Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 7-8

 


*Arewabooks: huguma*


https://arewabooks.com/u/huguma


Page 08


    

        Daga shigowarsa zuwa isowarsa gurin duka duka mintuna qalilan amma ya cika wajen da hayaniya da fadace fadace,sãahar ta lumshe idanunta tana jin wani bacin rai yana sake ratsata,ko ba'a gaya mata ba ta tabbatarwa kanta wannan shine mijin matar,sai taja kujera kawai ta zauna tana qare masa nazari hankali kwance,domin tayi imanin babu abinda zai hanashi karbar hukuncin dukka wannan haukar tashi.


*_Bayan awa d'aya_*


          Duk da yadda lamarin ya zamo mata Wani babban fami a rayuwarta,amma sai ta dinga jin nutsuwa tana shigarta da aikin data aiwatar yau cikin asibitin,duk kuwa da cewa bata da Wani relation da matar,amma tana jin tayi abinda ya kamata na ceto ta daga azzalumin namiji data tabbatarwa da kanta ire irensa suna da yawa a duniya,wasu matan da yawa saidai a lahira ubangiji zaiyi wannan hisabin,don basu da gata basu da me tsaya musu,babu kuma me qwato musu yanci da haqqunansu da mazan suka sanya takalma suka tattake. Karon farko taji tana da sha'awar bude qungiyar da zatayi aiki akan ire iren wadan nan zalunci da akewa mata,to amma gaba daya bata da wannan qwarin gwiwar a yanzu,ita kanta akwai sauran tarin matsaloli da qalubale,wasu sun shude wasu tana cikinsu,wasu kuma jikinta yana bata suna gaba suna jiran isowarta


"Sannu da aiki" farheen ta fada sanda sãahar ta saka key tana qoqarin kunna motar bayan ta kammala duk abinda ta qudirta yi a asibitin.


            Waiwayowa sãahar tayi ta kalli farheen din,qaramin murmushi yana subuce mata,duk da yadda zuciyarta ke wani irin zafi,tanason lallai saitayi mata bitar tata rayuwar,yayin da ita kuma ya sanya dukkan wani qarfi nata tana tanqwarata,tare da gaya mata bata da wannan buqatar,sãahar din bata amsa ba ta tayar da motar cikin nutsuwa tayi reverse suka fice daga harabar asibitin,anty farheen na sake jinjina mata qoqarin da tayi,da kuma yabawa sãahar din kan hannun wadanda ta danqa me gidan matar,ta tabbatar matat zata samu adalci.


           Saboda raunin da zuciyarta ta samu wannan ya sanya takejin jikinta gaba daya ba qwari,don haka suna isa gida ta fidda kayan jikinta ta watsa ruwa,ta sanya wata riga me taushi da akayita da zallar auduga,ta rage ribbom di kanta tabar wani siririn band.


           Tana zura slipper a fara sol din qafarta wayarta dake yashe saman madubi ta dauki tsuwwa,a kasalance ta isa gaban madubin tana kallon wayar. Baquwar number ce dai still,sai ta kauda kanta daga kallon wayar,sai a sannan ta tuna da saqonnin da ta gani a dazu,taja qarami tsaki tana barin gaban madubin,ta wuce Parlor abinta.


           Kadan ta taba abincin ta baro anty farheen acan ta dawo daki,idanunta akan agogo,tanason ganin lokaci zai bata daman yin baccin awanni biyu kafin sallar magrib,sai qarar wayarta ta sake mata kutse cikin tunaninta. Wannan karon tun batakai ga wayar ba ta fara jan tsaki,tana jin haushin kanta da bata sake kashe wayar ba.


               Sai data daga sannan ta lura da sunan BESTIE,tadan karyar da kanta gefe tana maqala wayar a kunnenta,ta koma bakin gadon ta zauna qafafunta zube a qasa tana sallama cikin lallausar siririyar muryarta


"na gode sosai bestie,na gode,kin gwadawa mahmud iya matsayina a wajenki,na gode"


"Oops......" Sãahar ta fada a hankali tana dora yatsunta saman goshinta,she really need a rest......ga afifa da tata rigimar a gefe


"Dama munyi haka dake?,ko ya nemi izinin kirana?"


"Oh sorry,na miki shishshigi ko?,am so sorry" afifa ta fada tana gimtse wayar. Siririn murmushi ya qwacewa sãahar,ta sani sarai rigima afifan keji,dakuma son cusa mata mahmud din qarfi da yaji,batasan yaushe ya samu wannan fadar haka a wajen afifan ba,har takeson mata tutsu saboda shi.


