Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 45-46

 


Page 45




           Kafafunta ne taji sunyi wani irin sanyi suna kamar zasu lanqwashe da kansu kai kace narkakkiyar roba ce,sai ta zame ta zauna sosai a qasa,ta ajjiye kudaden da suka kasance dollars masu tarin yawa bandir bandir gefe guda,ta zube takardun da kyau,ta soma dauka tana dubawa.


              Wani irin gumi ne ya fara yanko mata,tun daga tsakiyar kanta zuwa tafin qafafunta,kowacce takarda da original copy dinta,da kuma wadda aka sauya a manne da 'yar uwarta,indai idanunta dai dai suke gane mata......takardun dukka filayenta da sauran kadarorinta ne dake wajensa aka sauyasu da wasu sunaye na wasu mutane da batasansu ba,affidavit na court dake bada tabbacin sunayen da kuma mallakar dake jikin takardun na asali,takardun withdrawal da akayi daga joint account dinsu,statement of account gaba daya,dama rufe account din da akayi kwata kwata.


                   Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana,komai ya canza,ya tashi daga mallakinta zuwa mallakar ADAM ADAM,FAINUSA ADAM da kuma WARISHA KHADIRI,mutanen da batasan su waye ba banda sunan adam din dake maqale a jikin sunan kowannensu.


               Kamar wadda aka tsinkawa jijiyar hannu ta zaro takardar gaba, certificate of birth ne me dauke da sunayen dake a sama,FAINUSA ADAM da ADAM ADAM,kanta ya sake kullewa da kyau,wani irin tashin hankali ya dira a tsakiyar zuciya dama kwanyarta tunanin da ya darsu a ranta ya sanyata ci gaba da birkita takardun gabanta cikin hanzari,caraf hannunta ya sauka akan takardar shaidar zama ma'aurata ADAM/WARISHA.


                 Sosai hannuwanta suka fara rawa,da gaske ne ashe?, abinda raihanatu ta gaya mata da gaske ne?,adam yana da wata matar bayan ita?,da gaske ne adam ya shirya cin amanarta?,indai waccan matarsa ce su kuma yaran fa na waye?, tambayar data sanyata surar passport din data gani guda hudu a gabanta,wanda budeshi ya zame mata tamkar madubi ko amsa na dukka tambayoyin dake karakaina a tsakiyar kwanyarta zuwa zuciyarta,suna barazanar fasa mata tunani.


                  Fes kamannin yaran suka bayyana kansu da kansu,adam sak!,kamar yayi kaki ya ajjiye,ko kamar karan da aka samu gwanin iya rabo ya tsagashi gida biyu.


                 Dif komai ya tsaya mata,ta dinga jujjuya korayen fasfunan da suka kasance baqaqe wuluk a idanunta,fasfunan dake dauke da visa ta qasar england,visa din da zata basu damar zama a qasar na shekaru ?ai ?ai har shekaru biyar cif!. Da qyar ta qwaci kanta ta fusgi harshenta ta kawowa kanta da kanta dauki ta hanyar furta

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, la'ilaha illa anta subhanaka inji kuntu minazzalimin" ta fara maimaitawa wasu hawaye masu zafi suna malala daga idanun nata.


                Qoqarin hanawa kanta tashin hankalin kanta takeyi da gasken gaske,saboda yadda taji mararta tana qullewa,bata shirya asarar abinda yake cikinta ba,don haka tayita kokawa da numfashinta tana jansa tare da fitar dashi da sunan Allah,wata 'yar qaramar nutsuwa ta sauko mata,saidai zuciyarta na mata wani irin ciwo da zafi tana jin inda za'a dubata a yanzu qila a tarar ta kumbura.


            Miqewa tayi jiri yana dibarta ta wuce toilet dinsa,ta tsaya gaban sink ta kunna famfo ta daura alwala tana fatan tiririn yaji da zafin dake fita a fuskarta ya tsagaita,ta kusa kashe minti goma tana daura alwalar tana kuma maimaitawa,ita kadai tasan dimuwa da razanar da zuciyarta take ciki,daga bisani tilas ta daure famfon ta fito zuwa bedroom din.


