Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 39-40

 


Page 39




            Bata jima ba ta fito da fitsarin,ta miqawa afifan ta koma ta zauna tana lumshe idanunta,tana jin yadda jikinta yake qara zama weak,ita kanta tana mamakin wanann sauyin da bata taba jin irinsa ba.


           "Yes!!!!" Afifa ta fada da wani irin madaukakin sauti


"Alhamdulillah Alhamdulillah" ta maye gurbin furucin nata da sauri tana murza tafukan hannayenta waje daya.


             Sai a sannan saahar ta bude idanunta a hankali ta zubesu akan afifa dake tsaye tana ta faman buga murmushi,dukka hankalinta da idanunta nakan saahar


"Me wai?" Ta tambayeta a gajarce,sai fuskar afifan ta sake fadada da farinciki,abinda ke nuni da cewa farincikin dake danqare a zuciyarta ba kadan bane a wannan lokacin


"Congratulations mrs adam,congratulations" ido saahar ta fidda tana duban afifa


"Meye a kanki bestie,da ciwon kikemun murna ko kuwa?" Dariya ta saki a nishadance


"Wannan ciwon ai irinsa muka dade muna nema miki,you are pregnant bestie" cak komai ya tsayawa saahar saboda yadda maganar tazo mata a bazata na farko,na biyu kuma yanayin yadda cikin yazo,murna zatayi ko akasin hakan?,duk da tana da tsananin buqatarsa,tana cikin kewa da qishirwar samun yaro a kusa,tana qaunar yara qwarai da gaske har batasan iyaka ba,to amma kuma har yanzu basu cimma plan dinsu da adam ba,hakan na nufin cikin yazo a lokacin da basu shiryama zuwansa ba ko kuwa?.


"Bestie banason wasa,kina magana ne akan rayuwata fa" batace mata komai ba sai dauko strip din datayi mata test din dashi ta ajjiye mata a gabanta,layuka biyu gasunan sun bayyana radau kamar ma sunfi fitowa a jikin nata tsinken fiye da yadda suka saba fitowa,hakan yana nufin cikin ba na satin jiya ko yau bane.


            Kanta ta dago jikinta a sanyaye ta kalli afifa


"How comes afifa?"


"Min indillah" ta amsa mata kai tsaye tana goye da hannyenta a qirji,tana qarewa saahar nazari da karantar yadda ta karbi cikin a ranta.


                Akwai farinciki shinfide can qasan fuska da zuciyarta,amma ta karanci kamar akwai wani abu mai nauyi dake tasowa yana danne wannan,wanda jikinta yake bata koma meye baya rasa nasaba da adam


"Ciki dama yana iya samuwa ana tsaka da yi maka injection na planning?" Dukka girarta ta daga kafin ta amsa mata


"Yes mana saahar,akwai wanda ya isa halittar Allah wanzuwa aduk sanda yaso?,allura fa just wani qaramin garkuwa ne da bai isa ya hana Allah yin yadda yaga dama da bayinsa a duk sadda yaso ba" 


"That's absolutely true" ta furta a hankali tana gyada kai,bata iya sake cewa komai ba saahar din,sai ta samu kanta da cika da farinciki,dukkan wani kwadayinta da son haihuwarta yana dawowa sabo fil cikin ranta,farinciki takeji yana mamayarta irin wanda bata taba tsammanin zata tsinciki kanta a ciki ba,lallai haihuwa ni'ima ce,'ya'ya kuma rahama ce da babu kamarta(Allah ya azurta masu nema da samu,ya bayar dame albarka ya albarkaci diyoyin musulmai gaba daya).



"Ni ya kamata na yiwa mr adam wannan albishir din,ki kwanciyarki,zan prescribing maki wasu magunguna idan yazo zaku wuce sai ya tsaya ya siya miki,don't mind any changes da zakiji a jikinki,you will be alright in sha Allah soon" kai ta gyada tana lumshe idanunta,afifa ta dauki wayar saahar din da zummar kiran adam din yazo ya dauketa,tabar saahar da ido a lumshe,hannunta saman plate tummy dinta tana shafawa a hankali,tunani fal kwanyarta,wai ita din itace zata zama uwa,itace wata halitta yanzun haka ke rayuwa a jikinta,murmushi ya subuce mata,wata qaqqarfar soyayyar abinda duk ke kwance a marar tata ya fara sauka cikin zuciyarta.


