Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 5-6

 


LAST FREE PAGE 

PAGE 05




"Ban sani ba anty,nazo na sameshi ne a tsaye yana kallon motar,Tayi disappointing nashi sosai wallahi anty,ni kaina i was so shock da naganshi tsaye a wajen,nasan halinta,may be banza tayi dashi,ko kuma ta gaggaya masa maganganu marasa dadi" shuru farheen tayi tana juya kai cike da jimami,mahmud was so familiar,kusan sananne ne shi da mahaifinsa,matashin dake da arziqi da kuma nasaba cikakkiya,dan asalin garinta ne wato borno,wanda tayi imanin babu a inda bazai nema aure ko ya nemi mace a dauka a bashi ba da gudun gaske


"He really broke her heart........yayi mata illa da yawa,that's why ta kasa bari ta warke har yau" farheen ta fada tana sake ci gaba da juya kanta,kallonta afifa keyi itama tana hadiye wani abu me daci,ko zancansa ta tsani ayi itakam,batason tuna komai daya wuce a baya,tana jin kamar ba zata iya yafewa ba tabar komai kamar yadda abba yayi umarni ba


"Amma dolen dole......she need to move on,bazai yiwu ta rayu har abada a haka ba"


"Haka nake gayawa kaina kullum,nidai na riga na bashi phone number dinta,saidai ta hadiyi zuciya bayan yayi kiranta idan taso" qaramin murmushi ya subucewa farheen


"Babu wannan zancan,zamu ci gaba da lallabata ne tayi accepting koma meye zaizo mata,inajin yau da ita zamu wuce gida ma"


"Hakan yayi anty,nima dama yau zoo road zan wuce".


            Tana rungume da aleena tayi sallama da muryarta me cike da wani irin sanyi da maganadisun dake fusgar hankali,dukkansu mutum biyun dake falon suka waiwayo suna amsa mata sallamar cikin bata attention dinsu,fuskokinsu suka wadata da murmushi,farin dattijon dake zaune cikin sofa qafafunsa miqe,daga gefansa takardu ne masu yawa da kuma wani kyakkyawan biro a hannunsa,da alama yana signing ne,sai matashi me jini a jika me surkin kala wanda ya kwashe kamannin dattijon tsaf!,nutsuwa da cikar kamala ta lullube fuskar nan dake cike da danyan jini da jin shekaru da yake ganiyar yi.


"Abba......barka da warhaka" ta fada tana rusunawa a gabansa,ya saki murmushi yana ajjiye takardun hannunsa ya miqa mata hannun nasa yana cewa


"Bani amaryar nan tawa da batayi dani" wani dan qaramin murmushi daya fidda ainihin kyanta ta saki,ta matsa tana miqa masa aleena din,ya karbeta yana tsokanarta,saita maida kanta ga dan uwanta ta zauna sosai tana tanqwashe qafafunta


"Yaaya barka da yamma" hararar wasa yadan watsa mata bayan yadan dauke kansa daga takardun kadan


"Yamma ko dare,tunda na shigo nake nemanki da kyakkyawan albishir amma baku tashi shigowa ba sai yanzu,nima komawa zanyi da albishir dina" yanayin yadda yake magana da ita kadai ya isa ya gaya maka zallar shaquwa da kulawa da suke bata,yadda ita dinma take ganin girmansu da basu dukkan wani respect daya dace. Kai ta langabar gefe guda


"Haba yaaya,kada muyi haka don Allah,ban taba abu naji na matsu na samu feedback ba Allah sai wannan abun"


"Naqi nima" ya fada yana buda shafukan gaba da na takardun hannunsa. Idanunta ta maida ga abbansu dake zaune yana jinsu ba tare da yace komai ba


"Abba ka saka baki don Allah" murmushi ya saki,yana sauke qafafunsa dake harde a dazun waje daya yada gyara zamansa,yatsunsa na riqe da yatsun aleena daketa bangala masa dariya


"Kayi haquri mana yaaya qarami a gaya mata ko?,nima na matsu na tayata ji" kansa ya daga daga takardun yana rufesu fuskarsa da murmushi,ya ajjiyesu gefansa sannan ya dubeta kai tsaye


"Shikenan tunda abba yasa baki,zan gaya miki amma bisa sharadin kome na buqata zakiyimin?" Ya furta yana murmushi qasa qasa hadi da dan juya kansa,alamun deal ne idan har ta amince din.


