Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 43-44

 


Page 43




*_WASA FARIN GIRKI_*



         Totally adam ya sauya mata,ya sake zama wani me mugun sanyi tare da takatsantsan da damuwarta da duk wani buqata tata,a tsakiyar wannnan,watanni biyar da rasa wancan cikin wani cikin ya sake samuwa. A wannan karonma itama hankalinta baikai kai ba,tana dai yawan jin jikinta babu dadi sam,adam ne ya fara ganowa,ya kuma kaita asibiti da kansa don tabbatarwa. Irin girman farincikin data gani a idanu da fuskarsa ya ninka nata ya shanye,harda qwallarsa,ya rasa inda zai sakata. Lokacin da take gayawa afifa cikin murnar yadda adam ya karbi cikin,haka kawai jikinta ya sanyaya,amma ta hadiye abunta,cikin farinciki ta taya sãahar din murna. Komai adam ya hanata yi a gidan,shike komai,yayi hidimarta yayi tasa,ya kuma shirya ya fita aiki,bashi ma da wani cikakken lokacin kansa,ya dawo dakinta gaba daya ya tare,yabar nasa bedroom din,sai kuma ya fara bata tausayi,tayi qoqarin komawa dai dai itama,tare da sake saisaita tsarin gidanta,saidai duk da haka bai fasa yi mata hidima ba.


*******K'arfe sha daya na safe ta fito daga wanka,daure da babban towel daya rufe jikinta sosai,tana a tsaye gaban madubi tana ware gashinta daya jiqe don busar dashi da hand drayer,tana ware gashin tana kallon fuskarta,tayi fresh sosai ta kuma fara dan cikowa. Cikinta ya shiga wata na uku har ya fara nisa,wannan ya sanya ta fara samun sauqin laulaye laulayen da take fama dashi,taji jiki iya jin jiki,ta gasu,don kusan yafi cikinta na baya bata wahala.


          A nutse aka turo qofar dakin nata,ta maida dubanta ga qofar,adam ne ke shigowa da innocent face din nan nashi,yana sanye da shirt turtle neck me dogon hannu da trouser dinta data zauna masa a jiki sosai tayi masa kyau,idanunsa akan sãahar,yana jifanta da wani iri kallo dake cike da tarin soyayya,kamar zai cinyeta.


         Har ya iso ya ajjiye madaidaicin tray din hannunsa idanunsa na a kanta,sai daya daidaita zaman tray din saman madubin sannan ya sanya hannuwansa ya jawota jikinsa yana dora kansa a gefan kafadarta


"Qara kyau kike kullum my heart" dan qaramin murmushi ta saki


"Shine kaketa wani kallo na kamar zaka cinyeni?" Ta fada shagwabe sosai,sai ya saki dariya me qaramin sauti


"Bakisan matsayinki bane a zuciyata,da ba zakiyi mamakin irin kallon da nake miki ba" shuru tayi tana jin saukar numfashinsa a wuyanta,kowacce rana sake jinjina soyayyarta dake ninkuwa a zuciyar adam takeyi,a duk sanda kuma ta tuna da incident dinsu na watannin baya sai taji tana sake gayawa kanta tabbas sharrin shaidanne da kowacce irin zuciya bata iya tsallake masa idan yazo da qaddara.


            Dan janye jikinta tayi daga gareshi jin shurun nasa yayi yawa,ta waiwayo tana duban fuskarsa,damuwar da take hanga tun jiya ta sake ganinta muraran kwance saman fuskarsa,duk sai taji babu dadi,don ta tabbatar inda shine da tuni ya sakata a gaba da tambaya,har sai yaji menene?,ya kuma tayata sun magance abun koda da shawara ne


"Damuwa naketa gani fa a fuskarka" murmushi ya sake saki yana girgiza kai,tare da saka hannu ya maida gashinta dake son tsole mata ido baya


"Ba wani damuwa fa,kawai sauyin yanayi ne" fuska tadan bata


"Amma ko da ban cika mace ba,mata na rako duniya,almost three years amma ace na kasa gane damuwa a fuskar mijina?, c'mon,tell me kawai,ba'a boyewa abokin kuka mutuwa" ajiyar zuciya ya saki me nauyi dake alamta lallai akwai damuwar sosai a ransa,ya koma gefan gado ya zauna yana goye da hannayensa,idanunsan nan dake cike da wani irin kallo a kanta,sannan ya fara magana


