Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 41-42

 


Page 41




*******Daga lokacin data fahimci cewa ta farka,ta dawo cikin duniyar da batayi tsammanin dawowarta ciki ba,sai ta fara qoqarin bude idanunta don ta tabbatar da inda take din. A lokacin da kwanyarta ta fara yi mata bitar al'amari na qarshe daya faru da ita saita rasa dukka qwarin gwiwa karsashi da kuma sha'awar bude idanun nata,ta sake runtse idanun nata cikin jin zafi,wani abu me tsini na sukar qirjinta kamar an fiddo zuciyarta an shanyata tsakiyar qwalleliyar rana.


           Hannunta data daga a hankali takai saman cikinta ta shafa bayan ta tuna yadda taga jini yana bin qafafunta a kallo na qarshe data yiwa jikinta. "Saahar,kin farka ne,sannu" muryar anty labiba matar yaa saif dake zaune a gabanta ya ratsa kunnuwanta,bayan zuwa yin salla da maama ita da afifa suka fita yi. "Sannu saahar" anty labiba ta fada tana riqe hannunta dake saman cikin

"Ki daina motsa hannun, cannula din dake hannunki zata goce" ta fada cikin matsanancin jin tausayinta,daga yadda taga tana shafa cikin lallai shine abu na farko daya fara zuwa mata kenan a rai bayan ta farfado din,wanda tuni ya fice daga jikinta ta cikin jinin data dinga fitarwa me yawan gaske.


              Tare maama suka shigo ita da afifa,dukkansu rige rigen isowa gareta sukeyi


"Menene abun kukan kuma?,Allahn daya baki shi zai sake baki wani" abinda maama ta fada kenan cikin muryar lallashi,a nata zaton saahar din ta fuskanci babu cikin a jikinta.


           A mugun karye ta daga kai ta kalli maaman,xancan yayi mugun dukanta,wasu tawagar hawayen masu zafi suka kunno kai,saita maida idanunta kawai ta lumshe,abinda ya bawa hawayen damar saukowa da kyau.


            Tsahon zaman da sukayi tare da ita suna lallashinta idanunta na a rufe ba tare data iya budesu ba,taji ciwo sosai na rasa gudan jininta da tayi,amma a yanzun hankalinta yafi karkata ga mummunan ganin data yi a wayar adam din. Ciki tasan ubangijin da ya bata shi zai sake bata wani,ko a kusa ko a nesa kamar yadda ya kawo mata wannan,to amma kuma wannan baqon al'amari daya shigo rayuwar adam fa?,wanda kai tsaye zata iya kiransa da neman mace koda bata ce neman mata kai tsaye ba,iya maganganunsu kawai ya gama gaya mata adam ya jima da yarinyar,sunyi mugun sabo,kuma sun saba kasancewa da juna da irin mu'amalar dake iya wakana tsakanin ma'aurata

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta har ta fito fili ba tare data ankara ba,sai sautin muryar maama da tace


"Yauwa,ita zakiyita maimaitawa" sake motsa bakinta tayi a karo na biyu tana sake maimaita kalmar,hawayen na sake bin kuncinta.


             A matuqar sanyaye afifa ke sanya tissue tana dauke mata hawayen,saahar dinta jaruma ce da take da wani irin juriya dakiya da kuma cinye abu,irin tashin hankalin da take gani dimuwa da halin qunci sai take ganin kamar ya zarta yadda ya kamata ace an gani a fuskar macen data jima bata samu haihuwa ba ta hadu da miscarriage,saidai bata ga wani abu guda daya da zai dasa mata kowanne irin zargi a zuciyarta ba bare ta sanya ayar tambaya.


            Dai dai lokacin likitan yayi knocking qofar ya kuma tura ya shigo shida wata nurse dake riqe da file na saahar din


"Yauwa ta farka?"