              Ba tare data kawo komai a ranta ba,don ta dokanta taji feedback din ta gyada kai,lallausan murmushin nan nata yana fita a fuskarta


"We made it!" Ya fada with full excitement idonsa a kanta,don sosai ta sakashi jin alfahari da ita,musamman lokacin da  yake gaban alhj ahmad girema yake lissafa masa benefits da za'a iya samu a tattare da ita. Manyan idanunta a yaunta fiddo waje cikin jin mamaki da kuma farincikin da taji yana ratsata,yanayin data jima bata ji irinsa ba,sai tasa zara zaran yatsunta tana rufe fuskarta,qaramin kyakkyawan bakinta yana furta 


"Alhamdulillah" can qasa,cikin zuciyarta tana jin dadi data zama solution na problem din dan uwanta,a rayuwa tana qaunar taga ta zama silar warwarewar matsalar wani,yana daya daga cikin abubuwan dake faranta mata rai a duniyarta,bayan son yara da Allah ya jarabceta dashi


"Thank you sãahar...... thank you ummin abba(sunan da suke kiranta kenan sometimes,saboda taci sunan mahaifiyar mahaifinsu wato kakarsu kenan KHADEEJA)"


"Don't mention it yaaya" ta fada tana girgiza kai, murmushi har yanzu bai bar fuskarta ba,sai dukka hakan ya sanyaya musu rai,don sun jima basuga hakan ba tattare da ita,lallai abun ya sanya farinciki me yawa a zuciyarta


"Yauwa......saura deal dinmu kuma" ya fada yana tanqwashe qafafunsa


"Eheennn" ta fada tana gyada kai


"Yadda kika tsara komai muka bi kuma aka kai ga cimma gaci,wannan ya burge alhaji sosai,ya sanya masa interest akanki,ya nema alfarma a wajena ta ki karba aiki a company dinsa dake shirin durqushewa a yanzu yake fafutukar tayar dashi,zaki tsaya tare da yaronsa kuyi aiki tare alfarma ce ya roqeni,nayi rushing wajen accepting,saboda girma da kimarsa,na kuma san cewa bani da matsala ta wajenki" ya qarashe maganar yana ritsata da idanu.


              Kaf! Ya gama daureta da dukka wata jijiya dake jikinta,ya salam ya alhadi,me yasa yaya muhyi zaiyi mata haka?,yafi kowa saninta ciki da bai,yasan a yanzun bata da wani sauran buri,bata buqatar aiki ko kadan,infact fita ma waje tun bayan kammala karatunta bata dameta ba,tana ma daya daga cikin abubuwan data sanyasu a jerin ababen takura a wajenta,wannan ya sanya ma hatta da key din motarta ta dade da bada ajiyarsa,ta yaya zata iya fita kullum da sunan aiki?,ta kuma tunkari wata matsala,matsalarma ta company?.


             Yadda ta gaza cewa komai haka falon yayi Shuru,hakanan kuma daga abba har yaa muhyi basu janye idanuwansu daga kanta ba,abinda ya sake mata nauyi kenan,ta kasa motsawa bare ta amsa.


"Mama na" muryar abbanta ta yanke shirun dake wanzuwa a falon,ta daga kai a hankali


"Na'am abba"


"An baki dama kije kiyi tunani"


"To abba,na gode" ta fada har ranta tana jin dadi, atleast ta kubuta daga titsiyen da yaa muhyi yakeson yi mata


"Karki manta da istikhara" abba ya fada sanda take dab da fita a falon,kai ta jinjina


"In sha Allah" tanajin a ranta ta yaya zata sakeyin sake?,ta yaya zata manta da istikhara?, bayan taga illar hakan?,har abada ba zata sake yankewa kanta hukunci kai tsaye ba,bata fatan ruwan daya shanyeta a baya a yanzun ya sake mamayarta.


