Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 29

 '_TABARMAR KASHI*


Book 02Page 29



Sai da ya gama shiryawa tsaf cikin wasu lausasan pyjamas bagaqe a yau amadadin farare da yafi amfani dasu komai ya zauna luf a jikinsa,yaja stool ya zauna vana duba system dinsa.


Dukka hankalinsa va bayar akan bayanan da Dr anwar ya turo masa. Lokaci daya yaji wani gumi yana tsatstsafo masa,yasa hannunsa a tausashe ya share yana dungule hannunsa ya rufe bakinsa yana tsurawa system din ido


"'Yaya akayi maganin ya kasance daga hannun haliva qarama? me yasa maganin da bai kasance na lalurar fadeelan ba amma take shansa? me hakan ke nufi?" Ya viwa kansa tambayar yana jin hankalinsa yana tashi


"Take it easy" wata zuciyar ta gaya masa


"'Kayi bincike wisely" aka sake nanata masa. Miqewa yayi yana fita a bedroom din nasa a hankali, ya ciro wayarsa da ya bari a parlor ya fara kiran layin nadeeya. Bugu daya ta daga


"Yaa moha"


"Me sunan matar nan baga wata gajeriya me jiki dake aiki a sassan momy?" Dan shuru kadan nadeeya tayi sannan tace


"Ko adama?" Kai ya gyada


"Yes, kiyimin kiranta, amma banason kowa yasan na nemeta"


"To yaaya" ta fadi tana ajiye wayar, saita dubi su sãahar wanda suke zaune zasu fara cin abinci


"Ina zuwa AUNTY N" kai ta gyada mata,saita koma daki ta dauki mayafinta ta fice.


Tun daga yadda ta shiga parlor din zakasan a mugun razane take,ko ina na jikinta rawa yakeyi,gumi kuwa ya gama jiga mata jiki sharkaf. Yau ta shiga masifar da me fiddata sai Allah, dazun nan hajiyan ta gama yi mata kakkausar jan kunne kamar yadda ta saba a duk lokacin da aka karbo maganin, saidai kuma jan kunnen yau din yafi na kullum, kamar tasan abinda ya faru a hanyarta na kawo mata maganin. Da hannu ya yiwa nadeeya nuni akan ta tafi,ba musu ta juya,cikin zuciyarta tana taya adama alhini,ko wanne tsautsayi ne yasa ta shiga gonar toufeeq din? wanne irin laifi tayi masa haka?.


Tun kafin yace ta zauna gafafunta suka kasa daukarta, saita sulale tayi zaman dirshan a gurin. Kallo daya yayi mata ta fashe da kuka, tama mance da wani jan kunne na hajiya qaraman


"Wallahi bansan komai a kai ba indai batun magungunan ne" idanunsa kawai ya zuba mata yana mamakin rudewar da tayi. Sake debo rantsuwa tayi


"Na rantse da ikon Allah bansan komai ba"


“Tun yaushe ake kawo maganin?" Ya jefa mata tambayar

Shekara biyu…shekara biyu a cikin ta uku* ta bashi

amse kowanne sashe na jinta yana kakkarwa. Wani irin zafi idanunsa yaji sun fara yi masa, abinda zuciyarsa ke hasaso masa har bayaso sukai ga kwanyarsa bare ta sauya masa su ga dayan sashen na zuciyar tasa


*ki hada kayanki gaba daya,na sallameki daga aiki a gidan nan" abindia ya fada kenan. Faduwa tayi a gurin tana hurwa tana kuka sosai, saboda tasan muddin tabar aiki a gidan asirinta ya tonu,mutane masu yawan gaske ne suke neman damar yin aiki a gidan amma basu samu ba


Tsawa ya buga mata wanda ta sanya ba shiri ta tattara zaninta ta fice tana kuka. Shuru yayi yana maida jikinsa ga kujerar idanunsa a lumshe


"To maganin meye?" Tambayar da Dr anwar dinma bai bashi amsa ba, yace masa baida alaqa sam da ciwon fadeelan, suna kuma ci gaba da bincike.


"Wanne magani kenan ake bata yanxu?" Tambayar da tazo kansa kenan,ya kuma miqe a nutse ya sanya flip flops slippers dinsa yana baro sashen.


Tuni ta gama cin nata abincin ita da fadeelan, nadeeya ce tayi saura,don haka suka barta a falon suka wuce daki don ta shiryata ta bata maganinta tasha. Toilet ta kaita, kamar ko yaushe yanzu ta fara canza pattern na wankanta, zata hada mata kayan wankan gaba daya,tayi mata tsarki ta wanke mata bayanta da sauran inda hannunta bazai kai ba,sauran kuma saita tsaya tana kallonta tayi da kanta, tanayi tana gyara mata har su kammala. Sanda yayi sallama dakin basuji shi ba,suna bandakin tanata tsokanar fadeelan saboda yau ta dage bayan nata ma zata wanke da kanta.


A nutse ya garasa shigowa,ya maida murfin qofar ya rufe, idanunsa suka sauka akan dressing table din fadeelan inda kayan baccinta maganin nata da sauran tarkacen kayan nata suke.


Kai tsaye ya dauki robar maganin yana dubawa,sak irin maganin da yasan yana siyowa da kudinsa va damgashi ga hajiva garama har na tsahon watanni shid,bayan wata shidan kuwa baya taba batan lissafi zai sake kawo wani na wata shidan. Bude robar yayi ya zazzago maganin. Shine asin da asin babu banbamci, sai ya maida murfin maganin ya rufe ya maidashi inda vake vana fadin


"Hasbunallahu wani'imal wakil" wane sashe na zuciyarsa kuma na tambayar sa,waye yake bata kudin siyan maganin?. Lokaci daya komai ya rikice masa,lissafi yaso qwace masa,ga hajiyan da wani magani sabanin wanda ake baiwa fadeelan, ita kuma gata da irin maganin fadeelan ba tare da yasan waye yake siya ba.


