Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 35-36

 


Page 35




        Fuskarsa tadan canza kadan har hakan ya bayyana qarara


"Me kikayi dasu da yafi abinda yake gabanmu muhimmanci baby?" Kai ta yada gefe tana dan murmushi kadan,adam da gaske yake,so yake yaga tabbatuwar mafarkinsu,ya bawa abin muhimmanci qwarai da gaske fiye da yadda ita din ta bashi,kodon akwai banbancin muhalli gidaje da yanayin rayuwa da dukkaninsu suka fito daga ciki ne?,batason gaya masa Afifa ta arawa,don babu jituwa ko kadan tsakaninsu,don haka tace


"Wasu gyare gyare namu na mata nayi dasu" a tausashe ya kamo hannunta ya sanya cikin nashi yana duban qwayar idanunta


"Idan kikaji ana batun ready made to kece,ke din baki buqatar wata kwaskwarima ko sauran gyara,ko yaushe cikin kyau da daukan hankali kike baby,so please mu maida hankali mu tara abinda muka tara mu gabatar da qudurinmu kafin cikar shekarun da muka dibawa kanmu" kai ta gyada tana dubansa,zuciyarta na qara aminta dashi,ci gabansu yakeso da gasken gaske ita da dukkan abinda zasu zo nan gaba ta tsatsonta,akwai masoyi sama da haka a rayuwa?.


"In sha Allah,hakan bazai kuma faruwa ba" kai ya jinjina yana sakar mata murmushin nan nasa gami da gyada kansa.


             Suna shirin kwanciya ya saka hannunsa da sauri ya jawo locker din bedside dinsu ya ciro wani dan kati,sai ya fiddo idanunsa duka waje


"Kaiiiii!" Ya fada yana dafe kai,ta daga idanu tana dubansa sanda take zura santala santalan qafafunta cikin duvet


"Me?" Ta jefa masa tambayar tana kallon yadda ya dafe kai


"Yau ya kamata ace kinje allura,ni dake duka mun sha'afa" ya qarasa maganar yana ritsata da idanu jikinsa adan sanyaye,ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi,tadan juya qwayar idanunta sannan tace


"Shine duka hankalinka ya tashi haka?" Fuskarsa yadan sake hadi da qaramin murmushi sannan yace


"Banaso a samu matsalane baby"


"Matsala kuma?,kamar ba miji da mata ba?,kana tunanin duk babyn da zamu samu a yanzu ba zamu iya daukan nauyinsa ba?" Kansa ya girgixa a nutse ya maida katin saman drower din ya ajjiye yana duban idanunta


"Ba haka nake nufi ba.....amma kinsan komai yana da lokaci,kuma komai idan aka tsarashi yafi zuwa ta dadin rai" iska ta furzar daga bakinta tana dubansa,duk cikin tsarukan adam wannan ne kadai baiyi mata ba,wannan ne kadai takejin rawar zuciya da rashin tsaiwar hankalinta a kansa,har yau har kwanan gobe ta gaza sabawa,ta kasa jin gamsuwa da nutsuwa da hukuncin,duk kuwa da cewa ta gaza musanta masa ko qalubalantarsa,tasan koda tayi yunqurin hakan yana da tarin hujjojin da zai bata da zasu mamaye tunaninta


"Ko baka da wanann halin na tabbatar ina da gatan da bazan rasa komai ba" kansa ya fara girgizawa da sauri


"Noooo.....Allah ya kiyaye,ta yaya hakanma zata faru?,ya za'a yi nabarwa wasu hidimarki?,har abada,meye amfanina baby?,karki qara fadin hakan,inason na nunawa duniya ne i can make it happen,i can do it,we shall live happily,wannan din akwai lokaci na musamman dana tanadarwa zuwansa" kyawawan idanunta na saman fuskarsa tana dan lumshesu da budesu, zuciyar ta na bata mabanbantan ra'ayi,ta yaya zaka tsarawa kanka abinda Allah ne kadai yake da ikon tsarawa bawa?,ta buda baki a hankali zatace wani abu,sai yasa tafin hannunsa ya rufe tausasan labbanta yana girgiza kai,sannan daga bisani ya birkitota jikinsa yana lullubeta da soyayyarsa.