              Gefe guda ta zauna,ta zubawa takardun da kudaden da fiye da rabinsu haqqinta ne ido,shi yasa ta daina jin alert?,ya zare duk wani kudi data nema da guminta?,ya yiwa matarsa da yaransa wadanda batasan da zamansu ba visa na barin qasar?,ya dauke duk wata dukiya tata ya maidata mallakinsa?,ya hanata haihuwa,ya hanata morar komai nata,ya yaudareta yaudara mafi muni,ya shiga rayuwarta a lokacin da taqi baiwa kowanne namiji fuska,yayi amfani da iya kalamansa, kyakkyawar mu'amala da kulawa mai matuqar nauyi da zurfi,irin kulawar da komai taurin kai da kafiyarki dole ki amshi soyayyar mutum,ya hada da wayo da dabara irin wanda itadin qarancin shekarunta basukai kansu ba,ya cusa mata soyayyarsa ya mallaketa yake kuma neman sanyata cikin musiba mara misali,me ta yiwa adam haka na cutarwa tsahon rayuwarsu da zaiyi mata wannan mummunar sakayyar?.


           Ji tayi kamar zuciyarta tana narkewa,kukanta yanason fitowa fili ta yishi sosai,amma zuciyartata tana tunasar da ita


"Lokacine daya kamata ace kinyi abinda ya dace,ba lokacin kuka bane yanzu" maganar data fito daga can qarqashin zuciyarta kenan,ta kuma zaburar da ita,ta barota daga inda take zaunen,ta dawo ta tattara takardun da kudin,passport din da komai da komai yadda suke a tsare a jakar,bayan ta gama ta zuge jakar,ta daukota ta fita daga dakin,bayan taja kowacce qofa ta maidata yadda take,tamkar ma bata shiga dakin ba.


              Doguwar riga me sulbi ta zura saman kayan jikinta,ta yane kanta da mayafin rigar,bayan ta shafa fuskarta da hoda ta zizara kwalli daya qarawa idanunta haske,duk da yawan kukan da tasha,sannan ta wuce zuwa farfajiyar gidan,ta bude motarta ta jefa jakar a ciki,ta tashi motar ta fice a gidan da gudun tsiya.


          Kai tsaye gidansu ta nufa,tanason ta yiwa jakar ajiya a muhalli me kyau,tanason taga iya gudun ruwan adam,tanason ya kama kanshi da kanshi ta hanya mafi sauqi da dacewa.


            Qasa da mintinan data saba isa gida a yau ta isa,don gudu tayi sosai saman titi,tanason ta riga adam komawa gida,batason yasan cewa ma tafita kwata kwata daga gidan.


          Biyu cikin ma'aikatan gidansu ne suka taso suna mata sannu da zuwa,a yau din bata cikin dukkan wani yanayi na walwala ko sakewar data saba yi musu,don haka sama sama ta amsa musu,ta bude baya ta dauki jakar,saita barwa marwa key din motar tace ta rufe mata,ta wuce gidan dauke da jakar.


              Gidan babu kowa sai masu aikin daketa kaikawo,ko maama ma a sannan tana daki a kwance tana hutawa,da kallo ta bita lokacin data shiga dakin,ta miqe ta zauna tana ci gaba da nazartarta


"Ajiya na kawo miki maama,wasu kaya ne masu muhimmanci,don Allah karki barsu nan kusa,nima ajiya aka ban,ina tsoron tabasu ko kuma nayi sakaci wajen ajiyarsu" abinda tace da maama din kenan,sai tabi jakar da kallo sannan ta sake maida dubanta ga sãahar


"To shikenan,amma dai,kedin lafiya lau kike kuwa?" Wani abu me nauyi ya sauka a qirjinta,tana jin kamar ta budewa maama zuciyarta taga tsantsar damuwa da kuma tashin hankalin da take ciki,to amma idan ta aikata hakan tasan zata jefata ne a damuwar data ninka tata. Dukkaninsu wani irin so suke mata,sam basu ajeta nan kusa ba a zukatansu


