Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 9-10

 


*Arewabooks: huguma*


https://arewabooks.com/u/huguma


Page 09



           Kwana file din yayi a nan,bayan sallahr asuba ta kammala azkar dinta ta jawoshi tana zaune daga saman abun sallarta,ta buda a hankali ta fara karantawa kamar yadda yaa muhyi yace tayi din.


            Very interesting,komai na kamfanin a tsare yake cikin wani tsari mai burgewa,banda batajin son aikin cikin ruhinta zata iya cewa company din ya burgeta,kuma kamar tana da gudunmawar da zata iya bayarwa tabbas gurin saitashi. Tsayawa tayi cak da biron dake hannunta bayan ta kammala signing tana duban sunan CEO din dake rubuce cikin ruwan gold daga gefen takardar MUHAMMAD TAUFEEQ. Zame hannunta tayi a hankali daga saman takardar tana kallon sunan,a hankali tunaninta ya koma can baya,sai yanzun ta tuna yaa muhyi ya gaya mata zasuyi aiki ne tare da yaronsa


"Jaffal qalam" ta fada can qasan ranta tana maida file din ta rufe,ta riga ta saka hannu,tabbas data janye,batason a kaita sashen da zatayi aiki tare da kowa,amma ya zatayi?,yaa muhyi ya riga ya daureta da jijiyar jikinta.


          A gaggauce ta isa parking lot na gidan sanda yake shirin shiga motarsa,ya dakata ya waiwayo yana dubanta tana dan haki saboda saurin da takeyi,file din ta miqa masa


"Ya akayi?" Ya tambayeta tun kafin ya buda bayan ya karba


"Na cike yaaya" ta fada tana langabe kanta,sosai murmushi ya wadaci fuskarsa,alamun maganar tayi masa dadi sosai,ya fara buda file din ya duba sannan ya dora idonsa a kanta


"Thank you sisi,na gode da baki bani kunya ba baki kuma watsa min qasa a ido ba" yadda yayi appreciating nata saita kasa neman komai daga wajensa,ta saki qaramin murmushi ta gyada kai kawai


"Next week on Monday zaki fara shiga office dinki,komai da kike buqata kiyimin magana baki da matsalarsa in sha Allah,already shi partner din naki ya fara shiga cikin wannan satin" yana maganar yana danne danne a wayarsa. Daga kai yayi 


"Na saka miki kudi ko zaki buqaci yin siyayya"


"Oh no yaaya,ina da kudi a account dina fa,sannan last week yaa Saifullahi ya sakamin shima"


"I know,hal jaza'ul ihsani illal ihsan" kai ta jijjiga a hankali,sai taji cikin ranta tana jin dadin abinda tayi masan,tunda shima har qasan zuciya da fuskarsa abun ya faranta masa.


           Ciki ta koma ta fara shiryawa don wucewa gida,already dama tana da intention na zuwa yin shopping din,akwai kayayyakin amfaninta da sukayi low.


**********Lafiyayyun motocine qirar range rover baqaqe sidik ke wulwula gudu saman kwalta wata nabin wata har guda hudu a jere. Tun daga inda suka taho wato cikin filin sauka da tashin jiragen saman malam aminu kano wato aminu kano international airport har zuwa cikin rukunin gidajen dake unguwar nasarawa GRA,duk inda suka gifta daukan idanu da kuma hankulan al'umma sukeyi tare da saka kokwanton cikin zukatan al'umma na tunanin mamallakan motocin da babu cikakkiyar number a jiki kamar ta kowanne abun hawa,sai wasu qididdigaggun haruffa da kuma lambobi da sukazo a jere data sauran kowacce mota dake bin 'yaruwarta.


         A hankali suka nutsa cikin nasarawa,sannan kai tsaye suka fada titin guda abdullahi road,kafin su tsaya qofar bristol palace. Cikin gaggawa kuma security din dake tsaron qofar gidan suka wangale musu gate ba tare da tsananta bincike ba,dukka motocin suka shige ciki,suka kuma samu wajena gurbin da aka tanada don ajjiye motoci suka faka. Cikin qasa da minti daya dukka qofofin motar suka bude banda guda daya tak,mutanen dake ciki sanye da baqaqen suit suka firfito,kowa ya samu guri ya tsaya,biyu daga cikinsu kuma suka bi hanyar da zata sadasu da reception na hotel din cikin sassarfa.