*_W A S H E G A R I_*


         Shirye take tsaf cikin wata lafiyayyar lafaya wadda ta kusan zame mata al'ada sanyatan,a duk sanda ta sakata din kuma sai kamanninta su canza,ka rasa fahimtar da wanne yare zata dangantata,wani irin kyau shigar take mata mai daukan hankali.


           Golden yellow ce da aka yiwa ado da brown color,dukkan takalmi jaka da dan kunne zuwa sarqa da tayi amfani dasu sunyi matuqar dacewa da shigar tata.


           A nutse suke takowa ita da adam din suna hira qasa qasa,sanye yake da joggers pants dogo har qasa da kuma wata shirt me gajeran hannu,hannunsa yana riqe da hand bag dinta,daya hannun nasa kuma yana riqe da key din motarta,cikin kulawa tamkar wani bodyguard dinta.


         Da kansa ya bude mata motar ta shiga ta zauna,sannan ya zagaya ya ajjiye mata hand bag din a kujerar me zaman banza,ya kuma durqusa saitin window din yana jifanta da wani narkakken kallo


"Karfe nawa zaki dawo?" Murmushin nan dake qarawa fuskarta kyau da daraja ta saki


"Zan iya kaiwa yammaci,inason na biya ta gidan momee" kai ya jinjina


"Banjin yau zan fita,inaso na huta,naso mu kasance tare,amma ba damuwa,da yammar ki zauna zan shigo gidan saimu wuce tare" kai ta jinjina masa,yayi kissing hannunsa ya hura mata iskar sannan yaja da baya,ta saki murmushi ta maida masa martani,ta kunna motar yaja baya ta tasheta ta fice a gidan a hankali.


          Ajiyar zuciya ta saki idanunta nakan titi,kwanya da zuciyarta gaba daya ba abinda take bita sai kyakkyawan xaman dake tsakaninta da adam,wani irin zama me cike da fahimtar juna qauna tausayi da zallar soyayya,iyakar zamansu na shekara biyu ba zata iya tuna ranar data bata masa rai ko ya bata mata ba,kullum ita dashi cikin tattalin junansu suke.


           Lallausan sautin wayarta ya katse mata tunaninta,ta dan dubi wayar kadan dake gefanta,sunan BESTIE A ya bayyana kan screen din wayar,ta saki murmushi har qaramin bakinta yana motsawa,ta miqa hannu ta daga wayar ta sakata a handsfree.


            "Zaki shigo kuwa?,ko oga adam ya hanaki?" Murmushi ya qwacewa Saahar


"Hooo afifa ta adam....."


"A'ah.....adam dai na saahar,bar wannan zancan" ta katsi numfashinta,da alamu batason zancan


"To shi kam baice komai ba,infact ma ina kan hanya,ina fatan kina gida baki wuce zoo road din ba"


"Eh bankai ga tafiya ba,daman yau sai dare nake da niyyar tafiya"


"Okay saina qaraso" daga haka ta gimtse wayar ta ajeta a gefe tana dora dukka hannuwanta kan sitiyarin ta dafeshi,ta sauke ajiyar zuciya sosai,tana mamakin irin wannan rashin jituwa tsakanin adam da afifan,ta sani adam yana tsananin sonta,yana kuma yin komai don ita da kuma girman qaunar da yake mata,yayin da afifa take challenging duk wani tsari ko shiri na adam din,komai nasa baiyi mata ba,bai kuma dace da tsari da kuma hasashen da takewa rayuwar saahar din ba,saidai dukkaninsu ta yiwa kowa uzuri,ta tabbatar dukkaninsu qaunarta a zukatansu ne ta kawo wannan sabanin a junansu.


