Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 69-70

 69


Tunda ya fara ci din baice komai


ba,cikinsa kawai yake kaiwa,wani dadi da

gardin abincin yana ratsa kunnensa da

kyau,zai iya cewa ya manta rabon da ya

dorawa harshensa abinci me dandano irin

wannan,cike da qamshin ganyayyaki da spices

masu gara lafiya da qamsasa abinci.


"it's delicious ko abby?" Fadeela dake leqen

idonsa ta fada,kai ya gyada kawai


"Anty N ce ta dafa fa,ta iya abinci sosai"

dakatawa yayi da cin abincin,ya maida

dubansa ga nadeeya 


"how a nanny turn to a cook?" Cikin gogarin daidata kanta ta masa gamsashen bayani ganin yadda ya hade rai nadeeya tace


"Tafi kowa iya girki a gidan nan,ka tambaya fadeela,coffe din nan ma ita ta hadashi" ransa yadan baci kadan,saboda ba'a kowanne hannu yakeson yaci abinci ba


"Amma.....you know my rules?"


"Am sorry yaaya,ta fimu tsafta da komai da kimai Allah i swear" shuru ya danyi,sai ya ture abincin ya balle gorar ruwa ya zuba a cup ya fara sha.


Ranar har dare suna tare har sai da sãahar ta kira nadeeya a waya fadeela tazo tayi mata shirin bacci 


"Kizo ku gaisa saiki dauketa please anty N"

"Sorry nadeeya,ina uzurine ta nan haka,ki daure ki kawomin ita"


"Okay" ta amsa mata tana kashe wayar.


Basu jima ba suka snigo fadeela rungume dia ledojin tarin tarkacenta na cive ciye da wasa,daya hannun nata wata ledar ce, wadda ta tuburewa abby din nata sai daya bawa anty N din tata kyautar doguwar riga,sai wani designer din turare wanda zahirin gaskiya nashine na qashin kansa da yake amfani dashi wasu lokutan ya siyosu don ya ajjiye fadeela ta sanya rigima,to be honest baison sharing personal abubuwansa da mutane,amma fadeela ta daukarma anty N dinta.


Sai data gama shiryata tsaf ta gudu gurin abby din nata tace yau a can zata kwana,ta dawo ta gama shirin nata baccin sannan ta zazzage ledar. Komai na ciki ya dauki hankalinta sosai da sosai,daga turaren har doguwar rigar, kana kallonsu kasan na musamman ne,tayi murmushi tana sake in gaunar fadeelan da yadda itama take sonta,ta yiwa kayan guri ta kwanta.



********Kamar kowacce safiya bayan alfir ya gama ketowa,yayi dukka azkar dinsa da addu'o'in sa,gym yake shiga wanda a nan hantsi yake riskarsa.


Guri ne dake cike da dukka qarafuna da nau'in kayayyakin motsa jiki,wajen yana da girma sosai, kuma an masa tsari me kyau,kamar ba cikin gida aka yishi ba,kai kace daya daga cikin ire iren guraren motsa jiki na alfarma da aka gina ne domin neman kudi.


Farare qal din sport wear ne a jlkinsa na kamfanin LULULEMON ATHLETICA,da suka fidda qirar jikinsa qwarai,shafaffen cikinsa dake da wani irin tattarar muscles,singalilin qafafunsa dake dauke da gargasa,a tsaye suke kyam suma da alama naman gurin ya saba da zallar gudu da motsa jiki,dantsensa da hannun rigar ya kamashi tsam shima,ya hada zufa sosai amma hakan bai sanya ya rage gudun treadmill machine din ba.


