Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 3

 



Book 02 Page 03



Fitowarta kenan daga kitchen bayan ta gama shan coffee ta maida mug din,qofar falon da taji an bude da sauri ya sanyata waiwayawa da sauri,cikin zallar mamaki ta tsaya cak,tana duban fadeela dake takowa da gudu tamkar almara ta cukukiyeta tana kiran sunanta da garfi. Zubewa tayi saman gwiwarta tana riqe yarinyar da kyau tare da tattaba likinta a rude


"Fadee,waye ya kawoki? kinsan gidan nan? ya jikin naki? kin warke ne?"


"Babu wani ya jikinta,kamar dai irin da gasken nan kin damu da ita" muryar afifa da sautin muryar fadeela ya fiddota daga daki ya wanzu a falon


"Wallahi,gashi mu mun laluboki mun kawo kanji" nadeeva ta fadi tana takowa Sosai cikin falon,tare da kallon kusurwoyinsa,mamaki yana saukar mata tare da tarin tambayoyi fal cikin kanta. Migewa tayi dauke da fadeela tana murmushi


"Babu yadda zanyi ne sister nadeeya,kada kiji haushina" ta furta tana mata tayin gurin zama


"Fushi nake dake saboda haka bazan zauna ba,rakiya kawai na yowa abba" idanu sãahar ta fiddo waie cikin mamaki 


"Wai Dr?" Sai ta jiniina kai


"Suna waje shida abban gidan nan" sosai mamaki ya kama sãahar,sai ta sauke fadeela ta kama hannunta sukayi kitchen don samarwa dr jarma din wani abun shan.


Falon sai ya zamana babu sai su biyu ita da afifa,afifan ta qaraso tana murmushi


"Yaudai naga sister nadeeya,ki zauna mana" tana murmushin itama ta zauna,sannan tace


"Don Allah bestie kiyi haquri, kaina ya kulle,tambayoyi ne dani fal bakina,kuma nasan aunty N ba zata taba tsaiwa tayimin dogon sharhin da nakeso ba,and na tabbata kedin kina da amsar kowacce tambaya tawa" hannu afifa ta miga tana murmushi


"Kaina ya kawomin wasu tambayoyin da kike dasu,nasan kuma dole ki bugaci amsarsu,zo muie ciki" tsam ta mige tabi bayanta,suka wuce kai tsave zuwa dakinsu säahar din.


Ko afifa bata fada ba nadeeya tasan dakin na saahar ne,don kusan yadda ta tsara dakinta na gidansu haka wannan,har yafi wancan nesa ba kusa ba,komai a kammale cike da tsafta da qamshi da wani irin tattausan yanayi.


Tana dauke da babban tray din fadeela na biye da ita tana zuba mata labari a nutse daya bayan daya,riqe take da gefan doguwar rigarta tana biye da ita kamar jela,kai kace guduwa zatayi ta barta. Tun kafin su qarasa sai kunya ta kamata ganin yadda Dr da abbanta suka bisu da idanu kamar dai irin kana zancan mutum sai kuma kukaga tahowarsa daga nesa. Ta qarasa gabansu cikin girmamawar nan da kuma mutuntawa takai qasa tana gaida dr jarma,tare ta bude murafun abubuwan shan da tazo dasu tana zuba masa fadeela na matso mata da cups din. Cikin matugar kulawa ya amsa


"Amma daa saura kadan nima nayi fushi dake,kin biyewa wancan tsatstsauran kuna shirin yin sakarci?" Sai ya maida dubansa ga dr girema


"Ban taba sanin ita ke kulamin da jikata ba sai da muka iso gidan nan na fahimci hakan,bana fatar wannan alaqar ta yanke ta tsaya iya haka" dr mahmud ya fada yana jin wani karsashi yana shigarsa. Tun farkon saninsa da sãahar ta kwanta masa,yanayin kamun kanta,sanin kima da martabar dan adam, da tsantsar tarbiyyar daya gani daga gareta,duk kuwa da zurfin karatun bokon da take dashi...hakan ba qaramin burgeshi yayi ba, dabi' unta sun banbanta dana sa'o'i da takwarorinta masu matakin karatu da gata irin nata.


"Ga 'yarki nan na kawo miki,zata zauna tayi jinya a gurinki" kalaman da dr mahmud ya fada kenan lokacin da sukayo masa rakiya zasu koma shida nadeeya,maganar da tadan daurewa sãahar kai,anya da sanin wancan dan wulaqancin Dr jarma ya kawo mata fadeela?.


"In sha Allah zaka jini,na gode qwarai da ziyara,duk da ba takanas akazomi ba,sahun diyarka ka biyo" muryar dr mamman girema kenan yake fadiwa dr jarma


"Diyata ta cancanci a biyota,idan ban jika bama mamman ni zaka iini,ni zan fara nemanka ma"

"Karka damu" ya fada yana murmushi,sannan ya maida masa murfin motar,suka tayar da motocin suna ficewa a gidan.