"Ba komai,kawai yau inajin weakness ne,gida ma zan wuce nadan kwanta,zan samu relief in sha Allah idan na tashi" kai tadan jinjina tana dan jin tantama,amma dai bata sake hango komai dazai bata hujja ba


"Allah ya qara lafiya,ya raba lafiya,kinqi bari a kawo miki me tayaki hidimar gida,ke kadai a family kin fita zakka sãahar,ba wanda babu me aiki a gidansa sai ke" murmushin da yafi kama da yaqe ta saki


"Maama saina haihu in sha Allah"


"Dolenki ai" ta fada tana miqewa da jakar a hannunta.


            Kamar a zuwa haka a komawa ta dinga tsala gudu,cikin mintuna qalilan ta isa gidan,ta qarasa da motarta parking lot ta kasheta ta fito zuwa cikin gidan.


           A parlor ta zube,dauriyarta tana nan qarewa,ba abinda ke mata yawo a idanu sai hotunan yaran dake jikin passport din,da sunan ADAM a matsayin ubansu,da kuma matar dake a mazaunin matarsa, kuma mahaifiya ga yaran kamar yadda ta gani a sauran takardun dake dauke da gurbin da ake buqatar sunan mahaifiya. To hakan me yake nufi?,tun asali adam baya sonta kenan?, auren jari yaso yayi da ita?,ko cin amana ne zallah ya sauka zuwa zuciyarsa?,mummunar zuciya suka hadu da iblis sukayi masa muguwar kururuwa?,adam da d'a?,wanda ba ita ta haifa ba?,adam da mata bayan ita da duniya ta gama sani?,ya maye gurbin kowacce kadara tata da dukiyarta da sunan 'ya'yansa?,wanann wacce irin azzalumar duniya ce muke rayuwa a cikinta?.


             Duk yadda taso ci gaba da jurewa abun ya faskara,kuka ta zauna tanayi wiwiwi a falon,tafukan hannayenta shinfide saman fuskarta. Karar shigowar motarsa harabar gidan ya sanyata miqewa,kai tsaye ta wuce dakinta,ta kuma zarce bedroom ta fara hada ruwan wanka tana zare kayan jikinta,sam batason adam ya fuskanci komai bare wani abu ya darsu a ransa,don haka ta hada ruwa me dumi sosai,wanda tana gab da fara wankan ya Murda qofar dakin ya shigo, muryarsa cike da wani irin nishadi da a karon farko sãahar ta fassarashi,cikin muryar shauqi da nuna zallar soyayya yake kiranta


"Heart!,heart kina ina?" Lamarin da ya sakata lumshe idanuwa,wasu hawaye masu dumin gaske suka sulalo mata


"Har tsahon yaushe zai dauka yana yaudararta kafin ya gaya mata gaskiya?,ko kuma har sai lokacin da zata bude ido ta laluba sama da qasa babushi?,ya tattara komai nasa da ba nasa ba sun bar qasar shida iyalinsa?.


            Gyaran murya tayi masa,saiya murda qofar bandakin


"Budemin nayi joining dinki mana" bata iya furta komai ba saboda ta tabbatar muryarta ta shaqe,saita sakeyi masa gyaran murya,dai dai sanda kira ya shigo wayarsa,saiya maida hankali kan kiran ya juya yana ficewa daga dakin tare da daga wayar duk a lokaci guda.



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[31/08, 12:30 pm] +234 703 451 7171: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 46



         Sake fashewa tayi da kuka cikin bathtub din,tanajin kamar ana matsa zuciyarta,ta jima a hakan sannan ta fito daga bandakin,tana takawa a hankali saboda yadda mararta ta riqe, idanunta suka sauka akan ledar daya shigo da ita ya ajjiye mata,wadda kullum yake kawo mata dukka abinda ta zabi ci kafin fitarsa,a yau sai taji ta tsani ledar da kuma tsani wanda ya kawo ledar,ta matsa gaban madubi tana goge ruwan jikinta,bata da karsashi ko sha'awar komai,kawai zata daure tayi komai ne don batason ya fuskanci wani abu,batason bashi qofar da zai dago akwai wani abu daya faru bayan fitarsa,tanason ta kamashi ne red handed,tana son ya kawo kanshi da kanshi,a dole ta shafa mai,ta zaro wata doguwar rigar ta zura,dai dai sanda taji an budo qofar da qarfi,har sai data hadu da bango ta bada wani bammm!.


