Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 2

 


* TABARMAR KASHI_*6


Book 02 Page 02





"Ke da mahaifinta dama ba burinku kenan ba? vanzu haka tana asibiti, kuma ko meye ya faru da ita kune ke da alhakin hakan" daga haka ta katse wayar,tabar sãahar da waya a hannu.

"Gaskiya ta fada,meye laifin yarinya da zaku shiga rayuwarta ku gigita mata ita?,rana daya saboda baki shiri da mahaifinta ya birkitaki ke kuma ki tattaro ki bar yarinya kwatsam?"


"Bai isa ya birkitani ba,baida wannan qarfin ikon,abinda na sani kawai bazan taba iya rayuwa dashi a muhalli daya ba muna shagar iska daya”


"'I dan kukayi kisan kai ai ku kuka sani" afifa ta fada cikin jin haushi tana migewa a wajen.

Maganar Allah itama zuwa yanzun haushinsu takeji,kamar masu ganin hanjin juna? babu dama su hadi guri guda sai kowa ya hau tashi kamar kububuwa?.


Tun daga lokacin da nadeeya ta kirata har zuwa wayewar gari ta gaza moruwa gaba daya, lokaci lokaci sai ta samu kanta da duba wayarta,tanason kiran nadeeyan amma kuma batason tayi abinda zai sanya zuciyarta karyewa. Ko a daren jiya baccinta rabi da rabi ne,iya baccin data samu yi din cike yake da mafarkan fadeela na koke koke,abinda ya hadu kenan yayi mata rubdugu ya kassara duk wani walwala da karsashinta. Don ko da safe kwance tayi a daki,ta kasa fita ko ina. Ba abinda takeson gani a wannan lokacin irin fuskar fadeela,ta rungume yarinyar a jikinta kamar yadda suka saba,to amma kuma ta yaya?,batason cin fuska da cin zarafi don haka ya zama dole komai wuya komai daci ta nisanci dukan abinda yake da jibi da MT JARMA.


Zuwa la'asar juriyarta da dukka

haqurinta ya qare,wunin daki tayi ita kadai afifa yau tana asibiti gaba daya,ta kalli agogo,biyar saura,lokaci irin wannan lokaci ne nayin karatunsu ita da fadeela,ko ya halin karatunta ya shiga ciki?,duk yadda taso ta jure sai da qwalla ta cika idanunta,saboda ta tuna algawarin da tayi mata na har ta gama exam tare zasuyi karatun,to saura guda biyu ta kammala ta baro gidan,batasan waye ya tallafeta sukayi karatun biyun da sukayi saura ba. Batasan ya akayi ba sai kawai ta samu kanta da laluben number nadeeya cikin jerin calls dinta na yau,ta danna number tayi dialing.


Hannunsa zube a aljihun silky trouser dinsa daya dace da short sleeve shirt din dake jikinsa,yana takawa a nutse tamkar saboda shi daya akayi hanyar da zata sadaka da dakunan AMENITY na asibitin. Manyan dakuna dake dauke da dukkan wasu kayan buqata tamkar kana gidanka. Ko baka sanshi ba kalli fuskarsa kasan wani kwantaccen fushi ne zalla a samanta,saidai tarin nutsuwar da yake da ita data cakude da miskilancinsa ya sanya ba lallai ka lura da hakan ba kai tsaye.

Babu abinda ke amsa kuwwa a kunnensa sai bayanan Dr anwar,wanda yake jaddada masa dole ya kiyaye yasan meye asalin abinda ya sanya fadeela a wanann mummunar damuwar,dole ne yayi qoqarin sama mata abinda zai sanya hankalinta kwanciya ya dawo da ita walwalarta,ko don lalurar da take da ita, wadda ta ragu sosai fiye da baya. Shi kansa dr anwar mantawa yakeyi wani lokaci da lalurar tata,saboda komawa baya da takeyi tana raguwa da kadan da kadan a yan watannin da sãahar din ta kasance da ita. Idan yayi zuzzurfan tunani hakan yana nufin babu makawa sai ta dawo cikin rayuwarsu?,kenan tayi galaba dukka shirinta yayi tasiri kenan?,sai ya furzar da iska me zafi daga bakinsa,ransa yana gonewa,yana jin wani irin zafin yarinyar a ransa. Daga ranar da ya shata layi tsakaninsa da kowacce diya mace,babu macen data sake shigowa rayuwarsa tayi masa wannan karan tsayen sai ita. Dai dai sanda ya isa gofar dakin,ya sanya hannu ya murda handle din ya bude,saidai kafin yakai ga shiga yaji sautin siririyar muryar fadeela da ko yaushe bata rabuwa da kuka tana kiran sunan