            Tafiyar mintuna talatin kacal ta sadar da ita da shagari quaters,ta gangara layin dake shimfide da kwalta,gidajensa bisa tsarin da kana kallo kasan kusan dukka mazauna wajen suna da sukuni na rayuwa.


            Gida me lamba 0009 ta tsaida motarta ta danna horn,babu jimawa mai gadin gidan ya bayyana,ya kuma dage qofar gidan cikin gaggawa sakamakon gane motar da yayi,ya maida qofar ya rufe bayan shigewarta da sauri yabi bayanta.


            Duk da kasancewarsa ya fara manyanta amma hakan bai hanashi bude mata qofa ba yana fadin


"Barka da zuwa uwar dakina" yayi maganar yana dariya,ita dimma murmushi takeyi


"Baaba habu barka kadai,lallai yau nazo a sa'a,kamar kowa yana gidan ko?" Ta fada tana bin rumfar adana motocin dake gidan da kallo,wadda ke dauke da motocin uku na baqi,sauran kuma duka motar mai gidan da matar gidan ne


"Aikuwa duka basu jima da shigowa ba,sunzo alhaji dr ne" idanu ta fiddo adan rude


"Me ya samu abban?"


"Ba komai fa,jiya ne yadan kwana da zazzabi" da sauri ta fita a motar baaba habu ya kulle mata,ta bude jakarta ta cire kudi ta miqa masa


"Ayiwa iyali cefane" hannu biyu yasa ya karba yana kwarara mata godiya,bata tsaya saurarensa ba,don idan da sabo ta saba da godiyar baaba habu da bata qarewa.


"Allah ya tsareki ya kareki daga dukkan abunqi da kuma sharrin me sharri" ya furta yana juya kudin a hannunsa,ya jima baiga mutane masu kirki da karamci ba irin ahalin gidan Dr Mamman girema ba.


"maama" ta fada da hanzarinta sanda take shiga falon,saika dauka sun dauki wasu shekaru basu hadu ba,zallar kewa da kuma qaunar ganin mahaifiyarta ya bayyana muraran a muryarta,kiran kuwa ya iske matar har cikin kitchen dinta dake falon,tayi hanzarin daukar butar shayin data cika da zazzafan baqin tea wanda yasha hadin kayan qamshi masu kwantar da hankali ta fito tana cewa.


           Fara tasss kamar diyarta saahar din,doguwa ce itama,amma shekaru da girma sun sanyata tayi jiki,duk da bamai yawa bane amma ya hadiye tsahon nata kaf,saita shiga jerin sahun mata masu matsaikatan tsaho kamar saahar din,kallo daya zakayi mata kasan cewa ta zuba tashen kyau qwarai da gaske zamanin quruciya kamar yadda diyarta a yanzu take.


"Eheeennn....aifa saike saahar,bansan ranar girmanki ba" ta fada murmushi na fita a fuskarta.


         ?an?ameta tayi sosai kamar zata koma cikinta


"I miss you maama"


"Sakeni saahar,kayan ruwan zafi ne a hannuna" sakin nata tayi tana gaidata,sannan ta karbi kayan hannun nata suka jera zuwa falon Dr,cikin sakalci take qorafi


"Yanzun abba baiji dadi ba amma maama a rasa me gayamin,banda Allah ya kawoni?"


"Bafa wani ciwo bane,zazzabi ne da ciwon kai,kuma hakan baya rasa nasaba da stress da rashin hutu"


"Amma ya kamata zuwa yanzu abba ya zauna ya huta,me yake nema Allah yayi masa komai" dan kyabe baki maama tayi


"Naji su yasir na magana akai,ban sani ba ko yanzun zai yarda ya huta din" daidai lokacin da suke isowa qofar falon,maama na gaba saahar din tana biye da ita.


