Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 61-62

 



Page 61


Tsaf ta gyara gurin bayan ta gama bata abincin,duk da akwai wadda ke da alhakin hakan amma bata jira ba,ta shiga toilet dinta ta wanke hannunta,ta zari towel din dake ajiye musamman saboda goge hannu tana gogewa

baaba ramatu ta shigo.

Tayi mamakin yawan abincin da taga taci

"Ke ai baki iya bayarwa ba,new nanny ta fiki iyawa" baki ta kama tana dariya "'yeee,zakici qaniyarki,yau nice ban iya bada abinci ba?,tun kina koyar yadda akecin abincin to ni nake baki don gidanku" dariya ta saki tana buga tsalle a gadon,abinda yasa sãahar murmushi kenan tana dan binta da kallo,abinda ta karanta,yarinyar nada sauqin kai,sanann irin mutanen nan ne masu son abinda zai nishadantar dasu,a yadda ta karanta gasa da minti arba'in a tarayyarsu,tana bugatar kulawa da zata dace da hankalinta.



A dakin ta barsu,ta dauki excuse don ta kintsa kanta da dakinta. Tana shiga ta zare mayafin jikinta ta ajjiye saman gado tana furzar da iska daga bakinta,yarinyar ta shiga ranta lokaci guda fiye da yadda tayi zaton zata kasance,wani abu takeji game da ita a ranta,tana jin kamar daga jininta ta fito.

Sai data gama shirya kayanta a wardrobe tsaf ta fidda komai ta ajjiyeshi a muhallinsa,bath stuff dinta ta kaisu bandaki,sannan ta zare kayan jikinta ta shiga bandaki tayi wanka. Koda ta fito cikin wata doguwar riga ta lallausar auduga ta shirya,ta

gabatar da sallah,zuwa lokacin dakin ya fara

kama qamshin turarukanta masu sanyin

qamshi.


Hijabinta ta zare ta tsaya bakin mudubi

tana taje gashinta,ta gama tana hadeshi akayi

knocking,ta qarasa a nutse ya yafa qaramin

hijab ta bude gofar.

Me dafa abincin sashence,itama sanye da

uniform dinta,saidai su nasu akwai banbancin

color dana sashen hajiya qarama dana sauran

ma'aikatan dake gidan,nasu din fari ne qal da

ratsin bagi 


"Its time for dinner maa" ta fada cikin

rusunawa


"Alright,thank you" ta fada cikin sauqin kanta da ba kasafai yake bayyana tattare da ita ba.


Ciki ta koma ta fidda slippers din da aka bata cikin wata jaka,wanda qa'ida ne na dukka ma'aikacin da zai fara aiki cikin gidan,ta sanya a qafafunta,saita kashe wayarta ta jona a charge da nufin sanda zata dawo ya cika,sai tayi kiran dukkan wanda ya kamata,don batason suyi kiranta bayan bata nan,ta maida qaramin hijabin daya sauka har kusan qugunta sannan ta fito a dakin.

Kai tsaye dakin fadeela ta koma,ta sameta sunata rigima da baaba ramatu akan kayan da zata sanya, kowa da yake gidan ya saba da wannan agenda din nasu,sosai take maidata kamar kakarta. Cikin hikima da dabara ta fidda mata wasu kayan,da lallashi ta sakata ta sanyasu,bayan tayi mata alqawarin bata zabin kayan baccin duk da takeson sakawa,sannan suka fito cin abincin ita da fadeela da baaba ramatu.

A gasa sãahar ta sauko musu dasu,sabanin yadda suka saka ci a saman table. Sãahar ta buda abincin tana gare masa kallo. Abinci ne yankunan Europe da Asia,saita ajiye murfin warmer din tana duban fuskokinsu. Ba wani karsashi a fuskar baaba ramatu,amma fadeelan har zumudin a zuba mata takeyi. Damar zubawa ta bawa baaba ramatu,ita kuma ta zubawa fadeela,sannan ta zauna ta bata da kanta kamar wancan lokacin,sai data tabbatar ta qoshi sannan ta zauna sosai,kadan ta tsakura ta ture,don ba jituwa tsakaninta da abinci, especially ma abincin dare, tafi qaunar coffee fiye da komai a rayuwarta.

