Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 33-34

 


Page 34




******Tamkar wadda aka yiwa dukan tsiya haka take dawowa cikin dakin,duk wani karsashi data fita dashi babu shi afifa sam bata lura da sauyin yanayinta ba,saboda lokacin da ta dawo din tana amsa waya ne,tana gamawa kuma ta dora mata da hirar da sukeyi dazun kafin ya fita


"Epilepsy duk bahaushen asali yana mata kallon farfadiya,ciwon da aka dangantashi da aljanu,amma kuma mu a likitance ba aikin aljanu bane,aikin daga gazawar qwaqwalwa ne,na gaya miki dalilan dazu da irin yadda akeson a basu kulawa.....yanzu kuma bari kiga w......" Maqale mata maganar tayi,saboda waiwayowa da tayi taga sãahar din dafe da kanta hannu bibbiyu. Da sauri ta ajjiye system din hannunta dake dauke da zanen qwaqwalwa ta nufi sãahar din


"Me yake faruwa?,kin fita lafiya kuma saiki dawomin a haka?" Ta fada tana dafa kafadarta. Kanta ta dago da idanunta da suka cika da qwalla,cikin matuqar sarewa da mutuwar jiki tace


"Inajin kamar na fara gajiya da rayuwar nan"


"Me kuma ya faru haka ana zaune qalau?,ko yaa muhyi dinne?" Kai ta gyada tana sharce qwallar data ziraro mata


"Shine,yana maganar na sake duba akan hukuncin ajjiye aikina,ni kuma wallahi Allah afifa bazan taba iya sake taka kamfanin MT jarma da sunan ma'aikaciya ba,bazan iya daukan cin fuska ko cin kashi daga gurin kowanne d'a namiji ba a yanzu,na fuskanci iya abinda zan iya dauka,ina buqatar nutsuwa,inason nayi nesa daga dukkan wani namiji da abinda ya danganceshi,wai har kun manta da irin abinda na fuskanta ne?" Kai afifa ta girgiza,ta kama hannuwan sãahar din dukka biyun


"Cool down mana bestie,taya zamu manta da wadan nan baqaqen ranakun a rayuwarmu?,yaa muhyi ba cewa yayi ki koma ba lallai,cewa yayi kiyi tunani, kina iya cewa ba zaki iya komawa ba ya baki uzuri,na tabbatar bazai sake cewa komai ba,please kada ki ja ciwon kanki ya tashi,calm down bestie" kai ta jinjina tana jin sassauci natsuwa na saukar mata kadan kadan,sai ta lumshe ido ta dafa hannun afifa


"Thank you for always being with me afifa" murmushi ta saki tana jin tausayi da qaunar 'yar uwarta


"Ba buqatar ki godemin,domin kamar na aikata dole na ne.....yanzu ki kwanta kawai,dare ya farayi,gobe zan qarasa miki bayanin" bata musawa afifan ba,don a yanzun itama ba abinda take buqata irin ta zauna silent ko hayaqin da takeji cikin kanta zai sauka.


            Ta kwanta ne kawai ta kuma rufe ido,amma duk wani motsi na afifa tana jinsa,har afifan ta gama abinda zatayi ta rage musu hasken fitilar dakin zuwa kala me duhu ta kwanta.


           Cikin duhun dakin idanunta keta walainiya,ba abinda ke gilmawa qwaqwalwata irin abinda ya faru da ita,rayuwarta ta baya data shude kamar zuwa da tafiyar ruwan sama,ta runtse idanunta da kyau tana girgiza kai,saboda bata shirya tuna irin wannan abun ba cikin daren daya fara nisa,saidai duk yadda takai ga toshe tunanin sai daya fara dawo mata da kansa.



*_WACECE SÃAHAR?,ME YA FARU DA ITA?,ku biyoni muje mu gani_*


*NAMIJI tabarmar k'ashi*


           Madaidaicin gida ne dake dauke da dakunan bacci manya guda biyu a qasa,da kuma mayalwacin parlor dake dauke da dukkan wani nau'i na kayayyakin da rayuwa ke buqata ga masu qarfi da kuma wadatar abun hannu.


               Qawataccen dining area da aka zubawa dining me kyau da daukar idanu na gilashi,da kuma qofar qawataccen kitchen din mamallakiyar gidan, kitchen din daya tara dukkan wani abu daya kamata ace akwaishi ga kitchen din diya mace.


         Tun daga manyan hotunan masu gidan dake manne a bango hudu na gidan kadai ya isa ya gaya maka irin gidan daka shigo,hotunane da aka daukesu bisa tsari da burgewa,gogewa da kuma sanin ilimin zamani,hotunan dake fallasa zallar soyayya qauna kulawa da kuma shaquwa tsantsa daga idanun mutanen da siffofinsu ke manne jikin taswirar.


