Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 37-38

 


Page 37



         Ta farkon macace da aqalla ta doshi shekara hamsin da biyar,saidai a ido ba zakace haka ba,saboda yanayin yadda take,kallo daya zakayi mata ka fuskanci gogaggiyar macace wadda tasan kan rayuwa sosai,idanunta fes suke,akwai wayewa mai tsanani a tattare da ita,gajeriya ce mai gogaggiyar baqar fata,tana da manyan idanuwa da dogon hanci,wannan ya qawata mata fuska sosai,ta bayan nata kuwa doguwa ce,wannan itace momee din adam,wadda suke kama sosai ta fuska.


            "Kina hanya ashe?,har na fidda rai?" Ta fada cikin madaukakiyar fara'a,cikin kunya da kara irin wadda kowacce diya keji ga surukarta saahar tadan duqar dakai


"Ina hanya momee.....barka da yamma,ina wuni?" Ta gaida baquwar dake tare da momee din wadda ta kafeta da idanu cikin wani irin kallo na qurilla,har saahar din na jinsa har cikin jininta.


             Da sauri ta murmusa cikin nuna kulawa


"Lafiya lou,kina lafiya?" Ta amsa da hausarta data dan baci kadan,da alama su momee din sun fita qwarewa nesa ba kusa ba


"Lafiya lau alhmdlh"


"Ki shiga ciki bari na rakata na dawo" momee ta fada suna juyawa da baquwar


"Ina mamakin yadda adam ya samu kyakkyawar yarinya haka,kyanta na bani tsoro k......" Saahar ta jiyo muryar baquwar,wadda bata qarasa jin abinda take fadi din ba,katsewa tayi ko nisan data fara yi mata ne bata sani ba,ta sanya kai cikin parlor din momee din,wanda a yanzun ya zama abun sha'awa cike da kayan alatu.


             'yar budurwar da ake kira da raihanatu ta amsa sallamar saahar din cikin mayalwacin murmushi da kuma tarin kirki da girmamawar da takewa saahar,ta qaraso da sauri tana karbar ledar hannunta hannu bibbiyu har kamar zata kai qasa tana cewa


"Sannu da zuwa anty" cikin fara'a Sahar din itama ta maida mata


"Sannu raiha sarkin aiki,ya gida ya aiki?"


"Alhamdulillah anty,bari na kawo miki ruwa" ta yiwa ledar guri a wajen,ta juya da sauri ta doshi kitchen dinsu dake manne da parlor din,saahar ta bita da kallo.


         Yarinyar diya ce ga qanwar momee,momee din ta dauko riqonta,itake mata komai,kamar yadda yarinyar itama itace komai na gidan,yarinyar nada wani irin hankali kirki da kuma nutsuwa,bata da surutu sam,hakanan bata da shiga shirgin da ba nata ba.


         Cikin mintin da bai gaza daya ba raiha ta gabatar ma da saahar drinks masu sanyi hade da ruwa,tana murmushi tace


"Mun cinye abincin rana anty,bamu gama kuma na dare ba kiyi haquri" murmushi ya subuce mata


"Ni ba baquwa bace raihana,kada ki damu" ta girgiza kai tana murmushi itama,har cikin zuciyarta tana jin qaunar anty saahar din,saboda sauqin kai kirkinta kyauta da kuma kyautatawarta,matsayinta dana mahaifinta,kyawunta ko iliminta sam bai sanya mata girman kai ba ko jin ita din wata bace,uwa uba kuma yadda ta dauki momee din a matsayinta na surukarta.


         Bata taba komai a ciki ba,don ta fito gida a qoshe,har zuwa sanda momee ta dawo parlon ta zauna tana cewa


"Sannu da zuwa,har na cire rai ai" a kunyace saahar ta saki murmushi,tadan sunkui da kai tana murza zoben hannunta


"Ina sane momee,ga saqon nan" sosai ta washe baki cikin fara'a,ta miqe tsam ta dauko ledar da kanta tana budawa.