          Aje wayar kawai tayi gefe ba tare data bi bayan afifa ba,tasan zata gama fushinta ta huce ne,infact ma a yanzu hutawa takesonyi,idan ta tashi koma meye taji dashi. Ta sauke ajiyar zuciya ta kwanta sosai a tsagin hannun damanta kamar yadda ta saba,ta lumshe manyan idanunta a hankali,eyelashes dinta masu tsaho da baqi suka yiwa kyawawan tsagar idanunta rumfa.


*********K'arfe takwas da mintuna na dare agogon dake maqale a bangon falon ya nuna,farheen na tsaye daga dining area tana hadawa yaa muhyi fruit salad,daga qasan falon kuma,can saman qawatacce kuma lallausan carfet din da aka yiwa Parlor din ado dashi,sãahar ce zaune,sanye cikin wata farar long sleeve shirt turtle neck da aka yiwa adon flowers qananu daga wajen qirjin da pink flowers,kanta babu dankwali sai band data matse gashinta daketa qyalli yana daukar idanu,duk da cewa dare ne,amma hakan bazai hanaka jin sassanyan qamshin da jikinta yake fitarwa ba,wanda ya riga ya gama runewa a jikin fatarta komai gumi da zafi,fuskarta tayi wani fresh farinta me surkin ja ya bayyana sosai,duk kuwa da cewa ko dan kunne babu a kunnuwanta amma hakan baya hanaka hango baiwar kyan da Allah ya bata. Aleena na zaune tsakiyar qafafunta,khalifa kuma yana zaune daga gefanta tana masa homework. Lokaci lokaci farheen na daga kai tana dubansu sannan taci gaba da aikinta,yanayin yadda sãahar din ke matuqar son yara zai baka mamaki,a haka a ido sam batayi kama da meson yara ba.


           Sallamar yaa muhyi cikin Parlor din ita ta tashi karatun,khalipha yayi gurinsa da gudu aleena ta fara daga masa hannu tana bangale masa da dariya,dole ya qaraso ya dauketa,ya zauna saman kujera yana ji dasu duka su biyun,da khalipha dake surutu,da aleena dake gwaranci.


"sannu da zuwa yaa" sãahar ta fada tana miqewa tsaye da zummar barin falon. Waiwayowa yayi yana dan karkata hankalinsa a kanta


"Barkanki khadijatou"


"Ya aikin?" Ta sake fada tana duqawa ta dauki wayarta


"Alhamdulillah.....zan shiga ciki yanzu zan watsa ruwa,after one hour ki sameni"


"Okay" ta fada tana jinjina kai,sai ta juya ta wuce zuwa dakinta tana jiyo 'yar hayaniyarsu da yaran.


             Saman sofa bed ta zauna tana gwada kiran afifa wadda ta dauki fushi da ita,bugu biyu ta daga


"Me kika kirani kice min?"


"Relax mana" ta fada very calm


"Dadina dake hayaniya sa saurin daukan temper"


"Eheeen,ya muke dake?" Maganar ta saka sãahar sakin qaramin murmushi saman kyakkyawar fuskarta,tasan magana ce kawai afifa keson gaya mata


"Koma ya muke din ba wani abu bane,nayi miki laifi kiyi haquri,am sorry" ajiyar zuciya afifa ta sauke,sãahar din tana da wata baiwa cikin halaye da dabi'unta,tasan dukka hanyar da zata zauna da kowa da zamantakewa ya hadasu,hakanan tasan hanya mafi sauqi na sauke mutum daga kan fishinsa nan take


"Is ok"


"Everything will be alright......but for now please,ki manta da issue dinsa.... mahmud ko?" Ta fada calmly. Idanu afifa ta fidda kamar tana gabanta


"Ya salam...... you can't remember his name sãahar,Allahu yahdik" ta qarashe maganar tana dafe goshinta


"Whatever afifa,i need space don Allah,ki dakatar dashi"


"Zan gwada"


"Zaki gwada..... like how?"


"You are more than you think,ya dauki al'amarinki da girma sãahar,ba lallai don na mishi bayani ya fahimta ba"


"Ya rage nashi" ta fada very careless tana dage kafadunta. Ita gaba daya al'amarin maza baya burgeta sam,ko meye zasuyi,shin meye bata gani ba?,wanne hali nasu ne yayi mata saura?,hirar gaba daya bata burgeta don haka ta sako wani topic din daban.


              Sai da suka cinye awa dayan da yaa muhyi din ya bata sannan ta ajjiye wayar,ta shiga bandaki ta daura alwala,ta dawo ta fidda abaya ta dora saman rigar jikinta,ta yane kanta da mayafin abayar.