              Sanda ta isko falon tuni afifa ta gama cin nata takeaway din,hira ma sukeyi da farheen,dukansu suka bita da kallo,yanayinta ya sauya ba kamar yadda tabar wajen ba a dazun,saidai ba wanda yace komai da ita,ta dora aleena saman cinyar farheen ta zauna itama,dai dai sanda baaba rabi ta fito


"Tunda kuka shigo nake cigiyarki,akace kin shiga wajen alhaji" ta fada cikin fara'a da nuna kulawa,hannu tasa ta zame veil din kanta baya tana lumshe ido,cikin jikinta tana jin wata gajiya da weakness yana ratsata,wanda tasan bata komai bace ta zancan yaa muhyi ne,sumarta me santsi dake gaban goshinta ta fito sosai


"Zan samu coffee?" Kai ta jinjina da sauri


"Ai bana zama babu shi saboda ke" daga haka ta juya cikin kitchen din a gaggauce.


          Bata ce da kowa komai ba,sai suma basu tambayeta ba,tana da zurfin ciki sãahar din sosai,ba komai take iya bayaninsa kota fadi ba


"Ki rakani gida mana kiyimin weekend din nan a can?" Farheen ta fada tana duban sãahar,saita bude idanunta tana kallon farheen,cikin zuciyarta tana jin ta gamsu ta bita din,to amma kuma kamar ta kusanta kanta ne da yaa muhyi da take fatan a kwanakin da abba yace taje tayi tunani daga nan har abada zancan da yazo mata dashi yabi ruwa,bata da wani interest akan aikin ko kadan,amma kuma qin amincewarta tamkar ta damtsi qasa ta watsawa idanun yaa muhyi din


"Zaki din?,khalipha nata kewarki" ta fada cikin kwnatar da murya,khalipha shine makami daya da zatayi amfani dashi ta amintar da ita ta bita gidan,Allah ya jarabceta da son yara matuqa da gaske.


           Sai da baaba rabi ta kawo mata coffee din taji tana cewa ta hada mata kayanta kala biyu sannan ta fahimci ta aminta zata din


"Miskili kafi mahaukaci ban haushi" anty farheen ta fada a ranta tana murmushi,a hakanma ita daya ke iyawa da sãahar,tana da dadin zama idan ka karanceta,idan ba haka ba kuma ba zaka taba jin dadin zama da ita ba,infact ma ba zaka taba fahimtar tata ba.


         Tana rungume da aleena a seat din baya,yaa muhyi da anty farheen na gaba suna hirarsu,komai suke tattaunawa tana jinsu amma bata sanya musu baki ba,ta dade tana kwatanta cewa inama ace dukkan maza nagartattu ne kamar yayun nata,lallai inda addini ya halasta aure tsakanin dan uwa da dan uwa,ta tabbatar cewa bata da sauran matsala a rayuwarta.


             Tafiyar da bata wuce minti talatin da biyar ba suka isa unguwar,ya muhyi dake tuqi a nutse ya saka signal,ya shiga layin da ya shiga hannun damansa a hankali. A qofar wani qawataccen gida dake dauke da manyan katangu ya tsaya,a ido kawai idan ka kalleshi zaka san cewa akwai sukunin rayuwa me yawa tattare da me gidan. Ya danna hon,cikin sakannin da basu wuce biyar ba aka wangale masa qofar,daya daga cikin masu tsaron qofar gidan mutum biyu ya rusuna cikin girmamawa har zuwa sanda motar ta sulala ta shige ciki kai tsaye zuwa yalwataccen parking lot na gidan.


              Ko kafin yakai ga tsaida motar su fita masu aikin farheen su biyu sun iso,daya nanny dinsu khalipha ce daya kuma tana kula da tsaftace sashen farheen,don sam bata yarda koda wasa me aiki ta karbi wani abu da ya shafi hidimar mai gidanta ba komai qanqantarta.


             Cikin girmamawa suke yiwa sãahar barka da zuwa,don dukkaninsu bawai baquwar su bace,kai tsaye ma za'a kirata da 'yar gida,saboda zaman shekaru kusan biyu da tayi dasu,har yanzu kuma bata rufa wata biyu bata zo tayi kwana daya ko biyu ba,daki ne da ita na musamman a gidan.