          Manyan kaji ne broilers da suka qanqare saboda dadewa cikin freezer,cikin ma'aikata gidansu ta sanya wata cikinsu ta ciro mata


"Allah dai yayi miki albarka,ai baqi nayi,duka naman gidan ya qare,gashi ni kuma banason girki babu nama ko kadan" saita qwalawa raiha kira,cikin minti daya ta iso gurin,harara ta jefa mata


"Kina abu kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,dauki wannan naman,ki cire wani daga ciki kiyimin farfesu"


"Tom momee" ta amsa a ladance,ta sukunya ta dauki ledar ta wuce kitchen din.


           Kamar ko yaushe hira sosai momee ke janta da ita,harda abinda saahar ke ganin bai shafeta ba,to amma tana baiwa momee din uzurin banbacin al'ada da yare dake tsakaninsu,sannan kuma irin wayewarta daban da wayewar sauran surukai data sani.


            Mafi yawa saidai ta amsa da eh ko a'ah,ko kuma tayi murmushi wani lokacin,tun tana zuba idon ganin adam har aka kirayi sallar magariba,a sannan raiha tayi mata jagora zuwa dakinta,duk da momee din tayi mata tayin shiga nata dakin tayi sallar amma sai tace a'ah,don ba zata iya sakewa ba.


             Sai a sannan ta samu sukunin kiran adam din,amma harta qaraci ringing dinta bai daga ba,ta haqura ta ajjiye wayar zuciyarta na gaya mata yana sallah ne hala.


              Tana idarwa ta sake gwada kirannasa,cikin sa'a ta shiga,ta bada dukkan hankalinta ga wayar tana jira ya daga.


             Dab da zata tsinke ya daga din,muryarsa can qasa yayi sallama,ta amsa masa cikin kulawa


"Nayita jiranka dear.....kuma baka shigo ba" dan gyaran murya yayi kadan


"Ban samu na fita din bama,throughout yau ina gida" hankalinta ya sake kaiwa ga muryarsa


"Lafiya kake?"


"Me kika gani?"


"Muryanka was so cool.....kaman jikinka ba qwari"


"Yeah.....bacci nayi ban tashi ba har yamma,shi ya kashemin jiki"


"Alright,na taho kenan?"


"No,ai nayi alqawari,zan shigo saimu dawo tare"


"Okay"


"I missed you" ya fada cikin tsananin kulawa, murmushi ya subuce mata


"I missed you too,saika qaraso" daga haka sukayi sallama ta ajjiye wayar taci gaba da lazuminta,lokaci lokaci tunani yana waftar hankalinta ya kaishi ga wani abu na daban,bata bar dakin ba har sai datayi sallar isha'i.


            A falo ta samu momee,ta baje dabgen kajin tana kaiwa ciki,tayi d'ai d'ai saman kujera kamar ita daya ta rage a duniyar.


            Raihana ta qwala kira har kusan sau uku a jere


"Maza hadawa diyata abinci taci" ta amsa a aladabce,ba jima ta dawo da babban tray ta ajjiye gabanta


"Zauna mana muci" saahar ta yiwa yarinyar tayi,saita girgiza kai,tamkar taga hararar da momee din ke watsa mata ta gefan ido


"Zanci nawa yanzu anty,wannan naki ne".


             Batayi nisa dacin abincin ba ta qoshi,dama ita tun tale tale bata cikin sahun mutanen da abinci ya dama,tana rufe warmers din adam na shigowa.


          Hannayensa zube a aljihun wandonsa,cikin wasu shirt da trouser yake sanye,shi din gwanin wanka ne,akwai iya daukan ado me jan hankali,idanunsa a kanta,haka yake mata irin wannan kallon ko gaban waye.


          Kallo daya tayi masa ta dauke kanta daga sashensa,yayi mata kyau amma jikinsa babu kuzari kamar yadda taji dazu a waya,sai daya iso cikin Parlor din sannan yayi sallama yana laluben wajen zama,saahar din ta miqe tsam da tray din bayan tayi masa sannu da zuwa ta nufi kitchen dasu,duk da yadda momee ke cewa ta zauna raiha tazo ta kwashe.


