Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 27

 


Book 02Page 27



"Amma toufeeq kamar ni?, meye amfanina a cikin gidan idan ban kula da fadeela ba" ido ya lumshe sannan ya bude,ya gaji gaba daya bayason wani daru


"Karki wani damu, tattaromin magungunan ki bani, ni zan ci gaba da kula da hakan" a bazata maganar tazo mata,har hakan yaso ya rudata amma ta daure


"Haka ma zaka ce dani toufeeq? yayi kyau shikenan, kaje kawai" ya dauka ya kawo qarshen maganar, amma sal ta sake cewa


"ya kuke ciki da meenal?,dazu ta dawo tana kuka,ta bata lokaci tana bada direction na abincin da za'a dafa maka,sai kuma naga da takai maka babu abinda ka taba a ciki,me yake faruwa?" Idanunsa yadan rufe kadan,a yadda ya fuskanci yanayinta ko meye zai fada mata a yanzun zata bata masa lokacine ta qara masa hayaqi akai, saidai duk da haka yana bugatar ya datse dabi'ar daukar abinci takai masa company,alhalin suna da kitchen, sannan kowanne kalar abinci yakeso yana daga office jibril zai iya masa order dinsa


"Mun fita da madam dauko fadeela daga school" idanu tadan bude da kyau tana kallonsa. Tunda suke dashi bata taba jin ranar da ya zarce daga office dauko fadeela makaranta ba sai yau,yau din kenan har hakan ta fara?, har yarinyar taci nasarar juyar masa da hanakali da sauya masa ra'ayi da tsari?,duk kuwa da tarin taurin kansa da kafiyarsa akan tsarinsa?, wanda ko ita ba kasafai takecin nasarar canzashi ba?. Bata gama wannan mamakin ba ta ganshi ya miqe sannan yace


"So please hajiya ki fahimtar da ita basai tayi wahalar kawomin ba,i will be alright, bazan rasa duk abinda nake bugata ba" mamaki ya hanata cewa komai,shi sam baima wani zurfafa dubanta ba bare ya gane ya dora mata


"Zan wuce ciki.da wuri nakeso na kwanta"


"Jacob baya nan,ko a kai maka dinner?" Ta sake garfin halin fada tana ritsashi da ido tare da son tabbatar da zarginta akan säahar . Hannu yasa ya shafi tattausar sumarsa


"No, ba damuwa,i will get something to eat" sai yayi mata sallama yana ficewa. Labiba da haseena, tabbas yana gab da yi musu mummunan warning din da ko sunansa sukaji zasu san nayi,yana musu kara da alkunya ne kawai saboda iyayensa, hajiya qarama da dr jarma,don kwata kwata baya saka mansura a lissafinsa.


Yana shirin fita a sashen adama na isowa, hankalinta yayi gaba sosai don haka bata lura da shi ba har sai da yayi dab da ita, cikin zafin nama ta kauce masa abinda ya sanya ta bugi bango ledar dake hannunta ta. yage,magungunan ciki suka zubo qasa. Cikin tsananin rudewa tare da tuna kakkausan gargadin da hajiyan tayi mata wajen kula da maganin har zuwa sanda zata kawo mata shi,sai ta sulale a gurin tana tattarosu tana zabga salati.


Kansa ya dauke yana ci gaba da tafiya. Har ya gota yá dawo da baya sakamakon wani tunani da ya darsu a ransa. Akwai masu aiki a gidaje kamar haka da suke ta'ammali da kayan maye qwayoyi ba tare da iyayen gidansu sun sani ba,wasu ma idan aka samu tsautsayi har su koyawa yaran gidan


"Ke.. zo nan" kiran da ya sanya hantar cikin adama juyawa,ta dawo da hanzari ta zube a gabansa


"Wadan nan magungunan fa?"