             Duk da agurguje ba tare kuma da nufin tayi kwalliya ba ta shirya,amma kyanta ya fita sosai,zakayi tsammanin zama tayi tayi wata kwalliya ta musamman,tana da baiwar komai ta ra?a a jikinta yi mata kyau yakeyi.


            Cikin takardu ta sameshi,gefansa ta zauna tana wasa da yatsun aleena dake zaune jingine da pillow don kada takai ga faduwa,ya dubeta yana ture takardun gabansa,ya zaro wani file mara nauyi,saidai ya banbanta da dukka takardun wajen,bangonsa fari ne tas,anyi masa ado da zaiba,kallo daya zakasan na musamman ne ko kuma yana dauke da wasu muhimman bayanai.


            Budawa yayi daya bayan daya yana dan dubawa cikin nazari,daga bangon farko har zuwa bangon qarshe,sannan ya maidashi ya rufe,ya ajjiye shi a tsakaninsu yana kiran sunanta idanunsa a kanta


"Na'am yaaa"


"Kiyi haquri na miki laifi,na karba takardun amsar aiki daga MT GROUP OF COMPANY,ba tare dana jira jin hukuncin da kika yanke ba,am sorry na miki katsalandan" kanta ta daga a hankali,ta sauke dubanta ga yaa muhyi din tana jin wani abu me nauyi yana sauka saman kanta zuwa qirjinta,wani abun kuma da bata tantance meye ba yana mamaye qirjinta,maganganun nasa sunyi mata nauyi qwarai,saboda bata zaci jinsu a wannan lokacin ba,saidai abu daya da take tunawa,yaa muhyi din yafi qarfin komai a wajenta,ta tabbatar shi din masoyi ne me qaunar dukka wani abu da zai baiwa zuciya da rayuwarta farinciki,bijirewa saka hannun karbar aikin dai dai yake da ta tozartashi


"Ga file din ki wuce dashi daki,ki duba sosai ki saka hannu a duk inda ya dace,amma kafin sannan,har yanzu kina da chance,idan kikaji baki nutsu ba ko baki gamsu ba,kada ki damu ki dawo da dukka takardun" ya fada yana miqa mata su.


            Hannu ta miqa itama ta karba,sannan ta miqe cikin sanyi da mutuwar jiki,kamar wadda aka bibbigewa gwiwoyi ta doshi qofar fita,yaa muhyi din ya rakata da kallo har sai data bacewa ganinsa. Kansa ya jinjina,cikin ransa yana fatan saituwar al'amuranta,yana jin kamar ya runtse idanu ya bude yaga sãahar dinsu ta baya ta dawo,ba wannan sãahar din da duk wani buri na rayuwa ya fice daga rayuwarta sa tunaninta ba da mugun gudun tsiya,sanadin wani abu daya shude shekara biyu baya.


           Kamar wani abun tsoro haka ta ajjiye file din saman madubi,ta koma gefan gado ta zauna,ta dafe gefe da gefe da dukka tafukan hannayenta tana kallon file din daga inda take zaune tamkar wadda ke nazarin karatu daga allon computer,tako ina tana jin sanyin jiki,mutuwar jiki dama rashin karsashi,saidai ko daya cikin istikharar data sanya a gaba takeyi bataji a ranta ta fasa aikin kota watsar da tayin yaa muhyi ba.



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[04/08, 4:21 pm] +234 907 013 9442: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

             Page 07


*Arewabooks:huguma*

https://arewabooks.com/u/huguma




         "yayanki ya saka hope da yawa a kanki,ya kambamaki da yawa,Allah yasa dai zaki fishsheshi" sãahar dake tsakiyar duniyar tunani ta tsinciki maganar farheen kaman daga sama. Kadan ta waiwayo ta dubi farheen,kamar zatace wani abu sai kuma ta fasa,ta sake maida kanta ga tuqin,wanda har suka isa asibitin bata kuma cewa uffan ba.


            Tunda suka shiga dakin suka gaisa da mara lafiyan da relatives na anty farheen,sai ta kama hannun khalifa suka fita a dakin,saboda idanun mutum biyu da suka fara uzzura mata,zata iya cewa tasan daya,saboda tana ganin pictures dinsa cikin hotunan farheen,dayan ne batasan daga ina yake ba,amma tana kyautata zaton dan uwan mijin thurayya me haihuwar ne.