"AUNTY N,don Allah ki dawo, Allah bazan zauna ba nima idan baki dawo ba,kinmin alqawari amma shine baki cika ba? kullum kuka nakeyi,amma abby yace bazanzo ba,a nan zan zauna,kema kiyi zamanki". Dukkansu ita da nadeeya basuga shigowarsa ba,bare baaba ramatu dake sallah saman abun sallah.


Kai tsaye ya sanya hannu ya zare wayar dake magale a kunnen fadeela,ya juya a nutse yana fita a dakin,ransa na zafi.


"Hello..

...hello,nadeee" sautin lallausar

muryarta ya sauka a kunnensa lokacin da yake magala wayar a kunnensa,ya lumshe ido yana jin tsanar


"Nawa kike da bugatar a biyaki ki dawo cikin ravuwar da kika riga kika shigeta cikin shirin faruwar hakan?" Cak komai ya tsaye mata,cikin mamaki ta kalli number,ta sake tabbatarwa number nadeeya ce,don dama ita din bata taba ajiyar number dinsa a wayarta ba,saita sauke wayar daga kunnenta kawai ta katse kiran,saboda bata jin zata iya tsaiwa ta saurareshi.


Komawa tayi ta lafe a gado,zuciyarta na wani bugawa a jejjere,kwata kwata ta manta da sautin murvarsa cikin kwanyarta,don bata sake iinta ba sai a yau din. Idanunta ta mayar ta kulle,sautika biyu na tsalle tsakanin qirjinta da kunnuwanta,sautin innocent fadeela,da kuma sautin deep and husky voice dinsa.


Labbansa na qasa ya cije lokacin da ya fahimci ta kashe masa waya ne,abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa,sai ya sake tunzura ya kuma dannawa number din nata kira.


Karar wayarta a karo na biyu ya

sanyata bude idanunta,ta kalli wayar,kamar ba zata daga ba sai kuma taga nadeeya dince,ta dannan Koren shudi ta sanya kiran a handsfree


"Muddin kika sake kashemin waya sai na baki mamaki,don har cikin gidanku zan iskeki,nace nawa kikeso a biyaki ki dawo bakin aikinki?"

Yayi maganar cike da wata izza da gasaita.

Tunawa tayi da matsayinta a rayuwa,da kima da kuma darajarta ta diya mace,wannan ya bata qwarin gwiwa,ta mige ta zauna sosai saman gadonta


"Bazan dawo ba!" Ta gaya masa kanta tsaye,ta kuma dakata tana jiran abinda zaya fadi. Har tsakiyar kansa yaji saukar muryar tata da kalaman da suke nuna rashin toro ko daga gafa


"Dole ki dawo,ki qarasa abinda kika fara shiryawa,dole ki dawo inason naga iya gudun ruwanki na kuma qurewa wasanki gudu donki tabbatar da banbamcin dake tsakaninmu" ya fadu a zafafe. Katse wayar kawai tayi saboda yadda deep voice dinsa ke shiga kanta sosai,tana ratsa jijiyoyin jikinta tana jin kamar yana a cikin dakinne. Ba iya katse kiran ta tsaya ba,gaba daya wayarma ta kashe,ta koma ta kwanta rub da ciki idanunta a lumshe,muryarsa naci gaba da yawo a kanta.


Abu guda daya data sake amincewa dashi,yana da izza izgili da girman kai,ta fahimci akwai damuwa sosai cikin muryarsa, damuwar kuma bata rasa nasaba da ciwon fadeela daya sanyasu dukka a damuwaryanaso ne ta dawo taci gaba da kula da fadeelan duk da ransa baiso hakan ba.amma shi baisan hanyar da zai lallaba mutumin da yake neman abu a gurinsa ba,a haka zata koma? kai koda da sigar lallashi yazo mata bata jin zata koma,bare a yadda yazo mata cikin izza da gadara,sai ta gyara kwanciyarta ranta na turereniyar abubuwa guda biyu,tausayin fadeela da kuma takaicin kalamansa.