"Ta farka dr" anty labiba ta amsa masa


"Ma sha Allah" ya fada yana tsaiwa daga gefan saahar din


"Sannu ko?" Ya sake fada yana duban fuskarta,sai a sannan ta bude idanunta a hankali da suka tasa saboda hawayen daketa fita daga cikinsu akai akai


"Ya da kuka kuma madam?,sorry for the lost.....kiyi addu'a,next year kamar war haka sai kiganki saman gadon nan rungume da babynki alive and healthier" idanunta ta mayar kawai ta lumshe,abinda takeji cikin zuciya da qirjinta ta tabbatar babu me iya fahimta,da rufaffun idanuwan nata ta amsawa likita dukka tambayoyin sa,sai ya rufe file din nata yadan dubi afifa


"Idan me gidanta ya shigo a turomin shi,inason magana dashi kafin na fita duty"


"Okay,in sha Allah" ta amsawa likitan bayan ta daga kanta daga wayar da take dannawa, zuciyarta duka babu dadi,duk sanda daya daga cikinsu ya shiga damuwa ko tashin hankali,kusan su biyu suke raba wannan damuwar da dukka sakamakon da zai biyo baya.


           Yanayin yadda taga kukanta yana tabasu tare da sake sanyasu damuwa ya saka dole ta tattara abinta ta cinye ta hadiye tana kiran sunayen Allah can qasan ranta,don ita kadai tasan qunci da bala'in da zuciyarta take ciki,dukkansu sun sanyata a gaba kowanne tambayarta yake me takeso?,me yake damunta?,bisa taimakon afifa da anty labiba ta shiga bandaki ta gyara jikinta tayi wanka,ta fito afifa ta shiryata sannan ta zauna yaa zaid yana ajjiye mata plate din abinci a gefanta


"Banason naga komai a cikinsa" wani marayan busashen murmushi ta saki,ta karyar dakai zuciyarta na karyewa,bata jin a yau maqogoranta zaiyi wani amfani,don bata tsammanin akwai wani abu me tauri kamar abinci da zai iya wucewa ta gurin saboda tsabar quntacewa da gurin yayi. Ganin da gaske ba zata iya cin abincin ba dole suka haqura,afifa ta hada mata kakkauran tea,ita da yaa zaid suka sanyata a gaba,aka samu tasha rabin cup,ta buqaci zata kwanta,shuru take da buqata,kadaici takeson samu ko zatayi wani tunani me amfani kan bala'in dake tunkaro rayuwar aurenta koma kai tsaye tace ya tunkarota,tashin hankali da musibar da ko wanne lokaci hankalinta ke tashi, tsigar jikinta ke zubawa idan taga wata mace cikin irinsa,yau gashi AKAN KANTA.....tamkar almara......tamkar cikin tarikicen tarkacen mafarkai,saidai kash......wannan din a zahiri ne,gaskiya ne,ba mafarki hikaya ko tatsuniya ko almara bace.


           Dukkaninsu sun dauka bacci ne ya sake dauketa,don haka yaa saif da yaa muhyi suka dauki iyalansu suka wuce gida,ya zaid shima ya wuce bayan maama ta sanyashi ya dauki masu aikin gidan biyu da suke tare anan tace su tsaya su karbo abincin dare,hamisu driver ya dawo dasu zuwa magrib.


            Shuru dakin yayi,daga afifa dake faman research a wani website sai maama dake jan carbi counter,sallamar adam dake gaba momee na biye dashi shi ya ratsa shurun da dakin yayi.


           Har tsakiyar kanta taji saukar muryar adam din,bata motsa daga yadda take ba har suka qarasa shigowa,tana jin sanda maama ke gaisawa da momee cikin surukuta tare da bata kujerar zama,yayin da adam ya matso dab da gadonta,ya miqa hannunsa a hankali ya sanya shi cikin nata yana kallon kyakkyawar fuskarta data fada tayi wani fayau da ita.


             Ji tayi kamar ya manna mata wuta,da da hali abinda tafiso a yanzun shine ta zare hannunta daga cikin nasa,to amma bata son tayi wani abu da zai fuskanci idanunta biyu,don bata shirya kallon fuskarsa ba a yanzu.


            Kamar afifa ta shiga zuciyarta sai kuwa ta isarwa da adam din saqon likita,ya zame hannunsa ya juya ya fita zuwa office din likitan.