           Afifa bata sanar da saahar zuwan adam ba,ta sanya an saukeshi a Parlor din baqi na gidan,ta sanya me aikin gidan takai masa ruwa da lemo,sannan ta shiga daki ta zura dogon hijabi ta fito.


          Ta iskeshi zaune a falon,cikin shigar qananun kaya,ya cika falon da turarensa,hannunsa riqe da wayarsa yana chart.


            Baki afifa ta tabe sannan tayi sallama,ya daga kai yana amsa mata sallamar,fuskarsa kadaran kadaham,haka kawai jininsa bai taba zuwa daya da yarinyar ba ko sau daya,kamar yadda itama nata jinin da nasa bai haduwa sam,kawai dai kowa yana dakewa ne saboda darajar saahar dake a tsakaninsu.


           Hannun kujerar dake daura da qofar fita ta zauna tana cewa


"Sannu da zuwa mr adam" zamansa ya gyara,ya maida wayar aljihunsa,ba tare da ya amsa mata ba ya jefa mata tambayar


"Ina baby?"


"Babynka tana ciki,yanzu zata fito....." Sai tadan dakata,ta fidda iska kadan daga bakinta,bayan ta sake canzawa fuskarta yanayi,babu sauran sassaucin data shigo dashi


"Na fara iskeka ne don nayi miki kyakkyawan albishir din cewa ka kusa zama uba,babyn naka na dauke da wani babyn naku......i mean matarka nada juna biyu" ta qarashe maganar tana zube dukka idanunta akan fuskarsa,tana fatan ko yaya ta fusgi wani reaction nasa,wanda shi zai bata kowacce irin dama da takeson samu daga gareshi.


             Cak komai ya tsaya a falon tsakaninta da adam din,kafin daga bisani ya sakar mata murmushi yana juya key din motar dake hannunsa


"Ban taba zaton ke mutuniyar kirki bace irin yau,kin iya kawo kyakkyawan albishir,duk da naso na fara jin hakan daga bakin baby...... anyways.....ke da ita duk daya ne,ina taya junanmu murna" ya qarashe maganar yana tsareta shima da nasa kallon.


           Murmushi ta saki tana murza hannunta


"Haka ne abinda ya kamata ya fito daga bakin kowanne magidanci na qwarai.....shikenan daga yau allurar planning ta qare,saika maida hankali ga kula da abinda yake cikin nata,yadda kake kula da duk wani kudi da zai shigo ko ya fita ta account dinta,da yadda kake kiyaye lokuttan yin salary dinta da sauran komai nata.....ina fatan yaron da ba'a shirya zuwansa duniya ba..... ubangiji ya qaddari zuwan nasa ta silar innarsa afifa......zai samu kulawa matuqa da qauna hadi da soyayya,kwatankwacin wadda ake iqirarin ana yiwa mamansa......yanzu zan turo maka babyn naka,ku sauka lafiya" daga haka ta miqe tana ficewa daga falon,yayin da adam ya miqe tsaye yana rakata da ido,zuciyarsa na suya sosai.


            Ya akayi yarinyar ta rainashi har haka?, waye ya gaya mata sirrin rayuwarsu da yadda suka tsara zasu tafi da ita tsakaninsa da matarsa mallakinsa?,me yarinyar ke nufi akansa?,wanne kallo takeyi masa?,akwai maganganu da yawa da yakeson gaya mata don tasan shi din ba sa'anta bane,to amma kuma ta riga tayi nisa ba ta yadda zai iya amayar mata da dukkan abinda yakeson fada din.


            Sosai Zuciyarsa ke quna,ransa yayi matuqar baci da maganganun afifan,a zafafe ya fita a falon,ya bude motarsa ya zauna yana jiran fitowar saahar,ya tabbatar banda saahar na sonshi so na gasken gaske,yayi amannar da tuni afifa ta dade da tarwatsa kyakkyawar mu'amala ta fahimtar juna kyautatawa da girmamawar dake tsakaninsa da ita.