              A kitchen din ta sameta ta gama cin abincin tana wanke plates din,da hanzari ta karba kwanukan tana mata sannu, murmushi saahar din tayi ganin yadda ta tarbeta kamar wadda tayi wani aiki me yawa


"Aike za'a yiwa sannu"sai kawai taja kujerar plastic ta zauna tana bin yadda raiha ke gudanar da aikin nata cikin nutsuwa,batabar kitchen din ba har sai da adam ya  leqo yayi mata magana.


             Sunyi gaba shida momee din,ta tsaya tana tattara jakarta data gani a bude,ta danyi mamaki,don tasan a zuge tabar jakar,to amma sai wata zuciyar ta bata may be ta manta ne,a buden ta barta,tunda babu wani baqo cikin gidan bare parlor din bare ta zargi wani abun.


           "C'mon momee,please kibar maganar nan" muryar adam kenan dake fita a kasalance idanunsa nakan saahar dake fitowa,waiwayowa momee din tayi kafin ta maida dubanta ga adam


"Okay,amma kayi tunani akai ka gani,think twice kafin yanke hukunci"


"Nasan abinda nakeyi fa" ya amsa mata kai tsaye yana dosar motar saahar da key din ke hannunsa,ya buda mazaunin mai zaman banza yana jira isowarta.


            Sai data yiwa momee saida safe,ta rakata da addu'o'i kamar zata rusuna mata har qofar motar,saahar din ta shige a kunyace kan yadda momee din ke mata,sannan ya zagaya shima ya shiga seat dinsa,ya tayar da motar suka fice a gidan.


            Shuru ne ya ratsa motar,tunanin saahar ya dauketa ya wulwula da ita can baya,wasu watanni masu dan dama da suka shude cikin rayuwar aurenta da adam,koda cikin tarin mafarkai,bata taba tsammanin zatayi mafarki guda daya da zai nuna mata nan gaba momee zata sota ba,zata amsheta hannun bibbiyu a matsayin suruka ba,sai gashi a yanzun......cikin wani hali da yafi kama da juyin juyi momee ta amsheta har fiye ma da yadda take nunawa adam qauna da kulawa,duk da kasancewarsa tilon d'a a gareta.


            Saukar hannun adam saman nata hannun ya fargar da ita,ta waiwayo ta zube masa kyawawan idanunta da suka tilasta masa lumshe nasa idanun


"Yaadai?,akwai matsala ne?" Tattausan murmushi ta sakar masa tana girgiza kai


"Babu" sai yaja hannun nata zuwa bakinsa a tausashe yayi kissing bayan hannun,wani abu ya sauka a zuciyarta,ko yaushe adam baya gajiya da ita,hakanan baya gajiya da bayyana zallar soyayyarsa a gareta.


********Misalin qarfe shida ne na yamma,dai dai lokacin babu abinda gidan yake fitarwa sai daddadan qamshin turaren wuta daya wadaci kowanne lungu da saqo na gidan,sai sauran burbushin qamshin daddadan abincinta da tuni ya gama zama ready saman dining table.


            Saahar din irin matan nan ne da suka kai sunan mata ta kowanne fanni na rayuwa,suka kai qololuwa gurin iya zamantakewar gidan aure,suka kuma qware tare da ci gaba da neman sani cikin kowacce rana ta ubangiji ga dukkan macen data amsa sunanta,ta kuma qware gami da sanin dukka hanyoyin kyautatama miji,tare da zama tauraruwarsa.


           Tun daga abinda ya shafi kyan sura,gayu dake cakude da ilimi da kuma tsantsar tsafta,kawaici haquri da iya mu'amala,uwa uba iya girki da kuma gyaran kai kowanne lokaci lungu da saqo,ta yadda zata dace da muradin adam,tasan yadda zata hadawa kanta nau'in dukkan wani abu da zai daga martabarta da darajarta na diya mace awajen miji.