            Ya sameshi yana shirin fita daga duty,to amma shigowar adam din ya sanyashi tsayawa da hada takardunsa da yakeyi ya masa izinin zama,ya zauna kujerar da take fuskantar dr,ya bashi hannu sukayi musabaha. Gyaran murya kadan yayi sannan yace


"Kaine me gidan saahar girema ko?" Kai ya jinjina yana dubansa


"Ma sha Allah,kasan cewa zubewar cikinta nada alaqa da shan tablet na zubda ciki?" Sosai fuskar adam din ta nuna zallar mamaki da alhini


"Tablet kuma dr?,haka kuka gani?" Kai ya jinjina masa cikin yanayi na tabbatarwa


"Yes,and after that ma.....mahaifarta ta dan samu rauni gaskiya sanadiyyar injection na planning da kuma wannan tablet din masu qarfi da tasha"


"Nasan da zancan injection,infact ma da yardarta aka fara"


"But haihuwarta nawa?" Likitan ya jefa masa tambayar yana kallonsa cikin mamaki


"Ko daya,duka duka ba bamu cika two years da aure ba until now" mamaki qarara ya bayyana kan fuskar likitan


"Amma....sorry mr adam,waye ya baku wannan shawarar?,bakusan allurar planning koda ka haihu bata masu haihuwa daya ko biyu bane?" Iska adam ya furzar daga bakinsa,dr yadan lumshe ido sannan yace


"Am sorry kada na zaqe da yawa,duk da cikin aikinmu ne mu bada shawara ga hanyar da zata bulle ma mara lafiyarmu don samun ingantacciyar lafiya kuma cikakkiya......a likitance kada ta sake ta'ammali da wani qwaya ko allura na zubda ciki ko hana haihuwa,don a yanzu haka mahaifarta ta samu rauni sosai,koda a gaba fa sake samun ciki sai an bashi special care matuqar inason juna biyunta yayi surviving har zuwa haihuwa" shuru adam yayi yana gyada kai,kafin ya sauke ajiyar zuciya yana kallon likitan


"Akwai wanda yasan dukka wadan nan bayanan?" Kansa ya girgixa cikin halin ko in kula


"Babu,but sister dinta taso taji wani abu daga gareni,so amma kuma tunda kaine ka kawota kuma kaine mijinta, that's why bance komai ba,coz kaine kafi cancanta mu tattauna maganar da kai"


"Okay dr,na gode,inason please kada wanda yasan da wannan,zanyi qoqari in sha Allah na kiyaye lafiyarta,zan kuma bincika abinda ya kawo wadan nan matsalolin"


"Hakan yayi kyau" daga haka sukayi sallama da likitan ya baro office din.


              Tsahon zaman da sukayi a dakin shida momee din taqi koda bude idanunta bare su gaisa,har suka gama zamansu sukayi sallama suka wuce gida ita da adam din.


             Wata irin jinya saahar takeyi me wahala tare da qoqarin danne abinda ke cikin zuciyarta,jinyar ta zame mata guda biyu,ta zuciya data gangar jikinta,tayi masifar kewa tare da rashin jin dadin rasa abinda ke cikinta,saboda yadda ta qwallafa rai a kansa,ta kuma aza dukka burinta a kansa,sai gashi rana daya sanadin kuskuren adam tazo ta rasashi,abu na biyu mummunan ganin da tayi a wayar adam din,wanda ya zama silar tarwatsa wani sashe mai girma na farinciki da walwalar rayuwarta,banda Allah yasa kota ina tana da matallafa,da family me qarfi dake tattalin farincikinta.


            Da farko baccin qarya ya tsira duk sanda adam yazo har kuwa ya tafi koda awa nawa zaiyi,daga bisani ta fahimci abun yayi yawa,kuma har kamar an fara fahimtar ta,wannan yasa ta canza salo,zaizo kuma har ya tafi bata barin kowacce kalma ta hadata dashi,koda kuwa kallon fuskarsa batayi,rabon data dora qwayar idanunta akan fuskarsa tun randa fa kalli fuskar wayarta,duk sanda tayi yunqurin kallon nasa saita hangeshi cikin qazamin hoton da ya dauka shida yarinyar da bata gama tantance kamanninta ba cikin wani qazantaccen yanayi da ko a mafarki bata taba tunanin ganin hakan akan adam ba,dukka wani yarda da aminci daya samu daga zuciyarta sai taji a hankali a hankali yana sulalewa. Yanayin da yaga saahar din ta koma yayi matuqar girgiza adam din hadi da sanyashi cikin matuqar tashin hankali,yanason ko yaya ne ta bashi dama da zasuyi magana amma ta hana hakan faruwa,har zuwa randa aka basu sallama.


