fuskarta,kasa magana tayi sai ma gogarin sake migewa da takeyi saidai babu dama saboda ya tare ta da hannunsa


"Ina zakije nace? bake kika kawo kanki ba?" Ya sake fada yana lumshe idanunsa dake kan fuskarta,yana jin yadda komai na jikinsa ya fara wani irin aiki.


Gabanta ne ya fadi,sai yanzu ta fahimci wautar data tafka,ta sauke idanunta cikin toro da d'ari d'ari ga gangar jikinsa. A tube yake babu riga,sai tarin lallausat gargasar data cika girjinsa me santsi da laushi, gabanta ya sake faduwa ta maida idanunta ta kulle gam,qirar jikinsa toro yake bata, saboda jikinsa ya ginu da wasu irin muscles dake nuna yadda ya baiwa motsa jiki muhimmanci


"Me kikazo yimin?" Ya sake fada muryarsa na sake karyewa da yin laushi, labbanta dake walainiyar lipstick suna fusgar hankalinsa,yana jij kamar ya cinyesu


"Bab.....ba komai, just nazo ne gaya maka na gama shirin fita,saik kum......


"Sai kuma na baki sha'awa ko?, kikaji kinason ki rungume ni?" Ya garasa fada yana dage dukka girarsa sama. Ido ta fidda waje,abinda take gudu kenan zai manna mata sharri


"Allah ya kiyaye,meye abun sha'awar a nan?"


"Oh really?, dama kince babu maza a gidan nan ai ko?"


Shaf ta mance da maganar sai yanzu, amma ganin yana son raina mata wayo saita fara quna quni tana son qwatar kanta


"Banyi garya ba.....ka sakeni" ta fadi tana son janye hannunsa amma ko gezau, tako ina ya tsareta tas.va ma sake matso da ita sosai cikin jikinsa.


Sai data soma gajiya sannan ya zare hannun nasa,yana jin yadda jikinsa yake fidda gumi saboda saukar zazzabin nasa da kuma yanayin da yakejin jikin nasa a ciki. Da hanzari ta zare kanta daga duvet din tana nishi, tuni dankwalinta ya zame daga kanta, tana gyara yafen mayafinta ya yaye duvet din saman kansa yana dubanta gasa qasa


"Coffee please" ya fadi har yanzu muryarsa na cikin wani irin rauni


"'Ina kwana?" Ta fada cikin zafin rai da yadda gaba daya ya janyo ta yamutse


"Alhamdulillah" ya amsa mata a taqaice yana maida kansa cikin duvet din, don babu abinda ganinta yake qara masa sai shiga wani irin yanayi dake sanyashi birkicewa.


"Idan kika wuce baki kawomin ba sai kin gane baki da wayau" ya fada qasa qasa, kamar yasan shirinta kenan.


Baki ta tura gaba kamar ta fasa kuka,shi kam ba'a masa abin arzigi sam,inda tasan irin wannan cakumar zaiyi mata da ba shakka bata shigo dakinsa ba.

Tayi mamaki sosai sanda ta bude gofar dakin ta samu haseena zaune a gurin. Kallon kallo suka yiwa junansu,sai haseena din ta mige tsam ta kewaye säahar ga mamakinta sai ta kama handle din gofar ta tura ta shige.


Karon farko. wani abu mai nauyi ya tsaya mata saman zuciyarta, tabi qofar da tuni haseena din ta maidata ta rufe da kallo, sai taji ta kasa daga qafafunta


"Shin meye nawa?" Ta yiwa kanta tambayar, tanason garyata kanta da kanta game da damuwa da takaicin da taji a ranta. Kai ta girgiza tana son tabbatarwa kanta cewa ba komai bane ba kuma abinda ya shafeta bane don haka ta soma takawa tana wucewa kitchen din.