Sai daya gama iya lokutan daya saba yi din sannan ya tsaida treadmill din, vana furzar da iska daga bakinsa yana dan fidda numfashi me kauri ya sauko,ya dauki water bottle dinsa ya bude ya kafa kai yana shan ruwa. Sai daya kusan shanyeshi ya ajiye bottle din,ya zari qaramin towel din dake ajjiye musamman a guri daban yana goge zufar. Ba abinda bakinsa da zuciyarsa ke marari irin dandanon coffee din jiya,duk yadda yaso ya kauda kai yanzun haqurinsa ya tuqe,a yadda ya gama motsa jikin nan shi kadai jikinsa yake bugata,sai ya tsugunna ya sassauta daurin takalmin qafarsa,ya ajjiye towel din ya fita daga gym room din.


Yana tafe a veranda din da zata kaishi sassansa ma'aikatan da suke da aikin safe suna kawo gaisuwar su,da hannu yafi amsa musu sannan ya wuce cikin tsayayyen takunsa dake nuna zallar lafiya da mazantaka.


A falo ya zare takalmansa,ya zura wasu dake ajjiye a gurin ya qarasa shiga cikin falon,hancinsa na jiye masa qamshin girkin Jacob,mudassir da ya kammala gyaran sashen yana feshe ko ina da wani freshener na musamman dake kashe qwayoyin cuta,kafin ya kunna kowacce humidifier dake aiki a lungu da saqo na sassan,ya rusuna yana gaidashi. Dan dakatawa kadan yayi da tafiyar yana amsa gaisuwar tasa,tare da qoqarin karantarsa


"Ya akayi?" Ya jefa masa tambayar,kansa a qasa yana shafa kan nasa


"Sir, matata ce ke labor tun jiya,amma bata haihu ba,so na barosu ne a asibitin inason tafiya da wuri" 

agogo ya kalla sannan ya maida dubansa kansa


"Me yasa kazo aiki?,me yasa baka nema excuse ka tsaya ka kula da amanar da aka baka ba?" Ya fada cikin kaurara murya da alamun fada


"Banason ne..”


"Bakason me?,c'mon,saboda baa jikinka abun yake ba?, maza ka yiwa elyas magana,idan kuma saiiad ya shigo kace nace ya maka sallamar da zata isheka" godiya sosai ya zube yana masa,bai tsaya saurarensa ba ya wuce.

Har yayi gaba ya dakata yace


"idan ta wuce awa daya ka canza mata wani asibitin"


"Yes sir,in sha Allah" daga haka ya wuce hanyar da zata sadashi da hallway. Duk da yanayin da rayuwarsa ta tsinci kanta a ciki amma Allah ya zuba masa masifar tausayin mace me ciki,koda kuwa cikin qarami ne,saboda har yanzu idanuwansa suna iya tuna masa wahalar da maji tayi,tun daga farkon cikin nadeeya har zuwa qarshensa,har yau bai manta ba.


Wannan tunanin ya darsa masa ganin dacewar kiran majin ya gaya mata ya dawo,da wannan qudurin ya shiga dakinsa,saidai kafin yakai ga alkatawa sal ya manta menene ma yace zaiyi din,yakai gauro yakai mari amma ya kasa tunawa,sai kawai ya zare kayan jikinsa ya fada wanka.


Da sallama a bakin nadeeyan ta tura gofar dakin fadeela ta shiga,murmushi ya wadaci fuskarta tana kallonsu


"To bama dole kiyi kumatu ba? don Allah ki gani,da safen nan an tasheki ke daya kina cin kayan dadi ke kadai abinki" dariya kawai suka saka mata


"'Ke da baki tashi da wuri waye zai rage miki?"

Saahar ta fada tana goge hannun fadeela da tissue. Hamma nadeeya tayi


"Yanzunma wallahi yaa moha ne ya tasheni don Allah coffe zaki taimaka ki bani na kai masa da sauri,kada yace ya fasa sha nayi jinkiri " kai sãahar ta daga tadan kalli nadeeya tana mamaki a ranta,don anyi jinkiri kawai sai mutum yace ya fasa shan abu?