Hannayensa ya yarfar,nadamar karbar kiran dayi mata tayin dawowa na lullubeshi,tunda yake babu wani mahaluki daya taba masa abinda tayi masan, ji yayi kamar yayi jifa da wayar,ya juya wayar a hankali yana qare mata kallo


"Ta yimin dai dai, kuma haka shike nuna baka shirya samarwa 'yarka lafiya ba" sautin murvar Dr jarma ya ratsa kunnuwansa. Da sauri ya waiwaya bayansa yana duban mahaifin nasa,sam baiyi zato ko tsammanin ganinsa a gurin ba,tunda ma tun wancan satin sukayi sallama dashi ya tafi china,kuma a galla zai kwashe wata guda bai dawo ba. Rusunawa yayi ya rage tsahonsa


"Barka da warhaka"



"Aikai za'a yiwa barka muhammadu" daga furta hakan da yayi sai ya juya kawai ba tare da yace dashi komai ba. Da hanzari ya rufa masa baya sukaci gaba da takawa yana qoqarin cimmasa,abinka da sabon jini nan da nan ya tarar dashi,suka jera kafada dashi ya sake russunawa yana gaidashi sanda suke shiga verandar da zata sadasu da dakunan


"Barka kadai,ya goqari?" Ya amsa masa cikin salon gatse, kafin ya samu amsar mayar masa nadeeya ta fito daga dakinsu riqe da hannun fadeela wadda ke takawa da gafafunta,fuskarta a washe matuqa,tamkar ba ita ya fita ya bari da hawaye shabe shabe ba


"Yauwa,ku qarasa mota ku jirani ina zuwa" Dr jarma ya fadi yana takawa zuwa office din likitan. Hankalinsa rabuwa yayi biyu,sallamarsu akayi ko kuma Dr dinne ya sallami fadeelan da kansa?,ganin zai batawa kansa lokaci sai kawai yabi bayan dr jarma da tuni ya isa office din Dr anwar.


"In sha Allah nan da gobe ma zakuga ta mige sarai, damuwa ai matsala ce a zuciya,ita kuma zuciya idan ta samu cikakkiyar lafiya ta kubuta daga damuwa,to dukka gangar jiki ma zata samu cikakkiyar lafiya da kuzari" kai dr jarma da yaga shigowar toufeeq ya gyada


"Gaskiya ne dr,zama da damuwa dama a zuciya saidai idan kai kaso,sai kayita zamanka a haka tunda haka ka zaba,kowa kuma yayi rayuwarsa cikin farinciki" sarai dr anwar ya fahimci magana ce me harshen damo, tunda bawai yau ko jiya yasan familyn JARMA ba,kusan abubuwa da dama tare dashi akayi.

Hannu dr iarma ya bawa dr anwar yana masa godiya,sannan ya tako yana fita. Kallo daya touteeq yayi masa sai yayi masa nuni da zasuyi waya,yabi bayan abban nasa.


Motocinsa hudu ne a parking lot na asibitin, motar da yafi zama a ciki yaga ya nufa ya bude,sai yabi bayansa. Har ya sanya kai ya tsaya ya waiwayo yana kallonsa 


"Af,bari na maka bayani don sauke haqqinka na uba ko? zan kaita inda aka saba kula da ita,idan ta samu lafiya kaje ka daukota,idan kuma kaie din,ba ita kadai nakeso ka dauko ba,har wadda ta kula da ita din zataci gaba da kulawa da ita nakeson su dawo cikin gidan suci gaba da rayuwarsu yadda suka saba" daga haka ya shige motar sajjad ya rufe,ya sanya drivers suka tashi motocin suka bar harabar asibitin.


Sam kanshi ma a sanann a daure yake,bai kawo masa tunanin inda dr jarma din zai kaita ba


"Sir....zamu tafi ne?" Muryar jibril ta shiga kunnensa,sai ya amsa alamu da hannu,ya matso da motar ya bude masa ya shige ya rufe suma nasa motocin sukabi kwalta.

[11/09, 3:42 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*


No comments