           Dattijon da duka duka shekarunsa ba zasu haura hamsin da takwas ba,zaune saman luntsuma luntsuman sofa's dake zagaye da qawataccen falon.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[25/08, 6:13 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 36



         Daga gefansa Aafiya ce durqushe saman qafafunta,matashiyar da suke sa'anni ita da sahar din,baqar fata mai haske gareta sabanin saahar dake fara tasss,saidai komai nasu kusan daya ne,kama daga tsahon da girman jiki,sanye cikin wasu gray material da aka yiwa dinkin riga da skert budaddu,tarkacen takardun abban take hadawa,daga daya hannun nasa kuma yaaya saifullah ne yake zare abun auna bugun zuciyar daya cusa qasan abun awon jinin daya nada a hannun abban,wannan kusan ba sabon abu bane,kusan duk bayan wani lokaci yana yima abban irin wannan gwajin,na hawan jini dana suger saboda kula da lafiyar abban,duk da bashi da komai daga jinin har sugar din,Allah ya bashi cikakkiyar lafiya.


           Daga saman daya sofa din kuma yaaya muhyiddeen ne zaune,gefansa yaaya zainul-abideen da suke kira da yaa zain,dukansu hira suke a tsakaninsu,fuskar kowa qunshe cikin walwala da farincikin dake nuna zallar sukunin rayuwa da kwanciyar hankali daya samu matsugunni cikin rayuwar kowannensu.


           Hawaye taji yadan tsatstsafo cikin idanunta,sai taji tayi missing gidan dama kowa da kowa,harda rayuwarta ta baya,ada ita keda wannan matsayin,ko yaushe tana daga gefan abban tana kula da buqatunsa,yanzu kuwa aure ya nesantata da komai dama kowa.


          A shagwabe ta qarasa shigowa falon,ta kuma isa gaban abban daya tarbeta da dukkan kulawa,abu na farko ta fara qorafi akan rashin sanin rashin lafiyarsa


"Jiya ne kawai amma kinga yadda suka sanyani gaba"


"Me zakizo kiyi to,bayan gamu duk munxo?" Yaaya zain ya fadi,duk da ya girmeta,infact itacema qarama,amma time to time sai ya dan xungureta sunyi fadan sako da sako.


         Baki ta tabe ashagwabe


"Ni kaina na sani da abbana kawai"


"Gaskiyarki auta ina bayanki" yaaya  muhyiddeen ya fada yana murmushi,ta waiwaya tana sake masa murmushi


"Yauwa yaaya na na kaina" yaaya saifullah ne baice komai ba kasancewarsa shine babba,sai ta waiwaya tana gaidashi bayan ta gaida abban tayi masa sannu da jiki,ta gaida kowa ta waiwaya ga Aafiya


"Babu ko maraba bestie"


"Goyaki kawai zanyi yanzun nan,shine abinda ya rage ki gane nayi murna da zuwanki" dariya duka falon aka saki,don tsakanin Aafiya da saahar babu me shiga.


           Shigowar saahar ya sake jinkirta tafiyar yayun nata,a nan suka sake sabon breakfast gaba dayansu,duk kowa ya cika cikinsa a gidansa kafin fitowarsa,basu watse sunbar falon ba sai kusan qarfe daya saura bayan abba Dr yasha maganinsa yadan kwanta.


            Suna isa dakin aafiya dake gidan ta fara warware lafayar jikinta gami da warware agogon dake daure a tsintsiyar hannunta


"Bestie....bari nayi alwala nazo ki gyaramin kaina don Allah,ya dameni wallahi kwana biyun nan" idanu Aafiya ta fiddo


"Hala kin manta santsi da tsahon gashinki,sai yaushe zamu gama aikinsa" karyar da wuya tayi


"Haba mana bestie....."ta fada a karye


"Ya na iya dake,ina hutun sallah,idan kin fito sai muyi" Aafiya tayi maganar tana nutsewa cikin sofa din dakin gami da jan wayarta ta soma dannawa.