"Eh... na'am" ta fada a rude tana tuna gargadi na biyu data yi mata,kada ta nuna cewa maganin yana da alaqa da ita ko fadeela


"Uhmmnn" ya fadi yana tsuke fuskar nan tasa me sanya shakka da tsoro a zukatansu


"Ko kin fara shaye shayen muggan qwayoyi?" Ya fada kansa tsaye yana tura hannunsa cikin jallabiyyarsa ganin bata ds niyyar amsawa. Fassarar da yayi matan ta razanata matuqa,har batasan sanda ta daga kai da sauri tana rantse rantse ba


"Wallahi A'ah yallabai,magungunan fadeela ne hajiya tace na karbo daga bakin gate"


"Bakin gate kuma?" Ya tambaya cike da mamaki, saboda yasan duka magungunan da fadeela ke sha ba na nan bane, hasalima order dinsu ake mata na kusan million daya,yana damqasu a hannun hajiya qarama har sai sun qare sannan ya sake yi mata order din da kansa (nasan zakuyi mamaki,maganin million daya?,harma fiye da hakan sukan sha,sannan kamar yadda nace wasu da yawa masu gata a cikin masu lalurar EPILEPSY order magungunan nasu akeyi musu,a qalla a shekara sukan sha maganin million daya din, fatanmu Allah ya rabamu da dukkan wasu cututtukan zamani,ya qaremu da lafiya,su kuma ya basu lafiya,wadanda ya zame musu na

har abada ne kuma rabbi yasa ya zamar musu kaffara


"Eh.. .eh" kai ya jinjina,ko sun qare ne tayi order ba tare data sanar masa ba, sai ya samu kansa da lissafa adadin kwanakin da suka rage su qare din. 


Har ya daga qafarsa yaci karo da roba,ya

tsugunna yana dubawa sai yaga daya daga cikin robar

maganin da ya gani ne yanzu,ya waiwaya zai kirayeta

amma tuni har ta bace a gurin,ya juyata a

hannunsa,kwata kwata tasha banban da robar

magungunan fadeela,sai kawai ya jefata a aljihun rigarsa ya wuce.


******Dukka qafafunsa ya zuro waje yana juya zaman agogon hannunsa. Yau din shigar suit ce yayi wadda tayi matugar dacewa dashi,ta fidda kyana kai kace daya daga cikin jaruman Indian films ne. Yau din har da wani extra eye glasses daya mannawa fuskarsa me duhun kala,wannan ya sake qawata fuskar tasa qwarai. Karo na uku va kalli agogon nasa,ya fahimci tunda suka fara ajjiye fadeela a makaranta suke shanyashi,a kullum sai yayi zaman jiransu,duk sanda zata iso kuma tana yine kamar batasan ta sanyashi zaman jiran ba. Kaf duniya idan ka dauke Dr jarma babu wani mutum da yake iya zaman jira,sai ita data karya masa record.



Dago kan da zaiyi suna fitowa daga sassan, kamar kullum tana rataye da school bag din fadeela tana kuma riqe da lunch bag dinta, yarinyar itama na dauke da hand bag din sãahar. Sati kusan na biyu kenan da yake ganin fitowarsu a hakan, amma har yau ya gaza saba ganinsu a irin wannan yanayin,duk lokacin da suka fito din sal sun fisgi hankalinsa qwarai, saidai yau din hankalinsa ya dauku fiye da ko yaushe. Tuni ya sanyawa guards dinsa dokar zama cikin motocinsu a duk lokaci irin wannan har su fito su wuce. Shi kansa bazaice ga dalilin da yasa yayi hakan ba,kawai dai yana ji a jikinsa hakan shine abinda yafi dacewa.


•Yau din kamar murmushi da fara'ar fuskarta ya banbamta da na ko yaushe. Cikin shigarta da ko yaushe take fita zuwa office din da ita ta laffaya. Saidai kuma a yau din laffayar ta musamma ce. Wata irin lallausar farar laffaya ce me yarfin ruwan gold,wadda ta dace da siririn takalmin qafarta me tsinin dunduniya maras tsaho,wanda zara zaran dogayen yatsunta suka kwanta luf a ciki,komai nata a ranar kusan gold colour ne, sai hakan yayi masifar qara mata kyau da wani irin haske,lafiyayyar fatarta ta fita shar.