Suna daki tana shirya fadeelan wadda taketa gogarin bata labarin abby dinta, magana daya biyu saita sakoshi, murmushi kawai sãahar ke binta dashi,tunda batasan komai a kai ba,kawai dai tana ji a zuciyarta cewa yarinyar ta rabauta da uba daya san darajar diyarshi,yake bata dukkan kulawa,ya kuma damu da damuwarta. Ruwa me dumi sosai tayi mata wankan dashi,ta shiryata cikin wasu kayan bacci masu taushi dai dai da shekarunta,ta sake mata gashinta yadda zatafi in dadin kwanciya.


Har wani lumshe idanu fadeela keyi,tana jin dadi sosai a jikinta


"Aunty nanny kin iya wanka wallahi" dole dariyar da saahar batayi niyya ba ta qwace mata,ta rige siraran hannuwan fadeelan


"'Wankan ma akwai wanda yafi wani dadi?" Kai ta gyada


"Sosai,na abby da naki yafi dadi, amma shi abby sai ya daina yimin, waina girma,sai randa na fadi bani da lafiya shine yakemin" ta garasa maganar cikin karyewar murya dake nuna itama tasan halin ciwon da take ciki

"Aunty nanny,abby yace wai zan warke watarana hakane?" Qwalla ce ta cika idanuwan sãahar,saita jawo ta ta zaunar da ita saman cinyoyinta 


"In sha Allah, kina addu'a?"

§ . 865 4C16

"' Ai ban iya ba" fuskarta ta dago ta shafa, komai nata siriri,saita saki murmushi

"Zan koya miki,zamu dinga sallah abby's chubby" magaleta tayi tana dariya saboda sunan ya mata dadi. Dai dai lokacin aka turo gofar dakin fadeelan.

Dukkansu suka daga kai suna duban me shigowar,mommy qarama ce,cikin wasu kayan bacci da suka zubu,tayi rolling da wani qaramin mayafi kalar kayan,ikinta sai fidda qasaitaccen qamshi yakeyi. Miqewa fadeela tayi ta isa gurinta,saita miga hannu ta ruqota suka qaraso cikin dakin

"Mummy amma abby bazai kori wannan nanny din ba ko?,ita ina sonta sosai" ta fadi tana dora kanta akan cinyar hajiya garama. Hannu ta dora saman kanta tana shafawa,idanunta akan fuskar säahar

??

"'Indai ta kiyaye doka da qa'idoji,sannan ta riqe alkinta ta kula dake yadda akace mata"

"Mommy tana kula dani sosai" tayi maganar da accent na quruciya a muryarta

"Okay,jiki wajen baaba ramatu kice ta baki kayan dana bata ajiya", fellawa tayi da gudu ta fice, saita tattaro hankalinta kan säahar.

Idanu tadan kafeta dashi,wasu lokutan takanji shakka da kokwanto akan yarinyar,tana da wani irin kwarjini da bata ganinsa saman fuskar kaf ma'ikatan gidan sai ita,sannan daga shigowarta zuwa yanzu ta fahimci kwata kwata bata rawar jikin da dukka maaikacin daya shigo gidan yakeyi,kamar zai kwanta a hanyarta tabi ta kansa,dazu data kira mrs sadeega ta gaya mata haka yanayin ta mrs sadeeqa ta gaya mata haka yanayinta yake,bata da son yawa surutu da kuma hayaniya,MISKILA CE.

??

miskilar data fadi shi yafi qara kwanta mata,saboda tasan muddin tana da wanna dabi'ar ba zata saba da kowa ba,ba kuma zata zauna tayi hira da kowa ba akan abinda ya shafi gidan ba,aikinta kawai zata yita yi babu waiwaye ba duban kowa.

