Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 71

 


* TABARMAR KASHI_*



Page 71


Guri guda idanunsu suka hade,wani abu me matugar garfi ya fusgeta,ya kuma ratsata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin qafafunta,a hankali tray din dake hannunta ya sulale yayi d'ai d'ai a gasa,bata bawa kanta wani option ba da ya wuce juyawa cikin hanzari da sassarfa tana barin gurin.


Ko motsawa baiyi ba daga inda yake zaunen,tamkar an dasa shi a wajen ya bita da kallo harta qule ta bacewa ganinsa. Kaf tunaninsa ya katse ya kuma tsinke,babu abinda ke kai kawo a fuska da kuma zuciyarsa sai fuskarta,his ex president......me takeyi a gidan? wayo ya kawota cikin gidan?. A hankali ya sauke dubansa kan farantin da yayi d'ai d'ai a gurin,komai ya kama gabansa,tunanin da ya darsu a ransa ya sanyashi zaro wayarsa ya sake kiran number nadeeya,bugu daya ta dauka


"Waye kika aiko ya kawomin coffee?"


"Am sorry yaaya,muna magana ne da maii nannyn fadeela ne"


"Nanny?" Ya tambayeta da wani irin murya


"Eh yaa,am sorry ya mohai didn't intend to offend you" bai tsaya ce mata komai ba ya kashe wayar kawai


"What if itama ta shigo rayuwar su ne ta cutar masa da fadeela?" Shine kawai abinda ya samu zuciyarsa na jaddada masa,dukkan alamu sun nuna she's not in need bare yace hakan va sanyata aikatau,bata fito daga gidan da suke da qaramin qarfi ba bare yace a buqace take,ko kuma ta cancanci tayi aiki a wani guri, qaramin aiki ma irin wannan, she's well educated,tana da qualifications din da zata iya samun aiki ako ina Nigeria da waienta,amma sai ta zauna yin aikin nanny?no...ko daya zuciyarsa bata kwanta masa da hakan ba,kai tsaye ya tashi a wajen,ya bulla ta falonsa ya shiga ya dauki wayarsa ya fara neman layin mommy qarama.


Da gyar ta isa dakinta saboda wani irin bugawa da zuciyarta keyi,kamar zata balle qirjinta ta fito ko kuma ta amayota ta baki.


Gefan gado ta samu ta zauna tana maida numfashi,idanunta dukka a rufe,tana ganin shacin inuwarsa ta cikin duhun rufaffun idanunta


"Yaa moha,shine toufeeq? daddyn fadeela? ‚yayan nadeeya?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar,wanda motsin fadeela da sunan kiranta da takeyi tun kafin ta shigo dakin ya sanyata bude idanuwan nata,sai ta mige da hanzari ta fada toilet ta maida gofar ta rufe.


Tsaye tayi a jikin gofar tana jin sautin siriryar muryar yarinyar tana kiranta,sai zuciyarta ta gaza jurewa da shurun da tayi mata


"Anty N idan kin fito maji na jiranki" saita sake mata gyaran muryar alamar ta amsa


'i love you anty" ta fada tana dariya ta fice.

Hawaye masu zafi ne taji sun taru mata a ido,yarinyar ta saba gaya mata wanann kalmar duk sanda ta danyi wasu awanni bata ganta ba,a yanzun data gaya matan sai takeiin kamar furucin da zai shiga tsakaninta da ita kenan na qarshe ita fadeelan ......koda wasa batajin zata iya lamuntar zama gida daya da MT jarma,mutumin da ya wulaqantata,ya tozartata,yaci mutuncinta,mutumin da baisan darajar dan adam ba,sai taji tana jajantawa fadeela,yarinyar batayi sa'ar uba ba sam,ta fito daga tsatson da bai dace da halayyar yarinyar ba.


Wani kuzari ne yazo mata da ya sanyata bude gofar dakin ta fito,ta nufi qofar dakin ta murza mata key sannan ta dawo da sauri ta jawo luggage dinta ta fara zuba kayanta a ciki.


Cikin mintuna galilan ta gama hada dukka kayanta waje guda,dama ba wasu kaya masu yawa take bari cikin gidan ba,tunda kowanne sati tana zuwa gida ta maida wasu ta dauko wasu,ta zari Vail dinta dake saman couch ta nannade kanta zuwa wuyanta,ta jawo luggage din ta bude qofar dakin fa fito.


Tana sako gofarta a hallway din suka bangaji juna ita da nadeeya wadda ga biyota da iPad din ta bata maji din kamar yadda maji ta bugata. Da sauri nadeeya taja baya tana kallonta mamaki kadan na nunawa saman fuskarta 


"Ina zuwa haka da akwati da yammar nan?"