          A qalla mintuna biyar kyawawa sai ga mutum biyu daga cikinsu ya dawo,cikin azama da zafin nama ya isa ga motar dake tsaye dukka qofofinta a kulle yayi knocking baqin glass din motar,aka dan zugeshi kadan,yayi magana ta mintina sannan yabar wajen,ya koma bayan motar ya dage,yasa hannu ya fidda wasu kyawawan luggage guda biyu,biyu daga cikin mutanen dake tsaye daga bayansa suka matso,kowa ya riqe guda daya,sannan ya sake zagayawa right side na seat din bayan motar ya bude qofar,yaja baya cikin girmamawa don bawa mamallakin motar fitowa.


           Sakanni sittin cif kafin qafarsa ta fara fitowa,Sannan ya zuro qafarsa cikin kyakkyawan takalmi qirar kamfanin hermes na qasar france,sai daukar idanu yake saboda tsananin kyau da tsafta,ya sake daukar wasu sakannin kafin ya zuro dukka jikinsa zuwa waje. Zara zara yatsun hannunsa ya sanya yana qoqarin cire wayar dake maqale a kunnensa,kyakkyawar fuskarsa mai cike da wani irin kwarjini haiba da cikar zati a dinke tsaf!,babu alamun fara'a ko kadan tattare da ita.


             Fari ne,amma ba zaka kirashi kar ba,wani irin fari da bai cika haske da yawa ba,me murjajjen jiki da babu wani waje da yake a rame ko ya nuna alamun qashi,saima qaqqarfar siffarsa da cikakken zatinsa daya nuna kansa da kansa ta jikin lallausan yadin vicuna mai asalin kyau da tsada dake jikinsa,wanda aka yiwa wani irin dinki na musamman mai jan hankali,duka duka tsahon rigar bai wuce gwiwarsa ba,dogon hannu ne da rigar daya bai qarasa tsintsiyar hannu ba,an qawata hannun rigar da wasu irin links masu zubin gold,daga qasansu kadan kuma kyakkyawan agogon hannu ne baqi qirar kamfanin Casio daya kwanta luf saman fatarsa dame lullube da gargasa baqa sidik mai santsi,wadda ta fito har zuwa saman hannunsa da kuma saman kowanne yatsa nasa,zobe ne qwaya tal daga tsakiyar hannun nasa na wani irin qarfe mai daraja,wanda shi ba gold bane,hakanan ba azurfa ba.


              Yadda sumar kansa take baqa sidik a nannade sannan kuma a kwance,hakan gashin daya qawata gefe da gefen fuskarsa,zaka iya kiransa qasumba,saidai baiyi kama da qasumba hakanan baiyi kama da saje ba,saboda wani irin gyara na musamman da akayi masa,wanda yasa yafi qasumba kyan gani,yafi kuma saje tsari da qawatuwa,tun daga kumatunsa zuwa habarsa,ya kuma hade da qasan hancinsa. Baqar sumar da baqin yadin dake jikinsa suka hadu suka haska farar fatarsa tarrrr tamkar fitowar rana a farkon wuni. Eye glasses din daya sanya kuma ko kadan bai boye kyawawan qwayar idanunsa ba dake da wani irin shape mai matuqar fusgar hankali,idanun dake cike da wani irin kwarjini mai tarin yawa,kwarjinin da a kullum yake lullube da fushi da kuma fusata.


           Ko yaya ka qara taqi kadan kusa dashi kana iya shaqar daddadan qamshin turarensa da ba lallai ka gane ainihin wanne irin turare bane,saidai yakan sanya nutsuwa ga duk wanda ya shaqeshi,ya kuma qara kwarjini ga ma'abocin qamshin.


            Dukka hannayensa ya zube a aljihun lallausan yadin jikinsa,ya kuma daga kai yana kallon tsororuwar ginin hotel din cikin kamewa da nutsuwarsa,tamkar wanda yake nazarin wani abu,yayin da dukka mutanen suka zamana a tsare cikin shirin kota kwanar karbar umarni daga gareshi. Iska ya furza ya taka zuwa gaba,abinda ya sanya mutum biyu daga ciki sukayi gaba kamar masu masa jagora,sauran kuma suna biye dashi,yayin da daya daga gefansa wanda ke riqe da wani babban folder ya matso gefansa kadan


"May I continue sir" ya fada cikin matuqar girmamawa a russune,da hannu yayi masa nuni da eh,yaci gaba da takawa shi da sauran mutanen,yana biye dashi yana karanto masa komai daki daki. Dukkansu suka fara kutsa kai zuwa cikin main entrance na hotel din.