Zuzzurfan tunani nadeeya ta shiga,daya bayan daya qwaqwalwarta ke mata bitar maganganun da sukayi da afifa,akwai abubuwa da suka bata mamaki tausayi da kuma daure kai,ashe already yaa toufeeq da anty N din sunsan juna?,but itafa laifin yayanta take gani to be frankly,a nan bataga laifin sãahar ba,cikar diya macen kenan ko ita ba zata dauki izzar d'a namiji ba. Amma abinda yafi gigitata rayuwar da säahar din ta fuskanta,wadda ta tilastata sauyawa daga ainihin dabi'unta. Abu mafi ban mamakin shine daya zamana wai ta taba aure,babu abinda zai nuna maka alamun hakan tattare da ita tafi miliyoyin 'yammata cikar haiba da komai na halitta. Sake juya kanta tayi wata shawara me girma na tsargawa cikin ranta,sai ta kira sunan

Dr da


"Abbana"


"'Ya akayi?" Ya tambayi nadeeyan yana qoqarin ajiye wayarsa bayan ya gama duba wani abu.

Idanunta suka dan kai kan wayar,sai taga kamar hoton MAJI dinta


"Abba dama kana da hoton maji ne?" Bakinta ya subuce ta jefa masa tambayar,don basu taba magana makamanciyar irin wannan baidanunta a kansa tana kallonsa. Harara ya watsa mata


"Yau nine na koma abokin wasanki?" Janye dubanta tayi zuciyarta da gwiwarta tana karyewa


"Kayi haquri" ta fada a sanyaye,sai yaji tausayinta ya kamashi


"Me ya faru kika kira sunana?" Gara zamanta tayi


"Ka taba sanin wani abu akan anty säahar?"

Shuru ya danyi sannan ya girgiza kai


"A'ah,akwai wani abunne?,mahaifinta Dr mamman munyi karatu dashi tsahon shekara biyar,sanann musan juna sosai a wancan lokacin,yanayi da lokaci ya jefa kowa inda yaso sai kuma aka rabu,sai bayan dogon lokaci bayan mun hadu da muhyiddeen na

fahimci dansa ne,shekaru masu yawa kuma

sai yau Allah ya gaddara ganawarmu" kai ta

jinjina,sannan ta warwarewa dr jarma din

kome data ji daga afifa.


Tsahon lokaci yana jinjina kai ba tare da

yace komai ba


"Amma abba ni ina da shawara" juyawa yayi ya

dubeta

"Wacce irin shawara ce?"


******Tun daren ranar da aka kawota take

magale da sãahar,duk inda ta motsa sai ta

bita gafarta qafartaji takeyi kamar zata gudu

ta barta. Ko da sukazo kwanciya sai data

rungumeta sosai,a haka bacci yayi awon gaba da ita. 

Afifa na gefe tana kallonsu,dariya tayi lokacin da take zare jikinta daga na nadeeyan a hankali


"Ah kin hadu fa da chewing gum" murmushi sãahar tayi,tana shafa kan fadeela gami da maida mata gashinta da ya ya mutse baya


"Ta saba aiko a gida sai tayi bacci kafin na koma dakina" kai afifa ta gyada tana kallon fuskar fadeelan cikin tausayawa,farat daya taji yarinyar ta shiga ranta.


Kwana uku cakal amma sai ka dauka fadeelan ta shekara a gidan,ta sake sosai tana ta walwalarta da harkokinta,zuwanta sau ya sake raya gidan,baya rabo da motsinsu da kai kawonsu ita da saahar,maama dai 'yar kallo ce,amma ita kanta yarinyar ta shiga zuciyarta,idan ka gansu zaka dauka itama daya ce daga cikin jikokinta,hadda da dr girema fadeelan ta shiga zuciyarsa,yana kallonta kamar su Aleena,idan ka shigo gidan zakayi tunanin itama jikar gidan ce kamar su khalifa.


Fadeelan bata taba jin rayuwa tayi mata dadi ba kamar wannan lokacin,saahar ce komai nata,yadda take kula da ita a gida haka a nan,harna sama da gidan,saboda a nan din a sake take fiye da can da take ganin bata da wani hurumi da can din. Batun ciwo kuwa tun randa aka kawota babushi ya tafi,gefa guda kuma kullum sai sunyi waya da nadeeya da kuma dr Jarma,wanda ya dauke nadeeyan ya maidata gidansa,yace itama ta zauna a can na wani lokaci.


*****Duk yadda yakai ga son ya dauke kai ya bar musu fadeelan yaga iya gudun ruwansu amma ya gaza. A yau yana tsaka da aiki ya kashe system din ya mige gafafunsa saman table din hadi da relaxing bayansa jikin couch din da yake kai yana lumshe idanunsa,jiya ya kira nadeeya yayi mata titsiye,ta kuma tabbatar masa fadeelan tana can. Yaso qwarai ya tattara ya zuba musu idanu,to amma zuciyarsa ta kasa dauka,gidan gaba daya shuru,babu kowa,dr din ya dauke nadeeya kamar yadda ya dauke fadeela.