Wata jaka ta ajjiye mata tana Kallonta

"Ya lafiyar fadeelan?”


"Alhamdulillah" ta amsa mata a taqaice tana kwashe cosmetics din yarinyar data bazasu a gasa


"Madallah,wadannan...

...sune magungunan


ta,zaki dinga bata da safe da rana bayan ta dawo daga school sai da dare idan zata kwanta,kamar yanzun kenan,ba'a son fashi ko daga qafa,ki kula da kyau,ba kowa ake nunawa maganinsu ba,idan ya qare ni kadai zaki gayawa,zan sake kawo wasu,a ciki akwai tablet dinta,u are educated a yadda aka bani information dinki,so koda baki taba amfani da ita ba zaki iya hada mata ita,na sanya an dora komai daya dace a kanta,so amfani kawai zata fara yi da ita" kai ta gyada kawai

"Ki kular mata da tab,na tabbata bakisan darajarta ba,abace me tsada daga kamfani me daraja ta daya a duniya" sam sãahar din batasan murmushi ya subuce mata ba sai da taga hajiya qaraman na kallonta sosal,saita buge da gyada kai

"In sha Allah " ta fada hankali kwance,cikin ranta tana mamaki,haka 'yan aiki sukeji?,haka ake dizgasu? ta godewa Allah data rayu a gidansu taga yadda ake karrama masu aiki,ta godewa Allah da bata taba sha'awar dauko me aiki a ravuwarta ta baya ba,ashe suma suna jin babu dadi idan aka fadi wani kalma na qasqanci a kansu,suma mutanene kamar kowa,a yanzun abinda yasa itan bataji wannan ciwon ba,saboda tasan daga inda ta fito, tablet zata iya cewa dai dai take da 'yartsanar wasanta,batasan nawa ta lalata ba tun kafin tayi hankali,ta yayunta da maaminta kafin ta mallaki nata kala kala.

"Muddin wani abu ya sameta zan cirene cikin albashinki" wata dariyar taso taso mata amma saita danne ta sake gyada kai. Dauke idanunta hajiya qarama tayi daga kanta,tana mamakin yadda maganar bata dameta ba,ta fada ne don ta mata ciwo,amma bata alamun wannan a tare da ita ba.

"Nawa kika yanke salary dinki,monthly ko weekly?" Hajiyan ta fada bayan ta miqe tsaye

"Wannan ba matsala bane,aikin yafi salary din muhimmanci" da sauri ta waiwayo tana dubanta,maganar taba fusgar hankalinta,sai ta dawo da baya tana tsareta da ido


"Ban gane ba,meye alaqarki da yarinya da aikin yafi miki kudin muhimmanci?,ana aiki don kudi ne haka ne?" Kai ta gyada tana lumshe ido. Ta girgiza kanta a nutse

"Ba haka nake nufi ba,shi kula da yaro lada gareshi me tarin yawa,koda ba'a biyaka a nan duniya ba,ladanka na qiyama yana jiranka,abinda ubangiji zai maka sakayya dashi,yafi kudin da za'a baka" qogarin dai daita yanayinta hajiya qaraman tayi tana jinjina kai,sai ta juya ta fice kawai ba tare da tace mata komai ba.

Da kallo ta bita har ta fice,saita dauke dubanta daga kan hanyar tana qoqarin fidda abinda zuicyarta keson suranta mata,ta jawo ledar ta buda kayan da suke ciki. Tashi tayi ta yiwa tab din gurin ajiya me kyau,sannan ta dawo ta zazzage magungunan.