             Ta bayan asibitin suka bi ta fara shawagi cikin asibitin,dukka guraren da take bi din gurare ne da babu yawaitar mutane sosai,sai majinyata jifa jifa,abinda ya sake karya mata zuciya,tana sake godewa ubangiji da ya barta da lafiyarta bata salwanta ha,tabbas inda burin ADAM yakai ga cimma gaci,tayi imani dari bisa dari cewa har kamar wannan lokacin itama tana cikin jerin sahun wadanda zasu qulla kyakkyawar alaqa da asibiti,idan ma bata samu gurbin zama a cikinsa ba,zaman da ba wanda yasan ranar yankewarsa da ubangijin daya qaddara mata komai.


           Tafi tafi sai gata ta bulla ta bangaren 'yan haihuwa,cikin jiki da zuciyarta taji tana mararin shiga ta basu gudunmawa,don ta tabbatara akwai tarin mata masu raunin gaske a wajen,saidai ta manta cewar yau din bata riqo koda purse ba bare ta fito da kudi. HIBBA HASHIM ta tuna,wata qawa ga afifa dinta,idan bata manta ba kamar ta taba jin afifa na maganar anan take aiki,saita koma gefe daya ta tsaya,ta kunna wayarta wadda tun daren jiya take a kashe. Bata gama daidaita ba saqonnin kar ta kwana suka fara turereniyar shigowa da baquwar number da bata sani ba. Qaramin tsaki taja ta share saqonnin ba tare data duba ba,ta kira afifan. 

 

          Ta bata tabbacin a nan take,kuma ana samunta a yau din,cikin minti biyu ta kira mata ita,sai gata a bakin gurin,fuskarta fal fara'a. Tanason sãahar,tana masifar burgeta,gayunta kyanta da kuma iliminta,macace me ajin da jerawar mutum kadai da ita ya isa ya sake siya maka daraja da aji,don haka cikin girmamawa ta yiwa sãahar jagoranci zuwa gurin.


           A hankali take takawa,jiki da zuciyarta gaba daya sun raunana,tsohon ciwon dake danqare a zuciyarta ya fara balle kansa,wannan ya qaranta walwala sosai daga fuskarta.


            Muryar wata nurse shine abu na farko daya fara dukan dodon kunnenta,fada take sosai kamar me shirin antayawa matar dake tsaye a gabanta dauke da tulelen ciki zagi,ba abinda jikin matar keyi sai rawa,tana kuma share hawayen dake zarto mata


"Nidai don girman Allah malama kiyi haquri,ki bani gado,idan na haihu koma meye sai ayi,amma yanzu inajin haihuwata a kusa,koda yaushe zan iya haihuwa"


"To ina ruwan wani?,ki haihu din mana,wanda yayi miki cikinma bai damu ba bare mu da rana tsaka muka ganki dashi" saita juya tana niyyar wuce matar.


           Cak sãahar tayi a wajen,ta gagara zama samam kujerar da hibba ke mata tayin zaman,a nutse ta dauke manyan fararen idanunta daga kan matar zuwa kan hibba


"Me ya samu waccan matar" baki hibba ta tabe


"Kin ganta nan,ta kawo kanta asibiti da sunan haihuwa,amma ko pant din da za'a sakawa jariri babu,bare ayi maganar katin da tayi awo kudin gado da sauran abubuwan da ba gwamnati ce take biya ba,da aka tambayeta ina mijin sai tace ta baroshi gida yana bacci,muka ce lallai sai yazo,saboda yaronta breach ne,zamuyi qoqarin gyara masa kwanciyarsa,idan an samu nasara shikenan,idan ba'a samu ba dole sai ya biya kudi anyi mata C.S. Dajin haka hankalinta ya tashi,muka bata aron waya ta saka numbers dinsa ta kirashi,wallahi sai data kusa kiransa sau goma kafin ya daga,da gasken kuma baccin yakeyi abun mamakin,daya daga yaji itace sai cewa yayi 'dalla malama meye?' tayi masa bayanin komai,amma budar bakinsa cewa yayi,kada ta dameshi,idan ya gama baccin zaizo,idan zata iya jiransa ta jirashi,idan ba zata jirashi ba tayi duk yadda taga zata iya,sai ya kashe wayarsa.....kinsan abun takaicin?" Kasa cewa komai sãahar tayi bare ta amsa mata ba,duk da hakan hibba bata damu ba ta dora


"Dukka kudin matar nan idan tayi aikin tayi wahalar mijin take bawa wai a taru a rufawa juna asiri,wallahi duk da abinda yayi matan nan muna ta masifa amma bashi kariya takeyi a fakaice,abinda ya bamu haushi kenan mu duka,har yanzu kuma in gaya miki baizo ba,maganar da nake miki tun jiya fa abun nan ya faru,kudin data tara inda a hannunta ta ajjiye ba yaro daya ba ko biyar zata haifa zai mata komai ba" idanunta sãahar ta mayar ta rufe tana jin wani radadi tun daga cikin idanuwan nata har zuwa zuciyarta


"Allah ya tsinema makahon so" kalmar ta subuce daga bakinta ta fita da wani irin zafi da amo me motsa rai da zuciya.