            A gaggauce suka wuce zuwa lipter da zai sadasu da dakin da zai sauka,cikin mintunan da ba zasu wuce sakanni sittin ba ta tsaya,suna biye dashi har a sannan ta bude dukka suka fito. Kai tsaye har zuwa qofar dakin. Daga daga ciki yayi scanning card a bakin qofar,tayi qaramar qara alamun samun izinin shiga. 


           Palace suit,babban dakin dake da aqalla zai iya daukar mutum bakwai cif,two ensuite bedroom da kuma master bedroom guda daya,living room dining room kitchen da kuma corridor. Wannan shine cikakken zabinsa ga masauki,bayason takura bayason matsi,duk sanda tafiya ta kamashi zuwa wani gari da bashi da gida nashi mallakin kansa,ko kuma yake buqatar kebewa ko sauka ya huta sosai ba tare da kowa yasan ya shigo ba.


           Yadda yayi cak a tsaye yana sauraron bayanin da inyamurin ke kwararo masa haka sauran mutanen da suka shigo tare dashi suke a tsaye,dukkansu na jiran wani umarni nasa ne. Sosai ya kafe mutumin da idanu,duk da cewa bai kalleshi ba amma tsantsar kwarjinin da idanunsa ke dashi ya hudashi,tun daga fatarsa har zuwa jinin jikinsa ua harbawa kwanya da zuciyarsa,take muryarsa ta fara rawa,ya fada kwan gaba kwan baya cikin bayanansa,sai ya lumshe kyawawan idanunsa kawai, qwaqwalwarsa ta fara kaishi inda yake zato ko hasashe.


"Where is musaddiq?" Karon farko da muryarsa me taushi da wani irin amo a cikinta ta bayyana cikin sigar tambaya da alamun gajiya da jin soki burutsun bayanan da ake masa. Daya daga cikin mutanen ya matso da hanzari ya amsa masa


"Sir.....on his way"


"Ka kirashi,ka gaya masa yayi sauri,idan yazo ya karbi dukkan folders din dake hannun peter kafin ya nemeni,you can go" ya fada a taqaice yana sanya kansa ciki.


             Gaba daya gumi ya rufe mutumin da aka kira da peter din,tabbas yasan qaryarsa ta qare,tun daga watan da aka sanar da yiwuwar zuwansa kamfanin,yaketa shige da ficen ganin ya binne komai,ya kuma rufe bakin dukka wanda zaiyi ruwa da tsaki wajen kawo tarnaqi cikin walwalarsa,sai gashi a karon farko......tun ba'a je ko ina ba alamu sun fara nuna kansu. Ya san yaron sarai,bawai tun yau ba,aiki ya taba hadasu sau daya tak dashi kafin su suma ya karkata hankalinsa zuwa wata qasar,bai kwashe da dadi a hannunsa ba,yaji babu dadi qwarai,sai gashi wata mummunar qaddarar ta sake dawowa tana neman budadeshi.



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[04/08, 4:21 pm] +234 907 013 9442: *H U G U M A*


_*TABARMAR ?ASHI*_??

 

*Arewabooks: huguma*

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 10



          Har yayi taku biyu mutumin da yafi yawan magana dashi yadan sassauta muryarsa


"Am sir,am sorry.....akwai mutum biyu dakeson zama dakai,yanzu haka suna zaman jiranka"


"Who and who?" Kadan ya buda wani dan qaramin abun rubutu dake hannunsa sannan ya gaya masa sunan


"Mr Paul and mr isaac" fara takawa ya sakeyi zuwa ciki sannan ya amsashi


"Tell them to give me an hour,I will take a bath".


              A nutse ya tura daya daga cikin dakunan daya fi zabar zama a ciki,rabin hankalinsa nakan wata qaramar wayar hannu 'yar firit me qarancin tudu yana latsata. Ya lalubo wata number ya fara kira,dai dai sanda ya zauna gefen sofa bed,idanunsa na bisa fuskarsa data fito tarwai ta babban madubin dake dakin,sai kayi tsammanin ita yake kallo,saidai ko kadan,tunaninsa ya lula wata duniyar daban.


             Ba dadewa na'ura ta gaya masa layin a kashe yake,yaja tsaki yana sauke wayar a kunnensa,ya sake laluba wata number,wadda ita din bugu daya ta shiga.


            Muryar dattijuwa ce ta bayyana cikin wayar,muryar dake nuna zallar dattijanka da kamalar mamallakiyar muryar


"Barka da dare yallabai" shine abinda ta fara fada bayan amsa mata sallamarta da yayi


"Barka,kuna lafiya?"


