Breaking News

Tabarmar Kashi Book 2 Page 10

 


* _TABARMAR KASHI*


Book 02 Page 10



*_KALLON KALLO_*????


Hantsi ne wanda yazo mata a birkice,irin birkicewar da bata taba hasasota ba. Tun safiyar data tashi take jinta sukuku,amma ta danganta hakan da fitar da taketa son yi jama'a na tsaidata,saidai ta yanke a ranta gobe komai matsi taje din,don da zafi zafi ake dukan qarfe. A safiyar a daki tasa aka ajjiye mata breakfast dinta ta tsakura ta ajjiye,saboda kullum damuwa ce ke narkewa a zuciyarta,yadda taga dan uwanta Mahmud jarma ya dauki lamarin auren nan sai yake sake sakata cikin tashin hankali. Kamata yayi ace dukka wadan nan shire shiryen da zumudin akan auren toufeeq ne da meenal

'yaruwarsa,ba wai akan wata nanny ba. Da wannan baqinciki ta kwana ta tashi,da gyar ta samu wajen sha daya da rabi ta shiga wanka,ta fito ta shirya kamar kullum cikin shigar alfahari da fariya na wani dandaqegen lace,ta cika jikinta da turare,ta fito don ganin meye kuma yake gudana cikin gidan gaba daya,wanda kusan wannan din al'adarta ce,komai na gidan idanunta suna kai tana biye dashi saidai idan bata qasar tayi tafiya.


Tana takawa ne cikin jin izza tare da yadda take samun komai yadda takeso,idan ka cire yadda al'amuran a yanzu suketa son yi mata gardama,wanda ta tabbatar sako sako da dauke mata hankali da neman kudi sukayi shine musabbabiyyar faruwar hakan.

Zuciyarta a cike fal da qunar yadda gidan yake kasancewa kullum cikin hada hada da kai kawo jama'a,duka a shirin fara gudanar da bikin da batasan da meye yafi saura ba?,tana tsoron ma a qare dukka shagalin akan wannan auren data sanyawa suna MATACCE,azo bikin shalelenta abubuwa sugi armashi saboda komai an gudanar dashi a wannan.


Dai dai sanda take isowar farfajiyar gidan,biyu daga cikin security din gidan na qoqarin bude qofar gidan,sai ta tsaya cak tana jiran ganin su waye?


Wasu laflyayyun range rovers ne guda uku,biyu daga ciki ta sansu farin sani,mallakin toufeeq ne. Tunda ya siyesu suke ajjiye bai hau su ba,to amma ya akayi yau aka fiddasu daga gidan?,ina akaje dasu bata da masaniya?.

Waiwayawa tayi tana gogarin kiran daya daga cikin me kula da motocin gidan,saidai kowacce kalma dake bakinta ta qafe tas!,cikin sakannin da basu haura biyar ba yawun bakinta ya dauke,wani abu me nauyi da girma ya daki kanta,abinda ya sanya mata dawo da dubanta zuwa gabanta a hankali kamar me ciwon wuya.


Cikin wata lafiyayyar abayar take blue black. lya adon jiki kadai ya isa ya gaya maka daga wanne gabila da kuma kalar nau'in ahalinta


"alhamdulillah,alhamdulillah,a'uzu bi kalimatillahit taammati minsharri ma khalaqa,Allahumma anzil ni munzalan mubarakan wa'anta khairul munzaleen" addu'o'in data furtasu dukka a bayyane kuma daki daki,cikin nutsuwa ta haqiga,addu'o'i masu qarfi da tsananin tsari.


Wata mummunar faduwa gaban hajiya qarama yayi,ta runtse idanu da kyau tana kuma budesu,suka sauka fes akanta SHIFA

CE,maji,matar yayanta Mahmud,bayan shudewar shekaru talatin da wani abu,sai yau gata a gabanta,sun hade cikin gida daya,sun hade cikin gidan toufeeq,toufeeq din da tace ta sanya a ranta ita ta haifarwa saidai ta haifi wasu a gaba shi da nadeeya,toufeeq din da tace itace dashi har abada...

...kai alwashin

da taci suna da yawa,wasu lokaci yayi mata halacci ya bata damar cikasu,wasu kuwa har yanzu walagigi takeyi sun kasa cika kamar yadda taso.


Murmushin da ta gani saman fuskar shifa bayan isowarta dab da ita,ita da fararen danginta wanda koda baka tambaya ba zakasan cewa yes,larabawan Algeria ne shi ya sake dugunzuma hankalinta,murmushi?, murmushi fa a fuskar shifa,shin ko yawan shekaru da tsahon lokaci yasa ta manta wace ita a wajenta? ‚bata tunanin zata bari taga koda haqorinta muddin ta tuna ita din fauziyya ce


"Assalamualaikum hajja fauziyya" maji ta kawar mata da dukka wata tantama daga ranta. Ko wacce gaba ta jikinta sai data cika saboda tasirin sallama,amma kuma nuna hakan a tattare da ita babbar faduwa ce,don haka itama ta saki nata murmushin,murmushin da ko kadan bai shiga fuskar maji ba bare ya ratsa zuciyarta,tasan wace fauziyya,kuma bata tunanin shekaru zasu canza halinta