"Wow" yaji an fada cikin wani mugun zumudi, furucin da yaja hankalinsa aka fusgeshi har cikin kwanyarsa. A nutse ya waiwaya,ba kowa bane tsaye a wajen sai Jamal.


Saidai kuma wayace a hannunsa da alama wani abun daban yake kalla. Haka kawai yaji wani abu yazo ya tsaye masa a wuya. Ba yaune rana ta farko da yakejin kamar shigar bata dace da ita ba,amma sai yake gayawa kansa rayuwarta ce,bai kamata yayi mata shishshigi a ciki ba.


A yau din duk yadda yaso ya share kaman yadda ya saba sai yaji ya gaza dannewa. Wow din da Jamal ya furta sai yakejin kamar a kanta ne


"Dole ka kare martabar aure, ko ba komai sunnar ma'aiki ce daya kamata ace an tsare kimarta" wani sashe na zuciyarsa yaji yana gaya masa.


Cikin nutsatsen takunta ta iso bakin motar a hankali, kallo daya tayi masa ta janye idanunta tana rage kaifin fara' arta,wanda wanna din wata dabi'arta ce da tuni ya gama ganeta. Hannu tasa a nutse ta budewa fadeela seat din ta daya side din, qasan ranta tana gulmarsa. Zata iya cewa tsahon lokacin da ta dauka dashi zata iya rantsuwar bata taba gain dariyarsa kamar yadda sauran mutane sukeyi ba,wannan baqin eye glasses din da yasa ko yau din kuma tsautsayin kora da sauke kwandon masifar akan wa zai fada?.


Tambayar da ta yiwa kanta kenan, wadda tayi dai dai da saukar sautin muryarsa


"Ji mana" ya fadi yana zube mata zagayayyun idanunsa dake da haske qwarai. A nutse ta juya suka hada ido,a hankali idanun nasa suka sauka akan lips dinta daketa ayallin lip gloss. Tun wancan ranar bata sake maimaita saka jambaki ba,tunda yayi mata wannan abun. Bata fata ya maimaita kusanto jikinta,shi yasa ta daina sakashi kwata kwata a bakinta.


Dubansa ya sauka daga cikin idanunta zuwa lausasan lips din nata,haka kawai yaji ya hadiyi wani yawu. Sai kuma ya fara qoqarin saita kansa yana sake hade ransa


"Wannan shigar bata yi ba,go and change" sosai mamaki ya kamata,sai ta sauke dubanta a nutse ta a kallon kanta tun daga yatsun qafarta zuwa ainihin gangar jikinta,bataga ta inda ake ganin wani abu nata ba. Yana daya daga cikin abinda ya sa take yawan zabar shigar


laffaya saboda yadda take suturta kaso saba'in na surarta


"But......me shiga na yayi,is like fa kana shiga hurumin da ba naka ba" ta fada tana hade ranta da kyau. Wani kallo da ya dago ya aje mata sai da taji tabbas tayi subutar bakin bashi amsar da tayi a yanzun. Bai sake bata damar yin tunani na biyu ba taji kawai ya damqi hannunta,bai tsaya jiran komai ba ya nufi sassansu yana riqe da tsintsiyar hannun nata,yana jin zuciyarsa na wani irin zafi,ba tun yau ba shigar ke tsole masa ido,daga yau kuma ta bar yinta kwata kwata.