"Lafiya qalau walhamdulillah......yanzun nan tayi barci ko mintuna goma batayi ba" lumshe idanunsa masu kyau da daukan hankali yayi


"Alright......a shafamin kanta" kafin ta sake cewa komai ya katse wayar,ya durqusa a mugun kasalance yana zare takalmin qafarsa zuwa socks yana cillarwa waje daya,gaba daya yayi loosing duk wani interest akan aikin,abban bai taba nufarsa da wani aiki da yaji sam bayaso ba irin wannan,baisan me yasa ba. 


           Sai daya cire kayan jikinsa tsaf ya daura babban towel ya wuce bathroom. Wanda a qalla sai da ya shafe mintuna nasu dama kafin ya fito,tamkar wanda yake sauya fatar jikinsa.


            Lokacin daya fito din ya samu na'ura na gaya masa yana da baqi a living room,ya kauda idanunsa da suka dan canza launi sakamakon shigar ruwa cikinsu ya mayar ga madubi yana qoqarin tsane sumarsa data jiqe da ruwa,abu guda daya tak da zai fara gaya maka shi din ba asalin bahaushe bane,yana da jibi da wani yaren da aka sansu da irin wadan nan sumammakin.


            Kamar babu wanda yake jiransa haka ya kammala shirinsa a nutse cikin wasu farare qal din pajamas,ya zura dogayen qafafunsa wadanda kamar basa taka qasa cikin wasu lausasan baqaqen flip flops,sannan ya kwashi wayoyinsa ya wuce zuwa living room din.


            Mutum biyu ya samu a zaune,daya yasan da zuwansa,dayanne baiyi tsammanin zuwan nasa ba a dai dai wannan lokacin. Dukkansu suka miqe,daya matashin dake sanye da wata danyar shadda getzner daketa faman maiqo da qyalli ya miqa masa hannu kai tsaye sukayi musabaha,cikin salon da kana kalla zakasan akwai sanayya da shaquwa me qarfi a tsakaninsu,duk da fuskar dayan bata nuna hakan ba,har yanzu dai tana nan a yanayinta na dazu,daurewa da kuma rashin walwala. Matsowa daya matashin yayi,cikin girmamawa ya russuna


"Barka da yamma" kai yadan gyada masa sannan yace


"I hope ka karbi komai kamar yadda nace?"


"Eh na karba,but yace na gaya maka....." Kasa qarasawa yayi yana dan sosa kansa kadan,a nutse ya zauna,ya kuma zuba masa idanu bayan ya dora qafarsa daya akan daya,yayi relaxing sosai cikin kujerar,abinda ya sanya musaddiq ya sake diriricewa kenan,ya kuma yi nadamar karbar saqon peter


"Idan baka da abun cewa get out,i don't have time to wasted" salin alin musaddiq ya sanya kai zuwa waje,don bayajin zai iya qarasa fadin saqon,kwarjininsa yayi masa yawa,yana saka kai zai fita,daya daga cikin ma'aikatan dake aiki a restaurant din dake hotel din ya sako kai dauke da dukka nau'in kayayyakin buqata naci da nasha,wanda daya daga cikin aikin ma'aikatansa ne wato jibril,he's very serious akan dukka abinda yakeso,kafin ya fada anyi,wannan ya sanya yake ji dashi matuqa,baya kuma rabo dashi duk inda zashi.


              Tsaf aka shirya komai,jibril kuma ajjiye masa wanda zaici a dining room,sannan ya sanar masa


"Saina gama da mr isaac first,but before....." Sai ya waiwaya gareshi


"Kana da buqatar wani abu ne?" Kai ya girgiza


"No,banajin gaskiya"


"Okay,i will be back,zan sallamesu......ban cup daya na coffee" ya buqaci hakan.


          A duniya idan ka cire mahaifinta da yayyenta maza guda uku da Allah ya bata,babu wata sauran halitta ta d'a namiji data yarda dashi,babu wani d'a namiji da take masa kallon me imani,babu kuma wani d'a namiji da take dubansa a mazaunin nagartacce,dukkansu tana aunasu ne kan mizauni guda,ma'auni guda da kuma dabi'a guda daya,suna kuma tafiya ne a nata ganin kan tafarki guda.