          Idan ka shigo gidan ka sameta kaga yadda take tafiyar da gidanta cikin tsari da nutsuwa ba tare da ta buqaci me aiki ba zakiyi matuqar mamaki,duk da tarin gata da dukiyar da mahaifinta keda ita,amma wannan sam bai sanya ta dauki kanta takai wani bigire ba,tana ganin cewa cinyewar rayuwar mace a gidan aurenta shine ta bautatawa mijinta,tayi hidima cikin gidanta da dukka jikinta da hannuwanta.


             Kamar yanxun data kammala komai,tana sanye da wata gown ta wani farin material me santsi qal dashi,ta daure sassalkan gashinta cikin farin ribbom daya dace da rigar jikinta,jikinta na fidda wani sihirtaccen qamshi da babu lallai ka iya tantance ainihin turaren da tayi amfani dashi kai tsaye,qamshine mai tafi da zuciya da tsayawa arai,tana qaunar qamshi har batasan iyaka ba,zata iya saka ko nawa ne ta siyi turare muddin qamshinsa ya dace da tsarinta.


             Tana shirin zama ta tuna bata hada ruwan wankan adam din ba,saita aje wayar hannunta,ta juya cikin tafiyarta me kama da na me tausayin qasa ta wuce dakinsa sannan ta zarce toilet dinsa.


             Daga ciki ta jiyo qarar sautin wayarta,ta goge hannunta jikin rowels din dake rataye a bandakin cikin tsari,wanda da kanta ta zabarwa kanta tsarin duka toilets dinsu,take kuma kula dasu kamar ba muhallin qazanta ba saboda yadda suke samun kulawa.


               Special tone ta sanya masa,don haka kafin ta qaraso ta fahimci wanda yake kiran, murmushi ya subuce mata,ta juya qwayar idanunta sannan ta daga wayar ta kara a kunnenta


"Amincin Allah ya tabbata a gareka"


"Tare dake mace daya tamkar da dubu.....nazo wuce wani fish park ne naga suna gashin kifi,kina da buqata ne?" Take taji yawunta ya tsinke,ta tuna wanda taci shekaran jiya kamar ta tsinke harshenta,tunda take bata tana craving na kifi irin wannan karon ba


"Na gode qwarai da gaske dear,ina buqata idan har zan samu"


"Kin samu ma matar aljanna,kinfi gaba haka,kinfi qarfin ki nema abu ki rasa" ya fada a tausashe,sautin murmushinsa yana isa kunnuwanta,idanunta ta juya dadi yana dada ratsata,idan tace duk duniya babu miji kamar nata to ba shakka batayi kuskure ba,batajin a wannan lokacin akwai miji kamar nata,ko yaushe soyayyarsa a gareta sabuwa ce,kulawar data tabbatar mata da yawa sun rasata,wasu kuma suna kewarta,batasan dame zata amsa masa ba,saidai farincikin da takeji wanda a kullum baya gajiya da sanyata a cikinsa,a haka ya barta da waya a hannu tanata smiling,kafin daga bisani ta zame wayar daga kunnenta,ta koma ta zauna saman kujerar ta zauna,sannan taja wani english novel tana dubawa qafarta daya saman daya tana jiran qarasowarsa.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

.*H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

Page 38



          Horn dinsa kadai ya isar mata da saqon dawowarsa,ta ajjiye littafin a gefanta ta miqe a nutse tana takawa zuwa farfajiyar gidan.


            A tsakiya suka hade, yasa dukka hannayensa biyu ya tarbeta,ya dagata sama cak yana dariya


"Na jima banga macen da bata da nauyi kamarki ba"  dubansa tayi sosai da dukka idanunta,saiya lumshe idanunsa yana jinjina mata kai


"Ka jima kuma?,akwai wata ne bayan ni?" Idanunsa dukka ya ware yana dubanta gami da girgiza kai


"Babu,har abada kuma ba za'a samu ba,idan mutane na cewa kada ki yarda da mijinki muddin zaice miki bayanke babu qari,banda adam a ciki,ki rubuta ki ajjiye,ina miki magana ne kan qanne na da nake dasu wanda momee ta riqesu kafin daga baya ta aurar dasu tun a ghana" murmushi ta saki tana saqalo wuyansa


"Nima nafison na zauna a haka,don banason ka daina daukata" ta fada tana langabe kai.