Sosai tayi gogarin dadaita muryarta


"Gida zan koma nadeeya" razani ne ya nuna

sosai a fuskarta,sai lokacin ta samu damar

qarewa birkitaccen yanayin sãahar din kallo


"'Gida kamar vaaya anty N,me ya faru?"

Hannun nadeeya ta laluba ta sanya mata key din dakin a hannunta


"Kuyi haquri,bazan iya ci gaba da zama tare daku ba"


"Me kike cewa säahar? don Allah me


mukayi miki? …baaba ramatu!" Nadeeya ta

gwalawa baaba kira a rude ganin sãahar ta

ja luggage dinta tana barin hallway din zuwa

falonsu,wanda daga shi sai babban falonsu sai

fita daga sashen gaba daya.


Kiran baaba ramatu din da tayi yaja

hankalin fadeela ta fito daga dakin nadeeya

din


"Baaba,wai anty nanny ce kawai ta hada

kayanta wai gida zata koma"

"Subhanallahi,me ya faru?,me akayi mata?"


"Wallahi ban sani ba baaba" nadeeya ta bata

amsa ita da fadeelan suna rige rigen cimmata.

A falon garshe suka tareta har baaba

ramatun


"Haba Khadija,me ya faru haka rana tsaka zaki

ce gida zaki koma"


"'Ba komai baaba,na ajiye aikin ne" teddy din hannunta fadeela ta yar,ta kama hannun sãahar ta rige tsam


"Don Allah anty karki taft,idan kuma zaki tafin bari na dauko kayana mu tafi tare" zuciyarta ta sosu da yadda taga yarinyar ta rude lokaci daya,sai ta tsugunna a gabanta tana riqe da hannayenta


"Tafiya ta zama dole faddee na,kiyi haquri kinji,babu komai, sister nadeeya tana tare da ke,zata kula da ke,hakama baaba ramatu" saita zame hannun zata miqe,amma fadeelan taqi sakinta,ta fara hawaye tana cewa


"Allah ni bazan zauna bake zanbi"


"Am sorry my faddee" ta fada tana shafa sumarta da ta gama gyara mata ita dazu da azahar,tayi mata ado da wasu pink din ribbons.


Zame hannunta tayi ta soma nufar waje,tana qwararawa kanta gwiwa daga raunin da zuciyarta ke shirin yi,batason ta karaya har taji ba zata iya tafiya ta barsu ba,tanason ta tsira da mutuncinta,wanda ta tabbatar idan tana gidan a qarqashinsa babu inda mutuncinta zaije,tunda har ya nemi take mata kima da martabar ta a muhallin da ba nashi ba....yaya kenan zai faru a yanzun da zata zamanto qarqashin ci da sha da inuwar gidansa?.


Iska me zafi ya furzar daga bakinsa sanda ya gama jin komai daga bakin hajiya garama,zuciyarsa bata nutsu ba,yafi gasgata akwai manufa cikin shigowarta rayuwarsu,don haka zuciyarsa tafi aminta da sallamarta daga gidan,koda ko wanne irin kulawa take bawa fadeelan.


A hankali kunnuwansa suka fara jiyo masa sautin kukan fadeelan,ya mige a nutse yana riqe da wayarsa a aljihunsa,ya kuma tunkari barandarsa ta inda yake iya ganin komai dake faruwa a farfajiyar gidan.


Itace a gaba janye da luggage dinta,fadeela na biye da ita,nadeeya da baaba ramatu kuma suna biye da su cikin hanzari da alama suna nufin dakatar da ita ne,sauran maaikatan gidan kuma sunyi carko carko cikin damuwa,kowa ya kasa aikata komai,saboda basusan maqasudin abinda ke faruwa ba.


Ransa ya sosu da ganin yadda fadeelan ke binta gudu gudu sauri sauri,amma ko sau daya bata tsaya ba bare ta waiwayo ta dubi kukan da takeyi ba

"Fadeela!" Ya kirata a tsawace,abinda bai taba yi ba tsahon rayuwarsu shi da ita.


Dukkansu suka tsaya cak,har saahar din da kiran nasa yayi wata irin tsawa a tsakiyar kanta,ta kuma runtse ido tana fatan Allah ya sanya ba dukan fadeelan zaiyi ba.


A zafafe yake takowa har ya iso gurin


"Tashi ki wuce ciki!" Ya fadi da muguwar tsawar da ta sanya nadeeya ja baya da sauri ta koma bayan baaba ramatu ta boye,saboda a yau din gaba daya a birkice take ganin yaa moha din.