            Su biyu ne cikin motar kan hanyarsu ta dawowa daga shopping ita da ya zaid,suna tafe a hankali yana qoqarin cusa mata ra'ayin aikinta,ta bashi aron kunnuwanta kawai,bawai don tana jin qaunar abun ya shigeta ba,abinda ta lura dashi dukkansu suna supporting aikin,suna kuma so tayi,ta karanci a nasi ganin suna hasashen hakan zai rage mata zaman kadaici ne,yayi attaching nata sosai da mutane,ya dawo mata da dukka yarda aminci da walwala da kuma mu'amalarta da kowa yadda take a baya.


            Signal din da taga ya saka yana niyyar shiga guda abdullahi road bayan suna kan hanya dai dai shi yadan ja hankalinta


"Yaa zaid.....ina zamu qara zuwa?"


"Oh my goodness" zaid ya fada yana dariya harda dukan sitiyarin mota


"Anya zancan afifa bai zama gaskiya ba?" Saita waiwayo da hanzari


"Da tace me?" Yadda ta tambayeshi da sauri tana narke fuska ya sake bashi dariya


"Tsoron duka mutane kikaji,you didn't trust anyone". Tabbas gaskiya afifa ta fada,idan kai tsaye akace ta tsani maza ba'a yi mata qarya ba,ita kadai tasan abinda ta fuskanta,wani abun bazai fadu ba. Sai taji zuciyarta ta tabu,har hakan ya bayyana baro baro saman fuskarta,ya zaid yadan juya kadan ya kalleta kafin ya maida hankalinsa akan tuqin da yakeyi,cikin sigar lallashi da kwantar da murya yace


"Ba duka aka taru aka zama daya ba,dole duk runtsi duk tsanani akwai mutane na haqiqa,akwai nagartattu fiye da tunaninki,akwai masu soyayya saboda Allah,suke kuma nemanta ido rufe,banason wannan kudin goron da kike mana,saboda saka hakan da zakiyi a ranki zaiyita hunting dinki to the rest of your life idan har baki canza ba" 


"Bazan maka musu ba ya zaid,amma I doubt gaskiya" ta fada da karyayyar zuciya da kuma karyayyar murya,har taji kaman hawaye suna tsatstsafowa daga qwayar idanunta. Murmushi ya saki kadan,baisan ta yadda zasu sauya tunaninta ba a kullum,amma suna fatan watan wataran HASKE zai bayyanar mata. Yasan duk yadda zai kwatanta mata a yanzun babu lalallai ta miqa hankali nazarinta da tsinkayenta zuwa wajen,don haka ya rufe chapter din ya dauko wani batun na daban,saidai ya riga ya karya zuciyarta,ta kasa sakewa.


              Riqe da glass coffee mug din a hannunsa da yake kurba time to time,yana zaune daya daga cikin kujeru hudu dake gurin,sauran biyun baqinsa ne a kai,idanunsa akan takardun dasu Mr Paul suka gabatar masa yana irga adadinsu da idanunsa ba tare da yakai ga tabasu ba. A nutse ya ajjiye mug din yasa hannu ya rufe file din 


"We will contact you after two weeks" kai suka jinjina cikin fara'a suka miqa masa hannu,saidai kafin yakai nasa hannun muryarta ta ratsa dodon kunnensa


"Hi......" Ta furta, cikin qasa da second biyar kuma ta bayyana a gabansu.


           Dukka su ukun suke kallonta,saidai kowannensu da irin kallon da yake mata,mr isaac da Mr Paul kallo suke mata na zallar burgesu da tayi,kyawunta kuma ya ratsa har cikin jininsu,yayin da nasa idanun suka cika da tsananin bacin rai da haushi mara misali. Idanunsa ya janye daga kanta ya miqa musu hannu sukayi musabahar da basuyi din ba,sannan ya miqe yasa hannu daya ya dauki mug dinsa,daya hannun kuma ya fara danna wayarsa yana son kiran jibril yaso ya shiga masa da file din. Cikin second kadan ya iso,ya masa nuni da takardun,yasa hannu biyu ya dauka ya wuce dasu.


              Tana tsaye a gurin,ta zuba masa dukka idanuwanta,tana jin wata mahaukaciyar qaunarsa tana tasiri a jikinta da zuciyarta,tana jin kamar ta taka da gudu ta rungumeshi cikin jikinta,ta kwantar da kanta saman ingarman qirjin nan nasa,ta kuma shafi gefan fuskarsa dake dauke da lallausan gashin da tana iya hango gyaran da yasha ya kuma kwanta luf. Saidai inaaaa,tasan hakan shine babban kuskuren da zata tafka a rayuwarta,tasan wayeshi qwarai da gaske,ko a yanzun ma tana cin albarkacin wani abu ne,tabbas!,da bata isa ta bibiyeshi har haka ba.