             Dariya ya saki yana duban idanunta


"Kina tunanin akwai qibar da zatayi sanadin da zan daina daukan matata masoyiyata?,babu ita,muje ciki na baki kifinki" daga haka ya taka da ita zuwa ciki suna hira qasa qasa.


            Tun hankalinsa baikai kan yadda take cin kifin hannu baka hannu qwarya ba har ya ankara,ya tsaya da abinda yakeyi yana kallonta,sai ya kama hannunta da take qoqarin kaiwa baki ya riqe yana dubanta cikin kokwanto,suka hada idanu saita sakar masa murmushi


"Please dear,don Allah ka barni na qarasa mana"


"Yaushe kika zama hadamammiya ne?" Wuyanta ta langabe tana kallonsa


"Nima ban sani ba,kawai dai na wayi gari inason kifi fiye da komai" hannun ya sakar mata,sannan ya koma da baya ya zauna yana fuskantarta,yanayin fuskarsa yana dan canzawa kadan bada wani alamu me yawa ba


"Tun yaushe?" Ya jefa mata tambayar,wanda ita tuni taci gaba da cin kifinta,ta daga kai suka hada ido


"Dearrrr.....ka bari na gama tukunna,ban qoshi ba Allah" shuru ya danyi yana ci gaba da kallonta,kafin ya miqe yana zare kayan jikinsa saboda wanka da yakeson shiga.


            Tun daga shirinsa zuwa zaman cin abincinsa da shirin kwanciya baccin da sukayi ta lura kamar kuzarinsa ya ragu,da tayi complain sai yace


"Yau nayi overwork baby,jikina duka ciwo yakemin" tsam ta miqe,ta shiga kitchen ta hada masa ruwa me dumi,daga gefansa ta zauna ta miqa masa mug din


"Ga wannan kasha,yana sauke gajiya" kurba daya yayi ya miqa mata,saita langabe kai tana kallon fuskarsa


"Ai baka sha ba dear" kansa ya girgixa yana dan qaramin murmushi


"Cikina ya cika fa,ko kin manta abinci na gama ci yanzu?,ba space,hakanma is okay,thank you".


           A sanyaye ta sauka daga saman gadon,yadan bita da kallo sannan ya gyara zamansa sosai saman gadon yana dubanta


"Yauwa kafin ki fita kiban wancan briefcase din,ki dawo a kitchen din kizo ki gani" miqa masan tayi taje ta ajjiye mug din a kitchen din sannan ta dawo,ta zauna daga gefansa tana kallon takardun daya fito dasu.


           Biyu daga ciki ya zaro ya miqa mata,ta karba amma tana masa duban neman qarin bayani


"Wadan nan filayen ne da mukayi zamu siya ni dake,an gama cinikinsu kamar sauran,ga takardun ki saka hannu" a nutse ta karanta rubutun dake jikin takardan,kamar kullum kamar kuma ko wanne lokaci,duk sadda suka siya wata kadara tare dashi,maimakon sunansu su biyun sunanta yake sanyawa,tasha masa qorafin shi da ita duk daya ne,koda sunansa ya saka dinma ai babu laifi.