Zama tayi sosai tana binsu da kallo,mamaki yana dan kamata,wasu irin tablet da babu rubutu a jikin robobinsu bare kaga bayanin da kowanne magani ke zuwa dashi. Ta jujjuya mazuban dukka plain fararen mazubi ne, abun sai ya daure mata kai,ta dinga juyasu daga gaba zuwa baya har batasan adadi ba,kanta ya daure sosai,gefe guda na zuciyarta kuma ya cika wa wasi wasi da fargaba. Motsin shigowar fadeela ya sanyata ajiye bottle din,ta daga kai tana dubanta,hannunta riqe da wata babbar sweet,cikin sakalci da salo na shagwaba ta zauna gefanta

"Uncle dina ne ya kawomin,yace gobe shima zaibi abby na,munyi waya da abby ta wayarshi, yace a barmin tab dina a bude zai dinga kirana kullum ta google meet muyi video call" cikin dauriya ta saki murmushi

"In sha Allahu" ta fada tana tattare kayan magungunan,ta maidasu cikin ledar,ta sake kadema fadeela gadonta ta saisaita sanyin ac din dakin da kuma hasken,ta rakata toilet tayi brush suka dawo tare. Sai data tabbatar tay bacci sannan ta zauna gefanta tana kallon doguwar fuskarta,abubuwa da yawa data taras a gidan suna dawo mata kanta,tun daga shigowarta gidan kawo yanzu,haka kawai jikinta yake bata akwai wani qalubale,akwai wani abu tattare da rayuwar yarinyar,ina mahaifiyarta?,don daga baaba ramatu har hajiya qarama tasan sunyi girman da ba zasu haifi kamar fadeela ba,to amma tana da mahaifi,shi din me yasa bazai zauna kusa da yarinyarshi ba? ko don babban lalurar daka iya zamewa naqasu ga rayuwar mutum?. Da wannan tunanin ta tashi daga gurin ta fita a dakin bayan ta tofeta da addu'a ta shafeta da ita,ta rufe dakin ta shige nata ba tare da tabi takan magungunan da hajiya qarama ta bata ba,haka kawai ranta da jikinta taji basu aminta data dauka ta bawa yarinyar ba. Zuwa lokacin wutar dake bada haske a hallway din ta sauya launi,alamun dake nuna lokacin baccin yayi kenan.

Sai da tayi sallar shafa'i da wutiri sannan ta zare wayarta a charge,ta zauna sosal saman gadon ta shafe jikinta da addu'o'i sannan ta kunna wayarta tana duba time. Taso shigowa da wuri ta kira kowa amma lokaci ya qwace mata sanadiyyar shigowar hajiya qarama,yanzun kam dare yayi ba zata iya kiran kowa ba a cikinsu.

Wayar na gama daidaituwa saqon

mahmud ya shigo har guda uku a jere,yau kam dai ta duba,saqon fatan alkhairi ne tare da nuna zallar kewarta da zaiyi,afifa ta gaya masa ta samu aiki amma ba'a kano ba. Ko data gama karantawar batayi reply ba ta soma kiran afifa,bugu biyu ta daga

"Nanny bestie,me ya faru da wayarki tun dazun switched off?,ko gidan basa bari a daga waya ne?" Ta garashe maganar cikin shaqiyanci da zolaya

"Ban sani ba,mu hadu a WhatsApp" daga haka ta gintse kiran,ta sani ai tunda ta zabi wannan aikin ta shiga uku gurin afifa,qilan sai tayi kamar zata zautata da tsokanarta.

[05/09, 6:07 am] +234 902 488 9500: *HUGUMA*


*_TABARMAR KASHI_*


Page 62


Bata sake tsokanar tata ba bayan sun hau online,suka gaisa saidai ta tambayeta ya vanayin alkin

"There's is something terrible a cikinsa" ta amsa mata har zucivarta tana in akwai wani abu

"'Kaman yaya?" Afifa ta tambayeta cikin fargabar kada ta sake fadawa wata cutarwar kwatankwacin na baya. A nutse ta gaya mata komai,ba jimawa voicenote me yawa. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama saurara,dukka maganganun afifa akan hanya suke,kuma taji dadin yadda ta qwarara mata gwiwa


"But afifa how she can survive without medication?"