           Ganin ya fara barin inda take din ba tare daya nuna wata alama na sanin wanzuwarta a wajen ba yasa itama ta cira qafarta dake sanye da high heels ta fara binsa


"Hello" ta gada da muryarta mai yauqi,shuru ba amsa,wannan ya sanya tadan qara daga qafa


"Muhammad" tayi kiransa da ainihin zallar sunansa. Shi kansa a karan kansa yasan girma qima da martabar me asalin sunan,mahaifinsa ya dauka ya bashi shi,zaiyi wuya ka kirashi da sunan zalla ya iya tafiya ya barka a guri saboda girmamawa ga sunan kansa,batasan hakan yana masa tasiri ba,tana kiransa ne kawai duk sanda taji nishadin kiran nasa da sunan nasa. Ya tsaya cak,har zuwa sanda yaji qarasowarta bayansa dab dashi,cikin deep voice dinsa yace mata


"Ki juya ki koma inda kika fito"


"Saboda me?,don kai fa nazo"


"Ba matsala bace......i said ki juya ki koma inda kika fito,if not....." Maqale hannayenta tayi a qirji,alamun gargadinsa ko a jikinta


"Idan nace a nan zan kwana fa,kuma a kusa dakai?"


"You are mad,ki gwada ki gani" ya fada yana jin zallar tsanarta tana shigarsa,cikin second kadan tasa kansa ya fara ciwo,duk duniya ita daya ta isa ta tsaya haka a gabansa a matsayinta na MACE ya fada sau daya ta maida masa,ita dimma tana cin wata daraja ne guda daya,sai ya fara yin gaba ba tare daya waiwayo ba.


           Baisan daga ina ba,baisan ya akayi ba......saiji yayi an masa wawar runguma ta baya,he was shock beyond the words,bai taba zata ba bai taba kawowa ba,bai taba tunani haukan LABIBA yakai haka ba. Wani irin mahaukacin fushi ya yunquro masa,yana waiwayo ya zube mata yatsunsa guda biyar saman fuskarta.


             Hannu bibbiyu ta saka tana dafe dukka kuncinta guda biyun hadi da rintse idanu tamkar ita aka mara bayan ta saki wayar hannunta da take dannawa don rage tsahon lokacin jiran yaa zaid,sai kuma ta bude idanun nata a hankali tana laluben daga inda wannan zazzafan marin ya fito,dai dai lokacin da ya fara magana cikin deep voice dinsa data cika da tsananin fushi


"Shashasha wawiya, I can't tolerate it, next time kika sake gwada irin haka kiyi tsammanin abinda yafi haka" yayi wurgi da mug din hannunsa ya hadu da qarfen dake riqe da fitilun gurin ya tarwatse,baiko bi ta kansa ba ya wuce yana taku da sassarfa duk da hakan kuma majestically.


            Mutuwar zaune sãahar tayi,kunnuwanta suna bitar mugayen maganganun da yanzun nan kunnuwanta suka saurara,duk da cewa bataga fuskarsa da kyau ba amma muryarsa ta fita clearly kamar a gabanta yake maganar,a hankali kalaman suka fara mata suya a qirji tamkar ita aka gayawa,me yasa maza suka raina mata?,itace tambayar data dinga yi mata sukuwa cikin tsakiyar kanta,idanunta nakan labiba data sulale a gun tana kuka,kukan nata ya dinga taba sãahar,ta lumshe ido tana jin kamar ita ya zaga. Me tayi masa ne da har zai daga hannu saboda zallar rashin sanin darajar mace ya zabga mata irin wannan marin?,bata iya shiga abinda babu ruwanta ba,da ta qarasa ta daga labiba data zube a gun tana kuka sosai,ta bata haquri tare da bata shawarar ta manta dashi koda ba zata iya rama abinda yayi mata ba.


           Kasa jure sautin kukan nata tayi,saboda yana son taso mata da nata tsohon ciwon,don haka ta miqe a gaggauce ta zagayawa zuwa inda yaa zaid ya ajjiye motarsa,tayi amfani da key din daya bata ta bude motar ta shige tana maida numfashi ranta a matuqar jagule.



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[07/08, 11:50 am] +234 902 488 9500: TABURMAR KISHI




*H U G U M A*


_*TABARMAR ?ASHI*_??

 

No comments