           Da sauri ta daga kai tana dubansa,shima ita yake kallo,ta tsirashi da idanu,wani lafiyayyen tashin hankali ne a kwance saman fuskarsa,ta hadiye wani abu me daci da tauri,nata bacin ran yana son yin tasirin da taketa danne masa tun awannin dazu,amma kuma sai tayi wani qaqqarfan yunquri ta kauda shi gefe,ta maye gurbinsa da lallausan murmushin da idan kayi masa nazari me kyau zakasan cewa zallar yaqe ne takeyi me masifar ciwo


"Sannu da zuwa,ka dade kuma cemin kayi da wuri zaka dawo" ta fada a shagwabe kamar yadda ta saba. Wani abu me matuqar girma ya hadiye a maqoshinsa,wanda ita kanta dake tsaye tana iya ganin yadda maqwallatonsa maqogaronsa yayi sama sannan yayi qasa,mummunar faduwar gaba da kokwanto suka lullubeshi,yayi namijin qoqarin qaqaro murmushin da yafi kama da kuka,cikin sanyin murya yace


"Eh......na dan tsaya ne,momee na raka wani guri" murmushi ta kuma saki tana gyada kai,amma kuma zuciyarta na wani irin qonewa,ba zata iya ci gaba dayi masa wannan murmushin tana kallon fuskar da take da mugun baqi a idanunta ba,don haka ta waske ta hanyar juyawa zuwa ga ledar tana cewa


"Let me see me aka kawomin" baice komai ba sai cika qofar da yayi ya juya ya fita a dakin,ta daga kanta a hankali tana sakin ledar ta fadi qasa,tabi qofar daya bar mata a bude da kallo,ruwan hawaye suna cika idanunta,dukkan wani tabbaci da yaqini yana sake samuwa a tatttare da ita.


          A daren babu wani abu data iya ci,hakanan bata sake ganin adam ba,sai sintiri da motsinsa me qarfi data dinga jiyowa daga dakinsa zuwa parlor,haka ta duqunquna cikin duvet,idanunta a runtse zazzabi yanason kamata.


             Sai wajen sha biyu saura sannan ya shigo dakin,har a sannan tana kwance ne kawai idanunta sun soye,babu wani alamun bacci,tana ga monitoring motsin adam din. Yana kunna fitilar dakin ta miqe tana hamma tamkar daga bacci ta tashi,ta kalleshi suka hada idanu tana mutstsuka ido


"Kada kacemin sai yanzu ka shigo?,har nayi baccin farko?" Ta fada tana qare masa kallo,daga shigowarsa gida zuwa yanzu har wata rama taga yayi,fuskarsa ta fada,ya firgice gaba daya


"Eh sai yanzu......ina wani aiki ne"


"Maimakon ka kirani na tayaka saika barni nayi bacci ni kadai?" Ta saje fada a shagwabe,kamar amma gasa zuciyarta,bata iya jin amsar daya bata ba,sai kansa daya shafa.


           Saukowa tayi da niyyar zuwa tayi fitsari sannan ta daura alwala ko zataji sauqin zuciyarta,amma mararta ta riqe gam,saita zauna daga bakin gadon tana cije lebe,kanta a qasa tana ambaton sunan Allah


"Yau su waye da waye sukazo gidan nan kam?" A hankali ta daga kai ta kalleshi,yana zaune gefan gadon ko kayan jikinsa baiyi nufin cirewa ba,kai ta girgiza


"Ai yau ni kadai ka bari a gidan na wuni kamar tsohuwar mayya" ta amsa masa tana kafeshi da ido,sai ya danyi jim sannan ya zame ya kwanta kamar wanda zazzabi ke shirin saukar masa.