              Kai tsaye ta wuce motar yaa Saifullahi,yaa saif din ya ranqwafo yana kallonta


"Ki koma matar mijinki mana,ina cewa ke ya budewa motar yana jiranki ki shiga?". Kanta ta langabe,idanunta nason kawo ruwa amma kuma tana hana hakan faruwa,su dukka basu sani ba,sam a yanzun bata da sha'awar komawarta gidan adam,to amma kuma idan tace ma ba zata koma din ba tasan bata isa ba,dole saita bada gamsashshiyar hujjar da zata zame mata garkuwa,ta kuma zama silar da zasu karbi uzurinta suyi mata yadda takeso,su barta a gida ta gama warkewa,ta kuma yi nazari a tsanake kan makomar zamanta da adam,ta gano daga ina kuskuren yake?,sakacinta ne ko nasa?,amma hakan dukka ba zata samu ba,don duk da yadda suke gatantata,suke kuma shagwabata ba shakka basa lamuntar wasa da harkar aure,ba kanta farau ba,ta gani daga kan yayarta wadda ya zaid yake bi Anty ANUUM.


            Tana fita a motar yaa Saifullahi adam ya nufo gurin da sassarfa,yamatso da nufin tallafa mata ta isa motar duk da tana takawa sosai amma saita zame,ta matsa gefe kadan dashi tayi gaba ta barshi.


          Bai sare ba ya bita,ya kuma cimmata tana kici kicin bude motar,sai ya bude mata front seat,sabanin ita dake qoqarin bude back seat.


          Karon farko ta daga manyan fararen idanunta ta zube masa su ba tare da tace komai ba. Wani abu yaji ya dakeshi sosai,kwarjini tayi masa sosai,haryaji yana shirin narkewa a wajen,saiya kauda nasa idanun,bai sake dubanta ba har zuwa sanda tashige ya maida qofar ya rufe ya zagaya ya tashi motar suka fice daga harabar asibitin.


             Shuru ne kawai ya baqunci motar,kaiba zaka ce akwai mai rai a cikinta ba,karo nafarko tun aurensu da irin hakan ta faru. Saahar din wata irin macace ta daban da take da matuqar qoqari wajen iya kula da miji,taka tsantsan tare da qoqarin barin dukkan wani abu da adam bayaso,bata daukan fushi dashi koda ya bata mata,tafi gane ta sanar masa su tattauna su yiwa kansu sulhu,a tsahon zamansu na wannan shekarun babu wanda ya taba jin kansu,sun zama wadansu irin ababen koyi da kwatance ga kowa.

[29/08, 4:35 pm] +234 907 013 9442: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 42



"Saahar" adam din ya kira sunanta kai tsaye da wata irin murya dake shaking,sarai ta jishi amma saita lumshe idanu kawai batare data amsa ba. Sake kiran sunanta yayi amma kamar dazun,ya fahimci ba zata amsashi ba koda zai kwana yana kiran sunanta,a duk sanda take cikin maquracin bacin rai, dabi'ar miskilanci itace abokiyarta a sannan. Samun tabbacin ba zata amsa masa ba sai ya fada jero mata kalamai na kare kai da kaifin harshe da kuma zaqin iya tsara kalamai da Allah ya bashi. Wata irin baiwa ce dashi kansa yake alfahari da ita,baiwar da yasan cewa ta siyo masa abubuwa masu yawa masu tsada da daraja.....cikinsu kuwa harda ita saahar din.


             Dukka wata kalma da yasan zata iya tasiri a zuciyar saahar din a lokacin ya arota yayi amfani da ita,to amma ko gezau,kamar ma bata wajen,abinda yayi matuqar karyashi,don bata taba gwada masa irin wannan dabi'ar ba.