"Indai sauri kikeyi to yanxun kam sai milk tea wanda na dafawa faddee,babu coffee"


RA

"Ya salam....a zubamin nayi shahada,idan kuma nasha maruka to kin jawomin tare zamuyi jinya" ta fada tana zare ido.


Miqewa sãahar tayi cikin fuskar mamaki


"Maruka kuma? haba dai"


"Allah ba komai bane wajen yaa moha,yaushe ya daina ne? tafiyata karatu fa" maganar sai tadan daure mata kai,to amma batason tsawaitawa tunda ba huruminta bane,don haka fadeelan na biye da ita tana bata labarin tsaurin yaa moha din har suka isa kitchen, itadai tana saurarenta harta gama zuba milk tea din a wani siririn qawataccen silver flask, qamshin flavour din da yakeyi da su cardamom gaba daya ya cika kitchen din


"Yawuna ya tsinke Allah,wannan wanne irin tea ne? don Allah anty N ki ragemin" dariya nadeeyan ta bata,yadda tayi maganar da gaske cikin marairaicewa


"Ya rage miki,bana zaton zai iya shanyewa" dukka ta zaro fararen idanunta waje


"Wa? niii?yaa moha din zance ya ragemin abu?,idan kin ganni a lahira kaini akai" da mamaki ta juyo tana dubanta


"Wanne irin mutum ne shikam haka?"


Abinda takeson cewa kenan,amma saita maida maganarta ta hadiye. Idan ta saba yin hakan da nata yayyun,nan din ai ba gidansu bane,kowa da irin tsarinsa da nasa ra'ayin,so ba huruminta bane.


Yana amsa waya ya fito daga dakinsa,yayi fes cikin wasu fararen kayan still, da alama zabinsa kenan farin abu ko kuma abu me haske,musamman idan ka duba vanavin furniture din dake qawataccen falonsa. Da ido ya tsire tea din har ya kammala wayar,ya kashe ta ya ajjiye wayar a gefe yana hada hannayensa guri daya,kafin ya maida dubansa ga nadeeya


"Me ya hau kanki ne?,wannan yanzu coffee ne?ko dama inashan tea da madara?" Tasan dama tsaf hakan zai iya faruwa,don haka ta sake maida fuskarta kalar tausayi


"Ba wancan yaaya...amma please kasha wannan,idan baiyi ba Allah na rantse, kayimin hukunci"


"Ya isa,Gate out" ya fada calmly,da sassarfa ta juya ta fice tana dafe qirjinta saboda arzigin data auna yau bata shiga ukunsa ba.


Kaman bazai sha ba kamar dai jiya,sai qamshin ya buwayi hancinsa,a daqile ya dauki cup din idanunsa akan TV ya kurba. Kasa wassafa komai yayi a ransa, saboda qamshi da gardin madarar daya kai masa ko ina,karon farko bayan shekaru masu dama ya samu tea din da yafi masa coffe dadi.

_tom,nikam nace tun yanzu MR JARMA?,WAI YA HADUWAR ZATA KAYA NE? KOWA NA YABON DAN UWANSA BA TARE DA YASAN WAYE SHI BA.MUJE ZUWA_

*DON ALFARMAR ANNABI MUHAMMADU

ME FITARWA KIYI HAKURI KIBAR MANA

KAYANMU*

[07/09, 4:25 pm] +234 703 451 7171: *HUGUMA*


Page 70

. Baisan ya akayi ba,shidai ya tsinci hannunsa riqe da empty cup,ya maida a hankali ya ajjiye yana tunanin rabonsa da shan madara a tea,sai gashi yanzu ya shanye ta tsaf,har yana jin buqatar qarin wani tea din,to amma bayason ya aika din,zaidai binciki yadda ake sarrafashi.