Komawa yayi ya zauna saman sofa bed,har ta gama wankan suka fito tana tsane mata gashinta da hoodie towel din data rataya mata saman kanta.


"Abby...." Fadeela ta fadi, abinda ya jawo hankalin sãahar sal tadan ja da baya tana boye jikinta a qofar.


"Abbyyy..." Maganar yarinyar ta magale mata a maqoshi,a hankali yatsun hannunta dana gafafunta suka fara motsawa suna shacking. Dukkaninsu suka fahimci abinda ke shirin faruwa da ita,lokaci guda kuma kowanne ya taso da mugun hanzari suka nufo fadeelan,shi ta gaba sãahar ta baya,suka kuma isa gareta lokaci guda tare da rarumota cikin jikinsu saboda kada tayi mummunar faduwar da zata ji ciwo.


Shi yayi nasarar rungume fadeelan,yayin da säahar ta saki wani irin kuka mara sauti cikin narkewar zuciya tana kiran sunan fadeela


"Shshshsh" ya fada yana dora yatsansa saman lips dinsa duk da cewa shima cikin tashin hankalin yake


"Stop crying" ya sake fada da muryarsa da taynkaushi.va mige a nutse ya kaita saman sofa bed ya kwantar da ita sosai yana ambaton sunan Allah a ransa. Ta dauki tsahon kwanaki masu dama rabon da ta samu wannan attack din,kusan zai iya cewa harma ya manta,ya kuma tsammaci lalurar ta tafi kenan. Idanunsa suna kan agogo yana yana lissafa adadin mintunan kamar yadda ya saba,yayin da sautin kukan säahar ke shiga masa kunnuwa,sai ya dinga jin kamar ana soka masa allura cikin qwaqwalwarsa,wani irin ciwon kai ya fara saukar masa kadan kadan har cikin idanunsa.


Wannan karon bata gara ba akan mintunan data saba yi, ta bude idanunta a hankali tana kallonsu.


"Aunty N,faduwa nayi ko? ‚na dauka na warke na daina faduwa" furucin da ya sanya sãahar tsananta kukanta,hawaye masu yawa suka jige mata fuska ta kasa controlling dinsu, gaba daya hannuwanta suna cikin na fadeela ta rigeta tsam


"Zaki daina daughter, zaki daina in sha Allah very soon, in sha Allah,in sha Allah, i promise" duk da yadda kansa yake sarawa hakan bai hanashi dubanta ba,bai taba ganin hawayenta da kukanta ba kamar yau, kamar ma ta fishi shiga tashin hankali. A nutse ta mige ta dauko tissue ta dawo ta zauna a gefanta tana share mata majinar data zuba daga bakinta hade da yawu. Hannu fadeelan ta miga tana share mata fuska


"Ki daina kuka anty N,na dauka na warke ne, amma ai na saba" migewa tsaye yayi yana saka hannunsa a aljihun wandonsa kansa yana sake sarawa,yanajin kalaman fadeela har cikin zuciyarsa,yana jin kamar ya gaza.


_WASHEGARL



Cikin jikinta fadeelan ta kwana a daren jiya,da safe ma tace yau ba school, tunda juma'a ce ta zauna a gida ta haqura. Da safer tayi mata duk abinda ya kamata, duk da cewa Zuciyarta babu dadi,haka gangar jikinta babu kuzari, amma haka ta daure ta koma sashensu.

Me share share ta samu yana aikinsa,kamar yadda toufeeq din ya maidashi akin sassafe, shida zuwa bakwai ya gama komai,idan kuma ya makara saidai ya bari kuma sai bayan sun fita office. Gefe yaja yana sadda kansa gasa sanda yaji sallamarta


"Good morning maa" ya fada ba tare daya kalleta ba


"Morning"' ta amsa masa tana wucewa. Samun kanta tayi da kallon gofar dakin nasa, ba alamun da mutum a ciki,duk da cewa daman kusan kullum kamar haka qofar yake, amma yau sai taji abun yadan ja hankalinta, duk da haka ta watsar ta isa nata dakin tana shiryawa a hanzarce don kada tayi late.


Ta zarta lokacin shirin nata, amma ga mamakinta har ta kammala shiryawa ta fito bataji wanann sassanyan qamshin nasa da duk safiya yake gaya mata kammala shirin boss din ba. Ta iso parlor babu kowa, dama jacob ne zaka samu ya raya falon da qamshin abincinsa, shima tunda yaje gida wanna yayi qaura. Yankewa tayi ta fita farfajiyar gidan saidai kafin ma ta qarasa duka taga babu motocin da suke fita din ko guda daya


"Good morning madam,ya jikin oga din?" Muryar jibril dake magana cikin girmamawa ya furta. Da dan sauri ta waiwayo


"Jikin oga kuma?" Ta tambayi kanta da kanta,ta tambayi jibril din kamar zubewar kimarta ne, saita amshe kawai


"Jiki da sauqi alhmdlh"


"Allah ya qara afuwa"


"Ameen" ta amsashi. Qafafunta babu qarfi sam ta koma ciki, taja burki a falon ta tsaya tana tunanin meye abunyi?, at last taga babu wani abu da ya rage illa ta shiga dakin da kanta.

[24/09, 8:19 am] Mimah Yusuf: "HUGUMA*



'_TABARMAR KASHI*


No comments