             Motsa bakinta tayi,yasan qorafin data saba zatayi masa,sai ya saki murmushi ya daga mata hannu


"Bazan fasa saka sunanki ba fa,karkiyi ma magana,don na saka sunanki sai meye?,komai dana mallaka naki ne fa,bare ni dake din mun riga mun zama abu daya,saka hannu kawai" ya fada yana miqa mata biro,cikin sanyin jiki tare da jinjina qauna soyayya da kuma fahimtar juna me zurfi dake tsakaninta da adam din ta yi signing da signature dinta,wata irin sign me matuqar kyau da tsari,ta miqa masa takardun tana cewa


"Allah yasa musu albarka.....ina alfahari da irin tunaninka da qoqarinka" ta fada tana jinjina kai,tsarin daya kawo musu naci gaba ita sam bata taba kawowa ranta tayi hakan ba,daga aurensu zuwa yanzu suna da filaye masu suna filaye da suka hada kudi suka siya masu yawan gaske,hakanan zunzurutun kudin dake join account dinsu dake maqare da kudin da suke zubawa duk wata daga cikin albashin kowannensu,wanda dashi suke saka ran amfani da filinsu da yafi kowanne girma su tayar da ginin katafaren kamfani.


            Murmushi yayi bayan ya mayar da takardan cikin takardunss,ya sanya hannunsa ya rungumeta tsam cikin jikinsa yana shaqar lallausan qamshinsa


"Ni yafi dacewa nayi wannan godiyar" saita kwantar da kanta saman qirjinsa tana sakin murmushi,zuciyarta fes,cike da zallar farinciki hadi da samun nutsuwa da cikakkiyar gamsuwa da kalar mijin da take da.


***********Tsaye tayi bayan gama wanke mata kan tana goge ruwan kan nata da qaramin towel don dake saman kanta wanda ke dauke da tambarin katafaren gurin gyaran kai da jiki na mata Thairaphy saloon and spa,zare towel din tayi ta ajjiye,afifa dake zaune tana duba wani magazine ta daga kai tana dubanta


"Ya dai"


"Kifi zanje nemowa,nan haka nasan ba za'a rasa ba" ta fada tana maida rolling Vail dinta saman gown din jikinta da hanzari, rufe magazine din afifa tayi tana kallonta


"Amma kinsan ba'a yi gyaran jikin ba ko?,karmu bata lokaci fa"


"Manta kawai,yanzu zan dawo" ta fada tana zaro key din motarta daga jakar,cikin sauri ta nufi qofa


"Bansan qaunar data shiga tsakaninki da kifi ba"


"Nima haka"ta bata amsa a qagauce,sai afifan ta bita da kallo,wani abu ya darsu a ranta, murmushi ya qwace mata tana jinjina kai


"Allah ameen"ta fada tana ci gaba da gyada kai kamar qadangaruwa,kafin muryar daya daga cikin ma'aikatan dake wajen ta katse mata tunani,ta miqe tana zare nata dankwalin,gashinta me cika da tsaho ya bayyana,ma'aikaciyar taja mata kujera ta zauna aka fara gyara mata nata gashin.


           Afifa na zaune daga saman kujerar tana karantar yadda saahar kema kifin wani irin ci,zargin dake ranta yana sake tabbatuwa,iya saninta da asaahar bame ciye ciye bace,hasalima ko yunwa zatayi mata meye bata yarda taci abinci a waje, especially idan wajen na jama'a ne kamar haka,tana da wani irin halayya dda dabi'a ta daban data banbanta data koww,batace mata komai ba har sai data gama,ta wanke hannunta da kyau ta sauke ajiyar zuciya hadi da murmushi tana kallon afifa,sai afifan ta tabe baki tana kau da kai


"Wanda yaci shi kadai dai shi kadai zai mutu" murmushi mai sauti ya kufcewa saahar,tasa hannu tana rufe bakinta


"Am sorry bestie,na manta gaba daya,gaskiya ban kyauta ba,but zan fanshi kaina,zan siyo miki wani harfa sai kinci kin ture" 


"Banso" ta fada tana jefa mata hararar wasa,cikin zuciyarta cike fal da wani irin farinciki kyakkyawa fata da kuma zato me qarfi akan saahar din.


              Awa biyu suka gama abinda sukeyi sukabar wajen suka wuce  zoo road gidansu afifa,tun cikin mota ta fara jin jikinta yayi laushi,kasala duka ta rufeta,ga wani yanayi da yake saukar mata kamar zazzabin cikin qashi.