*********A tsaye suke suna fuskantar juna,duk da cewa ita din bashi take kalla ba hakanan akwai 'yar tazara a tsakaninsu. Irin kallon da yake mata kadai zai gaya maka zallar yadda zuciyarsa ta narke da soyayyarta

"Zan tafi.don Allah ina roon kici gaba da bani dama"

"Allah ya kiyaye ka gaida gida" ta fada tana
Juyawa,zuciyarta a quntace saboda abubuwa biyu,na farko tasa yasa an tilastata ta bashi damar zuwa zance gidan mutane,taso ta furje amma Dr girema ya kirata da kansa,yayi masa irin fadan da bai taba mata irinsa ba,sannan kuma ya tabbatar mata wa'adin sati biyu kacal ke gareta,ruwanta ta bashi dama ta bude masa zuciyarta ta fadada tunaninta su fahimci juna,ruwanta ne kuma taqi. Maganganun dr sun daga mata hankali sosai,don bai taba mata magana da salon fada da bacin rai irin haka ba.

•Ci gaba da kallonta mahmud yayi har zuwa sanda ta bacewa ganinsa,ya sauke hannunsa yana furzar da iska daga bakinsa,sannan ya juya yana nufar inda gurd dinsa da ya masa rakiya yake. Hakan yayi dai dai da shigowarsa ta qaramar qofar gidan,yana sanye da wani lallausan yadi da aka yiwa dinkin african kaftan na maza,fuskarsa ta cika da wani irin kwarjini,elyas da jibril na biye dashi.

Dawowarsu kenan daga masallacin layinsu wansa aka gudanar sa taro da akanv duk sanda aka samu dama,kusan duk wan ke muqami ko babba a unguwar yana halartar taron. Lokaci guda idanunsu suka sarge ana juna,murmushi mahmud ya saki cikin hanzar ya maida akalarsa zuwa gabansa

"Sir" ya furta yana saluting nashi cikin murmushi,fuskar toufeeg ta motsa kadan alamun murmushin shina yayi, ya migawa mahmud din hannu
"Barka da yamma sir"

"Barka,kana lafiya?"

"Lafiya alhamdulillah,kwana da yawa sir,tun a
Singapore,ban zaci zamu sake haduwa nan kusa ba"

"Gashi Allah ya nufi hakan" ya fadi yana maida hannunsa ga aljihunsa fuskarsa a dan sake ba kamar yadda take ba

"'Gaskiya ne,ina fatan zamu sake haduwa anan kurkusa"

"In sha Allah" ya fada yana gyada kanshi

"Nazo ne wajen qanwata da kuka riqemin a gidanku"

"A nan din?" Ya fadi cikin mamaki

"Yes sir" ya fada yana waiwaya hadi da
duban inda sãahar ta tsaya a dazun. A ran
toufeeq din ya danji mamaki,me kuma zaya
kawo qanwar mahmud gana gidan?,ko cikin
qawayen nadeeya ne?,shine tunanin da yafi
kwanta masa

"She's my soulmate,inata qoqarin ganin mun
dai daita ne,she's my wife to be in sha Allah"
sake daurewa kansa yayi,har ya kalla ainihin
sashen cikin gidan ba tare da ya shirya ba,sai
ya gyada kai yana sake bashi hannu

"Allah ya taimaka" ya fadi ya zame hannunsa
bayan sunyi musabaha yayi ciki.
Dab da zai shiga sashensa nadeeya ta
fito tana laluben sãahar sabida shurun da taji
tun bayan fitarta,tayi masa sannu da zuwa
ya amsa yana tambayar fadeela,sai tace
masa tayi bacci yanzun nan bayan ta gana
jiran dawowarsa,yana wucewa ciki yana gaya mata ta kawo masa cottee nan da kamar awa daya, murmushi ta saki gain yadda ta zama addicted da coffee din nanny,shi da baya cin komai a hannun kowa. Har ya zarta ya dawo da baya yana tambayarta waye yayi bago a gidan?