          Har suka isa gida,bata tada kai koda sau daya ta kalleshi ba,ta sani muddin ma tace zata kalleshi to ba abinda zata hango tattare da adam din face baqinsa da zuciya da idanuwanta zasu dinga gani,hakanan matuqar tace zata bude baki tayi wata magana.....to lallai kalmar da dukka zata fita a bakinta muninta zaiyi yawan da zata iya haifar da faruwar komai.


            Yana tsaida motar ta budeta ta fice a gaggauce,cikin zafin nama shima ya bude bangarensa ya take mata baya,yakuma yi nasarar cimmata a tsakiyar falon gidan,ya sha gabanta yana kallon fusatattun idanuwanta da suka tashi daga ainihin launinsu na fari qal da baqi sidik din qwayar idanuwa,zuwa pink da surkin red. Wani mugun kwarjini tayi masa da ya qarasa karyashi gaba daya,sai yayi qasa da qwayar idanuwansa yana cewa


"Dukkan laifin da kike tuhumata dashi saahar na yarda na aikata.....amma ban aikata babban laifin da zuciyarki ke miki hasashen na aikata din ba,ban taba yi ba na rantse miki da girman Allah"

"Ka bani guri na wuce adam!" Furucin ya fita daga bakinta da wani irin madaukakin sauti daya canza tone na muryarta,karo nafarko data taba tanka masa tun daga waccar ranar da abun ya faru

"Bazan matsa ba saahar,kiyimin dukka kalar hukuncin da kikeso muddin zaki tsaya muyi magana koda ba zaki fahimceni ba". Juyawa tayi kawai ta doshi hanyar fita ba tare data sake koda motsa bakinta da nufin tankawa maganarsa ba. Yayi wata muguwar zabura yabi bayanta,don ya tabbatar tana nufin ficewa daga gidansa,wanda faruwar hakan yana nufin faruwar komai da komai,yana nufin tonuwar asirinsa,yana kuma nufin subucewarsa daga kafatanin rayuwarsa,abinda a yanzun bai shirya masa ba.


          Hannu yasa ya maida qofar parlor din ya rufe,ya kuma murza key ya zare key din ya jefa a aljihun rigarsa,sai yasa dukka hannuwansa ya hade a nasa,ya kuma sulale a wajen ya tsugunna bisa gwiwoyinsa,sannan ya buda tafukan hannayen nata ya saka fuskarsa a ciki ya rufe ruf tare da kubcewar kuka.


         Duk da a yanzun batajin adam din bisa kowanne matsayi a zuciyarta,bata jinsa kwata kwata daga guraben da a baya yakai,amma kukansa yazo mata a bazata,ya kuma bata mamaki,kuka koda ga qaramin yaro abune me cin rai da zuciya gaba daya,bare ga babban mutum da yakai munzalin magidanci kamar adam,saidai wannan ko daya bai kashe wutar dake ruruwa cikin zuciyarta ba.


"Na roqeki kiyimin alfarma ki yafemin,kiyi haquri kiyimin dukka kalar hukuncin da kikaga dama,amma karki nesanceni,kada ki gujemin,ina mai hadaki da girman Allah......ki yafemin,na miki alqawari ba zaki sake samuna da wani laifi kwatankwacin wannan ba,sharrin zuciya da na shaidan ne,duk sanda kika sake kamani da laifi mai shigen wanan bama wannan din ba,na amince na kuma lamunce miki kiyimin dukka irin hukuncin da kikaga dama" duk yadda taso ya sakar mata hannu ya barta da abinda takeji a zuciyarta amma yaqi bata wannan damar,yaci gaba da amfani da baiwar iya sarrafa kalamai da yake da ita,ya dinga zaftare tsananin fushi da bacin ran da suka kafa sansani mai girma da qarfi a zuciyarta,har sai da yayi nasarar ture kaso mai girma daga cikinsa


"Ka sakarmin hannu.......har yanzu bansan makomar zamana ni dakai ba...."


"Har sai yaushe saahar?,me kikeso nayi miki wanda zai wanke wannan mummunan laifin da na aikata?"