           Sallamar saahar din kawai ya iya amsawa,ba tare daya waiwayo ya dubeta ba ya tayar da motar ya figeta suka fice daga gidan,saahar da batasan abinda ke faruwa ba ta bishi da kallo galala cike da mamaki


"Na dauka zaka shiga ka gaida ummi ne ai" ta fadi a sanyaye tana mamakin abinda ya canjashi da matsanancin fushi haka lokaci guda.


            Shuru baice mata komai ba,sai mamaki ya sake kamata,ta gaza dannewa saboda bata saba ganin irin wannan yanayin a tare dashi ba


"Dear......lafiya kuwa?,ko wani abu ya faru?" Da wani irin gudu ya gangara gefan titi ya tsaida motar,cikin tsawa da hargagi ya soma magana


"Saboda zallar rainin hankali ma ni kike tambaya lafiya?,bayan kinsan komai?,kinsan abinda ya farun?,ki aiko 'yaruwarki ta cikin mutunci ta wulaqantani,ashe yawo kike dani kina bayar da labarin ina karbar dukiyarki,kina gayawa duniya nidin makwadaici ne?,to ki sani ba abinda zanyi da dukiyarki,ki kuma gayawa wannan banzar 'yar uwarki taki afifa ta fit......."


"Ya isa!!" Ta fada da qarfi zuciyarta na wata irin suya,mamakin adam yana cikata,ta dinga kallonsa sosai waiko zataga wani sign na fara shaye shaye a tare dashi,tunda take dashi ko kallon banza bai taba hadata dashi ba bare tsawa har irin haka ba, zata iya jure komai amma banda zagin afifa,don ita din Wani sashe ce ta jikinta


"Ta yaya zaka zo kana hukuntani akan al'amarin da bansan dashi ba?,har kana qoqarin zagin afifa,afifan da bata nufinmu da komai sai alkhairi?"


"Kedai!,amma banda ni,yadda ta tsaneni nima haka na tsaneta,i hate her with passion,idiot....." Saiya finciki motar da kyau,har saahar nayin gaba zata daki gaban motar ta kare da hannayenta, hankalinta ya tashi sosai,bata saba ganin tashin hankali ba,kamar yadda bata taba ganin bacin rai makamancin haka daga gurin adam ba,duk da tasan yana da fushi amma bai taba kwatanta mata ba.


           Kuka ta fashe dashi tana dora kanta saman cinyarta,wanne abu afifa dinta ta yiwa adam da zai dauki irin wannan mugun fushin?. Suna isa gidan yaci burki,ya fita yabarta a motar bayan ya kashe. Da hanzari itama ta fita a motar tabi bayansa,saidai bata cimmasa cikin falo ba,tana niyyar binsa daki da take jiyo motsinsa da qarfi sai gashi ya fito,hannunsa dauke da wani file.

[28/08, 5:18 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 40



        Yana daga tsayi ya wurgoshi kusa da ita,abinda ya baiwa dukka takardun ciki damar fitowa suka warwatsu a falon


"Ga komai naki nan,ki duba dukka abinda babu a ciki ki rubuta zan biyaki,sauran abinda mukayi hadaka kuma ki lissafa nawa ne na cire miki naki" ya qarashe maganar cikin fushi. Iya wuya zuciya tazo mata,sai taji ba zata iya jurewa wannan abun nasa ba,bayan batasan me tayi masa ba,ta miqe a fusace karo na farko a tarihin zamansu data taba maida masa magana 


"Basai ka fake da abinda afifa tayi maka ba,zaka iya cin mutuncina duk ta yadda kaso adam,na gode" kuka ya qwace mata ta juya da hanzari ta nufi bedroom dinta.


            Sautin kukanta bai hanashi wucewa dakinsa ba yana jan mugun tsaki,amma tsakanin awa daya zuwa biyu sai wayarsa tayi qara,ya kalli wayar yaja tsaki,banda me kiran nada muhimmanci a wajensa ba abinda zai sanyashi daga wata waya a yanzu,shi daya yasan iya adadin yadda ransa yake a bace da kuma irin rudanin daya samu kansa a ciki a iya ranar yau,komai yazo masa a bazata,ya miqa hannu ya daga wayar yana maqaleta a kunnensa.