"Wa'alaikummus salam,baqi ne haka damu? marhaban bikum" wani murmushin maji ta saki har sai da farare tas din hagoranta da toufeeq ya gado suka bayyana,wanda shekaru bai ragesu da komai ba. Waiwayawa bayanta tayi kadan ta kalli 'yan uwanta da suka yo gaba,suka bar sauran suna fidda luggage dinsu


"'Baqi? baqi,nidai nafi gaban baquwa,saboda daukan ciki wata tara,naquda ta kwana biyu cur babu sassauci a gasar da babu uwa ko uba,haihuwa zuwa raino har na tsahon shekara shida....kin tuna,su kuma dukka wadan nan da kika gani,bari nayi miki taqaitaccen bayani duk da idanunki na shaida sun gama gaya miki,wadan nan sun zarta baqi,ahali ne kuma halastattun dangi ga d'ana

Muhammad toufeeq,d'a na halali ga mahmud umar jarma….mun shigo cikin gidan d'ana da

sunan Allah tare da dukkan amincinsa,zamu zauna adadin yadda Allah ya deba mana,amincin Allah a gareki" ta furta tana miga mata hannu. Tamkar an shukata haka hajiya qarama taji,tsahon shekaru yau matar da take kalla a matsayin matsala yau ta sake waiwayarta,ta yarfa mata maganganu a gaban masu aiki da dukka hadiman gidan da sukayi tsaye suna mamakin jin bayanan maji. Tunda suke basu taba ganin gilmawar wata mace da sunan mahaifiya ce ga sir toufeeq ba,kowa yana kallon hajiya qarama ne a matsayin uwar kowa,hatta da Dr jarma. Ganin ta gagara bata hannun sai ita ta kamo nata hannun ta hade guri guda a sukayi musabahar,ta sake sakar mata murmushi tana cewa


"Kada ki manta,har yanzu a mazaunin qanwata kike,saboda haka daga zamana zuwa fitata hukuncina zai iya hawa kan kowa,ciki harda ke a mazaunina na uwa ga dan da ake qarqashinsa yake bada ci da sha da suttura harda mafaka ga kowa,saina tabbatar da wanzuwar matar alkhairi a gareshi wadda zata kula da rayuwarsa sanann na sake barwa Allah shi amana,kamar yadda nayi tsahon rayuwarsa ta baya, alqawarin kuma Allah gaskiya ne,ya kulamin da su fiye da yadda zato yayi tsammani" sai ta zame hannun nata daga na hajiya qaraman,kai tsaye ta cusa kanta zuwa cikin gidan ba tare data nema jagoranci daga kowa ba.


Wata iska me nauyi da zafi ta zuqa ta kuma fesar,me yake shirin faruwa?


"Kada ki damu, kwanaki bakwai kawai zatayi idan ta dade ta koma inda ta fito,ta barki da yaran da take taqamar a kansu,ki kuma sake mantar dasu suna da wata uwa a duniya wai ita shifa har abada" wannan saqar da zuciyarta tayi mata ita ta kawo sassauci cikin ranta,sai ta juya cikin gida tabi bayan su maji din. Dole ne kamar kullum tayi amfani da kissa da kyau


Cikin hararrami ta dinga bada umarnin kwashe kayansu maji zuwa dakunan da sajjad ya shirya musu,tun a ranar hajiya qarama taga wani irin banbanci muraran,wato shi tuwo dai ba'a taba canza masa suna,daga nadeeya har fadeela babu wanda ya yarda ya saki maji koda kuwa na minti daya ne,suna maqale da ita,bayan sun gama koke koken su,don koda wasa basu taba sanya ran zuwanta ba,nadeeyan rabonta da gain majin tun kafin ta tafi makaranta karatu,yanzu haka shekara kusan shida kenan dr jarma saidai ya bata haquri yace ba yanxu ba,shi ko toufeeq sai ya dauki zancan da gaske saiya shashantar dashi har kayanta ta taba hadawa da yace mata gobe ko jibi zai siya mata ticket tabi jirgi

Zuwa Algeria,amma ranar data kirashi yana airport ma zai tashi zuwa dubai haka taci kukanta ta haqura.


A yau din da taga majin sai takejin kamar duk duniya bata da sauran wata bugata,taci kukanta qwarai,amma yadda maji din ke kwantar mata da hankali tare da jaddada mata ta yiwa yaa moha uzuri sai ta samu relief. Duk wani shiga da fita na hajiya qaraman idanun maji na biye da ita,saidai kawai tayi murmushi ta girgiza kai,koda nadeeya ta tambayeta takance


"B komai nadeeya, Allah yayi muku albarka,ya tsaremin ku"


Tun kafin ya iso gidan labarin zuwanta ya riskeshi daga bakin nadeeya da kuma fadeela data rasa inda zata sanya ranta saboda murna,yau gata ga maji. Yana toilet cikin bathtub amma zuciyarsa na wani irin daka,yana jin doki da son haduwa da mahaifiyar da tayi silar kawoshi duniya,wadda rabonsa da ita shekara gome kenan cif,amma wani irin abu me kama da toro da shakkarta yana tasowa hadi da danne wancan dokin da yake ji. A qalla ya kusa kashe awa guda kafin ya garasa wankan ya fito,ya daur towel a qugunsa yasa qarami yana sharce ruwan dake kwance cikin gargasarsa data yiwa murdadden jikinsa ado.