"Sai nayi tunani" ta fada kanta tsaye. Da gaske tana buqatar nutsuwa,tana buqatar tayi tunani me kyau,tana buqatar su zauna ita dashi su tattauna,tana kuma da buqatar lalubar daga inda matsalar take. Lamarin babban abun tashin hankali ne daga gurin diya mace,ba kowa ke iya jurewa ta fuskanci irin wannan babban qalubalen ba.


           Ya qyaletan kamar yadda taso,ba kuma wai ya qyaleta bane dukka yadda ta buqata,yayi kane kane tsakanin dakinta da nasa,wunin ranar gaba daya bai zauna guri daya ba,dukka hidimar gidan ya dauka ya aza a wuyansa,dukka wani abu da saahar din keda buqata shi ya dinga yi mata,duk da bata buqaci komai daga wajensa ba,daga bisani da taga bashi da niyyar bata space kamar yadda ta buqata,sai ta murza key ta rufe dakin.


            Tayi kuka tayi kuka har taji babu dadi,tayi addu'a da dukkan iyawarta da nau'ikan addu'o'in data sani,ta nema ubangiji ya shiga lamarinta ya kuma bata juriya,taji ta muzanta da yawa ta kuma qasqanta,ta kalli kanta a madubi har sau babu adadi,tanason zaqulo abinda ta rasa,tanason zaqulo inda ta gaza,tana kuma son gano wanne GURBI ne da bata cikewa adam ba har ya tsinciki kansa cikin irin wannan qazamin sahun?. Saidai a dukka hasashe da dogon nazarin da tayi,bata tsinkayi abu daya da ta kasa cikawa adam ba.


           Babu wanda yasan halin da take ciki,babu kuma wanda tayi niyyar gayawa koda afifa kuwa,tanaji har cikin zuciyarta ba zata iya tonawa adam asiri ba,sun fara hawa matakin fara samun zuri'a,ko taqi ko taso,a yau ko kuma gobe ana iya kiransa da uban 'ya'yanta,shike da matsala ita ke zaune dashi,su tattauna a tsakaninsu su kamo bakin zaren tare tana ganin shine hanyar da zasu samu mafita.


          Tun washegarin ranar data dawo momee ta bata aron rahina a cewarta har sai jikinta ya warware tunda ita din bata da ra'ayin me aiki,yarinyar itake komai na gidan tamkar saahar ba a kwance take ba,ita din bata iya hassala komai,daga kwanciya sai kwanciya,damuwa ta farmaketa ta cimmata a lokacin da bata taba hasashen wata matsala ko damuwa cikin rayuwarta ba,tana ganin komai nata ya cika cif cif,gibi guda daya daya ragema rayuwarta na rashin haihuwa shima ya cikashe!,ashe qalubalen yana gaba!.


             Sati guda bata ko yarda sun sake hada hanya da adam ba,har sai zuwa ranar data gamsu a karan kanta lokaci yayi daya kamata ta fuskanceshi da dukka tarin tambayoyi da tuhume tuhumenta. Ranar tun da safe bayan ya fita itama ta fito ta qwarara jikinta,rahina nata murnar ganin fitowar saahar din,kusan wunin ranar tare sukayi komai da ita,har zuwa magrib inda saahar ta wuce dakinta.


            Qarfe takwas da wani abu na dare tana gaban madubi tana daure dogon gashinta mai santsi da baya rabo da gyara adam ya turo qofar dakin ya shigo,idanu suka hada saita janye nata idanun ta maida kan mudubin,yayin da shi kuma ya kafeta da kallonsa cike da kewarta,jikinsa fes da alama tun daxun ya shigo,yayi wanka ya canza kayansa cikin wasu qananun kaya da suka amsheshi qwarai.

 

          Hannunsa ya cire daga aljihunsa,yaji bazai iya ci gaba da jurewa shariyarta ba,ya tako zuwa inda take,ya tsaya dab da bayanta yana kallon kyakkyawar fuskarta ta madubin,ta sake haske,fuskarta tayi fayau.


          Jikinta ta zame daga wajen,ya bita da kallo,ya motsa bakinsa zaiyi magana,ta rigashi ta hanyar masa nuni da wajen zama,sannan itama ta koma daga gefan gadonta ta zauna.