"Momee ce......" Sai yayi shuru yana duban wani gurin


"Uhmmm,me tayi momee din?" Kansa ya girgixa sannan cikin damuwa yaci gaba da magana


"Wai lallai saina canza mota motar da take hawa,jarinta kuma yayi qasa,saboda ta tana kudinta sosai wanna zuwan da tayi Ghana,tana buqatar wasu kudi ta dora jarinta" qaramin murmushi sãahar ta saki,duk da taji maganar wani iri,saboda motar momee din ba wani dadewa tayi ba,hasalima tata ce adam din yake hawa,momee ta nuna sha'awarta,sãahar din tace yabar mata,gif ne ya Saifullahi ya bata. Bataji komai ba,don iyakar kirki matar tana dashi,hakanan soyayyar da take nuna mata ko adam data haifa baya samun ire irenta ma,bata qaunar bacin ranta ko dis!. Uwa uba kuma ita din tana comparing momee da maama dinta,ta tabbatar yadda adam yake sonta yake kuma girmama iyayenta......ba shakka zai iya yiwa abba da maama komai muddin yana da dama


"To meye abun damuwa a ciki dear?,uwa ce fa?,ko ranka tana ce kana so ba zaka iya cirewa ka bata ba?" Kai ya girgiza da sauri


"No heart.....ba haka bane,kinsan a yanzu babu agenda na taba kudaden dake hannuna....infact ma ni banason taba abinda yake ba mallakina bane ni kadai" ido tadan fidda tana kallonsa,sai kuma ta bata fuska tayi kicin kicin


"Kanason gayamin momee bata haifeni ba,kai kadaine danta" dariya sosai ya saki


"Nidai bance ba,kawai dai banason taba kudin ya kawo delay wajen cikar burinmu,inason kafin babymu ya iso duniya,yazo ya samu mahaifinsa wanda yake tsaye saman qafafunsa,sai ra?i inuwa ko alfarmar kowa ba" ya qarashe maganar bayan ya iso gabanta,ya dora hannunsa plate tummy dinta da har yau yake mamaki da kuma tantamar tabbatuwar samuwarsa.


         K'awataccen murmushi ta saki,ta dora nata hannun saman nasa,wannan ya bashi damar dago fuskarta yana kalla


"An soso miki inda yake miki qaiqayi ko?,na lura kafuwar kamfanin ma bata dameki ba kamar yadda kika damu da zuwan babyn nan" kai ta jinjina


"Allah ya jarabceni da son yara,inajin ranar dana haihu bazan iya bacci ba,har ina rayawa a raina,wannan tsananin son yaran kada ya zama tawa jarrabawar kenan,na mutu ban haihu ba" 


"Komai lokaci ne,gashi yanzu yana hanya?"


"In sha Allah" ta fada tana jin wani farinciki yana lullubeta,ta jarabtu da son wannan cikin fiye da cikinta na baya.


           Zame jikinta tayi daga nasa,ta matsa zuwa side bed drawer dinta,ta budeta,sannan ta jawo safe dinta,ta ciro wani bangul guda biyu me kyan gaske daketa daukar ido,ta qaraso wajen adam dake tsaye daga bayanta, hannayensa cikin aljihun wandonsa yana kallonta. Miqa masa tayi


"Abun hannun nan yana da matuqar muhimmanci a wajena,amma duk muhimmancinsa baikai na miji na gari irinka ba,na amince ka siyar dashi,ka siyawa momee duk abinda takeso,idan da saura a zuba a kudaden da suka rage mana na gininmu,koda foundation a fara sakawa na ginin" baya yaja yana zare idanu


"What?, a'ah,ba za'a yi haka dani ba,Allah ya sawwaqe"ya fada yana yarfar da hannu,fuska ta bata tana kallonsa,sai shima ya tsaya ya zuba mata ido yana kallon yadda rashin jin dadi ya ratsa har cikin zuicyarta


"Ni ba kyauta na baka ba,ka rubuta idan komai na kamfani ya kammala zaka biyani" dariya ya saki sosai


"Matata me wayo,to godiya nake" ya fada yasa hannu biyu ya karba yana juya abun hannun,wanda ya tabbatar idan aka kaishi kasuwa kudade ne masu nauyi za'a karba. Ya sani yayi kuma imani sãahar ta dabance ko cikin mata,tana cikin sahun mutanen da idan suka soka qaramin abu bai sanyawa su gujeka,zasu iya sadaukar maka da dukkan farincikinsu muddin zasu samu soyayya da kulawa daga gareka,hakanan idan suka qika,zaiyi wuya wani abu yasa su soka.