Cikin wani sassauqan yadi mara nauyi ya shirya,duk da ba wani zaman ado yayi ba amma kyansa ya fito ainun,rashin walwalarsa ta qaru a 'yan kwanakin saboda damuwar da dr da sailad sukeson jafeshi a cewarsa. Kamar yau din,bashi da niyyar fita amma hakanan ya fita bayan sajjad ya gama ce masa dangin amarya zasu zo su sake ajjiye wasu kayayyaki.

Wani takaici yazo masa wuya ya tsaya masa.don me za'a dinga masa shige da fice a sashe?,bayan shi ya fadi cewa bayason dukka wadan nan abubuwan amma anqi sauraronsa.

Hasalima shi sashensa ba gurin shigar kowa bane,wannan ya sanya dai dai da masu aiki kebantattu gareshi, su daya sai sajjad ke shiga masa guri. Baisan me yasa sajjad din be gyara spare part din dake gidan ba suje suyi koma meye a can,key din ya jefa masa ya tattara ya fita ko breakfast dinsa da Jacob ya hada bai tsaya yayi ba.


Flip flops slippers masu taushi ya saka,wadanda suka bayyana sirrin fara tas din doguwar qafarsa,ya jefa wayarsa a aljihu yana fitowa. A falon suka hade da Jacob wanda yake sanye da afron


"Welcome sir,the food is ready" a ga'ida ya zauna din yaci,to amma haka kawai yakejin bashi da nutsuwar hakan


"Not now i will be back" daga haka ya Sanya kansa yana fita daga sashen nasa cikin takun nan nasa na nutsuwa da kamewa.


Lokacin da muryarsa ta bada sautin sallama maji na zaune fadeela na saman gafafunta kamar zata koma cikinta,fadeela na tare dasu nawwara,houria hessa,minafah ,maysam,banaan,amjad,taraneem,tayma da saneem,kusan su sha biyar 'yan mata kamar nadeeva akazo dasu,sai manya masu dan shekaru kusan saannin maji,wasu kuma basu qarasa shekarunta ba suma sun kusa su takwas. Dukansu suna taya nadeeya shirya gifts da kayayyakin bikukuwan al'adar al'ummar gasar Algeria da maji ta shirya gabatarwa. Sarqoqi ne na wuya hannu da gafa na alfarma,dukkansu na gold,coins na gold da kuma wasu irin velvet gown tare,pakistani bride gown masu azabar kyau da tsada,wanda aka samar daga zare mafi tsada da kuma daraja,tare da wasu duwatsu masu tsada.

Ga trousseau package dake dauke da dukka nau'in jewellery na gold da zatayi amfani dasu throughout bikin gaba daya. Kudi sosai marasa misali maii ta kashe, kamar yadda tayi gayya sosai ba tare da jin kudin jirgi ba,duk da kusan kowa shi ya yiwa kansa kudin jirgi,banda

'yammatan da tace suna wuyanta,family ne da sukayi suna a qasar,saboda sun hada komai malanta da kuma dukiya. Dakuna manya manya guda biyu masu girman gaske a wadace ya ishesu,aka zuba musu kuma dukka nau'in abinda zasu bugata bisa jagorancin baaba ramatu data kasa zaune ta kasa tsaye,takaicinta ya cika zuciyar hajiya garama,saidai babu damar yin magana ko wani motsi kada abinda ke lullube a zukata ya bayyana.


Kusan babu wadda idanunta bai sauka a kansa ba cikin 'yammatan,zukatansu suka fara raurawa.wasu suka samu nasarar kau da kawunansu,wasu suka kasa,tamkar babu tsala tsalan mazan larabawa a Algeria.


Kallon kallon suka yiwa juna shi da maji din,kowa a cikinsu zuciya na motsawa da wani irin yanayi,kewa da soyayyar d'a da mahaifi ta fara aikinta. Duk yadda maji taso daurewa saida qwalla ta cika idanunta,amma tayi namijin goqarin hanasu zubowa duk da basu koma ba. Ta tafi tabar moha din nata dan qanqani a gabanta da qananun shekaru,sai gashi yau ya bayyana a gabanta a matsayin magidanci harda d'iya. Nadeeya ce ta janye 'yanmatan suka fice bayan sun gama gaidashi,sunata daburtawa su sa nadeeya,ita bata qware a larabci ba,su kuma hausar tasu duka kame kame,kai tsaye ma idan kace basu iya ba bakayi kuskure ba.

[14/09, 7:42 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*



* TABARMAR KASHI_*

No comments