          Koda ta dawo kwanciyar ta tayi,ta kuma saki jiki sosai kamar wadda ke bacci,tana jinsa yanata juyi,ta kwanta ya tashi ya miqe ya fita ya dawo,har zuwa sanda addu'a taci qarfin idanunta baccin da takewa kanta fata yazo.


             Washegari bayan ta farka daga baccin daya dauketa bayan sallar asuba baya dakin,data fito falo sai taji motsinsa a bedroom dinsa,koda fa leqa ya yiwa komai na dakin filla filla


"Halan furniture zaka sake mana?" Ta fada tana dariya,ba fara'a ko daya a fuskarsa,sai kai daya girgiza


"Sanitation nakeyi" ya amsa mata a taqaice

"Ya kamata, shikenan yau bari na fansheka na hada mana breakfast" bata jira cewarsa ba ta juya ta fice.


           Tana girkin tunani fal zuciyarta da ranta, sauqinta daya tun jiya bata fasa kiran sunan Allah a baki da zuci ba,tana samun raguwar quncin sosai da sukunin zuciya,tanason gayawa afifa,to amma ta tabbatar yadda afifa keda haushin adam komai ma zata dagulashi,ashe akwai abinda 'yaruwarta keji a jikinta shi yasa ta tsani adam har haka?,me yasa ita bata taba jin komai a kansa ba?,sai tarin yarda da aminci?,ko don ita za'a jarraba?,shi yasa komai nasa yayi tasiri a kanta?,bata taba manta yadda haduwarsu da adam ta samo asali,a b u k,yana level 400 gab dasu fara final exam,tana level 200. 


            Sam adam ba ajinta bane,hasali ma sãahar din tun a sannan da take da shekaru qanana she has a CHARISMA that attract many people to her,ba kowanne namiji ke iya tararta da sunan soyayya ba,amma adam din ya daukarma ransa saiya siya soyayyarta,yana da baiwar BAKI da IYA TSARA MAGANA(abubuwa biyun dake cutar 'yammatan wannan zamanin kenan game da maza),tun daga randa ya bayyana mata soyayyarsa tayi gaba a wajen ta barshi kamar sauran samarin dake yawo a kanta,ya shiga ya fita yasan komai a kanta,ya zaqulo dukkan wani abu dake burge sãahar,abinda tafiso da wanda bataso,ya maida kansa irin wannan mutumin sak,a duk inda yasan zasu hadu,sai yayi wani abu daya tabbatar zai burgeta ko kuma yana cikin likes dinta.


       Ya jima yana bibiyarta da rayuwarta kafin ta daina ganinsa tsaf,abinka da zuciya da akace tanason me kyautata mata,tana kuma qin me munana mata,tun bata damu ba har ta fara jin babu dadi,basa makaranta daya da afifa,afifa na northwest a sannan,a b u k din da take kuma ita bamai kule kulen qawaye bace,tana da mugun miskilanci sosai,idan kaga sakewarta to irin iyayen nan masu zuwa da qananun yara,a nan ne zaka ga jerarrun fararen haqoranta,wannan din kuma sai ya sanya mata farinjini sosai gurin matan,gefe guda ga mazan dakeson miqa soyayyarsu a gareta,wadanda sukasan ita din me ajice kuma tafi qarfin ajin ajinsi,suna fatan koda abota ko qawance tayi dasu uwa uba tana da wata irin basira,tana da brain qwarai da gaske,wadan nan su suka sanyata zama sananniya sosai. 


             Sai bayan wani lokaci sannan ya dawo,ko a sannan bata sake masa yadda yakeso ba,saidai an samu improvement akan yadda suke a baya,da wannan ya samu qofa ya kuma baje duk wata basirarsa,wadda sai data kusa qarewa tasss kafin ya samu dasa qaqqarfar soyayyarsa a zuciyarta.