           Duk da akwao banbancin siffa da kyau daga barayin mutumin dake jikin hoton zuwa ga matar dake tare dashi,amma wannan bazai zama cikas zuwa ga burgewar da zasu yiwa zuciyarka ba,hakanan bai zama cikas ga bayyanuwar soyayyar dake idanun kowannensu ba.


            Komai na falon a kammale yake a tsaftace hakanan a kintse,cikin wata irin tsafta kulawa da kuma sassanyan qamshin dake gauraye da sanyin ac din dake karakina cikin falon da kuma kewayensa,wani irin yanayi daka iya karyar da zuciyar dake da rauni,ya kuma bawa kowacce irin rai nutsuwa da gamsuwa.


              Daga saman gidan shima Parlor ne dauke da bedroom guda daya,saidai yafi dukka bedrooms din gidan girma da yalwa,shine kuma yake a mazaunin master bedroom,saidai shi parlor din baikai girman na qasa ba,saidai yana da jan hankali da alatu sosai har kamar ma yaso yafi falon qasan,hakan kuma baya rasa nasaba da kasancewarsa falon me gidan,wanda daga shi sai matarsa ke mu'amalantar sa.


           Cikin daya daga cikin bedrooms na gidan,dakin baccin dake da wani irin tsari da aka shiryashi cikin unique colors,qofa guda daya tal dake cikin dakin baccin ta bude a hankali.


         Sambaleliyar matashiya ce ta fito,doguwa mai matsakaicin tsaho,murjajjen jikin da ya hana bayyanuwar tsahonta,ya sanya tsahon ya zamana ado a gareta,fara ce sol farin dake da surki surkin ja a cakude dashi.


           Sassalkar sumar kanta mai tsaho santsi da kuma cika kadai ta isa ta gaya maka cewa ita din ba BAHAUSHIYA bace,saidai wani yaren daga cikin yarukan da Allah ya albarkaci qasata nigeria dasu.


            Kai tsaye zaka iya kiranta da KYAKKYAWA cikin mata dake da kyau a ajin farko,wani baiwar kyau da Allah ya bata tun tana ciki zuwa isowarta duniya,kyan dake iya zama barazana ga rayuwar diya macen da bata samu kyakkyawar tarbiyya ba,ko bata hadu da iyayen qwarai ba,wani irin kyau mai sanyi da tsayawa a rai,wanda ya cakuda da tsafta iya kulawa da kai da kuma gayu sannan ilimi ya hada dukkansu yayi masa ado na musamman.


           Towel ne kawai daure a qirjinta,cikin wata irin nutsuwa take takowa har ta iso gaban makeken mudubinta,har ta miqa hannu zata dauki daya daga cikin tsadaddun mayukan shafawarta saita fasa,ta daga kai tana kallon agogon bangon dake manne saman mudubin wanda yayi wata qaramar qara dake nuna awa guda cif ta cika.


         Zagayayyun fararen idanunta ta janye daga kan agogon cike da mamaki,saita dauki man ta bude,ta dan tsaya tana dubansa kamar yaune rana ta farko data fara ganinsa,ba zata iya tuna when last da ta bari man shafawarta ya qare ba,hakan yana nufin dole gobe taje shopping kenan,saita lakaci man ta fara shafe lafiyayyar fatarta cikin hanzari,tana yi tana duban wayarta dake ajjiye a gefe.


            Kasa daurewa tayi,gani takeyi kamar ta kasa saurin da ya kamata ace tayin,ta jawo wayar tana loda wasu numbers dake alamta ta jima da haddace su,suka cika cif ta danna kira,SOULMATE sunan ya bayyana baro baro kan screen din wayar tata.


              User busy ta saka mata,mamaki ya kamata,ta sake maimaita kiran aka sake sanar mata ana amfani da layin,saita aje wayar kawai ta mayar da hankalinta kacokam akan shiryawar da takeyi din,saidai can qasan zuciyarta bata daina mamakin wasu abubuwa da take gani cikin satin nan ba,wanda kai tsaye zata iya kiransu da BA?IN ABUBUWA.


           Kamar ko yaushe ta shirya tsaf cikin wata lafiyayyar rigar bacci da ta saka kudi masu nauyi ta siya duk don saboda ta burge mijin nata,masoyin da duk duniya idan ka dauke iyaye da kuma AFIFA bata da kamarshi,tayi checking kanta da kanta ta tabbatar komai yayi fiye da yadda ADAM keson ganinta a kowanne dare,saita saki qaramin murmushin da ya sanya dimple din dake dukka kumatunta lobawa,ta kawo qaramin baby hijab ta saka,sannan ta dauki wayarta laptop da sauran wasu tarkace da takeson dubawa na sauran aikin office da bata qarasa ba,ta zura slippers a qafarta ta fito.


             Sai data kashe kowanne qwai da sauran kayan electronics dake aiki a qasan sannan ta haura saman cikin takun nan nata kamar tafiyar wahainiya,wanda ya zame mata halitta cikin jininta yake.