"Nanny N ce,ko ba mahmud ba?" Kai ya jinjina,sai kuma yayi gaba ba tare da ya sake cewa komai ba,amma can qasan ransa cike yake da mamaki,mahmud ke son nanny din gidansa?,abun sai yaji baiyi making sense ba,so amma shi din ba mai damuwa da shiga rayuwar wasu bane,don haka tun bai isa sashensa ba ya tattara lamarin ya watsar.

Sai daya gama komai ya sauya kayan jikinsa zuwa wata shirt,v neck ne daya fidda sirrin ginannen girjinsa me yawan gargasa,sai dogon wandon joggers pants,qafarsa saye da socks da baya rabo da ita yawancin lokuta.

Farfajiya ce ta musamman da akayi mata gofa daga cikin falonsa, wanda aka qawatata da wasu irin sofas masu retractable canopy a samansu,wanda zasu baka daman zama comfortable kamar kana kan gado,samansu ya zauna yayi relaxing sosai sannan ya kunna system dinsa bayan ya duba lokaci ya tabbatar lokacin da suka sanva don yin meeting dinsu through video call da directors na companies dinsa dake gasashe daban daban lokacin ya cika,ya bude system din ya saita komai sannan yayi group call in general.

Ba jimawa kusan kowa ya daga din,mutanene da sukasan muhimmancin lokaci da kuma na aikinsu,don haka komai suna yinsa ne akan lokacin da aka tsara zaa yi din. Cikin salo da qwarewa da sanin makamar aiki suke tattaunawa,da zallar qwarewa a harshensa na furta kalmomin yaren turanci,a haka suka cinye awa guda cif,wanda basu qara ba kuma basu rage ba aka tsaida taron,suka sanya wani lokacin da zasu sake haduwa su tattauna.

Sake zama yayi saman sosai saman sofa din,yana gyara rumfar dake saman sofa din. A yanzun yana jin aminci da nutsuwa sosai akan kasuwancinsa,dukka directors dinsa amintattu ne,ya tabbatar koda babu shi zasu iya gudanar da kamfanin fiye ma da yadda zaiyi.

Wayarsa ya ciro ya lalubi number nadeeya,bugu daya ta daga

"Yaa gani nan,kana ta baya ne?"

"Yeah be hurry"

"Okay tom" ta amsa masa,tana maida dubanta kan säahar dake hada coffe din zata dora masa

"Don Allah yafi na ko yaushe,zan tambayi wani abune, inaso a bani da wuri,kinsan yaa moha shi da girki two and one ne" murmushi tayi tana girgiza kai,tuni ta fahimci hakan al,yanason laflyayyen abincihakanan baya shiri da yunwa.

Tun kafin ya kashe kiran da ya yiwa nadeeyan yaga kira nata shigowa wayar tasa baisan number din ba bashi da niyyar picking,saidai yana gogarin katse kiran nadeeva din kiran ya shigo ya daga lokaci guda ba tare da ya shirya ba,dai dai lokacin kuma true caller dinsa ya nuna masa sunan me kiran AMEESHA!.

lya sunan kawai ya haifar da wani irin bala'i cikin zuciyarsa,lokacin da sautin muryarta kuma ya baqunci kunnensa sai ya ja fikinsa ya sauko daga saman sofa din yayi tsaye,kowacce jijiya ta jikinsa tana miqewa

"Ina fatan kana lafiya,babu wata doguwar gaisuwa,don na tabbatar ba amsamin zakayi ba.....inason naga 'yata,inason a bani lokaci nazo na dauketa tayimin hutu,tunda nasan zuwa sati me zuwa zasu fara exam,upper kuma sun gama..