*_BAYAN AWA DAYA_*


          Ajjiye wayar yayi,ya shiga toilet dinsa ya fidda kayan jikinsa yayi wanka,ya dawo ya shirya cikin armless riga da boxer dinta,ya feshe kansa da turare sannan ya wuce dakinta.


             Yayi mamakin tarar da ita tana kuka har sannan,yayi tsaye a kanta yana kallonta,sai yaji zuciyarsa ta karyo,ya qarasa kusa da ita ya dora hannunsa saman bayanta


"Awa nawa kikayi kina wannan kukan da bashi da amfani?,bayan kinsan bake kadai bace?" Maganar tasa tazo mata a bazata,sai kukan nata ya tsaya cak,yadda yayi maganar juna biyun dake jikinta kadai ya tabbatar mata shima yana maraba dashi,sabanin yadda tayita tunanin da yadda zata fahimtar dashi. Bata gama wannan tunanin ba taji ya sanya hannunsa duka biyun ya dagota ya rungumeta yana fadin


"Am sorry,raina ne a bace" ajiyar zuciya ta saki tana narkewa a qirjinsa,cikin lokaci qalilan komai ya wuce a tsakaninsu kamar komai bai faru ba,kasancewar basu saba samun sabani a tsakaninsu irin haka ba,sai ya bude sabon shafin tattalinta tare da nunawa abinda ke cikinta zallar qauna muraran,wannan ya wanke komai daga zukatansu.


*********Cikin kwanakin da suka biyo baya komai ya koma normal,hankalin saahar ya sake kwanciya sosai da yadda adam ke tattalinta yana nunawa cikin jikinta qauna,har excuse ya nema mata daga wajen aiki saboda laulayin da take fama dashi,laulayi takeyi sosai,yau lafiya gobe babu lafiya,gaba daya hankalin 'yan gidansu yana kanta,tun daga kan abba har ya zaid da take bi,kowa tattalinta da kuma riritata yakeyi,kamar itace zata haifa musu jikan farko. Saidai duk irin riritar da suke nuna mata bata kai rabin wadda adam ke mata ba.



********Zaune take saman couche,ta miqe qafafunta sosai yadda zata sake,chiffon armless short gown ce a jikinta,wanda rashin tsahonta ya bawa sambala sambalan kyawawan qafafunta damar bayyana.


              Waya suke da momee,wadda kullum kwanan duniya sai ta kirata tayi mata sannu da jiki,tun abun yana sata jin kunya da nauyi harta fara sabawa,sukayi sallama da ita dai dai sanda adam ke fitowa daga kitchen,hannuwansa duka biyun riqe da mug dake dan fitar da tururi,qamshin kayan qamshi na tashi a ciki.


           Tun kafin ya qaraso ta miqe ta zauna sosai,shima ita yake kallo fuskarsa tana fitar da murmushi,ya soma takowa a hankali saita maqale kafada a shagwabe


"Jan rai ko?"


"Yes" ya amsa mata kai tsaye yana dariya qasa qasa. Kunnuwanta ta kama tana dariya kadan kadan


"Na tuba,don Allah a bani nasha" idanu yadan zubata,yadda tayin tayi masifar burgeshi,kyanta kuma ya sake fita muraran,sai yaji jikinsa yadan saki amma kuma ta wani sashen wata zuciyar ta qara masa qaimi tare da karsashi,ya qarasa gabanta yadan russuna ya miqa mata cup din


"Thanks dear" ta furta da sassanyar muryarta bayan ta saka dukka hannuwanta guda biyun ta karbi mug din cikin zallar kwadayin shan tea din,ta sanya bakinta ta kurba,saita lumshe ido tana sakin murmushi saboda dadin da ya ratsa ta sosai


"Na yarda yau kadai.....ka fini iya hada black tea" murmushi ya sakar mata ba tare da yace komai ba,ba kuma tare da ya dauke kallonsa daga kan fuskarta ba,ta sake kai cup din bakinta ta sake sipping,dai dai lokacin da qaramar wayarsa dake kan wani dan teburin gilashi tare da babbar wayarsa dake charge ta dauki qara,ya qarasa a hankali,ya zareta daga charging ya karata a kunnensa idanunsa har yanzu akan fuskar saahar


"Yanzu?....kamar dai gobe...... alright on my way" ya fada a hankali,saiya cire wayar daga kunnensa ya tako inda saahar take.