          Tana idar da sallah Aafiya ta fara gyara matan,tanayi suna taba hira,abunda ya daukesu mai tsaho,sanda suka gama data duba agogo saita fidda idanu waje,ita da zataje asibiti allura?,lokaci ya qure tasan yanzun haka nurse din dake mata allurar ta tashi,batason kuma yauma su sake missing allurar kamar jiya,ta fuskanci hankalin adam bazai kwanta ba sai ta tabbatar masa tayin


"Bestie taimaka kiyimin allura mana" sosai ta waiwayo tana duban saahar


"Allura?,baki da lafiya ne?" Aafiya ta jefa mata tambayar dai dai sanda take amsar allurar daga hannun saahar.


            Juya allurar ta fara yi tana kuma qoqarin karantar allurar meye,dukka idanunta ta fitar waje,cikin mugun gigita ta watsasu kan fuskar saahar


"Wannan allurar kice?,ko acan pharmacy din sukayi mistake din baki ita?"


           Janye idanunta saahar din tayi daga kallon tuhumar da Aafiya keyi mata,bayan ta tsareta da dukkan kallo na idanu da kuma kunnuwanta,sam ta sha'afa cewa wani babban sirri ne,sirri ne da suka tsarashi tsakaninta da adam,bata tunani duk duniya akwai mahaluqin da yasan da wannan babban sirrin idan ka dauke  mommee din adam din


"Allurar planning bestie?,tun yaushe kika fara?" Aafiya ta jefawa saahar tambayar tana tsareta da dukkan wani kallo dazai nunawa dan adam tsantsar tuhumar da ake masa mai tsananin qarfi da kaifi.


            Shuru saahar tayiwa Aafiya ba tare data amsa mata ba,yayin da Aafiya taci gaba da tsareta da kallon tana jin wani daci yana ratsata har saman harshenta,kwanyarta ta cika da nau'ikan tani iri daban daban,zuciya nata yi mata hasashe kala kala.


          Tasan saahar sosai har fiye da yunwar cikinta,shurun da tayi yana tabbatar mata da cewa batayi shirin amsa mata tambayarta ba,kuma muddin ta kafe akan abu,la shakka bata isa ya juyata kota sauya mata ra'ayi ba,don haka ta kwantanta yin barazana gareta ko zata samu taji bayanan da zuciyarta keda muradin ji daga bakin 'yar uwartata. Wannan ya sanya ta miqe tsam da allurar a hannunta tayi qofar fita a dakin.


          Cikin wani irin zafin nama da dukkaninsu basusan saahar din tana dashi ba ta miqe,cikin matuqar sa'a ta samu nasarar cafkar hannun Aafiya


"Ina zaki?" Waiwayowa tayi ta watsa mata wani kallo


"Zanje na nunawa maama da abba abinda kike aikatawa kanki"


"Baki da hankali ne?"


"Nice bani da hankali ko kuma kece saahar?" Ta kirayi sunanta kai tsaye abinda ba kasafai take yinsa ba.


          Ta fahimci Aafiya takai qololuwar fushi,kuma bata da sauran zabi illa ta gaya mata abinda take da buqatar ji din


"Zauna sai muyi magana a nutse"


"Bazan zauna ba har saikin gayan komai,yaushe kika fara wannan allurar,keda ko bari baki taba yiba tsahon shekara biyu da aurenki,muna nan munata addu'ar ganin qwanki a duniya?"


"Satin farko na aurena" sosai maganar ta daki Aafiya,har sai data dan ja baya kadan,to amma tana buqatar samun cikakken qarin bayani daga bakin saahar din don ta samu makama


"Satin farko kuma?,shi adam din ya sani ko munafuntarsa kike?" Gyara zama tayi tana jin tambayoyin Aafiya sunkai mata ko ina,ta gaji da jera mata tambayoyin da taketa faman yi


"Kin fiya takura da zaqule zaqule,xama mukayi mukayi shawara muka yanke hakan ni dashi,duka duka saura watanni kadan watannin da muka diba su cika na dainayin allurar gaba daya,so please don Allah banason kowa yaji zancan nan,tunda dai mun kusa kammalawa".