"Ka sakarmim hannu mana,kama wuce ga'ida fa" ta sake fada da nata zafin sanda suka isa qofar dakinta. Fusgota yayi ya jefata jikin qofar yana binta da kallo. Take tsoro ya kamata cikin ranta tana mamakin abinda ya Sanya farar qwayar idanunsa sauya kala lokaci guda


"Idan na sake jin bakinki sai na shayar dake mamaki" ya fada da zafinsa shima,sai yasa hannu ya murda handle din dakin ya buda qofar ya tura saahar din ciki. Tamkar kurma haka ta zama,tayi tsaye tana kallonsa sanda ya bude closet dinta yanata debo kaya yana zubawa saman gadonta. Batace masa komai ba har ya kammala,ba tare da ya rufe ba ya tako a nutse ya tsaya gaban kayan


"Ba kwalliyar ki akace kije ki nuna musu ba da zaki dinga sanya wannan abar,tun randa kika fara zuwa aiki har yau,ki cireta ki zabi wasu daga cikin kayan nan ki saka ki fito" Sosai ranta ya baci, ita ko kadan bata taba sanya laffayar da sunan kwalliya ba,hasalima tana sakata ne saboda tsaro, batasan yawan kallo, tana da tarin kaya lace atamfa shaddodi da sauransu kayayyakin qyale ayale na mata, amma duk ciki tafi qaunar sakata muddin zata shiga taron daya hada hadakar maza da mata. Abinda bata sani ba,a duk sanda ta saka laffayar tana yi mata mugun kyau ne,tare da sake nuna zallar dangantakarta da shuwa


"Bazan iya canza kowanne kaya ba" ta fada masa kai tsaye tana dauke kanta daga sashensa zuwa wani sashe na daban hadi da goye hannunta a qirjinta.


Ko motsinsa bataji ba bare ta sanya ran yana dakin,har zuciyarta ta fara gaya mata ya fita ne,abun mamaki sai taji hucinsa dab da ita,kafin tayi kowanne motsi taji ya kama daurin lafayar dake qugunta data yiwa daurin zarge ya wareshi,a take ta fara warwarewa daga jikinta.


A mugun razane ta kama laffayar ta cukuikuyeta,don tabbas muddin ta warware din ta gama tozarta a idanunsa,zai ga shape na komai nata ne,don wasu rubber material ne a jikinta me golding masu tsayawa dai dai jikin mutum. Hannu daya ya sanya ya zare laffayar a jikinta qwayar idanunsa cikin nata yana karantar yadda hankalinta yayi wani mugun tashi,yayin da ita kuma ta dage tana gogarin tattarota, wani tashin hankali yana bayyana qarara cikin idanunta. Ko kusa ko alama garfinsu baizo daya ba,tayi imanin idan akaci gaba da haka dukka laffayar zata zame ne ta barta gayanta.


Dole badon ta shirya ba cikin rawar murya tace


"Am sorry i will change it please" yadda tayi maganar da mugun sanyi muryarta na rawa ya karya lagonsa,sai kawai ya sake mata laffayar yana cewa


"Kin dauka ni abokin wasanki ne?, Bayan na biya sadakinki duniya ta shaida ke din kin zama halal din da zan iya yin komai dake ba tare da na zama abun zargi ba shine har kike da zarrar tsaiwa kina fadamin wannan maganar na ina wuce hurumina?" Sake rigeta kawai tayi da kyau cikin tunanin mafita


"Bakisan zan iya mai dake naked ba kuma nace kiyita zama a hakan a gabana?, kuma banyi laifi ba har wajen Allah?" Daga furtawar kawai da yayi sai taji kamar ma ya maidata tsirarar, abinda ya sake mugun razanata kenan ta kasa cewa komai sai karyar da wuya da tayi. Ya gano ta karaya sosai,sai yaja baya yana qara nisan tazarar dake tsakaninsu


"na baki minti daya" ya fada yana sake ja da baya hadi da maida jikinsa ya jingin da mudubi. Cikin rudewa take dubansa,yana nufin a gabansa zata tube ta canza kayan? tashin hankali

[24/09, 8:19 am] Mimah Yusuf: "HUGUMA*


No comments