           Ba kowa a falon,sai butar shayin data barshi yana sha a dazun da sautan cups da suka bata,dukka sai data killacesu sannan ta dawo zuwa babbar qofar da zaga sadata da bedroom din nasa,tana mamakin yadda akayi duk motsinta na yau baiji ba.


              Da sallama a bakinta ta tura qofar,yana zaune sosai saman lafiyayyen gadon,ya jingina bayansa da fuskar gadon,saman cinyarsa kuwa na'urar laptop ce daya zubawa dukkanin idanunsa,yakuma bata hankalinsa dari bisa dari,koma me yakeyi da alama yaja hankalinsa matuqa.


             Sautin muryarta ya sanyashi daga kai a hankali ya watsa mata manyan idanunsa,sai ya fidda qaramin murmushi daga labbansa idanunsa nadan lumshewa saboda yadda ta dauki hankalinsa,har yaji ma komai ya fita daga kansa,shi kansa yasan Allah yayi masa baiwar kyakkyawar mace,Allah ya bashi macen da yasan qarfin ikonsa ko wani qoqarinsa.... dukiyarsa ko iliminsa,wayo da dabara dukka basu isa su bashi SÃAHAR ba face tsananin rabo da kuma irin sa'arsa,wadda tunda ya fara gwagwarmaya a rayuwarsa ya fahimci shi din me sa'ar ne.


            Kyawawan idanunta masu zubin gold ta narke masa tana kallonsa cikin salon kallon tuhuma,takuma maqale kafadarta tana kebe baki,sai ya daga hannayensa dukka biyun sama


"Am sorry baby" saita sake kafadarta ta fara takowar saidai har yanzu bata saki fuskarta ba.


             Kai tsaye tayi qoqarin shigewa jikinsa sanda ta iso abinda zai zata ba,tana shigewar ne tare da qoqarin kai idanunta kan allon computer dinsa,saidai tun kafin kwanyarta ta gama tantance komai ya saka daya hannun ya rufe system din ba tare daya kasheta ba,yasa daya hannun kuma ya riqota cikin jikinsa sosai yana jifanta da wani irin kallo


"Bansan lokaci ya tafi har haka ba baby" ya qarasa maganar yana kissing goshinta,a shagwabe tace dashi da muryarta dake da wani irin zaqi da taushi


"Duka cikin satin nan haka kake mun,bansan yaushe na koyi bata lokaci akan computer da waya ba...... nidai ka gayamin,ko wata ka samo?". Tsam ya janyeta daga jikinsa yana duban qwayar idanunta,yanayin fuskarsa ya canza daga walwala zuwa wani yanayi na daban,idanunsu suka sarqe waje daya,sai ya girgiza mata kai


"Banason na qara jin wannan kalmar daga bakinki,ina dake ta yaya idanuwana zasu iya ganomin wata macen?,kinsan matsayinki a raina kuwa?,kinsan yadda kike a zuciyata?,beside ma.....mu da muke qoqarin ganin munkai rayuwarmu wani mataki na kwatance......ina nake da lokacin da zan kalli wata diya mace?,wai kina tunanin a duniya ma akwai macen data kai kyanki kuwa?" Kanta ta cusa a qirjinsa dariya tana subuce mata,a duk sanda adam yake gaya mata irin wadan nan kalaman,tana jin kanta acan qololuwar sama,tana jin duk duniya babu macen da ta kaita sa'a,babu macen da tayi dacen mijin qwarai kamarta,tana jin cewa zata iya tsayawa takarar macen da tafi kowacce mace sa'ar miji a duk fadin duniya,zuciyarta kuma na sake nutsewa cikin shauqin son adam da kuma qara amincewa dashi da kuma sallama masa rayuwarta gangar jikinta dama komai data mallaka.


           Saman kanta ya dora nasa kan yana shafa sumarta da yake matuqar so yana kuma sake fito mata da abinda yake zuciyarsa a kanta,tayi shuru tana saurarensa,kowacce gaba ta jikinta tana saki cikin zallar shauqin so.


           Sun jima a haka kafin ya umarceta ta bashi ruwa a parlor,ta sauka a hankali ta fice tana takawa tana jinta kamar tana yawo a gajimare,yayin da shi kuma ya bita da kallo,yana jin sha'awarta na sake fusgarsa da wani irin shauqi a kanta.


             Kafin ta dawo ya kashe system din yama yi ready din kwanciya,ta hauro gadon ta tsiyaya ruwan ta miqa masa.


             Sai daya kammala sha sannan ya bata cup din yana cewa


"Wannan watan ya akayi salary dinku yayi delay?" Maida cup din tayi ta ajjiye,sanna ta juyo gunsa


"Sun shigo fa tun kwana uku,kawai na dan ari kudin ne na siya wasu abubuwa dasu,amma gobe nake sa ran zan tura main account din gaba daya".



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[24/08, 1:41 pm] +234 902 488 9500: *H U G U M A*

No comments