            Rusunawa yayi yayi kissing goshinta


"Ayimin afwa baby,fita ce ta kamani yanzu,just one hour zanyi zuwan da dawowar...... I hope ba damuwa?" Kai ta jinjina masa tana lumshe kyawawan fararen idanunta


"Babu dear" ciki ya wuce,ba jimawa ya fito,ya canza kaya zuwa qananun kaya,sai zabga qamshi yakeyi,ya mata kyau sosai,ya sunkuya ya sake kissing dinta,har ya wuce ta kira sunansa


"Kayi kyau da yawa,Allah yasa ba zance zaka je ba" ta fada tana langabar da kai. Dariya sosai ya saki,sai ya dawo ya tsugunna a gabanta


"Bayan ke babu wata,idan akwai ma Allah yasa ta makance ta gurgunce koma ta mutu....."baki ta kama tana dariya


"Nidai ba ruwa na,irin wannan mummunan fata haka"


"Eh kuma har zuciyata na fada ba,bazan wuce hour dayan ba zan dawo in sha Allah" ya fada yana miqewa da dan hanzari sanda wayarsa ta qara yin qara alamun ana sake kiransa. Hakanan ta samu kanta da binsa da kallo har ya fice.


            A nan falon taci gaba da zama tana kallon wani film da mbc2 suke haskawa,film ne daya shafi soldiers battle,tana son irin films din sosai. 


              Kamar daga sama taji qarar waya,a mamakance ta waiwaya tana duban daga inda sound din ke fita. Wayar adam ce a wajen,tadan zubawa wayar ido tana mamakin yadda akayi yau ya manta wayarsa,shi da kwana biyun nan baya sake da waya,ko yaushe tana hannunsa,bini bini ya dauka ya duba,har wani sabon suna ta saka masa saboda maitar riqe waya daya koya,ko cikin dare idan ta farka da yake a kwanakin nan bata fiya kwana da qoshin lafiya ba sai ta ganshi riqe da waya,tun tana daukan abun da wasa har taga ya zama gaske,tayi masa complain sai yace akwai wata sabuwar harka ne da yakeson ya gwada shiga,so ana wayar masa dakai ne yadda business din yake,wanda kuma yake masa bayanin ba qasar nan yake ba,yana china, akwai tazarar 7hrs tsakaninmu,darensu shine ranarmu,lokacin shi kuma yana office bazaiyu ya maida hankali ba akan waya ya ajiye aiki,ranarsu kuma shine darenmu,a sannan shi yana da chance nayin chart,shi yasa yake tashi a daren.

 

              Ta gamsu,saboda ya yarda da adam din,bata taba kamashi da wani laifi da zai sanya zuciyarta tayi ?ar ko rawa a kansa ba.


             Kira bayan kira haka ya dinga shigowa,hakanan taji qarar wayar ta dameta,saita yanke shawarar sanyata a silent,don ita din ba gwanar daga masa waya bace,koda za'a kira wayarsa sau dubu bazata waiwaya ta kalleta ba,ada har qorafin hakan yake mata


"Idan kirane mai muhimmanci ko kuma samuwa ce kinga shikenan ta wucemu" dariya kawai takeyi,saboda bata jin zata iya,tana da dabi'a na tsame kai daga abinda ba huruminta bane bai kuma shafeta ba.


              Da sauri ta koma ta zauna sanda ta miqe da nufin cimma inda wayar take saboda wani hadadden ciwon mara na tashin hankali da taji ya soketa,ta runtse idanunta ta kuma dafe mararta da kyau tana kiran sunan Allah tana jujjuya kanta saboda azaba. Akalla ta kusa kwashe minti biyar a haka tana juya kanta hagu da dama,gefe guda kuma qarar wayar naci gaba da cika mata kunnuwa. Ta bude idanunta a hankali bayan ciwon ya lafa tana share gumin daya tsatstsafo mata a goshi,qafafunta babu cikakken qwari ta miqe ta nufi wayar.