            Baraka ta miqa hannu zata karba aleena sãahar ta hanata,tadai barta da hand bag da kuma qaramar luggage dinta ta wuce ciki rungume da yarinyar dake lafe a qirjinta,don tuni tayi bacci. Bata sauketa ko ina ba sai data dangana da ita har gadonta dake dakin farheen,ta fito Parlor ta samu farheen din na gayawa baraka ta tsaftace dakin da sãahar din zata sauka,duk da fes yake,sannan kuma lubabatu ta tambayi abinda sãahar din zataci a dora mata. Kai sãahar ta girgiza,cikin lallausar muryar ta take fadin


"don't mind,I can take care of myself"


"Really?,kinsan dole a kula da amanar auta" farheen ta fada cikin sigar tsokana kamar yadda ta saba takan zolayeta haka time to time. Dole wani murmushin ya sake kubcewa sãahar,ta motsa bakinta kadan,farheen na daya daga cikin mutane masu matuqar muhimmanci a rayuwarta,ba zata iya fadin adadin yadda taji dadin zama da ita ba a shekarun baya,har yanzun kuma tana jin dadin kasancewa da ita,shi yasa duk duniya ba inda take iya tafiya ta kwana idan na nan gidan ba.


        Cikin qanqanin lokaci baraka ta gama kintsa dakin ta kuma shirya mata kayanta, bath set dinta ta fitar,ta zare kayan jikinya ta daura babban lallausan farin towel,ta zare farin ribbom din kanta,yalwataccen gashinta mai tsaho da sulbi ya baje saman lallausar farar fatar jikinta,hakan ya qarawa fuskarta wani kyau da haiba,tamkar ire iren jaruman indai mata,kai tsaye ta dauki kayan wankanta tana takawa a nutsenta zuwa toilet,ta hada ruwan wanka me dumi sosai ta shige,tayi wanka sosai da ruwan ya ratsata, idanunta a lumshe cikin shower din tana qoqarin tattara dukka wasu qananun damuwoyi da taci karo dasu a wunin yau tana watsar dasu daya bayan daya,so takeyi yau din tayi bacci me kyau ta kuma huta sosai,daga qarshe ta dauraye jikinta dake faman fidda qamshin shower gel dinta mai matuqar kyau da tsada,ta nade fatarta daketa sulbi cikin towel ta fito bayan ta sanya pad,kasancewar tana fashin sallah ne.


              

FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[04/08, 4:21 pm] +234 907 013 9442: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

             Page 06


*Arewabooks:huguma*

https://arewabooks.com/u/huguma



Sai data fara busar da kanta da ya jiqe,sannan ta shirya cikin wasu cotton kayan bacci masu tsananin taushi,riga da wandon da bai sauka har qasa ba,kadan ya rage yakai idon sahu,ta mulke kanta da turaren gashi kamar yadda ta saba ya zame mata al'ada,hakanan ta shafe jikinta da nau'ikan turarukan da sai zatayi bacci take using nasu.


            Cikin sofa bed ta kalmashe qafafunta bayan ta rage haske dakin,ta ja wayarta ta kunna data,tanason shiga media ta karanta news ko zata rage tsahon daren sai taji ana knocking,ta daga manyan idanunta da suka rusuna zuwa lokacin ta kallo qofar sannan ta bada izinin shigowar. Baraka ce,cikin girmamawa ta isar mata da saqon farheen na ta fito taci abinci,kai ta girgiza


"Am okay,kice mata saida safe ma hadu" kai ta jinjina sannan ta juya zata fice


"Ammm,amma idan zan samu black tea ko coffee ina so"


"Babu amma yanzu yanzu saina hada miki"


"Na gode" ta fada a tausashe,baraka ta juya ta fita tana ja mata qofar.


             Tana shirin buda wayar saiga kira ya shigo mata,tsaiwa tayi cak tana kallon numbers din dake faman harbawa saman screen din wayar,baquwar number ce don babu ita cikin kaf 'yan tsirarun contact da ta adana cikin wayarta. Ba kowacce number take saving ba,sai number dake da matuqar muhimmanci da amfani a tattare da ita. Wannan yasa taqi daga kiran,har ta gama ruri ta katse,saita sake kunna data din ta shiga abinda tayi niyyar yi tun farko.