              Afifa dake tuqi ta waiwayo ta kalli saahar din 


"Anci kifi anyi dam baki ya mutu" ta fada cikin salon tsokana,wannan ya bawa saahar damar muskutawa tana yatsina fuska


"Jikina me a mace kaman fever keson kamani"


"Ya salam......aiko mu qarasa gida nayi miki test na gani,amma me zai hada madam adam da maleria ma?" Fuska ta yatsina tana jin jikinta sosai babu dadi


"Ba wani test fa,kusan last two weeks ina jin hakan,ko aiki ma daurewa kawai nakeyi,nafi zaton maleria din na kwaso,kinsan munje wata ziyara da momee munyi kwana daya" tsaki afifa taja cikin ranta,yadda bata qaunar d'an matar haka uwarma,saidai ba yadda zatayi sun riga sun zama daya a yanzun,tunda suna auren 'yar uwarta kuma aminiyarta tun daga quruciya har zuwa girma,sai bata sake cewa saahar din komai ba,har zuwa sanda suka qaraso gidan.


           A harabar gidansu ta tsaida motar,saahar ta rigata fita ta wuce ciki,sai data kashe motar ta kulleta sannan tabi bayanta.


             Saman kujerar falo ta sami saahar din a zaune,ummi mahaifiyar afifa tsaye a kanta suna magana,matar data debo dukka kamannin Dr mamman girema,wanda ko ba'a gaya maka ba zaka fuskanci JINI DAYA ne ke yawo a jikinsu,ba zaka kirata da yayarsa ba,saboda shekarun dake kwance a jiki da fuskarta basu kai na dr mamman din ba,don haka zaifi dacewa ka bata matsayi na qanwarsa.


"Ki duba saahar afifa kafin ku shiga shiriritar taku" abinda ummi ta fada kenan tana wucewa kitchen.


            Dakin afifan da bashi da maraba dana saahar suka kwasa suka wuce,dukkansu tun kafin auren saahar ba zaka banbance dakin waccar da waccar cikin gidansu ba,kowacce tana iya amfani da dakin 'yar uwarta,ta kuma yi tasarrufi dashi yadda taga dama,har zuwa yanzun da duka dakunan afifa ke amfani dasu,duk da ita dinma ta kusa kaucewa tabar gaban iyayenta,don akwai kudin khalifa idress a kanta,akwai abinda ya kawo tsaikon sanya rana da mahaifin afifa ya roqa a daga masa,yanason kammaluwarsa kafin saka ranar.


            Kan yalwataccen gadon afifan saahar ta zube tana fidda iska daga bakinta,tana daga kwancen tana kallon afifa ta gama hada komai da zata buqata sannan ta kalleta


"Taso mu gani" miqewa tayi tana cire dankwalin kanta da takejin ya mata nauyi ta ajjiye a gefe 


"Amma da ki fara da yimin allura ta ko?"


"Waime?,allurar planning?" Kai ta gyada mata a kasalance,wani abu mai tauri yazo ya tsayawa afifa a wuya,ta allura ma take ana batun duba lafiyarta?,duk da hakan afifa ta shanye bacin ranta,don tasan zaiyi wuya idan ramin data ginawa adam din baiyi zuruf ya afka ba,don ba zatace ramin data ginawa saahar ba,domin a gareta ba rami bane wannan,abinda tayin dai dai yake da tudun muntsira data ja hannun saahar din ta kaita ba tare da ita kanta ta sani ba


"To madam biyayya vice's qauna,taso na fara duba lafiyarki tukunna,tunda itace gaba da komai" duk da jikinta ba dadi sai data saki qaramin murmushi ta girgiza kai,tabi qaramar robar da afifa ke miqa mata da kallo


"Me zanyi da wannan?"


"Fitsarinki nake buqata" dan kafe afifa tayi da kallo kamar me tunani,sai kuma tasa hannu ta karba ta shige toilet din afifan.



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[28/08, 5:18 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma


No comments