             Da hannunsa ya dinga bata breakfast din har taci ta qoshi,ya tattare plates din zai fita dasu yana cewa


"Bari na watsa ruwa,inason zan dan fita,sai naga waya kamata ya siya banguls din" miqewa tayi a nutse tana daure lallausan gashinta da wani qaramin scarf kalar english wears din jikinta


"Yaukam ko ladan hada maka ruwan wanka ka barni na samu please" ta fada a shagwabe,kai ya girgiza


"Indai nine na yafe" tsaiwa tayi tana dubansa,kamar me tuna wani abu


"Amma,yau kusan two weeks kana hanani shiga dakinka,why?" Ta fada tana bata fuska, murmushi ya sakar mata,ya kama kumatunta yaja


"Banason kiyi dukkan wani aiki bare ki wahala,idan kika shiga da zummar hadamin ruwan wanka,zakice zakimin gyaran daki ne,don dakin yayi qazanta da yawa,abinda ni kuma bana so kenan" kanta ta kawar gefe cikin nuna tata rigimar


"Wannan gatan yayi yawa,ba'a kaina aka fara samun ciki ba,gidanmu cike yake da 'yan aikin da idan na buqata za'a kawomin,amma banason,saboda me?,aure nazo bautar Allah,ba zaman jin dadi da baiwa zuciya da rayuka abinda sukeso ba,ina fatan samun dacewa" ta qarasa maganar tana zube idanunta a kansa. 


           Kai ya jinjina,shi kansa shaida ne,gata kyau ko wani matsayi na rayuwa bai sanyata ta dakaki kanta a gidan aurenta ba


"Shikenan,let's go" ya fadi yana bata hanya,saita miqe tana harararshi


"Da ladan kakemin buqulu?"


"Ban isa ba" ya fada yana daga hannu sama alamun surrender.


           Koda suka shiga dakin bataga wani datti me yawa da yake magana a kai ba,ta hada masa ruwan yayi wankan a gurguje ya fito ya shirya,tana zaune daga gefan gadonsa suna hira har ya kammala,sannan suka fito tare,sai taga yana saka key yana kulle dakin,abinda ya maidashi dabi'a kenan a kwanakin,to amma da yake tana da nata bedroom din,kuma ba wani abu take ajjiyewa cikin dakin ba,sai bata taba damuwa ba,yayi kissing nata lightly a forehead dinta sannan ya wuce.


          Ba abinda zatayi,yau ko aiki ba zata fita ba,don haka tayi zamanta a Parlor,ta kunna kallo,jita jifa tana taba chart a wayarta.


            Sallar azahar ce kadai ta tasheta,tayi sallar ta duba fridge ta dauko fresh samosa da adam din ya mata order ya cika mata fridge dashi wai saboda yunwar dare,ta soyata,ta hado da hollandia me sanyi ta dawo ta zauna.


             Tana tsaka daci kiran afifa ya shigo wayarta


"Uwar biyu" ta fada cikin salon tsokana


"Allah yasa,tabbas da kin samu kyautar kujerar umra daga adam" zuciyar afifa daga can ta tsinke,batasan wanne suna zata bawa adam ba,har yanzu zuciyarta bata taba nutsuwa da komai na adam ba,ta rasa me yasa?,duk da cewa ya bada dalilai masu yawa da yaci ace kowa ya gamsu ya kuma aminta dashi,amma ta nata bangaren hakan ya gaza samuwa


"Allah yasa" ta amsawa sãahar din


"Kudaden nan sunzo ko?" Kai ta girgiza tana sipping madarar


"A'ah,anya?,banga alert ba"


"Haba?,amma tun jiya da dare fa,kuma sunyi debiting dina,receipt din na manta banyi generating ba"


"Karki damu,zan duba balance,nasan sunzo ma"


"A'ah,duba dai yanzu ki gayamin,amana ce ya zaid ya bani kuma kafin na gaya masa na saka sai nayi confirming ya shiga Account dinki" qaramin murmushin dake qara mata kyau tayi


"Bestie koni kika siyar kikaci kudin kinci halak"


"Na sani,amma yanzun ki duba tukunna" ta fada tana katse kiran,ta ajiye wayar a gefe tana jiran kiran sãahar,akwai abinda takeson takai sãahar din gashi,addu'a kuma take takai gano.