             Ba'a dauki dogon lokaci ba kiran ya sake shigo mata,taja qaramin tsaki tana jin kamar tayi rejecting,amma saita fasa,taci gaba da kallon yadda wayar ke neman a kawo mata agaji,harta gaji da ?urari ta sake yankewa,katsewarta da minti daya kacal saqo ya shigo


_"please......do me a favor,ki daga kirana koda na second biyar ne,zan gode da hakan,mahmud abba gana"_


          Wani dogon tsaki ta saki kamar zata cire halshenta,wani abu mai tauri yazo ya tsaya mata a wuya,ta lumshe ido tare da danne makashin wayarta yana kasheta gaba daya qirjinta na wani irin dokawa,kenan afifa ta raba number wayarta?,me yasa afifa zatayi mata haka,ta rufe ido kamar batasan komai ba......kamar komai bai faru ba?". Ita daya cikin dakin amma bacin rai ya cikata,haka ta dinga hararar wayar dake ajjiye a gefe kamar itace mahmud din,cikin ranta tana qiyasta gamuwarta da afifa,a haka farheen dake cikin shigar wasu lafiyayyun kayan bacci masu matuqar kyau da daukan hankali ta turo qofar ta shigo dakin, hannunta dauke da coffe din sãahar.


           Da kallo sãahar din tadan bi farheen,zamanta da ita ta koyi abubuwa masu tarin yawa,ta kuma gane ashe a baya ita din amsa sunan mace kawai takeyi ba tare da tasan ma'anar hakan ba,sai data zauna da farheen din na tsahon shekaru biyu da Wani abun,taci gaba da kallonta cikin rai da zuciyarta tana jin inama itace farheen din,bata da wata damuwa kaf rayuwarta,Allah ya bata miji irin yaa muhyi dinta,ya kuma azurtata da zuri'a yara lafiyayyu har guda biyu,gidanta tamkar ita ta zabawa kanta shi,duk ko me takeso tana samu,inda itace ita me zata nema kuwa a duniya?.


"Gayamin ta yaya zakiyi kumari,kin kama black tea da coffee kin riqesu tsam" farheen ta fada tana dire cup din saman bedside,idanunta akan fuskar sãahar tana qoqarin karantar yanayinta da take shinshinar kamar ya sauya.


        Karamin murmushin da yafi kama da yaqe ta dan saki


"Bana jin yunwa,bazan iya cin abinci kuma banajin yunwa ba" kallonta farheen tayi tayi murmushi

"Koda bakiji yunwa ba ki kamanta ci koda babu yawa" lumshe ido kawai tayi ta gyada mata kai


"Ba wani abu da kike buqata ko?" Kai ta sake gyadawa tana qoqarin zama sosai saman sofa bed din


"To sai da safe"


"Khalipha fa?" Waiwaya kadan farheen tayi


"Kina buqatar dan tayin kwana ne?" Kai ta gyada


"Kin manta ne tare muke kwana dama duk sanda nazo?" 


"Haka ne,zan sa baraka ta kawo miki shi,saida safe"


"Allah ya kaimu" ta amsa tana miqa hannu ta jawo mug din tana kaiwa bakinta.


           Ba jimawa baraka ta shigo da khalipha wanda keta faman barci,an shirya shi cikin kayan bacci da alama ya jima dayin baccin,ta kwantar mata dashi saman gadon taja mata qofar. Ko rabin coffe din bata sha ba taji ya isheta,ta maidashi saman qaramin plate din tangaran din da farheen ta hado mata dashi,ta miqe a nutse ta shiga toilet tayi brush sannan ta dawo ta rage hasken fitilun dakin,ta hanye gado tana lullubesu da bargo ita da khalipha bayan taja yaron cikin jikinta tana jin tamkar ita ta haifeshi.