          Bai mata qarya ba ya gaya mata wayeshi,su din ba masu shi bane,yana rayuwa ne da mamansa wadda ita ke daukar nauyin karatunsa da komai nasa,yana fargabar gidansu kamar ba zasu bashi aurenta ba,amma da yake Dr mamman girema dattijone,duk da yadda ya muhyi da yaa Saifullahi sundan nuna basaso,abinda ya tsayawa adam a rai kenan,amma dr mamman ya tsaya akayi komai,ba takurawa ba tsawwalawa,abinda ya girgiza kowa ya bawa kowa mamaki. A irin zallar kyau tsarin halitta gata da kuma aji na sãahar,ba wanda ya taba kawowa zata auri mutum me qaramin matsayi da matakin wadata a rayuwa irin ADAM. Sam ita ba wannan take dubawa ba,mutum ce da bata dauki rayuwarta da zafi can can ba, soyayya da kulawar da momee din adam ke nuna mata kawai ta isa ka kalla ka qara kalla,duk da cewa farko farkon aurensu,wata irin tsana ta yiwa afifan,qiri qiri ta nuna bata sonta,wanda ba wanda yasan meye dalili,amma dare daya komai ya canza,ta sata a jikinta da soyayyar da ko adam din bai sameta ba.


         Tun asali haka kawai wata irin rashin jituwa ke a tsakanin afifa da adam,wanda sai a wanann lokacin sãahar din wasu abubuwan suka fara zuwa kanta,ta fara tariyar dalilin da abubuwan daka iya jawo haka,ciki harda wannan yanayin data tsinci kanta a ciki a yanzu.


      A sauqaqe ta hada simple breakfast,ta samu ta durawa cikinta tea da chips ta miqa masa ta wuce nata dakin.


          Wanka tayi ta shirya kanta cikin sauqaqan kaya,tana cikin hutu ne data dauka a gurin aiki saboda yanayin laulayinta me dauke da ciwo,don haka ta shirya kanta cikin wata simple gown,ta koma saman gado tayi kwanciyarta ba tare data sake koma masa ba,zuciyarta cike da tunanuka iri daban daban,duk da yadda taketa qoqarin hana kanta,ko don lafiyar abinda yake cikinta.


           Tana jinsa yana waya sama sama amma bata iya tantance ainihin abinda yake fada,sai kai kawonsa lokaci zuwa lokaci,kusan awa biyu cikakku sannan ya tura qofar dakin nata,tana daga kwancen ta daga kai ta kalleshi,gaba daya yayi wani hajaran majaran dashi,suka hada ido,yau ko yaqen da yake ta qoqarin mata tun daga jiya zuwa yau ya kasa,sai haqora daya bude mata kawai


"Ko zaki tashi kema ayi miki sanitation din?" Idanunta tadan juya kadan,baqincikinsa yana sake cikata,ta gama fahimtar inda ya dosa tsaf,don haka hankali kwance tace masa


"Ka manta kowanne wata daga gida ina kiran masu aiki suyimin irin wannan gyaran?"


"Na sani,yau ni nake sha'awar nayi miki" ya fada adan diririce da kuma alamun zaquwa,bata sake ce masa komai ba,ta miqe tsam ta kwashe duvet dinta tayi hanyar falo,don wani sanyo sanyi takeji dake nuna alamun zazzabi yana tafe.


           Tun idanunta suna kan tv tana sauraren motsinsa daga dakinta har baccin da bata samu isashe ba daren jiya yazo ya sureta,baccin da babu komai cikinsa sai takura da mafarkai marasa dadi,wannan ya sanya batayi nisa ba ta farka,mararta ta cika da fitsari,ta yaye duvet din ta sauke qafafunta qasa ta nufi bedroom dinta.


           Yana zaune saman bedside drawer dinta,ya aza dukka hannayensa guda biyu saman kansa ya dafe,kamar wanda mummunan ciwon kai ya cimma,ya maida komai inda ya jawoshi,saidai dakin ba abinda yayi face hargitsewa,ta san za'a rina,don bashi da cikakkiyar nutsuwar maida mata dakinta yadda yake,kawai ta barshi ne don taga iyakacin gudun nasa ruwan,ta kuma sake badda tunaninsa.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[01/09, 12:45 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

No comments