         Tana murmushi ta soma checking balance dinsu ta USSD CODE,tayi na farko yayi cancelling,ta sake gwadawa har sau uku yana cancelling,tayi duk wami qoqari na checking din amma yaqi yiwuwa,abinka dame ciki,haka kawai abun ya zafafeta,sai ta soma trying number wani ma'aikacin banking da suke ajiyar.


             Sanda ta gama masa bayanin cewa yayi


"It seems like anyi disconnecting duk wani details naki daga Account din,to amma kuma ina doubting,saboda indai za'a yi hakan saida saninki da yardarki,anyway,gobe zan shiga bankin,zan duba miki komai in sha Allah" godiya tayi masa ta sauke wayar,duk da cewa wani bangare na zuciyarta cike yake da mamaki,amma wani sashen kuma cikin tantama yake,kanta ya kulle dason gane gaskiya da kuma meye dai dai?,ganin zata batawa kanta lokaci saita ajiye komai,don bata da tabbacin gaskiyar ko rashinta akan duk abinda zuciyarta zata raya mata,taci gaba da cin samosa dinta.


           Takai plates din kitchen kenan ta fito taji ana knocking,ta fasa zaman da tayi niyya,ta isa qofar falon ta budeta.


           Mamaki ne sosai ya kamata ganin raihanatu,don tsahon aurensu da adam batajin yarinyar tazo gidan yakai sau uku,duk da yadda takeson yarinyar saboda hankali da nutsuwarta,da kuma yadda take girmamata.

[30/08, 4:39 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 44



          Ta taba yiwa momee din complain akan hakan,tabe baki tayi


"Na rabaki da wannan,wannan me baqin halin,sumumu kasau" murmushi ta danyi kadan,can qasan zuciyarta cike da mamaki,bata taba ganin wani abu na rashin kyautawa raihanatu tayi ba,duk tsahon zuwanta gidan kullum cikin hidima takewa momee,bata tana tsallake umarninta,tausayi da nutsuwarta yake qarawa sãahar qaunarta,wannan ya sanya koda kayan bayarwa zata fitar,raihanan take baiwa,ko yanzu kayan jikinta na sãahar dinne,don ba kasafai momee ke mata dinki ba,takance tana yi mata, yarinyar ce kamar ba mace ba,batason kwalliya bata sawa, sãahar dai bata taba ganinta cikin qazanta ba,ko yaushe fess take da tsaftatattun kaya.


"Shigo ciki mana" sãahar ta fada ganin wani abu me kama da tsoro a fuskar raihana dake tsaye daga bakin qofa,hannunta dauke da ledar dake nuna aikenta momee tayi ta biyo nan,sau biyu tana waigawa tana kallon bayanta kafin ta fado falon.


          A qasa ta zauna, sãahar ta tasheta tace ta koma saman kujera


"Ya gida yasu momee?" Ta fara tambayarta ganin har yanzu batace komai ba tana nufar qofar kitchen,hannunta taji an riqo,saita juyo,fuskarta ta sauka akan raihanatu. K'walla ta gani cike fal da idanun nata,yanayinta ya sake sauyawa qwarai,kowanne lokaci zata iya sakin kuka


"Ki zauna anty don Allah,magana nakeson zamuyi,gida nakeson komawa da sauri,kada momee ta fahimci na biya wani gurin" kai ta jinjina,saita dawo da baya ta zauna dab da raihanatu ta zuba mata ido,jikinta yayi wani mugun sanyi da kuma mutuwa,wanda batasan dalilin hakan ba,sai taji gabanta yana faduwa kadan kadan lokacin da taga raihana ta sad da kanta qasa,qwalla tana diga.


             Tsahon zamanta da yarinyar bata taba zama irin haka da ita ba,zuciyarta ta shiga fargaba da taraddadi,kafin tace wani abu raihanatu cikin rawar murya ta fara magana


"Kafin rasuwar mamana ta gayamin duniya a yanzu cike take da mutane azzalumai,marasa amana,marasa kuma saka alkhairi da alkhairi,na sake tabbatarwa a yanzu akan yayar mahaifiyata,na kuma sake tabbatarwa a yanzu a zamanki da yaya adam da momee. Bazan taba nutsuwa ba,bazan taba samun kwanciyar hankali ba idan har na bari akayo miki wannan zaluncin,bayan kunnuwa na sunji amma na gagara gaya miki" sai tayi shuru hawayen naci gaba da zuba tana hadiyar zuciya