"Yes,her illness needs treatment,idan ba haka ba abun zaiyita worsening ne,so that zanyi prescribing miki wasu magunguna,su zata dinga sha zasu taimaka mata in sha Allah,but kafin sannan ki samo history na ciwon nata,yanayin yadda yake mata idan ya tashi da kuma asalinsa,ki ajiye wadancan,tunda babu sahihanci a cikinsu". Sosai suka tattauna da afifan,sai taji dadin shawarwarin data bata game da yadda zata kula da fadeela din,shawarwarin da afifan ta bata saita tsinci kusakurai da yawa game da yadda ake kula da yarinyar.


Basu rabu ba sai can dare,don daya ma ta kusa,ta sauka ta daura alwala ta gabatar da sallar dare kamar yadda ta saba,ta miga bugatunta wa ubangiji idanunta cike fal da hawaye. Wannan din wani sirrin rayuwarta ne da babu wanda ya sani sai afifa. Data kammala fita tayi ta dubo fadeela,ta sake gyara mata kwanciya da rufa gaba daya sannan ta jawo gofar dakin ta fice,a ranta tana jin rashin kamatar barinta ta dinga kwana ita daya alhalin tana da irin wannan lalurar,anytime zata iya far mata.


*WASHEGAR I*


Komai na gidan ta fuskanci cikin tsarin yahudanci zata iya cewa yake tafiya,safiya a garesu tamkar dare ne,don ba da wuri suke tashi ba sam,fadeela ce kawai za'a yiwa abincin tafiya makaranta,a kuma shiryata ta wuce. Kowa rayuwarsa yakeyi,saidai idan an hadu a gaisa,kowa yayi aikinsa kuma ya kama gabansa,sai idan wani aikin ya sake hadaku.


Tun bayan data shirya fadeela driver ya dauketa saita shiga dakin yrinyar,da kanta ta yiwa dakin gyara,ta fidda duk wani sharp objects da zai iya cutar da ita idan ciwonta ya tashi,ta gyara komai ta sanyashi a muhallin da koda faduwa tazo mata ba zata cutu ba

Teddy's manya tayi list cikin abubuwan da fadeelan ke bugata,tanason aje mata agurare mabanbanta ya zama ko ina dakin bai cika da wani abu me tsini ko tauri ba,tashin ciwon unexpected abu ne,tanason tayi abinda zai zame mata first aid koda ba wani a kusa da ita.

Tana tsaka da aikin me gyaran dakin ta shigo,sai kawai ta sallameta,da kanta ta shiga walking closet dinta,cike yake da kaya masu kyau da tsada na alfarma,saidai alamu sun nuna akwai kayan da ba'a sanya mata su,ko ba'a damu da saka mata su din bane oho ta gyarata fes ta sake jera komai. Bata fita a dakin ba sai garfe daya,sai sukayi clashing da baaba ramatu.


Baya ta jaye mata cikin girmamawa,fuskarta da fara'a tace


"Naji shurun yayi yawa nace bari na dubaki" murmushi tayi


"Ina ciki ina aikin gyaran dakin fadeela"

"'''ah,ina mabaruka?"


"Ni na sallameta,akwai gyaran da na yiwa dakin ne"


"To madalla,sannu da qoqari" baaba ramatu ta fada,har cikin ranta tana jin cewa yanzun fadeela ta samu nanny din da zaiyi wuya korarta,tun daga jiya zuwa yau taga tarin banbamce banbamcen da sauran masu kula da itan da tayi a baya.


Cikin sati guda kacal ta gama fahimtar

dukkan wasu tsare tsare na gidan,sannan

itama ta gama tsarawa kanta yadda zata rayu

da kowa. Cikin sati guda din nan kacal suny!

wani mugun sabo da fadeelan,yarinyar tana da

wani irin shiga rai da kuma masifaffen wayo

dake da alaqa da kaifi basirarta a makaranta.