             Tashin hankali sosai ya shigi Aafiya,ita da tayi karatun lafiya tasan illar da hakan zai iya haifarwa da saahar,ta sani.....saahar ta saya ne kawai,ba zancan tare da adam sukayi shawarar aikata hakan,tunda duk mahaluqin daya kwana ya tashi yasan saahar din mada mugun son yara kamar me,tana iya yin komai saboda yara,tana kuma iya barin komai saboda yara,naturally ma akan ce dukka wani ko wata auta suna da son yara,to na saahar har ya wuce misali,abun kamar cikin jininta ne,ada maama ta dauka iya na quruciya ne,saidai har girmanta har zuwa aurenta abun yana nan tare da ita,to ta yaya koda dukka jikinta kunne ne zata amince saahar zatayi planning bisa radin kanta?.


          To amma koma meye a yanzun tashin hankali ba nata bane,idan illa take gudarwa saahar kome meye zuwa yanzu allurar ta dade dayi mata,fada tashin hankali da masifa ta tabbatar ba zasuyi tasirin komai ba,ta sauke ajiyar zuciya bayan dabara ta fado mata,ta dawo a hankali jiki a sanyaye ta zauna daga gefan saahar,ta kamo dukka hannuwanta ta sanya a nata


"Idan wani ya fahimceku bestie wani bazai fahimceku ba,idan wani bai zagi adam ba wani zai zageshi,don me kina da buqatar irin wannan allurar kinsan zan iya yi miki amma baki nemana nayi miki asirinku a rufe basai sun fallasa sirrinku ba?" Sosai maganar ta bawa saahar mamaki a yadda tasan hali da dabi'ar Aafiyan tata,ta kafeta da idanu,wani sashe na zuciyarta ta gaza gasgata zancan afiyan,wani bangaren kuma na gasgatata,tunda ita din kaifi daya ce,bata qarya don a sota,hakanan duk yadda magana takai ga rashin yi maka dadi zata gayamaka ita muddin dai gaskiya ce.


             Hannuwanta ta kamo cikin son gamsar da saahar din tayi yadda takeso


"Wannan din sirrinku ne,kuma sai amintaccenku ya kamata ya sani,tashi nayi miki" ta qarashe maganar tana sakin hannayen saahar din,ta soma zuqe ruwan allurar cikin syringe tana mita


"Shekara biyu amma bestie ace kina da wani sirri da kike boyemin,duk yadda muke dake,na sake yarda adam ya shiga tsakaninmu" sai zuwa sannan tadan saki murmushi,idan da sabo ta saba jin wannan tababar da suke akan juna,aafiya na qorafi akan adam koda yaushe,kamar yadda adam ke qorafi akan aafiya,batasan yadda zata hada kawunansu su fuskanci juna ba.


          "Next month idan kin tashi zuwa ki sameni a asibiti,don banason maama ta gani ta tambayi ba'asin yin allurar"


"Wai meye ya sanyaki saukowa haka da wuri bestie?" Saahar ta jefawa aafiya tambayar da tun dazun take cin zuciyarta,ta kuma shiga cikin kokwanto


"Saboda inason abinda bestie na takeso,kinason adam,kinason duk abinda yakeso,ni kuma inason bestie na,kuma dole na tayata son duk abinda takeso muddin da gasken ina sonta"ta amsa mata kai tsaye idanunta cikin qwayar idanun saahar.


          Janye idanunta tayi daga na Aafiyan tana son gamsar da kanta da gasken aafiya take,don ita din kaifi daya ce,dadi ko wuya basa sakata canza ra'ayinta.