"Na baro yaya adam a gida yanzu suna shirya yadda zasu qarasa murqushe dukiyarki" ta tsaya da zancan tana kallon sãahar. Ido sosai sãahar din ta zuba mata,maganar tana neman matsugunni a kunnuwanta sannan ta isa ga kwanyarta,tsahon wasu sakanni sannan ta danyi murmushi tace


"Ba murqushewa zaiyi ba ba raihanatu,nina dauka da kaina na bashi,ba bangula guda biyu ba?" Kai ta girgiza alamun a'ah


"Duk wata dukiya dake hannunki da wadda take hannunsa,bama wannan ba anty.....kinsan yaa adam yana da wata matar bayan ke?" Wani irin mugun hautsinawa kanta yayi,mararta kuma ta damqe guri guda kamar curarren alkaki,amai ya taso masa me bala'in zafi tare da tashin hankalin daya daki zuciyarta,saita miqe da mugun gudu ta nufi kitchen wanda shine yafi kusa da ita.


             Sosai ta dinga kwarara amai,har sai dan samosa da madarar da tasha babu jimawa suka fice gaba daya,a sannan raihanatu tana tsaye a bayanta tanayi mata sannu cikin tashin hankali,a wahalce sãahar ta gama kuskure bakinta tana maida numfashi ta juyo tana duban raihanatu data gama tsurewa gaba daya,zuciyarta kuma ta fara shiga tsoro da nadamar abinda yasa ta gaya mata wannan babban sirrin


"Kiyi haquri anty,ban gaya miki don na daga hankalinki ba,na gaya miki ne saboda kina da kirki,ke din mutuniyar arziqi ce,barin wasu mutane masu mummunar zuciya su cutar daku babban zunubi ne" hannu ta dora a kafadar raihanatu


"Karki damu raihanatu,jikina yana bani da dukkan gaskiyarki kikayi maganar nan" saita jawo yarinyar jikinta tana jin zuciyarta tana karyewa,duk da a yanzu tana gayawa kanta ba rauni take buqata ba,tana buqatar qarfin hali da dauriya me tarin yawa don ta gano ainihin gaskiyar maganar,duk da wani sashe na zuciyar yana mata tantama,anya adam?,adam da momee?,zasu aikata?.


"Na gode raihanatu" ta fada sannan ta janyeta daga jikinta,hannuwan sãahar duka biyun raihanatu ta kamo ta riqe,abinda bata taba yi ba,cikin rawar murya tace


"Amma don Allah anty kiyimin alqawarin ba wanda zaisan ni na gaya miki maganar nan"


"Komai rintsi komai tsanani raihanatu,na miki wannan alqawarin" tana nan tsaye kamar statue har raihanatu ta fice a gidan. Gaba daya ji tayi kamar an yashe komai daga cikin kanta,ta rasa dukkan wata idea da matakin daya kamata ta fara dauka,babu abinda yake mata amsa kuwwa a kunne sai YAYA ADAM YANA DA WATA MATAR BAYAN KE,ta yaya hakan zata kasance?,ta yaya hakan zata yiwu?,bayan ko yaushe suna tare da dam?,shiba matafiyi ba ba komai ba bare tace yayi amfani da wannan damar yayi auren a wani garin bata sani ba?,sai ta sulale ta zauna a wajen,tasa hannunta guda biyun ta dafe kanta wanda taji yana sara mata,kanta taji yana cushewa,zai buga da kalar tunanin da take takurawa kanta dashi,saita fara karanto sunayen Allah,da haka ta samu taja jikinta ta koma falon ta zube saman kujera.


          Tunda ta kwanta bata tashi ba sai da akayi sallar la'asar,kana kallonta zakace bata da lafiya,dab da kiran magariba adam ya shigo,tana daga kwancen ta daga kanta tana kallonsa,fuskarsa cike da walwala da wani irin nishadi wanda batasan daga ina ya samo asali ba,saita samu kanta da qarewa fuskarka kallo da kyau,zuciyarta tana nazartarsa,nazarin da bata taba yinsa a kan adam ba.


            Ganinta a kwance yasa ya sauke hannayensa daya ware mata yana jiran ta shigo ya rungumeta,duka sai walwalarsa ta koma,ya tako da sassarfa cikin nuna damuwa me yawa ya iso gareta


"Heart,what happened?" Yayi maganar yana dagota zuwa jikinsa


'banajin dadi" ta bashi amsa a taqaice


"What?,kada dai ace a kwance kika wuni?"kai ta sake gyada masa


"Ya salam,me yasa baki kirani ba?,amma baki kyautamin ba, please please karki qara yimin haka,idan wani abu ya sameki fa?" Yayi maganar kamar zai fashe da kuka,sai ya kwantar da ita,ya ciro waya,saiji tayi yana kiran wani likitansa. Drip yasa aka daura mata,wai tafijin qwarin jikinta,ya kasa zaune ya kasa tsaye,bayan fitar likitan ya shiga kitchen ya dora abincin dare,yayi yayi ta fada me takeson ci tace masa babu komai.