Sannu sannu dukkan wasu ayyuka da sauran

ma'aikatan gidan kewa yarinyar,kama daga

abincinta,gyara dakinta,hada kayan wankinta

a bayar zuwa laundry room duka ta qiya

kowa yayi mata,dukka sun koma wuyan

sãahar. Wani irin girma take bata,tana jinta a

ranta ta zarta mata kowa a gidan,kafin tayi

wata guda sai ya zamana sun koma tamkar

ya da uwa,hatta da dakinta idan zata koma

sai bayan yarinyar tayi bacci,data farka ta

sauko a gadonta komai asuba zataji ana

mata knocking,indai taji wannan bugun tasan

fadeela ce,tare xasu qarasa kwanan,ayi shirin

makaranta. Ayyukan makaranta kuwa shima

ya koma aikin s?aharlesson dinta da ake mata

still dai shima taqi malamin,a nan ne fadeela

ta lura kamar akwai rauni wajen karatun

addininta,da kanta ta zauna ta tsara yadda

zata fara koya mata,duk da ason ranta yarinyar

ta shiga islamiyya,to amma batasan yadda

zata tunkari masu gidan da maganar ba.


A nata bangaren ayyukan fadeela gaba daya nishadi suka sanyata,sun debe mata kewar yara sosai,sun kuma nesantata da dukkan wani namiji kamar yadda take da muradi,tana jinta kamar a killace,babu idanun kowa a kanta,ta samu cikakkiyar nutsuwa da gamsuwa cikin gidan,hajiya qarama da takejin kamar zata zame mata matsala ko akwai wani illa tare da ita,saita fuskanci ba wani damuwa tayi da sassan ba,saita share kwanaki ma bata shigo ba,sai idan fadeela taje mata. To amma,shin da gaske fadeelan jikarta ce?,idan jikarta ce ta yaya mu'amala irin wannan zata wanzu tsakanin jika da kaaka?,tanason sanin labarinsu,tana son sanin ainihin wacece hajiya garama a wajen fadeela,to amma ita din bata cikin sahun mutanen da suke shiga lamuran da sukayi yaqinin basu shafi rayuwarsu ba.

*****K'arfe biyar da wasu yan mintuna na yammacin ranar ne,dai dai sanda madaidaiciyar motar me kyau ke shigowa cikin gidan,wanda da shigowarta da isowar masu aikin gidan duka duka bazaiyi minti biyu ba,cikin gaggawa kowanne ya iso,saboda sanin mamallakiyar motar,kowa yana gudun tsira da mutuncinsa.


Bude murfin motar tayi,sannan ta qwalawa daya daga cikinsu kira,matsowa tayi da gaggawa,bakinta dake tauna chewing gum ta motsa


"Daukarmin hand bag dita"


"Tom" ta fada tana buda daya side din da jakar take ta dauka ta riqe


"Kai jama'a,mutum ba uban kowa ba sai shegen ji da kai da izzar banza" tayi gorafi gasa qasa,saidai ya fidda sautin gunaguni

"Me kike cewa?" Labiba ta tambaya taba juyowa,murmushi tadan saki a rikice 


"Bab.....babu komai,cewa nayi maraba da dawowa" bata sake cewa komai ba ta fita a motartabar musu aikin kashewa da rufeta hadi da rigo mata key din. Cikin jin kai take takawa,sanye da wani skinny jeans da yabi jikinta sosai ya lafe, kamar a jikin nata aka dinkashi,manyan mazaunanta da suke da wani irin dan banzan tsini sun fita sosai,saidai kuma shafaffen qirjinta dake boye a t shirt din jikinta ya kawo cikas waien cikar adon da akesonyi da bayyana abinda akeson a bayyana din. Kitson attache ne a kanta daya zuba har gadon baya,ya bullo da qasan gantalelallen mayafin data yane kanta dashi wanda iyakarsa wuyanta.