               Tana jin kamar kada ta tafi tabar gidan saboda tsananin sabo da kuma soyayyar dake tsakaninta da familyn ta,amma dole qarfe uku da rabi ta yiwa maama sallama 


"Da wuri haka bestie?" Aafiya ta tambayeta sanda ta isketa tsaye a falo bayan shigarta kitchen kenan ta hada musu banana smoothie


"Munyi da adam zai sameni gidan momee da yammar nan,daga can saimu wuce gida" tabe baki Aafiyan tayi


"Ya kamata,muje na taka miki"


"To bani smoothie din na shanye mana kafin na tafi,kinsan akwai amana tsakanina dashi"


"Na zaci ai sauri bazai barki kisha ba" qaramin murmushi kawai saahar din ta saki,batasan me yasa duk Wani abu daya shafi adam ba aafiya bata maraba dashi,zuwanta daya tsahon shekara biyun nan gidansu adam din,ta kuma yimata rakiya da qyar,bayan sun fito kuma tayi shuru cikin mota kamar wadda ruwa ya shanye


"Yadai bestie?"


"Mamar adam din nan sam bata yimin ba,wai yaushe ta fara sonki ne bestie?" Aafiyan ta jefawa saahar dake driving tambaya.


            Dan qaramin bakinta ta bude cikin alamun mamaki sannan ta bushe da dariya,ta san halin Aafiya ba kowanne mutum bane yake mata a karon farko


"Ni banga aibun momee ba,bata da matsala,tana daukata kamar wata qawarta,bata taba takuramin ba,hasalima bata iya boyen duk wata damuwarta,so kuma ni dama bata taba nunamin qiyayya ba"


"K'nnnnn,haka ne" Aafiya ta fada a taqaice tana jawo wasu takardu dake ajjiye gaban motar sahar din ta tara dubawa,shuru ya ratsa motar kafin ta sake dago kai


"Waye zai bude joint account kuma?"


"Adam ne ya karbosu,bai gayan na waye ba yace na ajjiye masa kawai" saita gyada kai ta maida takardun da ba'a kai ga cikewa ba inda ta daukosu,ta gyara zamanta tana dauko wata hirar daban.


           Har bakin mota Aafiya ta rakota,saahar tanata mita


"Wallahi wallahi kin bani mamaki,ban taba zaton aure zai nesantamu ba,tsahon shekara biyu cur amma zan iya irga zuwanki gidana da yatsun hannuna?,wanne laifi mukayi miki?,tun adam na min qorafi har ya koma gorantamin kan cewa baki damu dani ba,ni daya na damu dake,ko yaa zain da yake namiji ya fiki zuwa gida na fa" qaramin murmushi Aafiya ta sake


"Ke kuma sai kika yarda da zancan adam?,ki rabu dashi so yake ya hadamu,aiki bestie kema kin sani,amma na miki alqawarin zuwa in sha Allah ending next month" hannu kawai saahar ta sanya tana rufe qofar motarta


"Kice kawai baki shirya zuwa ba,basai kin fitomin ta haka ba"


"Seriouse,Allah da gaske nake miki" ta fada tana dariya bayan taja ta bata hanya,tana nan tsaye har saahar dake galla mata harara ta mirror din motar ta fice daga gidan,Aafiya ta saki ajiyar zuciya sannan ta juya a hankali tana komawa cikin gidan.


             Minti ashirin kacal suka kaita unguwar sharada. Saboda ta danyi gudu ba laifi,bataso taje ta samu adam ya isa yana jiranta.


              A farfajiyar gidan ta tsaida motarta ta kasheta ta fito,ta fara takawa cikin nutsuwa da takuntan nan zuwa cikin gidan tana gyara laffayarta.


              Gab da zata qarasa qofar da zata sadata da ainihin falon gidan mata biyu suka fito,daya a gaba daya a baya,sai tadanja da baya ta tsaya don basu damar wucewa.



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[25/08, 6:13 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma

No comments