           Ajiyar zuciya ta saki mai nauyi sanda ta lissafa shekarun yaron,yazo dai dai da shekarun faruwar wani abu daya sameta a baya,ta gyarawa yaron kwanciyar cikin jikinta,tana iya jinsa sanda yake sauke ajiyar zuciya,sai wasu hawaye masu dumi suka ratso ta idanunta,ta sanya tafin hannunta da sauri tana gogesu,qasa qasa bakinta na furta


"Aamantu billah, Alhamdulillah ala kulli haal" ta qarashe maganar ne tare da rintse idanuwanta hadi da tilastawa zuciyarta kauda dukka wani abu da zai kawowa mata hutu da nutsuwa cikin sassanyan daren da wata iska me dadi wadda ke dauke da hadari take kadawa. Sai Allah ya taimaketa bata jima a duniyar tunani tana bulayi ba bacci yayi nasarar daukarta yayi awon gaba da ita.


           Washegari tun bayan sallar asuba bata koma ba,wannan din kusan dabi'arta ce,tana zama ne saman abun sallah har sai alfijir ya keto gari ya danyi haske. Ko yau dinma tana zaune,tana dab da kammala addu'o'in ta khalipha dake barci farka,ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana murza idanunsa,a nutse ta waiwaya tana kallonsa,suka dan zubawa juna ido na wasu sakanni,sai ya sauko daga saman gadon da sauri,ta bude masa hannayenta ya fado ciki ta maida ta rungumeshi tsam tana sakin murmushi


"Kaji dadin ganina?" Ta tambayeshi har cikin ranta zuciyarta na mata sanyi,sanyin daya hadu dana hasken azkar din data gama yi,ya kuma gauraya da iskar safiya me dadi dake kai kawo tana kutsowa harta windows din dakin bayan ta samu nasarar daga labulen dake maqale a jiki kadan kadan. Kai ya jinjina yana dariya


"Na cewa daddy dama ya kaini,yace sai weekends,i missed you small mom" kyakkyawan murmushi ya qwace mata,tasa hannu taja kumatunsa


"I missed you too my little dad". Tun daga lokacin bai barta ta huta ba,akwai sabo sosai tsakaninta da khalipha din,wanna yasa yake sakewa sosai da ita fiye da momynsa farheen,yayita mata hira da tabara ita kuma tana biye masa. Allah ya halicci zuciyarta da matuqar soyayyar yara da kuma qaunarsu,duk inda taga yaro hankalinta yana kai,haka tayita hidima dashi,tayi masa wanka itama tayi,ta kintsa dakin da kanta ba tare data jira su baraka ba,taja hannunsa suka wuce kitchen abinda ta jima batayi ba,tana tambayarsa me yakeson ci,ya gaya mata ta soma fiddo kayan da zata hada breakfast din dashi.


          Mamaki ya kama lubabatu sanda ta samesu a kitchen


"Da kinyi magana saina taso na hada miki abinda kike da buqata,yau din hutun qarshen mako ne,nasan masu gidan basa tashi da wuri,shi yasa banyi safkon fitowa ba" 


"Karki damu" ta amsata a taqaice,saita miqa mata abinda zata tayata dashi taci gaba da hidimar hada break din tana sauraren khalifa. Ita kanta a jikinta yau dadi takeji,ko ba komai tadan motsa jikinta,don ta jima batayi girki ba,duk da yana daya daga cikin hobbies dinta,amma wani dalili mai nauyi ya kasheshi murus daga ruhinta.


         Awa biyu ta gama komai ta zubawa khalipha komai a plate daya,yanata murna yau an hada mishi delicious,yaqi yarda ko lubabatu ta dauka masa plate din takai masa Parlor. Sãhaar na murmushin wauta da dadin quruciya irin na yaro ta sakashi a gaba suka fito.