            Dukka idanunta ta zuba masa,wani bacin rai yana motsawa daga qasan zuciyarta zuwa saman fuskarta,idan tace ta taba jin tashin hankali mai gauraye da bacin rai irin wannan tayi qarya,tayi namijin qoqari qwarai,ta tattare dukkan abinda ke taso matan,ta jefa masa tambayar data dade tana son amayar da ita,ko zata samu sauqin radadin dake yankar naman zuciyarta kowanne dare zuwa rana


"Yaushe ka fara neman mata adam?" A hargitse ya kalleta,don tambayar ta dakeshi qwarai,yanayin fuskarsa ta sauya yayi wani mugun laushi


"Idan kikace neman mata.....kina nufin zina fa kenan?" Kai ta jinjina kai masa


"Qwarai kuwa,domin abinda idanuwa suka karanto kenan,qwaqwalwata kuma ta fahimta"


"Subhanallah,wa'iyazubillah" ya fada fuskarsa na nuna girman yadda furucin yayi masa radadi a zuciya,tsahon wasu sakanni sannan ya iya daga kai ya dubeta


"Ba neman mata nakeyi ba,duk da tarayyar da mukeyi akwai sabon Allah a ciki,tunda zataga tsiraici na zanga nata..... Ta rudeni watanni uku baya da suka shude,banda ita na rantse da Allah ban taba neman kowa ba,ban taba tarayya da kowacce mace ba,kuma tun daga ranar ban sake kulata ba,ban sake bi ta kanta ba"


"Ta ina na gaza maka adam?,ko akwai wani waje da na gaza maka daka rufeni ka kasa gayamin?" Kai ya girgiza da sauri


"Ke din ta kowacce fuska kin kerewa kowacce mace,idan nace kowacce mace.....ina nufin nau'in kowacce mace daga kowanne jinsi da yare na duniya ni a wajena" wayarsa dake aljihunsa ya ciro,ya kuma fidda layukansa gaba daya ya lanqwashesu suka karye,sannan ya qarasa gabanta ya ajjiye mata wayar


"Idan kinso daga yau ni adam na ajjiye wayatama gaba daya sai sanda kika lamunce min,kiyi haquri ki yafemin,kici gaba da zama dani,sannan ki lullube sirrina,na miki alqawari saahar,muddin na sauya ko naci amana,na yarda amanar Allah ta cini nima" kalmarsa ta qarshe tayi masifar yi mata nauyin da har sai data tilasta mata rufe idanuwanta,amanar Allah ta cishi?,lallai da gaske yake mata,ba shakka ya canza ya kuma shiryu da gasken gaske.


              Ta dauki wannan kalmar ta azata bisa babban ma'auni,ta bata matsayi me girma,irin matsayin daya zarta ta qiyasceshi,a nata dabi'ar da kuma kyakkyawar tarbiyyar data samu,girman ubangiji ya wuce wani dan adam yayi wasa dashi,ko ya fake a bayansa ya aiwatar da dukka abinda son zuciya da qaawar duniya zai sawwarawa mutum. Ta dauki wannan kalmar a matsayin madogara,ta fifitata ta karbi nadamar adam,cikin sati guda ta fara qoqarin daidaita kanta tare da daidaita dukka lamuranta,ta dinga kokawa da kanta da yaqi da kanta tana son komawa ainihin saahar,tare da qoqarin maida komai a tsakaninsu ya koma bisa mizanin daidaito.


             Cikin lokaci qalilan ya sake canza mata,ya zame mata tamkar bawa dake qarqashin ikon uban gidansa,sai abinda tace shi zai aiwatar,sai abinda ta zaba,ya ninka dukka kyautatawa da kuma soyayyar da yake nuna mata,kulawa da tattali marasa misali,cikin wata guda kacal ya mantar da ita komai,ya kuma sake amintar da ita,ya nisanci dukka abinda zai kawo zargi da kokwanto a tsakaninsu shi da ita. Rayuwa taci gaba da tafiya sannu a hankali,wannan amincin.....wannan yardar.....wannan hadakar da wannan gamayyar dake a tsakaninsu tana ci gaba da wanzuwa.


*_WASA FARIN GIRKI_*??

[30/08, 4:39 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma

No comments