Har ta doshi sassan hajiya qarama suka shaida mata ta fita, amma ba nisa tayi ba,saita sauya akalarta ta wuce sassan fadeela,tanason ta saba da yarinyar,to amma matsalar ita batasan yadda zata shawo kanta su shaqu ba.


Dai dai lokacin da sãahar ke zaune a madaidaicin falonsu na biyu,suna zaune qasan carfet ita da fadeelan, ita tana cin abinci sãahar din na monitoring dinta,a daya bangaren tana duba homeworks din da aka basu ranar a makaranta.


Sanye take da brown din chiffon gown budaddiya sosai,sai kanta data yafawa vail na plain chiffon din shima brown da bai garasa na jikin rigar haske ba, kyakkyawar fuskarta tayi fresh,tes take fatarta na nan da glowing dinta,babu digon ko tabo ballantana qurji,pink lips dinta sai shegin lips balm sukeyi,zara zara yatsunta take sanyawa tana buda book din page by page tana ganin performance din fadeelan a homeworks dinta na baya.


Sau biyu tana buda baki da niyyar yin magana tana dora mata yatsa akan lips tace


"Shshshsh" tasan tanason yin Santi ne akan abincin da takeci, wanda säahar dince yau ta dafa. A karo na uku data hanata saita langabar da kai

"Please aunty ki barni nace wani abu mana" yadda tayi maganar yayi masifar baiwa sãahar dariya,saita rufe littafin tana murmushi idanunta akan fadeela


"Say it fadee"


"Wallahi anty ban tabacin abinci me dadin wannan ba,kamar daga aljanna aka kawosa" ba shiri dariya sosai ta kubcewa saahar,saita miga hannu ta dauki pillow ta saka mata daga gefanta

"'Bari na tareki kada santi yasa ki fadi" dariya itama ta saki sukaci gaba da yi tare


"Please aunty nanny,zaki ci gaba da dafamin abinci?,harda wanda zanje school dashi don

Allah,nasan abincina sai yafi na kowa dadi" idanu ta lumshe tana gyada kai,a yadda takejin fadeela kamar jininta babu hidimar da bazata ivayi mata ba

"Alright,amma idan satin nan ya wuce baki gama haddace suratul a'alah ba,to zan daina,kin yarda?"

"'Na yarda aunty,nayi algawarin jibi zan gama" ido ta ya fidda tana dubanta da mamaki

"Really?" Kai ta jijiga mata alamun da gaske take.

"Hi fadeela" muryar labiba dake tsaye a kansu ta ratsa kunnuwansu,dukkaninsu babu wanda yasan da shigowarta bare wanzuwarta a gurin.


Daga kansu sukayi kusan lokaci guda suka

dubeta,dai dai lokacin idanunsu suka gauraya

da juna ita da sãahar.

Dan ja baya kadan tayi cikin yanayin dake

nuna qaramar razana

"Ya salam" ta furta can gasan ranta,tana

hadiye wani abu me tauri a maqoshinta,a

ina aka samo wannan cikin gidan?" Ta yiwa

kanta tambayar da batasan amsarta ba,zataso

ta jefa tambayar ga baquwar fuskar,amma

idanunta zuwa fuskarta suna fidda wani irin

kwarini.

Sãahar ce ta fara janye idanun nata daga

kanta,ranta yana dan baci da yadda ta riskesu

gatsau kai tsaye tayi musu kuma tsaye a

ka,saita maida idanunta ga duba littafin

hannun nata ba tare data sake dagowa ta

dubeta ba,saidai a jikinta tana jin kamar tasan

fuskar,kamar ta taba ganinta a wani waje.