"Wallahi kam" hibba ta amsata ba tare data lura bada ita take ba


"Kuyi mata komai ni zan biya,ku bani number wayar mijin nata,he must pay na duk neglect dinsa akan matarsa,ba baiwa bace d'iya ce kamar yadda yake d'a ga wasu" ta fada a mugun zafafe. Har yanzu maza suna bautar da mata?,har yanzu maza suna amfani da raunin 'ya'ya mata suna cutar dasu,suna illata su,wadda ke kan wani doro mai matuqar hatsari ga dukka rayuwar kowacce d'iya mace na mutuwa ko rayuwa ma basu barta ba bare me lafiya?. Ta daga idanunta da suka canza launi daga inda take zaune tana duban inda matar ke tsaye,kallo daya zakayi mata ka tabbatar tana cikin tsananin tashin hankali,kuka kawai takeyi,bata ko duba da cewa ita din ba qaramar yarinya bace,taimako da agaji kawai take nema,ya manna mata abinda zai iya zama ajalinta ya kuma gaza bata kulawa a sanda tafi buqatar hakan,koda da kudinta ne wanda ta hada da guminta da qarfin jiki dana zuciya,ba tare datayi la'akari da nauyinta yana bisa wuyansa ba


"Ina danginta?"


"Ba 'yar nan qasar bace,aurota yayi,kamar nijer naji tace" daidai sanda hibba ta gama bawa sãahar information matar ta kama qugunta ta durqushe tana murqususun dake nuna ciwonta ya fara kankama da gaske. Sãahar din na tsaye sanda nurses din suka kamata bisa jagorancin hibba suka shiga labor room din da ita. Kasa zama tayi,wani tsumammen bacin rai yana taso mata kamar zai shaqeta,wasu abubuwa da suka shude mata cikin rayuwarta a yau suka fara motsawa,suna son dawo mata da abinda ya shude a baya, situation din da matar ke ciki yayi mata baban famin data kasa shanyewa,saida wasu hawaye masu zafi suka sauko mata,ta saka tissue din data riqo a hannunta saboda khalifa ta daukesu a mugun sanyaye.


           Muryar farheen ce ta katseta,ta waiwaya daga sashen da takejin amon muryar tata


"Nayita nemanku ban ganku ba,inason nace ku dawo ciki,dakin babu kowa" farheen ta fada tana karantar wasu abubuwa masu zafi dake fita daga qwayar idanun sãahar. Kai ta girgiza


"Zan shigo,amma saina gama wani dan aiki a nan"


"Patient dinki ta sauka fa,ta samu baby girl" muryar hibba dake qarasowa gurin da hanzari ta katse tambayar da farheen ke shirin jefawa sãahar


"Alhamdulillah" sãahar ta fada tana lumshe idanunta,har cikin ranta tana jin bacin ranta yana raguwa,wanne irin sa'a akayi haka komai ya daidaita cikin hukuncin ubangiji?,ba tare da ankai ruwa rana ba duk da babyn ba'a dai dai take ba?. 


        Tun kafin farheen ta jefa tambayarta ta gama karantar komai, saita harde hannuwa tana saurarensu ita da hibba har suka gama maganganunsu,hibba ta koma dakin ta gani idan an gama gyara babyn ta dauko musu ita.


"Amma......daga haka ba wani abun zaki sake aiwatarwa ba?" Farheen ta tambayi sãahar sanda taga tana latsa wayarta. Karamin murmushi kawai ta fidda ba tare da tacewa farheen komai ba,ta riga ta qudirta a ranta,sai kuma ta aiwatar. Bugu biyu aka daga wayar daga can bangaren,suka kuma fara magana da matar dake riqe da wayar a daya sashen.


           A nutse farheen ta dauke dubanta daga kan sãahar dake shigar da qorafi tamkar aleena ko afifa aka yiwa hakan ta juya ga bayanta,inda muryar magidancin da duka duka bazai wuce shekara arba'in ba a duniya ke tashi cike da hayaniya da kuma hargowa,cikin nuna zallar gogewa a rashin mutunci.



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[04/08, 4:21 pm] +234 907 013 9442: *H U G U M A*


_*TABARMAR ?ASHI*_??

No comments