            Suna fitowar sukayi kacibus da farheen,a shirye tsaf tana zuba qamshi,hannunta dauke da aleena da tayi mata kwalliya da wata designer overall kusan shigarta ta ko yaushe kenan


"To bismillahi,shi yasa yau banji ifce ifcensa a parlor ba,ashe an tafi inda akafi kauri" farheen ta fada tana kallon khalipha,wanda tuni shi ya samu guri yayi zaman dirshan abinsa. Sãahar dake kallon khalipha tana sha'awar rayuwarsa,bashi da wata matsala ko damuwa,abinci kam zaici duk wanda aka bashi a sanda kuma yaso,baisan ma mommyn nasa nayi ba,ta maida idonta ga aleena daketa bangala mata dariya tana kuma dago mata hannu alamun tanason ta dauketa ne


"Beauty na baxan daukeki na bata wannan kwalliyar ba,banyi wanka ba"


"A hakan?" Farheen ta fada


"muna tashi kitchen muka shiga,bari na watsa ruwa nazo muyi hira" sãahar din ta fada tana juyawa da dan hanzari


"Dubiya ma zaki rakani,kada ki jima,so nake muje mu dawo daddyn khalipha yacemin da azahar zayaje daurin aure".


          Batason zuwa yau ko ina saboda jiya ta fita,to amma dubiya ce tasan daga asibitin ba wani gurin zasu wuce ba. Minti kusan talatin ta kwashe a toilet din sannan ta fito,ta tsane jikinta ta fara mulke fatarta da lotion.


            Cikin qasa da minti talatin ta shirya cikin vintage bubu gown ta chiffon material,ta yane kanta da dan siririn veil din da yazo hade da rigar tayi rolling dashi, kyakkyawar fuskarta ta fita ta tsakiyar mayafin,siririn agogon casio ta daurawa tsintsiyar hannunta wanda yazo ne tare da qaramar barimar data sawa kunnuwanta,don ba kasafai takeson kaya masu damu ko nauyi ba,saidai idan ya zamana ba yadda zatayi. Bata dauki komai ba banda wayarta data riqe a hannunta bayan ta feshe jikinta da turarukanta na dindindin guda biyu masu tsananin sanyin qamshi da jimawa a waje basu bar gurin ba,ta zura takalmanta masu matsakaicin tudu Golden goose brand ta fita a dakin.

 

           A tsaye ta samu farheen tana serving yaa muhyi dake sanye da jallabiyya,da alama tashinsa a barci kenan yunwa ta fiddo shi,don ba kasafai yake cin abincin a sassan ba. 


            Tana juya masa tea ta dago ta kalli sãahar


"Tabarakar rahman" farheen ta fada tana murmushi,saboda har ga Allah ta gaza jurewa kyan da sãahar din tayi,cikin ranta da zuciyarta ta cika da fatan ubangiji ya shiga lamarinta. Daga kai yaa muhyi yayi ya kalli farheen din


"Me ya faru?"


"Bakaga auta ba?" Idanunsa ya maida ga sãahar sannan ya dawo dasu kan farheen bayan ya karbi tea din daga hannunta,shi kansa kowacce rana sallolinsa biyar tana cikin addu'o'in sa,ajjiye mace kamar sãahar din a gida abune da bazaiyiwu ba,duk kuwa girman jarrabawar data fuskanta,gidan aure shine solution.


             Cikin girmamawa ta qaraso ta gaida yaa muhyi din,cikin ranta tana addu'ar Allah ya kauda hankalinsa,kada ya sake tayar mata da dukka wata magana data shafi aikin company din nan,saidai addu'artata bata ci ba,suna gama gaisawa ya jeho maganar


"Kiran wayar professor ne ya tasheni......yanamin tuni game da batunki" shuru ne ya ratsa saboda ta rasa amsar bashi,shi kuma kamar bai kula ba ya dora


"Kiyi qoqarin hada amsarki nan kusa,don kusan nashi shirin ya kammala,cikin satin nan ko sati na gaba zaku kama aikinku" 


"To,in sha Allah" ta amsa masa a sanyaye,gabanta yana dan faduwa,zasu kama aiki ko ita dawa dawa?,ta tabbatar harka ce data shafi mu'amala da maza,magana ake ta company wanda bazaiyiwu ace mata bane zallah.


           Wannan maganar ita ta sake sanyata ta zama so silent sanda suke hanyar asibiti ita da farheen,duk da cewa ita ke driving,amma yadda ta bawa kwalta dukka hankalinta ya isa ka fahimci tana wani nazari ne da daban.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[04/08, 4:21 pm] +234 907 013 9442: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??


_Arewabooks:Huguma_

https://arewabooks.com/u/huguma


No comments