"'Stop!" Ya tsaidata a tsawace, yanajin wani abu na masa tururi tun daga zuciyarsa zuwa saman fuskarsa

"Lokaci na farko kuma na qarshe da zanyi warning dinki,ki cire a ranki cewa kin taba haihuwa da toufeeq jarma,ki cire a ranki cewa kina da 'ya a duniya tare dani,wannan shine gargadina gareki" yayi maganar yana nuna gabansa cikin wani irin fushi da deepness a cikin muryarsa

"Ta yaya? ka taba ganin an raba uwa da
'yarta?,laifin dana aikata tsakanina da ubangiji na ne,so bai shafi alaqata da dangantakata da

'yata ba,inata kawaici,inata dannewa,ina tsoro da fargabar kiranka,for what! fadeela yata ce, kuma har abada ba'a taba canzawa tuwo suna"

"Idan kin isa ki kusanceta da taqi daya tak!,kiga yadda sunanki zai sauya" ya fada cikin tsawa da matsanancin fada

"Bazan kusanceta a zahiri ba,amma zan kusanceta ta hanyar da duniya zata sake shaidawa diyata ce halak malak'

"Go ahead. karki fasa,zan nuna miki other side dina da baki taba gani ba,stupid idiot" ya fadi yana wurgar da wayaryasa hannunsa ya shafi sumar kansa da qarfi hadi da yarfar da hannunsa.

"Ka dinga yawan ambaton Allah duk sanda zuciyarka ta zafafa" daya daga cikin maganganun maji suka fado masa a ransa,sai ya koma da baya da baya ya zauna gefan sofa din,qafafunsa a qasa,ya lumshe idanunsa yana kiran

"Hasbunallahu wani'imal wakil,wala'udwana illa alazzalimin,ya hayyu ya qayyumu birahmatika astagis, aslih li sha'any kullah,fala takilni ila nafsy darfata ainin" a hankali sai numfashinsa dava fara canzawa sakamakon tuna wace ameesha da tabon da ta barwa rayuwarsa ya fara daidaita.

Duban sãahar data shirya tea din nadeeya tayi

"Don Allah anty N,taimakeni,magana mukeyi me muhimmanci da maji banason ta katse,ki migawa yaa moha din,yana ta baya idan kuma ta falonsa zaki shiga ki tambaya guards zasu saita miki" duban nadeeyan tayi,sai taji ta kasa musanta mata. Ba sau daya ba ba sau biyu ba,a kwanaki goman da yayi da dawowa tana nemanta alfarma taje su gaisa,har ta gaji ta daina,batason taji wani abu a ranta kota dauka wani abune na daban,don haka ta gyada kanta tana gyara yafen dan mayafin pakistani dress din dake kanta,wanda ya lullube asirin sumarta me tsaho cika santsi da kuma laushi,ta juya a hankali tana fita a kitchen din

"Maji tace tanaso yau ku gaisa, wana biyu bataga fuskar diyarta ba,kamar ma tace akwai maganar da zakuyi,zan rige wayar harki dawo"

"Alright" ta fada tana murmushi,haka nan itama Allah ya sanya mata gaunar matar kamar yadda take gaunarta,tana burgeta,tana da wata irin kamala da dattako sosal.

Haka nan takejin gafafunta babu nauyi sanda ta nufi gofar bayan da zata sadata da farfajiyar da yake din, taci gaba da takawa a nutsen,sassanyar iskar dake gurin tana kada turaren iikinta zuwa kowanne sashe na wajen.

Kafin ta garaso ta hangi mutum zaune saman bagar sofa din da aka yiwa farar shimfida,saidai bata iya ganinsa fuskarsa saboda yayi qasa da kansa. Tana sake kusanto gurin tana kasa sarrafa idanunta daga dauke dubanta daqa kansa,cikin jikinta takejin kamar tana dosar wani mutum ne data taba saninsa ko ganinsa,a haka har ya rage saura taqi kadan ta cimmasa,ta bude bakinta da taji ya soma rawa da nufin yin sallama,dai dai lokacin da ya daga fararen manyan idanunsa da suka rune zuwa kalar jaaa.

*HUGUMA*

No comments