Duka duka mintuna biyar sun isheta ta kammala hadawa, wasa wasa sai gashi tana dosar minti goma tana dawurwura cikin kitchen din, kadan kadan wani irin bacin rai ya soma hayewa zuciyarta,wanda ya janye dukka wata nutsuwa da walwalarta,sai data zuba coffe powder din spoon uku sannan ta tuna yayi yawa, ta zare dot din ta zubar tana sake hada wani. A hankali ta saki spoon din sugar ta koma da baya ta jingina da kitchen cabinet din, tamkar yayewar hijabi ta hango abinda ya faru da ita shekarun baya. Adam take gani fes saman gadonta na aure tare da wata,lokacin da ta kamasu a zahiri,yaci gaba da duban qwayar idanunta ba tare da ya bar abinda yakeyi din ba. Sakin cokalin tayi a qasa,kamar wadda aka fusga ta nufi hanyar kitchen din tana in kanta kamar zai fashe lokaci guda zuciyarta na sake haska mata shigar haseena dakinsa cikin wata banzar rigar bacci da wani gantalallen mayafi dan mitsitsi.


Da wani irin qarfi ta buda qofar dakin, abinda ya jawo hankalinsu kenan su duka biyun,shi da yake zaune saman gadon da haseena dake tsaye a qasa amma dab da gadon hawaye suna wanke mata fuska. A hankali idonta ya sauka akan jikinsa da babu riga,sai ginannen qirjinsa dake bayyane, saboda duvet din ya dawo iya cinvarsa zuwa gafafunsa


"Bacemin a gun" ya fada a tsawace, sai haseena ta juya da sassarfa tana fita a dakin, sautin kukan da taketa cinyewa yana qwace mata. Jiri jiri ta soma ji,tana jin tsawar har cikin kwanyarta itama, fara takawa tayi zuwa gefansa don ta lalubi wayarta da kuma dankwalinta tabar masa dakin itama


"Where is my coffee?" Ya tambayeta da muryarsa deep inside fushi yana azalzalarsa


"Ban dafa ba" ta bashi amsa kai tsaye tana jin kamar zuciyarta zata tsage. Idonsa ya lumshe kana ya budesu,yana hangen tsiwar nan fal idanunta


"Har yanzu ban koya miki darasi ba shi yasa baki fasa yimin rashin kunya ba......


"Me yasa zaki barta ta shigomin daki a cikin yanayin da nake ciki?,idan da a tsaye ta ganni kinsan abinda zai faru?"


"Sai kayi mata abinda kace kana yiwa mata, tunda dama budurwa ce ina kyautata zaton indai bawai ka karba yadda kace kana karba ba,qila shine dalilin bibiyar.....waima meye nawa a ciki?,live your life, bani da case" ta bashi amsa da wani irin zafi har cikin ranta tana in qunar da batasan dalilinta ba, kalamansa kuma suna dawo mata.


Kamar ta yanki zuciyarsa da reza haka yaji,wani irin fushi ya taso masa, ita batasan dukka laifukan ta ba? ta yaya zata dinga bari mata suna samun access dashi ta kowacce hanya?,a kirashi a waya ta bashi su,su shigar masa office su shigar masa sashe harma ta fita ta barwa yarinyar sashensa? yarinyar da ko falonsa na farko bai taba bari ta shiga ba yau gata cikin bedroom dinsa a lokacin da yake cikin wani yanayi?, banda Allah yasa yana kwance tasan iya dadin zubar da mutuncinsa zaiyi?, koda bai shirya aurenta ba wanna zai zama sanadin da dole ya aureta. Maganganunta suka sanyashi jin he is nothing, bazai qyaleta ba yau sai ya nuna mata

BAMBAMCIN DAKE TSAKANINSU.



"Kema yau zanyi miki abinda nake musun, kinga daga nan zaki gane dalilin da yasa suke bibiyar tawa" Ya fada yana sanya hannunsa yayi mata kyakkyawar fuzgar da bata dire ko a ina ba sai saman jikinsa. Dukkan jikinta ne ya dauki rawa lokacin da suka samu sadarwa tsakanin ilkinsu a sannan ta gane me yake nufi da yace ya godewa Allah data sameshi a zaune. Cikin kwanyarta taji kamar zata zauce sanda ya riqe fuskarta da kyau a tsakiyar tafin hannunsa,ya kuma hade bakunansu guri daya.

[25/09, 8:56 am] +234 703 451 7171: "HUGUMA*


*_TABARMAR KASHI_

No comments