Tana jinta ta isa gaban fadeela ta zauna

tana ta janta da surutu,lokaci lokaci idanunta

suna satar kallon sãahar,wadda bata sake

duban sashenta ba,koda ace suna da dabi ar

yahudawa,a qalla tunda musulmi ne su tay!

musu sallama sanda ta riskesu

"Na gama anty" fadeela ta fada bayan ta ajiye

gorar ruwan hannunta

"Good bari na dauko miki hijab,qur ani zamu

fara yi" saita kife littafin ta mige zuwa dakin

fadeelan. Kallo labiba ta bita dashi hankalinta yana tashi, ko ita da take mace ta tabbatar

ta kuma yaqini hakanan ta sallama wannan

din ta cika mace wani abu me cakude da

kishi da tashin hankalin wanzuwarta a gidan

yazo yayi mata tsaye,sai ta maida dubanta ga

fadeela dake qoqarin dauke plate din da taga gama cin abincin tana tattare inda ta bata da

tissue,abinda bata taba gani yarinyar tayi ba "Wacece wannan uktie?" Duban labiban kawai

tayi,da yake itama miskilar kanta ce,kafin tace

komai baaba ramatu ta shigo falon,hannunta

dauke da humidifier da tasan sãahar na

yawan ajjiyeta a gurin saboda tsananin son

qamshinta,waccan ta lalace ta sauyo musu

wata,tana respecting duk wasu buqatu na

sãahar din,don zata iya cewa tsahon zamanta

a gidan,bata taba jin dadin zama da wani

mutum a gidan ba kamarta

"'Barka da dawowa" baaba ramatu ta fadi tana

duban labiba

"Yaushe akayi baquwa a gidan nan?" Ta jefa mata tambayar ba tare data amsa marabar ta

ba

"Ba baquwa bace,kawai ita ke kula da fadeela

yanzun" a take fuskar labiban ta washe,ta saki

garamar dariya. 


"A'ah ramatu,kice nanny ce kawai,basai kin

wahalar da harshenki ba" tayi furucin dukka

a kunnen säahar data qaraso gurin hannunta

dauke da gogaggen hijabin fadeela,cikin

wadanda ta dinko mata da kudinta,saboda

tazo ta risketa bata da jiba ko daya,sai wani

fingilalle V shape na uniform dinta.

Hada idanu sukayi da labiban,sai sauran

maganar ta magale mata a magoshi,ta mige

daga zaman da tayi tana fadin

"Zan jira mommy a sassanta, fadeela enjoy

your new nanny" saita dan daafa kan

fadeelan ta soma takawa tana barin falon.

Ran baaba ramatu ba dadi ta ajjiye

humidifier din,tasan halin kowa a gidan,don

kusan kowa a gabanta yayi girmansa, ta samu

guri ta zauna lokacin da sãahar ke sanyawa

fadeela hijab din nata,daga can qasan

zuciyarta tana fassara kallon da kalaman labiba. Ta fahimci ma'anarsu fes,to amma abinda ya bata mamaki daga haduwar farko ko maganar farko babu a tsakaninsu me ya haifar da wannan matsanancin kishin cikin qwayar idanunta?

"Wannan itace labiba, kuma za'a iya cewa ita din ganwa ce ga mahaifin fadeela,wato

'yar matar babansa ce,tana da wasu halaye marasa kyau wani lokacin,sai kinyi haquri da ita" a nutse ta daga kai ta kalli baaba ramatu,saita saki kyakkyawar murmushin nan nata da ba kasafai take yinsa ba,ta taka tana debo litattafansu

"Karki damu baaba ramatu,haquri da ita bai zama dole ba,tunda bani da case da ita" jinjina kai baaba ramatu tayi,tasan sarai tana da kawaici da kuma sanyin hali,hakanan bata da kwaramniya ko hayaniya,amma labiban fa?,tayi imanin koda bata shiga gonarta ba ita zata shiga tata,saidai fatan Allah ya kiyaye.

[05/09, 6:07 am] +234 902 488 9500: *HUGUMA*


*_TABARMAR KASHI_**

No comments