             Tana isa wayar ta danyi blinking light alamun shigowar saqo,ba inda idanunta suka sauka sai kan fuskar wayar. Da sauri ta zare idanunta daga fuskar wayar tana lumshe su,gabanta na wani irin dokawa labbanta na furta


"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" tana fatan ta bude idanunta taga ba abinda suka gane mata bane da farko. Saidai a wannan karon data sake bude idanun nata abinda ta gani ya zarta wanda ta gani da farko,dukkan jikinta ya dauki rawa,taji a sannan bata da sauran zabi da ya wuce ta dauki wayar.


            Tana daukan wayar qafafunta suka gaza daukarta,dole ta zame ta koma da baya ta zauna saman kujera, hannuwanta kamar ba zasu iya riqe wayar da kyau ba,ta fara qoqarin gwada password din dake kan wayar.


            Duk password din da ta saka sai yace mata wrong,daga qarshe ta gwada saka qarshen number wayarsa,a take ta bude,saqon da bai gama fitowa ba ya bayyana muraran.


            K'azaman kalmomi masu munin gani bare kuma kunnuwa su iya jumurin sauraronsu,wani gumi mai zafi ya shiga tsatstsafo mata ta kowacce kafar gashi dake jikinta,zuciyarta ta ninka bugunta kamar zatayi tsalle ta fito daga qirjinta,kanta yayi wata irin sarawa ta fara gani dishi dishi sanda ta fara bin charts din dake inbox din da number wayar da babu suna a kanta. Wasu irin qazaman saqonni da ko ita da take halalin adam bata tunanin sun taba musayar irinsu a tsakaninsu,hotuna na kowanne sashe na jikin yarinyar,harda muhallin da ko mahaifiyar yarinyar tana tunanin zaiyi wuya ta sake katarin ganinsa tun bayan da shari'a ta hau kanta. Ganin abun take kamar al'mara,ganin abun takeyi kamar ba adam dinta bane,kamar ma ba wayarsa bace,ba abinda ke kaikawo cikin kwanya da zuciyarta da sunan adam din da kuma fuskarsa. Video na qarshe da idanunta suka gaza kalla wayar ta sulale a hannunta ta fadi tare da wani hadadden ciwon mara da bata taba jin makamancinsa ba,sai kawai ta cure a wajen tana jin numfashinta na shirin barin gangar jikinta.


               Wannan yayi dai dai da bude qofar falon da adam din yayi cikin gaggawa,har yayi nisa ya tuna yabar wayarsa,duk da yasan baida matsala,kuma bashi da haufi matarsa bata taba wayarsa,amma haka kawai yau din yaji ya kasa samun nutsuwa,yaji bashi da gamsuwar tafiya,dole ya juyo da kan motarsa ya dawo ya dauki wayar sannan ya koma.


         Sam bai lura da inda ya aje wayar ba,idanunsa akan saahar dake cure guri daya kamar alkaki suka fara sauka. Da hanzari ya qaraso yana kiran sunanta,duk da azabar ciwon da takeji a mararta amma hakan bai hanata daga kai ta watsa masa wani kallo da jajayen idanunta ba. Sosai yasha jinin jikinsa amma zuciyarsa na gaya masa komai normal ne,ya miqa hannu gareta,ta tattara dukka ragowar qarfinta ta miqe tana jin mararta kamar zata rabe biyu


"Kada ka yarda ka tabani,karka qaraso inda nake......" Bata kai ga qarasawa ba numfashinta ya soma sarqewa,tana jin wani abu me dumi ya ratso ta jikinta ya soma bin qafafunta yana gangarowa,duk da yanayin gushewar hankali da take kan gabar yi,amma hakan bai hanata qoqarin ganin abinda ke faruwa da ita ba,idanunsu shi da ita suka sauka lokaci daya akan jinin dake malala saman tiles din falon,bai jira cewarta ba ya qarasa gareta da hanzari yana riqeta,zuwa lokacin itama tuni ta qarasa ficewa daga hayyacinta,saboda qarin tashin hankalin fitar jinin da ta gani daga jikinta.

[29/08, 4:35 pm] +234 907 013 9442: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

No comments