            Wanzuwarsa a kitchen din ya bata damar sake zurfafa cikin tunaninta,ta dinga hango mode dinsa tun daga shigowarsa gidan kawo yanzu,tarin qauna kulawa da kuma riritawa ce zallah,sai zuciyarta ta cika da kokwanto,amma kuma ta rasa meye yake bata qwarin gwiwa da tabbaci.


        Karin ruwan babu abinda ya qara mata,saboda wata irin narkakkiyar damuwa ce dake kwance qasan a zuciya,a haka suka kwana. Washegari tunda wuri ya hada mata breakfast ya shirya yace mata zai fita,amma azahar ko la'asar zai dawo. Har ya fita saita miqe ta bishi,a qofar dakinsa sukaci karo,yasa hannu ya jawo qofar yana kullewa da dan sauri,yayin da idanunsa ke a kanta yana kasheta da murmushi.


"Akwai wani abu ne?,ko kinaso na taho miki da wani abun?" Kai ta girgiza


"A'ah,zan dan fita strolling ne idan na gaji da kwanciyar"


"Ba damuwa,amma ko nasa momee ta kawo miki raihanatu?"kiran sunan kawai yasa gabanta ya fadi,saboda tuna gagarumin abun da muddin ta samu tabbacin afkuwarsa,zai zama sila ta guntulewar alaqar auratayya tsakaninta da adam,duk yadda take da kai, muddin kai din maha'inci ko maciyin amana ne.....to tana shata layi me girma a tsakaninka da ita.


"Ka barta,na danji dadin jikin ai" ta amsa masa.


     Kasa komawa dakinta tayi bayan fitarsa,taja jiki ta zauna saman kujera,kamar kuma wadda aka mintsina saita miqe da sauri,kai tsaye ta doshi dakin adam. Tambayar kanta takeyi me zataje tayi a dakin?,tunda ta tabbatar ya rufe dakin a gabanta,kuma bata da sauran spare key da zai bata damar shiga?,amma duk da wannan tunanin sai ta gaza tsaida kanta daga dosar dakin da takeyi.


               Sau daya ta murda dakin bawai don tana tantama ko tana da masaniyar bai rufe ba,amma cikin iko da qudurar ubangiji taji ya bude,mamaki ya cikata,ta tsaya tana duban qofar bayan ta bude,ta leqa sai ta fahimci yana sauri ne bai murza key din da kyau ba,lock din bai gama shiga ba ya zare ya dauka ya shige. Sakin wannan tunanin tayi ta wuce dakin da gaggawa.


           Cak ta tsaya tana qarewa dakin kallo,tana nazarin ta ina zata fara binciken da zai bata shaida ko tabbacin abinda take zargi?,shikam adam ma bashi da safe irin nata,saboda yasha gaya mata ya yarda da ita. Wani tunani ya fado mata,a dazu da suka shiga dakin taga yanata kaffa kaffa da wardrobe dinsa,tun bata ankara ba har hankalinta yakai kai,amma bata kawo komai a ranta ba ko kadan,saboda tasan zuwa yanzu ya wanke dukkan wani zarginsa a ranta.


          Cike da fargaba ta buda wardrobe din,cikin ranta tana addu'ar Allah yasa komai ya zama hasashe ne,Allah yasa komai ya zama tunani ne,muddin ta samu adam da cin amanarta,batasan ta yadda zuciyarta zata iya dauka ba.


            Tsaf ta bincike wardrobe din,saidai bataga komai ba,tasa hannu tana shirin rufewa idanunta ya sauka daga can qasanta,wani abu me kama da jaka ta gani a jingine daga can gefe,saita tsugunna ta jawo,jakace baqa mai cike da zips kala kala,tunda take da adam bata taba ganin jakar ba,wannan ya qara mata qaimi da karsashi,ta fara bude zips din,take kudade masu tarin yawa daure cikin kyauraye da kuma takardu masu yawa suka fado.

[31/08, 12:30 pm] +234 703 451 7171: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma

No comments