Miqewa ya sakeyi yana kaiwa bakin corridor din dab da wasu flowers dake fidda sanyi me qamshi,ransa yana zafi sosai game da yarinyar. A baya yana lallaba rayuwarsa,yana yinta hankali kwance ba tare da wata baquwar fuska ta kutso musu ba.

Amma daga bayyanarta cikin watanni kacal tana neman ta zame musu qarfen gafa


"Idan kabar mata fadeela tayi winning a kanka" daga can tsakiyar zuciyarsa ake gaya masa,kamar an zaburar dashi ya dawo da baya ya dauki wayarsa yayi kiran number dr jarma.


Bugu biyu ya daga ya koma ya zauna sosai yana gaidashi cikin girmamawa. Kadaran kadaham ya amsa masa,cikin kamewar nan tasa yace


"Abba idan babu damuwa zan qarasa na dauki fadeela, kusan hutunsu nex week zai qare,ya kamata ta dawo ta shirya a nutsr kafin lokacin" gyara zamansa dr jarma yayi


"Eh to ai babu laifi.

..ummm... babu laifi,amma

idan kaje ka tano harda yarinyar khadijatu me kula da ita din kenan" hannunsa ya dunqule guri daya yana shigar da tafin hannunsa ciki


"Okay abba" ya fadi yana jin kamar dr jarma din yayi masa wata mummunar bushara


"Ka dauki saiiad kuma ku tafi tare" dr jarma ya gara fada,saboda yanason ya samu me masa monitoring abubuwa "In sha Allah" ya fada sanann ya gimtse wayar.


Iska me zafi ya furzar daga bakinsa zuciyarsa na sake soyewa da bacin rai da kuma damuwa,dr yana girmamawa al'amuranta da yawa,ya bata wani matsayi me girma,ya bata kuma yarda dari bisa dari


"Ya Allah, ya rabb,kada ka sanya yarinyar nan ta zame mana sharri cikii rayuwarmu,dukka abinda ya qulla ya Allah ga wargazashi" ya samu kansa da furtawa.


Lokaci ya duba yaga akwai sauran lokaci da zai isheshi yaje ya dawo,sai ya fada toilet ba tare da ya kira sajjad ba,nufinsa idan ya gama shiryawa sai ya kirashi,idan yace baya cikin gidan shikenan sai yayi tafiyarsa,ya tabbatar aikin Sanya Ido zaije yayi,shi kuwa sam sam bazai iya wani tsaiwa lallabata ko neman alfarma daga gareta ba.


Tsaf ya shirya cikin kamala da wani ajiyayyen kyau da kwarininsa cikin wani lallausan vadin boyel me garancin kauri,fari ne qal kamar yadda kake iya hango fara tas din singlet dinsa daga ciki,rufaffen takalmi ya saka charcoal color na kamfanin Stuart Weizmann me asalin kvau da tsada. Kansa sai dake dauke sassalkar sumar daya gada daga bangare biyu,dr girema asalin shuwa dan qasar borno,da kuma maji balarabiyar

Algeria ta kwanta luf saman kansa tana sheqi da fidda tattausan qamshi. Lafiyayyar fatarsa yake daurawa agogo,dai dai lokacin sajjad ya tura gofar ya shigo sanye da wata abaya ta maza,da alama yana cikin gidan yana hutawa,idanunsa akan TOUFEEQ da yayi wani mugun kyau


"Yanzu nake shirin kiranka ka fito zaka yimin

rakiya"


"Amma dai my man.....

.Wannan kwalliyar

zance zakaje?" Ya jefa masa tambayar cikin shakku. Kyawawan fararen idanunsa ya dago ya watsa masa,bayan ya dakata daga sanya agogon,wani abu yayi masa tsaye a wuya,kamar zaiyi magana sai ya maida bakinsa ya rufe yaci gaba da daura agogonsa,don yiwa sajjad magana ma bata bakine,kome zai fada bazai fasa jansa da magana ba,kuma gobe sai ya qara. Shi kuma a yadda yanzun yakejin zuciyarsa ko doguwar magana bayason yi. Gaban dressing table dinsa ya qarasa,ya dauki turarukansa ya fara feshe jikinsa daga wuyansa zuwa qirji,sannan ya sauya wani ya feshe sauran sassan jikinsa dashi,ya ciri key din mota guda daya daga inda yake ajiyesu yayi gaba yana fadin


"Kada ka wuce minti uku,ina parking lot" ya garasa fita ba tare daya waiwayoshi ba.

Qaramar dariya sajjad ya saki yana dan buga qafansa, already yasan da fitar,tuni Dr ya sanar masa,amma baisan da wurwuri haka zasuje ba


"Ko second daya ka bani sai fa na rakaka" yayi zancan shi daya,sai ya juya ya fita daga dakin.bava iin zai canza komai a jikinsa,don dakin,baya jin zai canza komal a jikinsa,don haka takalmi kawai ya sanya ya biyo bayanshi.

[11/09, 3:42 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*

No comments