"Abby tafiya zatayi ta barmu,me mukayi mata,don Allah ka bata haquri"


"Ba abinda kukayi mata,ko bata tafi ba daman zan sallameta,saboda bata dace ta rayu daku ba" maganganun nasa sai suka zame mata tamkar zubar dafi tsakiyar naman zuciyarta,tana da muradin ko sau daya ta waiwaya ta sake kallon fadeelan dake kuka iya qarfinta saboda ita kadai,amma kalmarsa ta sanya ta lanqwasa zuciyarta taci gaba da takawa ba tare data waiwayo ba. Tsawar data sake ji ya yiwa fadeela karo na biyu ya sanya qwallar dake magale a idanunta qarasa gangarowa,zuciyarta na kwarara da wata matsananciyar tsanarsa,sai ta qara sauri tana ficewa a gidan,lokacin da ya sanya hannu daya ya dauketa cak ya nufi cikin gidan,ta qwalla garar kiran sunanta full, abinda bata taba yi ba


"Anty saahaaarrrr" kamar zata shide,sai ya dageta ya rungumeta tsam a jikinsa zuciyarsa na wani irin bugawa a mugun jargiy,yana jin kamar ana yankar naman zuciyarsa.


Duk yadda taso riqe qwallarta cikin mota amma abun ya faskara,sai tasa tafukan hannayenta kawai ta lullube fuskarta tana sauke hawaye masu dumi qwarai,ba abinda ke dawo mata cikin kwanyarta sai sautin kukan fadeela da yadda ta qwalla kiran sunanta har zuwa sanda sautin ya dusashe daga kunnuwanta. Sanda suka isa qofar gidansu ta cire kudin ta miqawa me napep,yana fadin


"Hajiya ga canjinki fa" ko waiwayowa bata iyayi ba ta daga masa hannu,ya fuskanci me take nufi sai hau zabga godiya yaja macnine dinsa yayi gaba


Baaba habu ne ya karba mata kayan,yadda yake mata sannu da zuwa yaji batace komai ba sai ilkinsa ya bashi akwai matsala,don haka bai sake cewa komai ba ya migawa jamilu luggage din yace ya garasa mata ciki da ita.


Can gasan magoshinta tayi sallama,falon nasu ba kowa kaman yaushe,yana nan a tsaftace da qamshinsa,da kuma ac dake bada iska me sanyin dadi,sai gamshin sanwar dare dake sirarowa kai tsaye daga kitchen dinsu.


Baaba rabi ce ta fito daga kitchen din sai taci burki tana cewa


"Ah ah,maraba da farar diya,kece yanzun nan akan hanya?" Kai ta gyada muryarta can qasa 


"'Nice baaba rabi,barkanmu da yamma"


"Yauwa barka kadai" daga haka tayi hanyar bedroom dinta tana tambayar maama


"Basu jima da fita ba ita da afifa"


"To yayi" abinda ta fadi kenan ta wuce shige dakin nata.


Saman gadonta ta zube kamar wata kayan wanki tana qoqarin samarwa kanta saugin abinda takeji a zuciyarta,tayi lamo idanunta a rufe tana jin yadda zuciyarta ke gonewa. Inda ace ta san wannan gidan nasa ne,inda tasan ace wannan ahalin nasa ne inda ace tasan wannan diyar tasa ce.....to babu shakka,duk yadda zuciyarta zata kai ga tausayinta ba zata taba rabarsu ba.


Duk iya yadda yake tunanin zai iya lallashinta ko kuma ya bata baki amma abun ya faskara,har ya gaji da lallashin,ya koma bakin window din dakinsa yayi tsaye yana duban farfajiyar gidan, zuciyarsa na masa mugun zafi. Me yasa suna zamansu lafiya suna lallaba rayuwarsu zata shigo ta hargitsasu?,bayajin fadeela ta taba kuka irin wannan,koda kuwa ranar data rabu da mahaifiyar da tayi silar kawota duniya ne. Wai me yasa ne su mata basu da tausayi?,basu da imani?,a duk sanda zuciyoyinsu masu cike da ra'ayoyin qeta da son kai ta mosa musu,tabbas sai sun shiga rayuwar dukkan wanda suka hara sun aiwatar da koma meye sukayi niyya. Bayajin zai saurari kuka ko rigingimun fadeela,zata gaji ta haqura ta bari, dole ta koyi rayuwa babu mutanen da zasu zame mata baraza ko matsala,kamar yadda suka tashi shi da NADEEYA,suka rayu kuma a hakan,babu kuma wani abu da ya canza kalar qaddararsu,gasunan cikin qoshin lafiya da wadatar Allah.


No comments